Hausa Novels

Rayuwar Nimcyluv a birni hausa novel

Rayuwar Nimcyluv a birni hausa novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*RAYUWAR NIMCY LUV  A BIRNI*

 

 

Short story

 

_Zainab Habib(Mom Islam_

 

 

 

 

Elegant online writers

 

 

Daga farkon littafin har ƙarsensa sadukarwa ne gareki NIMCY LUV kiyi inda kikeso dashi 😘.

 

 

Chapter 9-10

Na’ima na zuwa kan Audu mai gadi ta takashi tare da wucewa da gudu tana mai tuntsirewa da dariya , Audu mai gadi ya tsala ihu wanda yaja ankalin Zainab ta fito da gudu tana cewa “meya faru ?”

Na’ima dake tsaye tana dariya tace “koyon ƙarfi nake ”

A fusace Zainab tazo gabanta ta wanketa da mari ,kafin ta fara magana cikin ƙaraji.

“Walhi bari Alhji ya dawo bazan iya zama dake ba ,sam bakida tarbiya mai yasa zai kawomin ke ai saiki sakamin cutar hawan jini “Zainab ta karashe maganar tana nunata da yatsanta.

Baki buɗe Na’ima ke kallon Zainab ,a zuciyarta ko cewa take “idan kinsan wata ai bakisan wata ba ,wallahi kikayi wasa sai incewa babana zan auri yaya sai muga ta faɗi “wai tsutsa ta kada kuɗin cizo.

A fili kuma ta juya ta shige ɗakinta ta barsu a gurin.

4:11pm Na’ima na kitchen tana dafa indomie wanda aka juye masa mangyaɗa gwangwani biyu kuma indimien guda biyu ce ƙanana , a cewarta kowa yaci damai (kuɗinsa).

Ƙwai kuwa sai data fasa guda goma ta soya indomien gidan nata tashin ƙamshi .

Karin wasu littafai da zaku so

Zainab dake kwance a ɗaki kanta na ciwo ta taso sbda wani irin hautsinawa da cikinta keyi sanadiyar wannan ƙamshi da taji ,kai tsaye ta nufi kitchen ta sami Na’ima ta baje a kan tails tana uban zuba loma ,Zainab na shirin magana amai ya fara taso mata ta ruga da gudu hannunta rufe da bakinta ta shige toilet ,amai tayi sosai wanda yasa ta galabaita ,bayan ta kuskure bakinta ta fito hannunta dafe da kai ta zauna gaban mirror ta fara kuka….!

 

 

Mucigaba ko a’a ?

 

Mom Islam 08141799224

Leave a Comment

error: Content is protected !!