Hausa Novels

Rayuwar Ameera Hausa Novels

Rayuwar Ameera Hausa Novels

 

 

 

 

 

 

 

 

*RAYUWAR AMEERAH*

 

By

Mrs bb

Mom muhseen

 

Wattpad name

Humaira3461.

 

DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAI“`

 

 

 

 

 

*page 1*

 

 

Kuka takeyi kamar ance Mata yau zata mutum Don duk Wanda yake sauraren Mai irin wannan kukan saiya tausaya mata, saboda dakaji

Kasan tanacikin kuncin zuciya kasan kukan bakin ciki maitarin yawa.

 

Wata ce kusada ita itama fuskar ta tabaci da ruwan hawaye, zakace yayar Mai kukan ce Amma kuma diyarta.

Dagota tayi tazaunar kusada ita tana goge Mata hawayen yayin da itakuma nata suke zuba kamar ruwan fanfo.

 

Cikin muryanta tana kerma tace” *Ameerah* saunawa zance kikulle kunnenki daga sauraren irin maganganun da akeyi akanki nagaya maki watarana sai zuciyarki tabuga saboda biyewa maganganun mutanen da dama jira akeyi, idan kikabiye kuka tsaf hawayenki zasu kare.Allah baya bacci kicigaba dagaya mashi babu dare babu rana cikin yi nake nasan kinayi kicigaba dayi, duk Wanda kikaji ance yayi hakuri baici riba bah to *Ameerah* baiyi dayawabah kiyi hakuri kisaka dangana cikin Al,amurran rayuwarki komi lokacine insha Allah watarana kukanmu zaizama dariya…..”

 

 

Na tsani Yariman Yusuf Hausa Novels

Ajiyar zuciya kawai takeyi saboda kukan datasha cikin muryanta datashake bata fita sosai,

“Tace Mama ni bakomi ne yake sakani cikin damuwaba irin shegantani da akeyi duk sadda nafita ko naje makaranta wallahi mama da tabon wannan kalmar nake dawowa, shin wai dagaske banida uba mama meyasa kinkasa sanar Dani Ainahin tarihin rayuwarmu.”

 

“Kullum idan natanbayeki saikiceman inyi hakuri bayanzu bah idan bakigayaman yanzu bah sai yaushe mama,kingani zaman aure yagagareni saboda wannan yana daya daga ciki, mutanen gidan nan kullum bakinsu akan *AMEERAH* yake duk wata sharar dasuka kwaso akaina, shin menayi menatarewa wani ne acikin rayuwata mama kingani saboda irin wannan ko kawa banda, duk wadda tarabeni sai ansamu masu rabani da ita nikenan haka zankare rayuwata banda damar rabar kowa…”

 

 

“kinagani nan kanwata da kanena sukansu mesuke fada kaina kinaji dazu irin bakar maganar da hindatu take fada akaina, babansu yana kawo abinci dan su Amma nafisu zakewa wajen cika cikina har nayi guziri natafi dashi makaranta,

Kanwata comon imerging to su sunman balle wadanda zaman haya yadani dasu saifah matan mijinki….”

 

 

“Don Allah *Ameerah* kiyi shiru haka nan kiyi hakuri insha Allah komi zaiyi sauki….. Cikin sabon kuka tace yaushe abubuwan zasuyi sauki ehy mama kigayaman yaushe ne… Mijinki na aibatani matansa ban tsirababa,ga yaranshi ban tsirabah haka ga mutanen gari shin inazanshiga inji dadin rayuwa ta ne ehy banida damar rabar mutane mama,

Aurena dai dai dai har uku babu inda nake yin shekara ansakoni…ko Ina da irin bala,in danake taddawa shin so ake inyi bindiga infashe kowa yahuta ehyy…..tacigaba da wani irin kuka Mai tada hankali don ita kanta mamar rungumeta tayi suka Kama kukan tare babu Mai lallashin wani cikinsu….

 

 

“Muryanta tayi wata irin shakewa tace *akan ka akeman duk irin abunda yakefaruwa a rayuwata ko koma waye kai idan harkana raye bazan fasa yimaka fatan tozarcibah yanda ake man wala gigi darayuwa kaima ubangiji yasa taka rayuwar tayi haka NATSANEKA NATSANEKA BABANA BAZAN TABAH YAFEMA BAH”*

 

 

Rufemata baki tayi dakarfi don karda kishiyoyinta sujisu, don yanzu ayi taro dansu “Ameerah kirufa mana asiri kiyi shiru karkitara mana jama,a anan kinagani kadan akejira ko”””

 

 

“kikyaleni kowama yaji wallahi bazan yafemai bah tunda har yabarni cikin irin wannan rayuwar, sai kuka wiwiwi”

 

*Ameerah* tadade kafin ta lallashi kanta tayi shiru,

Sai ajiyar zuciya takeyi zuwacen bacci yadauketa mamar tagyara Mata kwanciya saman dan gadon da katifa bata wadace shibah.

 

Takalli yanda fuskar tayi jajir dan kuka tace”yah Allah ka rangwanta wah bayinka wannan *rayuwar* hakika muna cikin jarabta kakawomana karshenta lapia kasakawa *Ameerah* hakuri da dangana acikin zuciyarta”

 

 

“Tabbas *ABDULLAH* Adduar *Ameerah* saita tabbata kanka don Allah baya barin hakkin wani kan wani kuka insha Allah da sannu zaka gane kuskurenka yadda katozarni da yarka Allah bazai barkaba wallahi mujezuwa lokaci nayi”

 

 

*Ameerah* tadade tana bacci don batayin nadare saboda karatu exam takusa baifi kwanaki takwas bah,

Mama tafita don dora sanwar rana kasancewar itace da girki agidan.

 

Duk suna cikin harabar tsakar gidan daga Mai barar gyada saimai dinki yaran kowace suna tayata.

Mama takama kokowar hura huta saidai abun bakin cikin ansamu wani daya zubawa murhun ruwa yayi sharkaf,

 

Dariya tajiyo duk sunkwashe da ita yaran kishiyoyin,

Sukau babu wadda takula tah aikin gabansu sukeyi…

Wani yaro murtala yace”wallahi bala dan iskane inaganin sadda yasawa murhun ruwa yafito daga bayi.. Yacigaba da dariyarshi sauran suna tayashi.

 

 

“Cikin bakinciki mama tace haba murtala kuma kaganshi maimakon kahanashi yanzu kagani dole zakuyita jiran abinci ko…”

 

“Akanme zanhanashi uwani wallahi cewama nayi yacigaba don kinbani haushi jiya sosai”

 

Uwar yaron tanajinshi yana tsula rashin kunyarsa Amma ko tak batace mashiba,

Haka mama tashiga aikin gyaranshi tasamu tagama kafin maigidan yadawo idan ranta yayi dubu saiyabaci.

 

 

Tana cikin aikin hindatu da musty sukashigo,sai dariyar su suke abunsu babu sallama balle gaida uwarsu dake duke tana faman shan wahala..

Bakin kofa Hindu tazube “washh Allahna mama wallahi yunwa nakeji wai haryanzu bakiyi komibah tsakani da Allah kina kwararmu munshawo wannan uwar ranar mudawo bakima dora sanwar bah ko”

 

Kamar tanajin tsoranta tace”haba Hindu bakiga aikin danakeba, ai saiki ajiye abayarki kizo kitayani bawai kikama man surutubah”

 

“wah wai ni Wallahi mama bazan iyaba keda yazamarwa dole saikiyi tafama, nidai aibazan rasa nasawa ga bakinaba”

 

Tamike tashige dakin”musty jeka waje samoman ledoji kajiko insamu wutar tatashi”

 

“Mikewa yayi shima yayi wata irin mika tareda hamma yace Allah yakiyaye ni musty yashige shima”

 

Laure Mata tabiyu agidan takwashe da dariya tace Ahab dankima kenan sunmaki balle wasu dabakida iko dasu Allah yakara badai kin ce dole sai mijinmu bah mujezuwa ba,ayi komiba”

 

Idon mama yacika tab da kwallah taduka tacigaba da aikinta,

Kamar anjehota tafito daga dakin datake tafita tayo yaye yayen ledoji dadai makashin wuta tadawo saidai mamar taji anjanyeta gefe taduka tafara hada wutar

Kankace me wuta tatashi tadauko tukunya tadora tazuba ruwa tarufe…

 

Tajiyo ga mamar tace”kije daki Zan maki mezaku dafa ne”

 

“Idonta nafitar da kwallah tace shinkafa ce kwano daya sai wake shikuma rabin kwano,sai tashshi daza,a daka”

 

 

“Mama kije insha Allah duk zanyi KO jekihuta,”

 

Laure facet”aikin kashi anan kadai zaki iya sharemata hawayen daga haka babu kari”

Basuce Mata komibah mama tasamo kujera tafara dakan yajin *Ameerah* kuma tacigaba da gyaran waken don ruwan yasoma yin zafi bakaken maganganune kawai suketa fada akansu Amma basuce dasu komi bah.

 

Hindu tafito da tabarma tashimfida takoma tadauko wata leda yar babba haka,

Musty yana kusada ita tace dan kane taimakeni daukomana wajen dazamu juye naman.

Yako mike yaje yadauko ya akawo namane Mai sunan nama mairai da lapia,

Balango yasha suya dan banzan nan yacika plate din da musty yakawo sai maltina da gwangwanin peak taruwa ga pure watar nan maishegen sanyi har wata zufah yake dan sanyi.

 

Yaran gidan duk sun zagayesu kowa yayi tsugunni kamar almajiri yana jiran acemai anshi,

Murmushin mugunta hindu keyi tace wallahi yau ko miyanku zaikare dan maita sidin takadda babu dan isakan dazanbah,

Shegu kunsan kuga abun mutum kuzo kuyita lashe baki Amma bakujin kunyar yiwa uwata rashin kunya ko.”

 

 

“Zakutashi kuban waje kosaina daukeku da marirrika musty yace kyalesu kigani wani katon icce yadauko yace idan nadawo bakubar wajenbah saina sabauta Ku yan iska”

 

 

“Cikin hayagaga laure tace wallahi mustapha idan kataba man yaro saina makantaka billahil azim karkafara, dan uwarku aiku sukaga kunayi shiyasa sukeyi”

 

“Hindu tace to uwarsu ce ko tamu kemeyasa bazasuyi makiba oh saitamu dakowa yaraina to zandauki mataki babba wallahi bari baban yadawo duk saiyaci ubanku”

 

 

Ameerah da mama aikinsu sukeyi babu Wanda yace kala haka hindu da musty suka zauna sunacin wannan naman suna korawa da maltina babu Wanda suka ba,

Cewa take idan mutum yaji haushi Yatashi yanemi nakanshi nima gumina nane nan shiyasa saiwanda nakeso zanbah dagani sai dan uwana uwa daya uba daya ehee ko musty yace sosai kuwa yar uwa,idan kaji haushi kafita kayi bara kila kasamu sidin kwano suka kwashe da wata irin dariya babu Wanda yace komi,

 

Laure jitake kamar takamasu dabugu saidai tasan malam bazai daukabah don idan akwai abunda yatsana kenan atabamashi yara, don duk manyan dasuke gidan bayajidasu irin yadda yakeson su hindu da musty saboda yace haihuwar su ce takawo mashi aikinyi donhaka har abada sune asama yafi fita su fiye dakowa shiyasa suke taka duk Wanda sukeso cikinsu Kuwa harda wadda tahaifasu.

 

Ameerah bata gama sanwar bah sai anakiran la,asar daidai dawowar malam garba,

Godiya mama tayi tayiwa Ameerah don daya yanzu yafara cimata mutunci kowa saiyasan halindasuke,

 

Anraba anbawa kowa Amma wadda tasha wahalar koloma batasamu bah, don yace duk randa tasake cimashi abincin gida wallahi saisubar mashi gidan itada uwarta. Shiyasa ma batasaka raibah duk yadda mama taso ta anshi nasu hindu tunda sunce basuci cewatayi tayafe zataje gidan inna baraka taci.

 

“haba Ameerah yazakiyi sanwa dakanki Amma kuma kiharamtawa kanki ita totunda bazakici nasubah niganawa kici tunda bakin zauna da yunwabah,”

 

“Mama bani naharamtawa kaina bah mijinki shiya haramtamun kuma kinasane daduk irin matakin dazai dauka akanmu, yace badani yake neman abincinshi bah don yaranshi niba yarsa bace banga laipinsa dan yahanani abincin saba, wallahi dadai nadauki abincin nan naci gara yunwa takasheni wallahi don kinsan dacewar cin abincin su hindu kamar nasiyowa kaina bakinciki ne, da nasaurari kalaman bakinsu gara nasaurari kukan da cikina keyi, zanje wajen inna baraka nasan yanzu zatafara toya awara inada hamsin zansiya acen naci…….jisukai kawai hindu tana cewa,

 

“Yafiye maki alkairi don wallahi dakin cishi saikinyi amanshi don dadai nabaki kasona agidan nan gara banabawa kare kinsan kare daiko toshi zanba, mtss mutum sai matattar zuciya shibaga zaman aurebah shubaga kasuwanci bah babu wani abun azo agane kinkalewa uwarmu kina bata wuya… To ko yawon iskancin dakike fakewa kinacewa makaranta kikezuwa bkismo ko sile kashh Amma Anci baya ke barikinma taki under Mikey………..cikin tsananin tsawa wadda tunda suke agidan babu Wanda yatabajin Ameerah tayi tace *ya ishekiiii idan kikasake furta kalma guda tabatanci gareni wallahi saina sabaitaki sai ankasa ansarki gabada asibitocin katsinaaaa*

 

Shiru kaji gidan yayi kamar anyi mutuwa, mama runtse ido tayi tadafe kunne yayinda hindu takame kammm tayi huking don bilhakki dagaskiya tatsorata tayi tunanin zata bude ido taganta kwance sumamma don yadda Ameerah ta daga hannu sama kamar zata mareta…. Numfashin Ameerah sai sama dakasa yakeyi kamar zaifice,

 

Fit hindu tabar gidan don wallahi tsoro takeji irin wannan zuciyar ce idan mutum yyayi komi yana iya aikatawa,

Mama tana share hawaye tarungumeta tana lallashi don har yanzu numfashin baidawo daidai bah.

 

 

Zuwacen kuma sai yadauke daf jikinta yasaki,

Mama wata irin bugawa kirjinta yayidon ganin halin datake ciki tafara girgizata

“Ke Ameerah miye haka karkiyiman haka mana kitashi wallahi banshirya rabuwa dakebah, wayyo Allah na yah Allah narokeka kaka woman dauki inazansa

*rayuwa* ta innalillahi wa inna ilahir raju,un

 

 

 

*MAMAN MUHSEEN CE*

 

 

*LOVE U FANS*

 

 

*PLS COMMENT AND SHARE*

Leave a Comment

error: Content is protected !!