Ni’imatullah Hausa Novel Complete

Ni’imatullah Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Ni’imatullah Hausa Novel Complete

NI’IMATULLAH

 

 

 

BY HAAJARA ABLA

 

 

ANNURI WRITERS ASSOCIATION

(Annuri is the best).

 

 

Ina godiya ga Allah subahanahu wata’ala da ya bani ikon rubuta wanan littafi mai suna a sama ya ubangiji ka bani ikon isar da sak’on da nake son isarwa,ubangiji kasa mu amfana da abin da ke cikin sa…..

Ni'imatullah

*wanan labarin k’agaggen labari ne banyisa dan wani ko wata ba idan ka/ki labarin yaci karo da naki sai kiyi hakuri ki gafarceni Allah ya bamu ikon amfana da abinda zamu karanta.

 

 

 

 

Shafi na d’aya 1

 

Direct hotel d’in ta nufa bayan tayi parking d’in motar ta a gefe,room num 23 saida tahau lifta sanan ta sauka tayi wata ya’r tafiya sanan ta isa d’akin,knocking tayi kamar yadda ta saba haka akazo aka bud’e mata ta shia ciki aka rufo k’ofar.

Zama tayi a kujerar dake cikin bedroom d’in tareda cire mayafin ta ta ajjesa gefe inda ta wurgawa ahajin dake gefanta kallo yana ta murmushi da yak’e,wani kallo ta watsa masa da yakasa banbancewa na so ne ko kuma nak’i ne cikin kawar dawani tunani yace da ita”sannu da zuwa baby fatan kinzo lafiya?”

“Yawwa Alhaji lafiya kalau saidai nasha hanya inaso zanyi wanka sanan zanci abinci idan da dama zanyi bacci.”

“Babu matsala baby bari nasa a miki order mai zakici?”

“Abinda aka saba.”

“Ok babu damuwa lemme call them.”

Bata bashi amsa ba ta shige bathroom d’in ta sakarwa kanta shawa,cikin minti k’alilan ta kammalah wanka ta fito tayi alwala sanan ta tada sallah.

Ya saba da halin ta haka yayi zaman jiranta haka ta idar ta koma karatun al’qur’ani bayan tayi kamar awa d’aya tayi addu’a sanan ta juyo ta kallesa tare da tashi ta koma kan kujerar ta janyo table d’in gabanta tafara cin abincin sanan tace dashi”let eat together alhaji.” Cike da jin dad’i haka ya matsa kunerar datake ya fara cin abincin yana jin wani azababben dad’i yana shigar sa hak’ik’a yana mutuk’ar son NI’IMATULLAH komai nata na mussaman ne yana burgesa gata da addini amma ya rasa dalilinta na zama yar bariki kwararriya ma kuwa ya rasa dalilin hakan,cikin kawar da tunanin sa ya juya ya kalleta hankali kwance take cin abinci sanan yace”am baby inaso zamuyi magana dake kuma maganar mai mutuk’ar mahimmanci ce dan Allah inaso ki yarda da ita ki karb’eta hannu biyu biyu.”

“Ina jinka alhaji.”

“Yawwa NI’IMATULLAH daman inaso ki bani damane inaso zan aureki inaso ki bani dama ki kaini wajen iyayenki na nemi aura……. kafin ya k’arasa tini NI’IMATULLAH ta tashi tashak’o wuyansa idanuwanta sunyi cazur tuni zum janza laune dakyar murya a shake ta iya cewa aure ni zaka aura alhaji ni…..kafin ta k’arasa aituni ta zube inda shima Alhajin ya zube cike da tashin hankali dan Allah ne ya cecesa amma da tuni yau kwanan sa ya k’are wajen NI’IMATULLAH da gudu ya shiga band’aki ya kunnawa kansa shawa…

 

 

 

Tunani kala kala ne a zuciyaraa shi yama fara tunanin anya kuwa yarinyar nan ba aljana bace yanzu idan ba aljana ba tayaya ma akayi duk wanan girman nasa da k’arfi amma ta shak’esa kuma ya kasa komai Allah dai yasa ba aljana bace gaba d’aya tsoro ya kamasa haka ya fito daga ban d’akin ko ta kanta baibi ba ya kama gabansa ya fita yabar hotel d’in ma gaba d’aya…

See also  Tsautsayin Tauna Hausa Novel Complete

 

A cikin wanan halin NI’IMATULLAH ta wayi gari misalin k’arfe biyu narana tashi tayi gaba d’aya jikin ta yayi mata nauyi haka tayi wanka tayi sallolim dasuka wuce ta sanan ta karanta al’qur’aniyanda ya sawwak’a ta koma ta kwanta gaba d’aya jikin ta a sanyaye yake har sai yaushene zata samu nutsuwa har sai yaushe ne zata samu gata harsai yaushe abubuwan da suke faruwa da ita zasu zama tamkar tarihi ne… tana cikin tune tunann tane taji anyi knocking cewa tayi ya shigo mai saving food ne ya kawo mata haka ta tashi taci sanan ta koma ta kwanta aikuwa atake bacci ya d’auketa bata farka ba sai yamma. Tashi tayi tasake yin wanka tayi sallah sanan ta fito reception ta basau kud’in kwana d’aya ta zauna a wajen hotel d’in dan shan iska dan jinta kawai take sai a hankali…..

 

 

 

Tana zauneta zubawa shuke shuken wajen ido tana ta kalon yadda iska take kad’asu sunta lilo sosai ake iskar bata ankara ba kawai sai saukar ruwansama taji. “Washhh Allah ta fad’a a fli batakai ga rufe bakin taba wani matanshi yaro yayi mata rumfa da lema juyowa tayi ta kallesa sanan tace masa ta gode”karki damu basai Kinyi godiya ba ai kamar ki yadda Allah ya zuba miki kyu da zati da suru idan akace mu muga ruwa yana dukanki mu kyale ai sai a kamamu.”

Murmushi tayi a taka’ice sanan tace”nagode.”

Karki damu ko zan iya rakaki d’akin.”

Gaskiya aa.” Ta bashi amsa kai tsaye.

D’aga gira yayi ta yan duniya sanan yace mai yasa”kawai dai I’m not in the mood nagode zaka iya tafiya.”

“Ohhh banso na takura miki ba amma number fa.”

“I’m sorry ban fito dan raba number a arha har haka ba.”

“Sorry ta acc fa.”

“Ba laifi ta bashi amsa sanan ta karb’i wayar ta saka masa number acc nata nan take taga ya mata transfer na 50k. Sanan yace”tsayawa da mai kyu kamarki wanan yayi kad’an ma a tukuici.”

Murmushi ta sake masa sanan tace”gobe kazo NZ hotel room 0010 misali k’arfe shida na yamma if u are free u can come.”

Cike da jin dad’i yace”nagode nagode….

Zai tambayi sunan ta kenan ta d’aga masa hannu haka ya bata lemar ta juya har saida ya daina ganin ta sanan ya koma cikin motarsa yana murna yayi sabuwar kamu gata yarinyar sharaf.

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Komawa tayi ta kwanta ta d’auki wayar ta tafara chat misalin k’arfe goma kuma ta rufe wayar ta d’aukko ta bud’e app d’in da take shiga danyi typing na littafin novel….

 

 

Shiga tayi tafara dube dube labari take rubutawa amma gaba d’aya a wanan karon labarin baiyi ba sam tana da masoya sosai da sosai a zahiri da kuma bad’ini shaharriyar marubuciya ce tana rubutu cike da kwarewa da baiwa gashi tana da masoya sosai a wanan karon ta fara rubutu amma rubutun baya tafiya yanda mutane zasu so labarin yak’i tafiya yak’i yin dad’i ko kad’an wani tsaki taja sanan ta wurgar da wayar gefe taja dogon numfashi a fili tace ina buk’atar wanda zai tayani kwana…. bata b’ata lokaci ba wajen kiran abokin harkarta bai dau lokaci ba yazo nidai haajara na basu waje ina musu addu’ar shiriya….

See also  Yayana Zain Hausa Novel Free Pages

 

 

Washe gari da sassafe ta shirya ta hau motar ta ta nufi gida……

 

 

Daga alkalamin haajara abla.ku nuna min yanda kuka karb’i littafin ta hanyar comments dinku nagode haajara abla takuce

 

 

 

 

ANNURI WRITERS ASSOCIATION

(annuri is the best).

 

 

NI’IMATULLAH

 

 

 

 

By HAAJARA ABLA

 

 

 

 

 

HAK’IK’A NAJI DAD’I SOSAI DA ADDU’O’IN KU AGARENI INA KUMA MUTUKAR MIK’A GODIYA GA FANS D’INA A DUK INDA KUKE HAAJARA ABLA TAKUCE ONE LOVE

 

 

 

 

SHAFI NA BIYU 2

 

Cike da k’osawa da tafiyar datake a mota zuwa umguwar tasu,da yake unguwayce ta talakawa gabad’aya binta a mota bashi da dad’i,daga tayi karo da wancen dutsen sai wancen ramin haka ta k’araso har k’ofar gidan su sanye da hijab har k’asa a jikinta tana zuwa ta tarar malam baya kofar gida direct cikin gidan ta nufa…..

 

Baba jummai ce zaune bisa tabarma tana tankad’en garin masara zatayi tuwa inda murja take cikin d’akin ta ita da yaranta…

 

Sallama NI’IMATULLAH tayi ta shiga gidan kanta tsaye kamar dai wacce aka aketa taje ta dawo daga aiken hankalinta kwance. Zuwa tayi ta tsugunna ta gaida baba jummai dake zaune a tabarma. Amsawa tayi a wani shek’ek’e ta d’ago tana kallon ta sannan tafa magana kamar haka”wai har sai yaushe zaki canza iyeee sai yaushe zaki canza NI’IMATULLAH kullum kina hanyar yawo ko kunya bakya ji bazaki iya zaman gidan iyayen kiba ance ki fito da miji amma hakan ya gagara.”

D’agowq tayi da fuska inda atake idonta ya kad’a yayi jajur dakyar ta iya rusunawa ta daidaita nutsuwarta sanan ta fara magana kamar haka”kiyi hakuri dan Allah Baba insha Allah watarana sai labari insha Allah bazan sake ba…. kafin takai aya murja tayi wuf ta fito daga d’aki tana bud’a tana magana”ahayyye nanayee ai bayau muka saba jin haka daga gareki ba shegiya munafuka yar bariki karuwa wacce batasan ciwon kanta ba kinyi asarar hali gaki nan a fuska kamar mutuniyar arziki amma ta banza ce a haka dai haka za’a k’are.” Batare da NI’IMATULLAH ta juya ta kalletaba balle ma tasan Allah yayi ruwan wata murja a wajen ba haka tayi watsi da zagin datake mata sanan ta tashi tayi hanyar d’akin ta… babu yanda murja zatayi da ita haka ta koma d’akinta tana ta k’ara tsinewa NI’IMATULLAH da aibata ta…..

 

 

Idan da sabo ta saba dajin kalar wanan zagin dan kuwa bayau aka fara ba kuma bayau za’a gama ba…

Hijab d’in dake jikinta ta cire ta ajje gefan katifar ta tana zaune saiga Abbas ya shigo shida Abba kallon yaron tayi taga sunyi bak’i sun lalace gawata riga duk ta yage a jikin su yaran dai sun fit hayyacin su, da gudu suka rugo suka rungumeta tare da fad’in “sannu da zuwa Anty sannu da zuwa” k’aramin wato Abbas da baifi shekara shid ba yace da ita.”Anty Amma dai bazaki sake tafiya ki barmu ba ko,sau d’aya ake bamu abinci shima Baba jummai ke bamu amma idan girkin babar su Aisha ne ata bamu saidai muyi bara idan mun samu muci idan bamu samuba mu kwana da yinwa… Abba ne yace “Anty kinga dukan da babar su Aisha tayi min jiya kalli bayana yanda ya fashe akan ban gani ba na buge habu ya fad’i k’asa kuma da malam ya dawo babu abinda yace saima k’aramin da yayi, yaron ya fad’a yana d’aga rigarsa,wani kalar shatin bulalane yayi kamar wajen ya k’one duk bayan sa ai batasan lokacin da ta rungumosu ba ta fashe da kuk mai tsuma zuciya,dakyar ta samu ta tsagaita sanan tace kuyi hakuri watarna sai labari ka manta abbas ance mai hakuri yakan dafa dutse har yashe romansa.” Ta fad’a tana k’ak’aro murmurshin yak’e dan hankulan yaran su kwanta…

 

 

Cire musu kayan tayi ta musu wanka sanan ta dafa musu lafiyayyen abinci da yake daman tana da komai da komai a d’akin haka sukaci abinci harda nama sakamakon kamshin da yacika gidan yasa y’ayan gidan suka ringa lek’asu bata kula dasu ba saida k’annan nata suka k’oshi sanan aka basu haka kamar mayu suka ringa wawa harda ita murjar…

See also  Dubu Jikar Mai Carbi Hausa Novel

 

 

Bayan sun k’oshi ta zaunar dasu tana koya musu karatu kamar yadda ta saba…

 

 

Tana cikin wani yanayi da ya zame mata jiki daman wanan shine yanayin ta ako da yaushe sai yanayin d’aya datake abin da take danshi dan da babu shi da bata kasance a yanda take ba,zama tayi tana tunani yau rabonta da school sati biyu kenan gashi sunata shirye shiryen yin final exam haka ta kud’iri niyyar gobe insha Allah zataje school dan ganin abin da ke wakana….

 

 

Bud’e data tayi tahau kan yanar gizo gizo sharhi ake sosai akan littafin data fara rubutawa a shekaran jiya taga mutuk’ar mabiya da masoya sai addu’o’in masara kala kala datake gani, murmushi tayi ciken da jin dad’in yanayi ta rasa ma mai yabawa mutane sha’awa game da wanan shirmen ma datake rubutawa amma gashi sai rububi mutane suke suna neman yaushe zata musu wani typing d’in cike da jin dad’i ta fara bawa wad’an da suka samu ammasa kowa yana tambayar labarin yayi dad’i amma wani abu guda d’aya shine ita kanta batasan sanda ma ta k’irk’iri labarin ba sanan batasa yadda zata kaya ba haka ta ringa bawa mutane amsa cikin yanayin da yake faranta mata rai take mantawa da tarin k’alubale da kuma matsalolin rayuwar ta…..

 

 

Tana cikin wanan yanayin ne taji malam yana kwankwasa kofarta kamar yadda ya saba yana fad’a sosai kamar zaici babu…

Fitowa tayi sanye da hijab d’inta ta tsugunna har k’asa ta gaisheshi.”dakata malama ba zuwa nayi dan na amsa gaisuwar kiba wallahi NI’IMATULLAH sai na d’auki kwakkwaran matakin akanki kuma gidan ubanwa kike zuwa kina kwana eyeeee.”

“Dan Allah malam kayi hakuri insha Allah bazan sakeba.” Tafad’a tana kuka sosai kamar an aiko mata da mutuwa… jikinsa ne yayi sanyi kamar yadda ya saba amma duk da haka saida yayi mata fad’a sosai kuma ta sheda masa bazata sake ba,haka yayi mata addu’ar shiriya ya barta anan tana sharar kuka….

 

 

 

Wahe gari da misalin goma tayiwa su Abbas wanka ta shiryasu sukaci abinci ta d’aukesu amota zuwa makaranta data sasu daman idan tana nan ita take kaisu da kanta kuma wuni suke islamiyya ce had’e da boko,bayan ta kaisu ta ajjesu ne ta nufi makarantar su itama…

 

 

Kamar yadda ta saba inda take parking anan tayi parking ta fito tana d’aukar jakarta da hijab d’inta har k’asa tan cikin duba bayan motar tane taji an d’ane ta da ihuuu….

“Ohhhh ni NI’NU karki b’allani dan Allah. Cike da jin dad’i da farin ciki NU’AIMA ta juya ta kallo NI’IMATULLAH sanan ta sake rungumeta sosai tana fad’in”nayi kewarki NINU nayi kewarki ai wallahi da tuni yau saidai ki ganni a gidan malam dan bazan iya jurewa rashin ganin kiba ni wai bikiga har rama nayi ba.”

“Ohhhhh NINU taska wanan surutu naki dai kullum k’aruwa yake ki barni da rungumar nan haka kada ki karyani.” Dariya sukayi su biyu dai dai sanda INAYATULLAH taja wani uban tsaki tare da fad’in “wallah NU’AIMA ranki zaiyi mummunan b’acin banace ki fita daga harkar wanan karuwar ba bakyaji ko to wallahi saina fad’awa momy idan muka koma.”

Cike da jin zafin kalaman INAYATULLAH NI’IMATULLAH ta kalleta tayi murmushi sanan tacwa NU’AIMA “NINU kinga kin b’atawa yar uwr ki rai ki bata hak’uri na barku lafiya.”

“Aa NINU dan Allah karki tafi ki tsaya ki saurareni dan Allah….. ina saboda NI’IMATULLAH har ta shiga aki hawaye yana wanke fuskarta taji zafin maganar INAYATULLAH data kirata da karuwa amma ya zatayi hakane karuwa ce ita a fili ta furta ni karuwa ce kin fad’i gaskiya INAYATULLAH ta fad’a tana zubar da hawaye mai d’aci….

 

 

“Haba INAYA mai yasa kike shiga harkar da babu ruwanki dan Allah kibarni inyi rayuwata mai yasa zaki fad’awa NI’IMATULLAH haka,hakan da kikai kin kyuta kenan she’is my best friend among the world’ maiyasa zakice mata haka.”

“Saboda sunan tane.” INAYA ta fad’a tana hararar NU’AIMA.

NU’AIMA ce kamar wadda ruwa ya cinye ta a hankali tace sunan tane kuma sunan ta kamar yaya itafa mutuniyar arziki ce ko kula maza batayi INAYATULLAH kuma ni inasonta sosai mai yasa zaki kirata da wanan mummunan sunan da bashi da dad’in ko ji………



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Ni’imatullah Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top