Hausa Novels

Norhan Hausa Novel Complete

Norhan Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: NORHAN

 

By Sapnah Borno

 

D’an k’aramin k’auye ne wanda yake k’aramar hukumar maiduguri mai suna (mafah) cikin anguwar mai anguwa layine sai gidaje wanda a k’alla bazasu wuce sha biyu ba, bakin wani k’ofar gida kamar d’an akurki wata mata ce sai k’aton murhu gabanta tana jefa d’anwake yara sun zagayeta cikin fad’a take fad’in “Amin!Aminu!Aminu!” Wani saurayi ne fari ya taso kan wani dandamali yazo wajen yayi ass down gashin kansa irin na y’an daba kallo d’aya zakayi mishi ka fahimci ba bahaushe bane don fari ne tass cikin hausar sa irinta shuwa arab wacce bata fita daidai yace”Deluwa wai miye hakane inzaki samin d’anwaken ni kisamin ina sauri fa zan wuce zan d’auki passenger kuma idan na makara babu passenger fa, sai kwad’a mini k’ira kikeyi meyafaru ne wai?” Matar daya k’ira Deluwa harara ta jefa mishi tace”wallahi albasa batai halin ruwa ba, ina mahaifiyar ka ni kake gayawa haka, to wai ina wancan shegiyar mai kama da bulala sai ka k’irata tazo tasawa mutane d’anwaken ita sam batason temakon mutum inace saina sayar har zata samu taci abinci nida na riketa gaba da baya babu uwa babu uba waye zai mata hakan inbani ba, je ciki ka k’irawo min ita dama tafito, munafukar banza”

 

Aminu juyawa yayi ya shiga d’an gidan nasu mai kamar akurki yana shiga d’an k’aramin filin gidan nasu ya shiga kwad’a k’ira”Norhan!Norhan!”wata yarinya ce ta fito kyakkyawa fara tass tamkar balarabiya sai dai kana ganinta kaga yar wahala irin wannan yaran da suke shan wahalar rayuwa, sanye take da wani kod’ad’an hijab wanda yagama faffarkewa sai doguwar rigar atamfa wacce harta fara diddigewa sabida tsufewa tana mitsika ido cikin hausarta irin ta shuwa arab na kauye tace”Ya Aminu gani nan” yana kallon ta yace”Norhan meyasa kike haka ne wlh kin san Deluwa ba baki abinci zatayi ba gara ki fito kije kitayata saida d’anwaken nan kiyita hak’uri kinji yar k’anwata wlh Deluwa hakkinki kad’ai ma ya isheta” daga haka ya juya ya fice daga gidan, Norhan fitowa tayi ta nufi wajen jifar d’anwaken tana zuwa ta shiga zubawa yaran dake layi. Haka har suka gama suna tattare kayan zasu shige gida Deluwa tace”ke mai wayo to bari kiji kinyi kad’an wlh, nace uban kuturu ma yayi kad’an ni Deluwa anyi kad’an a cuceni wlh tallahi, wato kingama sharar baccinki shine yanxu zaki fito to nidai gaskiya yau banida hamsin d’in da zanbaki ga naira ashirin kya sai k’osai dashi” Norhan wacce ke wasa da fararen yatsun hanunta ce ta d’ago tace”Iyah ki hak’uri ba k’in fitowa naiba wallahi kaina yake mini ciyo” Deluwa tace”naji nidai ishirin d’inma kinci sa’a na baki shine kawai don wallahi inda zan biye mugun halinki ko biyar bazan baki bama” Norhan batace komai ba ta gama tattare wajen sana’ar tasu sukayi cikin gida.

 

Washe gari tun sassafe Norhan ta tashi ta tattare filin gidan nasu bayan ta gama ta d’auki uban bokitai ta nufi rijiyar dake anguwar tasu don d’ebo ruwa yauma sanye take da kayan nata na jiya.

 

Wata yarinya ce zasuzo d’aya da Norhan a shekaru sai dai ita ta baiwa Norhan d’in watanni akasin Norhan wacce bata cika 17yrs ba, sanye yarinyar take da uniform tana tsaye kan mahaifiyar ta ta turbud’e fuska sai cika take tana batsewa tace”iyah nifah naira d’ari bawani isata take ba kinsan wallahi makarantar nan nisa gareta aringa adalci gaskiya” Deluwa tana murmushi tace”to shalele ga naira d’ari biyu aje ayi karatu nidai nasan wallahi inkika zama likita wannan karkarar sai mun zam abin nunawa shisa nake dagewa wajen ganin kinyi karatun bokoko d’iyar albarka “ murmushi yarinyar tayi kafin ta juya tayi wucewar ta bayan ancika mata kula da d’anwake, Norhan rakub’e tayi jikin wani bango hanunta rik’e da bokitayen ruwa tana hawaye tana kallon yar uwartata wacce take tafiya makara.

 

Wani d’an almajiri wanda ke hurawa Deluwa wutane yace”lahh Norhan kuka kuma kike waya dakeki?” Sai lokacin Deluwa takai kallon ta inda Norhan ke rakub’e tana goge hawayenta da bakin hijab ta cire takalmin k’afarta ta wurgeta dashi tana fad’in “don kutumar ubanki kukama aibaki farashi ba, nace baki farashi ba yoh kina tunanin zan zauna gindin murhu inyi Sana’a ne kawai don ke wlh kinyi kad’an inayin sana’a ne don Talatuwa tazama likita anma kekam ai munanan dake gindin murhu wlh” haka Deluwa ta gama masifarta da zagegenta Norhan dai batace komai ba ta wuce cikin gida ta juye ruwan datake d’ebowa.

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Misalin k’arfe biyu na rana Norhan wacce tayi alwala sallah tayi bayan ta idar tayi shirinta na islamiya ta fito zata tafi kenan Deluwa tace”keh wai bance kibar zuwa wannan islamiyar bane maza jeki kicire inifon d’in nan maza ga gero na nan kizo ki surfamin” Norhan tana hawaye tace”don Allah iya kiyi hak’uri wlh zan surfa idan nadawo banaso hadda ta wuceni” wani irin dirty slap Deluwa ta saukewa Norhan nan Norhan ta fad’i dafe da kuncinta tana kwala ihu don sosai marin ya shigeta, har shatin yatsun Deluwa yafito a kan farar fuskar tata cikin masifa tace”kin wuce kinyi wannan surfen ko saina hau ruwan cikin ki anan wajen?” Dai dai Aminu ya shigo yana busa sigarin sa yace”haba Deluwa meyasa babu Allah ne aranki wlh karki mance kama tudini tudan kinawa marainiya haka mu idan anyi mana zakiji dad’i ne wlh karkiga ina busa hayak’i ina dumuwa duk shaye shayen danake nasan dai dai nasan akasin haka” yayi maganar yana d’aga Norhan yana a fad’in “tashi yar k’anwata kiyi hak’uri jekiyi surfen kici gaba da hak’uri watarana sai labari”

 

Norhan surfe taje tafarayi babu k’ak’autawa ga uban yunwa dake cinta, tana gamawa Deluwa ta wurga mata naira goma tace”kya saya koko kisha”

 

 

Deluwa ce da yanma tana dawowa daga k’aramar kasuwa da lodin kayayyakin d’anwake data sayo daidai zata shige gida saiga aminiyarta iyatu tana tahowa da murmushinta tace”Deluwa ikon Allah daga kasuwa kike ne?” Deluwa tayi murmushi tace “ahh mutan binni antaho ne yaushe agari?” Iyahtu tace”aina kwan biyu da zuwa jibi ma nake shirin komawa insha Allahu, don kin san gidan danake aikatau d’in basu cika zama a nan maiduguri ba, a habuja suke yawan zama to yanxu ma dai maganar danake miki suntafi can Habujan shiyasa kikaga nadawo anma jibi zan koma dan sunce zasu dawo akwai bikin da zasuyi, ashe dai ana nan ana sana’ar d’anwaken ai jiya na jiyoki kinata faman fad’a ashe dai wannan tsinanniyar yarinya bata daina saki magana ba” Deluwa tace”hmm kedai barni ai wannan yarinyar wlh tana wuyana jinake kamar inkarta kowa ma ya huta, nifa dazaki tahi da ita can binnin ma taje can tayi aikatau insamu kud’i da ita ai inaso wlh” Iyatu tace”Toh ai indai kikace intai da ita wlh sai muje d’in yanxu dai jibi zan tahi kyayi k’ok’arin ki sata ta had’a tsummokaranta ma wuce kawai”

 

 

“Haba magajiya kindai san ni kikace zan kwana tare da wannan Alhajin anma yanxu kawai don ankawo sabbin y’an mata shine za acanza shawara gaskiya nidai ba a kyautamin ba wallahi”

 

Matar da aka ambata da magajiya wata k’atuwar matace taci uban bleaching ta sanya d’an kunne a hanci tasha uban gashin doki murmushi tayi tace”haba Billy kefa bakya ganewa ai wad’annan sune sabbi kibari mana musamu kudi masu yawa aike kinjima a wannan harkar kiyi hak’uri yanzu kije na zabe ku ku goma kuje bakin titi da yanman nan zamu fi samun customers ai”

 

 

This book is not free

 

08093772168 S.Born

NORHAN

 

By Sapnah Borno

 

2…

 

Billy bata sake cewa komai ba ta mik’e suka fice su goma suka nufi bakin titin dake k’ofar gidan magajiya suka tsaya layi layi! Manyan motoci ne ke sharara gudu kawai saman titin inda masu motocin suke paker wa wajen suna d’iban y’an matan.

 

Ajmal wanda yayi parking motar sa gefen titi ne ya sauk’a don sayan fruit gefen titin kallo d’aya yayiwa yan matan ya d’auke kai ba tare daya sake kallon su ba. Aunty wacce ke cikin mota ce taketa kallon su itama batace komai ba har Ajmal ya dawo cikin motar suka cigaba da tafiya, Aunty tace “A.j yanzu wad’annan yanmatan they are all ladies of the night? Su kuma haka Allah yayisu masuda mafad’i they are just like that dubi fa yadda manyan mutane ke picking nasu a mota, duk sanda zamubi wannan hanyar by this time sai mungansu” Ajmal murmushi yayi yace”Allah ya shiryesu dai Aunty” wani mugun kallo ta Jefo mishi tace”Allah dai Ya tsine musu wallahi shegu y’an iska” bai sake cewa komai ba yacigaba da driving har suka kawo gaban wani katafaren yayi horn masu gadi suka bud’e mishi gate ya kutsa kai ciki, sosai gidan ya had’u don gidane na masu dashi abun ba acewa komai.

 

 

Washe gari da sassafe saida Deluwa taga Aminu ya fita aiki ta gama had’a kayan Norhan wanda basuda maraba da tsunmo kara tana ta cewa”ai kyayi maza kiyi kwaskwarima ki hito ku wuce don wlh nima ruwan gidana kad’an ne, kuma kikaje binni zagewa zakiyi kiyi aiki don wallahi nidai kika yarda kika nok’e gidan masu kud’i baki aiki to zanje har binnin inci miki uba Shegiya mai idon mayu hito maza don nasan iyatuce wannan mai kwankwasa k’ofar” Norhan wacce take kuka tace”iyah don Allah kibarni anan” wani irin fisgota Deluwa tayi tayiyo waje da ida dai nan iyatu ta shigo gidan tana fad’in “Deluwa nifa sauri nake ta hito maza mu wuce kar mu makara” Norhan tana hawaye haka suka d’auki hanya itada iyatu suka nufi wajen hawa motar maiduguri bayan sun shiga iyatu tace”tofa kisani kudin motar nan dana biya maki shi cikin kud’in aikinki za acire shi” Norhan dai batace komai ba sai had’a kai datayi da gwaiwa tana faman rusa kuka har suka kawo cikin maiduguri, adaidaita sahu iyatu ta d’aukan masu tare da fad’a mishi sunan anguwar da zai kaisu, babu lokaci ya kama hanya suka shiga tafiyar minti arba’in ta kawosu anguwar Norhan tun sanda suka shigo anguwar tagama sadak’ar da cewar yau kwananta ne ya k’are don da ganin wannan manyan gidajen dake anguwar tsoro ya kamata ita ko a mafarki ma bata tab’a kallon ire irensu ba.

 

Gaban wani gida ta nunawa adaidaita sahu tace”d’an sahu nan zaka ajiye mu” tana sakkowa tun kafin ta baiwa d’an sahu kud’in gate man yace”aikuwa iyatuh su Hajiya basu dawo ba, barrister ne kad’ai agidan don yau ya shigo garin sai dai satin gaba ki dawo” dai dai nan Barrister ya fito don zuwa mosque iyatu tana ganinshi tace”inayini Alhaji karami” babu yabo babu fallasa yace”lfy lau” kallo d’aya yayiwa Norhan wacce take rakub’e jikin gate d’in su bai sake kallon inda take ba yayi wucewar sa.

 

Iyatuh tace”sai kizo muje can d’ayan gidan danake aikin dama ance gida biyu maganin gobara” Norhan tabi bayanta suka shiga adaidaitan daya kawo su iyatuh tace”sabon layi zaka kaimu” tafiyar minti goma shabiyar ce ta kawosu gidan magajiya dayake anguwar gangare, iyatu ta ciri kud’in d’an sahu ta bashi lokacin ana sallar la’asar Norhan dai yunwa sai nuk’urk’usarta takeyi wanda hakan yasa takejin kamar zata fad’i.

 

 

Haka suka k’arasa gidan magajiya kasancewar yanmace babu kowa tsakar gidan ko wacce tana d’aki tana shirye shiryenta kamar yadda suka saba don da zarar k’arfe shida na yamma tayi zasuje bakin titi suyi layi layi kamar yadda suka saba.

 

Iyatuh ganin babu kowa tsakar gidan ta wuce d’akinta tare da Norhan tace”zauna nan kijirani inazuwa “zuwa daga haka ta fito zuwa b’angaren magajiya da sallama ta shiga ta rusuna ta gaida magajiya, magajiya tace”to iyatuh wancan watan daya wuce nace wanke wanke kawai zaki keyi yanxu dai harda shara dakuma gyaran d’akuna zan k’ara miki albashi daga yanxu kudinki dai sun zama dubu talatin” iyatuh sai godiya take ta mike ta fita, kitchen ta nufa ta karb’a musu abinci sannan ta koma d’akin…

 

Paid book ne 300 naira kacal 08093772168

 

S.borno ce

[03/07, 10:26 pm] +234 803 192 1625: 💖💘NORHAN 💖💞

 

By Sapnah Borno 📚✍️

 

Paid book 300

 

3..

 

Norhan cewa tayi “Baba iyatu inason inyi sallah ina ake alwala?” Iyatu ta had’e rai tace”Allahu akbar to sannu uwar masu addini wlh nidai ba jiranki zanba atoh gara kin bari bayan mun gama cin abincin namu kyaje kiyi sallar” Norhan bata kuma cewa komai ba har suka gama cin abin, sosai taci abincin don ita rabonta da shinkafawa tun sallar azumin bara lokacin Abbanta yana raye, bayan sun gama ne iyatu ta nuna mata toilet dake d’akin tare da yadda ake anfani dashi, alwala tayi ta fito ta rama sallolinta ta jima tana azkar bayan ta idar daga bisani ta kwanta kan tiles haka barci ya kwasheta a kwajen ta cukuikuye waje d’aya sabida sanyi, ita kuwa Iyatu katifar ta mai d’aukar mutum biyu ta haye tayi kwanciyar ta.

 

K’iran asubar farko Norhan ta farka don ita ko a can gidan su haka take tashi, bayin dake cikin d’akin tashiga duk da cewar iyatu ta nuna mata yadda ake anfani dashi hakan bai hanata jin tsoron tab’awa ba a tsorace dai tayi wanka ta d’auro alwala ta dawo d’akin har zuwa wannan lokacin iyatuh bata tashi ba baccinta take hankali kwance, Norhan ta jima tana azkar a zaune har barci ya kwashe ta, sai kusan k’arfe bakwai iyatuh ta tashi tayi sallah tana idarwa tace”keeh har barcima kikeyi to wlh maza maza taso muje kiyi sharan filin gidan nikuma zanyi wanke wanke” part d’in magajiya suka fara shiga don gaishe ta magajiya bayan ta amsa musu gaisuwar tanata kallon Norhan kafin tace”iyatuh tare kuka taho ne daga can garin naku?” Iyatuh tana murmushi tace”ehh Hajiya anma zan kaita wani gidane tayi aiki can d’ayan gidan aikin nawa, kuma munje basa gari suna can Abuja!to shine dai nace bara inzo nan d’in da ita kafin su dawo” magajiya tana murmushi tace”masha Allah ai bama sai kin kaita can d’in ba kibarta nan kawai anjima zamu fita da ita kasuwa saita zazzab’i kayayyakin datake so kibarta nan b’angaren karkisata aikin komai zan k’ara miki albashi daga yanxu zan baki dubu hamsin duk wata” iyatuh harda kuka tana hawaye tace”ohh Hajiya tabbas ked’in yar aljannah ce wlh yanxu ina natab’a ganin dubu hamsin a zahirin gaske?anma dalilin ki gashi zan gansu to Allah ya saka” magajiya tana murmushi tace”zaki iya tafiya”Norhan dai haka kawai taji hankalin ta bai kwanta da magajiya ba haka ta zauna gefe batacewa komai, can magajiya tace”yaya sunanki y’an mata?” A takaice tace “Norhan” magajiya tace”to Norhan za akawomiki kayan kari yanxu ki karya sai mufita inmiki sayayya”

 

Bayan Norhan ta kammala breakfast magajiya ta d’auketa suka nufi wani mall kayayyaki masu tsada ta sai mata da mayuka na gyaran jiki sai takalma da turaruka babu abinda bata sai mata ba, itadai Norhan bata k’ara tsorata ba saida taji awajen biyan kud’i an anbaci dubu d’ari biyu da ashirin.

 

Sai kusan yamma suka dawo gida nan tasa billy ta kaita saloon aikuwa cikin shagon saloon duk mamaki ya rufesu ganin irin tsawon gashin yarinyar, Norhan dai tsaf tsaf tayi kyau kamar ba wannan Norhan d’in ta karkarar mafah ba, bayan dawowar su magajiya tasata tayi wanka wani black Arabian gown tasa masha Allah kyau ne kawai ke d’iga a jikin ta, itadai zuwa yanzu banda tsoro babu abinda ke damunta don batasan menene dalilin dayasa akace saitayi wannan uban adon ba, ga yanmata cike a gidan duk sunyi wankan yanma za aje bakin titi sai binsu takeyi da kallo don ita har yanxu bata fahimci komai ba.

 

 

Dai dai gabatowar magrib magajiya tace”yauwa keh Norhan abinda nakeso dake shine kinga wannan y’an matan da suka fita kibisu zakiga sun tsaya bakin titi inkinga masu motoci sun tsaya sunce kishiga kuje, kice kefa sabuwa ce don haka kinada babban farashi kinji koh?” Norhan kamar zatayi kuka tace”inshiga muje inakuma?” Magajiya tana murmushi tace”keeh ashe sauna ce ban sani ba?zakuje ne kawai ku kwana fa bawani abun damuwa bane kinji koh” Norhan gabad’aya hankalin ta yakai k’ololuwa wajen tashi sai dai batace komai ba har magajiya ta koma cikin gida tanajin dad’i don yadda taga kyawun Norhan tasa zata samu kud’i sosai a jikin yarinyar.

 

Khaleel ne kwance kan three seater dake palorn sa wayarsa ce tayi ruri ahankali ya bud’e lumsassun idanun sa ganin wanda ke k’iran wayar yasa ya d’aga, daga d’aya b’angaren Khalifa yace”Barrister wai miskilancin harni sai anyiwa ne tun rana ina k’iran ka baka d’agawa kana gida ne?” Khalil yace”uhmm ni yanzu nake ganin k’iran ka karkamin sharri” khaleefa yace”Ohhk gani zuwa” babu b’ata lokaci khaleefa ya iso jin ana nocking k’ofar palorn ahankali ya mik’e ya bud’e k’ofar tsayawa yayi bakin k’ofar bayan ya bud’e khaleefa ya had’e rai yace”meye hakan barr nifa banson wulakanci bama shigowa zanyi ba kawai ka taso muje can gidan Aunty zan amsa wani abu” Khaleel baice komai ba ya d’auko wayoyin sa da car keys suka fito! Warming motar sa yayi kafin suka fice agidan sunyi nisa cikin tafiyar kahaleel yace”ahm khaleefa nifa bazan shiga gidan Aunty ba, zan jiraka waje don Allah karma kace tare muke pls” khaleefa ya had’a rai yace”why all this barrister nifa inaga kamar bayan miskilancin ma harda wulak’anta mutane ka iya wannan bayi bane wlh, karfa ka manta Aunty k’anwar Abbanka ce, nikuma yayar ummana ce so bai kamata inyi mata k’arya ba wlh zance tare muke” Barrister jin haka ya sauk’o suka shiga cikin gidan Aunty! Zainab ce zaune bakin tab tana wanke socks suka shigo gidan tana murmushi tace”lah! Yaya khaleel dama kana gari? Inayininku” Khaleel kallo d’aya yayi mata yace”Aunty fa?” Tace”tana ciki” khaleefa yace”zainab yaya schoo d’in ince dai anata k’ok’ari?” Tayi murmushi bata sake cewa komai ba tabisu da kallo har suka shige cikin palorn bayan sun zauna suka gaishe da Aunty tanata kallon Khaleel tace”kai Khaleel wato har yanxu kakiyin aure sai dai azubamaka ido wlh kayiwa kanka fad’a, idan kud’i ne karigada katarasu gidajen akwaisu to kodai yan matan ne baka samu ba sai anemo?” Khaleefa banda murmushi babu abinda yakeyi don yasan babu abinda Khaleel ya tsana irin maganar aure shi a cewar sa y’an matan nan duka basa burgeshi yafison ya nemo wacce zasuzo shekaru guda itace kawai zata fahimci halinsa dakuma ra’ayinsa sai su zauna lfy” Ahankali yana shafa kai yace”no Aunty insha Allah soon zanyi” Aunty ta tab’e baki tace”to Allah dai ya kyauta, su ummy basu dawo daga abuja ba wannan karon ko yaran basuyi hutu bane?” Khaleel yana latsa waya yace”uhmm wannan karan bazasu zo ba sai next month” basu wani jima gidan ba suka fito Khaleel driving kawai yake yak’i ko kallon inda khaleefa yake balle yasa ran zai kulashi,Khaleefa sanin halin cousin d’in nashi da yayi yasa baice komai ba dai dai wani junction khaleefa yace”Barrister bara insayawa ummah fruit anan wajen” parking Khaleel yayi gefen titi Khaleefa ya sauk’a ya sayawa ummah grapes! Barrister yana kallon gefen titin idanun shi suka sauk’a kan Norhan wacce take tsaye bakin titin fuskar nan tata a had’e kamar an aiko mata mutuwa, ido hud’u sukayi, yamata wani mugun kallo da sauri ta d’auke kai daidai nan wata benz ta tsaya wajen da take, wani babban mutum ne ya fito cikin motar kana ganinsa kaga Alhaji mai naira, yana washe hak’ora ya fito iso gaban Norhan ya tsaya da sauri taja baya! Mutumin ya jinginu jikin motar yace”masha Allah to y’an mata nawane farashin ki?” Wani mugun kallo ta watsa mishi hawaye suna kawowa idonta, tayi saurin matsawa gefe taci gaba da tsayuwarta, duk wannan abun da ake akan idanun barrister don ya kasa d’auke ido kan abinda ke faruwa,wannan mutumin ganin Norhan bata bashi fuska ba sai ya d’auki wata awajen ya wuce da ita, motoci sunfi biyar suna tsayawa amma Norhan ko kallon arziki batayi musu balle kuma akaiga ta shiga motar tasu.

 

Khaleefa harya bud’e mota ya shiga barrister bai san cewar ya shigo ba don abun ya bashi mamaki sai dai shi har yanxu bai fahimci me y’anmatan nan keyi a bakin titi ba ya daiga sai d’iban su akeyi a motoci.

 

Khaleefa ne yayi murmushi yace”hala baka bin wannan hanyar da yanmaci koh barrister?” Sai a lokacin ya dena kallon gefen titi ya juyo yana kallon khaleefa yace”wai khaleefa me matan nan keyi haka anan?”

 

 

Littafin kudi ne 300 kacal 08093772168

Leave a Comment

error: Content is protected !!