Romantic Hausa Novels Complete Download

Romantic hausa novels complete download

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Romantic Hausa Novels Complete

Romantic Hausa Novels Complete Download

Karanta Littafin a Daren Farko

DAREN FARKO

Marubuciya: RABI’ATU NASIDI ABUBAKAR.

Kotun tayi tsit, kowa yayi jugum ana sauraron abinda zai fito daga bakin alqalin Wanda ya sukuyar da kansa yana rubuce-rubuce.

 

Lauyoyi da sauran ma’aikata wadanda suke da alhakin xama a kotun saboda sauraron shari’ah, kowanne yana zaune a mazauninsa daya dace dashi, haka ‘yan kallo da iyayen yarinyar da ake gudanar da shari’ar a kanta, al’amarin ya ba kowa tausayi shiyasa indai mutun ya kalli fuskokin kaso tara cikin mahalarta kotun sai kaga kowa cikin matsananciyar damuwa musamman wadanda abin ya shafa, iyayenta da ‘yan uwanta kenan.

 

Mai sharia Usman Muhammad ya daga kansa a hankali ya dubi wacce ake qara tana tsaye inda ake tsaida wadanda ake tuhuma hannayenta biyu sanye da ankwa. Baqar Riga ce da baqin hijabi sanye a jikinta kanta ba dankwali, idanuwanta sunyi wani irin ja saboda tsabar kuka, bata son dago kai ta dubi kowa saboda tsanar kanta da tayi, don haka ma da alqali ya kira sunanta bata dago kanta ba ta dai amsa cikin dusasshiyar murya wadda daqyar ake iya jin abinda take fada. Alqalin ya kuma cewa “Fatima Musa” ta amsa “na’am” “ke kika kashe Abubakar Siddiq Wanda akafi sani da doctor Khalifa”??? Fatima tayi shiru alqali ya maimaita tambayar har sau uku bata yi magana ba, yadda kasan kotun ba kowa saboda tsabar shiru. Kowa Fatima da mai sharia yake kallo ana sauraron abinda Fatin xata ce amma taja bakinta tayi shiru kamar dama can yadda Allah ya halicceta bata da bakin magana.

 

Mai sharia Muhammad Bamaina yana magana cikin yanayi na tausasa harshe yace “Fatima kotu tana tuhumarki da laifin kashe mijinki Dr. Khalifa kamar yadda aka kama ki da gawarsa shiyasa muke son ki bayyanawa kotu gaskiyar al’amari da bakinki tunda ke ba bebiya bace kuma ba kurma bace kina jin abinda muke fada kuma kina iya magana, idan ke kika kashe shi ki fadawa kotun , sannan ki fadi dalilin dayasa kika kashe shi, idan ba ke bace ki danyi magana kiyi bayani.

 

Fatima ta dago kanta a karo na farko ta dubi jama’ar kotun suka had a Ido da mahaifiyarta wadda ta zuba tagumi duk da nisan dake tsakaninsu da Fatima, Fati tasan kuka take wiwi tana girgiza kai, Fati ta dubi mai sharia said kawai taji kanta yana juyawa qafafunta suka shiga rawa, hakan yasa suka gaza ci gaba da daukarta gangar jikinta ta zube a gun, nan take mai sharia Usman M. Bamaina ya daga sharia zuwa uku ga watan gone un Allah ya kaimu.

 

Kotu ta rude da hayaniya, koke-koken iyayen Fati da ‘yan uwanta ya cika kotun, ga ‘yar uwarsu a matsanancin hali amma ba yadda xa ayi su taimaketa, suna ji suna gani wash ‘yan sanda mata suka daga Fati aka five da ita gaggawa saboda numfashinta me yake sama-sama kamar xai dauke.

************×*×**********×****×******×**********

Yammaci me aqalla zamu iya kiran lokacin qarfe biyar na gamma da wasu mintuna, Ummi na xaune gefen tabarma ta hada kai da gwuiwa tana kuka kamar ranta zai fita, Goggo Abu ce gefenta itama tana goge hawaye cikin yanayi na tsananin damuwa ko barka sansu ba kaga halin da suke ciki said ka taya su wannan kuka da suke, ko ba a maka bayani ba kasan damuwar dazata sa ayi irin wannan kuka ya is a a tayashi kuka. Malam Musa ya shigo da carbi a hannunsa yayi sallama ya tsaya daga can bakin qofa yana kallonsu tsawon mintuna biyar sannan ya qaraso inda suke, Allah sarki bawan Allah mai sauqin kai wanda bai dauki duniya baking komai ba, fuskarsa cike da tausayi da karaya yake kallonsu ya kasa magana, xuwa can Goggo Abu ta goge hawayenta cikin qarfn halo race Malam ka dawo? Sannu da zuwa. Ya daga mata hannu yace gaisuwar taki tunda idanuwanku baxasu daina xubda hawaye ba akan damuwar da muka samu kanmu ciki.

See also  Macijine Shi Hausa Novel Complete

 

Goggo Abu tace “Malam to yaya xanyi tunda abinnan ya faru Ummi bata daina kuka ba, nayi lallashin duniyar nan yarinyar nan taqi ta daina kuka had na rasa wacce kalma zan gaya mata wadda zatasa tayi haquri. Malam have “Ummi kiyi haquri komu da muka haifi Fatima babu abinda zamu iya akan wannan lamarin sai addu’a. Cikin matsananciyar damuwa Ummi tace “Shin Baba shikenan saga haquri babu abinda zaku iya gaya min wanda xan samu sassauci a zuciyata game da halin da Fatima take ciki?? Wayyo Allah kaicon rayuwata ni Ummi in har xan xauna ina rayuwa a cikin tunanin Fatima na kulle a kurkuku ana tuhumarta da laifin da ni daku da duk duniya sun san baxata taba iya aikatashi ba. Yaya xa’ayi ace Fatima xata kashe rai? Kisan ma ace tarasa Wanda data kashe sai mijinta? Ka dubi wannan al’amari ayi wani abu akai har yaushe muna xaune Fatima na cikin mummunan xargi irin wannan.

 

Malam Musa yai zaman dirshan a wurin yace “Ummi to yaya xamuyu”? Saboda girman Allah me kike ganin xamu iyayi kinsan indai ace munada bakin yi din da yanxu va wannan xancen akeyi ba. Kinsan mudai ba kudi garemu ba, kuma ko idan mutum nada kudi in akace case din me xafi ne da tsanani iron wannan baka da ta cewa, kudinka baxa suyi amfani ba don baxa su sayi ran da aka kashe ba balletana ka sya domain ko diyya da ake biya idan wani ya kashe wani ba a irin wannan yanayin ake biyan diyya ba, kinsan ita sharia sabanin hankali CE duk yadda kake tunaninta ta wuce nan. Kuma idan ma muna da abin yin yanxu baxamu iya ba idan Fatima ba ita ta kashe Dr. Khalifa ba tai magana mana a kotu, kinaji kina gani daxu a kotu tayi shiru, ta bude bakinta tace ba ita ta kashe shi ba ta fadi yadda abu ya faru aqalla idan ma akwai abinda xa ayi ayi tunda tayi shiru me xa’ace?? Ya girgixa kai cikin dan xuciya yace “Allah kadai yasan yadda wannan abu ya kasance sai kuma Fatima.

 

Ummi ta ciji yatsa har yanxu kuka take mai ciwo a rai tace ” Shikenan Goggo tunda kuma kun yarda Fatee ita ta kashe Doctor sai kusa I do itama a kasheta ba tare da haqqinta ba, amma dai inaso Ku Sani ko ku kuka haifi mutum baku kuka halicceshi ba yadda kake da haqqin yayi ma biyayya haka shima yanada haqqinsa a kanka idan ka danne Allahu Subhanahu wa ta’ala xai tuhumeka Baba. Nikam ba zan bar maganar Fatee ta wuce haka ba, ba xan bari a cigaba da xalintarta akan abinda bata aikata ba, xan shiga in fita ko xan rasa xanin daurawa sai na taimaki Fatee In Shaa Allahu.

 

 

Malam yace Ummi bana shakku akan abinda kika fada mun tabbatar zaki aikata fiye da abinda kika fada akan Fatima qaunar dake tsakaninku ta wuce a fadeta da baki, Allah kadai yasan iyakacinta, sai dai inaso kisani ba wai mun yarda cewa Fatee itace ta aikata kisan ba, ki fahimci wani abu daya Ummi bamu da kudin da xamu iya daukar lawyer da xai kare Fatee, baki da buqatar mu gaya miki halin da muke ciki na qa-qani kayin rayuwa a gidannan kinsan kome da ina mukaga halin daukar lawyer sannan idan ma mun dauka da wacce hujja xamu fidda Fatee daga wannan zargi tunda taqi magana? Wannan shine dalilin dayasa muka miqawa Allah lamuranmu , idan Fatee ba ita ta kashe Doctor ba In Shaa Allah Allah xai bayyanar da gaskiyar al’amari Allah xai kawo mana mafita.

 

 

Ummi duk wanda nasa ya shiga matsanancin hali irin wannan ya gama kwanciyar hankali kada ki dauka bamu damu da ita ba illa iyaka shi lamari irin wannan idan kaga kanka a cikinsa baka tsananta damuwa wadda ita dama rayuwa jarbawa ce a cikinta, idan Allah ya jarrrabeka da wani lamari ka gode masa kawai ka roqeshi ya baka juriyar cin wannan jarbawa da yayi maka domin ba wanda ya isa ya kaucewa jarbawar Ubangiji. Kiyi haquri Ummi.

See also  Sirrin Boye Hausa Novels

 

 

Ta jinjina kai face ” Na haqura Baba, na da kuka da hawaye tunda baka son ganin hawayen said dai ba xan iya haquri da Fatee ba koda nima xan shiga halin da take ciki, ko nima zan rasa raina, idan ba halin daukar lawyer ai Muna da halin daukar akwai guraren da ake taimako a samu agaji su taimako ne a gabansu kawai gabansu ba kudi ba, su ake kira gatan mara gata. Goggo tace Allah shine gatan mara tata shi xai xama gatanmu, Ummi kiyi haquri. Tayi murmushin qarfin hali tace Goggo na kanyi mamakin masu cewa inyi haquri akan maganar Fatee, waya ce banyi haquri ba? Tabbas nayi haquri domin na haqura da duk wani farin ciki In Shaa Allahu akan nemawa Fatee haqqinta sai inda qarfina ya qare koda hakan shi xai kasance abinda zan aikata na qarshe a rayuwa ta.

 

***********××************

Suna a wani dab daki Mara girma Ummi da Barrister Nuruddeen, aka bude wata qofar dakin, wani kakkauran Dan sanda ne a gaba fuskarsa ba fara’a, Fatee na bite dashi a baya kamar ko yaushe baqar rigar nan itace a jikinta da baqin hijabi kai ba dankwali ta rame sosai tayi duhu idanuwannan kamar gauta saboda jan da sukayi, hannayenta biyu cikin ankwa, wani dan sanda a bayanta saidai shi fuskarsa akwai sassaucin ra’ayi.

 

Fatee ta dubi Ummi tayi murmushi cikin dusasshiyar muryarta tace “Ummi kune”? Dan sandan yace Ku gaggauta yin abinda ya kawoku Dan kar kuyi asarar lokacinku. Ummi ta girgixa kai hawaye wasu na bin wash ta taso ta dafa kafadar Fatima tace sannu Fati da izinin Allah zai kawo mana Marita a cikin al’amarinnan, min Shiga tashin hankali da damuwa akan halin da kike ciki Fati inajin ciwon damuwarki kamar zuciyata xata buga saboda tashin hankali. Wannan shine Barrister Nuruddeen Mustapha, na daukeshi ne don ya xamo lauyan da xai kareki a kotu. Fati inaso ki bamu hadin kai duk tambayoyin da xai miki ki bashi amsa sannan idan anje kotu a xama na gaba ki bude baki kiyi magana.

 

 

Fatima tayi murmushi hade da hawaye tace “Ummi bansan da wani kalamai amfani gun gode miki ba, komi na fada ba xai wadatar da xuciyata ba har inji cewa na nuna miki godiya ta kan soyayyar da kikemin da kuma qoqarin da kike don ganin kin ceci rayuwata daga wahala. Saidai inaso ki fahimci wani abu duk yadda kaso yankewa mutum wahala idan Allah bai qaddara lokacin yankewar wannan wahala tasa tayi ba baza ka iya yanke masa ba.

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Na godewa Allah daya qaddara min shiga wannan hali ina fatan wannan jarrabawar da Allah yayimin ta zamo kaffara a gareni, Ummi inaso ki sani ban tsananta baqin ciki akan halin da nake ciki ba ni a karan kaina wannan kukan dako yaushe xa aga idanuwana nayi ina yinsu ne saboda tausayin iyayena daku yan’uwana bisa halin da xaku Shiga da baqin cikin halin dana tsinci kaina a cikinsa, da kuma uwa uba rashin mijina Wanda zuciyata bata da juriya akan wadannan abubuwa biyu, wannan damuwar ba xanyi kuka ba in har akan halin danake ciki ne.

 

 

Zaman danake Ummi ina jiran ranar da za ayanke min hukuncin kisa ne inbi mijina. Idan har akwai taimakon da nake buqata daga gareku ayanxu shine ku taimaka a yanke min hukunci in huta wannan damuwar kuma ku huta domin idan an kasheni kun daina ganina dole wata rana Ku haquri, idan ko ina Raye haka xakuyi ta zama cikin damuwa.

 

 

Wannan shine dalilin dayasa naki magana a kotu kuma ina nan akan bakana na ba xance komai a kotu ba don bani da abin cewa duk abinda xan furta bai wuce ince bani na kashe Doctor ba, idan nace ba ni na kashe shi ba ina neman kariya kenan wadda ke nufin in ci gaba da rayuwata a duniya ba.

See also  Hayar Mace Hausa Novel

 

 

Ummi kiyi haquri kiba iyayena da duk yan’uwana haquri ki roqar min su gafara kowa yayi haquri ya manta dani bana buqatar taimakon kowa a gareku sai addu’a, na gode qwarai da gaske kada ki sake wahalar da kanki gun dauko min lauya……. Ummi ta katseta cikin huci tace “Fatima kin amince ki dauki laifin da ba naki ba, kin amince ki kashe kanki? Wayake kin taimako kin amince ki jawa dukkan zuriarku abin fadi?

 

Kina xaton wannan ba xai xama mugun aibi ga xuri’arki ba? Wanda xai ja a dinga aibata muku zuria mata su rasa maxajen aure?

 

Kina xaton idan an kashe ki wani xai sake zama lafiya cikin iyayenki da yan’uwanki?

To ki sauya tunani lauya tunda kince baki so na janye shi, amma ko shakka babu kuskurene babba wanda xaki tafka idan har kikayi iqirarin kece kika kashe Dr. Khalifa alhalin ba ke kika kashe shi ba.

 

Fatima tace to idan ni na kashe shi fa Ummi?

Ummi tayi murmushin takaici tace bakece kika kashe Doctor ba, don kuwa baki da dalilin kashe shi, kina fadin hakanne kawai Dan kin gaji da da duniya bakya son rayuwa a halin da kina son ki gaggauta barinta, shiyasa kike furta abinda xai raba ranki da hangar jikinki…. Dan sanda yace “lokaci yayi” Ummi ta ce kayi haquri ina fada mata abinda xai amfaneta ne. Yace bashi da amfani gareta da sai ta karba kidaina wahalar da kanki.

Ya tisa qeyar Fatee, kallon data waiwayo tayiwa Ummin ta wuce shiyasa tsigar jikin Ummi ta shiga tashi ta zube qasa ta riqe kanta da hannu bibbiyu. Shi kansa Barrister Nura jikinsa yayi sanyi, ya jima xaune a gun yana kallon Ummi, daga can yadan ja numfashi yace “tashi mu tafi Ummi fun anan na tabbatar yarinyar nan Fatee ba ita ta kashe Doctor ba duk da cewa taqi amincewa da duk wani taimako daxa a bata ta rufe duk wata qofa ta kariya daxa a bata, ba wani abune kuma yasa tayi hakan ba tayine kawai saboda baqin cikin dake damun xuciyarta Wanda yake tafarfasa xuciyarta yasa rayuwa ta fita a xuciyarta.

Hakan yasa taqi magana a kotu wannan taqi yarda da taimakon da za a bata, ba komi Allah yana tare da masu gaskiya, sannan baya goyon bayan xalinci, indai bata da haqqi da sannu xakiga hukuncin da Allah xaiyi.

Ummi bata kuma cewa komi ba har suka fice daga gun.

*********×××************

Da sauri ya goge hawayen dake xuba a idonsa jin sallamar matarsa, Goggo Abu ta xauna sharaf a gabansa jikinta na rawa ta ajiye flask din abincin da tazo kawo masa, yadda jikinta ke rawa haka muryarta take rawa, tace Innalillahi wa inna ilaihirraji’un Malam kuka kake? Yayi dan murmushi yace “haba dai kuka ba kuka nake ba Zainabu” race “don Allah kar kace haka Malam bayan ba gani da idona kana kukan kuma naji shasshekar kuka, Malam idan kayi kuka akan wannan al’amari mu kuma yaya xamuyi da ranmu? Kai kake nuna mana muyi haquri bisa fushi da yin Allah me xai sa kai kayi? Malam Musa yace ” Zainabu al’amarinnan yana matuqar bani mamaki da daure min kai, yaya xa ayi Fatima ta iya kashe mutum? Idan mince ba ita ta kashe shi ba wane ya kashe shi? Alhalin daga ita sai shi a gidan dakin a rufe da sakata ta ciki. Me yasa Fatima ta kashe Doctor Khalifa me yayi mata? Meye iyayen Khalifa basu yi mana ba? Shi kansa Khalifa n meye bai yi mama ba? Ace Fatima ta rasa tukuicin da xata sakawa wadannan bayin Allah sai da wannan mummunan aikin? Goggo Abu tace “Malam ka yarda Fati ta kashe Doctor Khalifa? Yace “to Zainabu idan ba ita bace waye? Daga ita sai shi a daki ya shiga ya rufe qofa shi xai kashe kansa ne Zainabu?” Tayi shiru na lokaci mai tsawo, daga bisani ta jinjina kai tace ” ko shakka babu a cikin wannan al’amari akwai rikitar da qwaqwalwa sannan duk Wanda yayi wannan aikin Wanda yasan sirrin gidanne , tabbas Fati ba ita ta kashe Doctor ba don bata da dalilin kashe shi ko tanada dalilin kashe shi bata da qarfin halin da data aikata wannan mumnunan aikin, saboda xuciyarta ta tana da sauqi akan al’amura, Allah kadai yasan yadda al’amarin ya kasance.

Cikin sanyin murya Malam yace “Zainabu nima abinda yake damuna kenan kowa ma haka yake fada su Kansu iyayen Khalifa haka suke cewa basu yarda Fati ta kashe shi ba, to amma me yasa baxa tayi magana a kotu ba idan aka cigaba da tafiya a wannan hali xa a samu mafita? Tunda ba it a bace tayi magana mana ” wannan shine abinda ya damu kowa ma ba kai kadai ba Malam.

downloadRomantic hausa novels complete downloadRomantic hausa novels complete downloadRomantic hausa novels complete download.

 

Romantic hausa novels complete downloadRomantic hausa novels complete downloadRomantic hausa novels complete downloadRomantic hausa novels complete download.

 



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Romantic Hausa Novels Complete Download]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

1 thought on “Romantic Hausa Novels Complete Download”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top