Entertainment

Rariya Hausa Matatar Gaskiya Karanta Labarun Mu

Rariya Hausa Matatar Gaskiya Karanta Labarun Mu

 

Rariya hausa

 

 

 

 

 

 

 

Rariya Hausa Matatar Gaskiya Karanta Labarun Mu

1987-October- 23

Sintiri yake hannun goye a bayan shi, tsakanin zauren gidan shi sanye yake da janfa! Shigowa da sauri wata dattijuwa tayi ta zub’e akan gwiwarta cikin hakki, sai da ta dai-daita nutsuwarta sannan tace.

“Allah Ya taimaki me martaba! Ubangiji ya kare takawa lafiya! Allah ya bawa takawa Abinda yake nima! A gafarce Ni da kitsen  da nayi!”

 

Shiru zauren ya dauka! Kafin yayi magana cikin sansanyar murya yace..

“Ina jinki Jakadiya!”

 

Sake risinawa tayi sosai sannan tace.

“Allah taimaki Sarki Jalaludeen! Adalin Sarkin mu! Me kaunar Al’ummar shi!”

 

Shiru tayi sannan ta had’iye yawu kafin ta cigaba da cewa.

“Allah ya karama nisan kwana! K’wark’waranka Ummu Rumana tana kan gwiwa! Ita da Fulani Hasiyah”

 

Shiru yayi kamar bayi zauren, sannan ya d’aga mata hannu!

Mik’ewa tayi cikin sauri tace.

“Na Barka lafiya! Allah ya kawo maganin Izza lafiya”

 

Tunda ta bashi labarin Rumana tana kan gwiwa yaji duk wata nutsuwar shi ya kwace,

Ajiyar zuciya ya sauke Kafin ya koma kan shimfid’ar shi da yasha kwalliya da dardumai tare da kilisai, ya zauna a yanzun a halin da yake ciki mutum d’aya yake bukatar gani a cikin wannan yanayin! Wato tsohon amininshi Magaji!

 

Mik’ewa yayi tare da nufar cikin d’akin shi, ya sauya kayan shi ya b’adda kama, sannan ya nufi kofar dake cikin Zauren shi wanda zai fidda ka wajen masarautar Daura.

 

——

A hanyar fita Jakadiya suka yi karo da Shamaki!

“A’ah Jigal kazamin tsuntsu,”

 

“A’ah me abu da abinsu kura da kalabin kitse daga ina haka”

 

Murmushi tayi da alamun abinda ya gaya mata yayi mata dad’i tace.

“Hmm! Maraba da gasheshe kura taga bakin jaki”

 

Gyara tsayuwar yayi sosai dan ya fahimci akwai magana a bakinta.

Juyawa yayi hagu da dama yace.

“Da kukan kura, da bacewar akuya duk d’aya ce! Meke tafe dake”

 

Mika hannunta tayi cikin muzurai tace.

“Da babbar rowa gara karamar kyauta”

 

Zuba mata ido yayi aikuwa ta kauda kanta, kamar ba ita tayi maganar ba. Jinjina kai yayi sannan ya sanya hannu a cikin aljuhun shi ya ciro kud’i ya mika mata.

 

Murmushi tayi sannan ta kirga kuɗin kafin tace.

“Cinikin duniya, diban nono!”

 

“Hmm me tsegumi bashi rabuwa da waiwaya! Meke faru”

 

Juyar da kai tayi sannan tace.

“Bikin farar kaza! Su balbala gayyar sod’i ce, Fulani Hasiyah da K’wark’warar Sarki suna bisa gwiwarsu! Amma wannan karon zakarar dawaki ne kukanshi bana Alkhairin bane, zan koma ciki.”

 

“Kina nufin!”

 

“Gyaran hanci, yafi gyaran gona! Koma me nake nufi kasan baza a nunawa ringing wata ba, dan da alamu cikin su dole asami d’aya ta”

 

Shiru yayi bai tanka mata ba ya kad’e saka tarar shi yayi gaba, yana magana.

“Tab bashi yuwa, an san da wuyar biri ake d’aura shi a k’ugu! Dole mu hana haihuwar d’a namiji a cikin wannan masarautar!”

 

“Assalamu alaikum!”

Da sauri ta zub’e akan gwiwarta, tace.

“Allah Ya taimaki! Fulani Sakonki ya isa ga sarki Jalaludeen!”

 

Juya bayanta tayi tana kallon yan tsuntsayen da suke shawagi a cikin kejinsu! Sannan ta mai da idanunta kan jaririyar da take nad’e cikin kunshi zani.

 

“Kije ki duba min Rumana! Ki nemi amintacciyar baiwa ki bata gadin Rumana, idan ta haihu kar a kai ga fad’a takawa”

 

Gyad’a kai kawai Jakadiya tayi, sannan ta mik’e da sauri tare da barin d’akin. Tana murmushi sannan tace.

“Mutanen duniya kudan doki ne, dole abisu a hankali! Muje zuwa”

 

Da sauri ta wuce zuwa hanyar da zai kaita shashin k’wark’wara Rumana, tana shiga kamar wacce yazo da haihuwar. Korar unguwar zoman tayi, takira wata cikin bayin ta turata Katanga bayi, sai gasu tare da wata baiwa dattijuwa itama.

“Larai ki gyara abinda aka haifa, naga kamar ta sume kar labarin haihuwar ya isa ga takawa! Duba min ma tukun me ta haifa”

 

Dake k’wark’wara Rumana a durkushe take, d’aga zanin Baiwa Larai tayi, ta janyo abinda aka samu. A d’imauce ta d’ago kanta tana kallon Jakadiya, bakinta na rawa tace.

“Ranki shi dad’e! Ai magajin masarauta aka samu.”

 

Wata irin zabura Jakadiya tayi cikin mamaki tare da lekawa, taga abinda aka samu d’a namiji ne kyakyawa dashi, kaman shi da sarki Jamaluddin ya b’aci, hasken fatar uwar shi.

Takowa tayi ta d’ago kan Rumana wacce take sume bayan haihuwar ta, tace.

“Ki nad’e jaririn ki tabbatar kin yanke cibiya”

 

Tana gama fad’ar haka tabar cikin dakin da sauri, kallon unguwar zomar tayi, sannan tace.

” Zaku iya tafiya, dan ta sauka lafiya kuma.”

 

Sai tayi shiru sannan ta wuce bayan taga barin su gurin, b’ata nufi shashin Fulani ba, fita tayi daga masarautar,

 

Wani gida ta nuna sannan ta wuce zauren gidan, babu sallama ta akfa musu.

“Toh tauraruwa mai wutsiya! Meke tafe dake!”

 

Murmushi tayi sannan tace.

“An kawo kare dan haushi, ya buge da kukan akuya!”

 

Zubur ya mik’e jikin shi na rawa,

“Karya ne Jakadiya! Masallacin kura kare bashi limancin”

 

“Allah sarki! Harbi ga wutsiya kuskure ne” Inji Jakadiya.

 

“Me haka ke nufi?”

Ya wurgata mata tambaya,

Rariya Hausa Matatar Gaskiya Karanta Labarun Mu

 

“Eh hakan yana nufin duk matan sarki babu wacce tayi nasarar da Rumana tayi,”

 

“Aikin banza kiba a kunne! Sani ake zance.”

“Na Barka lafiya”

Ta ficce da sauri, daga cikin gidan ta nufi masarautar tana juyawa murmushi tayi sannan tace.

 

“Komi gaggawar hasara dole ta jira samu”

 

Shashin Fulani ta nufa, cikin sauri ko sallama ba tayi ba ta zub’e a gaban fulani, cikin hali ta sunkuyar da kai zuciyarta cike da fargaba, dan duk wata munakisa da kutungwailarta bata kamo kafar Fulani Hasiyah ba.

“Me Rumana ta samu?!”

Tambayar da Fulani ta wurgo mata ya katse mata tunanin da take.

“Ranki shi dad’e! Ina niman afuwarki, Allah ya huci zuciyarki! Hmm ta sami abinda Takawa yake mafarkin samu ne”

 

Murmushi Fulani Hasiyah ta sake, har sai da Jakadiya ta d’ago kanta tana mamakinta sannan tace.

“Allah ya huci zuciyarki! Farin ciki kike na gani!”

 

“Ki dauki y’ar ki kaita inda Rumana take! Sannan wacce kika bari a gurin! Ki sanya Bak’o ya aikata inda bazata dawo ba! Gawar sai ku mata sutura a tabbatar da Rumana ce ta haihuwa Y’a mace! sauran bayanin kin fahimta, ina yaso Jaririyar ki san hikimar da zaki kara!”

Takowa tayi gaban Jakadiya tana kallon cikin idanunta, ta cigaba da cewa.

“Abinda wancan yace, shi nace kirarin me tsoro kin fahimta”

 

Gyad’a kai Jakadiya tayi cikin tsantsar tsoro tace.

“Uwar d’akina aka mutu ma balle lalacewa! Ai zancenki kamar an binne Rumana da ranta ne, balle Larai”

 

“Muguwar aniya bata karewa tukunya,” Inji Fulani.

 

Sunkuyar da kai Jakadiya tayi dan ta fahimci sakon Fulani, a hankali tace.

“Allah kad’ai ke kaunar kura”

 

Fita Jakadiya tayi bayan ta dauki jaririyar sannan tace.

” Duk inda jirgi yaje, inda hakuri wata rana kunkuru zashi sai dai ya jima bai isa ba! Fulani dani kike zancen”

 

Tana shiga inda Rumana take ta kori larai sannan ta dauki d’an Rumana ta ajiye mata yar da tazo da ita, sannan ta fita da Yaron da Rumana ta haifa.

 

 

Bayan Sa’a d’aya aka fidda sanarwar mutuwar Rumana bayan ta haihu, sai mutuwar Baiwar da ta amshi haihuwar sakamakon gubar da tasha.

——

 

Tun bayan fitar Mai martaba Sarki Jalaludeen, ya nufi gidan abokin shi, sun jima suna tattaunawa kafin ya bar gidan, zuwa masarautar a cikin shigar shi na tsofi tukuf ya isa shashinsa, yana cire kayan. Ya tsinkayo Muryar Jakadiya.

Gaban shine yayi mugun Fad’uwa ya fito daga d’akin yana kallonta.

 

“Ina me niman afuwarka! Ya shugabana! Fulani Hasiyah ta sauka lafiya an sami magajinka! Sai Kuma abin alhinin da ya kuma faruwa shine, Uwar d’akina ta haifi Y’a mace Amma kuma rai yayi halin sa.”

 

Ji yayi jiri ya nemi ka dashi, zama yayi a kujeran dake zauren shi tare da dage kan shi, yana jin wani irin ciwon kai tare da zafin da kan shi yayi.

 

“Jeki!”

“Allah ya baka hakuri da danganar rashinta”

 

Tana fita ya kira fuskarshi akan ta tafin hannunshi kwalla na zuba mishi. Tuno ranar da Jakadiya ta kawo mishi ita yayi, cikin shigar alkyaba tare da wata riga me santsi, a cikin kuruciyarta dan lokacin bazata wuce sha uku sha huɗu ba, shi yayi nasarar koya mata sanin waye shi, a daren ya tabbatar da ita ma matar shi ce. Abubuwa sun tafi kuma sun dawo mishi.

 

Dakyar ya shirya sannan ya fito.

Aka yi jana’izar ta aka kaita gidanta na gaskiya, dake ba a fita da duk wanda yake cikin masarautar misali sarki ko matansa, ko yaran shi a a masarautar akwai makabarta.

Tunda ya duka kan kabarinta yake zubda kwalla da sosai sai Da Waziri da Sarkin malamai suka d’ago shi.

 

Bayan kwana bakwai aka rad’awa Yaran suna, Namijin aka sanya mishi Jamaludeen ita kuma mace. Aka sanya mata Jamalah, dukda anyi rasuwa haka ya takaita shagalin da aka shirya

——

1990-March-09

“Bazan bari haka ta kuma faruwa ba,dole nayi amfani da damar da masani.”

 

 

“A’ah Shamaki! Idan junarka samakone, toh wani a tafe ya kwana! Kabi a sannu sai mu kai labari idan kuma kayi, fitar burtu tabbas zamu iya fad’a holoko hadarin ƙaƙa”

 

“Lallai Jakadiya kin zama ciki, me manta kyautar juya. Tsaf na shirya.”

 

“Hmmmm! Shamaki kamar yadda Gara takan kalli dutse sai gani sai hange haka zamu cigaba da zuba idanun mu dan kana kuskura, zaka yi borin tukunya idan tayi borin kanta zata b’ata.”

 

“Jakadiya jeki yau babu alkhairi a tattare dake sai zallar sharri.”

 

Fita tayi da sauri, tabar gidan.

—–

1997-july-29

A babbar Asibitin garin katsani aka kawo sarki Jalaludeen wanda ya dad’e daga kan dokinshi zai tafi hawan sallah, hankalin kowa a tashe.

 

Sai da ya shafe wata shida kafin aka sallame shi akan keken guragun, inda baya iya ko magana sai dai nuni da hannu, kuma bai cika nunawa kowa ba, sai Jamal wanda lokacin yake shekaru goma sha daya. Shine yakewa mahaifin shi komai, dan yaki yarda da kowa sai Jamal din, wani lokaci haka zai sanya shi a gaba yana kallon shi.

—–

2003-5-17.

“Don Allah! Jakadiya na rokeki ki barni naga Mai Martaba! Ko sau d’aya ne! Kinji don Allah.”

 

“Kinga Rumana ki fitar min tun ina ganin girman ki! In ba haka ba zan sanya a wulakantanki.”

 

Haka Rumana ta zuba mata ido, kwalla na zubo mata tace.

“Jakadiya! Kina b’oye min wani abu, amma ba komai! Me hankali shi yake gane dingishin kwad’o.”

Rariya Hausa Matatar Gaskiya Karanta Labarun Mu

Tana gama fad’ar haka ta bar dakin Jakadiya, ta nufi hanyar gidansu. Da gudu aka bangajeta, tsayawa tayi, tana kallon yaran mace da namiji, a zuciye namijin ya biyo macen, ita kuma ta koma bayan Rumana ta b’oye tana dariya tana cewa..

“An gaya maka d’in me idanun mage.”

 

Cikin sansanyar murya yace.

“Jamalah”

D’ago kai Rumana tayi tana kallon shi, sannan ta juya ga ita Yarinyar tace.

“Ki mishi magana kar ya tab’a Ni dan Umma Fulani bata mishi fad’a sai Abba!”

 

Kura mishi ido tayi tun daga kanshi har zuwa kafar shi, kai karewa har da girar shi da gashin idanunshi, wanda suka yi wani kama da Sarkin Jalaludeen, hasken fatar shi da kwayar idanunshi, zuciyarta ce tayi wani irin bugawa, lokacin d’aya ta shiga kokwanto da zuciyarta, zazzakar muryan yarinyar ta katse mata kallon shi tace.

“Don Allah! Ki mishi fad’a”

 

Zuciyarta na bugawa cikin sauri da tace.

“Yarima! Karka tab’a kaji”

“Yawwa! Ki gaya mishi nice Babba bashi ba, dan Umma Fulani tace na bashi awa biyu”

 

Wani irin bugu zuciyarta yayi kamar zai faso kirjinta, sai da ta dage kirjin.

Cikin wani irin murya tace.

“Don Allah! Naci Arziki karka tab’a ta”

 

Gyad’a mata kai yayi sannan yace.

“Shi kenan! Umma bazan tab’a ba”

Kallon juna suka yi, ya kauda akanshi da sauri, sabida cika mishi ido da tayi, cizon lips dinshi yayi sannan ya bar gurin, da ido ta bishi.

 

Tana mamakin yaron, tasamu labarin abinda ta haifa ya mutu, shine sarki yasaka aka dawo da ita cikin bayi, sannan kuma taji labarin Fulani Hasiyah ta haifi yan biyu.

 

 

_Tohfa Gamu a wani masarautar ban sani ba ko zaki so labarin idan yayi muku ku tab’a Ni ta hanyar Voter wannan pagen ko da kuma comments dinku! Bana tamtama da Yan Whatsp dan suna ƙoƙarin bani lokacin su Nagode 🤝 sosai, ta Vote da comments zansan kuna tare dani_

[6/11, 12:55 PM] My Zahrah: 🌹🥀🌷

*ƘWARƘWARAH*

🌼🏵️🌺

”'{ITAMA MATAR SARKI CE}”’

 

_LOVE TRIANGLE♥️_

 

 

 

 

Mai_Dambu

Oum-Muwaddah

Rariya Hausa Matatar Gaskiya Karanta Labarun Mu

 

_Allah Jiya kun bani dariya daga masu rudewa a sunan book sai Mrs Umar da tace bata fahimtar Hausar ga shafinku nan daku aka fara💋_

2️⃣

Juyawa tayi ta koma shashin Jakadiya, ta kura mata ido! Sannan tace.

“Kina b’oye min wani sirri”

 

“Kinga ki bar gidan nan ko nace ki fita ki koma inda kika fito! Barinki da nayi a raye shine kuskure na! Da na kasheki ko sa aka kashe ki, da baki kawo labari ba.”

 

Wani irin kallon Rumana take bin Jakadiya dashi, sannan tace.

“Tabbas duk wanda ya ce garinsu da nisa, ba a kama shi ya kuɓu ce ba.”

Murmushi Jakadiya tayi sannan tace.

“Idan rakuminki ya b’ata..”

“Ba sai kin juya min ba na ganshi kuma yana tsakanin ku! Sai dai wannan raƙumin ba taciwa! Kuma bazata isa ga tanadu ba, na rantse miki dole ne cin kasuwa da makiyi! Ko kuma so ko baku so sai na sai na baku mamaki”

 

Dariya Jakadiya tayi sannan tace.

” Idan farauta taki kyau, ko kunkuru guduwa yake, balle kuma ke da kike a matsayin baiwa k’wark’wara ma mara kima”

 

Dariya sosai Rumana tayi sannan tace..

“Aiko da girgizar kunar tafi magarya! Balle aje ga lissafi ai biyu tafi d’aya koda rabi ne, k’wark’wara da ai tafi baiwar mara daraja da kima, Jakadiya.”

Takawa tayi gaban Jakadiya ta sake murmushi musamman da taga idanun Jakadiya a waje cike da tsoro ta sake dariya sannan tace.

” Kura kenan ga tsoro, ga baka tsoro a dana tsoronki dan yanzun bani da ikon miki komai, amma tabbas lokaci zai zo kare sai ya fiki daraja.”

 

 

Tana gama fad’ar haka ta juya tayi ficcewarta, tana fita Jakadiya taja tsaki tana cewa.

*Hhhh! Wai bishi zatawa kunkuru gori, wato ita dan ta zauna da sarki shine tafimu kima, ayi dai mugani ina tusa zata hura wuta*

 

Koda Jakadiya taje shashin Fulani ba gaya mata ba, dan akwai nufi a ranta.

 

Dan haka tayi tunanin Amfani da wata damar dan cimma wata damar.

 

Sosa Kai tayi sannan tace.

“Uwar d’akina! Baya goya marayu! Uwar mara uwa! Gatan marayu! Uwar d’akina daga ke babu wani kari! Duk sauran bayanai suka biyo.”

Rariya Hausa Matatar Gaskiya Karanta Labarun Mu

D’ago kai tayi tana kallon tana kallon Jakadiya. Gyara zama Jakadiya tayi sannan tace..

“Dama wata yar abu na gani nake son tsegumta miki! Uwar d’akina akan Jamal ne ko za a dauka mishi baiwar data manyanta”

 

Wani irin kallon ta mata sannan ta kauda kanta, kafin tace.

“Wa kike ga zamu tura?!”

 

“Rumanah!!!”

A hargitse ta wurga mata kallo sannan tace.

“Baki da hankali! Rumana kuma”

 

Gyad’a kai tayi sannan tace.

“Allah ya huci zuciyarki! Takawa baida lafiya! Kuma Shamaki shine akabawa rikon kwarya! Sannan Galadima yana da buri akan mulkin! Shine nake ganin idan da hali a fara koyawa Yarima Jamal sha’anin mulki, kafin lokacin da zai karbi kujerar shi, amma idan bai miki ba shi kenan! Allah ya huci zuciyarki na barki lafiya”

 

Har zata mike Fulani tace mata.

“Dakata! Me yasa kika zab’i Rumana”

 

Murmushi tayi a ranta tace.

*Ganin gida kare, yan zagi kura kin fad’a tarkonsu*

 

A zahirance kuwa tace.

“Sabida itace bazata iya cutar da jinin mai martaba ba, sannan zata kaunaci Yarima Jamal kar ya!”

 

Gyara Zama Fulani tayi sannan tace.

“Wannan shawararki ta hauka ce! Taya ina Mahaifiyarshi ya kaunaci wata”

 

“Allah ya kara miki nisan kwana! Domin cimma wata nasarar dole sai an sadaukar da wasu nasarorin! Idan kika amince wannan me sauki ne! Idan kika ki kuma tabbas duk wacce za’a kawo za a saye ta domin cimma kudirin su akanmu”

 

Jinjina kai tayi sannan tace.

“Kije zan nime ki”

 

“Ki huta lafiya! Allah ya tsare gabanki da bayanki! Hutawarki lafiya yar sarki jikar sarki, Uwar sarki matar sarki.”

 

Tafita Jakadiya tayi sannan ta sake murmushi tace.

“Fulani Hasiyah! Sai na lalata miki rayuwarki! Kamar yadda kika tab’a wulakantani, idan da rabon kura a takobi, sai a sayar a sayi akuya!”

 

Bayan kwana takwas Fulani Hasiyah takira Jakadiya ta faɗa mata ta amince, Amma bisa sharad’i kar wata doguwar alaka ta shiga tsakanin Rumana da Jamal.

 

Tun daga  ranar Aka kai Rumana Shashin Jamal take kula da duk wani abinsa, cikin so da kauna. Dan tana kewar Mai Martaba.

 

—–

_Bayan shekara sha shida(16Yrs)_

 

Abubuwa sun faru a cikin masarautar Daura! Wasu ma bazai iya fahimtar komai ba, tun bayan faduwar Sarki Jalaludeen, sai aka nad’a Kamin shi Shamaki wato Abdu

Tsugunne yayi gaban mai martaba yana mishi alola, yana idarwa ya kalli Mai Martaba cikin murmushi yace.

“Abba na gama maka ko zamu tafi”

 

Lumshe idanunshi yayi cikin jin dadi sannan ya motsa hannun shi, wanda akala kusan shekaru wani abu kenan yana zaune a gurin.

Dan lokacin da Jamal ya gama Secondry school ya bada shawarar a fita dashi waje, kuma akayi Na’am da shawarar inda aka fita da shi, sai dai babu nasara dan an tabbatar da cewa lafiyan shi lau.

 

Sabida lalura Mai Martaba Jamal yaki tafiya wata makaranta nesa da gida, yayi ƙoƙarin koya mishi abubuwan kamar idan yana son abu ya nuna da ido, ko da hannu. Na hannun ne ya gaggara. Tura shi yayi suka nufi masallaci, duk inda suka ratsa sai an zub’e domin mika musu gaisuwa, koda suka isa masallaci ya.

 

Bayan sun dawo gida Ya gyarawa Mai Martaba gurin zaman shi, har zai fita “Jamal!”

Ya kira sunan shi. Cike da farin ciki ya koma gaban shi ya durkusa dakyar ya iya d’aga harshen shi yace.

 

“Idan muguwar kaza ta shiga cikin akurki, kowacce kaza sai ta sare. Ban gaya maka haka dan karya maka gwiwa ba sai dai Sa’a tafi gata, ka zama me jin kai da tausayi. Sannan kaje gurin Magaji.”

 

Tunda Jamal ya fita yake bin bayan shi da ido.

_Rumanah! Kin tafi kin barni, da ace ki kika haifi Jamal da bazan zubda kwalla me yawa ba_

 

Gyad’a kai yayi sannan ya mik’e tare da barin d’akin jikin s

……

 

Duk abinda Mai Martaba da Jamal suka tattauna sai da Jakadiya ta kwaso tass sannan ta nufi gidan Galadima.

Tana shiga gidan ta fara kirari.

“Gafara dai nazo ganin Fari me farin aniya! B’auna saniyar sake! Turnuku kake, namijin zaki uban  namun daji!  Garnakaki kake kafin namijin zaki hatsabibanci! Gaba salama bayan salama”

 

Gyara zama yayi cikin izza ya kalleta, sannan ya d’aga mata hannu.

“Ina jinki”

“Kowa ya keta rigar tasa, yasan inda zare yake!”

 

Kauda kai yayi sannan yace.

“A bakin  tsoho fito keda daraja, ina jinki”

 

Sosai kanta tayi cikin munafunci tace.

“Ya tafi gidan Magaji”

 

Murmushi yayi sannan yace.

“Maganin biri, karen maguzawa! Kyaleshi Yaje”

Rariya Hausa Matatar Gaskiya Karanta Labarun Mu

“Gyara zama tayi sannan tace.

“Biri a hannun malam yake guɗa, a hannun bamaguje kuka yake”

 

“Hmmmm! Naji ance ana ganinki da Shamaki? Indai bazaki tsaya iya Ni ba toh bana bukatar duk wata tsegumi”

 

Karya wuya tayi cikin damuwa sannan tace.

“Ina ruga basu zauna lafiya ba, ai runji zama lafiya! Duk yadda kace shi kenan.”

 

Tana gama fad’ar haka ta bar zauren tana me bankawa kofar harara tace.

“Harbi ga dan jaki gado ne, dani kuke zance.”

 

—–

Tunda nayi wayo muke kara kaina da mahaifiyata! Daga nan sai nan, kuma munfi ratsa dazuzzuka! Yau ma a hannun wani mutum muka fad’a wanda yake janye damu ƙamar wasu dabobi, Fad’uwa Mahaifiyata tayi na kira sunanta da Karfi.

“Annah!”Dole ya tsaya zama nayi na  daura kanta akan cinyata, ina kallon shi, kwalla cike a idanuna nace.

“Taimaka mana da ruwan sha mana baka ga yadda bakinta ya bushe bane.”

 

Wurga min gorar yayi sannan ya koma gefe, sai da tasha sosai sannan ya kuma wurgo mana gurasa, jikina na rawa na bata, ta dan ci sannan nima naci.

 

“Zaku iya tashi dan saura kad’an mu isa masarautar Daura”

 

Haka na d’agata muka cigaba da tafiya.

 

Sai da muka yi tafiya sosai sannan muka shigo garin. Ta baya muka bi, bayan ya sunce mana daurin muka cigaba da tafi, dukkan dukkan shekaruna bazasu wucce sha biyar ba,

 

Kofar masarautar ya zauna ya kuma umarce mu  da zama, kwanciya Annah tayi a jikina tace.

“Junnuh karki tab’a cin amanar kowa ko a had’a kai dake aci amanar wani, Junnuh ki kare kimarki da darajar ki, Junnuh karki ɗaura idanunki akan abin wani! Junnuh duniya da abin cikin ta duk sha’anin ne na Ubangiji, Junnuh kiji tsoron Allah a cikin alamarinki. Banda karya indai ba dan ki wanke kanki bane, banda mugunta koda ke akawa kiyi ƙoƙari ki rama da Alkhairin! Junnuh abinda ya baki tsoro wata rana shi zai baki tausayi, abinda ya saki kuka wata rana shi zai sanyaki dariya! Junnuh Ban san duniyar da muke ba, amma karki manta ke Y’ace  mai daraja.”

 

Kuka nake sosai dan abinda Annah take fada min kamar wasiyya take bani,  taya zan rayu idan babu mahaifiyata.

 

Tawowa suke a cikin wata mota wacce lokacin babu ita sosai a kasar Hausa, sai gidajen sarakuna, tarin da Annah take yasani mik’ewa ina cewa mutumin da ya kawo mu magana, sai wayam na gani babu shi babu labarin shi, Ma’ana yayi tafiyar shi. Bakina na rawa nace.

“Annah! Ya tafi”

Tarin da take har dani, durkusawa nayi ina me rike da ita, nace.

“Annah karki tafi! Don Allah ki tsaya dani zan noma miki lafiya”

Daga nesa ya hango mu, musamman Ni wacce na birkice da kuka, ina girgiza Annah.

“Aswad! Shin me ka fahimtar da Abinda Baba Magaji yace?!”

 

“Yarima Jamal! Ni kaina Hausar ta min tsauri, Wai kar Ingarma ya rena gudun kura! Abin nufi karka rena abinda yake faruwa a cikin masarautar”

 

“Tsaya a can da alamu, ana niman taimako ne.”

 

Har sun wucce suka kuma dawowa, buɗe motar yayi.

Sautin kuka na ya sauka a kunnen shi, lumshe idanunshi yayi sannan ya buɗe a hankali ya sauko daga cikin motar ya iso inda muke kallona yayi sannan yace.

“Aswad! Zoka taimaka mu kaita cikin masarautar”

 

Da sauri na mike, tare da kare Annah, na d’ago kaina na sauke akan kyakyawar fuskar shi, shima Ni yake kallo.

Zuciyata ce tayi wani irin bugawa, lokaci guda. Sauke idanuna nayi daga fuskar shi na sunkuyar da kai na kasa dan ya cika min ido.

 

Har lokacin zuciya bata bar bugawa ba, tab’a gefena yayi shida abokin shi suka dauki Annah suka sakata a cikin motar so me kama da kunkuru.

 

Juyawa yayi ya kalle Ni, Sannan yace.

“Hmm! Muje”

Wani irin abu nake ji yana yawo akaina, lokaci guda na rasa nutsuwa ta, uwa uba jin muryan shi da kayan shi ya jefani cikin wata duniya na daban, me haka ke nufi dani, halin da Mahaifiyata take ciki zanji dashi ko da halin da na fad’a sakamakon ganin wannan me kyan, na shiga tara Ni Junnuh.

Lallai bahaushe yayi gaskiya da yace.

“Duk wanda ya koma rumbun sa, shi zai fad’i tsadar Toka”

 

Duk da kan Annah yana cinyata bai hana idan na d’ago kaina sai mun had’a idanun mu, da sauri nake….

 

_Afuwa daga nan bazan kuma posting ba, naga kamar baki so daga shi har Jan Parih, Amma zan cigaba dayi A Whatsp dan naga kamar can sunfi bin book din akan nan🙌🏼_

 

 

 

Oum-Muwaddah

[6/11, 12:55 PM] My Zahrah: 🌹🥀🌷

*ƘWARƘWARAH*

🌼🏵️🌺

”'{ITAMA MATAR SARKI CE}”’

 

_LOVE TRIANGLE♥️_

 

Mai_Dambu

Oum-Muwaddah

 

_Me Dambu karin maganar tayi tsauri bamu fahimta🤣🙄 Sha’anin gidan Sarautar Hausa Bakwai dole sai da Harshen damo! Insha Allah zan rage bawai zan daina ba! Kuyi Vote da comments Whatsp suna macen kokari sai dai ina son ku gane cewa Hausa itace yare na hudu a duniya! Bawai na fad’i haka dan komai bane dukda Hausa tana cikin jerin da 66 a yarurruka duniya! Amma a nan gaba dole zata doke kowace Yare! Idan aka saka Larabcin, English, French, sai Hausa ku nazarci magana ta Ni Bahaushiya ce gaba da baya kuma ina Alfahari da haka! Turanci bazai kaimu ko ina ba! Kuyi kokarin bibiyar karin magana dan kar muje inda za a kiramu gwarawa😍😍😘😎_

 

3️⃣

 

Tsigar jikina ne ke mik’ewa, a hankali na fara ambaton Allah, har muka shiga cikin masarautar  can wani guri na daban suka kai mu sannan suka tsaya.

Fita d’aya yayi shi yana cikin motar, hannun shi na d’an buga jikin motar. Can sai gasu tare da wata babbar mata, tana zuwa ta kalle Ni cikin sakin fuska.

“Ke zaki iya fitowa!”

 

A hankali na fito matar da me tuka motar ya taimaka mata suka fitar da Annah, can suka tafi da ita, ina tsaye kamar doluwa.

Sai da mutumin ya dawo yace.

“Eh baki biyo mu bane! Muje na kaiki inda Mamanki take.”

 

A hankali nake takawa har muka kule, ji nake Kamar na juya na kalle shi amma munyi nisa, wani daki aka kai mu, inda yake cikin wasu manyan dakuna, karasawa nayi inda Annah take, tana kwance. Zama nayi ina kallon fuskarta da tayi fayau.

 

Rike hannunta nayi kwalla na zubo min.

“Matsa za a dubata.”

 

Matsawa nayi gefe can, duk wata kulawar da take buƙatar anyi mata, amma no any holp.

Ina ji ina gani jikinta ya kuma birkicewa, har me dubata ya mike ya fita, cusa kai na nayi cikin cinyoyina ina gigitaciyar kuka.

“Ke dalla kiwa mutane shiru kinzo kin addabi mutane da kuk.”

 

Shigowar shi tare da mutanen da suka kawo da abokin tafiyar shi yasata shiru ta fara kirari.

“Lafiya zaki! Namiji uban yan boko! Giwa me tafiyar kasaita! Uba a gida Uba adawa! Lafiya Sarkinmu na gobe Yariman na yau Allah yaja zamanin Yarima Jamal.”

D’aga mata hannu yayi sannan ya kalli Likitan yace.

“Dr meye matsalar!”

 

Gyara tsayuwar likitan yayi sannan yace.

“Wallahi birkicewar da numfashita yake shine abin tashin hankalin, kowani lokaci zamu iya rasata”

 

Kwalla kara nayi na rarrafa zuwa inda take na rungume kanta, nace.

“Don Allah! Karku ce min zan rasata, wallahi ita d’aya gare Ni ban san kowa ba sai ita, idan na rasata zan iya shiga wani hali bani da kowa sai ita”

Fita suka yi can sai ga wata mata sun shigo tana gaba yana Binta a baya, cikin tsantsar girmamawa.

Zuwa tayi inda nake ta janye hannuna daga jikin Annah tace.

“Muje!”

“Don Allah!”

Yatsa tasa a bakinta, sannan tayi magana kasa kasa tace.

“Ke mace ce! Bai dace kina d’aga muryarki a gaban kowa ba, sannan wancan me sanye da zuleka da kaftanin Yarima ne, kuma idan kika cigaba da damun shi  zai iya sawa a hukuntaki, muje.”

 

Haka muka fita ina waiwayen Innata, hawaye na zuba min, har muka ficce a dakin, jingina yayi da jikin bangon, ya zuba mata ido sannan yace.

“Yanzun meye tunanin ka akan halin da take ciki?”

 

Gyara tsayuwar likitan yayi sannan yace..

“Ranka shi dad’e! Zan kira abokina ko Allah zai taimaka ya mana wani abu.

 

Fita suka yi bayi mata manya da yara sai zub’ewa suke a gaban shi suna kwasar gaisuwa. Hannu kawai yake iya daga musu, sannan ya isa wani madaidaiciyar daki yayi sallama, fitowa matar tayi ta barni. Can kasa da murya yace.

“Umma! Kice karta dami mara lafiyar da kuka”

 

“Toh! Ranka shi dad’e”

Duk sai yaji wani iri duk lokacin da magana ta haɗa su toh tana bashi wani irin girma ne na daban shi kuma a nashi bangaren a Uwa ya dauketa baya jin dadin kiranshi da take yi a Yarima. A hankali ya juya tare da barin kofar ta ya fita daga katangar bayin.

 

“Tashi ki je! Karki yi kuka ki mata addu’a Allah zai bata lafiya kinji Y’ata”

 

Gyad’a kai tayi sannan ta juya ta bar d’akin.

 

…….

Shiga Zauren Umma Fulani yayi ya sami Jakadiya tayi tsamo tsamo, kamar wacce aka zuba mata ruwan zafi.

 

Wani irin kallon ya bita dashi wanda yasata mik’ewa zata bar zauren, cikin muryan shi ne sanyi yace.

“Dawo!”

 

Yadda yayi maganar Ita kanta Fulani sai da ta kalle shi, balle Jakadiya.

“Tuba nake! D’an Sarki jikar Sarki, na tuba Saraki bazan kuma ba, a yafe Min laifina.”

 

Bai kalleta ba ya nuna mata hanyar fita, da sauri ta fita har tana tuntube.

 

Zama yayi bai ce komai ba itama Fulanin bata ce mishi cikanka ba, sai da ya mik’e zai fita tace.

“Yarima! Yawan shekaru ba shine wayo !”

Ita Fulani tana nufi me yasa zai yi abu bai sanar da ita ba,

Rariya Hausa Matatar Gaskiya Karanta Labarun Mu

Dawowa yayi ya zauna cikin damuwa sannan ya gyad’a mata kai yace.

“Afuwa! Umma na, bazan kuma ba Insha Allah.”

 

Bata kuma kallon shi ba.

“Kafin kowa sanin guntun goro yafi, katon dutse”

Sannan taya zai danganta alamarin ga wata ba ita ba.

 

Shiru yayi cikin jin haushi amma dole yayi Hakuri dan yasan wannan aikin Jakadiya ce,

Shigowar Jakadiya ta zub’e a gaban shi tare da cewa.

“Takawarka lafiya, Ga Aswad a waje yana jiranka”

 

Kallon Umman shi yayi sannan yace.

“Allah ya hucci zuciyarki! Baza a kuma abinda zai fusata ki ba.”

 

“Hmm! Umma! Umma biyu amma umma d’aya tafi su.”

Ni dai nice Mahaifiyarka, babu wata bayana,

“Tuba nake! Allah ya huci zuciyarki.”

 

Fita yayi yana kuma jin dole ya takawa Jakadiya birki, dan ya gama fahimtar.

 

Yana isa gurin Aswad, ya kura mishi ido.

“Akwai matsala! Dan matar kamar ta rasu, itama Yarinyar tana can cikin wani hali.”

 

“Ta rasu ne ko kamar ta rasu?!”

“Muje dai mugani”

Suna zuwa likitan na fitowa shi da abokinsa.

“Kuyi hakuri! Matar ta rasu”

 

Wani gigitaciyar kuka Junnuh ta saka tare da nufar dakin, ta fad’a kan gawar Mahaifiyarta.

“Me yasa? Wacece Ni? Me yasa baki gaya min komai ba?”

 

Shiga wasu mata suka yi aka fito da ni, sannan suka kai Ni d’akin matar nan, kuka nake naji jiri ya kwashe Ni a gurin,

 

Bayan wasu lokuta na farka, ina kallon dakin, a hankali abinda ya faru ya shiga dawo min.

Mik’ewa nayi na zauna kamar wacce aka tsikare da allura na fito daga dakin, kowa sha’anin gabanshi yake, rab’ewa bango nayi na nufi dakin matar da aka saka Innata na bud’e zan sakai naji tana cewa.

“Dole! Na dakatar da Rumana, sannan shima Yarima dole nasan abinyi akanshi”

Rariya Hausa Matatar Gaskiya Karanta Labarun Mu

Tura kai nayi nace.

“Ina Innata take.”

Kallona tayi sannan tace..

“Taje lahira koyar sallama! Maza fice min a d’aki”

 

Da sauri na fita, kallon Jakadiya tayi sannan tace.

“Jakadiya! Ya zaki yi da wannan Yarinyar.”

 

“Wacce kenan?!”

“Wannan da tashiga mana! Kinga abinda na samu a tsumokarar uwar! Sannan wannan hatimin wata.”

 

Karba tayi tana juyawa sannan ta duba cikin tsumokarar, tasami wani abu da suka danganci Junnuh amma dan bakar mugunta, suka kasafta kayan tsakaninsu.

 

Komawa daki nayi na Zauna, tare da fashewa da kuka.

 

Ina cikin kuka Matar nan ta shigo, gani ina kuka tace.

“Subhanallahi kuka kuma! Ki tuna sallah?”

 

Girgiza kai nayi cikin shashekar kuka nac.

“Banyi ba”

 

“Tashi maza kiyi ga buta nan! Ban daki yana can gefen”

Haka na fito daga dakin nayita kallon yadda suka rayuwar su nayi, a hankali na wuce na kama ruwa sannan na fito.

 

 

 

—–

Abinci ya gama bawa Abban shi, sannan ya kalle yadda Jamal din yake cikin damuwa.

“Jamal!”

 

D’ago kan shi yayi yana kallon Abban shi, Sannan ya mai da kanshi kasa.

“Akwai matsala ko? Sannan baka gaya min abinda Magaji yace maka ba.”

 

Gyara zama yayi sannan yace.

“Abba! Abinda yace min gaskiya bazan iya ba! Abba Ni bana son sha’anin mulki da abinda yake cikin ta, bana son rayuwar da batawa bace.”

Rariya Hausa Matatar Gaskiya Karanta Labarun Mu

“Ta yaro kyau take bata karko.”

Dama yasan haka zai faru dan tun tashin Jamal bai damu da sha’anin mulki ba, gwara Jamala, ita kan tana son mulki da abinda yake cikin ta, ita badan mace ce ba, da babu abinda zai hanata zuwa hawar sallah wato itama ta hau doki.

 

Abinda Ya sani dole Jamal ya zama sarki.

 

“Shi kenan tunda baka son mulki! Idan nayi lissafi daidai shekaru ka 25, kuma iya kwalejin gwamnati kimiyya da fasaha dake Katsina kayi, ko dan degree nan babu. Iya rayuwarka kana yinta ne saboda Ni, zan baka sako zuwa ga mataimakin shugaban Jami’ar AHMADU Bello kaje kaima samu ilimin da zaka kwaci kanka a hannun Jama’a.”

 

“Abba idan na tafi waye zai kula da kai! Don Allah kabar maganar tafiya ko ina nan”

 

yayi maganar kamar zai saka kuka.

“Kai ko kunya baka ji ba! Jamalah ta gama jami’ar ta, yanzun tana bautar ƙasa kai kana nan a gida kuma kace baka son mulki”

 

“Shi kenan, Abba na! Amma akwai wata nauyin da na d’auka na, kuma zan tafi nabarta.”

 

Kallon shi yayi sa’annan yace.

“Wacece ita?!”

 

Nan ya zauna ya bashi labarinta, sannan yace.

“Abbana! Mahaifiyarta ta rasu! Ban san me zan iya mata ba, kuma ina tunanin Yarinyar bata san daga inda suka fito ba!”

 

Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace.

 

“Wato tsuguno bata kare ba, an sayar da kare an sayi mage, kenan saboda ita zaka hakura da tafiyar kenan?!”

 

……..

*_Insha Allah nan gaba kadan zan ajiye rubutun sabida Azumi musamman Parih! Amma wannan Book din zan cigaba ba lokaci zuwa lokaci zaku nan samun Update a amma sai irin da asuba haka zakuna samun Update sai naji Ra’ayin ku_*

 

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!