Kannywood News

Ni kadai nasan wahalar da na sha aure na da Sani Danja inji Mansura Isah

Ni kadai nasan wahalar da na sha aure na da Sani Danja inji Mansura Isah

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Mansurah Isah, ta yi bayani mai ɗan tsawo kuma kai-tsaye dangane da mutuwar auren ta da fitaccen jarumi kuma mawaƙi Sani Musa Danja, inda ta bayyana cewa ita kaɗai ta san wahalar da ta sha a zaman ta da shi.

 

 

 

Haka kuma Mansura Isah ta ce rabuwar su ba ta sanya ta ɗauke shi a matsayin abokin gaba ba.

 

 

 

A wata hira da aka yi da Mansura Isah din a jaridar Daily Trust, wadda aka buga a yau, Mansurah ta ce wahalar da ta sha, ko wani abokin gabar ta ko ‘ya’yan shi ba za ta yi fatan su sha irin ta ba.

 

 

 

A hirar, wadda mujallar Fim ta fassaro, tsohuwar jarumar wato (Mansura Isah) ta ce mutane da ba su san halin da ta shiga a auren ta ba sun yi ta gaya mata baƙaƙen maganganu a lokacin da auren ya mutu.

 

 

 

 

 

Mansura Isah ta ce: “Mutane sun yi ta gaya mani magana a soshiyal midiya, da sauran kalamai na ɓatanci. Amma tuni na ci gaba da rayuwa ta”.

 

Kuma ta yi nuni da cewa, “Idan mace na shan wahala a gidan auren ta kuma ta yi shiru ba ta faɗa wa kowa ba, to idan ta mutu a ƙarshe sai mutane su ce me ya sa ba ta yi magana ba.

Mansura Isah taja Allah ya isakan mutuwar aurenta

Idan kuma ta buɗe baki ta yi magana ta nemi haƙƙin ta wanda har ya kai ga an sake ta, sai kuma mutane su koma su ɗora mata laifi. Hatta waɗanda ba su yi auren ba sai su riƙa gaya mata magana. Duk irin wannan ya faru a kai na”.

 

 

 

 

A kan batun ganin ta da aka yi da Sani a wajen fara haska fim ɗin ta mai suna ‘Fanan’ a gidan sinima kwanan baya a Kano, Mansurah ta faɗa wa jaridar cewa to ai tsohon mijin nata ba abokin gabar ta ba ne.

 

 

 

 

Mansura ta ce, “Ni ban ga wani laifi a ciki ba. Shi ne uban ‘ya’ya na, kuma aboki na ne sannan abokin aiki. Saboda haka na kasa gane abin da ya sa mutane su ke wannan maganar. Mu na cikin rayuwar zamani ne yanzu; don mun rabu ba ya nufin mu na gaba ne.”

Leave a Comment

error: Content is protected !!