Oga Habib Hausa Novel
Shafi na 1&5.
Bismillahir rahamanir rahim.
GARIN ABUJA.
Wani tabkeken Company ne, asamansa ansa,: SANAT YOGHURT.
Daga k’asan sunan kuma ayi rubutu da k’anan bak’i, kamar haka, :sanat yoghurt company , zone e apo Abuja.
tsaye nake ina kallan tsaruwar SANAT YOGHURT company, ina nan tsaye, sai naji wani yana cewa, “Barka da fitowa Oga Habib “. koda na juya dan ganin wannan wanda aka kira da Oga Habib.
Na makara sai dai motar da yashiga nabi da kallo, koda na duba motar da kyau sai naga, corolla S ce.
Motar nabi da kallo, motar black ce, mai pure white glass.
Gudu sosai motar ke yi.
Sunyi tafiya mai nisa sosai, dan har sun shiga garin kaduna.
Tafiya suke sosai, su biyu ne a motar Oga Habib, sai driver shi.
Habib cikin siririyar muryar shi, mai cike da izza, ya ce, “Bilya tsaya!.
D’an tsawa ce ya yi maganar, wanannan nature ne na Habib haka yake abisa lurar da nai me.
Bilya, cikin girmama Ogan shi, ya ce, “Oga Habib Lafiya zamu tsaya anan? kabari mushiga gari mana, kasan yanzu ba ko’ina ake parking ba”.
Habib cikin tsawa, ya ce, “Bilya na ce kayi drup d’ina anan kana kawo min wasu Questions”.
Bilya tsayawa ya yi, Habib ya d’auki faron da yasha ya rage ya fita da shi.
Bilya driver da mamaki, ya bi Habib da kallo, ya ce, “Oh wai dama gayannan fitsari zai yi ya ke min wani muzurai.
Habib da sauri ad’an tsorace ya dawo ya na haki alamun kamar yaga wani abun tsoro.
Bilya driver da sauri ya bud’e ma Habib burfin motar ya shiga.
Bilya cikin girmama ya ce, “Oga Habib lafiya kuwa? “.
Habib kamar ba zai magana ba, sai kuma ya ce, “Bilya gawar mutum nagani anjefar”.
Bilya cikin tsoro ya ta da motar zasu ta fi.
Habib ya da ka mai tsawa yace, “meye haka?, baka ji abinda na ce bane!? “.Bilya driver cikin bin umarnin Ogan shi Habib, ya tsaya da motar, ya kalli Habib, ya ce, “Oga Habib zamu d’augawa ne a mota?, kasan fa yanzu rayuwa ba kamar daba, gaskiya ricks ne Oga mu d’auki gawar da…… “.
Tsawar da Habib ya yi ma Bilya ne, ya sa ya yi shiru.
Habib cikin d’aga murya, ya ce, “ka fita ka duba min ka gani”.
Bilya fita yayi kawai dan bashi da yadda zai yi, amma a ainihin gaskiya a tsorace ya fita.
Bilya cikin tsoro ya fita ya dudduba amma bai ga wata gawa ba.
Bilya dawo wa ya yi, ya kalli Habib cikin girma, ya ce, “Oga Habib banga gawar kowa ba fa”.
Habib tsaki ya ja, ya fito daga motar.
Habib na ta fiya, Bilya na binsa aba-abaya.
Habib kallan Bilya ya yi, yana nuna mai abinda ya gani, ya ce, “Can me ye? “. Da d’an k’arfi ya yi maganar. Yana nuna gawar mutum da yagani kwance agun.
Bilya cikin tsoro ya ce, “Oga Habib zamu fa jefa rayuwarmu cikin had’ar…… “.
Tsawar da Habib ya yi ma Bilya ce tasa ya yi shiru, ya kama bakinsa bai k’arasa fad’in abinda ya ke fad’aba.
Habib cikin b’acin rai dan ya tsani arik’a jayayya da shi, cikin fushi ya ce, “Your very stopped, ina maga kana quarrel da ni, Bilya baka da wani amfani Wallahi”.
Idan da sabo Bilya yasaba da fad’an Habib. Hakan yasa Bilya cikin bin Umar nin Ogan shi yak’arasa inda gawar ta ke.
Bilya cikin al’ajabi ya ke, kallan gawar matashiyar budurwar, Bilya matsawa ya yi kusa da ita sai yaji kamar tana numfashi kad’an-kad’an.Hakan yasa Bilya dawo wa inda Habib ya ke tsaye.
Cikin girmamawa Bilya ya ce, “Oga Habib ba gawa bace,dan da alamun tana numfashi”.
Habib batare da ya kalli Bliya ba, ya ce,”ka d’akkota ka shigo mu tafi”.
Bilya da mamaki ya kalli Habib, amma gudun kar ya yi laifi yasa baice ko mai ba ya bi Umarnin Ogan nashi, ya je ya d’akko ta.
Habib tashi ya yi ya koma site d’in driver ya zauna.
Ita kuma Bilya ya shimfid’ar da ita a mazaunin baya.
Tafiya kad’an ta idasa da su Oga Habib kano.
Suna shiga kano sun yi tafi bawani sosai ba. Habib ya ce, “Bilya samu gu kai parking”
Bilya tsayawa ya yi, kamar yadda Ogansa ya Umar ce shi, ya ce, “Oga Habib mun tsaya”.
Wata private hospital Habib ya nuna ma Bilya ya ce, “Bilya ka shiga hospital d’in nan ka kaita”.
Bilya kamar zai yi kuka, dan shi a ganinsa idan ma tai mako Habib d’in ya ke son yi tom shi yi yi mana da kanshi ba sai ya bashi wahala ba.
Baliya badan ya soba ya d’akko wannan baiwar Allah da ke kwance kamar matatta ya shigar da ita hospital d’in.
Bilya na shiga aka amsheta.
Bilya kallan likitar ya yi, ya ce, “Likita dan Allah tare da Ogana muke, ki bata duk wata kulawa da ya ka mata zan dawo yanzu”.
Likitar cikin mamaki ta kalli Bilya ta ce, “Haba bawan Allah ya za ai bamu sanka ba, ka kawo mana yarinyar da bamu san taka mai-man abinda ke damunta ba, kuma ka ce mana wai za kaje ka dawo. Gaskiya ammana irin haka da yawa anan kano kuma basu dawowa. gaskiya haka ba zai yuwuba “.
Bilya cikin rok’on likitar ya ce, “Karki damu Insha Allah ni zan dawo nai miki alk’awari”. Likitar kallan Bilya ta yi ta ce, “sure”. Bilya cikin tabbatar wa ya ce, “Yess am very sure insha Allah “.
Bilya number shi ya ba likitar ya ce zai dawo ba da dad’ewa ba.
Dogon Yaro Hausa Novel Complete
Bilya fitowa ya yi inda ya yi parking d’in motar Oga Habib, ya shiga.
Habib bai tambayi Bilya ya sukai ba, shin tana da rai ko bata da rai make damunta, bai tambayi komai ba.
Shima kuma Bilya ganin bai tambaye shi ba yasa shima yaja bakinsa ya yi shiru.
Direct inda Oga Habib keda Meeting Bilya ya kai shi.
bliya na yi parking Habib ya sauka, hotel d’in da za su yi meeting d’in.
Lokacin da Habib ya shiga har sun gaggaji da jiran shi, dan harma sun fara fidda ran zai zo, in da shi Ka d’ai su ke jira dama.
Habib be fi hour d’aya da shiga taron ba ya fito ranshi a b’ace.
Habib cikin jin haushi ya bud’e murfin motar ya shiga ranshi da alamun b’ace ya ke.
Habib na shiga ya kalli Bilya cikin jin haushi, ya ce, “Jamu bar gurin nan aikin banza ai kin wofi”.
Bilya da sauri ya sa ma motar key suka bar gurin.
Bilya cikin jin tsoro ya kalli Habib ganin ranshi kamar ab’ace ya ke, ya ce, “Oga Habib ina zamu”.
Habib shiru ya yi ya yi banza da Bilya.
Bilya cigaba da tafiya ya yi batare da yasan ina zasu ba, so yake ya k’ara tambayar Habib amma kuma yana jin tsoro.
Wayar Habib ce ta yi ringing, Habib da sauri ya yi picking call d’in, dan ringing tone d’in mommy shi ce.
Habib cikin sakin fuska da murmushi, dan indai kaga Habib na waya yana murmushi tom mutum d’aya ce, wato Mahaifiyarshi.
Habib cikin sweet voice d’in sa, ya ce, “Mommyna kina lafiya”.
Banji mai akaje ba daga can b’angaran sai dai naji Habib ya ce, “Mommy ina hanya fa, na kusa dan Allah kijirani mana”.
Banji mai Mommyn Habib ta kuma cewa ba, sai ji nai ya ce, “Mommy ki barsu kawai, ni dama nasan bawai maganar kirki bace dan dai ma kin matsamin ne shiyasa nazo, Mommy wai fasaha suke so mu saida masu, suma su rik’a irin yoghurt d’in mu ak’asarsu, Wallahi Mommy tsabar haushi ko magana ban musuba nabar gun, dan dana san wannan maganar ce Allah Mommy da banje ba”.
Can b’angaran bajin me ake cewa nake yi ba, sai dai naji Habib nai mata fatan Allah ya dawo da ita lafiya, kuma dan Allah karta dad’e kamar yadda ta yi wannan karan.
Bilya ko jin wayar Oga Habib ce ta sa ya fahimci, Habib yagama abinda ya kawo shi kano, yanzu Abuja zasu nufa.
Hakan yasa Bilya ya kama hanyar Abuja.
tafiyar 4 hour’s ta kai su garin Abuja.
Bilya direct gida ya yi da Habib dan ya san ba zai koma Company ba, in dai ya yi tafiya ba ya komawa sai washe gari.
Bilya na aje Habib , Ya koma Company, dan Bilya aiki biyu ya ke ma Habib, yana aiki a SANAT YOGHURT.
Sanan kuma shike driving d’in Habib duk in da Habib zashi.
Albashi mai tsoka Habib ke biyan duk mai aikacin da ke aiki ak’ark’ashin sh. Wannan shine da lilin da yasa kusan duk suka jure cin mutuncin da Habib ke masu.
Bilya bayan ya koma SANAT YOGHURT COMPANY har an tashi ya koma gida, da ya ke gidan Oga Habib ya ke zaune.
Bilya bayan ya koma gida ne wayar shi tai ringing yad’aga, daga can b’angaran, fad’a sosai ta ke, ta ce, “Haba ya za ai kabarni da yarinya mara lafiya gashi ta farkaba tun d’azu amma kuma baka dawo ba”.
Bilya zaune ya tashi daga kwancan da ya ke, dan ya manta sham da maganar, wata Yarinya.
Bilya cikin damuwa alamun shima bai ji dad’in haka ba, ya ce, “Ayyah dan Allah ki yi hak’uri Wallahi na manta sham. kuma Wallahi yanzu haka ina Abuja, amma ki yi hak’uri da safe zan ma Ogana magana”.
“Gaskiya ni ba inda zan kaita, sai dai in tasan in da zata. Cewar likitar.
Bilya kashe wayar ya yi, ya ce mata dan Allah yana zuwa ta bashi minti d’aya.
Bilya cikin fargaba dan yasan Oga Habib ya hana shi kiran shi in dare ya yi.
Habib na kwance kan makeken gadonsa na alfarma sai game ya ke awayar shi dan shi Mayan game ne. Habib na cikin game kira ya shigo wayar shi.
Habib k’in picking call d’in ya yi, har sai da Bilya ya yi mai kira Uku.
Habib d’aga kiran ya yi ya, ya kanga akun nan shi, yana sauraran abinda Bilya zai ce masa.
Bilya ko cikin tsoran halin Ogan nashi da ba wuya ka b’ata mai rai, ya ce, “Oga Habib dama Yarinyar da muka tsinta ce d’azu, wadda muka kai hospital , tom shine likitar da naba Yarinyar ta kirani, yanzu , akan in zo ta far………. “.
Habib cikin tsawa ya katse, Bilya ya ce, ” Bilya kana ko da full sense, awannan lokacin zaka kirani kana min wannan maganar!?, Yarinya kuma da ka ke magana,duk yadda kaga dama kayi da ita bai shafan ba, karka kuskura ka sake min magana akanta!. “.
Wata zufa mai zafi ce ta fara karyoma Bilya. Ko tunanin mafita Bilya bai fara yi ba, kira ya kuma shigowa wayar shi.
Bilya koda ya duba yaga Number likitar nan ce, Bilya cikin rashin sanin abinda zai ce mata ya yi picking d’in call d’in.
Tun kafin ta yi magana, Bilya ya rigata da cewa, ” Ki yi hak’uri kinga yanzu dare ya yi ba damar in zo Kano, amma zuwa gobe zaki ganni”.
Likitar jin abinda Bilya ce yasa ta kashe wayarta.
Bilya sosai abinda Habib ya yi mai ya b’ata mai rai, taya zai ta kuramai ya d’auki ya rinyar, yanzu kuma yazo yana nai man lik’amai bala’i.
Bilya shiru ya yi, ya na nazari, ya ce, Tom ni yanzu ko ma kano nace zan je in d’akko ta ina zan kaita.
Bilya da sauri ya ba kanshi amsa da cewa, Wallahi sai dai in barma likitar ita, idan ma ta sake kirana bazan d’agaba.
Bilya blocking number likitar ta ya yi.
Cikin jin dad’in shawarar da yankema kanshi bacci ya kwasheshi.
Washe gari misalin k’arfe goma na safe, kamar yadda Habib ya saba sai ya je office sannan ake kai mai abin break fast , haka aka yi.
Bilya ko dama so ya ke ya yi magana da Oga Habib , amma bai samu dama ba, dan tunda ya d’akko shi da safe ya ke waya har suka isa company bai dai na ba. Wanan shine ya hana Bilya yi ma Oga Habib maganar Yarinyar.
Ga shi kuma tunda safe likitar ta da mai da kira, dan tana ganin ya yi blocking Number ta ta kira shi da wata Number. Hakan yasa Bilya ya ke son ganin Ogan nashi sosai.
Gashi in dai Habib ya shiga office d’in shi ganin shi na da wuya sosai, sai dai in Allah yasa ya fito.
Bilya na nan tsaye yana nai man hanyar da zai bi yaga Oga Habib , Sai ga masu kawo mai break fast sun iso, tattawan mata ne guda biyu, amma ba wai sun tsufa bane sosai.
Bilya na ganinsu cikin da bara, ya yi gurin su, ya ce, “Baba lami sannunku da k’ok’arin kula da Ogan mu “.
Tsofaffin cikin girmamawa su ka amsa ma Bilya.
Bilya kallan Baba Lami ya yi, ya ce, “Baba abin k’arin Ogan mu ne ko? “. “Eh Bilya shi ne”.
Suka bashi amsa.
“Baba ku kawo dan Allah in kai mai dama ina son magana da Oga Habib Wallahi amma narasa yadda zan yi”.
Wadda ya kira da Baba lami, wayayyar tsohuwa, murmushi ta yi, ta ce, “Tom Bilya ka dai son ko mai,ka san babu wanda Hajiya turai ta yadda ya ba Oga Habib abinci hannu da hannu sai mu, tom kuma dai kasan Oga Habib yadda ya ke abu kad’an za kai mai babu ruwansa da bashi ya d’auki mu aiki ba, yanzu sai ya da katar da Mutum aiki ba ruwansa, dan haka kayi hak’uri, amma idan nashiga zan gwada mai magana kana son ganinsa k’ila idan akaci sa’a yabari ka shiga”.
Godiya Bilya ya yi ma Baba lami. Sannan suka shiga.
Su Baba lami sun dad’e atsaye suna jiran Comment. Amma shiru.
Habib sai da ya gama abinda ya ke sannan ya basu izin shigowa.
Bayan sun Baba lami sun kaima Habib abin break fast ne. Har za su fita, Baba lami ta yi k’arfin halin bada sautin Bilya.
Baba Lami cikin girmamawa kamar yadda ta saba ba Habib d’in, ta ce, “, Oga Habib, dama yaran nan ne, driver ka, Bilya ya ke Son magana da kai wai”.
Habib batare da ya kalli Baba Lami ba, ya ce, “Ba yanzu ba”.
Baba Lami fita ta yi, tana alawadai da dukiyar da zata sa Mutum ya d’auki kan shi haka, kamar yadda Habib ya d’auki kan shi.
wata zuciyar ta ce mata tom kodai kyan shine yasa ya ke yin haka ne.Nan dai su Baba Lami suka fito suna mai Allah wa dai da ji da kai da tak’ama irinta Habib.
Bayan su Baba Lami sun fito ne.
Bilya ya k’arasa in da suke da saurinsa ya ce, “Yauwa Baba ya ce in shiga ko? “. Baba Lami cikin nuna rashin jin dad’in ta, ta ce, “ka yi hak’uri Bilya kasan yaron nan dama ba wai mutunci gare shiba, bai ganin kowa da Mutun ci, Wallahi ya hana. Sai dai ka yi hak’uri idan ya fito, ko in za ka kaishi wani gun”.
Bilya cikin d’an bacin rai ya ce, “Wallahi Baba Oga Habib na mulkamu yadda ya ke so, amma babu da muwa, ko mai nada lokaci, akwai lokaci”.
Baba Lami ta fiya su kayi bayan sun ba Bilya Hak’uri.
Bilya ko yana nan tsaye yana ganin fitowar Habib amma shiru, har akai Sallar azahar.
Bilya na nan tsaye kira yak’a shigowa wayar shi tai ringing, Bilya na dubawa yaga Number likitar ce, sosai gabansa ya fad’i dan k’aryarsa ta k’are.
Biya na d’auka ya ce, “Ki yi hak’uri dan Allah nima banso haka ta faruba, ko ba komai na k’arya alk’awarin da nai miki, amma Wallahi duk abinda kika ga ya faru ba laifina ba ne laifin Ogana ne, amma bari yanzu in turomiki Number sa, dan Allah ko kinkira bai d’aga ba karki gaji ki ta kira zai d’aga”.
Bilya na kashe kiran ya tura mata Number Habib.
aiko tana ganin Number ta danna mata kira, dan bata son yau ta sake kwana mata agida.
Habib ko na zaune a Office d’in shi yana aiki a laptop, kira ya shigowar shi.
Habib ko duba Number bai tsayiba ya ci gaba da aikinsa. Ita ko da yake taji abinda Bilya ya ce mata, hakan yasa taita kira.
Habib cikin jan tsaki ya d’aga kiran ya sa akunne, yana sauraran mai magana.
Ita ko likitar tana jin and’aga kiran ta ce, “Ranka shi dad’e dan Allah, kuzo ku amshi amanar da kuka ban dan Allah “. Habib cikin rashin fahimtar maganar, ya ce,”Wrong Number “. Yana fad’in haka ya katse kiran.
Likitar ko bata gaji ba k’ara kira ta yi, cikin b’acin rai ta ce, “Oh wai kunyi satar Yarinyar ne kuke tsoran asirinku ya tuni, koko ku ‘yan kidnappin…… “.
Habib cikin daka tsawa ya tsayar da ita, yana kunfar baka. Magana ya ke son yi ya kasa, kawai sai ya kashe wayar shi baki d’aya, dan shi harga Allah ya manta wata yarinya da suka kai hospital.
Bilya ko tunanin ko anda ce ne, yasa yakira, likitar dan ya ji yadda su kai da Habib.
Likitar cikin b’acin rai ta ce,ma Bilya “Karka rainamin hankali malam, yarinya kuma ku kuka sani, amma daga yau na gama kwana da ita”.
Bilya hak’uri ya ba likitar sosai sannan ya ce, mata,”Wallahi ba maganar wasa gobe zai yi samma kon zuwa kano d’in “. Ai ko haka akayi Bilya tun da daddare ya nemi permission gurin Ogan shi, akan tafiya kano.
Washe gari da wuri Bilya ya tafi kano, hakan yasa 12:00pm a kano tai mai.
Bilya bacin ya biya likitar hak’uri Sosai ya ba ta.Sannan ya zauna yana jiran fitowar ‘yar tsuntuwar tasu, shiga Ogan shi, wanda shi ya ma manta da batunta.
Bilya na nan zaune ‘Yar tsuntuwar su ta fito sanye ta ke da wata doguwar riga ta atamfa wadda likitar ce ta bata dan ganin bata da kaya, yasa likitar ta bata a tamfar.
Bilya kallanta ya yi, sannan ya ce, ” ‘Yan mata ke ‘Yar wana gari ce, yanzu in kaiki gidan ku, dan mu ahanyar mu ta zuwa kano muka tsince ki”.
Matashiyar budurwar da bazata haurama shekara goma sha bakwai ba.
Cikin siririyar muryarta ta ce, “Ni marainiya ce, bani da kowa, dan Allah ka tai ma ke ni”.
Bilya da tausayi ya ke kallanta, dan shi aganinshi tabbas marainiyarce. Bilya shiru ya yi, dan yasan bai da in da zai kaita.
Ito ko Yarinyar ganin Bilya ya yi shiru alamar ba zai tai maka mata ba, ya sa, ta ce, “Dan Allah katai makan Allah banda kowa”.
Bilya cikin tausaya mata ya ce, “zan tai make ki ki, amma tai makon ba mai tsawo bane, zan tai make ki ne kafin Hajiya turai ta dawo,kuma ni ba nan nake ba Abuja nake kin yarda zaki bini?, Sannan kuma duk sanda Hajiya turai ta dawo zaki kama gabanki , kin yarda? “.
Da sauri ta ce, “Eh na yarda na godee.
Bilya tashi ya yi Yarinyar na binshi aba suka je in da ya yi parking d’in motarsa da Ogan sa Habib ya yi masa kyautarta, suka tafi. Suka kama hanyar Abuja .
Kasan cewar Bilya yana gudu sosai da mota, hakan ya sa, ana Sallar magriba suka shiga gida.
Allah ko ya tai maki Bilya sosai dan lokacinda suka shiga ba kowa, duk ‘yan aikin gidan sun shi cikin gida, hakan yasa tana fitowa daga mota Bilya yaja hannunta da sauri ya kaita d’akin shi. Dan yasan gidan cike ya ke da magulmata.
Bilya dama tun kafin ya iso ya kira Baba lami ya yi mata bayanin ko mai, hakan yasa Bilya na isowa ya kira Baba Lami ya sanar da ita sun iso.
Baba lami na shiga d’akin Bilya.
Bilya ya kalleta ya ce, “Tom Baba kin san dai yadda gidan nan ya ke, Baba lami ga Yarinyar nan, dan Allah ta zauna gunki kafin Hajiya turai ta dawo”.
Baba lami batare da taima Bilya magana ba, gudun matsala dan ba wani lokaci sosai,Baba Lami taja hannun ‘Yar tsuntuwar ta yi d’akinta da ita da sauri.
Bayan sun shiga d’akine Baba Lami ta kalli Matashiyar budurwar ta ce, ” ‘Yan mata ya sunan ki? “. Cikin sanyin murya ta ce, “Sunana Hassana”.
“Yauwa Hassana dan Allah ki yi zamanki nan, karkisake ki fita waje, muta nan gidan nan magulmata ne, dan Allah ki kula, kafin Bilya ya samarmiki gurin zama”.
Sosai Baba Lami ke k’ok’arin b’oye Hassana.
Sai dai kash abinda Baba bata sani ba, aminiyarta wadda su ke aiki tare da ita da kanta ta kira Hajiya turai ta kai gulmar Lami ta kawo wata bak’uwar yarinya agidan, kuma abisa lurar da ta yi, Bilya ne zazo da Yarinyar ya ba Baba Lami ita”.
Hajiya turai ko, sosai hakan yab’ata mata rai, acewar ta ba laifin Bilya ba ne, lafin Oga Habib ne, saboda shi ya ba Bilya damar shigowa kai tsaye gidan.
Hajiya turai ranta ad’an b’ace takira Habib awaya.
Habib ko lokacin yana zaune a office d’in shi na SANAT YOGHURT, kiran Mahaifiyar shi abin soyuwa a zuciyar, ya shigo wayar shi
Habib cikin kirarin da ya saba yi ma Mommy shi, ya d’aga kiran ya ce, “Sai Mommyna ni kad’ai Allah ya k’arami lafiya, lafiya dai ko wannan kira haka a wannan lokacin? “.
Hajiya turai cikin basar da zancen Habib d’in ta ce, “Habib wacece ta ke zaune a gida”.
Habib cikin rashin fahimtar abinda Mahaifiyarta shi ta ce,ya ce, “Mommyna bangane maganarki ba”. “Habib za kai min maganarta ka ko ta banza, tom wacece aka ce min Bilya ya kawo gidan da zama?, Habib ni fa ina tsoran abinda ya faru ne ya sake faruwa”.
Habib cikin kwantar ma Mahaifiyar shi hankali, dan yaga alamar ta tsorata sosai da abinda ya faru Kwanakin baya.
Habib cikin sanyin muryar shi, ya ce, “Mommyna Allah ban san da zaman kowa ba, amma ki bari zan yi bincike yanzu”.
Hajiya turai kashe wayarta ta yi.
Habib ko Mahaifiyar shi na kashe kiran, ya kira Number Bilya. Bilya na d’agawa Habib ya ce, “Bilya da kai da wadda ka kawo da kuma wadda ka ba ajiyarta, kuzo yanzu”.
Cikin bilya sai da ya yi k’ara jin abinda Habib ya ce, hakan yasa da sauri ya bar SANAT YOGHURT, ya koma can gidan Habib d’in.
Bilya tun kafin ya isa yakira Baba Lami awaya ya ce su had’u wajan get harda Yarinyar da yabata ajiya.
Bilya na zuwa suka ya iske Baba da Hassana wajan get d’in suna jiranshi.
Bilya kallan Baba ya yi, ya ce, “Baba Wallahi ban tab’a ganin muna fukai ba kamar ‘yan aikin gidannan ba, yanzu wai har an samu wanda ya kaima Oga Habib gulmar zaman Yarinyar nan agidannan, yanzu haka yana nai manmu mu dukanmu”.
Baba lami dafe k’irji ta yi, ta ce, “Bilya kasan Allah yaron nan korarmu zai yi”.
Bilya kallan Baba Lami ya yi, ya ce, “Baba ni ba abinda ke damuna ba yanzu kenan”.
Bilya a motar shi ya d’auki su Baba, zuwa SANAT YOGHURT.
Koda suka shiga wajan Hassana kallan sunan da ke d’auke da tank’ameman Company ta ke, da kuma tsaruwa irin ta gurin, ko ina ‘yan akine sanye da Uniform d’in su green and orange .
kasan cewar Habib ya san da zuwan su Bilya , hakan yasa kai tsaye suka shiga tank’ameman Office d’in Oga Habib.
Habib na zaune yana ta aikinsa a laptop d’in shi, yana jin su Bilya amma yaci gaba da aikinshi. Habib sai da yagama abinda ya ke yi, sannan ya d’ago kai yana kallan su d’aya bayan d’aya.
Habib mai da kallan shi ga Bilya ya yi, ya ce…………………..
Labari ne mai cike da CAKWAKIYA, ku dai ku bini asannu zaku fahimce ni nan gaba kad’an
DUk mai son kasan cewa a group d’in Oga Habib.Tom Comment dole ne ‘Yar’uwa.
In kinkaranta daure ki Comment.
COMMENT PLEASE
OGA HABIB
*︎ARUMAI ︎ WRITERS ︎SSOCIATION️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa*_
*(︎.︎.︎)*
RUBUTWA DA TSARAWA
FADILA SANI BAKORI(Faddy baby).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
My Facebook group:Fadila SANI
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
Ba kowane lokaci ne mutane za su fahimce ka ba. K’aramar k’wak’walwa ba ta gane manyan kalamai. Babban kifi sai babbar gora.
Allah kasa mu dace.
Shafi na 6&7.
….. Bilya wacece wannan?, Habib ya yi maganar ba alamun fara’a a fuskar shi.
Bilya cikin girmamawa ya fara magana, kamar haka, “Oga Habib ita ce Yarinyar da muka tsinta, kace in d’akko ta ranar da muka je kano”.
Habib wani banzan kallo ya yi ma Bilya, sannan ya ce,cikin fad’a-fad’a ” da nace ka d’akkota sai kuma nace ka kaita gidana!? “.
Bilya cikin alamun ban hak’uri, ya ce, “ka yi hak’uri Oga Habib, na aikata kuskure, insha Allah haka bazai sake faruwa ba”.
Habib banza ya yi da Bilya yaci gaba da typing d’in sakon da ya ke yi, a laptop d’in da ke gaban shi. Habib sai da yagama abinda yake yi, duk su Bilya na tsaye suna jiran sakamakonsu. Sannan ya d’ago kai ya kalli Bilya ya ce, “Bilya daga nan karku koma min gida ku dukanku”.
Bilya cikin tsorata da jin kalaman Oga Habib, duk da dai yasan zai iya ai kata hakan,Bilya ya ce, “Oga Habib dan Allah k…….. “.
Habib hannu ya d’agama Bilya, sannan ya nuna masu k’ofar fita”.
Baba Lami da sauri ta k’araso in da Habib ya ke, ta ce, “Oga Habib dan Allah ka yi hak’uri munsa…. “.
Habib ranshi a d’an b’ace ya nuna ma Baba lami k’ofa ya ce, “Baba dan Allah ku fitarmin Office! “.
Baba lami fita tayi tana mai da nasanin amincema Bilya da ta yi ta amshi Hassana, gashi abin ja mata kurarta aiki.
Bilya ya je dai-dai k’ofar fita ya tsaya, cikin taushin murya raunanna, ya ce,”Ka yi hak’uri Oga Habib da abinda zan ce maka. Oga Habib amma da kasan bazaka taimaki yarinyar ba, da baka sani na d’akkota ba, Oga Habib sanin kankane bani da gida, ni ba d’an garinnan ba ne, yanzu da kakoreni ina ita zan kaita?, da ace mun barta a’inda muka ganta da Allah zai kawo wanda zai tai maketa, amma mu tai makon da mu kai mata ya zamana bashida amfani. Oga Habib ita fa mace ce,Idan munbarta tatafi ina zata?, Oga Habib dan Allah ina rok’onka dan Allah idan ka koreni tom ita dan Allah ka yi k’ok’ari ka ci ka aikin alkairin da ka yi niyyaryi tun farko akanta. Inda dama kai kayi niyyar taima kon….”.
Habib katse Bilya ya yi, alamun ranshi ya fara b’aci da magan-ganun Bilya. Ba kamar maganar shi ta k’arshe ba, wai dama shi ya yi niyyar taimakon ta bashi ba. Habib wani banzan kallo ya yi ma Bilya sannan ya ce, d’an zafafe, “Bilya ni na ce maka zan taimaketa?, dama da nace ma ka ka d’auketa sai aka cema hakan na nufin agidana zata zauna kenan!? “. Habib ya tambayi Bilya cikin d’aga murya.
Bilya shima da yake sosai Habib ya b’ata mai rai, cikin k’ok’arin danne fushinshi, dan yasan in dai ya ce zai sa fushi tom Habib ba zai ya yi abinda ya ke so ba, gara ya yi hak’uri ya danne fushinshi. Hakan yasa Bilya cikin danne fushinshi ya ce, ” Oga Habib hak’uri za kai ka tai maka mata, dan na tambayi yarinyar garinsu in kaita, ta ce min ita marainiya ce, shine ma dalilin da yasa nakaita gidanka”.
Habib cikin had’e rai ya ce, “Sai aka cema kuma shi maraya bashi da ‘yan’uwa, kira min yarinyar”.
Bilya fita ya yi, ya iske Baba Lami da Hassana tsaye.
Baba Lami kallan Bilya ta yi, ta ce, “Bilya ya hak’ura ne? “. “Hmmm Baba wannan ne zai hak’ura da wuri haka bai wahalar da mutane ba. Ni Baba Lami dama abinda ke damuna wannan yarinyar ya nuna Hassana da ke tsaye, kuma shine yasa ni taimakonta, shine na ke son yasan yadda zai yi da ita inda shi ya yi niyyar tai makon dama bani ba, shine yanzu da nai mai complain akanta, shine ya ce in kira mai ita”.
Baba lami kallan Hassana ta yi, ta ce, “Je ki kinji Allah ya tai make ki, yabarki. Baba lami mai da kallanta ta yi ga Bilya ta ce, ” Bilya mufa? “.
“Baba Lami ki rabu da shi kinji, ni na san yadda zan mai, Hajiya turai ta yarda da ni sosai, kuma kinga kema ta yarda da ke, shiyasa ta zab’eki da ki rik’a yi ma Oga Habib girki, dan haka ki bari kawai nasan yadda zanyi, Allah dai yasa in nakirata ta d’aga”.
Ameen Baba Lami ta ce.
Bilya kallan Hassana ya yi da har yanzu ta ke tsaye ta k’i tafiya, ya ce, “Je ki Office d’in ce inda muka fito yanzu”.
Hassana ko da bata fatan k’ara ganin Habib, kallan Bilya ta yi, ta ce, “Dan Allah ni dai kutai dani inda zaku, ni bana son zuwa dan Allah “.
Bilya dariya ya yi, dan yaga alamar ta tsorata da Habib sosai. Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce, “kinga ni yanzu haka nasan ni da Baba zai mai da mu, saboda Mahaifiyar shi tana son mu, da ma ke nake ji, inda bazasu yarda ba ki zauna agidansu, dan yanzu suna tsoran bak’o saboda abinda ya faru da su kwanakin baya, ki yi hak’uri ki je, idan Allah ya taimaka, duk da Oga Habib shegen mutum ne, k’ila ya barki”.
Hassana a tsorace ta tura Office d’in Habib ta shiga, dan ita bata son wulak’anci kuma ta lura OgaHabib irin masu wula k’anta mutanan nan ne, saboda kud’insu.
Habib na zaune yana mai cigaba da typing d’in da ya ke a laptop d’in shi, kayan da za’a kawo masu ne ya ke ta aikin lissafawa. Habib na zaune ya ji anturo k’ofa anshigo ba naiman izini ba komai. Habib d’ago kai ya yi yana mata kallan baki da hankali ne, Banza Habib ya yi da ita, ya ci gaba da typing d’in shi ya barta nan tsaye.
Hassana ko magana ta ke son yi tana tsoro dan taga Bilya ma yana mai fad’a bare ita. Hassana jin ya yi banza da ita babu alamunma zai gama abinda ya ke yi bare har ya yi mata magana. Hakan yasa ta ce,cikin rawar murya, kamar yadda ta lura kowa na cewa, “Oga Habib dama Oga Bilya ne ya ce min kana kirana”.
Habib ko cigaba da aikin da ya ke yi ya yi kamar bai jita ba, bamu ma wata ala da ta nuna mata yaji abinda ta ce, hakan yasa ta kuma cewa, “Oga Habib dama Oga bilya ne ya ce min inzo kana son gani n…… “.
Tsawar da Habib ya yi mata ce yasa ta yi shiru, cikin d’aga murya Habib ya nuna ta da d’an ya tsa, ya ce, “get out from my Office “.
Hassana fita ta yi jikinta na rawa, dan sosai ta tsorata da tsawar da Habib ya yi mata.
Hassana inda tabar Baba lami da Bilya ta je, amma bata gansu ba. Hassana guri ta samu ta zauna ta yi shiru kamar za tai kuka, tabbas tun yanzu da ba aje ko ina ba, ta fara da na sanin barin gida. Hassana na nan zaune tana kallan ma’aikan gurin kala-kala sai aikinsu suke, can wani d’aya daga cikin staff d’in gurin wanda tun d’azu ya lura da Lokacinda Hassana ta fito daga Office d’in Oga Habib. Inda Hassana ta ke tsugunne ya zo ya sameta, kallan Hassana ya yi, ya ce, “Bai war Allah lafiya kuwa? Nalura da ke tun d’azu keke gurinnan. Idan aiki kika zo naima aiba Office d’in Oga zaki ba, gurin manager zaki”.
Hassana d’aga kai ta yi tana kallan shi, sannan ta ce, “Ni ba aiki nazo naima ba, amma inna samu aikinma zan yi”.
“Ok, amma dan Allah ko zan iya sanin mekika zo naima, in ba aiki ba? “.
Hassana kallan shi ta yi, sai taji bata da zab’i kamar ta fad’a mai, inda taimo ta ke naima k’ila ya tai maketa. Hakan yasa Hassana ta kallai, ta ce, “Bansan kowa ba a nan Abuja, su Oganku suka tsinceni ahanyarsu ta tafiya kano,suka kawo ni nan, shine yanzu shi Wanda ake kira da Oga Habib, wai bazan zauna agidan shiba, shine shi Oga Bilya ya ce in je Office d’in shi ya na kirana, tom na je kuma ya Koreni”.
murmushi ya yi, staff d’in nan, ya ce, “Bilya ai ba wani bane staff ne kamar kowa anan, dan dai shi yana driving d’in Oga Habib ne, kuma in dai Oga Habib ne ya ce yana kiranki a Office d’in shi zai saurareki, sai dai in da kika je ne, kin mai ba dai-dai bane. Kuma maganar gaskiya in ma komawa kikayi ki mai magana kan ya d’aukeki aiki, amma maganar gaskiya Oga Habib ba zai kaiki gidan shiba, dan gidansu akwai tsaro sosai. Idan harshi ya ce kije, ki tashi ki koma ki je zai saurareki, in da yasan da zuwanki”.
Hassana tashi ta yi ta nufi office d’in Oga Habib, saboda bata da zab’in da ya wuce ta tashi ta je d’in.
Staff d’in nan kallan Hassana ya yi da tausayawa, dan mata masu ajima Oga Habib ba saurararsu ya ke ba bare ita.
Habib na zaune yana waya da Mommynshi, Hassana ta yi sallama ta shigo.
Habib kallo d’aya ya yi mata ya d’auke kanshi ya ci gaba da wayar shi. Jinai Habib na cewa, “Mommyna dan Allah ki barsu kawai, idan mutum na laifi irin haka ya kamata ai funishiment d’insa. Banajin abinda akecewa daga can b’angaran, sai dai naji Habib ya ce, “Ok, Mommy zasu dawo, amma ni idan tanine ma nafi son inyi driving d’in kaina. Abinci kuma ki rabu da Baba Lami inda ga Baba dije nan”.
Mahaifiyar Habib sosai ta nuna ma Habib in dai bai dawo da su bilya ba ranshi zai b’ace. Tana kaiwa nan ta kashe wayarta.
Habib ranshi b’ace ya kira bilya awaya, kira d’aya bilya ya d’aga, yana d’agawa Habib ya ce, “Bilya kazo Office d’ina yanzu”.
Habib mai da kallan shi ya yi ga, Hassana da ke gefa tsaye arakub’e.
Doguwar rigar da Likitarnan ta bata ce har yanzu ajikinta, sai wani haif hijab da tasa.
Habib d’auke kai ya yi daga kallanta, sannan bazato ba tsammani Hassana ta ji ya ce, “Ke ‘yar wata jaha ce?,kuma me yarabo da ke daga gidan ku? “.
Hassana kallan Habib ta yi taga ba’ita ya ke kallo ba hankalinsama akan laptop d’in gabansa ya ke, ba akanta ba. Hassana muryarta na cracking ta ce, “Ni yar kano ce, mamana da babana duk ‘yan jahar kano ne, Babana nada mata biyu. matar Babana tana da fad’a sosai, kuma macece mai son kanta da yawa. Babana tunda ya auri mamana Allah bai bata haihuwa ba, hakan yasa kakata wato Mahaifiyar Babana ta matsama Babana ya k’ara aure. Babana ya auri Umma Rabi ba dad’ewa Allah ya bata ciki ta haifi Aunty jamila, sai da Umma Rabi ta haihu uku sannan Allah ya ba Mamana cikina, tom kuma itama Umma Rabi lokacin tana da ciki, kusan tare sukayi rainon ciki ita da Mamana. Mamana ta haihu da kwana biyu Umma Rabi ma ta haifo yarinyarta mace. Hakan yasa Babana ya ce, sai dai ahad’a sunan mu.
Tom Mamana dama tunda ta haifeni bata da isassar lafiya, hakan yasa kwanana biyar aduniya Allah ya yi ma Mamana rasuwa. Babana sosai hankalinsa ya tashi da mutuwar Mamana saboda yafi jin dad’in zama da ita fiye da Umma Rabi. Tom mamana da ma ita ma ita kad’aice awajan Iyayanta kuma Allah ya yi masu rasuwa dad’ewa, hakan yasa Babana badan ya soba sai dan bashi da yarda zai yi ya d’auke ni ya ba Umma Rabi ni, ya ce ta had’amu ta shayar damu tare da ‘yarta.
Da da farko Umma Rabi ta Nuna ma Babana baza amsheni ba, amma sai Babana ya nuna mata dole ta amsheni, in da bai san Wanda zai kai ma niba. Hakan yasa dole Umma Rabi ta amsheni. Ranar suna Babana ya sa mana Hassana da Usaina ni da yarinyar Umma Rabi. Nasha wahala sosai awajan Umma Rabi dan ko kuka nake sai taga dama ta ke ban nono insha. Kuma koda zan riga Usaina tashi in dai Usaina ta tashi tom Umma Rabi sai ta d’auki Usaina ta lallasheta ta yi shuru sannan koda zata kulani.
Ahaka har muka girma. Tunda nafara wayau na fahimci Umma Rabi tafi son Usaina akaina. Babana dawuri ya samu Islamiya, ita Usaina bata cika zuwa ba saini, saboda ni kona ce ba zani ba dole za’a turani. Tun ina ‘yar k’arama ta na iya duk wani aikin gida, dan hatta wankinmu Nida Usaina ni ke mana, acewar Umma Rabi ni ce babba.
Babana duk lokacin da zaizo gida ya iske ina aiki sai yi ta fad’a ya ce Usaina tazo muyi tare. Wannan abinda da Babana ke yi shiya k’ara jawo min tsana sosai gurin Umma Rabi.
Ahaka rayuwa taita tafiya har muka girma , muka shiga secondary school. Tom da akwai wani teacher mu, wanda ya ke kula da duk abinda ya shafemu Nida Usaina, sai dai yana yawan yi min complain, akan wai Usaina ta fi ni tsafta, ni dai ban tab’a fad’amai wani abuba game da gidanmu, shine ya tsinto labari acikin gari. Tunda teacher Kabir ya tsinci labarin halinda nake, ya zamana yake yawan yimin kyautar kud’i. Sosai teacher Kabir ke min hidima hakan yasa har Babana ya sanshi.
Muna gama j. S. E. Babana ya ce, bazamu cigaba da karatuba aure zai mana. Tom dama ita Usaina akwai wini dake zuwa gunta harma ya yi ma Babana magana, ni kuma dama teacher Kabir shike Sona shima ya naimi izini gurin Mahaifina ya kuma bashi. Lokacin da Babana ya je ma da teacher Kabir maganar ya turo manyasa gidanmu ai maganar aurena da teacher Kabir . Teacher Kabir rok’on Babana ya yi akan dan Allah ya barni in kamma secondary school sannan. Kasan cewar Babana na son tarayyata sosai da teacher Kabir yasa ya yarda da abinda teacher Kabir ya ce. Koda Babana ya kaima Umma Rabi maganar saina kamma secondary school sannan za ai aurena, cewa ta yi itama Usaina abarsa sai ta kammala sai ayi duka tare. Aiko haka akayi. Muna S. S. S 3 first term, Babana ya sa ranar aure na da Teacher Kabir. Ita kuma Usaina da wani Jamilu d’an layinmu. Umma Rabi bata son tarayyar Jamilu da Usaina ko ka d’an bakamarma da taga teacher Kabir na min hidimaba sosai, ita kuma Usaina babu abinda ke shiga tsakaninta da Jamilu na kyauta. Da akwai wata rana teacher Kabir ya kawo min waya. Wannan kyautar da ya yi min tab’ata ma Umma Rabi rai sosai,hakan yasa tace sai dai in maida mai wai in ya auran ya sai min agidansa. Babana koda yazo yaji abinda Umma Rabi ta ce hanawa ya yi in maida ma teacher Kabir wayar shi”. Hassana shiru ta yi, tana goge hawayanta saboda wani kuka da ke son k’wace mata, saboda tunowar rabuwarta da teacher Kabir ta k’arshe da ta yi.
Hassana cikin murya mai kama da ta kuka taci gaba da magana kamar haka, “Ranar da bazan mantataba arayuwata, ita ce ranar wata laraba, Iyayan teacher Kabir suka zo gidan mu wai d’ansu Kabir ya janye maganar auran shi dani ya mai da ta kan Usaina. Bani ba har Babana ya girgiza da jin haka, mamaki da al’ajabi suka cika shi, saboda shi kanshi asanin kanshi Kabir bama sa wani jutuwa da Usaina, sai yau rana tsaka wai ace Kabir ya janye maganar auran shi da Hassana ya maida kan Usaina. Babana cema Iyayan teacher Kabir ya yi tom su bari zaiji daga bakin Kabir d’in sannan. Aiko haka akayi Babana kiran teacher Kabir ya yi ya tambayai ya akan maganar da Iyayanshi suka zo da ita”.
Bud’ar bakin teacher Kabir sai cewa ya yi, “Eh hakane shi Usaina ya ke so”.
Wannan maganar sosai ta d’aga hankalin Babana. Washe gari da safe Babana ranshi b’ace ya je d’akin Umma Rabi. Babana nazuwa ya kalli Umma Rabi, ya ce, “Rabi ina son kisan wani abu duk k’ula-k’ular da kika yi, ki ka maida auran Hassana ya koma kan ‘yarki tom tun wurima ki warware shi, dan ni bazan tab’a aura auran Usaina da Kabir ba, garama kisani tun wuri.
Haka Babana ya gama fad’anshi Baba Rabi bata tanka mai ba.
Abu kamar wasa yazo ya zamana gaske, dan teacher Kabir idan yazo gidanmu sai inga Usaina taje suna hira, ni ko ko gaisuwata baya amsawa. Abin ya daman Sosai, hakan yasa na kaima Babana k’arar teacher Kabir. Babana kallona ya yi cikin alamun tausaya min, dan ya lura ina son teacher Kabir sosai. Hakan yasa Babana cikin lallashi, ya ce, “Hassana kinsan dai wani baya aurar matar wani ko?, haka kuma wata bata auran mijin wani, inji hausawa sunce matar mutum kabarinsa. Tom Hassana dan Allah karki tambayan dalili dan nima ban sani ba, amma ina so ki hak’ura da Kabir “.
Wannan magana da Babana ya fad’a ji nai kamar ya lumamin wuk’a azuciya, dan Allah ya sani ina son teacher Kabir sosai, kodan shine saurayina na farko.
Kuka na fashema Babana da shi jin abinda ya ce.
Babana duk wata magana mai dad’i da zai fad’amin wadda zata sa in yi shiru ya fad’amin, amma ina na kasa. Sosai kukana ya d’agama Babana hankali. Ni ko kafin kace me sai ciwan kai tsabar kukan da nayi haka kaina ya yi ta min ciwo. Aranar dai da ciwan kai na kwana.
Iyayan Kabir ko sun yi ake kamar me akan Babana ya maida auran Hassana da Kabir kan Usaina ya k’i.
Umma Rabi ko ganin Babana yak’i amsar maganar Usaina da Kabir, yasa taturasu wajan k’aninta. Tom da ya ke shima k’anin nata gashi ga irin shi. Hakan yasa batare da binciken komai ba, ya amshi maganar, nan dai ya yi jagoranci aka tsaida ranar auran Usaina da Kabir, wata biyu masu zuwa.
Wannan ranar nayi kuka kamar raina zai fita. Wannan kukan da nayi sosai ya tadama Babana hankali. Kafin kace me hawan jinin Babana ya tashi. Washe gari da safe shiri-shiru Babana be ne meniba. Hakan yasa na lallab’a na tashi dan kaina sosai ya ke min ciwo. Ina tashi d’akin Babana natura nashiga. Ganin Babana kwance kuma harna tura d’akin bai tashi ba, yasa na k’arasa gun shi ad’an tsorace. kiran sunan Babana nayi ina bubbuga k’afarshi amma shiru. Kuka na fasha dan duk da ban san Mutuwa ba jikina ya bani kamar babu rai ajikinsa. Babana ya tafi yabarni yatafi in da bazan sake ganinsa ba. Haka akai zana’izar Babana.
Nayi kuka sosai dan Babana shine abokin shawara, shine abokin firata idan yana gida, shine wanda abu in yasaman nake fad’amawa sai ko teacher Kabir, tom shima anrabani da shi.
Bayan wata d’aya da rasuwar Babama, abubuwa sun cakud’e min, ga aiki na gidan duk ni ke yi, wanke-wanke, shara, girki, wankin kayan mu.
Ana gobe d’aurin auran teacher Kabir da Usaina na gudu saboda zuciyata bazata iya jure ganin auran teacher Kabir da wata ba, ba ni ba…………
idan dai kin karanta daure ki yi Comment ‘yar’u.
More comment more typing
OGA HABIB
*︎ARUMAI ︎ WRITERS ︎SSOCIATION️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa*_
*(︎.︎.︎)*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
Abokai na gaskiya suna da wuyar samu, suna da wuyar bari, suna da wuyar mantawa. Allah ka had’amu da abokai na gaskiya.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
My Facebook group Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
Shafi na 8&9.
Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, Oga Habib, wannan shine dalilin da ya sa, nahad’a kayana dadaddare na gudu, batare da kowa na gidanmu ya sani ba. Koda na fita gida lokacin duhu ya yi sosai. Tafiya nake amma ban san ina zani ba, ga duhun dare ya farayi, gashi tsakaninmu da titi akwai nisa sosai, haka na kama hanya ina tafiya ina sauri ga damuwa da tayi min yawa, ga yunwa rabona da abinci harna manta, sai dai in naji yunwa ta daman in dama kunu insha. Damuwa da yunwa da gajiyar da na yi ce, tasa na yanke jiki na fad’i ban sani ba, shine kuka tsinceni ainda kuka gani”. Hassana kallan Habib ta yi, ganin har yanzu bai fasa typing d’in da ya ke yi ba. Ita fa gani ta ke kamarma duk surutannan tana yin shine kawai amma bajinta ya ke ba. Hassana kallan Habib ta kuma yi, cikin fargaba ta ce, “Oga Habib Wannan shine da lilin barina gidanmu”. Hassana ta yi maganar da dad’ewa , dan hattacire ran Habib zai bata amsa ma.Sannan zuwa can ya d’ago kai yana kallanta, sai da Habib ya gama yima Hassana kallan cin mutunci sannan ya ce, “ya sunan ki ma kika ce? “. Hassana bakinta harrawa ya ke wajan ba Oga Habib amsa da cewa, “Hassana”.
Habib Kallanta ya yi, ya ce, “Hassana ke ba abin tausai ba ce, idan ke abin tausai cema tom ni ban tausaya miki ba, kuma ni bazan tai makeki ba. Duk wadda ta gudu daga gidan Iyayanta tom yawan bariki ta fito, dan haka fitar min daga office “. Habib ya fad’i maganar cikin d’aga murya. Jikin Hassana rawa ya farayi dan sosai ta tsorata da Habib.
Hassana kuka ta farayi, cikin muryar kuka ta ce, “Oga Habib dan Allah ka yi hak’uri, Wallahi bayawan bariki na fito yi ba, kona zauna gidan b…….. “. Tsawar da Habib ya yi ma Hassana ce tasa ta yi shiru.
Habib nuna mata hanyar fita ya yi da hannu, ya ce, “fitar min daga Office na ce, stupid kawai! “.
Hassana da saurin ta har tana d’an tintib’e ta fita daga office d’in. Saura kad’an Hassana su yi karo da Bilya shi kuma lokacin yazo shigowa.
Bilya da d’an damuwa ya bita da kallo dan duk da bai san labarin yarinyar ba, sosai ta ke bashi tausai, acewar shi yarinya k’arama haka ace bata san ina zata ba. Bilya cikin tausan Hassana ya k’arasa office d’in Oga Habib.Bilya cikin girmawa, ya ce, “Barka da hutawa Oga Habib, ka yi hak’uri dan Allah ka kirani banzo da wuri ba, bana kusa ne”.
Habib kallan Bilya ya yi, sannan ya ce,fuskar shi a d’aure, alamun ranshi ab’ace ya ke. “Bilya me yasa ka kai k’arata wajan Momyna”. Habib ya yi maganar cikin d’aga murya, dan shi aganinshi bai kamata ace yaron shiba, wanda ya ke ci ak’ark’ashin shi ya zartar da hukunci akanshi ace ya kai k’ararsa wajan mahaifiyarsa ba.
Bilya cikin kame-kame ya ce, “Oga Habib ba…… “. Habib d’agama Bilya hannu ya yi, ya ce, “ka adana kala manka, amma kabar kama k’afa da son da Mahaifita kema, dan kar hakan yasa kaji zaka iya yin koma, wannan shine last worning da zanma, duk sanda ka sake ma hajiya complain akaina, daga ranar Bilya kabar aike a k’ark’ashin Sanat yoghurt”. Habib na fad’in haka ya kalli Bilya, ya ce, ” Bilya da kai da Baba Lami na baku, suspension na one month”. Bilya da alamun tsoro ya d’ago kai yana kallan Habib, jin wai ya da katar da shi har wata d’aya.Bilya magana zai yi Habib ya nuna mai hanyar fita.
Fita Bilya ya yi, batare da yace ko mai ba. Bilya na fita ya iske Hassana can bakin get d’in wajan tsaye, ta yi shiru ita kad’ai. Bilya gurinta ya k’arasa, kallanta ya yi sannan ya ce, “korarki ya yi ko? “. Hassana kai ta d’agama Bilya.
Bilya shiru ya yi sannan, ya ce, ” Ni Wallahi duk namarasa abinda zance miki, ni kaina yanzu haka ya dakatar dani aiki harna tsawan wata d’aya, ga aurena saura wata biyu masu zuwa, ni kaina yanzu kinga in da munyi haka dashi ba damar in kwana gidansu sai dai in koma d’akin abokina da kwana. Tom kuma itama Baba Lami bata san kowa ba a Abuja, kuma kinga ya dakatar da ita aiki itama, yanzu na san sai dai ta koma garinsu. Bilya shiru ya yi, yana tunanin yadda zai yi da Hassana amma bai sani ba,hakan yasa, ya ce, “Hassana ni yanzu ma kaduna zan tafi, ki zauna nan anjima kad’an zaki ga manager ya fito, zaki ganshi da red d’in shirt da black jeans. Ki mai magana, in dai ya amince ya d’auke ki aiki shikenan, Oga Habib babu ruwansa da d’aukar ma aikata”.
Hassana kallan Bilya ta yi, ta ce, “Tom Oga Bilya, wajan kwana fa?, in ya d’aukeni aikin? “.
Shiru Bilya ya yi dan shi yama manta da wajan kwana sai yanzu ya tuna. Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce, “Hassana ki ci gaba da zama nan, idan kika ga Oga Habib ya fito, ki je ki sa ke rok’anshi, k’ila ya amince”. Bilya na kaiwa nan, ya yi ma Hassana fatan alkairi ya tafi.
Hassana cigaba da zama ta yi kamar yadda Bilya ya ce mata, tana jiran fitowar Oga Habib. Hassana har 8:00pm tana gun zaune, tana jiran taga fitowar Oga Habib amma shiru, Hassana tunini ta rik’ayi k’ilama ya tafi bata sani ba, inda ta je sallah. Wata zuciyar ta ce mata, tom idan ko haka ne ina zata kwana,uhm tom wai in ma naganshi lallene ya taimakan d’in. Hassana na cikin wannan tunanin taga motar Oga Habib ta fito. Hassana da saurinta har tana tuntub’e ta matsa wajan motar Habib d’in, shikuma lokacin ya tsaya yana ma mai gadin gun magana.
Hassana ko kafin tak’arasa Habib ya yi ma motar shi key. Hassana tsabar furgici da rashin sanin yadda za tayi, kawai sai ta zauna gun tana kuka.
Hassana na nan zaune tana kuka kamar wata ta b’abb’a, manager gun ya fito domin tafiya gida. Tsayawa ya yi ganin mutum a zaune, kuma bisa ga alama kamar kuka ya ke ji. Tsayawa manager ya yi ya fito daga motarshi, inda Hassana ta ke zaune tana kuka ya k’arasa. Tsananin hasken gun yasa tun kafin ya k’arasa ya k’are mata kallo. Kallanta ya yi da kyau sannan cikin siririyar muryar shi ya ce, “ke lafiya?, zaki zo nan ki zauna da daddarannan? “. Hassana da sauri ta d’ago kanta tana kallan manager. Manager ko jin Hassana ta yi shiru tana kallan shi, ya sa ya k’ara cewa, “, ke bakya ji ne! ? “. Ad’an tsawace ya yi maganar.
Hassana kallan Manager ta yi, cikin muryar kuka ta ce, “Bansan ina zani ba ne”. Manager da mamaki ya kalli Hassana, ya ce, “kamar ya baki san ina zaki ba?, tom waya kawoki nan? “.
Hassana kai tsaye batare da tunanin komai ba, ta ce, “Oga Habib ne ya tsinceni shida Oga Bilya, shine ya kawo ni nan, ni kuma bansan kowa ba a Abuja, kuma ya hana in sake zuwa mai gida”. Hassana ta idasa maganar cikin kuka.
Manager shiru ya yi yana mai ci gaba da kallan Hassana, dan shi gaba d’aya bai gane takan maganarta ba. Manager waya ya ciro ya kira Oga Habib.
Kira d’aya Habib ya d’aga yana tambayar manager lafiya, dan manager bai cika kiran shi airin wannan lokacin ba.
Manager ko Habib na d’agawa ya ce, “M. D. Dama wata Yarinya ce nan na gani wajan get zaune tana kuka, shine dana tambayeta ta ce min wai kaika kawota, ni dai gata nan bama wai gane kan zancan nata nayi ba”.
Habib ba tare da tunani wata yarinya ba ce, dan in yaga dama yanada girki. Habib shiru ya yi sannan ya ce, “Manager kawo ta nan gida”. Habib na cewa haka ya kashe wayarshi.
Manager ko kallan Hassana ya yi, ya ce, “zo mu je”. Hassana motar manager ta shiga. Manager gidan Habib ya kai Hassana kamar yadda Habib ya ce mai, ya kawo ta.Daya ke duk masu gadin gidan sun san Manager hakan yasa suna ganin shi suka bud’e mai get d’in ya shiga. Manager direct falon Oga Habib ya nufa, Hassana na biye da shi, sai kalle-kalle ta ke. Hassana azuciyarta ta ce, “Tabbas dole Oga Habib ya yi wulak’anci, ga kyau, ga kud’i, ga ilimi”. Manager ko da ya je bakin k’ofar Habib nocking ya yi.
Kasan cewar Habib ya san manager ne ya sa, ya ce, “yashigo”.
Manager shiga ya yi, da Hassana da ke biye da shi.
Hassana sosai ta rud’e da had’uwa irin ta falon Oga Habib. Ko mai na falon milk & Orange ne.
Habib ko kallo d’aya ya yi ma Hassana ya gane ta. Hakan yasa cikin d’an fad’a ya ce, “Manage dama wannan yarinyar ce? “. Manager cikin girmamawa ya ce, “M. D, ita ce”.
Habib kallan manager ya yi ya ce, “Manager me za ayi mata? “. “Tom M. D, nima dai ban sani ba, amma idan na fahimce ta kamar bata da wajan zama ne”. Manager kallan Hassana ya yi, ya ce, “Dame za a tai maka miki? “. Hassana cikin sanyin muryarta mai cike da rauni ta ce, “Dan Allah aiki nake so kuban, sai kuma gurin da zan rik’a kwana”. Manager kallan Oga Habib ya yi, sai yaga Habib ya d’auke idon shi akan shi. Hakan yasa manager ya ce, “Shikenan za ki rik’a mana swapping & mopping, morning &evening , zaki iya?” Manager ya kalli Hassana yana tambayarta.
“Eh zan iya “. Cewar Hassana.
Manager batare da tambayar Habib ba dan yasan in dai ya ce Habib zai tambaya, tom ba abin cewa zai yi ba, amma in ko ya riga ya yanke hukunci ya san sai dai ya yi mai tsiya daga baya. Hakan yasa manager ya ce, “Shikenan wajan kwana kuma sai ki rik’a kwana site d’in ‘yan aikin gidan nan”. Hassana cikin jin dad’in abin Manager ya ce, ta ce, “Nagode sosai, Allah ya saka maka da alkairi “. “Ameen”. cewar manager. Manager Kallan Habib ya yi jin bai ce komai ba, hakan yasa manager Kallan Hassana ya ce, “Biyo ni in nuna miki site d’in worker’s d’in gidan.
Shi dai Habib na jin manager bai ce mai ko mai ba. Haka manager da kan shi ya kai Hassana b’angaran masu aikin gidan. Bayan ya kaita ne, ya koma yima Oga Habib sallama.
Habib kallan manager ya yi, ya ce, “Manager ya zama First and last, ban hanaka d’aukar staff ba a company, amma ba dai zama nan ba, dan duk wata worker da ka gani agidan nan, Hajiya kawai suke ma aiki, amma ba Company ba”. Manager hak’uri ya ba Habib, sannan ya ce, “Insha Allah, M. D, haka ba zai kuma faruwa ba, wannan ma tausai ta ban, ganinta mace bahaushiya da nayi, kuma daga ganinta tana buk’atar tai mako, amma ka yi hak’uri “. Banza Habib ya yi da shi.
Manager tafi ya yi, dan ya san fushin kafin gobe ne, Oga Habib akwai saurin fushi, amma kuma baida wuyar sauka.
Hassana ko da ta k’arasa b’angaran masu aikin, cikin girmawa ta gaida su, sai dai duk kansu wani irin kallo suke ma Hassana.Hassana cikin tsarguwa da kallan da suke mata ta gaidasu,.
D’aya daga cikin su ce, ta ce, ma Hassana, “Baiwar Allah daga ina? “. “Nima ma aika ciyace kamar ku, sai dai ni ba acikin gidan nan zan rik’a aiki ba, a Sanat yoghurt zan rik’a aikina”. Da mamaki dukkan su suka kalli Hassana, dan su aiya saninsu ‘yan aikin gidannan ne kawai Hajiya turai ta yadda da su zauna anan. Wata wadda ake kira Jimmai daga cikin su, kallan Hassana ta yi, ta ce, “Baiwar Allah waye ya kawo ki gidannan? “. “Oga Habib”. Hassana ta basu amsa kai tsaye , dan ta gaji da tambayoyin da su ke mata. Hassana guri ta samu d’an nesa da su ta kwanta, dan ta gaji sosai dan ma Allah ya tai maketa ta yi sallarta.
Hassana kallan ma’aikatan gidan ta ke tana mamakin tom aikin me sukeyi haka, suke da yawa. Hassana kwanciya ta yi, tana kwanciya bacci ya d’auketa. Ma’aikatan gidan Hajiya turai sun sabo tun k’arfe shida na safe kowa ke tashi ya yi aikin da ya ke mazaunin nata. Hassana ko saboda gajiya kasa tashi ta yi.
Jimmai wadda ta ke kusan sa’a da Hassana zuwa ta yi, ta bubbuga Hasana da ke kwance tana baccin gajiya. Hassana bud’e ido ta yi tana kallan jimmai.
Jimmai ma kallan Hassana ta yi, ta ce, Baiwar Allah ki tashi hakanan, ki yi sallah mana.
Hassana tashi ta yi tana kallan jimmai, ta ce, “Dan Allah ina make wayinku? “. Jimmai hannun Hassana ta kama ta ce, “muje in kai ki.
Jimmai har toilet d’in su na ma’aikatan gidan ta kai Hassana sannan ta juyo ta dawo. Hassana da sauri ta yi sallah sannan ta kalli jimmai ta ce, “Dan Allah idan zani Sanat yoghurt, idan zan hau keke napep ina zan ce? “. Jimmai kallan Hassana ta yi, ta ce, “amma dai ke ba ‘yar garinnan ba ce ko? “. “Eh ni ba ‘yar nan ba ce “. “Ok, in kin samu keke napep ki ce zone, e nepar Sanat yoghurt duk wanda ya ke garin Abuja ai yasan sanat yughurt, za akaiki, har Sanat yoghurt. Hassana godiya ta yi ma Jimmai sannan ta kalli jimmai ta ce, “Dan Allah ko zaki ranta min kud’in keke napep d’in zan bi yaki, wallahi banda ko sisi”. Jimmai kallan Hassana ta yi da tausayawa ta ce, “Nawa zan baki? “. “Nawa su ke kaiwa? “. Hassana ta tambayi jimmai.
Jimmai d’ari biyu ta ba Hassana ta ce, “Gashi D’ari biyu ne ai ba nisa”. Hassana amsa ta yi taima Jimmai godiya. Hassana har ta juya zata tafi Jimmai ta kirata ta ce, “Ba dai da kayan jikinki zaki tafi ba ko? “. Jimmai ta tambayi Hassana ganin kamar da kayan jikinta zata tafi.Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, “Banda kaya haka nazo ni kad’ai “. Jimmai kallan Hassana ta yi, ta ce, “Ya su nan ki ne?, kuma dan Allah ko zan iya sanin labarinki”. Hassana ji tai zuciyarta ta aminta da Jimmai hakan yasa ta ce, “Sunana Hassana, kallo d’aya nai miki sai naji zuciyata ta aminta da ke, dan haka zan baki labarina amma ba yanzu ba, yanzu ina sauri zan tafi”. Hassana na kaiwa haka ta juya zata tafi. Da sauri Jimmai ta kamo hannun Hassana ta ce, “Duk da baki ne mi sanin Sunana ba, Sunana Jimmai, idan ba zaki damuba kirik’a sa kayana kafin ki samu naki”. Hassana sosai ta ji dad’in abinda jimmai tai mata, dama sosai ta ke jin kunyar fita da kayan jikinta dan sunyi datti sosai.
Jimmai ko ta kurama Hassana ta yi tai wanka ta yi break fast sannan tata fi.
Lokacin da Hassana ta isa sanart yoghurt, lokacin k’arfe goma na safe, ita da aikinta sharane da goge-goge su da ake buk’atar su je da wuri kafin kowa ya je dan su yi aikinsu. Hassana na shiga gurin ta na cin karo da manager. Sosai Manager ya yi ma Hassana fad’a akan zuwanta lale da ta yi, bayan yagama yi mata fad’ane ya mik’ama mata file d’in hannun shi, ya ce, ta kai Office d’in Oga Habib.
Hassana tsayawa ta yi, tana kallan file d’in, sannan manager ad’an tsawace ganin bata amsa ba, ya ce, “Ki amsa mana ki kaima Oga Habib, ki ce mai ya yi marking d’in abubun da muke buk’ata “. Hassana amsa ta yi dan bata da yadda zata yi, amma bata so har ta gama aiki agurinba ta kuma shiga office d’in Oga Habib. Hassana cikin sanyinta ta tura k’ofar office d’in Habib ta shiga.
Habib ko alokacin ya na kishingid’e kan sit, ya ji anturo k’ofar Office d’in shi an shigo…. …………
https://mynovels.com.ng/sabbin-kalaman-soyayya-na-samari-da-yan-mata/
PLEASE
COMMENT &
SHARE.
OGA HABIB
*︎ARUMAI ︎ WRITERS ︎SSOCIATION️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa*_
*(︎.︎.︎)*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
Mak’iyanka mutane uku ne:Mai k’in ka, da mai k’in masoyinka, da mai son mak’iyinka. Mai son uwa dole ne ya so d’anta. Allah ka had’amu da masu son mu fisabilillahi.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK’R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D’AN TARKU DA HAZIK’AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD’UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K’AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK’E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K’OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN
K’ABILA CE! K’ABILA CE!! K’ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K’ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D’AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K’ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT
08142904255.
Shafi na 10&11
Habib da kallo ya bi Hassana da shi.
Hassana ko cikin da burcewa da kallan da ya ke mata, ya sa ta mik’a mai file d’in hannunta, ta ce, “Oga Habib ga shi inji manager ya ce ka yi marking d’in abubun da ake buk’ata”. Hassana ta idasa maganar muryarta na rawa.
Habib amsar file d’in ya yi, batare da ya kalli ko inda ta ke. Habib na amsar file d’in Hassana ta juya da saurinta tafita office d’in.
Hassana na fita office d’in Habib ta had’u da wata staff itama agun ta ke aiki, amma ita tana cin masu programme d’in sanat yoghurt. Hassana da sauri ta k’arasa gunta ta ce, “Baiwar Allah dan Allah tambaya na ke? “. Wadda Hassana ta kira da ke, juyowa ta yi tana ma Hassana wani kallan lafiya.
Hassana itama kallanta ta yi, azuciyarta ta ce, kai gaskiya ‘yan aikin gunnan suncika ji da kai, sai kace wasu masu aikin banking. Ita ko staff d’in nan jin Hassana ba ta ce mata ko mai ba, ya sa juya ta cigaba da tafiyarya zuwa inda zata. Hassana ganin ta tafi ta barta gun tsaye da sauri tasha gabanta, ta ce, “Yi hak’uri dan Allah office d’in manager na ke nema? “. Wani irin kallo ta ke ma Hassana dan ita bata tab’a ganin Hassana ba a ma’aikatar nan ba. Hakan yasa ta kalli Hassana ta ce, “Wacece ke? “. Hassana batare da tadamu da irin kallan da ta ke mata ba, ta ce, “Ni new worker ce a factory nan”. Da hannu ta nuna mata office d’in manager ta juya tayi tafiyarya. Hassana ko kanta a k’asa ta juya ta nufi office d’in manager. Hassana na zuwa cikin girmamawa ta gaida manager dan tana ganin girmansa sosai, tai makon da ya yi mata. Hassana kallan manager ta yi, ta ce, “Oga Manager dama bansan site d’in da zan rik’a mopping bane”. Manager kallan Hassana ya yi, ya ce, ” supervisor zaki ma magana. Ki ji Office d’in kusa da nawa ita zata fad’a miki site d’in da zaki rik’a morpping d’in”. Hassana fita ta yi daga Office d’in manager ta shiga office d’in ku sa da na shi.
KyKkyawar budurwa ce, a ganinda nai mata baza ta wuce twenty five years ba. Zaune ta ke tana ta aikin dan na laptop d’in da ke gabanta. Hassana cikin girmamawa ta ce, “Barka da aiki Aunty”. Da sauri Billy ta d’ago tana kallan Hassana jin sunan da ta kirata da shi. Cikin b’acin rai Billy ta ce, dan ita jin kanta ta ke kamar wata ‘yar seventeen years. Hakan yasa cikin d’aga murya Billy ta ce, “Uwar ki ce Aunty “.dan ita aganinta Hassana kallan girma tai mata shiyasa ta kirata da Aunty.
Ita ko Hassana girmamata ta yi.
Hassana cikin girmawa ta ce, “Yi hak’uri dan Allah, ban sanda sunan da zan kiraki da shi bane, shiyasa”. Billy kallan Hassana ta yi, ta ce, “me ki ki so? “. “Ni sabuwar ma aikaciyarku ce, Oga manager ne ya d’aukan aiki zan rik’a shara da goge-goge, shine Manager ya ce inzo Office d’in ki, ke ce zaki fad’amin b’angaran da zan rik’a sharewa da gogewa”.Billy kallan Hassana ta yi, ta ce, “Ai muna da ‘yan mopping da yawa, amma inda ya riga ya d’auke ki, ki rik’a mopping d’in site d’in da engine su ke, amma fa dole zaki rik’a zuwa da wuri”. Hassana kallan ta ta yi, ta ce, “Aunty ai bansan site d’in ba”. “Ki samu wata staff d’in ki tambayeta zata nuna miki”. Hassana godiya ta yi mata ta juya zata tafi.Hassana ta na fitowa daga Office d’in supervisor ta had’u da wani staff da suka had’u jiya. Cikin zakin fuska da washema Hassana baki, yak’araso inda Hassana ta ke. Kallan Hassana ya yi, ya ce, ” ‘Yan mata ina fatan dai kin samu aiki”. Hassana cikin sakin fuska itama ta bashi amsa, ta ce, “Eh Wallahi na samu”. “Kai amma nai miki murna, kina cikin masu programme d’in sanat yoghurt ko? “. Hassana kai ta girgiza mai ta ce, “Ni aikina sharane da goge- goge”. “Ok, karki damu wata rana zaki zamama d’aya daga cikinmu, wasinmu duk daga haka suka fara, kin san dai aikin Company sai nada hak’uri, dan haka ki yi hak’uri ba kamar da supervisor d’in mu ba”.Hassana kallan shi ta yi, ta ce, “Dan Allah inane site d’in ku d’in can ne b’angaran da ta ban aikin”. Staff d’in nan da mamaki ya kalli Hassana, ya ce, “Kai, kin sanfa da yake batada hankali taba masu sharar gun suspension, gaskiya gun ya yi miki yawa ke kad’ai. Amma kinga yanzu ke new worker ce be kamata ki fara kai complain tun yanzu ba, amma daga kin yi one week ina yi bata dawo da wa inda ta ba suspension ba, tom ki kai ma manager complain akan haka”. Hassana godiya ta yi, mai sannan suka jera ya je ya nuna mata inda zata rik’a sharewa da gogewa, duk Hassana ta saba aikin wahala agida amma tasan wannan gun yafi k’arfin sharar mutum d’aya. Hakan yasa Hassana ta kalli staff d’in da ya rakora gun ta ce, mai”gaskiya gunnan ya yi min girma, bazan iya shareshi da goge shi ba ni kad’ai ba”. Kallan Hassana wannan staff d’in ya yi sannan ya ce, “Gaskiya sai dai ki yi hak’urin kwana ko biyu ne tukun nan, dan kinga wa inda ta dakatarma jiya su biyu daga sun mata magana akan tak’aro masu wasu gun ya yi masu yawa su kad’ai, shikenan wai su je gida su huta na wata biyu sai su dawo, Kin san manager gun nan sonta ya ke shiyasa ta ke abinda taga dama, ita kuma hankalinta nakan Oga Habib”. Hassana shiru kawai ta yi, amma tasan zata sha wahala ace aikin da wasu sukeyi su biyu suka kasa abata shi ita kad’ai.staff d’in nan kallan Hassana ya yi, ya ce, “Tom ni dai Sunana kabiru, amma mutane na kidana da barber for ladies,ki fa ya sunan ki? “. murmushi Hassana ta yi mai sannan ta ce, “Sunana Hassana”. kabiru kallan Hassana ya yi, ya ce, “kai amma gaskiya kinada suna mai dad’i , bari in je in yi abinda zanyi, sai anjima in munhad’u”. Kabiru ta fiya ya yi yabar Hassana gun tsaye tana kallan yadda ma aikatan ke ta aikin d’ura yughurt d’in da akai cikin robobi. Hassana na nan tsaye tana kallan aiki ga wani irin k’amshin swtrovery da ke tashi agun. Hassana na nan tsaye ta ji, andafa ta. Da sauri Hassana ta waigo tana kallan wadda ta da fata.matashiyar budurwar ce, zasu iya zama sa’a da Hassana, kallan Hassana ta yi, ta ce, “Amma dai ke new worker ce anan ko? “. Kai Hassana ta d’aga mata. “Ai dama tunda naga kina sauraran kabiru na san ke sabuwar ma’aikaciya ce nan, abinda zan fad’amiki ki rabu da Kabiru dan daga ganinki kina da mutunci da kamun kai, kabiru ko d’an iskan mai rai ne, biki ji sunan shi ba, barber for ladies,sannan idan supervisor tazo ta ganki tsaye ahaka, zaki samu matsala. B’angaran me ye aka d’auke ki”. Hassana kallanta ta yi, ta ce, “shara da goge- goge”. “Tom kinga ga rack can d’akko shi zaki yi, duk abinda ya zube kina gogewa, ki tafa bata yadda ta ganka a tsaye ba”. Hassana godiya ta yi mata, sannan ta zo gusa da su, da morpper d’inta duk abinda ya zube tana gogewa. Kafin lokacin tashi ya yi Hassana ta share duk inda ya ke ak’ark’ashin ai kinta. K’arfe 8:00pm Hassana ta fito domin ta fiya gida, sai a lokacin Hassana ta tuna bata da ko sisi, gashi tun d’azu taga fitar manager bare ta fad’a mai inda taga alamar yana da kirki sosai. Hassana wajan parking space ta shiga tana zuwa ta motar Oga Habib agun, azuciyar ta tace bai tafiba kenan, Ya Allah banda yadda zan yi kuma bazan gane gidan ba, Allah ka bashi ikon d’aukata. Hassana guri ta samu ta zauna tana tunanin yadda zata iya yima Oga Habib magana ya d’auketa. Wata zuciyar ta ce, kai Wallahi bazan iya ba, dan ko nayi ma ba d’aukata zai yi ba, wata zuciyar ta ce mata, tom idan baki mai magana ba, ai kin kwana a titi. Hassana na zaune tana wannan tunanin ga tunwa duk ta da meta, tun tea d’in da Jimmai ta bata da safe tasha har yanzu shi kad’ai ne a cikinta, d’azu tana gani staff d’in gunna fita cin abinci amma ita bata da kud’i sai dai ta hakura. Hassana na nan zaune, ta ga fitowar Oga Habib, yana zuwa ya fad’a motar shi. Hassana da sauri ta tashi ta nufi gun motar Oga Habib……………
TOFA IDAN OGA HABIB BAI D’AUKI HASSANA BA, YA ZATA YI????? ♀️♀️
ANYA KO KUNA GANIN OGA HABIB ZAI IYA D’AUKAR HASSANA?????
COMMENT &
SHERE
PLEASE
OGA HABIB
*︎ARUMAI ︎ WRITERS ︎SSOCIATION️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa*_
*(︎.︎.︎)*
TSARAWA
DA
RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy Baby).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
My Facebook group:Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
MATSALOLINMU A YAU GUDA BIYU NE:MU YI AIKI KAFIN MU YI NAZARI, KO MU YI TA NAZARI BA AIKI. ALLAH KASA MU RIK’A AMFANI DA LOKUTAN MU.
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK’R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D’AN TARKU DA HAZIK’AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD’UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K’AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK’E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K’OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN
K’ABILA CE! K’ABILA CE!! K’ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K’ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D’AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K’ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT
08142904255.
Shafi na 12&13.
Hassana cikin fargaba ta k’arasa gun motar Oga Habib. Sai dai Hassana na k’arasawa gun shi kuma yana sama motar shi key ya bar gurin. Hassana d’agama Habib hannu ta ke amma Habib na lure da ita, ya yi tafiyar shi, yana maganar zuci, ba dai yarinyar nan tana nufin in d’auketa bane a motata ko. K’wafa Habib ya yi yaja motar shi ya tafi.
Hassana ko rasa yadda zata yi ta yi, hanya ta kama takama tafiya a k’asa dan tana ganin zata Kane gidan. Tafiya sosai Hassana ta yi sannan ta isa gidansu Oga Habib. Lokacin 11:30 pm.Hassana na zuwa ta iske anrufe get d’in gidan, tom dama daga Habib ya dawo ake rufe gidan.Hassana cikin fargaba ta fara bubbuga get d’in gidan. Hassana ta dad’e atsaye tana bubbugawa sannan d’aya daga cikin get man’s d’in gidan yazo yana tambayar waye. Hassana cikin tsoro da jin yadda ya yi mata magana ta ce, “Hassana ce sabuwar ma aikaciyar da Oga Habib ya d’auka jiya”. Tom a k’a’idar gidan su Oga Habib duk ‘yar Aikin da aka d’auka sai an nuna ma masu gadin gidan gaba d’aya ita dan su shaida fuskarta. Wannan umarnine daga Hajiya turai. Hakan yasa ya koma ya tambayi sauran masu gadin, akan ko sun san da d’aukar sabuwar mai aiki a gidan. Nan suka ce mai a’a. Jennies dawowa ya yi, ya ce, ma Hassana, su babu wata mai aiki da aka d’auka jiya, dan haka tabar gun kafin ya fito.
Hassana cikin kuka da da nasanin barin gidansu da ta yi, ta ce, “Wallahi da gaske na ke, ka tambayi Oga Habib, ni ce wadda Oga Bilya drivern Oga Habib ya kawo, tom jiya suka d’aukan aiki, ko yau ta get d’in nan na wuce”. Shiru ya yi dan ya ji maganar ta kamar da k’amshin gaskiya, hakan yasa ya ce, “Ok, bari in kira Oga Habib tukun, idan yace abarki ki shigo tom zan bud’e miki, amma idan yak’i sai dai ki yi hak’uri”. Jennies number Habib ya kira. Lokacin Habib ya yi nisa sosai a bacci, ringing d’in wayar shine ya ta da Habib daga bacci. Habib cikin murya bacci ya d’aga wayar batare da ganin Number ko waye ba, ya sa akunne. Jennies naji Habib ya d’aga wayar ya ce, “Oga Habib dama wata Yarinya ce ta zu yanzu tana nocking get wai jiya aka d’auketa aiki a gidannan”. Habib najin haka ya yi tunanin yarinyar nan ce, acewar shi. Habib ce mai ya yi karka bud’e mata. Yana cewa haka ya kashewar. Jennies buga get d’in ya yi, ya ce, ma Hassana “knji ko, Oga Habib ya ce bai sanki ba, dan haka ki bar nan yanzun nan! “. Hassana matsawa ta yi daga jikin get d’in. D’annesa da get d’in, Hassana zuk’unna ta yi tana kuka.Habib ko tashi ya yi, ya zira jallabiyar shi ya nufi wajan get yana jan tsaki. Habib na zuwa ya yi ma d’aya daga cikin ma’aikatan magana, ya ce, “kubud’e min get “. Bayan an bud’e ma Habib get d’in fita ya yi, can nesa da gidansu yahangi Hassana zaune ta tura kanta tsakankanin cinyoyinta tana kuka. Habib daga idan ya ke tsaye, ya kira Hassana ya ce, “keee!! “. Hassana cikin tsoro tata shi zata gudu. Sai ji ta yi, Habib ya kuma cewa, “kee bakya jine”. Hassana da katawa ta yi daga gudun da za ta yi, ta k’arasa in da Habib ya ke tsaye. Habib kuma yana ganin Hassana ta taho ya shiga cikin gidan. Hassana shiga ta yi ita ma, Hassana nashiga ta iske Habib tsaye kamar ita ya je jira. Hassana k’arasawa in da Habib ya ke ta yi. Habib wani irin kallo ya yi ma Hassana mai cike da ma’anoni da dama, sannan ya ce, “Daga yau in dai kika wuce 7:00pm baki dawo ba, tom karki kuma buga ma mutane get, idan ba haka ba kuma Habib ya nunata da hannu, ya ce, “Sai dai ki nai mi gurin zama, amma ba dai gidannan ba”. Habib na fad’in haka ya tafi yabar Hassana nan tsaye k’irjinta na dukan uku-uku.Hassana cikin sauri ta je site d’in su, har sun rufema ta buga masu, suka bud’e mata. Jimmai ce ta tashi ta bud’e ma Hassana k’ofar, dama tun da zu ta ke tunanin lafiya, jin Hassana shirun da ta yi.Jimmai na bud’ewa ta kalli Hassana ta ce, “Hassana lafiya dai ko?, na jiki shiru tun d’azu”. “Kud’in napep ne banda shi, a k’asa na dawo shiya sa”. Jimmai sosai ta tausayama Hassana sannan ta d’akko ma Hassana abincin da ta d’ibar mata ta bata”. Hassana nagama cin abincin ta kwanta ta kama bacci, dan sosai ta gaji.
Washe gari da wuri Hassana ta tashi ta yi wanka, ta sa kayan Jimmai kamar yadda jimmai ta ce ta rik’a sawa, Sannan Jimmai ta ranci kud’in napep gurin karima, taba Hassana. Hassana sosai ta yi ma Jimmai godiya sannan ta ta fi. Hassana na isa ta ta cigaba da sharar b’angaran ta. Kafin wani lokacin Hassana ta gama share gurin ta goge”.
BAYAN SATI D’AYA.
Yau sati d’aya kenan da fara aikin Hassana a sanat yoghurt. Kullum Jimmai ke rantar kud’in napep tana ba Hassana, da sunan idan wata ya yi, anyi albashi Hassana ta biya su. Yau ma Hassana da wuri tata shi domin tafiya sanat yoghurt Company. Hassana sai da tama shirinta, ta tambayi Jimmai kud’in napep. Jimmai kallan Hassana ta yi ta ce, “Hassana Wallahi yau sai dai ki yi hak’uri , kin san ni dama daga wata ya yi an bani salary na na ke kaiwa gidanmu, tom wadda na ke rantar mi ki kud’i gurinta kuma, Wallahi ita ma kud’inta sun k’are”. Hassana shiru ta yi tana tunanin mafita , dan tasan sai dai ta je ak’asa, kuma idan har ta je a k’asa tom tabbas baza ta iya sharar da ta ke ba, dan yanzu haka ciwan baya ta ke, dan gurin nada girma kuma ita kad’ai ke aikin sharesa da gogesa. Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, “Jimmai ya zanyi?, dan Wallahi supervisor d’in mu bata da kirki ko ka d’an,bata karb’ar uzirin mutum in dai bai je aiki ba”. Jimmai dafa Hassana ta yi, ta ce, “K’awata ni gani na ke yi ki yi hak’uri da zuwa yau inda ya za ki yi, ba ki da kud’in napep “. Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, “Jimmai zata fa iya korata aiki akan haka, nace miki bata da kirki”.Shiru Jimmai ta yi, sai zuwa can ta ce, “Yauwa k’awata ko zaki je wajan get ki jira idan Oga Habib zai tafi sai ki fad’a mai baki da kud’in napep yau ba za ki samu zuwa aiki ba”Hassana da fe k’irji ta yi ta kalli Jimmai, ta ce, “Jimmai rufa min asiri, kin san ko waye Oga Habib!?”. Dariya Jimmai ta yi, ganin yadda Hassana ta dafe k’irji, ta ce, “Hmm Hassana ke nan, ni ko nasan waye Oga Habib, bashi da d’igon kirki ko kad’an, dama dan naji kin ce shiya d’auke ki aiki ne,shi yasa. kuma tunda har ya barki ki ke zaune anan ai ke da dama-dama, ni da ko hanya bana so ta had’ani da shi, dan ni Wallahi tsoran shima na ke ji”. Hassana kallan Jimmai ta yi da mamaki, ta ce, “Ki ce ba ni ka d’ai ke tsoransa ba, amma shine ki ka ce in rok’ai kud’in napep, bacin kin san ba ban zai ba, sai dai ma k’ila ya yi min wulak’anci”. “Hakane k’awata ki yi hak’urin zuwa yau, zuwa gobe insha Allah zamu san yadda za ai”. Hassan tom kawai ta ce ma Jimmai dan bata da yadda zatai. Amma tana tunanin yadda zasu kaya da supervisor d’in”.
Can sanat yoghurt ko,haka akai aiki gun batare da anshare ba, ko angoge.
Yau kwana uku kenan Hassana na zaune gida bata da kud’in zuwa company. Tom kuma dama Hassana ce kad’ai mai sharar b’angaran, Billy duk ta ba sauran masu sharar suspension.
Yaune kuma abokan Habib wa inda su kai karatu tare suka kawo mai ziyarar bazata. Habib na zaune a office d’in shi ba zato ba tsammani, ya ji nocking. Izinin shiga Habib ya basu. Sai dai Habib sumar tsaye ya yi, da mamaki ke kallansu, rungume su su duka biyu Habib ya yi, ya ce, “Faruq, Nasir, zan rama, nima duk sanda zan yi visiting naku, sai dai ku ganni, ba bu Anousing”. Habib zama ya yi yana nuna masu gurin zama. Wanda Habib ya kira da faruq, kallan Habib ya yi, ya yi murmushi ya ce, “Habib Allah ba zuwan siri bane mu kai, yanzu dai babu lokaci, mu shiga ciki Nasir yaga factory naka”. Habib jagora ya yi masu yana kaisu kona suna gani. Wanda aka kira da Nasir ko sai yaba girman gurin ya ke, da tsaruwa irin ta gurin ya ke. Faruq, kallan Habib ya yi, ya ce, “Habib kasan Allah ina jin dad’in Yoghurt d’in ku sosai,dan gaskiya mutanan Taraba, suna son yughurt d’in ku sosai, dan manyan-manyan restaurant d’in Taraba duk inda kaje zaka samu sanat yoghurt”. Murmushi Habib ya yi mai, ya ce, “Kasan ko kwanannan na ke son juwa Taraba dan bud’e sabon Company acan”. “kai Habib, wai yanzu state nawa ke da branch a can”. “Kano, Kaduna, sai nan Abuja”. Habib suna tafiya suna tattauna da abokansa har suka isa, site d’in da ake Yoghurt d’in. Duk company babu inda ya kai gun girma, kuma site d’in ne Hassana ke aikin sharewa da gogewawa. Gashi yau har kwana uku kenan Hassana bata zoba, gun ya yi datti sosai dan har k’udaje ke ke waye gun saboda yadda ya yi. manager ko yau satin shi d’aya kenan da yin tafiya, yabar komai a hannun supervisor. Habib sosai ya ji kunyar yadda friend’s d’in sa suka ga gurin. Hakan yasa Habib ya ja su suka koma Office d’in shi. Habib na kai su Office ya dawo gun ranshi ab’ace yana kallan ma’aikatan gun, Habib cikin daka tsawa da b’acin rai, ya kalli ma’aikatan gun ya ce, “Aikin waye wannan!? “. Yafad’i maganar ya na nuna gurin da hannu shi. Dukkan su shiru su kai dan ba sanin sunan Hassana su kai ba. Hakan yasa Habib ya kalli d’aya daga cikin staff d’in ya ce, “ki ramin supervisor “. Wanda Habib ya aika da saurinsa yabar gun ya nufi office d’in, Bill.
Billy na zaune da waya rik’e a hannunta tana charting ta ji ana mata nocking. Billy izinin shigowa ta bata. Staff d’in da Habib ya aika, kallan Billy ya yi, ya ce, “Sister Billy Oga Habib na kira”. Billy kallan staff d’in ta yi, ta ce, ka ce mai ganinan zuwa, yana office d’in shi ne? “. “A, a yana site d’in mu”. Yana fad’in haka ya juya ya tafi.
Billy kuwa jin Habib na kiranta powder ta k’ara shafawa da lipstick abakinta, sannan ta fita.
Habib na tsaye ranshi ab’ace, ga shi shi a ganinshi Billy ta b’ata mai lokaci. Habib na nan tsaye yana huci Billy ta tahu tana yauk’i ita Allah dole ga wadda Oga Habib ke kira. Billy na zuwa gaban Habib ta tsaya kamar zata shige jikinsa, ta ce, “Oga Habib ga ni”. Habib ko, kallan k’askanci ya yi ma Billy sannan, ya ce, “Yama sunan ki? “. Billy cikin mamaki wai ita Habib ke ce ma ya sunanta. Billy kallan Habib ta yi, ta ce, “Oga Habib yanzu kamant…. “. Habib hannu ya d’agama Billy sannan ya ce,”Daga nan zuwa minti shafiyar idan har ba agyara gurin nan ba, tom ki gama aiki a sanat yoghurt, sannan wannan ya zamana na farko da na k’arshe, aiki kika zo yi ko shirme?, in dai baki gyara ba tom zamu da katar da ke! “. Habib na fad’in haka ya juya ya bar gun ranshi b’ace ya bar gun.
Billy kuka ne kawai ba tai ba , dan a cewarta Habib ya tozartata gaban staff. Hakan yasa Billy ranta b’ace ta ce, “Wata idiot d’in ce ke kula da site d’in nan”. Wata daga cikin sttaf d’in ce ta ce, “supervisor new worker d’in nan ce, kuma yau kwana uku kenan bata zo ba, ina jin bata da lafiy…. “. Tsawar da Billy tai mata ce yasa tai shiru, ta ce”Allah yasa ubanta ne ya mutu tabar aiki amasana’artannan, kuma sai naci mutuncinta fiye da wanda Oga Habib ya ci min…………
COMMENT
&,
SHERE
PLEASE
OGA HABIB
*︎ARUMAI ︎ WRITERS ︎SSOCIATION️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa*_
*(︎.︎.︎)*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Fabby baby).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
Facebook group :Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
IDAN KA MUTU AN RUFE LABARINKA, AMMA ABUBUWA UKU SUNA RAYUWA A BAYANKA:
☝ILIMI DA
✌️HAIHUWA SAI
AIKIN ALHERIN DA KA SHUKA. ALLAH KA SA MU DACE.
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK’R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D’AN TARKU DA HAZIK’AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD’UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K’AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK’E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K’OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN
K’ABILA CE! K’ABILA CE!! K’ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K’ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D’AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K’ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT
08142904255.
Shafi na 14&15.
B’angaran friend’s d’in Habib, Habib na koma wa Office d’in su kai mai sallah su kace tafiya za su yi. Habib godiya ya yi masu sosai, sannan yasa aka cika masu bayan But d’in su da yoghurt.
B’angaran Hassana ko, Yau ta tashi da niyyar ko ak’asa ne sai ta je aiki dan zaman ya isheta, ga tsoran supervisor d’in su da ta ke yi, dan ana yawan fad’a mata rashin mutuncinta. Hassana da wuri ta shirya kamar yadda ta saba shiryawa ta kama hanya ak’asa ta tafi. Hassana ba ita ta isa sanat yoghurt ba, sai 9:30Am. Ita da ke zuwa tun seven o’clock. Tom dama Billy ta bada sak’o ta ce idan Hassana tazo aiki ace mata tana nai manta a office d’in ta. Hakan ce ta kasan ce, Hassana na zuwa wata daga cikin staff d’in ta sanar da ita sak’on supervisor d’in. Hassana cikin fargaba ta tura Office d’in supervisor ta shiga. Lokacin Billy na zaune tana aikin danna waya. Hassana cikin girmama ta ce, “Barka da aiki supervisor”. Da kai Billy ta amsa ma Hassana. Hassana kuma ci gaba da tsayuwa ta yi, tana jiran hukuncinta. Ita ko Billy tama manta da wata Hassana, hakan yasa ta kalleta ta ce, “Lafiya za ki zo ki tsamin akai? “. Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, “Supervisor dama wata staff ce ta ce kince idan nazo aiki nazo kina kirana”. Hassana ta ci gaba da cewa, “Supervisor Wallahi rashin kud’in napep ne ya hanani zuwa aiki, kwana uku da banzo ba, ko yauma ak’asa nazo”. Billy bar abinda ta ke yi awaya ta yi, ta d’aga kai tana kallan Hassana, ta ce, “Ki ce mai sharar site d’in da ake yoghurt ko? “. “Eh ni ce”. Cewar Hassana. “Billy kallan Hassana ta yi da b’acin rai dan sai abinda Habib ya yi mata yadowo mata farko, hakan yasa cikin d’aga murya ta ce, “Hassana ki ke ko me!?, mun da katar da ke aiki a k’ark’ashin sanat yoghurt Company “. Hassana cikin tsoro da fargaba jin abinda Billy ta ce mata, ta ce, “Supervisor dan Allah ki yi hak’uri insha Allah daga yau haka bazai kuma faruwa ba”. Billy ko inda Hassana ta ke bata kalla ba ta ce, “Nariga na gama magana, ki kalli time kigani ko yanzu k’arfe nawa kikazo aiki?, bama aiki da wanda bashi da experience, fitar min daga Office! “. Hassana fita ta yi batare da ta k’ara cewa ko mai ba, Hassana na fita ta nufi Office d’in Manager “.manager na zaune Hassana tai mai nocrking. Izinin shiga manager ya ba Hassana. Hassana shiga ta yi,Hassana cikin girmamawa ta gaida manager. Manager cikin sakin fuska ya amsa ma Hassana, ya ce, “Hassana lafiya dai ko? “. Hassana kamar zata yi kuka ta ce, “Manager supervisor ta dakatar da ni aiki”. Manager cikin tsoro ya d’aga kai yana kallan Hassana. Shiru manager ya yi na d’an wani lokaci sannan ya kalli Hassana ya ce, “me kika yi mata? “. Hassana cikin sanyin muryarta, ta ce, “Banzo aiki ba kwana uku, bani da kud’in napep, ko yauwa ak’asa nazo”. Shiru manager ya yi, sannan ya ciro kud’i yaba Hassana ya ce, “Hassana amshi kud’innan kinji sai ki amfani da su, ki yi hak’uri kinji naso kiyi aiki anan, tom amma inda haka ya faru sai dai hak’uri “. Hassana amsa ta yi taima manager godiya jin abinda ya ce, ta fita daga Office d’in. Hassana na ta fito daga Office d’in manager ta had’u da staff d’in da ta bata sak’on supervisor na kiranta. Staff d’in cikin tausayama Hassana ta k’araso inda Hassana ta ke, ta ce, ta koreki ko? “. Kai Hassana ta d’aga mata ta ce, ” Ta kore ni, na yi ma manager ma magana ma ko zai sa baki, amma ya ce min inyi hak’uri “. staff d’in kallan Hassana ta yi ranta ad’an bace, ta ce, “Ni da nasan zaki gurinsama da na hanaki, ai indai supervisor ta yanke hukunci bai iya yin komai, sai dai ya baka hak’uri bai iya sab’a maganarta”. Hassana sallama ta yi ma staff d’in ta tafi dan maganar ma da kyar ta ke yinta. Cikin kud’in da manager ya ba Hassana ta hau napep ta koma gidansu Oga Habib, duk da zuciyarta cike ta je da bargabar komawa gidan, in da yanzu tabar aiki ak’ark’ashin su, haka nan Hassana ta koma inda bata da yadda zata yi.Jimmai cikin mamaki ta ke kallan Hassana ganin Hassana ta dawo gida yanzu.Jimmai k’arasawa inda Hassana ta ke ta yi, ta ce, “Hassana lafiya kuwa naganki kin dawo? “. “Supervisor ta koran aiki”. Jimmai ta fe k’irji ta yi tana salati, ta ce, “manager kuma ya sani? “. “Eh ya sani, wai budurwarsa ce ba ya musu da abinda ta ce, inji wata staff”. Jimmai shiru ta yi, tana jimamin abinda ya faru. Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, “Jimmai tom kina ganin babu damuwa inci gaba da jama gidannan yanzu bana aiki ak’ark’ashin su? “. Jimmai kallan Hassana ta yi ta ce, “Tom nima dai ban sani ba, amma dai yau Hajiya turai zata dawo ai, shiyasama kikaga ko ina gidan aiki ake, tom ki bari ta dawo mugani”.
WACECE HAJIYA TURAI?.
Hajiya turai babbar macece cikakkar ‘yar boko. Ita kad’ai ce awajan mijinta wato Alhaji Idris mai kanti. Tun Habib na yaro Mahaifinsa ya rasu, hakan yasa Habib bai san Mahaifinsa ba. Hajiya turai babbar ‘yar jarida ce, yanzu haka Hajiya turai a B. B. C, London ta ke aiki, hakan yasa kusan koda yaushe Hajiya turai bata Nigeria.Ji da kai da miskilanci Habib duk a gurin Mahaifiyar shi ya gada. Hajiya turai tun da ta haifi Hassana k’anwar Habib ta tsaida haihuwa, dan ita gani ta ke baza ta iya d’awai niyar yara uku ba. Hassana ta yi girma kusan 18 years sannan Allah ya yi mata rasuwa, sanadiyar wata bak’uwar ‘yar aiki da Hajiya turai ta d’auka aiki, ashe had’in kai ne akai da ita aka zuba ma Hassana guba ta ci, wannan ne sanadiyar mutuwar Hassana har lahira. Mutuwar Hassana sosai ta d’agama Habib hankali dan idan ka cire Hajiya turai mahaifiyar Habib, tom babu wanda Habib ya ke zama dashi sunyi hira su ci abinci tare sai Hassana, yana kiranta da sanat, wannan shine dalilin da koda zai bud’e Company yin yoghurt ya sa ma mai suna Sanat yughurt. Tun rasuwar Hassana ya sa Hajiya turai ta bar yadda da kowa yana shigo mata gida barkatai. Wannan shine dalilin da yasa Hajiya turai har ‘yan Aiki ta daina d’auka tuma ta ke rik’e wa inda ta ke dasu da mahimmanci bata yadda Habib ya koresu ko sun yi wani abun, duk da ta yi kashedi sosai akan d’aukar wata sabuwar mai aki bata nan, wannan shine dalilin da yasa koda aka kai mata labarin zuwan Hassana taima Habib fad’a. Wannan ke nan”.
Sosai ‘yan aikin gidan Hajiya turai ke shirin tarbar ta. K’arfe hud’u na yamma jirginsu ya sauka, idan Habib da kan shi ya je ya d’akkota. Habib har falon Hajiya turai ya kaita, sanan ya kalleta yana murmushi ya ce, “Mommyna kin gaji ki yi wanka ki kwanta ki huta, sai kici abinci ko? “. Murmushi Hajiya Turai ta yi, ta ce, “Tom Habib ko na kwanta worker’s d’in gidan baza su barni in yi bacci ba, nasan yanzu zasu fara yimin aikin sannu da zuwa”. Habib d’an b’ata rai ya yi, sannan ya ce, “Mommyna ki kwanta ni zan yi gadinki babu wadda zata shigo falon ki sai in kin tashi”. Habib na fad’in haka ya fita ya ce, yana zuwa.
Habib b’angaran ‘yan aikin gidan ya je, kafin ya k’arasa ya samu Hassana da Jimmai suna wanki tare. Habib wani kallo ya yi masu wanda ya rikirkitasu du kansu, duk suka daburce. Bakamar Hassana ba da ta ke tsoran ko gurinta yazo yasan ankore aiki yazo ne ya koreta shima, hakan yasa Hassana cikin sark’ewar murya ta ce, “Ina wuni Oga Habib “. Habib banza ya yi da Hassana, sannan ya kellesu dukan su ya ce, “Hajiya ta dawo, kar wadda ta yi kuskuran shiga gurinta yanzu, sai bayan magriba”. Habib na fad’in haka ya juya. Hassana ko da Jamila kusan tare suka had’a baki wajan cewa, “tom babu wanda zai shiga zamu fad’a ma sauran”. Habib na tafiya, Jimmai ta kalli Hassana ta ce, “Ni dai Hassana duk da halin Oga Habib na wulak’anta mutane Wallahi yana burgeni sosai”. Kai Hassana ta jinjina ta ce, ” Ni dai abinda nasani kawai, nasan Oga Habib mai kyau ne shi, dan duk inda ake nai man maza masu kyau za asa shi, amma Wallahi bai tab’a burgeniba”. kai Jimmai ta jinjina sannan ta ce, “Hassana bari in je in sanar da sak’on Oga Habib, dan yanzu za kiga ‘yan iyayi sun fara shiga”. Jimmai sak’on Habib ta je ta sanarma duk wata wadda ke aiki agidan. Bayan jimmai ta dawo ne ta kalli Hassana ta ce, “Hassana zaki gaida Hajiya ko?, dan idan ma baki jeba sai magulmata sun kai mata gulma, kuma in dai suka rigaki zuwa gaskiya akwai damuwa”. Shiru Hassana ta yi, sannan zuwa can ta ce, “Zan je, kawai dai ina fargaba ne idan tak’i amintar zamana”. “A’a insha Allah zata zauna da ke, ai Hajiya bata da wani damuwa sosai”. Nan dai Jimmai taita kwantarma Hassana hankali akan zuwa gaida Hajiya Turai da zasu anjima.
Aiko kamar yadda Habib ya tsara haka akai, dan babu ‘yar aikin da tashiga gaida Hajiya Turai, kamar yadda suka sabayi da. Hajiya Turai bayan tata shine masu kai mata abinci sun kai mata taci, ta gama ci, tana zaune a falon ta, nan fa worker’s d’in gidan suka fara zuwa da d’ai-d’ai da d’ai-d’ai suna gaidata, Habib na zaune gefan Hajiyarsa suna fira, dan idan Hajiya Turai ta dawo dama indai yana gida tom yana falonta, babu inda zaka ga Habib sai a falon Hajiya Turai.
Jimmai da Hassana sune kusan k’arshen zuwa, Hassana cikin fargaba da fad’uwar gaba ta shigo falon Hajiya Turai, dan sallama ma sai dai Jammai ce ta yi masu. Tun kafin su zauna Hajiya Turai ta nuna Hassana da hannu ta ce, “Jimmai wacece wannan? “. Kafin Jimmai ta yi magana Baba lami wadda ke aiki cikin falon Hajiya Turai, ta ce, “Hajiya ai wannan zata yi sati biyu agidannan, nima dai ina ganinsu da Jimmai, dan rashin wayar da nayi ne ma da na sanar da kai “. Hajiya Turai kallan jimmai ta yi da ta yi shiru tana kallan Baba Lami, tana cewa azuciyarta dama ita ce me kaima Hajiya Turai gulma in bata nan. Hajiya Turai ko cikin alamun son d’aga murya ta ce, “Jimmai bakya ji ne?, na ce wacece wannan? “. Ta fad’i maganar tana nuna Hassana da hannu”. Jimmai cikin dabir cewa, ta ce, “Hajiya sabuwar ‘yar aiki ce “. Hajiya Turai kallan Hasssana ta yi ta ce, “Waye ya d’auke ki aiki? “. Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, “manager ne”. Hajiya Turai cikin mamaki ta ce, “Manager kuma, wana manager? “. Hassana ada barce taba Hajiya Turai amsa, da cewa, “Manager me aiki Company sanat yoghurt”. Hajiya Turai mai da kallanta ta yi ga Habib da ke zaune kamar bai jin abinda ake cewa, ta ce, “Habib wai me yarinyar nan ta ke son ce min ne?, nina cema manager Ina naiman k’arin mai aki da zai d’aukar min ‘yar aiki, kiramin manager kabanshi awaya”. Habib kallan Hajiya Turai ya yi yadda ta ke fad’a daga cewa an d’auki me aiki. Habib cikin sanyi ya ce, “Mommy ki bari anjima zan kira miki shi please “. Hajiya Turai mai da kallanta ta yi gun Hassana ta ce, “Ki je sai kuzo da manager “. Hassana tsuk’unnawa ta yi, kamar za tai kuka ta ce, “Hajiya dan Allah ki yi hak’uri, bansan gidan manager ba, hasalima ya koran aiki”.Hajiya Turai rasa takan zancen Hassana ta yi. Hajiya Turai magana ta za ta yi, sai ji tai Habib ya ce, “Me yasa manager ya koreki aiki? “. Yadda Habib ya yi maganar babu yadda za ai ka ce da Hassana ya ke”. Hassana kallan Habib ta yi, sannan ta ce, “Bani da kud’in napep ne, kwana uku banje aiki ba, ranar da aka koranma ak’asa naje, amma ko da naje sai aka ce Supervisor ta ce in je office d’in ta tana kirana, shine da naje ta ke sanar dani ta dakatar dani aiki, da nafad’ama mana yace sai dai in yi hak’uri “. Hassana ta idasa maganar cikin fargaba dan tana tsoran kar Habib ya ce sai dai tabar masu gida. Habib batare da ya kalli Hassana ba ya ce, “Go be ki koma aiki, kuma karki yadda ki wuce magriba baki dawo ba, Hajiya ta dawo dawuri zamu rufe gida, wuce ku tafi”.
Hassana da Jimmai da sauri suka tashi suka bar falon. Bayan su Hassana sun tafi ne, Hajiya Turai ta ce, “Habib bangane ba, kasan dai bana buk’atar k’arin mai aiki ko? “. Habib kallan Hajiya ya yi, cikin na tsuwa ya bata labarin yadda akai suka tsinci Hassana shida Bilya, da kuma labarin Hassana gaba d’aya haka Habib ya ba Hajiyarsa dan hankalinta ya kwanta, dan ya lura ta tsorata sosai da abinda ya faru shekaru biyu da suka wuce.
Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, “Shikenan ba damuwa ta ci gaba da aikinta “.
Nan Habib ya zauna suka cigaba da hira da Monmynsa sai dare sannan ya je ya kwanta.
Washe gari Hassana da wuri tata shi ta yi shirin zuwa aikinta da kud’in da manager ya bata da su ta biya kud’in napep. Hassana cikin fargaba da fad’uwar gaba tashiga sanat yoghurt, dan tana tsoran yadda zasu kwashe ita da supervisor……………..
COMMENT
&
SHERE
PLEASE
OGA HABIB
*︎ARUMAI ︎ WRITERS ︎SSOCIATION️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa*_
*(︎.︎.︎)*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
Facebook group :Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
BABBAN MABUD’IN ALHERI SHI NE ISTIGFARI. IDAN KA YAWAITA SHI MATSALOLINKA ZA SU KAUCE, DAMUWARKA ZA TA GUSHE, SAUK’I ZAI ZO MAKA. ALLAH KASA MU DACE.
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK’R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D’AN TARKU DA HAZIK’AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD’UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K’AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK’E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K’OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN
K’ABILA CE! K’ABILA CE!! K’ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K’ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D’AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K’ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT
08142904255.
Shafi na 16&17.
Hassana cikin tsoran Billy ta shiga cikin Sanat yughurt. Hassana direct inda ta ke sharewa ta nufa ta kama aikinta. Duk staff d’in da tazo da mamaki ta ke kallan Hassana, dan su asaninsu duk wadda Billy ta dakatar ta tafi kenan, hakan yasa suke bin Hassana da kallon mamaki. Hassana ta gama share gun tana morpping Billy ta shigo site d’in. Billy tun daga nesa ta ke kallan Hassana, dan tabbas idan idonta ba gizo ya ke mata ba, yarinyar da ta kora aiki jiya ce ta dawo yau. Hakan yasa Billy ta k’arasa inda Hassana ta ke.Billy kallan Hassana ta yi da kyau sannan ta ce, “Ke ba ke bace jiya na dakatar da ke aiki a Company nan? “? Hassana d’agowa ta yi tana kallan Billy sannan ta ce, “Ni ce”. Wani kallo Billy taima Hassana sannan ta ce, “Ok, biki ji bane sai na kuma maimai tawa ko me!? “.Hassana kallan Billy ta yi, ta ce, “supervisor Oga Habib ne yace in dawo in cigaba da aiki”. Billy kallan mamaki tai ma Hassana, dan tana da tabba cin k’arya tai ma Oga Habib. Hakan yasa Billy kallan Hassana ta ce, “Ke kafin insa ad’aukeke afitar dake daga nan, ki sauri ki bargunnan stupid kawai”. Hassana kallan Billy ta yi ta ce, “Supervisor Wallahi Oga Habib ne ya ce in dawo”. Shiru Billy ta yi tana tunanin tom ina Hassana zata ga Oga Habib, dan ko ita sai da dalili mai k’arfi ta ke shiga office d’in Oga Habib bare kuma Hassana, cewarta acikin zuciyarta. Hakan yasa Billy kallan Hassana ta ce, ki bar aikin kisaman office d’in manager”. Billy na fad’in haka ta juya ta tafi office d’in manager. Hassana bayan Billy ta fi, ta sameta office d’in manager kamar yadda Billy ta buk’ata. Billy ko na shiga office d’in, manager ta kalli Manager tana nuna mai Hassana ta ce, “manager waya dawo da yarinyar nan aiki? “. Manager shima da mamaki ya kalli Hassana, ya ce, “Hassana waya dawo da ke aiki, bacin Supervisor ta dakatar da ke? “. Hassana kallan manager ta yi, ta ce, “Oga Habib ne ya ce indawo in cigaba da aiki”. Billy ranta b’ace jin abinda Hassana ta kuma cewa ta ce, dan ita yanzu tafi tunanin manager ne yadawo da Hassana ya ce tace Oga Habib ne yadawo da ita. Inda ita a tunaninta Hassana ina zata ga Oga Habib, in ma taganshi tasan bata isa ba ta kai mai k’arar andakatar da ita aiki. Hakan yasa Billy ranta b’ace ta kalli manager ta ce, “Manager yau d’in nan zan aje aiki, Inda ni ban’isa in yanke hukunciba, in dai yarinyar nan bazatabar aiki anan ba, tom sai dai ni in aje aiki! “. Manager cikin damuwa ya kalli Hassana ya ce, “Hassana taya M, D, ya san ankoreki aiki? “. Hassana kallan manager ta yi ganin yadda ya damu jin Billy ta ce zata bar aiki. Manager dakama Hassana tsawa ya yi ganin Yana tambayarta ita kuma tunanin ta ke, ya ce, “Ke bakya jine?, nace taya M. D, yasan andakatar da ke aiki!? “. Hassana kallan manager ta yi ta ce, “Jiya Hajiyar Oga Habib ta dawo, tom bacin naje gaidata ne, ta ke tambar waya d’aukeni aiki, tom shine bayan nasanar da ita, nake fad’a mata amma andakatar dani aikin, tom da yake Oga Habib na gurin zaune, shine ya ke tambayata waya dakatar dani shine nace mai supervisor ce, shine yace yau in dawo aiki”.manager kallan Billy ya yi yace tom kinji yadda akai”. Billy itama kallan manager ta yi ta ce, “Wai bangane ba, idan nagane kana nufin yarinyar nan causing d’in Oga Habib ce ko me?, naji tana maganar gidansu ta ke ne kome ?”. Manager kallan Hassana ya yi ya ce,” je ki cigaba da aikinki”. Hassana fita office d’in ta yi tabar manager da Billy”.
Bayan Hassana ta fita ne, Billy ta kalli manager ta ce, “Manager ni fa gaskiya banyarda da dawowar aikin yarinyar nan ba”. Manager cikin taushin murya ya ce, “Tom Billy yanzu ya ki ke so ayi, aidai kinji daga m, d, ne dawowar ta”. “Eh naji daga Oga Habib ne, amma ai yanzu idan kaje kasamu Oga Habib ka ce mai kai ka dakatar da ita, nasan zai yarda, idan kuma bahakaba ni zan bar aiki anan, dan sai ta d’auka ita sa’atace, shiyasa ni na koreta aka dawo da ita”. Manager kallan Billy ya yi, ya ce, “Billy Yarinyar nan da kike gani m, d, da Bilya driver m, d, ne suka tsinceta, tom bata da Inda zata zauna shine dalilin ma da yasa M, D, barinta gidansu, nina rok’anmata, yanzu idan ya koreta ina zata?, ki yi hak’uri daga yau zata gyara “. “Shikenan badamuwa amma ta kiyaye ta rik’a zuwa aiki da wuri”. cewar Billy, sannan ta fita daga Office d’in manager”.
Hassana ko komawa ta yi taci gaba da aikinta, Hassana na tsaka da aiki ne, wata staff ta kalli Hassana ta ce, “Ke ce Hassana? “. “Eh ni ce”. “Tom Supervisor ta ce idan kin gama morpping d’in ki je tana kiranki”. Hassana da tom ta amsa. Aiko Hassana na gama wa ta je office d’in supervisor ta ce, “Supervisor ance kina kirana”. Billy sai da tagama abinda ta ke yi, sannan ta ba Hassana wani Cup ta ce taje ta wanke mata. Hassana amsa ta yi ta je ta wanke mata ta kawo mata. Bayan Hassana ta dawo ne, Billy ta kalli Hassana ta ce, “Hassana ki ke kome, dama kunne zanja miki, sannan kinsan ya zama dole a hukuntaki abisaga laifin da ki kai, na fashin da ki kai baki zoba, daga yau sai 10 o’clock zaki rik’a close”. Hassana kallanta Billy ta yi ta ce, “Supervisor dan Allah ki yi hak’uri,Oga Habib ya ce kar in wuce magriba ban dawo ba”.Billy Cikin d’aga murya ta ce, “Oh!, kina nufin duk da laifin da ki kai har wani ragin lokaci kika samu, tom wannan kuma ke ya shafa ni dai kinji abinda na ce miki, idan kuma kink’iji zamu rage a salary d’inki”. Shiru Billy ta yi sannan ta nuna ma Hassana hanyar fita, ta ce, “fitar min daga office. Hassana fita ta yi tana mamakin yadda Billy ke nuna mata tsana k’iri-k’iri”.
Hassana magriba na yi, kamar yadda Habib ya ce mata ta koma gida, magriba na yi Hassana ta shirta ta koma.
Tun daga wannan rana ya zamana kullum Hassana ta je aiki Billy ta dinka sata aiki kenan, daga yi min wancan sai yi min wancan, har wankin toilet d’in gun Billy Hassana ta ke sawa, acewarta abakacin tashin da wurin da ta ke yi. Ita kuma Hassana ta yi ma kanta alk’awarin duk abinda Billy ta sata zatayi baza tai mata musuba, hakan ya sa Hassana ta kuma ramewa sosai.
BAYAN SATI D’AYA.
Hassana sosai ta dage sai goge-goge ta ke yi so ta ke tagama tai ma manager magana ta tafi gida, saboda ciwan da kanta ya ke mata. Hassana na Cikin aiki wata staff ta ce, Hassana kije Office d’in manager ana kiranki”. Hassana sauri ta yi tak’arasa abinda ta ke yi, sannan ta je office d’in manager. Hassanan da mamaki ta ke kallan shi ta ce, “Oga Bilya kaine, yau she kadawo? “. Bilya murmushi ya yi ma Hassana sannan ya ce, “Hassana tun jiya na dawo,ya kike ya aiki? “. “Lafiya klau, barka da dawowa Oga Bilya”. Bilya kallan Hassana ya yi yace, ” Yauwa Hassana, zaki iya ko mawa ki ci gaba da aikinki, dama nakiraki ne mugaisa. Hassana kallan manager ta yi tace, “Manager bani da lafiya, dan Allah ina son zuwa gida yau da wuri in samu magani insha”. Manager kallan Hassana ya yi, sannan ya ce, ” ki fad’ama supervisor “. Hassana shiru ta yi dan tasan in dai ita ce ma babarinta za tai ba, amma ance mai naima baya fushi, hakan yasa ta fita Office d’in manager ta shiga na supervisor. Hassana na zuwa ta kalli supervisor ta ce, “Supervisor bani da lafiya, ina son zuwa gida dan Allah, zan sha magani”. ko inda Hassana ta ke Supervisor bata kallaba, ta ce, ” Idan kin je karki dawo”. Hassana najin haka tafita office d’in supervisor dama tasan ba barinta za tai ba. Hassana haka ta koma guri d’aya ta zauna dan bata iya komai tsabar ciwan kan da kanta ke mata. Hassana ba ita ta tashi ba sai magriba kamar yadda ta saba tashi. Hassana tafiya ta rik’ayi a k’asa kafin tasamu napep ga wani irin ciwo da kanta ke mata”.
Bilya ko yadawo bakin aiki, saboda Hajiya Turai na dawowa tasa Habib ya dawo da shi. Habib da sauri ya fito domin tafiya gida baya son magriba ta sa mai anan. Bilya ko dama yana ganin time d’in tafiya gidan Habib ya yi, ya shiga motar yana jiran fitowar Habib. Hakan yasa Habib na shiga Bilya jaya motar suka kama hanya. Bilya tsaye ya hanki Hassana can gefan titi daga gani abin hawa ta ke jira. Bilya Kallan Habib ya yi, ya ce, “Oga Habib dan Allah ga Hassana can ko zamu rage mata hanya? “.Habib banza ya yi da Bilya. Bilya ko jin Habib ya yi banza dashi yi tunanin ko be ji abinda ya ce bane, hakan yasa ya k’ara cewa, “Oga Habib ga Hassana can na ce, dan Allah ko murage mata hanya? “. Habib tsaki ya ja alamun Bilya ya da mai, Bilya ko najin haka ya kama bakinsa yayi shiru. Bilya yana ji yana gani suka wuce Hassana tsaye badan yaso ba, sai dan bashi da yadda zai yi. Habib sai da ya yi Sallar magriba sannan ya shiga site d’in Mommynsa. Habib na shiga ji yayi kamar ya juya ya koma, sai dai bashida yadda zai yi tariga ta ganshi, hakan yasa Habib ya kuma tamke fuska ya shiga falon.Farida da saurinta ta tashi zata yi welcoming d’in Habib. Habib hannu ya d’aga ma Farida. Farida ja tai tatsaya tana Kallan Habib kamar za tai Kuka, ta ce, “Broz Habib kana nufin bakai murnar ganinaba? “. “Yess “. Cewar Habib. “Farida bana murnar ganinki saboda shirman da kike min”. Farida Kallan Hajiya Turai ta yi, ta ce, “Mommy kinji fa abinda Broz Habib ya ce, wai baya murnar ga nina”. Farida ta fad’i maganar kamar zata yi kuka. Hajiya Turai hannun Farida ta kamo tana murmushi ta ce, Farida rabu da Habib shi bai san wacece Farida bane”., Habib ko ji yayi ba zai iya jure zama ba afalon Hajiya Turai hakan yasa Habib Kallan Momynsa ya ce, “Mommy zan shiga ciki ki bada tea akawomin”. Hajiya Turai Kallan Habib ta yi, ta ce, “Habib gobe zan wuce, jirgin safe zan hau”. Habib Kallan Hajiya Turai ya yi , cikin damuwa ya ce, ” Kai Mommy wannan karan kin koma da wuri”.murmushi Hajiya Turai ta yi, ta ce, “Habib kamar kana da damuwa Allah kalli face d’in ka ? “. “Babu abinda ke damuna Mommy”. Habib na fad’in haka ya wuce. Habib falon shi ya je yana jin wani iri acikin jikin shi, amma yarasa gane shikan shi me ke damunsa. Habib na nan kwance Farida ta shigo rik’e da tea a glass cup. Habib bai cika cin abinci ba da daddare sai dai yasha tea. Farida har inda Habib ya ke , ta k’araso, tea d’in hannunta ta mik’ama Habib ta ce, “Broz Habib gashi in ji Mommy ta ce kasha dan Allah badan ni ba”.Farida ta yi hakane saboda tasan da wuya Habib ya sha tea d’in. Habib amsa ya yi ita kuma Farida ta fita dan bataga fuskar zama ba. Habib haka ya ke jin shi wani iri ahaka ya samu sha tea d’in. Yana gama sha ya tashi ya yi Sallar issha’i sannan ya kwanta, dan sosai ya ke jin jikin shi ba dad’i, bakamar brain d’in shi ba tana mai ciwo sosai, haka dai Habib ya samu wani wahalallan bacci ya kwasheshi.
Washe gari tun asuba, Hajiya Turai taima Habib magana, ya shirya dan seven o’clock Am, ta ke son tafiya. Habib tashi ya yi badan wai yaji sauk’in yadda ya ke ji ba, wanka ya yi, ya yi shirinsa Cikin wata dark blue suit. Habib mota ya zauna yana jiran fitowar Hajiyarsa. Hajiya Turai da Farida suka fito Farida na rik’e da jakar Hajiya Turai. Hajiya Turai amsar jakarta ta yi hannun Farida ta ce, Farida ki koma gida. Farida ba Hajiya Turai ta yi saboda bata so tana mata musu. Bayan Hajiya Turai ta shiga motar, kallan Habib ta yi, ta ce, “Habib ko dai zuwan Farida ne yasa naganka haka so silent”. Habib kallan Mahaifiyarsa ya yi, ya ce, “Mommyna bashi bane, nima haka na ke jin jikina duk babu dad’i, ga jiya nayi wani mafarki da yaban tsoro sosai, amma karki damu nayi addu’a, kuma yanzu normal na ke jina”. Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, “Shikenan Habib, amma dan Allah kaje Hospital ka yi check up, dan Allah Habib na sanka da shiririta”. Habib ganin Hajiya Turai ta damu, yasa ya kalleta yana murmushi, ya ce, “Mommyna normally fa nake jina yanzu, karki damu yanzu daga na kaiki airport zan je ganin likita”. Habib action ya rik’ayi kamar mai lafiya, dan yasan in ya nuna ma mommysa ba ya jin dad’in jikinsa tom bazafa tatafi ba. Koda Habib ya kai Hajiya Turai airport. Hajiya Turai rak’on Habib ta yi sosai akan ya je Hospital aduba shi, nan dai Habib ya yi mata sallama ya nufi sanat yoghurt Company”.
Habib na zuwa Office d’in shi ya shiga, Habib na shiga ya kira Bilya awaya, ya ce, “Hello, Bilya ina sanat yoghurt, ka biya restaurant d’in kusa damu ka tahomin da abin break fast”. Habib na fad’in haka ya katse kiran.
Bilya ko lokacin da Habib ya kira shi tashinshi a bacci kenan, hakan yasa Cikin sauri Bilya ya shirya yaja motar shi yafita. Da safe da kuma dare Habib tea kawai ya ke iya sha, sai wainar k’wai. Bilya na shiga Sanat yughurt , ana sauke Hassana ita kuma a napep. Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce “Yauwa Hassana dan Allah amshi break fast d’in nan ki kai Office d’in Oga Habib. Hassana tsayawa ta yi tana kallan Bilya ta ce, “Oga Bilya dan Allah ka kaimai da kanka Allah bana son shiga office d’in Oga Habib. Bilya mik’ama Hassana ya yi, ya ce, “Hassana haka nan zakiyi Hak’uri ki amsa, tun d’azu Farida ke kirana in zo in kawota Sanat yughurt, Wallahi na manta sham sai yanzu na tuna, tom shine ke so inje in d’akkota, yanzu idan na shiga office d’in Oga Habib zai iya sani wani abun, ba zai barni in fito yanzu ba, dan Allah ki amsa ki kai mai”. Hassana amsa ta yi ta ce, “Haba Oga Bilya, ai Umarni zaka bani na aikata ba sai ka rok’eniba”. Dariya Bilya ya yi ya ce, “Bakomai Hassana girmanki ne, bari in je in dawo dama Wallahi ina son wata magana mai mahimmanci da ke”. Hassana itama murmushin ta yi tace, “Tom Oga Bilya sai kadawo”. Bilya tafiya ya yi Hassana kuma tana rik’e da break fast d’in Habib ta nufi office d’in shi”.
Hassana nocking ta yi. Tad’an dad’e atsaye tana nocking sannan Habib ya bata izinin shiga. Hassana na zuwa Cikin girmama ta ce, “Barka da safiya Oga Habib ga shi inji Oga Bilya, ya ce yanzu zai dawo”. Habib batare da ya amsa gaisuwar Hassana ba, dan zuwa yanzu sosai ya ke jin ciwo acikin jikin shi. Habib kallan Hassana ya yi, sai zuwa can ya tashi kamar zai amshi jug d’in hannun Hassana, sai kuma ya fasa, ya dafe kanshi da hannun shi guda d’aya ya mik’ama Hassana d’ayan hannun nashi, yana rin tse ido, ya ce da k’arfi dan har wanda ke waje sai da yaji. “Ahhhh rik’e min hannunaaaa!!? Habib ya fad’i maganar da k’arfi yana mik’ama Hassana hannun shi. Hassana sosai ta tsorata, Hakan yasa ta saki jug d’in hannunta ta bud’e k’ofar Office d’in zata fita. Sai dai ina ta makara kafin ta bud’e kofar sai dai taji anjawo hannunta da k’arfi…………………
A’A, WAI ME KE FARUWA NE?, NI FA BANGANEBA.
NASAN WASINKU DA DAMA ZASU CE HAKA.
KARKU DAMU ZAKU GANE.
LABARIN YANZUN YAFARA
BANDA LAFIYA DAN ALLAH INA BUK’ATAR ADDU’ARKU.
COMMENT
&
SHERE
PLEASE
OGA HABIB
*︎ARUMAI ︎ WRITERS ︎SSOCIATION️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa*_
*(︎.︎.︎)*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI ( Faddy baby).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
My Facebook group :Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
Ibnul-Qayyim (Allah Yayi masa Rahama) yana cewa: *”Lalle damuwa, baƙin ciki da qunci suna faruwa ne ta dalilai guda biyu: _Daya daga cikinsu shine son duniya da nemanta (ta kowace hanya), na biyu kuma rashin aikata ayyukan kwarai da (kyautata) ibada”_*
[Iddatus-Saabireen – P. 265].
Allah kasa mu dace.
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK’R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D’AN TARKU DA HAZIK’AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD’UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K’AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK’E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K’OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN
K’ABILA CE! K’ABILA CE!! K’ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K’ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D’AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K’ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT
08142904255.
Shafi na 18&19.
Hassana sosai ta tsorata, hakan yasa ta saki jug d’in hannunta ta bud’e k’ofar Office d’in zata fita, sai dai ina ta makara kafin ta bud’e k’ofar sai dai taji anjawo hannunta da k’arfi, an dawo da ita baya. Hassana cikin tsoro ta d’aga kai tana kallan Habib”.
Habib ko rik’e hannun Hassana ya yi da k’arfi da d’ayan hannunsa, d’ayan hannun kuma ya dafe kan shi da shi.
Hassana da Habib kusan atare suka yi k’ara wadda duk kusan wanda ke cikin Sanat Company babu wanda bai ji k’ararnan ba”.
Ita Hassana k’arar tsoran yanayin da taga Habib ne ta yi, shi kuma Habib ta sabon yanayin da yatsinci kan shi cike ce. Hassana cikin tsoro ta kalli Habib tana cewa, “Wayyo hannuna Oga Habib dan Allah ka yi hak’uri kasakanmin hannu”. Hassana ganin Habib kamar ba cikin hanyyacin shi ya ke ba, kuma ya rik’e hannunta katakam, ga zafin rik’on da ya yi mata take ji. Hakan yasa Hassana ta dage sai ihu ta ke”.
Dai-dai likacin ne kuma Bilya da Farida suka shigo Sanat company. Bilya da Farida da saurinsa suka k’arasa shiga cikin Sanat company. Inda suke jiyo ihun suka nufa. Dai-dai lokacin shima Manager ya fito daga Office d’in shi da sauri ya nufi na Oga Habib dan anan ya ke jiyo sautin k’arar. Atak’aice dai duk wani ma’aikacin da ke cikin Sanat yughurt, da saurinsa ya ke nufa inda ya ke jin alamun k’arar mutum”.
Manager da Bilya kusan atare suka turo k’ofar office d’in Oga Habib, inda Farida da Billy suka mara masu baya. Bilya cikin tashin hankali ya nufi inda Habib ya ke, ganin yarik’e hannun Hassana kata kam, yak’i saki, sai wasu magan-ganu da yake yi kad’an-kad’an, bazaka iya jin me yake cewa ba, kodan ihun da Hassana ta ke yine”.
Bilya cikin girmama da fargabar ganin yanayin da yaga Habib, ya ce, “Oga Habib lafiya karik’e mata hannu?, idan laifi taima dan Allah ka yi hak’uri “. Habib kallan Bilya ya yi yana zazzare ido. Bilya kallan Habib ya kuma yi da kyau, dan sosai abinda Habib ya yi ya ke naiman d’aure mai kai, dan asanin Bilya mata ma masu aji Habib bai kulaba bare kuma Hassana da ke a k’ark’ashinshi. Sannan idan ya lura da kyau kamar Habib bacikin hayyacin shi ya ke ba. Hakan yasa Bilya kama hannun Habib da niyyar fusge hannun Hassana.
Wani duka Habib ya ke ma Bilya a wuya, wanda sai da Bilya ya yi k’ara. Bilya da sauri ya matsa yana kallan Habib. Bilya manager ya kalla yana dafe gefan wuyan shi inda Habib ya nusai, yace, “Manager lafiyar Oga Habib k’alau kuwa? “. Manager kallan Bilya ya yi, ya ce, “Nima abinda nake tunani kenan, amma bari mugani”.
Manager matsawa ya yi kusa da Habib ya ce, “M. D, dan Allah ka yi hak’uri idan laifi taima, kasakar mata hannu yau zamu koreta daga ma’aikatar nan baki d’aya “. manager ganin Habib ya yi banza da shi yana kallan shi, hakan yasa ya kama hannun Habib da niyyar b’amb’are na Hassana”.
Habib duka ya kawo ma manager.
Allah ya tai maki manager ya kauce da sauri. Tun daga nan fa kowa ya fara baya-baya.
Hassana ko ganin haka suna nai man fita subarta daga ita sai Habib, ya sa ta fasa kuka tana cewa, “Wayyo Allah Oga Bilya dan Allah karku tafi, manager dan Allah kuzo ku taimaka min”.
Bilya kallan manager ya yi dadamuwa yace, manager akwai damuwafa, Wallahi Oga Habib baida Lafiya, dan kai kasan wannan abinda da yake yi ba halinsa bane, idan zaka kalli idon shima kamar baya cikin hayyacinsa”. Manager numfasawa ya yi sannan ya ce, “Wallahi maganarka hakane, nima abinda nake tunani kenan, yanzu ya kake ganin za ai? “. Shiru Bilya ya yi, Sannan ya ce, “Ni gani nake kawai mu kwaci yarinyar nan daga hannun shi, mu kai shi gida, ala bashi sai a kira likitan k’wak’walwa ya duba shi”. “Eh haka za ayi”. Cewar manager. Manager wasu k’arfafan samari da ke aiki gurin guda biyu yasa su tai maka masu”.
Bilya da manager ne suka yi jarimtar rik’e Oga Habib, sannan sauran staff d’in guda biyu suka k’wace hannun Hassana daga hannun Oga Habib da kyar. Sosai su manager suka sha wahala wajan sa Oga Habib a mota. Sannan Bilya ya shiga ya tuk’a motar da manager da Faruq kuma suka rik’e Oga Habib. Ahaka dai suka samu suka k’arasa gidansu Oga Habib”.
Hassana ko bayan ta samu an kwaceta da kyar daga hannun Oga Habib guri ta zamu tazauna tana sare hawayanta, da kuma al’ajabin abinda yasa mu Habib. Hassana na nan zaune supervisor tazo tana mata wani irin kallo mai ma’anoni da dama. Billy kallan Hassana ta yi tace, “Hassana ki ke ko?, sannu Hassana gaskiya kinyi k’okari, sai dai ina baki shawar duk abinda ki kaima Oga Habib kafin Hajiyarsa ta dawo ki yi gaggawar warware shi”. Billy na fad’in haka ta juya ta tafi, tabar Hassana nan tsaye da baki sake tana kallanta”.
Hassana maganar zuci tafara, “Tom wai me supervisor ta ke nufi da duk abinda ta yi ma Oga Habib, tom ita mai tai me?, me zata yi gaggawar warware wa?”. Nan dai Hassana ta gama tunaninta bata gane takan zancan Billy ba ta tashi”.
Can gidan su Oga Habib ko, da kyar su manager su kama Oga Habib suka shigar dashi d’aki, sai dai suna sashi suka rufe d’akin.
Bilya hankalin shi ta she ya ke kallan manager ya ce, “Manager karfa ace Oga Habib hauka ya ke, dan abin ya tadamin hankali, kalli yadda ya ke bige-bige! “.”tom Wallahi nima haka ne tunani, dan bisaga alamu wannan abinda ya ke kamar hauka ne, tom yanzu in ma munkira likita taya zai duba shi ayarda ya ke haka d’innan? “. Cewar manager.
Shiru Bilya yi yi sannan ya ce, “Gasakiya na fara tunanin kiran Hajiyarsa in fad’i mata halinda Oga Habib ya ke ciki, kasan hausawa sun ce da zafi-zafi ake dukan k’arfe, gara ai gaggawar fad’a mata, in dai Hajiya ce a yauma zaka iya ganinta, ko gobe da wuri”.
Haka ko akai, Bilya kiran Hajiya Turai ya yi yi, Bayan sun gaisa ne ya ce,” Hajiya a kwai damuwa fa, Oga Habib bashi da lafiya, kuma gaskiya yana yin ciwan yana buk’atar ki zo kusa da sauri”. Hajiya Turai shiru ta yi , sannan cikin damuwa ta ce, “Bakomai Bilya ganinan zuwa, idan na sauka idan nasamu ticket zan juyo yau”. Hajiya kamar yadda ta ce haka akai, tana sauka jirgi ta nemi ticket d’in Nigeria Allah ya te maketa ta kuma samu”.
K’arfe sha biyu na dare, jirginsu Hajiya Turai ya sauka. Bilya ne ya je d’akko Hajiya Turai. Hajiya Turai na issowa ta kalli Bilya cikin tsantsar damuwa, ta ce, “Bilya kai ni in ganshi”. Bilya cikin lallashi ya kalli Hajiya Turai ya ce, “ki yi hak’uri Hajiya yanzu nasan k’ila ya samu bacci zuwa gobe sai ki ganshi”. Hajiya Turai cikin d’aga murya ta ce, “Bilya kana nufin in kwanta in yi bacci banga halinda Habib ya ke ba, kai yanzu kana ganin zan iya bacci batare da na duba jikin Habib ba? “. Shiru Billy ya yi, sannan ya ce, “Hajiya ki yi hak’uri, Wallahi bazai yuwuba ne ki ganshi, ki dai bari sai goban”.”You are very stupid, Bilya ko kana hauka ne!, ko-ko wani abinne ya sa mai kuke b’oyemin!!? “. Hajiya Turai ta idasa maganar kamar zata yi kuka. Sannan ta ci gaba da cewa, “Bilya wai baku kira Family doctor mu bane ya duba shi? “.Bilya ganin Hajiya Turai tana nai man rud’ewa ya sa, Bilya cikin sanyin murya mai kwantar da hankali, ya ce, “Hajiya ki yi hak’uri, ina mai bak’in cikin sanar da ke halin da Oga Habib ya ke ayanzu haka, Hajiya Wallahi da kyar muka samu daga Sanat Company muka kawo shi gida, ayanzu haka maganar da na ke miki babu mai iya shiga inda Oga Habib ya ke, amma ban sani ba ko inda ke Mahaifiya ce zaki iya ganin shi”. Hajiya Turai kuka ta fasa, ta ce, “Innalilahi’wa inna’ilaihirraji’un , Bilya muje inga Halinda ya ke, dan Allah Bilya muje ka kaini”. Hajiya Turai hanyar part d’in Habib ta yi cikin tashin hankali ta na goge hawan da ke zubar mata”.
Bilya tsayawa ya yi yana jiran Hajiya Turai ta shiga.
Hajiya Turai ko na zuwa ta bud’e kofar ta afka. Sai dai kwance ta iske Habib yana bacci ya yi kaca-kaca da d’akin. Hajiya Turai zuk’unnawa ta yi tana kuka kad’an-kad’an gudin karta tada Habib daga bacci.
Bilya jin Hajiya Turai shiru, ya sa ya shiga d’akin, cikin damuwa Bilya ya kalli Hajiya Turai dan sosai ta bashi tausai, hakan yasa Bilya cikin damuwa ya kamo hannun Hajiya Turai, ya ce, “Ki yi hak’uri Hajiya kizo muje ki kwanta ki huta karki tada shi”.
Hajiya Turai tashi ta yi tabi bayan Bilya tana goge hawayanta, bayan sun fita ne, Hajiya Turai ta kalli Bilya ta ce, “Bilya dan Allah ko zaka koma ka kwana da shi? “. Shiru Billy ya yi sannan ya kalli Hajiya Turai, cikin taushin murya ya ce, “Hajiya Wallahi ko ke dan Oga Habib na bacci ne kika samu ganinshi, amma Wallahi idan idon shii biyu bazaki tab’a iya shiga inda ya ke ba, kwana wajan shi da akwai had’ari”. Hajiya Turai tana kuka ta kalli Bilya ta ce, “Bilya kana nufin Habib duka yake?, idan haka ne kana son cemin Habib hauka ya ke kenan? “. “Tom Hajiya bandai sani ba , amma dai tabbas Oga Habib duka ya ke”. Hajiya Turai ta fiya tayi tana Kuka tashiga site d’inta”.
Hajiya Turai adaran kusan zaune ta kwana, tsabar fargabar abinda ke damun Habib. Bayan Hajiya Turai ta Idar da Sallar asuba ne ta tashi ta shiga room d’in da Farida ta ke kwana, dan taga alamar Farida bata san ta dawo ba. Sai dai maganar da Hajiya Turai ta ji Farida na yi ne yasa ta tsaya.
Hajiya Turai tsayawa ta yi cikin furgici da gigin jin abinda Farida ta ke cewa, “Mommy Wallahi na so zuwa Office d’in nashi kafin ciwan ya riskeshi, amma sai drivern gidan ya yi min shiririta, ni yanzu abinda ke damuna shikenan yanzu babu yadda za ai yarinyar da yafarka ya gani shikenan da ita zai rik’a yadda ke nan? “. Daga can b’angaran na ji tace, “Haba Farida me yasa tun da kika tabbata ya sha tea d’in ka yadda kika rik’a nesa da shi?, bacin kinajin abinda malam mai buzu ya ce miki, ko ajiyan Farida sai da nakiraki nace miki karki yadda ki nesa da Habib, tahakanne zamu zasu abinda muke nema cikin sauki”. Farida shiru ta yi sannan ta ce, “Mommy ya zanyi dan Allah? “. Daga can b’angaran aka ce, “Farida kina jina ko? “? “Eh Mommy inaji”. “Yanzu Hajiya Turai ta dawo gidanne? “. Farida cikin tabbarwa inda batasan da dawowar Hajiya Turai ba, ta ce, “A’a Mommy ina tunanin yau zata dawo”. “Ok, yasunan yarinyar da kika ce alokacinda ciwan ya same itace kusa da ita? “. Shiru Farida ta yi dan ita batatab’a ganin Hassana ba ma sai jiya da abin yafaru, hakan yasa, ta ce, “Mommy bansan sunan yarinyar ba, amma ina tunani a Company nin shi yarinyar ta ke aiki”. “Shikenan ki yi k’ok’ari ki samomin sunan yarinyar”. Nan Farida taima Mahaifiyarta sallama ta kashe kiran”.
Hajiya Turai ko mutuwar tsaye ta yi, da ta gama jin duk abinda Farida ke cewa ita da Mahaifiyar. Daya ke Farida a Hans free ta sa wayar shi yasa Hajiya Turai taji duk abinda suka ce……….
TOfA WAI meke faruwa ne, nifa har yanzu bangane ba?????.
Karki damu ke dai kibini ahankali zaki gane
Dan Allah ayi hak’urin jina da akayi kwana biyu shiru, ina ba duk wani mai bibiyar littafin Oga Habib hak’uri, na jina shiru da aka yi kwana biyu, Allah Aimin uziri insha Allah haka bazai k’ara faruwa ba.
Masoya wa inda suka nuna min kulawa ta hanyar ganin text messsage d’in su nagodee, da masu kiran waya duk ina godiya sosai
COMMENT
&
SHERE
PLEASE
OGA HABIB
*︎ARUMAI ︎ WRITERS ︎SSOCIATION️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa*_
*(︎.︎.︎)*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy babuy).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
*☘️ADDU’A DAGA BAKIN ANNABI S.A.W.☘️*
_Ya Allah Ina Neman Tsarinka Daga Sharrin Jina Da Ganina, Da Sharrin Harshe na, Da Sharrin Zucuya ta, Da Kuma Sharrin Sha’awa ta… Yana Nufin Tsiraicinsa._
Abu Dawud,Tirmizy Da Nasa’i Suka Rawaito Shi.
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK’R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D’AN TARKU DA HAZIK’AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD’UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K’AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK’E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K’OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN
K’ABILA CE! K’ABILA CE!! K’ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K’ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA AKE POSTING.
KI GARZAYA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D’AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K’ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT
08142904255.
Shafi na 20&21
Hajiya Turai zufa ce ke keto mata ko ta’ina , dan sosai abinda ta ji Farida na fad’a ya tada mata hankali, ya rud’ata, Hajiya Turai maganar zuciya ta fara, tana cewa, “Yanzu abinda kunnena suka jimin hakane kuwa?, Kai ina bazai yuwuba ace Hajiya Murja zata iya had’a baki da ‘yarta su juya brain d’in Habib? “. Hajiya Turai zuciyarta ce ta bata amsa, da cewa, “Tom idan kince k’arya ne, abinda da kunnanki su ka jimiki fa? “. Shiru Hajiya Turai ta yi, sai zuwa can ta ce, “Tabbas abinda kunnena suka ji min hakane, tom amma meyasa Hajiya Murja zata juya k’wak’walwar Habib?, me Habib ya yi mata?, Sannan me Farida ta ke nufi da taso ace lokacinda lallurar ta samu Habib tana kusa dashi?, tasan da da’ita zai rik’a yarda?, me suke nufi da haka?, Sannan wata yarinya ce suke maganar lokacinda Habib ya farka da ita yayi tozali ?”. Hajiya Turai dafe kanta tayi kamar zata sa kuka tace, “Wayyo Allah wa zai amsa min wa’innan tambayoyin?, Yallah ga Habib nan kai kasan dalilin shigar wannan lallura jikinshi Ya Allah kakawo mai sauk’i”. Hajiya Turai fasa shiga d’akin Farida ta yi ta juya tana mai goge hawayan dake ambaliya cikin fuskarta. Hajiya Turai Bilya ta kira awaya, dan duk ma aikatan gidan mutum biyu ne Hajiya Turai ta yadda da su wa inda har ta ke naiman shawara agunsu, wato Bilya da Baba Lami.
Bilya na kwance tunanin halinda Habib ya ke Shikanshi kusan ya hana shi sakat. Bilya na awannan halinne kiran Hajiya Turai ya shigo wayar shi. Bilya cikin hanzari ya d’aga wayar, banji mai Hajiya Turai ta ce ba, sai dai naji Bilya ya ce, “Ok, Hajiya ganinan zuwa”.
Bilya tashi ya yi ya nufi part d’in Hajiya Turai. Bilya zaune ya iske Hajiya Turai tana kuka. Cikin damuwa Bilya ya samu gu ya zauna, sannan cikin sanyi murya mai cike da rauni ya kalli Hajiya Turai ya ce,”Hajiya tabbas na san dole kishiga damuwa, tom amma ita damuwar ce babu maganin abinda zatayi mana, ki yi hak’uri kima Oga Habib addu’a, dan ayanzu addu’arki ya ke buk’ata , nasan zata taimaka mai sosai wajan rage mai halinda ya ke ciki”.
Hajiya Turai da katawa ta yi daga kukan da ta keyi, ta d’ago tana kallan Bilya, Hajiya Turai cikin raunin murya mai kama da kuka ta ce, “Bilya ayanzu ba halinda Habib ya ke ciki ba nake ma kuka”HajiyaTurai shiru ta yi ta da kata nad’an wani lokaci, sannan ta ce, “Bilya d’akin Farida nayi sammakon shiga da niyyar in sanar da ita dawowata, amma sai kunnuwana suka ji min wasu zantuka da ta ke yi, tabbas Bilya da ace wanine ya fad’a min abinda kunnena yaji min yau Farida na fad’a Wallahi da bazan yarda ba”.Hajiya Turai shiru ta yi sannan ta ce, “Bilya alokacinda lallurannan ta samu Habib wata yarinya ce kusa da shi? “. Bilya cikin mamaki ya kalli Hajiya Turai jin abinda ta ce, amma sai ya waske kawai, ya ce, “Hajiya Hassana ce yarinyar da ke aiki Sanat company ta ke kwana gidannan”. “Me ya shigar da ita Office d’in Habib?. ”
” Eh tom gaskiya ban sani ba”. Hajiya Turai kallan Bilya ta yi ta ce, “Kaje yanzu ka tahomin da yarinyar ina son ganinta”. Bilya kallan Hajiya Turai ya yi zai yi magana ta d’aga mai hannu. Hakan yasa Bilya ya juya ya tafi yana tunanin lafiya Hajiya Turai ke son ganin Hassana, can wata zuciyar ta ce mai, “Tom ko dai maganar da tace taji, cemata akai ana zargin Hassana ne, ita taima Oga Habib wani abun”.Haka dai Bilya ya idasa b’angaran masu aikin gidan yana tunani kala-kala, shi dai addu’ar shi d’aya in ma wani sharinne aka k’ullama Hassana Allah ya kub’utar da ita. Bilya Jimmai ya gani tana shara. Kallanta ya yi, ya ce, “Hassana fa? “. “Tana ciki Oga Bilya”. “Ki ce mata Hajiyar naiman ta yanzu, tazo yanzu”. Bilya na fad’in haka ya juya ya tafi”.
Jimmai kuma barin sharar ta yi ta shiga ta kira Hassana. Lokacin Hassana na kwance tana bacci, Jimmai ta bubbuga ta ta ce, “Hassana ki tashi Hajiyar Oga Habib na son ganinki yanzu”. Hassana tashi ta yi tana kallan Jimmai ta ce, “Jimmai lafiya dai ko? “. “Tom nima dai bansani ba amma ki je kiji”. Hassana tashi ta yi ta sa Hijab d’in Jimmai ta tafi kiran da Hajiya ke mata, zuciyarta na cike da fargaban kiran”.
Hassana sallama ta yi, tana jiran abata izinin shiga.
Daga cikin falon Bilya ya ce, “Hassana ki shigo mana”. Hassana shiga ta yi, ta zuk’unna can gefa ta gaida Hajiyar Habib. HajiyaTurai ba tare da ta amsa gaisuwar da Hassana tai mata ba, ta kalli Hassana ta ce, “Hassana tambayarki na ke son yi, kuma ina so kifad’amin gaskiya? “. Hassana kallan Hajiya Turai ta yi gabanta na fad’uwa ta ce, “Inaji Hajiya, kuma insha Allah zan fad’amiki gaskiya”. Hajiya Turai, kallan Hassana ta yi na second’s sanan ta ce, “Watanki nawa da fara aiki a Sanat yughurt? “. “Wata na biyu na ke Hajiya”. Cewar Hassanan. “Ok, alokacinda lallurar nan ta samu Habib ance min kina Office d’in shi, hakane? “. Wata irin fad’uwar gabace ta samu Hassana dan sai maganar Billy ta dawo mata farko da ta ce mata, “Hassana ki yi gaggawar warware duk abinda ki kaima Oga Habib tun kafin Hajiyarsa ta dawo”.
Bilya ne ya kalli Hassana ganin ta fad’a kogon tunani, ya ce, “Hassana ke fa Hajiya ke saurare”.
Hassana kallan Hajiya Turai ta yi, sannan cikin sanyin murya ta ce, “Eh Hajiya inanan”. Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ce, “Me yashigar da ke Office d’in shi alokacin?”. Hassana Bilya ta nuna ma Hajiya Turai ta ce, “Hajiya Oga Bilya ne yaban ruwan tea in kaime”. shiru Hajiya Turai ta yi, dan tabbas idan bata mantaba taji Hajiya Murja ta ce ma, Mahaifiyarta, indai Farida ta tabbata ta ba Habib ruwan tea d’in yasha shikenan, Hajiya Turai azuciyarta ta ce, “Tom ko dai had’a kai su kai harda Bilyan ma?, nan dai Hajiya Turai da taga bata da mai amsa mata, maida kallanta ga Bilya ta yi, ta ce, “Bilya waya ce ka kaima Habib ruwan tea bacin kasan daga nan ake kai mai? “.Bilya cikin natsuwa ya ce, “Hajiya shi yace in kaime, nima bansan dalilinshi ba nahakan”. Hajiya Turai kallan tuhuwa taima Bilya sannan ta ce, “Tom meyasa baka kaime da kanka ba kaba Hassana? “. Bilya cikin full Confidence, ya ce, dan yaga kamar Hajiya Turai yau zarkin shi ta ke yi, hakan yasa ya ce, “Hajiya tun kafin in Tashi bacci Farida ta matsamin da kira akan sai dai in kaita Sanat yughurt, amma nace mata sai nayi wanka, rok’ona ta yi akan dan Allah in kaita, alabashi idan na dawo sai in yi wankan, tom ni kuma bazan iya musa mata ba, hakan yasa sai nace mata ganinnan zuwa, tom shine fa bayan takatse kiran ni kuma na yi sauri nashiga wanka. Tom ina fitowa daga wanka Oga Habib ya kirani akan in siyo mai tea in kai mai yanzu. Tom nasan idan Oga Habib ya na son Abu yadda yake, hakan yasa ina fitowa na manta da Farida na jirana na tafi, sai da nashiga Sanat company sannan natuna da tun d’azu Farida ke jirana. Tom nasan Oga Habib idan nashiga dakyar idan zai barni in fito yanzu zai iya sani wani abun, hakan yasa da naga Hassana na bata tea d’in nace ta kaime, ni kuma na dawo da niyyar d’aukar Farida, tom ahanyama muka had’u ta gaji da jirana ta taho a napep,na tsaida napep d’in na d’auketa. Shine fa muna shiga cikin Company muka ji wata irin razanannar k’ara Oga Habib ya yi”.
Bilya kallan Hajiya Turai ya yi ya ce, “wannan shine abinda nasani Hajiya, amma ga Hassana nan sai ta idasa miki bayani”.
Shiru Hajiya Turai ta yi dan tabbas a kwai alamun gaskiya a magan-ganun Bilya, hakan yasa Hajiya Turai ta kalli Hassana ta ce, “Hassana bayan shigarki Office d’in Habib me yafaru, alokacin? “. Hassana cikin sanyin murya ta ce, ” Hajiya Duk da Oga Habib nada idan mutum ya yi nocking ya dad’e bai amsa mai ba, amma gaskiya a Jiya da zan shiga office d’in shi, naji shirun ya yi yawa, dan har saida nafara tunanin ko dai baya office d’in ne, sannan zuwa can yace in shigo, koda nashiga jug d’in hannuna na mik’a mai na ce inji Oga Bilya ya ce zai dawo yanzu”. Shiru Hassana ta yi ta d’an numfasa, sannan ta ci gaba da cewa, ” gaskiya tunda nashiga Office d’in Oga Habib zan ita cewa babu lafiya atattare da yadda naga yana yin shi, dan koda na bashi sak’on Oga Bilya, bai amsamin ba bai kuma kallan ba, sai dai ya tashi tsaye ayanayin yadda naga jikinshi kamar rawa yake, hakan yasa sai naji tsoro naja baya, sai ji nai ya mik’on hannun shi ya ce, dan Allah in rik’e mai. Tom ni dama gaskiya ko ayanayin yadda naji maganarsa nasan ba lafiyar shi k’alau ba, hakan ya sa naruga zan bud’e k’ofa in fita, amma kafin in fita har yarik’omin hannu, dan su Oga Bilya ne ma suka k’watan daga hannun shi”.
Shiru Hassana ta yi sannan ta ce, “wannan shine abinda ya faru, Hajiya da nashiga office d’in Oga Habib kai mai tea d’in “.
Shiru Hajiya Turai ta yi tana kallan Hassana, dan akwai alamun gaskiya a maganar Hassana d’in, dan yanzu ta san abinda kunnan ta yaji mata hakane, Farida ce ta ba Habib wani tea d’in kenan, wato idan ta fahimta farida taso zuwa office d’in Habib kafin abinda ya sa mai ya sa mai.
Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, “Hassana je ki abinki”. Bayan Hassana ta tafi ne, Hajiya Turai ta kalli Bilya ta ce, Bilya kaje Zaria yau d’in nan ka tahomin da Baba lami, dan ina buk’atarta sosai, amma dan Allah kafin munje akaima Habib abin break fast, nasan tunjiya baici komai ba, inda bacikin hankalinshi ya ke ba.Bilya tashi ya yi Hajiya Turai, tafi bayansu suka tafi ganin halinda Habib ya kwana, tare da kai mai abin break fast. Bilya tsayawa ya yi daga k’ofar d’akin ya ce, “Hajiya ko za ki yi gaba? “. Hajiya Turai gaba ta yi batare da ta tankama Bilya ba.Hajiya Turai zaune ta iske Habib, sai dai kafin ta k’arasa inda ya ke Habib ya yo kan Hajiya Turai”.
Wani irin rik’o Habib ya yi ma Hajiya Turai, yana wujijjigata. Hajiya Turai tun tana daurewa tana cewa, “Habib ni ce fa, Habib mahaifiyarka ce fa ni, Habib kamanta ni ne ?, sakanni Habib da zafi! “. Haka Hajiya Turai ta idasa maganar cikin tashin hankali. Daga k’arshe da taga Habib tabbas bacikin hankalinshi ya ke ba, hakan yasa ta fasa k’ara ta ce, “Wayyo Bilya kana ina zo ka tai makamin! “.
Bilya da saurinsa ya shiga, kan Habib ya yo, Habib ko na ganin Bilya ya saki Hajiya Turai ya yi kan Bilya, sai dai Bilya na ganin haka ya fita da gudu. Hajiya Turai ko ta k’ofar baya ta fita itama. Hajiya Turai falon bedroom d’in da Habib ya ke ta zauna tana, kuka. Bilya zagayawa ya yi ta baya yashiga falon Habib d’in, zaune Bilya ya iske Hajiya Turai tana kuka “.
Bilya k’arasawa inda Hajiya Turai ta ke ya yi. Bilya cikin lallashi ya ce, “ki yi hak’uri Hajiya shi kuka da kika gani babu wani abunda zai miki sai dai ya samiki wani ciwan, yanzu abinda ya kamata muyi musan abinda ke damun Oga Habib”. Hajiya Turai d’aga kai tayi tana kallan Bilya ta ce, “Bilya na san meke damun Habib, shi yasa nake son ganin Baba lami da sauri, ka tafi Zaria yanzu dan Allah Bilya ka tahomin da Baba Lami”. “Shikenan Hajiya babu damuwa insha Allah yau d’innan zaki ga Baba Lami. Bilya na fad’in haka ya yi ma Hajiya Turai sallama ya kama hanyar Zaria.
Hajiya Turai ko na nan zaune tana tunanin, magan-ganun Farida na d’azu, ta ce, “wato idan nagane maganar Farida tana nufin wadda Habib ya tashi ya farka a halinda ya ke yagani, zai iya yadda da ita kenan.kai wai tom meye niyyar Farida ne akan Habib?, ya Allah ka kawo min Baba Lami yau”. Hajiya Turai fitowa daga falon Habib ta yi, tana fitowa ta had’u da Farida ita kuma da shirinta na barin gidan”.
Farida cikin mamaki ta kalli Hajiya Turai ta ce, “Kai Mommy ashe kin dawo?, yaushe kika dawo? “. Hajiya Turai ji tai kamar tai banza da Farida, sai da bata son ta nuna ma Farida komai, akwai lokaci acewarta. Hakan yasa Hajiya Turai ta ce, “Jiya da daddare lokacin kinyi bacci, Ina zaki ne haka? “. Hajiya Turai ta tambayi Farida.”Sak’o Mommyna ta aikan in amso mata, yanzu zan dawo”. “Ok”. Hajiya Turai ta ce mata sannan ta juya ta tafi. Hajiya Turai Bilya ta kira awaya, Bilya na d’agawa tace, “Hello Bilya kana jina ko? “. “Eh Hajiya Ina ji”. “Yauwa, Bilya idan baka riga katafi ba, ka je Sanat company yanzu dan Allah, ga Farida nan zata je yanzu, kayi k’okari ina son sanin abinda ya kaita”. “Shikenan babu damuwa, bari inje kafin ta isa”. Bilya na fad’in haka, ya juya yakama hanyar Sanat company”.
Hajiya Turai nagama wayar sai ga wata binta da ke mata wanki, Hajiya Turai kiranta ta yi, ta ce, “Binta kiramin yarinyar da ke aiki a Sanat yughurt”. Binta da saurinta ta juya ta tafi dan ida sak’on Hajiya Turai”.
Hassana na zaune ita kad’ai dan soran worker’s d’in Kowa ya kama gabanshi dan yin aikin da ya ke amazaunin nashi, binta tazo ta ce, “Ke Hajiya na kiranki, ta ce ki sameta a falonta”. Gaban Hassana fad’uwa ya yi jin wai Hajiya na kiranta. Azuciyarta ta ce, “Tom bayanzu ta kirani ba ba dad’ewa, Allah dai kasa lafiya”. Hassana tashi ta yi tanufi site d’in Hajiya Turai. Hassana zaune ta iske Hajiya Turai a falonta. Hassana cikin sanyin muryarta ta yi sallama, d’annesa da Hajiya Turai Hassana ta zauna, bayan Hassana ta zauna ne, ta kalli Hajiya Turai ta ce, “Hajiya gani ance kina kirana”. Hajiya Turai abin break fast d’in da suka kaima Habib suka dawo dashi ta mik’ama Hassana ta ce, “Kin san site d’in Habib? “. “Eh na sani”. “Yauwa, Hassana dan Allah me ba Habib abinci ne baya nan, na aikai Zaria, shine dan Allah nake son ki kai mai”.
Hassana cikin girmamawa ta ce”Tom”. D’aukar abin break fast d’in Hassana tayi ta tafi.Hajiya Turai tashi ta yi ta yi bedroom d’in ta fita tashiga Falon Habib ta na jiran zuwan Hassana taga ikon Allah, ta ga maganar da Farida ta fad’a gaskiya ne kok’aya”.
Hassana ko,
tambayr kanta ita kad’ai ta yi, ta ce, “Tom oga Habib ya warkene? “.Nan dai bata da mai bata amsa, haka Hassana ta nufi site d’in Habib da abincin gabanta na fad’uwa. kasan cewar Hassana ba taji labarin Habib na dukaba, hakan yasa ba wata fargabar hakan, ta bud’e k’ofar ta shiga kai tsaye………
COMMENT
&
SHERE
PLEASE
OGA HABIB
*︎ARUMAI ︎ WRITERS ︎SSOCIATION️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa*_
*(︎.︎.︎)*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK’R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D’AN TARKU DA HAZIK’AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD’UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K’AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK’E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K’OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN
K’ABILA CE! K’ABILA CE!! K’ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K’ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA AKE POSTING.
KI GARZAYA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D’AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K’ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT
08142904255.
Shafi na 22&23.
Habib na kwance ya juya baya, motsin bud’e k’ofar da yaji yasa ya juyo da sauri. Habib batare da yasan ko waye ba ya tashi da sauri ya yo kan Hassana. Hassana ko ganin yadda Habib yayo kanta da sauri sai abin ya bata tsoro, duk da bata san yana duka ba, Hassana gefe d’aya ta takure da break fast d’in dake hannunta.
Hajiya Turai da ke lekyan Hassana ta window, dafe kai tayi dan a tunaninta Habib zai rufe Hassana da duka ne, amma sai taga akasin hakan.
Habib na zuwa inda Hassana ta ke da sauri ya kamo hannunta yana janta cikin d’akin, Hassana da mamaki tabi Habib da kallo.
Habib ko kan lover chair d’in shi ya zaunar da Hassana shima ya zauna kusa da ita, ba baki sai dai kallanta kawai da yake yi. Hassana ko koda ganin yadda Habib yake kallanta da yanayin yadda yake acting ta kuma tabbatar da Habib bacikin hankalinshi ya ke ba. Hassana so ta ke ta kwace hannunta daga na Habib amma ta kasa, gashi duk cikin tsoro ta ke. Cikin jarumta da rawar murya Hassana ta ce, “Oga Habib ga abin break fast d’in ka, Hajiya ta ce in kawo ma”. Hassana ta nuna ma Habib abin break fast d’in. ruwan Lipton ne sai gwangwanin madara da na Nescafe da milo, Sai wainar k’wai. Habib kalla kawai ya yi batare da yace ma Hassana ko mai ba.
Hassana ko ganin Habib bai ce mata ko mai ba, sai ta kuma cewa, muryarta na rawa, “Oga Habib ka sakanmin hannuna in had’ama tea d’in “. Habib sakin hannun Hassana ya yi. Hassana kuma da sauri tatashi ta had’ama Habib tea d’in, bayan tagama had’a mai, kallan shi ta yi cikin rawar murya ta ce, “Oga Habib ga tea d’in? “. Habib hannu ya mik’ama Hassana ta mik’amai tea d’in. Hassana ko ganin ta yi abinda ya kawota tashi ta yi daniyyarta ta tafi. Habib ya yi saurin rik’o hannunta. Hassana cikin tsoro ta kalli Habib dan ita yanzu tsoro ma ya ke bata, dan daga ganin shi kasan bacikin hankalinshi ya ke ba, Hassana kamar zata yi kuka, ta ce, “Oga Habib Hajiya ke jirana dan Allah ka sakanmin hannu”.Habib kafad’a ya mak’alema Hassana alamun nak’i d’in. Babu yadda Hassana batayi ba Habib ya sakar mata hannu amma yak’i, Hassana kamar zata yi kuka ta kalli Habib ta ce, “Oga Habib dan Allah katai maka kasanmin hannuna dan Allah”. Hassana ta fad’i maganar kamar zatayi kuka. Habib sake mak’ema Hassana kafad’a ya yi.
Hajiya Turai ko tananan tsaye jikin window tana kallan duk abinda ke faruwa tsakanin Habib da Hassana. Hajiya Turai ganin Hassana ta fara kuka akan Habib ya saketa shi kuma yak’i yasa ta fita da sauri ta zagaya ta shiga bedroom d’in Habib d’in . Habib ko naganin Hajiya Turai ya saki Hassana ya yi kan Hajiya Turai. Habib na isa yarik’e Hajiya Turai yana jijjigata. Hajiya Turai bata san sanda ta fasa kuka ba, bawai jijjigar da Habib ya ke mata bace tasata kuka ba, a’a, bak’in cikin yadda aka rabata da d’anta guda ne yake sata kuka, ace wai ita ce yau Habib bai son gani in har yaganta sai dai yayi ta jijjigata, hakan yasa Hajiya Turai tai ta kuka, Habib kuma na ci gaba da jijjigata”.
Hassana ko ganin yadda Hajiya Turai ke kuka, yasa cikin tsoro ta nufi gurin da ta ke dan itama tsoro ta ke kar Habib ya yi mata yadda ya ke ma Hajiya Turai. Hassana na zuwa cikin tsoro da fargabar kar Habib itama ya yi mata abinda ya ke ma Mahaifiyar shi. Hassana tana kuka ta rik’e hanun Habib tana cewa,cikin kuka” Oga Habib dan Allah ka saketa, Mahaifiyarka ce fa, ka barta “. Hassana anshe Hajiya Turai ta yi daga hannun Habib. Hassana kama hannun Hajiya Turai ta yi tazaunar ta ita bakin gadon Habib tana cewa, “Hajiya dan Allah kiyi hak’uri kibar kuka, kinsan Oga Habib bazai miki hakaba cikin hankalin shi ba, ki yi hak’uri dan Allah kibar kukan Hajiya “. Hajiya Turai da katawa ta yi da kukan ta d’aga kai tana kallan Hassana, Hajiya Turai batare Da ta ce ma Hassana ko mai ba tashi ta fita daga d’akin”.
Hassana da kallo tabi Hajiya Turai, sannan itama ta tashi tabi bayan Hajiya Turai, sai dai kafin ta fita Habib ya yi saurin dawo da ita ta hanyar rik’o hannunta. Hassana kamar zata yi kuka ta kalli Habib, ta ce, “Oga Habib kasa kan min hannu dan Allah ina so zan tafi ne”. Habib mak’ema Hassana kafad’a ya yi. Duk yadda Hassana taso Habib ya saki hannunta k’i ya yi, k’arshe ta fashe da kuka.Haka Hassana ta yi kukanta ta gaji daga k’arshe ta yi shiru”.
Shiko Habib koda yaga Hassana na kuka kallanta kawai ya ke, kuma har yanzu yana rik’e da hannunta.
Hajiya Turai bayan ta koma falonta kuka ta yi sosai sai da ta gaji dan kanta sannan ta yi shiru. Hajiya Turai tashi ta yi ta koma falon Habib, ta window ta lek’a ta hango Hassana zaune da Habib kusa da ita yana rik’e da hannun Hassana kamar wata wadda tai mai laifi. Hajiya Turai kiran Hassana, ta yi,ta ce, Hassana kizo yanzu”. Hassana kallan Hajiya Turai ta yi, dake magana jikin window ta ce, “Hajiya tun d’azu nake son tashi Oga Habib ya hanani”. Hassana ta fad’i maganar kamar zata yi kuka.
Hajiya Turai cikin sanyin murya mai cike da rauni ta ce, “Hassana ki yi hak’uri kin ji dan Allah nasan yanzu Bilya zai shigo”. Hajiya Turai na fad’in haka tabar gun tana share hawayanta, dan sosai halinda Habib ya ke ciki ya ke damunta, uwa-uba kuma ganin yadda ya ke mata in tashiga wajan shi, wannan abin shike k’ara d’agama Hajiya Turai hankali”.
Bilya bashi ya dawo daga Zaria ba sai 3:13Pm. Haka Bilya da Baba Lami suka jera suka shiga falon Hajiya Turai. Zaune suka isketa kan caution ta yi ta gumi.
Bilya cikin tausayama halinda Hajiya Turai ta ke ciki ya yi sallama falon Hajiya Turai. Hajiya Turai d’aga kai ta yi tana kallan Bilya, sannan cikin sanyin murya ta amsa mai sallamar. Bilya da Baba lami shigowa sukai cikin falon suka zauna da nesa tsakaninsu da Hajiya Turai”.
Bilya Kallan Hajiya Turai ya yi ya ce, “Hajiya ga Baba lamin nan, bari inje inyi sallah ahanya ta saman”. Bilya na fad’in haka yatshi zai fita.
Hajiya Turai Kallan Bilya ta yi, cikin sanyin murya ta ce, “Bilya tun safe yarinyar nan na gurin Habib ya hanata fitowa, dan Allah ko za kai ma su musa magana ku shiga ku fito da ita? “. Bilya cikin damuwa da fad’uwar gaba ya kalli Hajiya Turai ya ce, “Ok, bar in yi sauri muje”. Bilya na fad’in haka ya juya ya fita daga falon. Bilya cikin tashin hankali ya nufi k’ofar da zata sada ka da falon Habib, ta window Bilya ya lek’a, dan a tunanin shima yanzu Habib ya yi ma Hassana illa, dan har yanzu Bai manta wujijjigawar da Habib ya yi ma Hajiya Turai ba, tom ita da ta ke mahaifiyarshima bare Kuma wata Hassana da tun lokacinda abin yasa meta da kyar aka kwaceta awajanshi. Bilya na maganganun zuci ya isa k’ofar, ta window Bilya ya lek’a da yake window abud’e ya ke”.
Zaune Bilya ya hangi Hassana da Habib da ke rik’e da hanbuta kata kam kamar irin yana tsoran za a kwace ta . Ajiyar zuciya Bilya ya yi ganin Hassana lafiya klau.
Hassana ko zaune ta ke sai zazzare ido ta ke kamar wadda tai k’arya asirinta yatonu.
Bilya komawa ya yi ya je bakin get yakira Musa. Musa yana d’aya daga cikin masu gadin gidan”.
Bilya na zuwa kusan mamayar Habib su kayi, amma dakyar suka iya k’wace Hassana daga hannun Habib. Hassana ko naganin Allah ya taimaketa ta kubuta daga hanun Habib da saurinta har tana tuntub’e wajan rugawa site d’in su.
Bilya ko suna kwace Hassana suka yi sauri suka rufe k’ofar suka bar Habib shi kad’ai”.
Hajiya Turai ko bayan fitar Bilya Kallan Baba Lami ta yi, ta ce, “Baba barka da zuwa, ya hanya, ki yi hak’uri Baba zaki ce ban ne mekiba lokacinda Habib ya koreki sai yau da buk’atata ta tashi, Baba dan Allah taimako zaki min kamar yadda ki kaimin kafin mutuwar Mahaifin Habib? “. Baba Lami Kallan Hajiya Turai ta yi, dan duk bata gane takan zancan ba ta ce, “Hajiya ina ji, wana irin tai mako zan baki? “. Shiru Hajiya Turai ta yi, tana tunanin ta inda zata fara yima Baba Lami bayani, sannan zuwa can ta ce, “Baba Habib ne baida lafiya, kuma ciwannashi kamar hauka, dan Baba Lami yanzu ko ni ban isa inje d’akin Habib ba, sai yarinya d’aya agidannan dan yauma ita akaba abin break fast d’in shi ta kai me, amma cikin ikon Allah ita Bai mata komai”. Baba Lami Kallan Hajiya Turai ta yi ta ce, “Hajiya to aiko idan haka ne akwai alamar tambaya ajikin yarinyar nan, wata yarinyar ce? “. Hajiya Turai Kallan Baba Lami ta yi ta ce, “Yarinyar da ya koreki keda Bilya akanta”. Shiru Baba Lami ta yi, Sannan ta ce, “Hajiya wai meye musabbabin ciwanne?, koko sai dai kuka wayi gari kuka ganshi ahaka?”. “Eh Tom Baba Lami, maganar ce nada mamaki da kuma d’aure kai, wato Baba Lami naje d’akin Farida sai naji tana waya da Hajiya Murja tana cewa ita yanzu abinda ke damunta yarinyar da ciwan ya riski Habib da tana wajan yanzu da ita zai rik’a yarda ba ita ba, ita abinda ke damunta kenan, tom da yake a speaker wayar ta ke, sai naji ita Hajiya Murja na cewa, Farida kuma kin tabbata kin bashi tea d’in ya sha, Farida ta bata amsa da Eh, tom shine fa ta ce wai ta binciko mata sunan yarinyar da ciwan yamu Habib agabanta”. Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ci gaba da cewa, “tom Baba Lami kinjin abinda ke faruwa, dan Allah ki taimakamin kamar yadda ki kaimin lokacinda Mahaifin Habib na da rai! “? “Karki damu Hajiya insha Allah, mu bari sai gobe inda yanzu yamma ta yi”. “Tom Allah ya kaimu goban Lafiya”. Cewar Hajiya Turai “.
B’angaran Hassana ko yanzu haka kwance ta ke tana mamakin da Oga Habib Bai yadda da kowa ya shiga inda ya ke sai ita, abinda ya k’ara d’aurema Hassana kai har Mahaifiyar shi ma taga bata isaba tashiga inda ya ke ba, nan dai Hassana ta na tunane-tunananta ta bacci ya kwasheta inda dama ba sallah zata yi ba”.
Bilya bashi ya k’ara shiga part d’in Hajiya Turai ba sai da ya yi Sallar magriba sannan. Zaune Bilya ya isketa kan sallaya ta yi ta gumi. Hajiya Turai na ganin Bilya ta ce, yauwa Bilya dama maganarka na keyi azuci yanzu haka,kamar kasan san ganinka nake yi. D’azu da nace ma kabimin bayan Farida, ya akayi? “. “Hajiya kamar yadda ki kayi tunani Sanat yughurt taje, tana zuwa suka had’u da supervisor gun, bayan sun gaisane da yake sunsan juna tom shine Farida ke tambayar supervisor sunan wadda Habib ya rik’ema hannu lokacin da lallurar ta sameta, dan acewarta ga supervisor ke kika aikota wai kina zargin Hassana, tom nan dai ta fad’a mata sunan Hassana”. Shiru Hajiya Turai ta yi Sannan ta ce, “Bilya dan Allah ka mik’ama Habib abinci kota window ne, dan ni Wallahi tsabar rud’ewa na manta kona rana ban bashi ba”.
Bilya amsar abinci ya yi ya je ya jira ma Habib shi ta window kamar yadda Hajiya Turai ta ce.
Sai dai abinda basu saniba Habib ko Kallan abinci bai yiba”.
Washe gari Hajiya Turai da Baba Lami da wuri suka yi sammakon zuwa zaria, inda Bilya ne zai kaisu.
Bayan sun fitone Hajiya Turai ta lek’a ta window tana kallan Habib zaune yake inda yasaba zama. Hajiya Turai ganin abinci jiya ta yi yadda aka kaishi yana nan ahaka. Hajiya Turai Bilya ta kira ta nunamawa ta ce, “Bilya kaga abincin jiya ko Habib bai ciba? “. “Eh Wallahi Hajiya nima haka nagani”. Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta kalli Bilya ta ce, “Bilya ku jirani amota kaida Baba Lami ina zuwa”.
Hajiya Turai site d’in worker’s d’in gidanta ta je, wata daga cikin masu yima Hajiya Turai aiki, Hajiya Turai ta aika takiramata Hassana.
Hassana ko lokacin tana kwance tana baccin safe,Binta ta shigo ta tada Hassanan, ta ce, “Hassana ki tashi Hajiyar Oga Habib na waje tana jiranki! “. Binta na fad’in haka ta juya ta tafi badare da ta tsaya taji amsar Hassana ba”.
Hassana ko tashi ta yi ta tafita tana mai addu’ar Allah yasa Hajiya Turai ba abinci zata kuma cewa ta kaima Habib ba. Hassana na wannan tunanin ta isa inda Hajiya Turai ke tsaye tana jiran fitowar Hassana”.
Hassana har k’asa ta juk’unna ta gaida Hajiya Turai tare da tambayarta ya mai jiki.
Hajiya Turai cikin sanyin murya ta ce, “Lafiya klau, Hassana dan Allah taimako zaki min na k’arshe? “. Hassana cikin girmamawa ta ce, “InajI Hajiya”. “Hassana dan Allah abinci zaki taimakamin ki kaima Habib, tun abincin jiya da kika kai mai haryanzu baici komai ba, jiya da nasa aka kaime nadare Yanzu haka abincin nacan baiciba, dan Allah Hassana ga abin break fast d’in shi can, dan Allah kije ki kai mai”. Shiru Hassana ta yi, sannan ta ce, “Tom Hajiya”. Hassana tashi ta yi tanufi site d’in Hajiya Turai d’akko break fast d’in Habib. Hajiya Turai amota ta samu su Bilya suka kama hanyar zaria”.
Hassana na tafiya zuwa b’angaran Habib tana tambayar kanta, “Wai meyasa ni Oga Habib baya dukana? , dan ayadda na lura kowama duka ya ke, kuma meye dalilin shina hanani fita da yake yi?”. Hassana shiru ta yi dan bata san mai amsa mata tambayoyinta ba. Hassana ta window ta fara lek’a Habib.
Kwance ta hango shi kan caution d’in falon, ya yi kwanciyar rubda ciki. Hassana kallan yadda Habib ya ke ta yi sai taga kamar yaji sauki, dan ayarda ta ganshi babu yadda za ai kace wai wani abu nadamun shi. Bud’e k’ofar d’akin Hassana ta yi tashiga”.
Habib na jin alamun shigowar mutum ya tashi da sauri yayo kan Hassana. Dan sai da Hassana ta ji tsoro ganin yadda ya yo kanta, amma kuma yana zuwa inda ta ke sai ya kamo hannunta ya ida shigoda ita falon”.
Hassana bayan ta zauna kallan Habib ta yi ta ce, “Oga Habib ga abin break fast d’in ka “. Hassana ta fad’i maganar tana mik’ama Habib kunun gyad’a”.
Habib amsar kukun ya yi, kafin kace me ya shanye shi tass. Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, “Oga Habib in k’arama? “. Habib Kallan Hassana kawai ya ke, amma ba bakin magana. Hassana ganin ba magana zai mata ba, yasa ta kuma k’ara mai kunun ta mik’a mai.
Habib amsar Cup d’in ya yi ya kuma d’agawa ya shanye tass, ya mik’a mata Hassana cup d’in. Hassana amsa ta yi tana mai tsananin jin tausan Habib. Mutumin da komai nashi anatse ya ke yi wai ace yau shike irin wannan shan kunun. Hassana k’ara ma Habib kunun ta yi, nanma ya d’aga kai ya shanye shi tass lokaci guda ya aje cup d’in. Bayan Habib ya gama shan kunun ne, Hassana ta tashi da niyyarta ta tafi. Amma Habib ya rik’eta ya hanata tafiya kamar jiya. Hassana cikin sanyi murya kamar ance mata Habib d’in jinta ya ke ta ce. “Oga Habib dan Allah kabarni in tafi zanyi wanki ne, innagama zan dawo “. Habib mak’ema Hassana kafad’a ya yi. Bubu irin wayan da dubarar da Hassana batai ma Habib ba dan yabarta ta tafi amma yak’i yana mai irik’e da hannunta. Dole Hassana ta yi hak’uri ta zauna tana mai addu’ar Allah yasa Hajiya Turai ta dawo da wuri”.
B’angaran su Hajiya Turai ko, sun isa zaria. Hajiya Turai ce ta kalli Baba Lami ta ce, “Baba Lami zadai ki gane gidan ko? “. Murmushi Baba Lami ta yi sannan ta ce, “zan gane mana Hajiya”.
Haka Baba Lami taita nuna ma Bilya hanya har ya kaisu gidan malam Ishu………..
Idan kin karanta ki daure ki yi Comment sister
SHERE
&
Comment
PLEASE
OGA HABIB
*︎ARUMAI ︎ WRITERS ︎SSOCIATION️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa*_
*(︎.︎.︎)*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
Facebook group:
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
Ibnul-Jawzī (rahimahulLah) yana cewa: *“Ka kiyayi roqon Allah game da wani lamari ba tare da ka rokeshi alherin dake cikin abin ba. Haƙiƙa, wani abinda zaku roqa game da rayuwar duniya na iya zama sanadin halakarku.”*
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK’R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D’AN TARKU DA HAZIK’AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD’UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K’AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK’E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K’OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN
K’ABILA CE! K’ABILA CE!! K’ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K’ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA AKE POSTING.
KI GARZAYA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D’AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K’ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT
08142904255.
Shafi na 24&25.
Haka Baba Lami tai ta nuna ma Bilya hanya har ya kaisu gidan malam Ishu.
Bilya na yin parking ya kalli Hajiya Turai ya ce, “Tom Hajiya ina jiranku”. Hajiya Turai kallan Baba Lami ta yi, ta ce, “Baba Lami muje”. Baba Lami da Hajiya Turai sallama suka yi suka shiga gidan malam Ishu. Lokacinda da suka shiga lokacin malam Ishu baya gida.
Malam Ishu fitattan malami ne mai almajirai, duk wata lallura da ke damunka in dai kaje gun shi insha Allah zaka sami sauk’i da yardar Allah. Inda malam Ishu ke sauke bak’in shi aka kai su Hajiya Turai. Su Hajiya Turai na nan zaune Malam Ishu ya dawo”.
Cikin girmama juna Hajiya Turai suka gaisa da Malam Ishu, bayan sun gama gaisawa ne. Hajiya Turai ta kalli Malam Ishu ta ce, “Malam dan Allah nazo ne katai makamin akan yarona d’aya shikenan min”. Malam Ishu kallan Hajiya Turai ya yi ya ce, “Hajiya meke damun shi? “. Hajiya Turai cikin natsuwa ta fara yima malam Ishu bayani”.
“Malam ciwanne kamar hauka-hauka, inda yanzu haka bacikin hayyacin shi ya ke komai ba”.
Malam Ishu da katar da Hajiya Turai ya yi tahanyar ce mata, “Hajiya ko ke baya ganewa? “. Hajiya Turai cikin sanyin murya ta ce, “Malam yanzu haka ko shiga d’akin shi nayi sai dai akwaceni hannun shi, bawai duka ya ke ba, amma idan yarik’e mutum yana shan wuya gun shi sosai, dan wujijjiga mutum ya ke, sosai”.
Shiru Malam Ishu ya yi sannan ya ce, “Babu damuwa insha Allahu zai warke, da akwai rubutun da zamu rik’a mai duk sati insha Allahu kodama iskace ta shafe zata kauce, idan ma sihirine zai karye, ke kodama ace da aljani aka had’ashi ya mai da shi haka insha Allah ayar Allah zata karya duk wani abinda ke jikinshi”.
Malam Ishu kallan Hajiya Turai ya yi, ya ce, “Hajiya ina zuwa”.
Malam Ishu fita yayi daga d’akin, ya kai kamar minti sha biyar da fita sai gashi ya dawo da gallon k’anana guda biyu a hannun shi. Malam Ishu mik’ama Hajiya Turai ya yi, ya ce, “Hajiya ga wannan arik’a bashi wannan na farar jarkar sha biyun rana d’aya da kuma sha biyun dare, wannan kuma safe , rana, dare, insha Allah kome ke damunsa Allah zai mai maganin shi, duk sati zaku rik’a zuwa kuna amsar mai, yanzu idan ya shanye wannan sai muga yadda jikin nashi zai yi, sannan insha Allah za’ai mai saukar alk’ur’ani mai girma”.
Godiya sosai Hajiya Turai tai ma Malam Ishu, sannan ta bashi kud’i masu yawa sosai, sannan sukai mai sallama suka tafi”.
Su Hajiya Turai suna a mota suna tafiya, Hajiya Turai ta kalli Baba Lami, ta ce, “Baba Lami nikam ina tunanin yadda Habib zai sha maganin nan, Kinga dai yadda akeyi da shi, sannan wa zai rik’a tashi yana ba Habib magani sha biyun dare?, ni kuma Baba Lami kinga yadda ya ke min, Wallahi duk hankalinama ya tashi narasa yadda zanyi gaba d’aya “. Hajiya Turai ta idasa maganar tana share hawayan da ke zibo mata”.
Shiru Baba Lami tayi, dan itama tun d’azu tunanin da take yi kenan. Ahaka dai suka isa gida batare da Baba Lami ta ce komai ba”.
Bayan Bilya ya yi parking sun fiffita a motar ne, Hajiya Turai ta kalli Bilya ta ce, “Na bani Bilya namanta tun d’azu na tura Hassana kema Habib abin break fast, Wallahi ina zuci-zucin ince ma mubari ya gama ku fitar da Hassana sannan mu tafi, amma Wallahi na manta sham, da nazo na shiga mota kawai muka tafi, dan Allah muje mugani ko yabarta ta fita”.
Wajan window Habib Hajiya Turai ta tsaya ta lek’a, zaune ta iske Hassana kamar jiya, Habib kuma na rik’e da hannunta. Hajiya Turai cikin damuwa ta kalli Bilya ta ce, “Bilya ka gani ko, ashe har yanzu yarinyar nan na nan yak’i barinta ta fita! “. “Tom Hajiya ni kaina Wallahi abun shiru kawai nake yi, amma ita kanta Hassana yanzu ta fara ban tausai, dan ita ke jinyar Oga Habib kusan”.
Shiru Hajiya Turai ta yi, Sannan ta ce, “Bilya kira Musa dan Allah ku fito da ita, nasan k’ila ko abinci basu ciba su duka, inda babu wanda zai yi hausar kai musu”.
Bilya kiran Musa ya yi shuka shiga d’akin Habib don fito da Hassana. Habib ko na ganin su ya tashi da saurinsa ya yo kansu.
Bilya da Musa rik’e Habib suke ita kuma Hassana ta tashi ta fita da saurinta, sannan suma suka saki Habib d’in suka gudu”.
Hassana sauran kad’an tabige Hajiya Turai, dan bata san da ita ba, saboda fitowar da tayi da gudu. Hajiya Turai kamo hannun Hassana ta yi, ta ce, “Sannu ko Hassana Allah ya yi miki albarka”. Da Ameen Hassana ta amsa. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi ta ce, “Bakici abincin rana ba ko? “. kai Hassana ta d’agama Hajiya Turai. Hajiya Turai kallanta ta yi, ta ce, “Hassana ya sha kunun da kika kaime? “. “Eh Hajiya yasha sosai dan duka ya shanye shima”. Hajiya Turai hannun Hassana ta kama tace, “Sannu da k’okari, muje falona kici abinci kema”.
Hajiya Turai tana rik’e da hannun Hassana har suka isa falon ta. Hajiya Turai d’aya daga cikin masu aikinta ta sa ta had’ama Hassana abinci, sannan tasa suka kai mata kan derning space . Hassana ko daya ke yunwa ta ke ji dan ko karyawa bata yi ba Hajiya Turai tasa ta kaima Habib abin k’arinshi. Sosai Hassana ta ci abincinta”.
Hajiya Turai ko tunaninta taya zata kuma rok’on Hassana ta kaima Habib shima.Hajiya Turai so take ta rok’i Hassana amma sai ta kasa dan tana tsoran kar Hassana tai mata kallan mai son kanta da yawa. Haka Hassana ta gama cin abincinta ta tashi ta yima Hajiya Turai godiya ta tafi. Hajiya Turai nason yima Hassana magana ta rok’eta ta kaima Habib abinci, amma ta kasa, haka nan ta yi hak’uri badan taso ba tana gani Hassana ta tafi”.
Hajiya Turai bayan ta yi Sallah ne, ta aika aka kira mata Baba Lami. Bayan Baba Lami ta zo ne, Hajiya Turai kallanta ta yi tace, “Baba Lami nace taya kike gani Habib zai sha maganin nan? “. Shiru Baba Lami ta yi, sannan ta ce, “Hajiya ni gani nake kamar yadda kike sa Bilya da Musa su kwace Hassana daga hannun Oga Habib, haka zaki sasu su d’ura mai maganin nan”. “Tom Baba Lami idan hakan ta yuwu na daran fa? “. Shiru Baba Lami ta yi, dan itama shi tafi tunani, sannan zuwa can ta ce, “Hajiya ni gani nake kima Bilya da Musa magana su rik’a tsayawa wajan Habib har lokacin shan maganin, alabashi idan sun bashi magani sai su koma inda suke kwanciya su kwanta, alabashi sai ki biyasu, bare kuma nasan daga Bilya har Musa sunada kirkin yi miki haka”. Shiru Hajiya Turai ta yi sannan ta ce, “Baba Lami kina ganin ba damuwa zasu yi ko? “. “Sosai ma kuwa, Hajiya ai Bilya da Musa dukansu ‘yan gidan Oga Habib ne, ina da tabbaci zasu yi”.
Hajiya Turai kallan Baba Lami ta yi, ta ce, “Baba kiramin Bilya sai muyi magana da shi, inji ta bakinshi”.
Baba Lami fita tayi sai gata da Bilya sun dawa. Baba Lami kallan Hajiya Turai ta yi ta ce, “Hajiya ga Bilyan nan naki rashi”., Hajiya Turai cikin sanyin murya ta ce, “Bilya dan Allah tai mako zakai min?, magani akaba Habib ya rik’asha sha biyun rana da na dare , shine dan Allah nake nai man alfarmarka kai da Musa kurik’a bashi, zan biyaku dan Allah Bilya ku yi min wannan tai makon”. Hajiya Turai ta idasa maganar cikin rok’o”.
Shiru Bilya ya yi sannan ya ce, “Hajiya Oga Habib matsayin shi agunmu ya wuce haka zamu iyamai abinda yafi hakama, amma matsalar guda d’aya ce, na farko dai kinsan baya yarda da kowa yashiga inda yake, na biyu kuma Hajiya kina gani jiya da aka kaima abinci yadda aka kaishi haka aka d’akko shi, amma idan kina da wata shawarar sai mubi”. Shiru Hajiya Turai ta yi bata ce komai ba”.
Baba Lami ce ta ce, “Bilya ni dama shawarata sai inga d’ura mai za kuyi, amma dama indai ta lallimice ai ba zai shaba”.
Bilya gudin kar Hajiya Turai taga kamar yak’ine yasa ya ce, “Shikenan ,Yaune za’afara bashi magani? “. Baba Lami ce ta amsa mai ta hanyar cewa”Eh”.
Hajiya Turai rubutun ta d’akko ta mik’ama Bilya ta ce, “Bilya wannan shine zai sha yanzu, wannan kuma shine na sha biyun daran,wannan kuma sai gobe zai fara shashi, dan Allah sai kai ma Musa bayani yanzu sai ku bashi”. Bilya amsar rubutun ya yi batare da yace komai ba yafita”.
Bayan fitar Bilya ne,Hajiya Turai ta kalli Baba Lami ta ce, “Baba ni ko duk yau banga Farida ba? “. “Nima kam yanzu nagama zancan azuciyarta”. Cewar Baba Lami”.
Farida ko tun safe tabar gidan, tana ganin fitar su Hajiya Turai itama ta fita, dama yaune sukai da Mahaifiyarta Hajiya Murja zata je. Bayan Farida ta isa gida ne, Hqjiya Murja kallanta tayi tace, “Farida sanin kankine bamu da wani wada tattan lokaci amma shine kikak’i zuwa da wuri, tun shekaran jiya da naima Malam magana aiki ya lallace ya ce kizo da wuri dan asan ta inda za ab’ulloma lamarin amma kikak’i sai yau! “. Farida cikin shagwab’a kamar zata yi kuka ta ce, “Mommy kefa kika ce min bakya so Hajiyar Oga Habib tasan zanzo, tom yaune suka tai zaria naimanma Oga Habib magani, shine fa suna tafiya nasamu nafito”. Shiru Hajiya Murja ta yi, sannan ta ce, “Shikenan tashi muje gidan malam”. Farida tashi ta yi suka tafi a motar Hajiya Murja”.
Farida da Mahaifiyarta zaune agaban Malam mai biyan buk’ata dole. Hajiya Murja kallan shi ta yi, ta ce, “Malam kamar yadda nafad’ama aiki dai kuskure aka samu bai yiba”. Bak’in katon da Hajiya Murja ta kira da Malam, cikin fad’a-fad’a ya ce, “Hajiya kunzo nan keda yarinyarki akan in muku aiki asama Yaron nan son yarinyarki nace muku ba zai yuwuba, saboda mu munayin abinda zai yuwune, sannan yaron nada wani murd’add’an hali, aikin zai bamu wahala, Nina baku shawarar juya gwagwalwar yaron nan, sannan asa mai k’inyarda da kowa sai ‘yarki kad’ai, sai kuyi amfani da damar yarda da ‘yarki da yake yi kuhad’asu aure, bayan aure in warware aikin da nai me, sannan kafin in baku maganinnan wana irin jan kunnene ban muku ba, na dad’e Ina nana ta muku karku sake yarinyarki tayi nesa dashi, amma taya kuka yi sakaci haka ta faru? “. Farida cikin rawar murya ta ce, “Wallahi yaron shine yajamin, yanzu dan Allah asake min wani abun wanda zaiwarware wancan konawane zan bada”. “Wata irin dariya ya yi sannan ya ce, “Ya sunan yarinyar da yake yadda da ita? “. Farida da Hajiya Murja had’a baki sukai wajan cewa, “Hassana”.
Wani ‘yan Zane-zane ya yi sannan ya ce, ” Abin bawani mai wuya bane, amma dole sai yaron nan ya kusanci yarinyar da yake yarda da ita yanzu haka, sannan koda wannan makarin sai karye, yanzu akwai abinda zan baki ki tabbatar kinba yarinyar taci shima yaron yaci, idan har ya kusanci yarinyar shikenan, zaki zama dake kad’ai yake yarda Mahaifiyarshi da kanta zata had’a auranki da shi”.
Hajiya Murja kallan bak’in k’aton banza ta yi, ta ce, “Ba komai ka bata abinda zata basu d’in, sannan ita yarinyar in sonsamune gudin matsala muna so arabata da gidan “. Wata mahaukaciyar dariya yayi ya ce, “Shikenan damuwarku da zo k’arshe, sai ni Malm mai biyan buk’ata dole, da kazo gurina buk’atarka bata biyaba, gara in bar aiki”. Haka yagama yi ma kanshi kirari sannan ya d’auki wani bak’in abu kamar d’inya ya ce, “Wannan abun da kike gani, daga kin je gida yanzu zaki jik’ashi aruwa ya kwana tom ruwanne zaki ba yarinyar ta sha shima yaron yasha”. Wata muguwar dariya ya yi sannan ya ce, “Aikinki yagama ci yarinya”.
Godiya sosai Hajiya Murja tai mai sannan takama hannun Farida suka bar gun suka je inda su kai parking d’in motarsu suka shiga suka kama hanyar gida. Suna cikin tafiya Farida ta kalli Mahaifiyarta ta ce, “Mommy nifa gaskiya ban yarda da abinda Malamin nan yace ba, gaskiya ni bazan bari ya kusan ci k’azamar yarinyar nan ba, kuma ko ba ma haka ba, ni dai ina kishin haka”. Kallan baki da hankali Hajiya Murja tai ma Farida, sannan ta ce, “yanzu ya kike so ayi, kina jidai abinda ya ce hakane kad’ai makarin abin, amma idan kina da wata shawarar tom? “. Eh ina da ita Mommy……….
Idan kin karanta daure kiyi Comment sister
SHERE
&
comment please
OGA HABIB
*︎ARUMAI ︎ WRITERS ︎SSOCIATION️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa*_
*(︎.︎.︎)*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
Facebook group :
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
_ Baya halatta likita ya ke6anta da mace mara lafiya (ya zanto daga shi sai ita) don duba lafiyarta, dole ya kamata a samu mijinta a wurin ko wani muharraminta a lokacin da ake dubata._
فتاوى اللجنة الدائمة 422/24
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK’R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D’AN TARKU DA HAZIK’AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD’UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K’AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK’E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K’OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN
K’ABILA CE! K’ABILA CE!! K’ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K’ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA AKE POSTING.
KI GARZAYA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D’AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K’ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT
08142904255.