Qisas Hausa Novel Complete
Tag: QISAS
~_HAYAT***_~
_*@Meerahgee*
_Free page_
*1*
D’akin tarone kamar yadda idanun mai kallo zai gani wanda yake d’auke da rundunar jami’an tsaron ‘yan sandar jihar Fikar da ke wannan qasa.
Ga dukkan alamu wannan taro nasu kan abu mai matuqar muhimmancine ga jiharsu da ma sauran al’ummar qasarsu, musamman yadda suka bada hankali matuqa kan jawabin da sepeta janar na jahar ke yi musu ka hatsabibin d’an ta’addan da ya buwayi jahar gabad’ayanta kuma yake shirin mamayar wasu sassan jahohin qasar.
“Yallab’ai a tunanina mu duba yuwuwar neman sulhu da _*Jaeez*_ shi ne kawai mafita ga jinin al’ummarmu da yake kwaranya….”
cikin dakatarwa sepeta yace “hakan ba zai yuwu ba, ba za mu zubar da kimarmu gurin saurarensa ba, akan me za mu zubar da kimarmu ta jamian tsaro mu nemo sulhu da wani d’an ta’adda?, hakan mafarki ne, akan kawo qarshen Jaeez mun nemi taimakon duk hukumomin da ya dace kuma ba da jimawa ba zai gurfana a kan gwiwarsa cikin qasqanci, a ruwa yake ko a iska, akan qasa ko akan tsauni rundunar wannan jaha ta Fakar za ta kawo qarshen Jaeez, na yi wannan alqawarin wa qasata!”
fiye da yadda ya saba magana cikin alfahari yayi a yau d’in cike da tabbatarwa.
*** *** ***
Cike da zafin nama da kuzarinta kamar kullum *Maidoki* ta iso gurin aikinta akan farar jincheng d’inta, maidoki ma’aikaciyar jaridace da take aiki da gidan Radion Fakar freedom, yayin da takasance mai rubutu da fashin baqi a shashin jaridar Fakar Today, yarinyace matashiya wacce Allah yayi wa nasibi da abubuwa da dama a rayuwa, ciki akwai kyakkyawar nasaba, qwarjini da kyawawan d’abiu.
Tayi fice a cikin jaharta har ma da maqwabtansu kasancewarta ta musamman kamar yadda komanta yake na musamman, fahimtar yadda take sai an nitsa cikin wannan labari, amma dai a taqaice Maidoki shiryayyiyar shirice daga wanda ya shiryata.
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
kamar kullum bayan gaishe-gashe tsakaninta da abokan aikinta cikin barkwanci, kai tsaye d’akin gabatar da shirye-shirye ta shiga domin gabatar da shirin da take da shi a yau d’in, tsawon minti talatin ya d’auketa kammala shirin ta fito daga kewayayyen glass da take ciki tana gyara bluetooth dake maqale a kunnenta fuskarta d’auke da murmushi ta d’aga wa wanda ke kula da na’ura babbar yatsarta ta bud’e qofa ta fice tana ce
“Ok, gani nan zuwa”
mashin d’inta ta hau da gaggawa ta fice daga gidan Radion ta d’au hanyar gidan Jaridar Fakar Today.
tsaye take a gaban Table d’in manaja yayin da idanunsa ke kan jaridar gabansa, a hankali ya zare glass ya ajiye tare da kallonta sannan ya nuna mata kujera ba tare da yayi magana ba.
tsawon minti biyu bayan zamanta bai ce komai ba kamar yadda ita ma ba ta ce da shi komai ba, can dai ya tura mata jaridar yana mai cewa
“a kullum rubutunki rubutune na fikira da jan hankali wanda yake d’aga darajar wannan gidan jaridar ta fakar today, amma a yau layi d’aya na abinda kika rubuta ya qara min yawan furfura, daga fitar jaridunnan zuwa yanzu da bai kai minti hamsin ba ko sama da haka, na amsa kiraye2n da suke daidai da qarar Ak47 a kan zuciyata……”
Cakwakiyar zance kenan, wai me kika rubutane maidoki?
“idan ba matsala za mu iya zuwa inda ka nufa yallabai, a dai abinda na rubuta bana buqatar sake dubawa, yana haddace a kaina, cewa nayi Jaeez makusancinmune, sauqi gurin nema, sauqi gurin samu, neman Jaeez ya fi sauqi fiye da neman ruwa a unguwannin qwaryar jaharmu, cikin awanni ashirin da hud’u gwamnati za ta iya damqe Jaeez domin ta fi kowa sanin inda yake, kamar nima, simple abinda na ce kenan….”
har da murmushinta.
“stupid!, wai kike iqrarin sauqin abinda kika fad’a….!!!? ya daki table da hanunsa cikin b’acin rai yace
“da wannan maganar da harbe kanki kika yi shi ya fi miki sauqi, toh amma, shi kenan, tunda sauqi gareshi ga ki ga hukuma, daman a fusace suke, da guguwar fushinsu za su bi ta kanki su dirkakeki ko ki kai su inda Jaeez yake tunda har ke ‘yar me rawar kai kin ce kin san inda yake !!!”
“abu mai sauqi yallabai, a minti hud’u zan fad’i inda za a samu Jaeez yayin da zan bar musu sauran awanni ashirin da uku da minti hamsin da shida gurin had’uwa da shi”
kallon kallo suka yi da shi yayin da takaicinta yake tumbatsa a ransa kamar ya rufeta da duka, bai tab’a tunanin yarinyar tana shaye shaye ba sai yau da ta jefa rayuwarsa a kwale kwalen azaba da shiga uku.
_*share share share*_!!!
Meerarku ce! Mrs A A
[23/07, 2:31 am] +234 803 800 7509: _*QISAS*_🥷
~_HAYAT***_~
_*@Meerahgee*_ 🦜
*2*
Juyawa tayi cike da qwarin gwiwa ta bar office d’in tana rera waqar qasa wato O! God of creation…..
Ya bi bayanta da kallo, da qyar ya tattaro yawu ya had’iye sannan ya zauna jagwab akan kujera ya dafe kansa da hanu biyu.
Adaidai lokacin da ta hau mashin d’inta motocin ‘yan sanda suka qaraso gidan jaridar, da kallo ta bi motar babu ko tsoro a fuskarta sai ma murmushi da ta yi ta sauke majinginar mashin d’in ta mai da hankalinta kan Inspector Basheer da yake nufota tare da yaransa.
“Maidoki, shararriyar ‘yar jaridar da haskenta ke haske nahiyarmu, kina da matuqar qwazo, jinjina gareki”
Tayi wani miskilin murmushin da ya bayyanar da zunzurutun kyaunta tace
“Yallab’ai, idan wad’annan baitocin yabone, to rubuce ya kamata in gansu a kan kwalin girmamawa”
Shi ma murmushin yayi sannan ya d’ora da cewa “matuqar, matuqar fasahar zance, maidoki” yana kad’a yatsunsa yayi maganar sannan ya d’aga kafad’a ya a cigaba da cewa
“Hukumarmu tana nemanki a ofishi domin amsa wasu tambayoyi, idan ba matsala za mu iya tafiya?”
Tayi murmushin ko a jikina sannan ta d’age kafad’u kamar yadda yayi tace
“Why not?, zan biku a baya”
“Umhm!”
Yace yana mata wani irin kallo sannan ya juya ya cigaba da tafiya tare da d’ora glass akan idanunsa, ta tayar da mashin d’inta ta bi bayansu har zuwa ga office d’insu kamar yadda suka buqata.
Kewayeta akayi da jami’ai masu matuqar girgiza gizon mai kallonsu, saboda qwarewarsu kan aiki da titsiye, ciki har da Inspector Basheer, yayin da idanunsu ke zube akanta cikin salon firgitarwa, amma baiwa irinta maidoki hakan bai sa ta rikicewa ba, sai ma zuba musu na mujiya da tayi tana shanye fargabarta, a wannan hali Commissioner ya shigo ya samesu ya nufi inda aka tanada dominsa ya zauna, gaba d’aya suka miqe suka sara masa, gwanar tana zaune tana cigaba da kallonsu, ya musu umurni su zauna sannan ya saita abin magana daidai bakinsa yana kallonta cikin dakiya yace
“Game da abinda kika rubuta a jaridar Fikar Today, me zaki ce?”
Kafinta motsa har Basheer ya cafe da cewa “Waye Ja’eez?”
Zak yace
“A ina zamu sameshi?”
Wani sefeta jerry yace “Ta yaya kika gano Jaeez sab’anin jami’an tsaro”?
“Wani tabbaci kike da shi cikin sauqi da saurin samoshi?”
Cewar Sifeta Dauda.
Commissioner ya buga bakin mic na gabansa, suka dagata da maganar ya sake kafeta da idanu yace
“Waye Jaeez?”
Yadda ya kafeta da idanu ita ma ta kafeshi da nata ta dafe goshi da yatsu biyu sannan ta yamutsa fuska tace
“Wacce tambayar zan fara amsawa yallab’ai…?”
“Fara da kowacce..!”
Ya yi maganar a kausashe.
“Ba gano Jaeez na yi ba, fahimtarsa na yi, yallab’ai ayyukan Jaeez su suka fahimtar da ni a inda yake, me yasa kuka kasa fahimtar hakan shi ne ban sani ba, maganar waye Jaeez kuma, nanata maganace, domin ayyukansa sun nuna wayeshi, d’an ta’adda mai had’ari, musamman ga ire-irenku, manyan ‘yan siyasa, da masu hannu da shuni, idan ka ga had’arin Ja’eez ya shafi talaka, to a matsayin fitina take, wacce take iya shafar wanda ma bai yi komai ba, aya ce ko?”
Ta mai da idanunta kan Basheer, idanu kawai ya bi ta da su, tayi murmushi ta d’auke kai ta fuskanci CP ta cigaba da cewa
“Yallab’ai, sanin dalilin da yasa Jaeez yake wad’annan ayyuka ya fi muhimmanci akan sanin inda yake, saboda salon ayyukansa sun nuna cewa d’aukar fansace a zuciyarsa, kamar yadda ka sani, kowani d’an ta’adda yana da dalilin ta’addancinsa da abinda yake so ya cimma, amma sanin inda yake, waye shi, duk abubuwane suma masu matuqar muhimmanci, kuma za a iya samun wad’annan ne ta hanya d’aya tak….”
Ta tsaya tana kallon CP, ganin ba zai yi magana ba sai ta murmusa tace
“Yallab’ai, na amsa dukkan tambayoyinka, ina da dattijan iyaye a gida, wato kakannina, za su shiga rud’ani idan suka ji an zo da ni nan, zan iya tafiya?”
“Saboda nan d’in d’akin gabatar da shirye-shiryenki ne da zaki fita bayan karanto tatsunuyoyinki?!”
“Kun ga Jaeez a jakatace ko kuma na goyoshi a gadon bayanane da zan zama me laifi?”
“Excuse me!” CP ya d’aga hanu wa Basheer, sannan yace
“Mene ne abu d’aya”?
” Excellent sir!, wannan ne tambayar da ta dace, abu d’ayan ba komai bane, sulhune!”
“Ke…!!”
Inspector ya yi nufin dakatar da ita, Cp ya sake dakatar da shi, sannan ya mata alamar ta cigaba.
Tayi murmushi sannan ta gyara zama tace
“Iyakarta kenan”
Ya nisa yace
“Ok, yanzu a mintuna hud’u, fad’a mana inda za mu samu Jaeez”
Ta sarqe yatsunta tare da kallon agogon tsintsiyar hanunta tace
“Duk wasu dabarunku na jami’ai ya kamata ku yi amfani da su cikin sulhun nan da na fad’a muku, ko da hakan yana nufin ku d’ana masa tarko da wannan sulhun ne, a nan za ku samo Jaeez, tabbaci Yallab’ai, zan iya tafiya”?
Tsawon minti biyu Cp na kallonta, karon farko yayi murmushi yace
“Za ki iya tafiya, amma…., idan yanayi ya zo da sauyi, za ki ganmu”
“Ready Sir!”
Hanyar fita ya nuna mata ta tashi tana murmushi ta fara tafiya tana cilla wayarta ta d’aukar rahoto tare da cafewa cike da nishad’i.
“Tana da matuqar wayo..!”
Cewar Cp, ya d’ora da cewa
“Ku bi diddiginta”
*****
A harabar gidansu ta tarar da kakanninta suna ta buge-bugen waya hankali a tashe, tayi ihun da ta saba tace
“Yeey!!!!, na rikirkitasu, ku zo maza in auna ku ko jininku yayi sama!!!”
Share#
Mrs A.A
[23/07, 2:31 am] +234 803 800 7509: _*QISAS*_🥷
~_HAYAT***_~
_*@Meerahgee*_ 🦜
*3*
Da kallon mamaki suke bin ta saboda dawowar bazatar da tayi musu, dan har labari ya riskesu cewa tana hanun policemen, yanzu haka iyayenta da ke qasar Egypt suke qoqarin kira bayan sun sanar da kawunanta abinda yake faruwa, amma wayar sai ta ai shiga.
“Happiness!”
Cewar kakanta namiji, da haka suke kiranta kasancewarsu tsoffin ‘yan boko, kuma a gurinsu ita farincikinsuce kasancewarta jika qwalli d’aya tak ta mace a gurinsu, asalin sunanta Khadeejah, amma iyayenta sukan kirata da Farha, a waje kuma akan kirata da maidoki, inkiyar mahaifinta, a kuma wani b’angaren ita d’in ma’abociyar hawa dokice, wanda hakan ya samo asali daga babanta, shi ya raineta da wasa da doki har hakan ya bi jikinta, ta qware sosai a wannan fannin, ta mai da hakan sababben abu a gurin amfani da doki wajen motsa jiki, kullum da safe sai tayi gudun doki sannan take samun cikakkiyar jin dad’in kowacce safiya.
“Yes tsoho…!”
“Aka ce an kamaki?”
“Wa ya ce?!, ok bar amsarka ma, ai na San me shegen bakin nan ne zai fad’a muku, Aku kawai!”
Tana maganar tana tafiya har ta kai bakin qofar falon sannan sannan ta tsaya ta juyo tace
“Koma dai Mene ne, gani nan ai na dawo, ni fa duk inda na shiga kada ma ku damu, zan raina musu hankali in yi tserewata..!”
“Ke dai Happiness ba za ki bar azarb’ab’i da cusa kanki a masifa ba ko?” Cewar kakarta ta mace.
Dafa kafad’ar kakar tayi tace
“Toh ni tsohuwa meye laifina, ai duk ke na d’auko, a dinga tuna baya dai ‘yar tsohuwa”
Ta ja kumatunta tana dariya.
“Ke kakar kike fad’a wa haka?”
yayi maganar daga tsayuwarsa a gurin, cikin tsiwa tace
“Ka min shiru!, d’an sa ido, akan kawo tsegumi wa tsofin nan sai na datse maka harshe, wada kawai!”
Ta wucesu tana mai waqar national anthem kamar yadda ta saba, idan tana son mai da zance past.
Murmushi kakannin suka yi, kakanta namijin yace “Uzairu ya kamata ka qara tsayi, dan ka guje wa wannan suna da happiness ta ke kiranka da shi.
“Duk a cikin soyayyane, idan ambaton hakan na mata dad’i, gwara dai in tabbata gajere, ina matuqar son yadda take kirana”
Gabad’aya suka yi dariya, dan sun saba da dramar Uzairu gajere da Happiness d’insu, dan kullum suna tare kamar ‘yan biyu dan shaquwa, amma ba jituwa, kullum a rigima suke, amma a hakan ba mai jure rashin d’aya na tsawon wuni kasancewarsu maqwabta.
*** *** ***
Da safe ta fice daga gida a mashin d’inta domin karb’o d’inki da telanta ya kirata yace idan tana gida ya zo ya kawo mata, ta ce a a, za ta zo ta karb’a da kanta, haka take, ba ta cika son jajub’o mutane gidansu ba, tana matuqar respect ga d’abi’ar kakanninta na qin hayaniyar yawan jama’a, sun fi son nutsattsen guri.
Tana cikin tafiya ta ji wayatar tana qara ta rage gudu ta d’auka ta kai kunnenta tayi sallama ta d’ora da fad’in
“My love, how are you in this morning?”
“Everything is Cool farha sweety, albishirinki”
“Ba goro ba, farinciki mother”
“Yanzu haka muna cikin Nigeria….!”
“What..!?”
Tace cikin yanayin zumud’i, yayin da hanun mashin yayi tangal-tangal kamar za ta fad’i, sai ta ji ta buga ma na gefenta, cikin rashin jin dad’i ta kai dubanta gareshi da hanzari za ta ba shi haquri, saidai kafin ma bakinta ya motsa ya d’aga mata hanu yace
“Sorry”
Sannan ya jinjina mata da babban yatsarsa tare da fincikar mashin d’insa yayi gaba, baki ta sake tana bin bayan mashin d’in da kallo, daga can kuma mother tana ta Kiran sunanta, ta mai da wayar kunnenta tace
“Sorry my love, wai me kike cewa ne?”
“Au ba ki ji abinda nake cewa ba?, wai ma me ya faru ne? na ji qarar abu marar dad’i”
“Ooo!, wannan?, wani hamagone ya shige gabana, kin san nigeriar tamu, d’an gaggawa kawai, kika ce kun dawo?, shi ne ma ba ki fad’a min ba, toh shikenan, na yi fushi, su umair da Yah Sauban duk na san kin sanar da su tunda wuri, har ma sun zo sun rigani ganinku, ni ce kawai ba a damu da ni ba, sai anjima….”
Ta katse wayar tare da ihun murna duk da a titi take, tana masifar son iyayenta, amma fa ta fi shaquwa da kakanninta, tamkar ma su ne maganad’isun rayuwarta.
Daga can Dr Safiyya tayi murmushi ta kalli Dr Ahmad tace
“Duk kai ka jawo Dr, ka san ‘yar rigimarka, complain take yi, har ma ta yi fushi”
Yayi dariyarsu ta manya tare da shafa sanqonsa yace
“Ina qara son Farha saboda irin salon rigimarta, ya na iya, sai ki shirya mu je biko”
“Kana qara sonta haka kullum kake fad’a, ni kuma fa” cewar Dr cike da zolaya.
“Ita rayuwatace, ke kuma duniyatace, d’aya ba zai amfaneni ba sai da d’aya”
“Allah?”
Ta tambayeshi tare da kashe ido d’aya, yace “zan tabbatar miki da hakan ne anjima”
Suka yi dariya gabad’aya cike da zallar farinciki.
***
Godiya tayi wa telan nata sannan ta fito da ledar kayan a hanunta ta nufi mashin tare da nufin sagaleshi a jikin mashin d’in, mannanniyar takardar da ta wanzu a jikin mashin d’in ne ya d’auki hankalinta, ta qura wa takardar idanu, da manyan baqi aka ruba *WELDONE* a jikinta, tsaki tayi ta fisge takardar ta jefar a qasa tana cewa
“Shirgi kawai, yanzu haka wani yarone ya manna min saboda rawar kai”
Haka take, ba ta cika son shirgi ba, duk kuma abinda bai mata ba, ba ta jinkirin sheqeshi daga rayuwarta.
Ko da ta koma gida gudu-gudu ta shirya cikin sabon d’inkinta na doguwar rigar atampa, sannan ta yane kanta da farin gyale, qafafunta ma fararen takalmane ma su tsini, sanyayyen qamshi ne ke fita daga jikinta, sai wanda ya kusanceta sosai ne zai iya jiyoshi, amma ita hakan ne daidai, bata son heavy perfume, ba sanya agogo a hanunta ba, amma akwai shiryayyun beats baqaqe cikin igiya a hanun nata, kamar koda yaushe idan tayi shirin fita aiki, yauma bluetooth ne maqale a kunnenta fari mai d’igon baqi a tsakiya, yayin da wayarta take cikin aljihun doguwar rigarta, ta riqe qaramar jaka a hanunta amma ba komai ne a ciki ba sai Biro, manad’in labarai, sai tarin cakulet kamar jakar tata shago ne, a hanun da ta riqe jakar akwai wata ‘yar paper da take dubawa yayin da hanun damanta yake aljihun rigarta wacce wayarta ke ciki.
Kamar daga sama ta ji muryar Uzairu yana ce yawa
“Ke doguwata, wannan kyau ne ko kuwa zallar kyau ne”
“Kai wada, ka fara shirirtarka kenan, daga nan kuma sai a tsiri tsegumin da za ayi bayan na fita, zo ma mu je ka kaini gurin aiki”
“Kai…!, yau wacce rana ce?, ba farinciki ba, qamshin farinciki na ji a zuciyata da kika fad’i hakan, idan na kai kuma bikin farincikin za a yi a gabad’ayar fadar zuciyata, hahaha..!”
“Shirme kawai!!!”
Ta jefa masa key tare da wuceshi.
Haka suka tafi suna ta barkwanci da fad’a a hanya har ya kai ta, suna tsayuwa ta sauke ta fauce key daga hanunsa tace
“Maza ja goshi ka tafi, ga d’ari biyar, na san za ta kai ka gida,wada kawai”
“Na gode doguwata, na san wannan ma duk tukuicin so ne, sai kin….”
Ya tsaya da maganar da yake yi idanunsa qir akan fitilar machine d’in, ya waro idanu yace
“Waye wannan kuma doguwata?”
“Me?, a ina?”
Da hanu ya nuna mata, ita ma ta d’an qara wa idanunta girma tana qoqarin fahimtar abinda hakan yake nufi.
Share only free pages#
Pay then read#
Mrs A.A
[23/07, 2:31 am] +234 803 800 7509: _*QISAS*_🥷
~_HAYAT***_~
_*@Meerahgee*_
*Free page*
*4*
Takarda ce a sagale a jikinta an rubuta ” *CORNER STONE* _take care!!!_.”
“Shirme kawai, wani mahaukacine wannan?, idan na koma gida zan tambayi maigadi ya fad’a min wanda yake zuwa jikin mashin d’ina yana min liqe-liqen banza”
Ta fad’a tare da cire takardar ta jefar.
“Hah, lallai koma waye mai wannan liqe-liqen ya tab’o gidan Rina, dan ba zan barshi ba…”
“Idan ka gama zubar sai ka tafi”
Ta wuceshi tana fad’in hakan, shi kuwa ya bita da kallo yana mata dariya.
***
Kwance take tana rubuce rubuce a laptop d’inta, ta ji sallamar daddynta, ta mance da wani fushi take yi ta tashi da gudunta ta d’afeshi, Dr Ahmad ya rungumeta sosai yana dariyar farinciki yace
“My love, na yi kewarki matuqa”
“Nima haka Daddy, saidai…”
“Bazata ce kawai dear, so nayi kawai ki ji mun shigo 9ja a lokacin da bakiyi tsammani ba, za ki fi farinciki…”
Ya ja hancinta, suka yi dariya gabad’aya, tace
“Matuqar farinciki Daddy, fatan tafiya tayi kyau”
“Sosai!, mun samu tarin nasarori a wannan tafiyar, asibitinmu za ta qara bunqasa duk a dalilin wannan tafiya..”
Tayi ihun murna ta sake qanqameshi, sai dariya yake mata, sai da ta yi ta masa tambayoyin da ta saba tana jin labaran abubuwan da suka je yi a Egypt sannan suka fito gurin Mummynta, nan ma murnar ta dinga yi saboda d’inbin alherorin da zai sami iyayenta dalilin tafiyar qarin ilmummuka kan abinda ya shafi aikinsu na likitanci, Dama can iyayenta sunyi zarra gurin qwarewar aiki, a fad’in qasa baki d’aya taurarunsu ke haskawa, suna kan lokacinsu, da qwazonsu da qoqarinsu ake kwatance har ma ake koyi.
“Sweet Farha, wani zance nake ji a gurin hajiya?, me ke tsakaninki da policemen?”
“Policemen?”
Dr Ahmad yace tare da zare glass idanunsa a waje.
“Eh, yanzu hajiya take fad’a min”
Baki bud’e yake kallonta, dan ba shi da labarin abinda jaridar ta fita d’auke da shi, baya qasar, kuma ko da yana nan ma bai cika samun lokacin kansa ba balle ya bibiyi abinda Jaridar take d’auke da shi, abinda ya sani d’iyarsa tana aiki da su kuma ta sha karb’ar lambar yabo.
A shagwab’e tace
“My love, tsarin aikine fa ya had’a mu da su, ita wannan tsohuwar rikicewane da ita, idan ba haka ba me zai had’a ni da ‘yan sanda?…”
“A qaryarki ba, ke dai ina jiye miki ranar da za ki had’u da Yah Abeed, wallahi sai ya kusan b’allaki…”
Umair da ya shigo da jarida a hanunsa ne ke fad’in hakan, kaka tace
“Subhanallahi, kai Umair wato ba ka da aiki sai yi wa yarinyar nan mummunan baki, ka ga Ahmad zan hana d’anka zuwa gidana, ban san me Happiness ta masa ba, idan qaryar tayi ina ruwanku da har sai kun karyata?, toh ga fili ga maidoki, Abeedun ya zo ya b’allata”
Dr yayi dariya yace “kai Umair ina ruwanka da wannan maganar, ko sai an hanaka zuwa d’eban albarka”?
Umair ya zauna yace. ” Dad ka daina biye wa wad’annan tsoffin, kullum ba su da aiki sai na kareta komi Girman laifinta, yanzu gashi nan, gani ya kori ji”
Ya miqa wa Dad, ya karb’a da sauri tare da mai da Glass idanunsa ya fara karanta inda Umair ya nuna masa, hankali a tashe ya saki Jaridar yayi salati yace
“Farha!?, what nonsense is this, are you in your sense?”
“Aa! Haba My love…”
“You shut up!!”
Sai da tayi vibrating a inda take zaune saboda tsoron tsawar, cikin tashin hankalin ya cigaba da cewa
“Kin san abinda kika fad’a kuwa?, Innalillahi…”
“Wai mene ne?” Cewar Dr. tare da d’aukar Jaridar ita ma dai hankalinta a tashen yake.
Sakin jaridar tayi kamar yadda Dr Ahmad ya sake ta koma ta zauna ragwab a kujera tare da dafe kai, Hajiya kaka tace
“Wai me kuke karantawane duk kuka firgice?”
Dr ne ya iya bayani wa su Hajiya, nan fa hankalin tsofin nan ya dugunzuma ya tashi.
“Da ke da aikin Jaridar duka sai na murzaku, ba zan tab’a sakaci da rayuwarki ba, ba zan iya jurar wani mummunan abu ya sameki ba, za ki canza akala kamar yadda na so tun farko, ke d’in likitace ba ‘yar Jarida ba, za ki bar qasar nan ko kina so ko ba kya so, shirmammiyar yarinya…!!!”
Yana haki ya qarasa maganar sannan ya zauna.
“Haba Dad, ni fa bani da matsala da aikina, kuma ita wannan maganar mun gamata da Cp, har ya sallameni tare da godiyar shawarwarin da na basu…”
“Shut up Farha!, Kar ki sa in miki shegen duka yanzu!, wa ya ce miki hukuma shashashai ne?, godiyar da suka miki ba godiya bace, tarko suka d’ana miki, yanzu duk wani motsin yana record, ban san wacce haukace a kanki ba Farha…”
“Ba wannan ba ma, abin tsoron shi Ja’eez d’in, yadda ta nuna ta san inda yake ba zai barta ba, sai ya mata bibiyar da ta fi ta ‘yan sandar, haka ma Yah Abeed yace, duk a kid’ime yake, kuma yana cikin fushi shiyasa bai shigo ba, dan zai iya dukanta…”
“Kai..kai dallah bana son shirme, Mene ne komai duka komai duka, yanzu dai dole ta bar qasar ma baki d’aya, ni kuma zan ji da komai a nan, Dr ta shi mu je dole in nemo izinin ganawa da Cp akan wannan maganar, kafin nan da daidaituwar komai, na soke miki fita…”
Da gudu tayi ciki tana kukan shagwab’a tare da bubbuga qafa tana fad’in
“Ni dai ina son aikina Dady…”
Bai bi ta kanta ba suka fice daga gidan tare da Umair, su kuma kakannin suka bi bayanta domin rarrashinta kamar yadda suka saba.
*** ***
Yau dai jikinta a sanyaye take sukuwa a dokin dan qaunar aikinta da ake son rabata da shi, ba ta hanu da fitan da aka ce Kar ta yi ba, a tunaninta gurin aiki ake nufi.
“Hmm, shi wannan Yah Abeed d’in ma sai na yi maganinsa, mai shisshigi kawai, tunda ya kawo jaridar da ta had’ani da iyayena, na qara tsanarsa ma…!”
Qarar gudun doki ta jiyo a bayan nata, ta tsagaita da maganar ta waiga dan ta ga waye?, tsai da dokinta tayi tana qare wa mahayin kallo, ba ta tab’a ganinsa a filin nan ba, abinda ta tabbatar kenan tun daga nesa, yawanci ta san structuren abokanta, musamman da wannan mahayin yake da rufaffiyar fuska, wannan ya tabbatar mata da hasashenta, a hankali ya qaraso inda take tsaye ya tsai da dokinsa suna fuskantar juna, tsawon minti biyu babu wanda yayi magana, a cikin minti na uku ya cire mask dake kan fuskarsa, take idanunta suka qara girma, zuciyarta ta harba da mugun qarfi saboda qarfin gizon da mahayin ya mata.
Share only free pages#
#pay then read.
Mrs A.A