Rayuwar Nafisat Hausa Novel

Hakurina Ya Kare Hausa Novel Complete

Rayuwar Nafisat Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: RAYUWAR NAFEESAT

 

 

 

 

 

Written by

Zahra Amg

 

 

 

Sabon littafi mai dauke da darasi ban tausayi zalincin soyayya

 

 

Marubuciyar littafin

 

 

NI DA YAYANA

 

 

 

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin k’ai tsira da aminchi su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W) da Alayansa da sahabbansa baki d’aya.

 

 

 

 

 

Page:1

 

 

 

 

 

“Nafisa! Nafisa!! Nafisa!!!”

wata kyakkyawar dattijuwar mata ce, ke kwala ma wata yarinya kira bak’a ce wuluk ga wargajejen baki hakoranta duk kalar goro, dan kiran yarinyar take tana jijiga jiki da gudu wata yarinya ‘yar kimanin shekara goma sha biyu, ta fito daga wani d’aki cikin rawar jiki ta fad’i gaban wannan matar bazato ba tsammani taji saukar icce jikinta ana dukanta “Dan ubanki ubanki ne, zai zo ya wanke min kayana ko uwarki da ta banzatar da ke, ta tafi yawon karuwanchi shegiya mai kama da Aljana, uwarki ta tafi karuwanchi ta barni da ‘kaya” jibgar ta take tana aibata mata Uwa tin Nafisa Na iya kuka ana jin muryarta har ta kai muryarta ta dashashe tana ga ma dukanta da iccen nan ta watsa mata, ruwan sanyi a jiki firgigi ta farko daga sumar da ta yi, sakamakon wani zugi ta ya kawo mata ziyara ruwa ne mai ‘Dan Karen sanyi ga shi anzuba gishiri a ciki mugunta matar nan take kalon yadda duk Nafisa ta rud’e tana kiran “wayyon Allah baba ladi kiyi hakuri zan wanke ki cire min wannan zafin da kika saka min” kuka take fil hakki, ita kuwa ladi tana tsaye kanta tana murmushin mugunta domin Allah ya sani ta tsani, Nafisat ga wani kyau da take dashi kamar ita tayi kanta kishi take da ita kamar me, mikewa nafisa tayi tana tangad’i har ta isa gaban kayan wanki kaya ne tuli guda kamar jaka, haka baba ladi ta maidata ita ke wanke mata kayanta Dana ‘yar lelenta kubra haka ta fara wanki tana yi tana sharar hawaye ita Kuma ladi nata banbamin ta tashi ta shige d’aki haka ta wanke kayannan tas, kafin ta gama zazzafi yayi mata sallama haka ta d’aure ta kammala mata wanki, ta share mata, gida ta dora tuwon dare tana cikin aikin abunchi ta dinga kwarara amai………

 

 

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Editing

Shere

 

 

 

 

Written by

Zahra amg

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.