Hausa Novels

Prince Sapwan Hausa Novel

Prince Sapwan Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Prince Sapwan Hausa Novel

Cike Makil International Airport na garin Katsina yake ,dan ko masaka tsinke babu.

 

 

Dogarai ne birjik da alama dai ko wani Ɗan sarki ne zaiyi tafiya sukazo rakiya ko kuma sukazo taryarsa.

 

 

5minutes da shigata airport din naji dirar mikiyar jirgi , ganin duk Dogaran sunyi gurin jirgin ne yasa muma muka bi bayansu dan baza’a barmu a baya ba.

 

 

kusan 1 hour da dirar jirgin kafin wani haɗaɗe kuma kyakyawan Saurayi kamar balarabe ya fito cikin tafiyar izza da ƙasaita, cikin shigarshi ta Yaran Sarakai masu ji da kuɗi da ilimi haɗi da saurauta, dan kallo daya zakayi masa kasan shi jinin Sarautane gaba da baya.

 

 

dan ko yanayin tafiyar da yake cikin kasaita da nuna isa, cikin yanga ya fara tafiya, yana lumshe ido alamar Iskar gurin tana yi mishi daɗin shaƙa.

 

 

Dogarai ne suka fara taka masa suna mai kwasan gaisuwa, ko kallo basu ishe shi ba da alama dai akwai shi da jin kai, dan ko alamar suna gurin baya nunawa.

 

 

tafiya kaɗan ya ƙarasa gurin wasu lumtsuma-lumtsuman motoci na alfarma, bayan motar na kalla, inda anan ne naga an rubuta Yarima Sapwan 1, wani Dogari ne yazo da sauri ya bude mishi motar shiga ya yi.

 

 

sauran ma duk shi-shiga suka yi, motar shi ce a tsakiya sai huɗu gaba huɗu baya sai tashi ta tara wadda take tsakiya wanda duk an rubuta musu Yarima 1, wato Yarima Sapwan wanda mudai a iya yanzu mun gane cewa sunan shi kennan Yarima Sapwan.

 

 

 

 

****************

 

 

 

“Fulani yau fa wannan Yaron zai dawo, da Alama dai duk abinda muka shirya ya lallace”, ya fada yana zama kan kushin din dakin, fuskarshi da tsananin ɓacin rai.

 

 

Karanta Littafin Ni da Yaya Arman

“menene na wannan ɓacin ran, ai ka kwantar da hankalinka a wannan dawowar zan halakar dashi a doron ƙasa domin , babu wanda zai gaji Sarautar masarautar Katsina sai Yarima Faiq”, wata mata ta fada , wadda take cikin shiga ta Alfarma ta matan Sarki.

 

 

 

Wani mugun kallo ya jefeta dashi, kafin ya saki wani munafiƙin murmushi da bazaka iya fassara ko na menene, ba.

 

 

 

 

******************

 

Prince Safwan Hausa Novels

Abincicika ne kala-kala shirye akan wani ƙayattacen dinning na Alfarma, sosai part din ya haɗu da za’a iya kiranshi da Aljannar duniya dan tsabar haɗuwarshi, ko ina ka duba cikin part din kayayyakin Sarauta ne na Alfarma, wata hamshaƙiyar matace tsakiyar parlourn cikin shiga ta kece raini .

 

 

 

**************

 

 

wani hamshakin gidan sarauta na cikin garin Katsina naga motocin Yarima Sap 1, sun shiga, sosai gidan sarautar ya haɗu da ko ina idan ka duba bayine da Dogarai birjik, ta ko ina kowa yana harkokin gabansa, direct motocin gaban fada suka tsaya sai da ya shari kusan 10 minutes kafin ya fito daga motar, bakin kofar fadan ya nufa, wani Dogari cikin masu tsaron kofar fada , ya yi saurin shiga fada dan sanar da Mai martaba isowar Yarima , sauran dogaran ne suka zube kasa suna kwasar gaisuwa.

 

 

 

Mai martaba ne, ya bashi Umarnin shigowa hakan yasa da sauri dogarin ya yi waje, domin isar da sakon Mai martaba.

 

 

 

ko jiran fadar sakon Mai martabar bai yiba ya shige ciki, yana yamutsa fuska.

 

 

tuni Mai martaba ya Sallami kowa dan zai gana da gudan jininshi, ko da ya shiga fadar kwalam babu kowa sai Mai martaba dake zauna kan kujerar mulki ta alfarma, wadda kana ganin yarda take walali kasan Akwai zinari a jikinta.

 

sosai kayan cikin fadar suka tafi dani domin komai na ciki na gargajiya ne, kusa da Mai martaba ya matsa .

 

 

da murmushi Abbun nashi ya kamo hannushi yana rungume shi , ɗuƙar da kanshi kasa ya yi, kafin yace.

 

 

“Sannu Abbuna An yini lafiya, na sameku lafiya?” ya fada yana yamutsa fuska kamar baya sonyi magana.

 

 

 

girgiza kanshi ya yi, kafin ya Ansa masa da “Alhamdulillah ya karatun?” jijjiga kai ya yi alamar Lafiya qlau.

 

 

 

murmushi ya yi, dan yasan wannan halin nashi na body language bazai iya barin shiba, sosai ya ringa janshi da fira amma amsar shi daga “uhmm, sai umuhmm”, gashi shikuma na fiskanci yana bala’in son suyi fira.

 

 

 

 

gajiya ya yi, da irin amsar da yake bashi hakan yasa, ya ja hannunshi, ta cikin part din ya bude wata kofa, wani kayattacen parlour kofar ta sadasu dashi, shi kuwa Prince Sap, bin Mahaifin nashi kawai yakeyi a baya, dan gaba daya jikinshi ya yi wani irin mugun week.

 

 

 

 

 

*******************

 

 

 

“ba Ɗan ba har Uwar so nakeyi na kaudasu daga cikin duniyar na, domin a halin yanzu su kaɗai ne ciwon kaina, dan ni ba Sarautar ce a gaba na ba, Karfin fada aji shi nakeso” wata mata ta fada fuska a murtuƙe babu alamar rahama.

 

 

 

“to yanzu Kilishi ya za’ayi kinga dai yanzu abubuwa sunason dagulewa”, ya fada a ruɗe.

 

 

 

wani murmushi ta saki wanda direct za’a iya kiranshi da na mugunta.

 

 

 

wata iriyar juyowa tayi, kafin tace “Na tsane ta, bana kaunar duk wani abu wanda ya fito daga jikin ta kuma ya zama dole daga ita har munafukin d’an na ta su ziyarce lahira nan kusa bada jimawa ba, ta fada ba tareda ta ji shakkar komai ba,

 

 

 

“Toh yanzu miye abun yi?”, ya fada yana zazzare idanu.

 

 

 

“karka damu Waziri, ka barmin komai a hannuna kaidai tashi ka tafi”, Kilishi ta fada tana zama ragwajaɓ kan kujera.

 

 

 

jiki a sanyaye, ya tashi ya fita , bin bayanshi tayi da murmushi kafin ta tashi ta fara Safa da Marwa .

 

 

 

*****************

 

 

 

parlourn ne babba wanda da gani kasan na Sarki ne, zaunar dashi ya yi, kafin ya zauna kusa dashi, hamshaƙiyar matar ɗazun ce ta shigo ɗakin fuskarta ɗauke da murmushi mai nuna tsaninanin farin cikin da take ciki.

 

 

 

 

murmushi shima naga ya saki, sosai Mai martaba ya riƙe baki yana cewa,”watakan Uwarka kawai kakeyiwa dariya ni bandani”, ya fada yana dan dukan kafadarshi.

 

 

 

Dariya Gimbiya Khadija tayi tana zama kusa da su, tana zama ya kwantar da kanshi kan kafaɗarta, haɗa ido suka yi da Mai martaba murnushi suka saki a tare kafin su daura hannayensu a kanshi su haɗa baki garin cewa ,”Allah ya yi, maka Albarka”, lumshe idanunshi ya yi, yajin sanyi cikin ranshi.

 

 

Kuyagin gidan ne, suka fara shshigowa da kololin Abinci iri-iri daga part daban-daban wai a bawa Prince ,shi kuwa da yasan Halin tsarin masarautar da yawan magautansa a cikin gidan shi yasa tunda ya taso baya cin abincin kowa sai na Mahaifiyar da kuma Nene Mahaifiyar Abbunshi domin su kada ya yarda dasu a Masarautar, domin ta ko ina hari ake kawo masa, shiyasa ko yana son ci Maamah dinshi ke hanashi domin ita tasan ko mai ke faruwa a cikin Masarautar nason ganin bayan Prince Sap.

 

 

 

************

 

 

“ke! Sapna dan Ubanki zoki karasamin wannan wanke-wanke dan ba ciwo ba ko mutuwa kike kina dawowa Wallahi saikin karasashi , dan duk cikin Gidan nan babu Baiwan wannan sallamamiyar Uwar taki mai bakar kafa , gayyar masu bakin jini, da shegen naci, tunda kika zo gidan nan, gaba daya arzikinmu ya rushe, komi ya lallace mana, Yoh inama dalilin Auren gayyar tsiya irinku”,ta fada tana daga tsuman da suka daura a kofar ɗakinsu a matsayin labule.

 

 

kwance take kasa tana ta muɗuɗuƙa da bulkayi kamar tarwaɗa sai wata mata fara tar dake kusa da ita tana yi mata sannu.

 

“Haba Aunty Tabawa kiyi hakuri ni bari in tashi inyi miki”, matar ta fada tana yinkurin tashi.

 

da sauri wata ƴar Yarinya tace “, Ummie barshi na tashi na karasa ai tama kusa gamawa saura kaɗan”, ta fada tana zama kan kujerar da aka ijiye a gurin.

 

da sauri Gwaggotabawa Tarawa finciki hannu Yarinyar tana cewa,”zan mugun saɓa miki Abasiyya , ke nasa?, ita nasa kuma ko zata mutu tana cikin yinshi sai ta yishi”, ta fada tana tura Abasiyya ɗakinta.

 

 

Ummie ce ta tashi zata fito waje ta cigaba da wanke-waken riƙe hannunta akayi da mamaki ta juyo dan ganin waye, ban sadda bakinmu ni da Oummu Juju ya hade gurin furta Fatabaraqallahu Ahssanunqaliqin, Yarinya ce da baza ta wuce 15 to 16 years ba tsaye, fara mai dara-daran idanu wanda kallo daya zaka yimusu kasan cewa, fararene tar saidai dan sirkin ja dake cikinsu wadda da ka gani kasan Wahalar ciwone ya maidasu haka, bakinta dan karami wanda yake dauke da siraran lips pink colour sai sheƙi suke, ga siririn hancinta wanda ya yi dai-dai da face nata, jikinta dan dai-dai ita bamai ƙibaba ita ba siririya ba dai-dai misali dai, sai diri mai daukar hankali, komai dai yaji a jikinta Masha Allah.

 

“Ummie barshi bari na cigaba nama kusa gamawa fah”, ta fada tana sakarwa mahaifiyar murmushi wanda da ka ganshi zakasan na karfin haline.

 

 

“zaki iya kuwa?, ki bari na karasa”, ta fada da a alamar tausayawa akan fuskarta.

 

“zan iya mana Ummie kalli na samu sauki fa”, ta fada tana……….

 

*muje zuwa…….*

2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!