Hausa Novels

Rana Daya Hausa Novel

Rana Daya Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Rana Daya Hausa Novel

PAGE 0⃣1⃣*

 

 

_Prime Lodge And Apartment hotels and suits – 1 Abba Kyari Abba Kolo Street Off Circular Road GRA Maiduguri, Borno state._

 

1:24pm

 

Samari ne guda biyu masu jini a jik’a wanda baza su wuce k’imanin shekaru ashirin da hud’u zuwa shida (24-26) ba, (kyawawa masu ginannen jiki.) Zaune suke bisa d’aya daga cikin teburan dake cikin restaurant na cikin Prime Lodge And Appartment hotels and suits suna fuskantar juna a yayinda kowanne ke da plate na fried rice had’e da co slow da kaza a gabanshi se kuma Schweps a gefe. Abincin nasu suke ci hankali kwance babu wata damuwa tattare da su. Kallo d’aya mutum ze musu yasan cewa ma’aikatan banki ne saboda corporate dressing da suke sanye da ita. Wanda ya kasance me haske sosai, mafi kyawu da kuma k’iran jiki yana sanye ne da sky blue long sleeves shirt with a red tie a yayinda d’ayan kuma ke sanye da white long sleeves shirt da black bow tie, duka da black pantsuit a yayinda suka mak’ala suit jacket nasu a jikin kujerun da suke zaune akai.

 

D’aya daga cikin wayoyin da suke kan table d’in ne ya shiga ringing, kyakkyawan ne yayi yunk’urin motsawa nuna alamun cewa wayarsa ne kenan. Drink nasa da yake zuk’a ya ajiye gefe guda sannan ya lek’a screen d’in ringing phone d’in wanda ya kasance iphone 7 plus jet black don ganin wake kira dum! Yaji zuciyansa ya buga.

 

“F*ck!” Ya fad’a a cike da tashin hankali a murya chan k’asa-k’asa.

 

“Triple A lafiya?” Abokin nasa ya tambaya immediately, yana mey maida hankalinshi sosai wajen abokin nashi da tashin hankali ya bayyana karara a fuskansa yana me goge hannunsa jikin wani brown multicolored hanky yayin da yake da aniyar daukar wayar. “Old man ne wallahi ya kirani d’azu da muke meeting gashi na manta shaf in kirashi bayan da muka gama” ya amsa sa da sauri gudun kar wayar ta tsinke. Swiping yayi ya d’aga tare da maqalashi a kunnenshi.

 

“Uhm uhm” yayi gyaran murya tare da fad’in “Halo Abba?” cikin sweet husky like voice nasa wanda there’s no doubt duk macen data kasance tana saurara dole ne ta tsinci kanta acikin wani yanayi. Murya ne da ke kwantar da hankalin me sauraronsa a yayinda yake sa ka mance duk wani damuwan da ke tattare da kai. Murya ne da ze iya sa bugun zuciyan mutum ya har6a, duk ba don komai ba se don coolness da calmness da take d’auke dashi.

 

“Prince?” Cewar Abba daga d’ayan 6angaren.

 

“Na’am Abba am sorry wallahi kai na ne yayi zafi kuma na manta in kiraka lokacin dana fito, I was in a meeting da ka kira d’azu” yayi mai bayani cike da biyayya.

 

“Oh haka ne? Nace kana ina ne?”

 

“Yanzu ina Prime Lodge ne ina cin abinci” ya amsa a takaice yana me duban rolex agogon da ke d’aure a tsintsiyar hannunsa.

 

“Alright ina buk’atan ganinka please as a matter of urgency” ya sanar dashi yana mey jaddada masa mahimmancin kiran.

 

“Sure Abba gani nan tahowa right away.”

 

“Toh seka zo, Allah ya kare” daga haka yayi hanging tare da miyar da wayan kan table din “Huh!” Ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya da ta ja hankalin abokin nashi.

 

“Guy how far? You seem tensed?” Tambayar abokin.

 

“It’s Abba” ya amsa sa a kasalance yana me nazari.

 

“Mai ya faru da shi?” Abokin ya kuma tambaya determinately yana kai cizo wa cinyan kazan da yake riqe dashi.

 

“Nima ban sani ba kawai de something smells not right don daga yadda yake magana mutum zesan da akwai wani abu a k’asa and I’ve got to find out” ya k’arasa tare da miqewa wanda hakan ya bawa mai rubutu daman k’arewa tsawonsa kallo, ba shakkka tsayayyen na miji ne don kuwa ko ba a auna ba ido ya nuna he’ll be nothing less than 6ft height. Damn!

 

“Abincin naka fah? Bazaka k’arisa ba?” Yayi saurin tambaya.

 

Karin wasu littafai da zaku so

“Kiran mahaifi fa Sultan? Kuma baka san me ake nufi da urgently bane? Urgently fa yace yake nema na I have to go, here” ya tsaya tare da zaro black wallet nasa na gucci dake cikin pantsuit nasa “Pay for those” ya sanar dashi tare da ajiye N4,000 akan table d’in ta gefen Sultan.

 

“Toh se yaushe kuma?”

 

“Kai dai ka k’ware a wajen tambayar silly questions” ya amsa shi yana juya ido “Of course gobe mana ko ka manta yau Wednesday ne gobe akwai office kuma ina da meeting?”

 

“Whatever!” Sultan ya amsa tare da jan k’aramar tsuka. Afzal be sake yi ta kansa ba ya shiga tattara assets da gadgets nasa then lastly suit nasa dake rataye jikin kujeran, ya6awa a hannunsa yayi sannan kaman yadda ya saba tafiya a hankali cike da k’asaita ya shiga takawa har ya fice daga building d’in ya shiga nufan inda yayi parking motarsa k’irar Genesis G80 dake jet black in color wacce tasha wanki k’al.

 

Bud’e k’ofan gaba yayi ya jefa suit d’in a baya tare da miqa sauran abubuwan da yake riqe dasu a passenger’s seat sannan ya tadda motar. Reverse yayi ya fita daga cikin harabar hotel d’in. Beyi nisa ba wayar sa dake jikin hanger ya shiga ringing ganin Abba ke kira again yaji gaban sa ya kuma bugawa wai me ke faruwa ne? Ya tambayi kansa. Ba tare da 6ata lokaci ba ya shiga neman car blutooth nasa wanda ke taimaka masa gun amsa waya ta hanyan sauqi ba tare da hankalinsa ya rabu ba a duk lokacin da yake tuk’i. A chan k’asar motan ya samu, be hankara ba yana d’aga kansa kawai yaga ya ma bar kan kwalta gabad’aya ya na nufan kan wata yarinyan da bazata wuce kuma baza ta gaza shekaru sha takwas (18 years) ba dake tsaye some meters away from him ta bud’e baki wide open in shock kawai tana jiran aikin gama ya gama; tsabagen yadda ta tsure ko motsawa takasa yi don ku6utar da kanta daga aukuwan wannan mumunar had’ari. Sanye take da baby pink color hijab me silky feel wanda ya mugun tafiya da golden skin color nata dake nan kaman irin na sudanese girls d’innan. Tana rik’e ne da manya-manyan ledoji da alama daga kasuwa take tayo siyayya da cefane. Ba shiri ya shiga neman inda brake nasa yake da niyyan takawa don hana aukuwan wannan had’ari dake neman afkuwa sede shima don yadda ya tsure ya ma rasa a ina brake d’in yake, ya juya sterring ma duk dabarar bata zo mai ba.

Kafin ya samu kan brake d’in ya taka ina aikin gama ya gama har ya buge ‘yar yarinyan da tuni ta zube a k’asa sede Alhamdulillah a nan Allah ya tsaida abun, Allah beso ya hau kanta ya tattake ta ba. Bonnet d’in ne ya bugeta ta gun k’afarta wanda hakan yayi sanadiyyar sum6ulewar ledojin dake hannunta na fashewa suka fashe na zubewa suma suka zube sukayi d’ai -d’ai a k’asa.

 

Wani wawan ihu ta k’urma kasancewan wannan ne karo na farko da mota ya ta6a bugeta a tarihin rayuwarta. Wallahi duk bakin Mami ne (mahaifiyarta,) abinda ta soma cewa a ranta kenan. Saida Mami tace mata tabari se yamma yayi taje aiken amman ta dage ita inba yanzu ba bazata je ba, toh ai ga irinta nan, abinda babba ya hango yaro koda ya hau kan tudu ba lalle ne ya gani ba.

 

Ba shiri mutanen da suke kusa duk suka yo kanta. Salati kawai Afzal yakeyi acikin motar har izuwa lokacin da ya fito yayi kan yarinyan dake ta shar6an ihu har yanzu wane wacce ake zare ma rai.

 

“Wayyoo ya karya min k’afa ya kasheni Mami! Kizo ki taimakeni” se ihu take tana salati. Kanta Afzal yayi da sauri tare da tsugunawa gabanta, k’afan nata data rik’e take ta ihu a yayinda yake mata zok’i ya aza hannunsa akai don duban ko taji mummunan rauni. Hannunsa na kaiwa akan jikinta baiwar Allah tayi tsit mutum na iya rantsewa liqe mata baki akayi. Tunda take a rayuwarta, a duk tarihin rayuwarta d’a na miji banda Papi (kakanta) be ta6a ta6a wani sashi a jikinta ba inba yau ba, idan an ta6ata toh a hannu ne wanda hakan ke faruwa a garin miqa ma wani abu ko makamancin hakan. Ko a secondary school saida akayi mata shedan hakan, har ya kaiga classmates nata suna kiranta da ustaziya suna mocking nata da sunan ‘yar mallam.

Shikenan yau nata ya k’are zatayi ciki, dama tunda ta fara menstral flow nata Maami tace mata duk sanda ta bari wani d’a na miji ya ta6ata toh zatayi ciki ranan, yau tana cikin wani yanayi. Wani irin d’an banzan ihu fiye da wad’anda take tayi tun d’azu ta saki, Afzal besan lokacin da ya sake ta ba ya shiga toshe kunnensa. Wannan wane irin mugun ihu ne! Yayi tunanin haka a cikin zuciyarshi.

 

A rayuwa idan akwai abinda ya tsana shine hayaniya kasancewar be saba da shi ba, shi kad’ai ne d’a a gun iyayensa. Baida yaya bale k’anin da ze tak’ura wa rayuwarsa, gidansu kullum tsit daga shi se Abban shi se Umminsa da kuma masu aiki.

 

Kunnensa ya shiga murzawa a tunaninsa ma ya kurmance ne. Sleepy like eyes nasa that are surrounded by long thick eyelashes ya d’ago yana kallonta cike da mamaki shin how is it possible ma ace mutum nada irin wannan murya me uban k’ara haka? To his ultimate dismay kawai yaga itama kallon nasa take ko kyaftawa babu.

 

Ta fannin ta kuwa tana iya rantsewa tunda tasan kanta inba a TV ba bata ta6a ganin kyakkyawan na miji kaman wannan dake tsugune a gabanta ba it became impossible to even blink. Shima kallon nata ya tsaya yi badan komi ba kuwa se domin tayi mai kama da wani wanda ya sani sede ya kasa tuna a ina. Sun d’au tsawon lokaci suna kallon juna, kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyarshi, daga bisani yarinyar ta kawar da kanta tare da kuma k’urma wani ihun da ya tsoratar dashi har yana neman tuntu6ewa.

 

“My goodness!” Yayi exclaiming a firgice anya kuwa ba aljana ya buge ba? Ya soma tunanin hakan a ransa.

“Wayyo bawan Allah ya karya min k’afa! Jama’a ku taimakeni!” Tasa kuka tana ta matse ‘yar k’wallan da ya ciko mata a ido.

 

“I’m sorry” ya fad’a a kid’ime don ko gabad’aya ta rud’ar dashi saidai wane k’ara yace mata. “For heaven’s sake kiyi hak’uri haka kibar kukan nan!” Ya sanar da ita a tsawace. Shi kansa besan lokacin da ya fusata ba. Saboda ta fara bashi haushi matuka, gashi de ya duba k’afan nata da take ta kururuwa mai bega wani ciwon arzikin da taji ba banda ‘yar k’urzine guiwanta da tayi maybe sed’an internal pain wanda baza a rasa ba. Then mesa take mai ihu tana cika mai kunne haka? Bata san cewa ya tsani hayaniya bane musamman na shirme mai k’ara da ihu irin wannan nata?

 

Shiru tayi tana kallon sa cike da mamaki na matuk’a lallai kuwa ya cika d’an halas. Ma tukuna bai da kunya tayi tunanin hakan. Na farko ya bugeta ya karya mata k’afa ya sanya mata asara kuma ya tsaya yana mata masifa? Na biyu kuwa mamakin ya za’ayi muryan na miji ya kasance da irin wannan dad’i da sanyi take. Bata ta6a jin murya irin nasa ba, tana iya rantsewa muryansa yafi na duk wani mahaluk’in data sani dad’i. Masifa yake amman yadda kalamun nasa suke slipping daga pink full inviting and perfect carved lips nasa yasa tama manta inda take da kuma inda ke mata ciwo. Ganin kallon da take mai bana k’arewa bane ya sashi feeling guilty, baida right na mata masifa, does he?

 

“Look am sorry but dan Allah ki dena mun wannan ihu haka and kibar kukan, yi hak’uri zan kai ki clinic su duba ki” kafin tayi magana wani mutum ya riga ta.

 

“Mallam kayi sauri mana kayi wani abu ko se lokaci ya k’ure tukuna zakayi abinda ya kamata?” Ya tambaya yana tsaye a kansu.

 

“I can handle this please duk kuna iya tafiya, ni na bugeta nasan abinda ya dace inyi, bana buk’atar wani ya gaya mun abinda zanyi so kuna iya tafiya” ya fad’a more like a command. D’aya bayan d’aya suka shiga watsewa ya rage daga Afzal se wannan drama queen dake ta faman kukan shagwa6a tun d’azu.

 

“Ke bakiya jin hak’uri ne kam?” Ya tambaya girarsa a murtuk’e yana me dawo da kallonsa a gareta like ta fara bashi haushi.

 

“Ban sani ba” ta murgud’a mai baki cike da rashin kunya “Wallahi ni gida gun Mami na zaka kaini ba wani asibiti ba. Haka kawai kana tuk’i ba ka kallon inda kake zuwa ka bugeni don mugunta da zalunci kuma yanzu ka tsaya kana min masifa wallahi Allah yafi ka, arghhhh! k’afa na” ta cigaba da ihun. Da mamaki yake kallonta, aje a bata san iya adadin shekarunsa ba amman ai ido ma ma’auni ne. Ita kanta tasan ya girmeta, inta haihuwan dabba nekam bema san kalan ta nawa ya ajiye ba. Secondly kodan wannan gigantic body structure na cikakken d’a na miji da Allah ya basa ma ai kad’ai ya isa yasa taji fakon sa tayi using respectable tone dashi amman har take kwatanta sa da azzalumi, gaskia wuyanta ya isa yanka. Mumunan harara ya watsa mata, wani ihun ta shiga k’urmawa. Ganin tana neman tara masa sabin jama’a ninkin na farkon yasa Afzal yayyafa wa zuciyansa ruwan don su rabu lafiya, duk wani feeling da girman kan da yake ji dashi ya sauk’e ya bata hak’uri. “I’m sorry” ya fad’a can ciki-ciki sede kaman bada ita yake ba ihun nata ta cigaba da rusawa chan da abin ya ishesa yace, “Wallahi idan baki min shiru ba allura zan miki” ya gwada tsorata ta don ko ba a gaya mishi ba tayi kalan me tsoron allura, yo mutumin da be karye ba yake ikirarin hakan kam ai se a hankali.

 

Allura?! ta nanata a zuciyanta. Rabonta da allura tun tana JSS1 time da tayi wani rashin lafiyan daya kusan kaita lahira, ai ba shiri tayi shiru.

 

“Better” yayi hissing yana maida hankalinsa kan k’afarta ta da take riqe dashi har a yanzun ta gurin ankle nata. Yunk’urin ta6awa yayi aiko ta make hannunsa da d’an karen zafi wanda ko be tambaya ba yasan she’s left handed (mutum me rubutu da aiki da hannun hagu) babu makawa sune hannun su keda uban zafi idan sunyi mari. Da wuri yaja hannun nasa baya yana murzawa kaman d’an yaro meanwhile yana kallonta cike da rashin yardan abinda ya faru, taya zata mareshi babba da shi? Ya tabbata bata da kunya.

 

“Ke!” Yayi exclaiming still not believing abin da ya faru “Ni kika mara?” Ya tambayeta cike da rashin yarda.

 

“Kuma ka sake yunk’urin ta6a ni na k’ara ma wani ba, ba nan kad’ai ba kuma na tara maka jama’a wallahi.” Totally floored ya tsaya yana kallon ta wace irin masifa ce ya jefa kanshi aciki yau? Da ba don kar ya shiga bakin jama’a ba da ya gwada mata rashin mutunci anan, da ya nuna mata waye Afzal Ahmad Amin (Triple A.) Wurga mata kud’in asibitin dayake da niyyan kaita yayi niyyan yi yayi tafiyarsa, taso ta kai kanta ko kuwa ta cigaba da zama anan d’in, how dare she slaps him? Danne zuciyarsa kawai yayi ya miqe “Tashi in kaiki clinic su dubaki in rabu da ke for good, ina da muhimman abubuwan da yafi zama gu d’aya dake.”

 

“Lallai ma bawan Allah ya tabbata ba kada kunya” tayi stating tana kallon cikin idanunsa a yayinda kyawun halittar da Allah yayi masa yake sake bayyana, ba abinda yafi burgeta kaman clean shave nasa da kuma silky gashin dake kwance a fuskansa a matsayin saje, only if yana tara gemu da tuni sajen da gemun sun had’e. Dama sau dayawa tana jin ana cewa maza kyawawa basu da mutunci sun kuma iya disregarding mata saboda gani suke kowa is after their beauty sede ita bazata bari ya raina taba, yo meye amfanin bakin da Allah ya bata? Right to freedom of speech.

 

“Ka karya min k’afa kuma ka tsaya kana cemin in mik’e? A ina aka ta6a yin hakan a garinku?” Ta tambaya kanta tsaye tana watsa mai harara.

 

“Now that tears it” Ya furta a fusace, tun d’azun yana d’aga mata k’afa yana saita kansa amma yarinyar nason kure hak’urin shi, dole yayi wani abu a kai kafin ta raina sa. Tsugunawa yayi ya cafko hannunta cike da mugunta yana murgud’awa.

“Ka sake ni!” Ta fad’a tana me k’ok’arin k’watan kanta sede takasa. Banza da ita yayi “Da farko dai ki iya wannan fitsararren bakin naki ko kisha zana anan wajen, kinga nayi maki kama da tsaranki ne?” Ya tsaya yana mata wani matsiyacin kallo. “Abu na biyu ” ya cigaba “Ni Afzal ban karya miki k’afa ba so ki daina min sharri.”

 

“Chan maka nide ka sake min hannu ka dena ta6ani” ganin baida niyyan saketa tace cike da tsiwa ” Se ta dalilin hakan ciki ya shiga jiki na tukuna ko me?!” Subhanallah wai me ke damun kwakwalwarta ne? Kunyan abinda ta fad’a ne ya kamata ita da kanta bale shi Afzal daya kasa gane ma meh tace balle abinda hakan ke nufi. Kanta ta kawar da wuri tare da rufe idon ta tana me cizan la66enta consciously.

 

Ta fannin Afzal kuwa kaman gunki yayi tsaye gun, ciki fa tace? Ta yaya? Wai shin ‘yar k’auyen ina ce wannan bala’d’add’iyar yarinyan da Allah ya had’asa da ita yau? Ba tantama ‘yar gudun hijira ce, bujakancin nata yayi yawa.

 

“Wallahi zan sa ihu” ta sake fad’a da bece komi ba har yanzu be kuma sake mata hannun ba.

 

“God help me!” ya fad’a yana dafe kansa. “Good idan bakiya son in ta6a ki ciki ya shiga jikinki kamar yadda kika ce to maza tashi kan k’afafunki, ki miqe-” katse sa tayi cike da rashin hakuri.

 

“Nak’i ka sani na dole mschww!” ta ja tsuka. Yunk’urin sake ta6ata yayi wannan karan don ya tsinka mata mari, tasa ihu “Wayyo dan Allah kayi hak’uri zan miqe zan miqe.”

 

“Good girl now up you go.”  Shiga miqewan tayi kaman yadda ya buk’ace ta amman ta kasa. “Wayyo wallahi bazan iya ba wallahi bawan Allah ka karya min k’afa” ta shiga rera kuka.

 

“Ban ce kibar min sharri ba?” Ya tambaya yana nad’e hannuwanshi akan faffad’an k’irjinshi.

 

Cike da shagwa6a tana murza idonta tace, “Ka fad’a amman wallahi ba sharri bane wayyo Mami na ni ka kaini gun Mami na.”

 

“Kin rantse de baza ki kulle wannan k’aton bakin naki daya cika ma mutane kunne da ihun banza da rashin kunya ba ko? Nasan yadda zanyi hakan” gano bakin zaren wato so yake ya sake ta6ata yasa tayi tsit.

 

“Ki miqe nace” ya buk’ace ta.

 

“Wai ba kada kunne ne? Ce maka akayi zan iya miqewan? Inda zan iya ai da nayi da jimawa ko jinka nid’in jin dad’in zama gu d’aya da kai ne? Dubi fa k’afa ka karya min.”

 

“Kika sake cewa na karya miki k’afa sena go6e wannan fitsararren bakin naki try me and see” ya fad’a threateningly.

 

“Azzalumi” ta furta can k’asa-k’asa yadda baze ji taba sede shegen nisan kunne ne dashi tsab ya jiyota.

 

“Kema ‘yar gudun hijira kawai” ya mayar mata. Harara ta watsa mishi tana cigaba da zum6uro bakinta, kallo ya k’are mata sannan daga bisani ya jata da hannu tare da d’agata a sama cak ya wulla ta into a bride like style sannan ya shiga takawa da ita. Cikin motar ya sata sannan ya rufe har a yanzun tana mai ihu.

 

“Wayyo 6arawo ze gudu da ni!” ta fad’a tana bubbuga glass na windon. So take ta bud’e k’ofar ta fita amman don k’auyenci irin nata bata iya ba. Yana shiga motan ya kunna ignition d’in har nan bata bar ihun ba yanzu kuma ba na ze gudu da ita take ba na cafanin Mami ne da suka zube, akan ya tsaya ta tattara sauran abubuwan da basu sha k’asa sosai ba saidai be ko saurara mata ba. Ganin hayaniyan nata bana k’arewa bane yayi pulling headphones nasa ya cika da loud music ya sanya yadda bazata kuma daminshi ba. Don kanta tayi shiru ganin ba mahalicci se Allah, har anan kuwa k’afan nata nakan yi mata zok’i. A hankali AC’n dake tashi acikin motan ya soma shiganta wani sanyin da bazata iya tuna when last ta ji irinsa ba ta soma ji probably tun da suka je competiton Kano da take ss2.

 

Afzal be sake ce mata komai ba seda suka isa asibitin inda yayi parking a harabar asibitin sannan ya fita ya bud’e mata k’ofar yana jiran ta fito itama.

“Ko ka manta ka karya min k’afa ne kake jiran in fita da kaina d’in?” Tayi inquiring cike da rashin kunya.

 

“Bance karki sake fad’in na karya miki k’afa ba?” Can k’asa-k’asa tace, “Ka fad’a amman ai gaskiya ne.”

 

“Kuma bana son gungunin nan bana son raini” ya fad’a a cikin tattausar murya. Ita dariya ma ya bata wa yaga Babanta da har zaice ga abinda yakeso da kuma abinda bayi so. Dariyan ta saki tana me mai kallon bakwai saura kwata cike da fitsara. Har maqora ta kai sa besan sanda ya fincikota daga cikin motar ba a fusace. Wani irin mumunar ihu ta k’urma bisa zogin da k’afan nata mai ciwo yayi mata bayan da ta taka mistakenly. Zubewa tayi take a gun a k’asa tana me raira kuka a yayinda ta rik’e gun idon sahun nata tana ihu. Ganin fa tana iya tara mishi jama’a ya jata da hannu d’aya putting her in a bride-like style kaman na d’azu ya shiga takawa da ita.

 

“Ka sauk’eni nikam bana so ka sauk’e ni nace mugu kawai shin baka san haramun ne ba ta6a wanda ba muharramin ka ba? Ka sauk’e ni!” Maida kallonsa yayi a gareta, “In sauk’eki?” ya tambayeta looking directly into her brown eyes a yayinda manly k’amshin jikinsa ya cika mata hanci, yau taji k’amshin da yafi turaren wutan Mami dad’i.

 

“Eh” ta fad’a tana me kawar da kanta a hankali, bata san me ba amman bata iya kallon cikin idanunsa na tsawon lokaci. Nodding kansa yayi sannan daga bisani ya janye hannayensa da suke riqe da ita, ai ba shiri ta zagaye hannayenta a wuyansa don maintaining balance nata da kuma hana kanta daga fad’uwa a k’asa to injure herself some more. Hak’i ta shiga yi na sosai sabida yadda zuciyarta ta mugun tsinke bata d’au rashin imanin nasa ya kai ga har zata ce ya saketa ya kuma yi hakan ba. Mak’irin murmushin da ya 6ullo da one-sided dimple nasa ya saki ganin wannan funny reaction natan ashede ba da gaske take ba “Dan Allah ka tare ni kar na fad’i” tayi rasping cike da tsoro ganin tana neman zamewa shikuwa baida niyyan preventing aukuwan hakan.

 

“In tare ki? Ina cewa kikayi in sake ki? Sai ki sakeni nima” ya fad’a in an I don’t care tone.

 

“Zan fad’i ne please ka tare ni.”

 

“Kin san da hakan kikace in sake ki?”

 

“Toh kai ma kasan zaka sakenin ka d’auke ni tun farko?” Har anan bata bari sun sake had’a ido ba.

 

“Kina magana ne?”

 

“A’a nayi shiru” ta furta a hankali. Mugun kallo ya watsa mata sannan ya rik’eta firmly suka k’arisa cikin asibitin inda akayi mata duk wasu gwaje gwajen da suka kamata aka gano spraining ankle (targade kafan) nata tayi a garin fad’uwan da tayi shiyasa ta kasa taka k’afan amman ba karyewa kaman yadda take ta kururuwa ba. Miqar da k’afan nata akayi inda tayita ihu wane wacce ke labor room. Shi de Afzal dake tsaye bakin k’ofa yana tsananin mamakin wacce irin roguwar yarinya ce wannan.

 

Bayan fitowan Dr ya basa prescription na drugs nata inda ya nufi gun cashier don biyan kudi sede hakan ya gagara kasancewan besan sunanta ba kuma a k’aidan asibitin bayan ko wani payment se anyi entering sunan patient da magunan da aka biya a record book. Excusing kan sa yayi ya wuce d’akin nata inda yayi knocking kamin nan yasa kai. Zaune bisa kan gadon d’akin ya tsince ta, ta zura wa k’afan nata da aka nad’e mata shi da bandage ido tana ta shessheqa. Tausayi da dariya duka ta bashi at a time, yana iya cewa tun da ya san kan sa be ta6a ganin drama queen kalan ta ba.

 

Ba’a dauki tsawon lokaci ba kafin k’amshin turarensa na Caron designs ya bugi hancinta kai tayi saurin d’agawa don ganin waye, ganin shi ne kuwa ta dukar da kan nata sannan ta shiga share hawayenta a hankali. Cike da k’asaita ya k’arisa gefen ta ya zauna daga baya kamin tace wani cikin ze sake mata idan ya matso kusa da ita.

 

Ganin ya kusan minti biyu zaune wajen batayi yunk’urin mai magana ba yayi deciding to go first, “What is your name?” ya tambayeta amman tamkar da gunki yake magana haka ta mar ko kallonsa batayi ba. “Hey dake nake magana fa” ya fad’a bayan wani lokaci. “Tell me your name in samu inyi settling bills naki” ai kaman me jiran ya kuma cewa wani abu kawai ta sa mai kuka, abinda yafi tsana kenan, ihun nan nata.

 

“Oh! Help me God'” ya furta tare da dafe kansa “Ke wai shikenan bakida sana’ar data fi ta kuka? Kukan me kuma kike min yanzu? Ni na ja miki k’afan ne? Seki je ki samu Dr’n kimar wannan kukan and not me” ya fada dalla dalla yadda zata gane.

 

“Mugu amman ai kai ka kawo ni seda na ce maka ka kaini gun Mami na kak’i Allah ze saqa min.” Dariya ne ya k’eto mar dukda cewa ta kwatantasa da mugun, muryansa ya gyara don 6atar da dariyar there’s no way ze bar ‘yar yarinya haka ta gane mar dariya.

 

“Whatever tell me your name, will you?”

 

“I won’t okay? Stop asking me to and just take me home I don’t want your drugs keep it” ta sanar dashi cike da tsiwa. Baki hangame ya bud’e yana kallonta da mamaki bil adadin. Na farko sam be kawo a ransa ma ta ta6a zuwa boko ba bale ta iya speaking fluent English haka. Na biyu taya zata kalli duk girmanshin nan ta mai masifa kaman wani d’anta ko shakkansa bata yi? Yau yana ganin wacce ta fisa taurin kai, ya lura idan yace shima ze nuna mata nasa taurin kan toh ba shakka baza su amfana da komi ba illa ma raina shi da zatayi don haka ya yayyafa wa zuciyarsa ruwan sanyi ya sauk’e duk wani tak’ama da jin kai nasa, fatansa kawai su rabu.

 

Numfasawa yayi don bata hak’uri amman ya kasa gashi har yanzun bata bar kukan da take ba.

 

“Okay I’m sorry” ya furta murya chan ciki-ciki bayan ya d’auki tsawon lokaci. “Nasan duk laifi nane kike nan but-”

 

“Amal… Amal Abdallah” ta sanar dashi cikin hawaye ta hanyan katse sa ba tare da ta d’ago kai ta kallesa ba. Kallonta yayi na ‘yan seconds sannan ya miqe yaje yayi settling bills d’in ya dawo ya tarar da ita still yadda ya barta.

 

 

 

*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~

So guys how was the chapter? Our very own first chapter. Was it a hit? Did you enjoy it? Are you craving for another update already?

 

RANA D’AYA

#RD

Love… Miemiebee

 

 

 

*RANA D’AYA!*

 

 

_Written by Miemiebee_

 

 

*PAGE 0⃣2⃣*

 

 

 

 

Seda ya d’auki tsawon lokacin da ya wuce tsammanin mutum sannan yace, “Ga magunan naki, ina kyautata zaton kin iya karatu za kuma ki iya gane dosage d-” bata basa dama ya k’arisa fad’in abinda yake da niyya ba ta katse shi “Mallam ba seka zageni ba am not an illiterate.”

 

“Serve you well” ya fad’a ba tare da nuna damuwa ba “Then kina iya tashi in kaiki gida.”

 

“Nagode kar ka damu I can bring myself home” taga alaman d’an rainin wayo ne shi to ya kwantar da bokatin hankalinsa, kar yace don ya ganta a haka zey raina mata wayo dan kuwa ita ba jahila bace saboda tayi karatun ta na secondary ba kuma a kowani gajan government school ba. No private school ne me kyau wanda ake kira da Ruby springfield college wanda ya kasance one of the best schools in Maiduguri.

 

“What gibberish are you saying?” Ya tambayeta a takaice. “See kar ki 6ata min lokaci, kar kiga don tun d’azun ina danne zuciya na ina binki a hankali ki d’au hakan ba a bakin komi ba. Ina da muhimman abubuwa a gaba na wanda sukafi tsayuwa anan ina rok’anki to take you home, now get up” ya buk’aceta cike da tsiwa sede ko motsawa Amal batayi ba. “Are you deaf?”

 

“I said to leave me alone!” Ta buga mai tsawan itama “Ka kama ka jawo min asara ina zaman zama na zaka wani kama kace min in tashi ka kaini gida? Me kakeson in cewa Mami bayan duk cafanin dana yo mata ka ta6ar6arar min dasu kabarni da babu? Don Allah ka barni kayi tafiyanka.”

 

“In ke baki san abunda ya kamata ba toh ni na sani a cewarki bazan biya ki asaran dana janyo miki bane? I’m aware of all that and zan mayar miki da komi kawai ni ki tashi in kaiki gida na bawa iyayenki hak’uri na fita hak’k’inki, I have other important things to attend to” ya sanar da ita. Kaman wacce bazata motsa ba se kuma ta shiga miqewa a hankali wanda a garin hakan ta kusa fad’i kasancewar k’afar nata da ta kasa takashi. Da sauri Afzal ya tarota, ganin bey saketa ba har yanzun kuma baida niyyan yin hakan ta shiga jan hannunta sai dai ta kasa.

 

“Don’t fight it” yace da ita “Muje” bata sake yunk’urin k’watan kanta ba har suka kai haraban asibitin inda yayi parking motarsa. Sanyata yayi a kujeran gaba sannan ya zagaya ya shiga shima tare da tada motar. A circular road inda ya kad’etan suka koma inda ya buk’ace ta da ta rubuta masa list na abubuwan datayi rashin nasu. Ba gardama ta amshi paper da biron ta lisafo komi harda kud’ad’e da amount nasu. Abu d’ad’d’aiku ne be samu ba wanda yamata alk’awarin bata kud’in idan ya kaita gida. A farko yaso su jesu kasuwan domin ta siyo amman tuna besan kan kasuwan ba sabida bai ta6a shiga ba seya fasa. A karo na biyu kuwa yayi tunanin ko zasu shiga su biyu tayi leading nasu but referring to her wounded leg yaga wuya kawai hakan zai bata so se yayi sticking to first decision d’in kawai: na miyar mata da kud’in. Kwatancen gidansu ya buk’ace ta da tayi mar wanda tayi ba tare da gardama ba. Chan cikin Jiddari suka shige. Tunda Afzal yake be ta6a shiga kwamacalan unguwa ba kaman wannan se yau, yasan war haka motansa ya fita daga kamanninsa ya dawo wani abun na daban saboda potholes da kwatamin daya rink’a shiga. Sun kai wani junction ta buk’ace sa daya tsaya.

 

“Ina ne gidan naku?” Abinda ya fara tambayarta kenan.

 

“Mota baya iya shiga layin zan k’arisa daga nan nagode.”

 

“Acewarki kawo ki kawai nayi saboda inada ra’ayin hakan? Am here to apologize to your parents and tsaya ba sekin karya min handle na mota ba” ya buk’ace ta ganin tun d’azun take k’ok’arin bud’ewa amman ta kasa. Fitowa yayi ya zagaya sannan ya bud’e mata k’ofar tare da miqa mata hannunsa.  A cewarta gabad’aya nufi yake da ta sanya nata aciki saboda ya taimaka ya fito da ita daga motan sede wani hanzari ba gudu ba tana gwada yunk’urin sa hannunta cikin nasa kawai taga yaja hannun nasa baya da sauri yana me kad’a mata kai “Tray d’in zaki miqa min” ya sanar da ita. Wani irin kunya kaman ta tone k’asa tasa kanta aciki ta jiyo amman wallahi seta rama ba shakka da gangan ya mata hakan don ya kunyatar da ita. “Kar ka damu ina da hannu I can manage” ta fad’a rai a murtik’e tare da murgud’a mai baki. Murmusawa yayi yaja gefe tare da crossing arms nasa a faffad’ar k’irjinsa yana me kallonta. Yasani sarai bazata iya fitowa ba harta sai ya taimaka mata toh why don’t he enjoy the moment?

 

Amal tafi minti biyu tana k’ok’arin fitowa amman ta gagara, ko kad’an k’afan nata baison nauyi ai kawai ta rushe da kuka har anan Afzal be motsa ba seda yabari ta sha wahala ta shiga neman taimako da kanta. Ganin ba mahalicci se Allah ta kewayo da kallonta a garesa, dagangan shiko ya shiga duban lokaci a agogon dake d’aure a hannunsa pretending as if beda masaniya game da abinda takeyi tun d’azu.

 

“Bawan Allah don Allah ka taimaka min bazan iya fita ba.” Dariya ne ya k’eto mar sosai amman ya dage ya danne tare da matsowa kusa da ita. “So kin iya magana da ladabi haka dama?” Ya tambayeta yana me k’are mata kallo.

 

“Ni ba abinda na buk’ata ba kenan” ta amsa tana me kawar da kanta haka kawai bata jin dad’in had’a ido dashi, “Ni ka taimaka min in samu in fita daga wannan motar nakan please!”

 

“Ohh! Rashin kunya kuma zakiyi min? Kinsan kad’an ne daga cin aiki na in barki har sekinyi tsami cikin motan nan ko? Don’t you dare me young lady.”

 

“A’a kayi hak’uri don Allah.” Cike da rashin mutunci ya taimaka mata ta samu ta fito daga motan suka shiga takawa zuwa gidan nasu wanda baida nisa daga inda Afzal yayi parking. Sede duk wani angle da suka wuce se sun zama topic and side of attraction. Surutu babu wanda basu ji ba amman duk haka suka manna musu har suka k’arisa gidansu Amal d’in.

 

Gida ne dai-dai da d’an talaka bawan Allah wanda za’a iya cewa be rasa ci da sha ba da kuma tufafi. D’akuna biyu ne gabad’aya a gidan a jere seda toilet d’aya daga other end d’in sekuma kitchen a opposite nashi, suna da famfo a tsakar gidan wanda ba sai anje ibo ruwa daga waje ba. Dai-dai Mami ta fito daga kitchen kenan su Amal suke k’arisowa tsakar gidan da Afzal riqe da ita, ai ba shiri tayi baya ta b’oye kanta cikin kitchen d’in tana me leqensu ta window. Salati kawai ta shiga yi ganin yadda mutumin dake sanye da suits ya riqo mata ‘ya a cewarta gabad’aya wani masifa Amal taje ta kwaso musu sanin sharpness na bakin ‘yar nata kaman razor. Tun farko dama bata goyi bayan zuwa aiken nan ba don de ba yadda ta iya ne Amal tafi k’arfinta gashi Papi (kakan Amal) da take d’an jin maganansa ma bai gida balle ya mata. Yau ina zata sa kanta Amal ta ibo musu abinda yafi k’arfinsu. Tunani kala-kala ba wanda ba tayi ba. Tunda suka shigo Afzal ke bin gidan da kallo, tabbas talakawa ne amman hakan be maida su k’azamai ba. Ko leather d’aya  be gani a k’asa ba ko ina an share tsaf ga kuma k’amshin turaren wutan dake tashi. Suna k’arisowa dai-dai tsakar gidan suka tsaya, se anan ya saketa tare da jan baya kad’an hakan ya bawa Amal daman sauk’e nauyayyiyar ajiyar zuciya.

 

“Ina Mamin naki?” Ya tambayeta ai take zuciyan Mami yawani har6a shikenan nata ya k’are yau ga Papi bayi nan yayi tafiya.

 

“Dake fa nake” Afzal ya kuma fad’i jin bata bashi amsa ba. Tsaida kewaye-kewayen da takeyi don neman Mami tayi tana me dawo da kallonta a garesa “Gani nayi tare muka shigo gidan taya kake tsammanin zan san inda take?” Ta tambayesa cike da rashin kunya. Cike da d’ambun mamaki Afzal ya tsaya yana kallonta shin wannan wacce irin fitsararriyar yarinya ce? Ace ko kunyan idonsa batayi ta rage wani abun? Sai dai ya daina mamakin hakan tuna ‘yan qauye da masifaffen rashin kunya ga kuma shaidan dayayi mata na ‘yar gudun hijira, tama daina basa mamakin. On the other side kuwa cikin Mami ya gama d’iban ruwa ji take kaman ta cafko Amal ta nad’a mata na jaki upon all the trouble data janyo masu still tana da bakin yima wannan security (as yadda ta ma Afzal shaida ganin sa sanye da suits) rashin kunya? Lallai kuwa tayi hak’uri ta rufa musu asiri.

 

“Mami!” Amal ta k’walla wa mahaifiyar nata kira, shiru kukeji ba amsa. “Mami don Allah ki fito daga b’uyan nan ni bance miki bala’i na kawo ba wannan mutumin gefe nan ne yazo baki hak’uri ya kad’e miki ‘ya” ta sanar a fili. Se anan Mami tad’an ji sukuni but even still ta kasa fitowa gani take kamar k’arya Amal keyi saboda sau dayawa takan yi mata hakan, ta d’ibo bala’i daga waje sannan ta fake tazo tace alkhairi ta kawo.

 

“Mami wallahi zan k’ariso in janyo ki daga kitchen d’innan” tafad’a tana kallon setin windon da Mami ke leqe daga gun ai tuni ta miyar da fuskarta ciki, ashe de Amal ta ganta. Numfasa tayi sannan ta fito alokacin kuwa Afzal ji yake idan be saki wannan dariyan daya k’eto mar ba ze iya mutuwa. Wannan wacce erin matsoraciyar uwa ce? Ai kam dole Amal tayi rashin kunya haka daga ganin mahaifiyar natan batayi kalan me tsiwa ba bale har ace zatayi discipline Amal.

 

Da k’yar d’in k’yar ya samu ya maida dariyan ciki ahaka ma seda yayi kad’an a waje wanda a sanadin haka Amal ta juya ta galla mai harara sede be ganta ba dake hankalinsa gabad’aya ya duk’ufa akan Mami yana mey mamakin yadda akayi basu kama sekace ba mahaifiyarta ba. Ashe bashi kad’ai ne bayi kama da Umminsa ba (mahaifiyar shi.)

 

“Sannu da zuwa bawan Allah” Mami ta fad’a tana nufo su cike da tsoro da fargaba.

 

“Yauwa Mami” Afzal ya amsa. “Ina yini?” Ya gaisheta cike da ladabi had’e da durk’usawa kad’an. Ai gaisuwan da Mami bata amsa ba kenan ta shiga basa hak’uri.

 

“Don Allah idan wani abun Baby tayi ma kayi hak’uri bawan Allah wallahi banida abun da zan iya baka banda hak’uri” tace ba alaman kwanciyan hankali a tattare da ita. Ido Amal ta juya cike da takaicin abinda Mami keyi gaban wannan maras mutuncin bawan Allah’n, taya zata tsaya tana basa hak’uri while shi ya kamata yayi hakan?

 

Afzal ya bud’e baki zeyi magana kenan Amal ta riga sa “Wai ni Mami yaushe nace miki nayi mar laifi? Dubi fa, dubi k’afa nafa” tayi maganan tana miqar da k’afanta a hankula so Mami could see “Karya min k’afa yayi.”

 

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Baby!” Mami tayi exclaiming tare da yin kan ‘yar nata tana me zaunar da ita a hankali bisa wani benchin dake kusa tana mata sannu in the process.

 

“Look Mami ni ban karya wa ‘yarki k’afa ba don’t listen to her” Cewar Afzal.

 

“Wallahi ya karya” Amal tayi saurin fad’i tana katse Mami “Idan ba karya min k’afa yayi ba toh seya fad’i dalilin daya sa ban iya taka k’afan.”

 

“Yi shiru Baby na sannu ai ko baki fad’a ba gashi kumburin k’afarki ta nuna kin karye saidai kariya nawa ne?”

 

“Kaman biyu ne inji likitan” ta fad’a bayan tasan sarai k’arya take. Se wani zum6uro baki take cike da shagwa6a a yayinda Mami ke ta mata sannu tana shafa k’afan a hankali.

Shi de Afzal ya rasa nayi, ya rasa menene yayi yau Allah ya had’a sa da dramatic people kallan wad’annan, ace ba babba ba yaro? Hmm shide gado ba gwaninta ba. Da kalan uwa me d’aura wa k’arya gindi haka ai ko hannu Amal ta d’aga ta zagi mutum a kan layi baza’a ga laifin ta ba tunda gashi ba tare da bincike ba mahaifiyar nata ta hau ta zauna akan k’aryan da ‘yar nata ta shirya na cewa an karya mata k’afa.

 

“Sannu ko Baby bari Papinki ya dawo a yanka miki d’aya daga cikin kajin kiwon nan. A kariya biyun har kika iya kike taka k’afan? Sannu.” Har anan bata yi ta kan Afzal dake tsaye duk mamaki yabi ya mamayesa ba.

 

“Mami?” Ya kirata ganin wannan draman nasu bana k’arewa bane gashi kuma yana da k’arancin lokaci.

 

“Tsaya tukuna bawan Allah in gama da ‘yar tawa ita kad’ai Allah ya bani-”

 

“Mami!” ya katse ta cike da rashin hak’uri, shi kansa besan lokacinda ya fusata har ya kira ta da tsiwa haka ba. Da mamaki both Mami da Amal suka juyo suna kallonsa, a yayinda zuciyan Amal ke raya mata itama ta miyar masa da masifan.

 

“Kinga na farko ni ban karya wa ‘yarki k’afa ba I admit I wasn’t watching the road attentively na gauce akan hannuna na yo kanta na kuma bugeta and am dearly sorry” ya fayyace mata. “Amman ban karya mata k’afa ba” ya k’arisa.

 

“Baka karya mata k’afa bafa kace? Ban gane ba, yo ko nufi kake kawai don ado likitan ya d’aure mata k’afar da bandeji?” Ta tambaya cike da mamaki tana kallon kumburarren k’afan Amal tare da kewayo da kallonta a gareshi, ba shakka akwai rainin hankali anan.

 

“Ni ba abinda nake nufi ba kenan amman de kam ban karya wa ‘yarki k’afa ba, targad’e ne ta samu tun achan kuma Dr’n ya sanar da ita hakan bansan dalilin da yasa tace miki kariya ne ba.”

 

“Hakane Baby?” Ta tambaya tana maido da kallonta akan Amal dake faman raba ido.

 

“Mami har sekin tambayeta ne? Da girma na ne zan tsaya ina miki wasa da hankali? Kuma idan da har banida niyyan admitting laifin da nayi do you think zan bar duk abinda nakeyi in nemi har gidanku domin in baku hak’uri akan hak’urin dana ba ita Amal d’in? Har kuma in kaita asibiti, think please” Daga yadda yake magana za a san ransa ya soma 6aci kuma bako k’arya acikin duk abinda ya fad’a.

 

“Hak’uri? Ni de baka ban hak’uri ba” cewar Amal tana murgud’a baki. “Allah ya karya min k’afa kar ki jisa Mami.”

 

“Baby kallen shin bawan Allahn nan karya miki k’afa yayi ko kuwa targad’en ce kamar yadda ya fad’i?”

 

Ganin fa an ganota ta soma kame-kame “Toh ni ina zan sani ko had’a baki sukayi da likitan don ya rufa mai asiri-” bugi Mami ta kai mata a cinya interrupting her, wanda a sanadin hakan ta sa ihu.

 

“Yanzu haka kawai kima bawan Allah sharri ya karya miki k’afa Baby? Shin yaushe zakiyi hankali?” Baki ta zumb’uro tana kukan munafirci a yayinda Mami ta juyo kan Afzal da yayi jugum yana kallon ikon Allah.

 

“Bawan Allah don Allah kayi hak’uri wallahi haka take gagara da rashin ji toh wane akanta akayi wahayinsa.”

 

“Ba sekin fad’a ba naga hakan a tattare da ita” ya fad’a yana meyi wa Amal kallon rainin hankalin dayasa ta murgud’a mai baki. “So am here to say sorry and take full responsibility” ya numfasa “Ga magunanta nan” anan ya miqa wa Mami leathern inda ta amsa “Dr yace karku tada hankalinku she’s going to be alright kuma gobe idan Allah ya kaimu zan dawo in maida ta asibitin don a sake dressing ankle natan kaman yadda likitan ya buk’ata. Za a cigaba da yin hakan na sati daga nan in shaa Allah k’afan zai warware.” Kafin Mami da akayi ma bayani tayi magana Amal ta hau k’orafi.

 

“Ni wallahi ban komawa asibitin” ta fad’a tana buga d’ayan k’afanta a k’asa stubbornly.

 

“Rufa min baki do Allah!” Mami ta ce da ita amman still se gunguni takeyi dake sam bata tsoron idon Mami. “Allah sarki bawan Allah lallai ka cika d’an halas mun kuma gode sosai, ina me sake baka hak’uri kuma.”

 

“Ba komai Mami ya wuce nine da godiya.”

 

“Allah yima albarka Babana.”

 

“Ameen” ya amsa da murmushi kad’an.

 

“Nace ba kar ka damu ba seka kuma dawowa bama anan tsallake gun wanzami zan kaita a sake duba k’afan nata gobe in shaa Allahu.”

 

“No Mami, I promised to take full responsibility so karki damu and here” ya fad’a yana ajiye ledojon a k’asa “Sakamakon hatsarin abubuwan da kika aiketa siya suka tarwatse so gasu I’m able to get some wad’anda ban samu ba kuma zan baku kud’in seku siya in kuka samu lokaci, I’m sorry” hannu ya zira a aljihun sa don ciro wallet nasa inda yaji wayam holy sh*t ashe ya baro sa acikin mota. “Excuse me please let me get my wallet.”

 

“Haba bawan Allah ai da ka bari, hakan ma mun gode wallahi ni na yafe sauran” fad’in Mami.

 

“Ni ban yafe ba” cewar Amal wane da ita aka kasa, ko ta kanta Afzal beyi ba yayi saurin katse Mami dake shirin yima Amal fad’a “No Mami please I insist, ai hak’k’in kune.”

 

“Toh shikenan tunda kace haka mun gode” ta fad’a tare da kewayo da kallonta akan Amal “Ke tashi ki bi bayansa ba seya sake shigowa nan inba yayi sahu biyu tunda duk ke kika jawo komi” cewar Mami.

 

“Taya ni na jawo? Ni na kaisa kad’eni?” Ta tambaya cike da rashin kunya.

 

“Da bance kibar aiken ba se da yamma kika k’i?” Zata kuma magana Mami tayi yunk’urin gwa6e bakinta nan take tayi shiru. Afzal da yayi shiru yana kallon su ne ya nisanta yace, “Karki damu Mami, let her be.”

 

“A’a don Allah kar muyi haka da kai. ”

 

“Mami-”

 

“Don Allah fa nace” hakan yasa yayi shiru.

 

“Toh shikenan” ya fad’a a hankali.

 

“Yauwa bari Baby ta bika seta amso kud’in tashi mana Baby” ta fad’a tana dawo da kallonta akan Baby dake faman zumbure-zumbure ko yunk’urin miqewa batayi ba. “Ko baki ji ni bane?”

 

“Toh ai bazan iya tashi ba.”

 

“Uhn uhn fa Baby kin san ni.”

 

“Don kinga Papi bai nan ba? Allah ze dawo dashi kuma wallahi sena k’irga mai komi” ba don tana so ba ta shiga miqewa wanda k’arshe saida Mami ta taimaka mata, k’ingishi ta shigayi tana takawa a hankali. Murmushi Afzal yayi sannan ya shiga bin bayanta.

 

“Toh gashi bawan Allah zaka tafi ban san sunanka ba.” Kewayo wa yayi cike da ladabi sannan yace “Afzal.”

 

“Afzal” ta nanata “Sunan larabawa ga me k’iran su, masha Allah” ta fad’a acikin wasa. Murmusawa yayi sannan yayi mata sallama ya fice alokacin har Amal ta isa bakin k’ofa tana tsaye tana kallon yaran dake wasa akan layi.

“Excuse me” yace da ita ganin tayi tsaye bakin k’ofan ba chance da ze wuce. Seda tayi muttering wasu kalamu chan k’asa iya jinta sannan taja gefe ya samu ya wuce. Bayan sa ta shiga bi sannan ta tsaya daga jikin wani bango a yayinda ya k’arisa gun motan nasa. Wallet d’in ya d’auko, dai-dai yazo bud’ewa kenan don sallamarta wayarsa dake inner aljihun suits jacket nasa ya shiga ringing. Ba tare da 6ata lokaci ba ya zaro, ganin Abba ke kira zuciyansa ya mugun har6awa yau ya shiga uku. Cike da fargaba ya d’aga sede kafin ya samu daman magana Abba ya riga sa.

 

“Yanzu Afzal in kiraka sau biyu in ce maka ina neman ka as a matter of urgency shine har yanzu ban ganka ba? Ai ko bangon duniya kake yaci ace ka dawo war haka” daga yadda yake magana mutum zaisan ransa ya 6aci matuk’a ba shakka Abban nan nashi mutum ne mai gajan hak’uri.

 

“Abba I’m so sorry-” katse sa Abba ya kuma yi “Wallahi ban san ka da halin nan ba, bansan kuma meyasa kake hakan ba amman karka damu ba seka zo d’inba domin shi wanda yake neman ma maganan ma ya gaji da jiran ka ya tafi” daga fad’in haka ya katse wayan ba tare da ya basa daman magana ba. Hankalin Afzal ya mugun tashi, rabon shi da ya 6atawa Abba rai irin na yau ya juma, probably tunda yake yaro lokacin da bai gama gano darajan iyaye ba. Yau ina zaisa kansa? A kullum shi me ladabi ne game da umarnin Abba, a kullum Abba na alfahari dashi se gashi yau all because of wannan fitsararriya ‘yar gudun hijirar ya 6atawa Abbansa rai to the extent da har Abba ya kashe waya a kansa abinda be ta6a yi ba. Yasani kafin Abba ya sauk’o ya soma mishi magana kuma se ranan da Allah ya nufa.

 

Ranshi a murtuk’e ya bud’e wallet d’in be ma san iya adadin kud’in daya d’iba ba tsabaragen all he wanted at that moment was yaga kansa a gida ya samu daman bawa Abba hak’uri tun kafin lokaci ya k’ure.

 

“Ke!” Ya daka mata tsawa wanda sanadin haka ta firgita. Tun da tasan kanta bayan wani PHE teacher’n su tun a JSS 3 ba wanda ya ta6a mata tsawa yakuma razana ta irin na yau. “Kinyi tsaye achan nine zan k’ariso miki da kud’in?” Ya jefa mata tambayar cike da tsiwa.

 

“Malam dakata fa!” ta tsorata iya tsoro amman dogon bakinta baze barta tayi shiru ba “Haka kawai bazaka sauk’e min haushin da kakeji a ka ba, a dalilin meh? Don wani ya kiraka ya 6ata maka rai se ka hau huce zafin ka a kaina kana min masifa? Da ni nace ka kad’eni kokuwa ni nace ka kawo ni gida? Ra’ayin da ya saka yin all of that shi zai sa ka tako har nan ka bani kud’in da kace zaka baiwa Mami in kai mata” ta fad’a kai a tsaye ko tsoron yadda yake kallonta cike da haushi da tsana batayi. Duban time a wrist watch dake d’aure a hannunsa yayi ganin he is running out of time yasa shi fasa aikata abinda yayi niyyan mata in ba haka ba belt nasa yayi niyyan zara ya nad’a mata na jaki a gurin tunda a gidansu ba meyi mata hakan. K’arisawa spot da take tsayen yayi sede yarinyan naku ko motsawa batayi ba dukda chan k’asan zuciyarta kuwa ta gama tsorata. A duk tunaninta mari ze kai mata setaji ya damqo hannunta, damqan da tana iya rantsewa ba a ta6a mata irin sa ba ai bata san lokacin da ta shiga ihu ba. Ji tayi k’asusuwan ta suna k’ara, wannan wani irin k’arfi yake da shi? Toh ita kam ya agaza ya rufa mata asiri kafin ya karya mata d’an hannu, ace ga kariya ga targad’e? Bazata iya ba.

 

“Naga alaman Allah ya had’aki da iyaye masu sanyin da ko tsawata miki basu iya yi as ko mey kikayi dai-dai ne a idansu kisani I’ll not let you disrespect me and get away with it, bazan bar k’aramar k’waron da bata kai inyi immediate sibling da ita ba ta raina ni, ko ki iya bakinki ko na koya miki yin hakan, maras kunya kawai.”

 

Sosai idonta ya cika da k’walla don azaba, “Ni ka sake min hannu kuma kar ka sake sa min sunan iyaye cikin zancenka, musamman na Abba na saboda ya rasu” ta fad’a cike da k’arfin hali. Ganin fa baida niyyan sake ta tasa ihu “Mami!” A lokacin har hawayen na neman gangarowa. Se anan ya saketa cike da wulak’anci regardless of her condition, wanda da ace ba bango a kusa da ita data fad’i a k’asa. Hannunta yaja out of nowhere tare da tusa mata kud’in aciki sannan ya juya ya kama tafiya. Kafin ya isa gun mota har Amal ta zaro kud’in ta k’irga, dubu hud’u ta gani “Hey!” Ta danna mai kira amman yayi banza da ita se a karo na biyu, nan ma ba juyawa yayi ba tsayuwa kawai yayi, “Ce ma akayi Papi na ya rasa na ciyar damu ne ko na sha da zaka wani kama ka bada dubu hud’u na abinda be taka kara ya karya ba?” Se anan ya juyo yana kallonta ashe de dubu hud’u ya zara “Zan d’au dubu d’aya, ban sani ba ko canji ze rage amman idan har ya kasance hakan, I’ll return your change for you ga sauran kud’in ka” nan ta zare dubu daga ciki tare da yin watsi da sauran a k’asa ta juya da k’ingishinta ta wuce layin gidansu leaving Afzal da baki wangalau a bud’e cike da mamaki, don shock k’wak’walwarsa tama kasa fahimtar dashi abinda wannan ‘yar gudun hijirar ta masa. Ji yake as if ya cafko ta ya nad’a mata na jaki shin wannan ya iyayenta suka girmar da ita? Fitsara sekace 6era, besan na gida ba balle bak’o. Lallai ta guji had’uwansu, yanzu baiwa Abba hak’uri ne ke gabansa dako seta gommaci kid’a da karatu.

 

 

 

 

*~*~*~*~*~*~*~*~*~*

So how was the chapter? One word for Amal?

In shaa Allahu bayan sallan azumi kuma semu d’aura daga inda muka tsaya. Na sako pages biyun nan ne domin mutane irinsu Meela da Sumayyah masu shegen maita da tak’uri  se kuma don wasu fans d’ina da suka d’au cewa na daina rubutun hausa gabad’aya. Wishing you all a faithful Ramadan ahead xoxo.

Leave a Comment

error: Content is protected !!