Hausa Novels

Rayuwata ce Hausa Novel Complete

Rayuwata ce Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

RAYUWATA CE!!

 

 

BY

Queen Ameerah…..🖊️

 

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

Sabon labari daya shafi wata rayuwa mai cike da son zuciya✔️

 

 

PAGE 1➡️2

____________”Ochhee” ya fada ya na lumshe ido, da sauri ta juyo ta na ce wa “Hilal lafiya” ciza lips ya yi ya na ce wa “babu komai” harararsa ta yi sannan ta gyara towel dinta ta shiga toilet, ya bita da kallo ya na sauke numfashi.

 

Leelah ce ta bude kofar dakin ta shigo ta kama kugu tana kallon Hilal, cikin fada ta ce “ina Moofeey” ba tare daya kalleta ba ya nuna mata toilet, ta daga murya ta na ce wa “wallahi Moofeey na gaji da jiranki tafiya zanyi na barku” daga cikin toilet din ta bata amsa da ce wa “please Leelah karki tafi” Leelah taja tsaki ta ce “na baki ten minutes ko ki sameni a can” ta juya ta fita ta na mita, Hilal ya bita da harara ya na ce wa “uwar fada”

Cikin sauri2 ta fito daga toilet din, ta kalli Hilal da ya ke mike saman gado, ta ce “yanzu Hilal baka fito min da kayan da zan saka ba?” Mikewa ya yi ya na ce wa “ay ke ce kika tafi kika barni da shock” murmushi ta yi ta ce “in dai ni ce ka hadu da shock” ta zauna gaban dressing mirror ta na shafawa shining skin dinta lotion, shi kuma ya bude wardrobe ya na fito mata da kaya.

 

A cikin sauri take gyara dogon gashinta saboda Leelah, Hilal ya matso ya karbi comb din hannunta ya na ce wa “Besty ki yi komai a hankali in dai saboda wannan uwar fadan ce ay mun san hanya” murmushi ta yi ta ce “Besty ay Leelah is my chewing gum” Hilal ya bata rai ya ce “ni kuma fa?” “You are my chocolatey” ta fada ta na bashi kiss ta mirror.

Hilal ya yi mata style mai kyau da gashinta ya yi dropping dinshi a tsakiya kasancewar gashin mai santsi ne sai ya yi squeezing a gefen fuskarta, ya saka white gel ya kwantar dashi.

Hakan yasa ya yi mutukar kyau. Moofeey ta yi murmushi ta ce “thanks my besty,” shi ma murmushi ya yi ya na kallon yanda ta yi masifar kyau mussamman cute lips dinta da suke shining din lip gloss, ya matso daf da ita ya bata light kiss akan lips, ta daki kafadarsa ta na tashi daga gaban mirror ta nufi inda ya ajiye mata kayan da zata saka, inner wears din ta fara dubawa ta kalli Hilal daya tsareta da ido ta juya masa baya, tana cikin saka hock din Brezier taji shi a daf da ita, ba tare data juyo ba ta ce “what’s” ya ce tayaki fa zanyi, no need” ta fada cikin golden voice dinta, Sai data gama saka komai ta juya ta kalleshi ya na tsaye ya na kallonta, harararsa ta yi ta cigaba da shiryawa,

Sosai ta yi kyau cikin crazy trouser, onion colour wanda kadan ya wuce gwuiwar ta ya kamata sosai ya fito da shape bom dinta, sai riga t-shirt cotton a gabanta an rubuta HAPPY BIRTHDAY SAUBAN,

ta saka silly gold din sarka doguwa har kirjinta, kafarta sanye leg race da takalmi hill, ta sanya p cap an rubuta MOOFEEY a jiki.

ta yi wani shegen kyau sai tashin kamshi take mai dadi duk in da ta juya boos dinta ne suke juyawa,

Ta yi wani fari da ido ta kalli Hilal ta ce “idan ka gama kallona sai ka same ni a falo ina jiranka” ta bude kofa ta fita ta barshi tsaye ya na binta da kallo.

 

A falo ta sami Leelah zaune akan kujera ta na danna I phone, ita ma ta yi kyau sosai ta na sanye da riga irinta moofeey da trouser baki ita ma a jikin p cap dinta an rubuta LEELAH, Moofeey ta yi hugging dinta ta na ce wa “my chewing gum” Leelah ta yi dariya ta ce “kin yi kyau my chocolatey”.

 

Hilal ya fito daga dakin ya na rike da karamar jakar Moofeey, shi ma ya na sanye da rigar birthday din sai dai bai sanya p cap ba sai wani shegen aski da ya ke kansa.

 

“Ohh besty ka fito min da phone’s dina” Moofeey ta fada ta na kallonsa, ba tare da ya yi magana ba ya mika mata jakarta, Leelah ta hararashi ta ce ya na abu kamar wani king, ita ma bai kula taba ya yi hanyar fita daga falon suma suka bi bayan sa, kana kallon su kaga stubborn children😁.

 

Suka fito parking space suka zabi motar da zasu fita da ita mai shegen kyau da tsada.

Leelah ce take driving, Hilal yana kusa da ita sai Moofeey a baya, a over speed ta figi motar suka fice gidan.

 

Basu tsaya ko ina ba sai cikin hotel din, ba tare da bata lokaci ba suka nufi hall din birthday tun kan su karasa Leelah ta fara rawa sa bo da irin kidan da yake tashi, Hilal ya kalleta ya ce “please karki zubar mana class ko kallonsa ba ta yi ba ta cigaba da rawarta, suna shiga ciki wurin ya kaure da ihun ganinsu, Sauban birthday boy ya taso ya yi hugging dinsu ya na ce wa “welcome my guys” ya yi wata shegiyar shiga gashin kansa ya koma kalar blue, sannan suka karasa high table wurin zamansu, suna zama Moofeey ta dauki shisha ta fara busawa cikin nishadi.______

 

Your comments is my confidence🤩

 

SHARE🙏🏻🙏🏻

 

🤹🏽‍♀️RAYUWATA CE🤹🏽‍♀️

 

 

Queen Ameerah…🖊️

[21/08, 12:14 pm] +234 903 602 2224: 🤹🏽‍♀️RAYUWATAH CE!!🤹🏽‍♀️

 

BY

Queen Ameerah……..🖊️

 

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

💗SABON LABARIN SOYAYYA MAI CIKE DA SON ZUCIYA💗

 

 

PAGE 3➡️4

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
____________Hilal ya zubawa Moofeey ido ya na kallon yadda take busa shisha ta na lumshe ido, murmushi ta yi wanda ya nuna beauty point dinta ta shafa fuskar Hilal ta ce “Besty kallon fa?” ya ja mumfashi ya ce “karfa kisha abun nan da yawa ki kasa tafiya” dariya Moofeey ta yi ta dauki glass cup din gabanta wanda ya ke dauke da juice ta yi mixing dinshi da syrup kurba ta yi kadan sannan ta mikawa Hilal, karba ya yi ya na kallon kyakkyawar fuskarta sannan ya shanye duka ya mika mata cup din, haka ta ringa zuba masa ya na shanyewa sai da ya gaji ya rike hannunta ya ce “ki barni haka please” 6ata rai ta yi ta na turo lips, murmushi ya saki ya yi kissing din lips din nata, ita ma murmushin ta yi tana juya masa sexy eyes dinta.

Leelah kuwa ta na tsakiyar hall tana rawa idan kaga yadda ta ke juya jikinta sai ka ce “yar” Naira Marley, friends kuwa sai zuba mata kudi suke kamar abin banza.

 

Wata classy girl ce fara doguwa mai kyau ta karaso wajen Moofeey da fara’arta ta zauna kusa da ita ta na ce wa, “sunana Zully tunda na zo wurin nan naga kin burgeni, dan Allah ina so ki zama kawata” wani murmushi Moofeey ta yi ta na lumshe sexy eyes dinta da suka fara buguwa, ta ce “karki damu sunana Moofeey, wannan shi ne babban abokina sunanshi Hilal,” Hilal ya dago ya hararari Moofeey. Ita kuwa Zully zuba masa ido ta yi ta na ce wa “woow shi ma ya na da kyau kamar kee gaskiya naji dadin haduwa daku”, murmushi Moofeey ta yi ta na mika mata cup din mix juice ta karba ta fara sha ta na ce wa “ni ina garin Kaduna ne Babana shi ne mataimakin Commissioner of police ina fatan ke ma a Kaduna ki ke?, shegen murmushi Moofeey ta yi ta ce “ay ni ina ko ina ma” da mamaki Zully ta kalleta ta ce “ban gane me ki ke nufi?” Moofeey ta yi dariya ta na kallon Hilal da shi ma ita yake kallo sannan ta ce “zaki gane idan kina tare dani,” murmushi Zully ta yi ta ce “na fuskanci tafiyarmu dake za ta yi dadi na yi farin cikin haduwa dake,” Moofeey ta ciza lips ta ce “gaskiya ne kanki ya na kawo wuta” Hilal ya mike ya na ce wa “Besty ina zuwa” Moofeey ta ce “okay dear” hira sosai Zully take yi wa Moofeey, ita kuwa sai da ta bata amsa a dunkule ko ta yi murmushi, Zully ta kusanci Lpy qalau Moofeey irin mutanan ne da ba’a gane kansu, hakan ya sa ta yi shiru kawai ta na kallon yadda take busa hayaki cikin kwarewa.

BIRTHDAY BOY ne ya zo wurinsu ya na ce wa “Moofeey biggirl kina enjoying” murmushi ta yi ta na juya eyes, Sauban ya ce “ya kamata ki taso mu yi pictures gasu Mubeen suna ta cigiyarki” ta ce “okay” ta na kallon Zully suka mike a tare.

 

Sosai suka ringa zuba pics da video, friends kowa ya na so ya yi hoto da Moofeey, after that Sauban ya yanka cake nan take wurin ya kara cika da music, lady’s and mens are busy romancing.

Sai a lakocin Moofeey ta tuna da Hilal dan ta lura baya wurin, duk da ta na cikin maye don da kyar take iya bude ido, Leelah ta fara nema tana can tsakiyar friends dinsu Moofeey ta ja hannunta ta na ce wa “ina Hilal?” Leelah ta ce “ba kuna tare dashi ba?” tsaki Moofeey ta yi sannan ta nufi hanyar fita daga hall din.

Tafiya ta ke a hankali idanuwanta a rufe da kyar take ganin gabanta a haka ta nufi garden din hotel din duk da dare ne akwai wadataccen haske a ko ina, ji ta yi an janyo hannunta ta fada jikin mutum, ajiyar zuciya ta sauke a hankali furta “Hilal” sa bo da kamshinsa da taji, ya kalli fuskarta ya ce “me ki ka fito yi?” ta bude idonta da kyar ta kalleshi ta ce “kai na ke nema” ta janye jikinta daga nashi ya yi murmushi ya na kokarin boye bottle din hannunsa karaf idonta yakai kai, kallonsa ta yi tana hade fuska, ya sunkuyar da kansa kasa, cikin fada ta ce “Hilal bana hanaka sha ba?” besty kiyi haƙuri ya fada yana kamo hannunta, ta fizge hannunta tana kokarin barin wajen, ya yi sauri ya rumgume ta yayi kasa da murya yana fadin Besty kar kiyi fushi dani, ta kalli cikin idonsa ta ce “Hilal na hanaka shan alcohol is haram” shi ma tsakiyar idonta yake kallo ya na mamakin halayyarta ita tana aikata laifi amma tana kokarin ganin ta hana wani sabawa Ubangiji, Besty inshaallh bazan kara ba ya fada kamar xaiyi mata kuka, murmushi ta yi, ta ce “promise”, ya mayar mata da murmushin yana kallon lips dinta, sai a lokacin ta raba jikinta da nashi tana harararsa, hannunta ya ruko yana ce wa ya kamata mu tafi gida Besty barci nake ji tunda kin hanani abinda nake so, murmushi ta yi ta daki kafadarsa tace kwana fa zamu yi, ya zaro ido yace please muje mu janyo Leelah mu tafi don kema yau kin jiku da yawa, lumshe ido tayi tace hakanma ban koshi ba, suna rike da hannun juna suka koma cikin hall din da kyar hilal ya janyo Leelah wacce take tikar uban rawa, haka ya cillata cikin mota ta na yi masa bala’i, ita ma Moofeey sai dauko ta ya yi don tafiyar ma ta kasa yi duk jikinta ya saki, wannan karon Hilal ne ya yi driving dinsu zuwa gida.

Ya na parking ya bude ya fito ya cillawa Leelah key din ya dauko moofeey kamar wata baby ya nufi cikin gida Leelah ta biyo bayansa tana zuba masa masifa, bai kulata ba direct dakin Moofeey ya yi ya kwantar da ita saman bed idonta yana rufe sai motsa baki take tana magana kasa kasa, yaja blanket ya rufe ta sannan ya bata kiss a koshi, ya fito daga dakin ya janyo mata kofa, ya na fitowa falo suka ci karo da Affan ya na shigowa da trolley dinsa, suka rumgume juna cikin farin ciki, Hilal ya ce dama yau zaka dawo, Affan yace na gaji duk na yi missing dinku, Hilal ya ce mu ma yanzu muka dawo daga BIRTHDAY

Leelah ce ta fito daga dakinta da gudu ta rumgume Affan, dariya Affan yayi ya na ce wa ina Moofeey, Hilal ya yi saurin ce wa ta yi barci, Leelah ta harareshi taja hannun Affan suka shiga dakin Moofeey, ta na kwance yanda Hilal ya barta tana ta motsa baki, Affan yayi murmushi ya ce Moofeey ta yi over ke nan, Leelah tace hmmmmmn kasan halin ay, please ku barta ta huta Hilal ya fada ya na tsaye jikin kofa, Affan yaja hannun Leelah suka fito ya na ce wa “sorry Besty” Hilal ya rufo mata kofa.

Suna fitowa Affan ya yi dakinsa don ya samu ya huta, ita ma Leelah ta yi nata dakin, Hilal ya rage shi kadai zaune a falo ya na tunanin abinda ya ke kasan zuciyarsa ya na tsoron ya bayyana shi._________

 

 

YOUR COMMENTS IS MY CONFIDENCE

 

 

SHARE

 

 

BY

Queen Ameerah……

Leave a Comment

error: Content is protected !!