Hausa Novels

Qaddarar Joda Hausa Novel Complete

Qaddarar Joda Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Kaduna state

Gudu motar tasu take bisa wani lalataccen hanya, titin wajen duk ya lallace dole duk gudun mutum idan yazo wani wajen sai ya rage gudun saboda rashin kyan hanyar,

 

Dan Allah baba ka rage gudun nan ji nake kamar zan haihu a hanyar nan, wata matashiyar mace ta fadi haka wacce a qalla bazata haura shekara talatin ba amma idan ba anfada maka ba baza ka kawo ta kai shekarun nan ba saboda hutu da kuma tsarin halittanta, farace mai matsakaicin jiki, tanada round face mai dauke da madaidaitan ido farare, idan ka kalli giranta zaka ga laya layan gashi wanda ke nuna alamun zatayi tsawon gashi, hancinta dogo masha Allah tareda da bakinta dai dai kiss komai dai masha Allah

 

 

Hanyar nan da ake dauka inza a je sabon birni ta riga chikum naga ya dauka, tareda ce mata uwar dakina kiyi haquri ki daure dole muyi sauri domin mutanen nan zasu iya cimmana a kowani lokaci kuma kinsan sakamakon cin mana bamai kyau bane.

 

 

 

Hawaye kawai ke zuba a idon wannan baiwar Allah, duk wanda ya ganta yasan a firgice take ga tsohon ciki, tunani kawai ta fada, shin yanzun mijinah a wani hali yake, shin ya mutu ko ko basu sami galaba a kanshi ba? Innalillahi wa inna ilaihirrajun kawai take maimaitawa

 

 

 

Ji tayi drivern yana ta salati yayin da yake qoqarin yaga ya tsayar da motar amma dayake mutum baya kaucewa qaddaranshi sai da motar ta daki wani qaton dutse da ke hanyar sannan ta tsaya, gaba daya motar hayaqi take gaban motar kuma yayi wani mugun lallacewa

 

 

 

Driver din ne ya samu ya fito daga motar cikin mawuyacin hali, sannan ya bude bayan inda wannan matar mai ciki take, a sume ya ganta, goshinta a fashe sannan duk ta qurqurje a hannunta, goran ruwan dake kusa da ita ya dauko ya sheqa mata sai tayi dogon ajiyan zuciya

 

 

Juyawa yayi yana duba hanya ko zai sami wadanda zasu taimaka mai amma baiga kowaba can yana dube dube sai ya hango motar mutanen nan dake binsu da sauri ya koma yace uwar dakina ki daure mu gudu daganan ga motar su nan ya qaraso ko cikin dajin nan ne mu shiga Allah zai dafa mana

 

Ai bata jira ya qarasa maganarshiba ta nema ciwon da takeji ta rasa sai gata ta duro akan sawayenta, daji kawai suka yanka suna gudu yayin da mutanen nan suka dafa masu suma da gudu tareda mugayen makamai a hannunsu,

 

 

Gudu kowa yasan idan ga macene ba kamar na namijiba balle ita da takejin alamomin naquda, gudun dai basuyi nisaba sai qaran harbi taji TASSSS take a gurin driver dinta ya fadi babu rai, innalillahi wa inna ilaihirrajium baba haruna dan Allah ka tashi take cewa amma shiru babu amsa, dago kai tayi da niyyan ihu ta hango saura kadan su cimmata, hakanan ta tashi ta barshi a gurin tana zubar da hawayen tausayin baba haruna da baisan komai ba amma qaddaranta yaja mashi rayuwarshi tana cikin maganar zucin nan ne sai taji ta fada wani gangare

 

Mulmulowo kawai take har ta isa ga wani dutse da ta bugi cikinta dashi nan take jini ya tsinke mata ga cikin yana wani irin hautsinewa ihu ta kwada sannan ta fadi sume a wajen.

 

 

 

 

 

 

Littafin nan na kudine duk wanda yakeso yayimin magana ta wannan numbern 09023019554

 

 

 

Pls Sister share it

Leave a Comment

error: Content is protected !!