Hausa Novels

Ni na raineta Hausa Novel

Ni na raineta Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*NI NA RAINETA*

 

*©M…*

 

 

*FCWA*

 

*Bismillahi rahamanir raheem*

 

 

1️⃣

 

 

 

“Wannan kwalliyar ai dole ki kasance ke kaɗai a wajen Abba, wallahi Amma kin yi kyau” cewar Tasleem tana kashe min ido ɗaya cikin dariyar shaƙiyanci, na rarumi pillown da ke kan kujera na jefa mata cikin dariya na ce “ja’ira mara kunyar yarinya” na shige hanyar da za ta sada ni da sashen Alhaji cikin takuna ɗagwas ɗagwas kamar budurwa, bakina ɗauke da sallama na tura ƙofar ɗakinsa, ban same shi a ciki ba sai dai na ji alamar shower da ke kunne wanda hakan ya tabbatar min yana banɗaki ne. Duk da komai na ɗakin yana nan tsaf da shi bai hana ni miƙewa ba na ƙara ƙalƙale wajen tare da jona burner na ƙara turaren wuta, gudun AC na ƙara sannan na nufi gado, hannuna na miƙa na ɗauki wayarsa da ke kan gadon na latsa don duba lokaci, Alhaji da ya fito daga wanka ya yi hanzarin isowa gareni ya amshi wayarsa ya ce “wai ba ni da halin ajiye waya sai kin taɓa Hadiza?”

 

Na taɓe baki na ce “lokaci na duba” ban kawo komai a raina ba duk da password ɗin da ya maƙala wa wayar tasa da bai taɓa sawa ba tsayin lokacin da muka ɗauka tare, sama da shekara ashirin a inuwar aure.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Abinci na gabatar masa marar nauyi ya tsakuri abin da zai tsakura ya miƙe yana faɗin “wallahi cikina a cunkushe yake,ɗan sa Inya ta dafa min shayi”

 

“Bari na dafa maka, Inya yanzu ai ina jin karatu take yi” na ce ina miƙewa.

 

“A’a Hajiyata kira ta a waya ki ce ta dafa min shayi ta kawo min, ke zauna a nan na kalli wannan kwalliyar da aka yi min na more” ya ce yana ɗaga min gira. Na yi murmushi na ce “an gama ranka ya daɗe” na ɗaga waya na saka Inya ta dafa shayin ta kawo min. Na juya ga Alhaji ina jin daɗin yadda soyayyarmu har yau bayan mun hayayyafa take nan kamar ta saurayi da budurwa. Hira muka shiga yi ta abin da yake faruwa a ƙasar har Inya ta shigo, sanye da sabuwar doguwar rigar da na siya musu ɗazu ita da Tasleem, ta ɓoye dogon gashinta cikin hula sai doguwar jelar da ta kitse da ke ta reto a ƙasan wuyanta, hannunta ɗauke da tray wanda aka ɗora flask ɗin shayi ƙarami na zamani da ƴan kofuna. Ta ɗora tray ɗin kan centre table ɗin da ke ɗakin tare da cewa “ga shi nan Amma”

 

“Na gode, Allah Ya yi miki albarka” na ce

 

“Ameen, sai da safenku” ta ce da murmushi ta yi waje.

 

Na dubi Alhaji da murmushi na ce “ga shayin da ka ɗauka ibada a kwanakin nan”

 

Ya yi ƴar dariya ya ce “yanzu na gane masa ne”. Hira ce ta kuma ɓarkewa a tsakaninmu kafin daga bisani muka koma ɗaki don kwanciya. Bayan na idar da addu’a na shafe jikina na dubi Alhaji da ya tsiri latse-latse a waya cikin ƴan kwanakin nan, na taɓe baki na ce “wai fisabilillahi me kake yi da waya ne duk dare yanzu”

 

Ya ɗago ya kalleni ya ce “Hadiza ai yanzu duk cinikayya ta koma ta yanar gizo, kuma kin ga ni ba wani samun lokaci nake da rana ba, yanzu nan muna magana ne da Basiru kan kayan da zai turo mini daga China”

 

“To Allah Ya taimaka” na ce ina gyara kwanciya, ya jima yana latse-latsensa kafin na ji kwanciyarsa a bayana yana rungumata, na yi murmushi kan yadda Alhaji sam ba ya gajiya da abu ɗaya kullum jin sa yake kamar sabon ango, sai da na sa ma masa nutsuwa sannan muka miƙe don tsarkake jikinmu, wayarsa da ke gefen pillownsa ta kawo haske idona ya kai kan screen ɗin,ban iya karantawa ba sai kalmar ƙarshe da na gani wani abu sannan aka ƙara da baby, Alhaji ya yi saurin ɗaukar wayar ya kashe bakiɗaya, jikina ya yi wani irin sanyi ƙalau na kasa motsa wa, ya ja siririn tsaki ya ce “yaron nan Basiru sam ba shi da hankali, bai son mutum na buƙatar hutu ba, yanzu fa muka gama magana da shi amma kin ga ya sake turon wani saƙo akan kaya.” Ya wuce hanyar toilet, na bi bayansa ina ƙaryata idanuwana da suka gane mini Baby, na tilasta wa zuciyata cewar Basiru idanuna suka gani, da wannan na samu na yaƙi zargin da ya so ya ɗarsu a zuciyata.

 

Assalatu na farko na tashi, sai dai ko da na tashi babu Alhaji babu dalilinsa, ba ɗabi’arsa ba ce tashi da wurwuri, wani lokacin ma sai na yi da gaske yake tashi, nauyin bacci garesa. Ƙarar famfo da na ji na ta zuba babu ƙaƙƙautawa sama da minti goma ya sa na nufi banɗakin da nake kyautata zaton Alhaji ne ke amfani da shi, ina ƙoƙarin buɗewa sai na ji kamar wanda yake magana da wani a ciki, na tura ƙofar na gansa tsaye da waya a kunne alamun waya yake, cikin daburcewa ya fara inda-inda tare da sauke wayar yana washe baki da cewa “ashe kin tashi, nima yanzu na tashi ba a yi ko minti biyar ba, Sagiru ya tasheni”

 

“Shi ne kake waya a banɗaki” na ce ina kallon yanayin da ya shiga na rikicewa.

 

“E, ai…” Ya fara sosa ƙeya daidai lokacin aka fara kiran sallah hakan ya sa ya ratsa ta gefena ya wuce da sauri, na bi bayansa da kallo ina mamakin wannan sabon sauyin da ya shigesa. Alwala na ɗaura zuciyata cike da tunannuka na nufi dadduma, na yi sallah, da na idar sai na tsinci kaina da kwararo addu’o’i ga mijina kan Allah Ya tsare min shi daga sharrin wannan zamani, ya kauda duk wani abu da zai shigo rayuwarmu wanda ba alheri ba, bayan na shafa na jawo Qur’ani na soma karantawa, da wannan na samu nutsuwar zuciya. Bayan na idar na rufe tare da miƙewa na nufi sashen yara don na faɗi abin da za a ɗora don na san sun tashi. Tasleem sam da asuba ba ta da mamora, duk yadda ka so ta yi maka aiki ba za ta yi ba, sai ta koma wannan baccin nata na ƙa’ida yayin da Inya kuma ba ta komawa bacci kamar Ni, sai an gama gyara gidan tass yara sun tafi makaranta ta karya sannan za ta koma, da sallama na tura ƙofar ɗakinsu Bahijja da Nadiya, sanye suke cikin kayan makaranta, Bahijja na duba littafi yayin da Nadia ke kwance kan gado tana bacci, “Amma ina kwana” cewar Bahijja.

 

Na yi murmushi na ce “lafiya lau, har kun yi wanka”

 

“E, yanzu na gama shirya Nadiya ta koma bacci” ta ce.

 

“Madalla, Allah Ya yi miki albarka, bari na saka Inya ta muku break fast” na ce ina ficewa.

 

Tura ƙofar ɗakin na yi da sallama, kamar yadda nake zato Tasleem na kwance ta koma bacci, yayin da Inya ke linke hijabi alamun wadda ta yi salla ce, da murmushi ta ce “Amma ina kwana?”

 

“Lafiya lau, kin tashi lafiya?”

 

“Lafiya lau” ta ce.

 

“Madalla, ki yi hanzarin ɗora doya da ƙwai don Allah kar ki bari yaran nan su makara” na ce ina ƙoƙarin fita.

 

“In sha Allah” ta ce.

 

Ko da na tura ƙofar ɗakin Alhaji gabana ne ya yanke ya faɗi dalilin ganinsa da na yi, ya yi ruf da ciki yana waya har wani shilla ƙafa yake alamun cike yake da shauƙin wayar.

 

“Da Basirun kake waya da safiyar nan?” Na ce muryata na kakkarwa.

 

Ya yi wata iriyar hantsilawa ya dira kan ƙafafunsa bayan ya kashe wayar yana sosa ƙeya ya ce…

 

 

*YA KUKA GA KAFCEN?*

 

 

#SHARE

 

 

 

Name: [My Novels (www.mynovels.com.ng)]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram



Powered by: www.mynovels.com.ng

3 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!