Hausa Novels

Nurul Ayn Hausa Novel

Nurul Ayn Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*NURUL-AAYN*

_[Hasken idaniya ta]_

 

 

_Story&written by_

*_AYUSH💞_*

 

 

_Elegant Online Writers_

 

 

*_FREE-BOOK_*

 

 

Page 5&6

 

*ASALIN LABARIN*

 

Sadeek da Ayush cousins ne, inda mahaifin Sadeek Alhaji Ahmad Muhammad da Mahaifiyar Ayush Hajiya Khadija Muhammad suka kasance Yaya da Ƙanwa. Iyayen su Ƴan Asalin Garin Ɓatagarawa ne dake jihar Katsina, su biyu Allah ya bawa iyayen su wato (Alhaji muhammad da Malama Aisha).Inda a lokacin da aka haifi Ahmad (mahaifin Sadeek) iyayen shi sun nuna mai gata saboda sun jima da Aure Allah bai basu Haihuwa ba sai bayan shekara goma suka same shi, shiyasa lokacin da ya fara girma ya banbanta da sauran yaran unguwar su dan shi har makaranta aka saka shi, cikin hukunci ubangiji ƙwaƙwalwar Ahmad ta buɗe sosai ko wane karatu akayi toh fa sai ya iya. Ahmad nada shekara goma aka haifi ƙanwar shi Khadija (mahaifiyar Ayush), Itama an nuna mata gata har ta kai lokacin shiga makaranta aka sanya ta. A lokacin ne Ahmad yake aji uku a secondary, Itama Khadija ta taso a cikin yara masu ƙoƙari, kasancewar Iyayen su suna da kuɗi yasa suka ɗauko musu malamin da zai dinga yi musu lesson a gida, kuma a koya musu Ƙur’ani(hadda) a ranar da basa zuwa islamiyya.

 

Kwanci tashi ba wuya Ahmad ya gama secondary, inda Karatun Khadija ya fara yin nisa haka ma ƙoƙarin ta yana ƙara gaba wannan yasa malaman su na makaranta suka nemi da ayi mata tsallaken aji, iyayenta basu yi gardama ba aka kai Khadija Aji ɗaya a secondary. Ahmad kuma mahaifin shi ya biya mai makaranta a ƙasar India inda zai karanci Medicine. Daga kan Ahmad da Khadija Allah bai sake bawa iyayen su haihuwa ba.

 

_Fifteen years later_

 

Bayan shekaru sha biyar(15), Ahmad ya kammala karatun shi na farko, inda ya ɗora da masters da Phd duk a ƙasar India kuma yake aiki a nan, sai bayan ya gama Phd ɗin shi sannan ya dawo Nigeria. A lokacin Khadija ta kusa Aure da wani Malamin jami’ar da tayi, kuma ta kammala karatun ta tana bautar ƙasa.

 

 

A lokacin ne Mahaifinsu (Alhaji Muhammad) ya nemi Ahmad da ya fito da matar Aure, saboda lokaci yana tafiya, Ahmad ya wakilta mahaifin shi da ya zaɓa masa Mata dan shi baya da wacce yake so. Haka kuma akayi Mahaifin shi ya zaɓa mai ‘ƴar abokin shi, Ahmad ya karɓi zaɓin kuma yayi godiya kasancewar ita ma Wacce aka bashi tana da Halaye masu kyau. Ba’a ɗauki lokaci ba aka gama magana inda aka haɗe Auren Ahmad dana Ƙanwar shi Khadija.

 

Kwanci tashi babu wuya, Aka shigo satin biki inda ta kowa ne ɓangare shiri suke na biki. A Ranar juma’a aka ɗaura Auren Ahmad Muhammad da Amaryar sa Bilkisu Aminu, sai Khadija Muhammad da Angon ta Prof Umar Ibrahim.

 

Bayan biki Ahmad ya ɗauki Amaryar shi Bilkisu suka koma Abuja kasancewar a can yake aiki har yana shirin buɗe Asibiti. A ɓangaren Khadija da Angon ta prof Umar Suka dawo garin kano kuma ya sama mata lecturing a wata kwaleji dake jihar kano.

 

 

Bayan shekara biyu da Aure, Allah yayi wa Mahaifin su Ahmad rasuwa(Alhaji Muhammad) sakamakon jinya daya sha, kuma a lokacin Matar Ahmad wato Bilkisu take tsaka da jegon ɗan ta mai suna Abubakar ana kiran shi da Sadeek, sunan mahaifin ta yaci.

 

Ahmad da Khadija sunyi rashi Babba, bayan mahaifiyar su ta fita takaba Ahmad ya nemi da ya maida ta gidan shi tace mai A’a, sai dakyar ta yarda. A lokacin Khadija ta haifi ɗanta Namiji,lokacin sadeek yayi wayo, Yaro yaci suna Ibrahim suna kiran shi da Khalil.

 

Haka Rayuwa ta cigaba da tafiya,a lokacin Ahmad ya ƙara samun Hanyoyin arziƙi, har ya gina Asibitin shi mai suna *A Muhammad & Fam Clinic* wato Ahmad Muhammad.

 

Bayan shekara biyu da haihuwar Sadeek da Khalil, Mahaifiyar Sadeek ta sake haihuwa inda ta haifi ‘ƴar ta mace, Ranar suna Yarinya taci sunan Mahaifiyar Baban ta wato Aisha suna kiran ta Islam. Islam nada shekara biyu, Khadija mahaifiyar Khalil ta samu ‘ƴa mace itama yarinya taci suna Aisha suna ce mata Ayush. A lokacin Sadeek da Khalil sun kusa gama primary.

 

Shekaru sun ja inda a yanzu Sadeek da Khalil Suna shekaru 22,kuma suna Ƙasar England suna karatun jami’a, inda Sadeek yake karantar Medicine(Karatun da Mahaifin shi yayi) Shi kuma Khalil yake karantar Accounting.

 

A lokacin Islam tana da shekaru goma sha biyu tana Aji biyu a ƙaramar sakandare, ita kuma Ayush tana da shekara goma tana aji Biyar a primary.

 

A duk lokacin dasu Sadeek suka zo hutu gida to Ayush tana tare da Sadeek saboda a gidan su yake hutun shi Kasancewar Khalil da Sadeek ɗin basu da wata tazara sosai shiyasa komai nasu a tare. Daga kan Ayush haihuwa ta tsayawa iyayen ta, inda mahaifiyar Sadeek ta sake haifar ɗanta namiji yaci sunan marigayi Muhammad suna kiranshi da Adeel.

 

Shekarar Su Sadeek Takwas a England suka dawo Nigeria, inda Sadeek Ya zama cikakken likita shi kuma Khalil ya zama babban ma’aikacin banki.

 

Islam tana da Shekara Ashirin kuma tana karantar Aikin jarida tana Aji huɗu a jami’ar Base university dake garin Abuja, yayin da Ayush take da shekaru goma sha takwas kuma tana karantar pharmacy a B. U. K dake jihar kano tana Aji biyu. Adeel kuwa yana Aji shida a secondary dake garin Abuja.

 

Shekaru biyu da suka wuce Allah yayi wa kakar su Rasuwa wato mahaifiyar Baban Sadeek da Mahaifiyar Maman Ayush. Wannan kenan.

 

 

*CI GABAN LABARI*

 

 

_Share fisabilillah🥰🙏_

 

 

_Ayi juma’a lafiya fans, ina jin daɗin sharhin ku, Allah ya bar ƙauna❤️🙏_

 

 

*_Ayush💞_*

Leave a Comment