Hausa Novels

Razani Hausa Novel Complete

Razani Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

RAZANI

 

Na

 

*ZAINAB A BARDE*

 

 

 

GARKUWA WRITTER’S ASSOCIATION*

{ _Marubuta masu garkuwa da alƙalami domin fadakar da al’ummah_}

 

_Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai_

 

 

*PAGE 1nd 2*

 

 

*Na sadauƙar da wannan littafi ga mahaifina Allah ya jiqansa da rahama*

 

 

 

“Abduuuuul” *IG* ya fada a tsawace yana buga table din dake gabansa! “dole ne kabar wannan binciken, kasan akan suwa kuwa kakeso kayi wannan aikin? to in baka sani ba ka sani idan har suka gano kana wannan binciken akansu, ina mai tabbatar maka saisun batar dakai daga doran duniya”

 

 

Kallon wanda aka kira da Abdul nayi, wanda yake tsaye idanuwansa sun kada sunyi jajir, jijiyoyin kansa sun firfito, fuskarsa tayi jajir abinka da farin mutum, tun fara maganar shugaban nasa baiyi magana ba sai yanzu, “amma Sir mutanan nan fah azzalumai ne dani dakai duk mun…”,

“dakata!” ya tsayar dashi ba tare da ya bari ya karasa abin da yake son fada ba,

“karka manta daya daga cikin mutanan nan sirikin ka ne mahaifin matar ka, kada kaba makiyanka dama, nace ka dakatar da binciken da kakeyi period”,

“owk Sir” ya fada yana mai kamewa tare da sara masa, yana mai fecewa daga office din, da kallo ya bisa harya fice daga office din yana girgiza kai yasan Abdul yanada taurin kai abu ne mawuyaci ya aje case dinnan cikin sauki, amma ya kudiri aniyar sa masa ido, dan kare lafiyar sa da rayuwarsa, ni nasan suwaye mutanan nan ba kananan taƙadirai bane, duk cikin jami’ansu babu kamar Abdul shiyasa a koda yaushe yake alfahari dashi.

 

 

 

 

Duk inda ya wuce sara masa suke amma ko kallo basu ishe shi ba, yana shiga office dinshi ya hada files masu mahimmanci yayi musu kyakkyawar ajiya saboda halin kota kwana, safa da marwa kawai yakeyi dan samo wa kansa mafita, har lokacin tashinsa yayi baita buka aikin komi ba, jakar loptop dinsa ya dauka tare da ficewa,

tunda ga nesa daya daga cikin jami’ansu ya hango ogan nasa, da gudu ya taho ya karbi jakar hannun sa “barka da fitowa Sir”ya fada yana sara masa hannu kawai ya daga masa, tun anan Umar yasan yau an taɓo oga daga haka shima yaja bakinsa ya tsuke har suka karasa wajan mota, ita kanta motar abin kallo ce, duba da irin haduwarta, kasan mamallakin motar naira ta zauna masa, gidan baya ya buɗe masa ya shiga sannan ya rufe, da sauri ya zagaya ya shiga mazaunin direba yaja suka bar wajan,

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
 

 

 

Amatu! Amatu! Amatu!!! dan uwarki wai mai kike a bandakin nan? wallhi inna shigo sai jikin ki ya gaya miki ko nakuda kike ya isa ace kin haihu, matar da bata wuce shekaru 35 ba ta fada tana kunfar baki, “haba Lami kedawaye haka kiketa tada jijiyar wuya? tundaga kofar gida ana jiyo ki, “yooo ba gara a jiyoni ba Asabe” nidawa kika sani a gidan? nida tsuntacciyar magen chan mana, wata shewa Asabe tayi irin ta tantiran yan duniyar nan, “ni wllhi Lami dama zaki bani ita na kaita aikatau wajan manyan hajiyoyi a binni” wata uwar harara Lami ta galla mata, “inna baki ita ni kuma ubanwaye zaina mun tallar” kuma kinsan malam bazai taba bari tayi nisa dashi ba, taɓe baki tayi tana “fadin ni kinga ba wannan ne ya kawo ni ba aron kudi nazo ki bani” shekeke ta kalleta, “bazan bayar ba nace bazan bayar ba! “haba Lami kar aji kanmu mana, sai kiyi kuma,

 

 

Ranta a matukar ɓace take kallon Lami amma se tai murmushi mai naima ai baya fushi ta ayyana haka a cikin zuciyarta, “toh sanmun dan abinda zan kai bakin salati tun safe ban karya ba wannan kam zaki samu” kudi ne dai baz… sauran maganar ta maƙale sakamakon fitowar Amatu daga bandaki, yarinyar da bazata wuce shaikara shatara zuwa ashirin a duniya ba, kyaukyauwa ajin farko, fara ce amma bawai irin farin nan mai cika ido ba, fari mai yellow yellow doguwa amma ba chan ba, tanada dogon hanci, da bakinta dan sut masha allah, duk yadda zan ma mai karatu bayani ta zuce nan, saide kana kallonta kasan akwai rashin wayewa a tattare da ita,

 

 

“Dan buhun ubanki sai yanzo kika gadamar fitowa” talla ce daii saikin jeta maza zoki dauka ki tafi kafin raina ya gama baci, “Inna Lami dan Allah ki bari na fara cin abinci” ta fada a yanayin tsoro, “inkinga kinci abinci a gidan nan to kin saida duka gyadar nan inko baki siyar ba babu ke babu abinci” maza dauki ki tafi munafukar banza mai suffar aljanu!!!

hawayan da suka silalo akan kuncinta tasa bayan hannunta ta goge, farantir gyadar ta dauka zaita dora akai kassss! taji saukar ranƙwashi “Allah yasa baqin halinki yasa kiqi zuwa inda za’a siye” ki dawo kuma mu gauraya nida ke tsintacciya kawi!!! dagudu ta fita daga gidan saboda kukan daya taho mata, tun tana yarinya karama Inna Lami take azzabtar da ita ga ƙiyaryar da take nuna mata ga kiranta da tsintacciyar mage da take bayan baffa yace mata shine mahaifinta, mahaifiyarta kuma da tazo haihuwarta ta rasu, tana kuka take wannan tunanin harta karasa inda yan mata sa’aninta suke siyar da kayan sana’ar su, tana zama sauran yan matan suka dauki kayan sana’arsu, suka koma chan gefe wanda duk ta girme su dansu bazasu wuce shekara 12/ 13 ba, “Allah ya sawaƙe mu zana guri daya da tsintacciya” daya daga cikin yan matan mai suna fadila ta fada, dariya sauran suka saka har suna tuntsurawa, kukan da take rikewa ne ya kufce mata, tanada hakuri ga sanyin hali bata iya fada ba.

 

 

 

 

“Mahammadar rasulillah Audil kai kuma daga ina haka? kamar anjefo ka ko wannan figaggiyar matar takace ta koro ka dan ko kashe mutum akace tayi bazan musa ba saboda baqin hali irin nata gakanan shekara huɗu da aure amma kamar baka yi ba, wadanda basuyi auran bama sun fika kyaun gani” kwanciya yayi akan kujerar da tsohuwar take kai tare da kwantar da kai akan cinyar ta, “Mahammadar rasulillahi sallallahu alaihi wasallam Audil karya ni zakayi? in kwanciya zakayi ka tafi wajan marar kunyar matarka mana mai ido a tsaƙar ka” shidai har yanzo baice mata uffan ba, saima rufe ido da yayi,” yooo ai gara kai da wannan gantalallan ƙanin naka, yoo dama wakeso na a gidannan inba kai din ba.

 

 

 

 

“Kaima gashi yau ko yar gasasshiyar kazar nan daka saba siyo min baka siyo min ba, “Dada wai baki iyayin shiru da bakin kine, kode battery magana ake sanya miki bansanni ba”? “ɗungure masa kai tayi uwarka da ubanka su ake sakawa battery magana bani ba, ko bakaji ba nace uwarka da ubanka ake sakawa battery ba ni ba” zaune ya tashi yana murmushi, “tsohuwar nan kin cika rigima” ya fada yana jan kumatunta, buge hannun tayi tana galla masa harara, “ni bari na wuce dama daga office nake nace bari na shigo” banza ta masa wai ita tayi fushi saboda yace mata rigimanmiya, harya kai kofa ya tsinkayo muryarta tana fadin “ka bani wasu yan kudade saboda wanda ka bani sun kare” karasa ficewa yayi yana mamakin abinda take da kudi ko sati ba’ayi ba ya bata 50k amma yanzo har tana batada kudi, “Big bro barka da dawowa ya aiki”?

 

 

 

Hannu kawai ya daga masa, baiko damu ba saboda yasan halin yayan nasa na rashin son magana, darect bangaran kakarsa(Dada) ya nufa, yana shiga yaji tana cewa “muskilancin banza da wofi mutum sai shegen girman kaii” “my sweet Dada waya tabo min keee? “Auzubillahi minalshaidanir rajin kai kuma daga ina ko sallama babu, amma duk da haka gara kai akan gantalallan yayanka” saita fara matsar kwalla ta kama gefan zani tana face majina, “dan kawai nace ya bani kudi, kudin da ya bani sun kare shine pah ya zageni tass harda cewa wanda ya bani ma saina biyasa”

 

 

Dry yakeson yi amma sai ya dake, “Dada badai kudi kikeso a baki ba? kai ta daga masa tana matse kwalla, hannu yasa acikin aljuhunsa a ciro kudi masu yawa ya bada, washe baki tayi tana fadin “kamalu ni dama nasan kafi wancan tsagagon kirki yooo ai har fura na dama masa amma tunda kaine kamin abin arzuki to kai zan bama furata” “aa Dada ni yanzo fita zanyi budurwata nachan na jirana” bai jira cewarta ba ya fice daga falon, “haba ta riƙe Mahammadar rasulillah Kamalu lallai wuyanka yayi kauri, toh bari Audil yazo ayiwa tufkar hanci” kirga kudin tashiga yi dubu talatin da biyar ne cif, mtwsss taja tsaki “marowaci ma baiji dadin halinsa ba, inda audil ya fika kenn mai zanyi da dubu talatin da biyar” saita kara rushewa ta kuka tana face majina, “Alkur’anin ubangiji saina kai kararka wajan uwarka inji ko ita tasaku kuna min haka, inanan ina jiranta tashigo, dama yau ko keyarta ban gani b.

 

 

 

Tundaga bakin kofar part dinsa yake jiyo kida na tashi, ya rasa wacce irin mata Allah ya bashi wajan aiki zafi maimakon gida yaji sanyi amma shima zafi, tundaga falon ko ina ka kalla tarkace ne, cups ne ledoji ne anci abu kuma ba’a tattare ba, sosai ransa ya qara baci ita batasan ta gyara muhallinta ba, wayarsa ya ciro a aljihu ya kira kanwarsa ringing daya ta dauka hello Big bro, “sameni a part dina yanzon nan” kitt ya kashe wayar, da kallo tabi wayar tana addu’ar Allah yasa ba wanin laifin akace tayi ba, tana fitowa falo taga mommy bata nan kawai saita fita tayi bangaran Abdul tana Addu’a a cikin zuciyarta dan tana mugun tsoran yayan nata, da sallama ta shiga, a tsaye ta tarar dashi, “ki gyara falon nan” daga haka ya haura sama, da kallo tabi falon ko ina kaca kaca sai kace ba mutum ke rayuwa a ciki ba a haka ta fara gyaran falon tana mita.

 

 

 

“A gaskiya Alh Tanimu ya kamata mu dauki mataki akan yaron nan dan abubuwan nasa suna *RAZANANI* ” mutumin mai kimanin shaikaru 55 ya fada yana huci, “calm down Alh Bello, ba muda wata matsala, a hannunmu fah kasar nan take sai yadda mukayi da ita” Alh Tanimu ya fada yana murmushi, murmushi Alh Bello yayi yana fadin “mu har akwai wanda zai tabamu a kasar nan ya zauna lfy, Alhaji magaji yace zamu zauna meeting akan yaron yau da karfe biyu na dare” dry suka kwashe da ita suna tafawa.

 

 

 

SHERE ND COMMENT

MORE COMMENT MORE TYPING

Name: [My Novels (www.mynovels.com.ng)]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na TelegramPowered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!