Hausa Novels

Rashin Uwa Ne Sanadi Hausa Novel

Rashin Uwa Ne Sanadi Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: RASHIN UWA NE SANADI

 

(TRUE LIFE STORY)

 

TSARAWA DA RUBUTAWA SALMEERT (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE

 

 

ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

 

(BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM)

 

 

 

PAGE 1-5.

 

 

 

 

 

 

“””””””””””””””””””””””””””””Wayyo Allah na, dan Allah Aunty Asabe, ki yi haƙuri, Wallahi Ummata ce bata, da Lafiya ga ta can kamar zata mutu, ki taimaka min mu kaita Asibiti, wallahi ta na cikin wani hali”, ta fada ta na kuka sosai kamar ranta zai fita.

 

“Ai sai dai ta mutu, dama abinda na dade ina buri kennan, na kashe kuɗi har ban san iyakarsu ba sai gashi a karin banza zata tafi, ahaaaaye, Nanaye”, ta fada da shewa tare da taɓa hannu.

 

 

“Dan Allah, to ko wayarki ce ki taimaka min da ita na kira Abba, dan Allah ki taimakeni kar na rasa Ummana,” ta fada ta na rike gwuiwowin ta tare da rokonta.

 

 

“Mtsewwwww dallas tashi ki bani wuri, na fada miki yau Uwarnan taki Ajalinta ne ya yi”, ta fada ta haurinta, ai kuwa ta sameta a hanci.

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

ba ɓata lokaci jini ya shiga tsiyaya a hancinta, ganin jinin yasa ta kara ruɗewa, da yake yarinya ce sosai, hakan yasa gaba daya ta tsani ganin jini ko kaɗan a jikinta.

 

 

 

da rarrafe, ta kara wurin wani matashin yaro da ke zaune ya na binta da wani mayan kallo wanda da ka gani ka san, bana Allah da Annabi ba ne.

 

 

“Dan Allah, Yayah ka taimaka muna, ko Yah Saleem ne ka kira man”, ta fada tana hawaye sosai.

 

 

kallon Mahaifiyar ya yi, da take zaune tana duba wani magazine da ke hannunta, ganin bata kallo ne yasa , yasa ya kara kallon Yarinyar sosai kafin kasa-kasa, ya ce “ooooh Sorry, daina kuka beauty, zan kira miki shi amma har sai kin yarda zaki bani, na sha”, kallonshi tayi da rashin fahimta, tare da ce wa “bangane mai kake nufi ba?”.

 

 

 

ta fada idonta tab kwallah, wani makirin murmushi ya saki, kafin ya rankwafo dai-dai kusa da ita, ba tare da sanin abinda zai aikata ba kawai, taji ya shafi kirjinta da ko ƙirgan dangi ba wani sosai ta fara ba.

 

 

 

da sauri ta matsa baya, tana kallonshi, daga kafaɗa ya yi, alamar zaki iya tafiya in bakya son taimakon.

 

 

 

 

har ta tashi, ta tuna halin da ta baro Ummarta ciki, na irin tsananin bukatuwar taimako da ta ke yi.

 

wasu hawaye ne, masu zafi ta ji sun sulalo mata, masu ɗumi sosai, juyawa ta yi ta kalleshi, wani irin lumshe idanunshi ya yi, yana lasar lips dinshi.

 

 

 

da sauri ta fice daga parlourn, part dinsu ta koma, anan ta samu Umma sai aman jini take, ga idanunta har sun fara kakkafewa, Alamar rai na niyyar yin halinshi.

 

 

 

da sauri ta karasa cikin parlourn tana cewa, “Umma! Umma!! Umma!!! Umma!!!!, ki taimakamin karki tafi ki barni, ke ce kawai gatana, Umma kar ki tafi ki barni, in kika tafi ban san yanda zanyi ba”, ta fada ta na kuka rurus.

 

 

 

baki ta shiga motsawa da alamar ta na son tayi magana, amma ta kasa, ita kuwa Awwa yarinya ce sosai ba ta san ta kanga kunnenta taji mai take son fada ba, sai jijigata da ta ke yi.

 

 

 

dai-dai shigowar wani Matashin yaro mai matuƙar kama da yarinyar , Umman ta fara shakuwa, jin shakuwar yasa ya kara yin sauri, tare da nufar inda yake jiyo kukan tare da shakuwar.

 

 

 

ya na karasawa gurin, tayi wata iriyar miƙa tare da salati, an kuwa rai ya yi, halinshi ta ce ga garinku nan, da Azabar sauri ya kara, gurin tare da fara kiran “Umma!, Umma!!, ki tashi mana” ya fada yana daga , hannunta, amma yaraf hannun ya koma, alamar da an gama komai.

 

 

 

ɗagowa ya yi, yana kallon Kanwar tashi da take, kallonshi hawayen ma sun daina zuba a idonta.

 

 

 

girgiza kai kawai, ya yi a razane ta saki wata kara, tare sa faɗi a sume.

 

 

 

a ruɗe ya tashi, tare da nufar part din Aunty tasu, yana shiga ya zube kasa kan carfet, tare da sakin wani marayan kuka mai tsuma zuciya, sosai yake kukan har numfashin shi hana wani shidewa.

 

 

 

wata Mahaukaciyar tsawa ta daka mishi tare da cewa, “Uwar mai zaisa kazo nan kanamin kuka, banason iskancin banza, tashi ka bani guri “, ta fada a tsawace.

 

 

“kiyi hakuri Aunty Um…..”, sai kuma ya kasa ƙarasa fadar abinda zaice, sakamakon kukan da ya kara ƙuɓuce mishi.

 

 

“Wai shin, nina daura mata, ciwan ne da zakuzo kunamin makoki, a daki, to wallahi ku tsaya kuji, bazan taɓa taimakawa wannan Uwar taku ba, ai tunda ta yi sanadiyar kuntatawa, rayuwata har tayi nasarar, shigowa gidan nan har ta haifeku, to wallahi bakuma ga komai ba, mu zuba ni da ku”, ta fada tana hararar shi.

 

 

 

girgiza kai ya yi, tare da ficewa a part din, direct Masallacin Unguwarsu da ake Sallar Asr , ya nufa bayan an Sallame sallar ya fada musu rasuwar Mahaifiyar tasu.

 

 

 

 

cike da jimami duk , suka tsatsaya, suna Sallalami, fita ya yi daga Masallacin.

 

 

gidan wata tsohuwa da suke matukar mutunci da ita ya nufa, sanar da ita ya yi, a rude ta nufo gidan, abinda ta gani ya tada hankalinta.

 

 

 

da sauri ta dauki ruwa a fridge tare da fesawa Hamideert da take, kwance itama a sume kamar gawa.

 

 

 

da kuka ta farka tana kiran “Ummana! Umma!! karki tafi ki barmu”, ta fada da kuka.

 

 

 

hawaye suka zubowa matar, sharewa tayi, kafin ta nufi kitchen , ruwan zafi ta hada tare da zuwa ta farawa gawar wanka, kafin ta gama har Saleeem ya ajiye Likaffanin da za’a shiryata da turaruka.

 

 

 

 

cikin minti kaɗan ta gama shiryata, bada jimawa ba wani mutumi ya shigo a mugun rude, ba inda ya tsaya sai a gaban gawar.

 

 

 

cikin kuka ya fara magana yana cewa”…………….

 

 

 

ƳAR LELEN ROYAL STAR CE

Leave a Comment

error: Content is protected !!