Rudani Hausa Novels Complete

Rudani Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*RUDANI* 🙊

 

 

NA

*IKILIMA ADAM*

 

_( KYAUTA DAGA ALLAH)_

 

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI , ALLAH INA GODIYA A GAREKA DAKABAN IKON FARA WANNAN LITTAFIN MAI CIKE DA RUDANI LAFIYA , ALLAH KASA IN KARESHI LAFIYA , LADAN DAKE CIKIN SA , ALLAH KABAMU , AKASIN HAKA, ALLAH KA YAFE MUNA .

ALLAH YA DAUKAKA MARUBUTA A DUK INDA SUKE , ALLAH YAKARA MANA BASIRA DA FIKIRA YA BAMU SAA ADUK ABUNDA MUKA SA AGABA.

 

_JINJINA DA BAN GIRMA GAREKI AYSHA ALIYU GARKUWA_

 

_MAMAN NUSAIBA GODYA TA MUSSAMAN AKAN SHAWARWARI_.

 

_MAMAN AMATULLAH INA KARA MIKA GAISUWA._

 

_UMMU SHUKURA SHUGABAN JARUMAI GODIYA BISA RAINON KI_

 

_FADILA SANI BAKORI , JINJINA GAREKI UWAR DAKINA._

 

_ABBA ABUBAKAR JINJINA AKAN KULA DA KAKE BAMU MU_

 

_ALL YAN KUNGIYAR JARUMAI INA MIKA.GAISUWA_

 

 

Littafin nan na kudine akan farashi Dari biyar kacal .

_Zaki tura kudin ta wannan account din._

_3115484026 ikilima_ _adam first bank_

 

_Ko kuma katin waya akan wannan lambar_

_09069080725_

 

_Bayan antura sai atura_ _mun evidence akan_ _wannan lambar_ _+22953726162_

 

 

 

 

 

Chapter 0️⃣1️⃣

 

 

Wani irin gurnani da nishi take wacce yake nuna tana gab da haihuwa , cike da *RUDANI* mijin nata yake Fadin Fadila kiyi nishi me karfi , kuma gashi Nurse din nan tunda ta tafi bata dawo ba , InshAllah zaki haihu dan ma kina da kokarin karanto adu’oi yakarashe zancen tareda shafa mata ruwa akan cikin ta , itakuwa azabure cikin tsananin tashin hankalin da take dake ciki murya a raunane tace ” Sufiyan Tawa takare shikenan zan bar duniyan nan zan bar maka wasiyya duk wuya duk rintsi kayi kokari ka zantar da Adalci akan sa, karka duba Alakar mu ko wani danganta na rokeka Safiyan , karkace zakamun kara danni jinin sa ce , wata shaka yasha daga gareta yayin da Nakudar yazo gab da gab yunkurawa tayi cikin ciza labban ta gumi na sassarfo mata ta ko ina sasssan jikin ta , wani irin nishi me karfi ta sakeyi tana zazzare idanu , wanda anan take nan da nan saiga jaririyar ta , tayi waje , itakuwa komawa tayi ta kwanta cikin mutuwar jiki tana kallon Safiyan da ya Rude ganin nurse bata zo ba har ta haihu , yana kokarin daga jaririyar , yaji Murjan Fadila tana fadin dan bani reza da zare kusa da kai nasha ganin yanda ake yanke cibi , aguje yaje yadauko ya mika mata zuba ma ta idanu yayi yana kallon yanda ta saita zaren ajikin cibiyar ga mamakin sa , sai gani yayi har ta yanka.

fuskar shi cike da hawaye ya dauko Jaririyar ya rungume Babu Babu sutura ajikin baby , sossai ya kurawa baby idanu yana sakin Murmushin me nuna zallan kywaun sa , daura mata jaririyar yayi akan cikin ta yayi yace ” bari inje in samo kayan da zansayawa jaririyar nan ki lullube ta da zani tunda , sai kuka take tsalawa cikin muryan tasu na jarirai ji kake iyeeen iyeeen ! iyeeen ! Nan da nan ta bade dakin da sautin muryan ta , Fadila dake jin jiki dan har ta soma fita hayyacin ta amma duk da hakan be hanata daga hannun ta , ta shafa kan jaririyar ba ,murmushi mai hade da kuka tayi tana kallon Sufiyan dashi din ma itake yake kallon cike da tausayawa , murya a sanyaye tace ” Safiyan Yarka ce ” jinin ka ce amma ina kara baka Amanar ta kasanya mata suna mai ma’ana amma kada kasanya mata sunana , kuma karka manta da sakon dana ajiye na letter bayan ankaini gushewa ta inason ka karanta .

Cikin raunin murya yace ” ai cuta ba mutuwa bace Fadila zafin nakuda ce kawai ke dawainiya dake ” daukar jaririyar yayi daga kanta ya lullube ta da zani , cikin damuwa yace ” kinga bansan yanda ake yiwa me sabuwar haihuwa bara naje makwafta nakai musu yar dan suzo su taimaka miki ,yakarashe zancen tareda barin dakin , Kamar wani zautacce.

See also  Labarina Hausa Novel Complete

 

Fadila kuwa soma matsa cikin nata take tana yunkurin taga uwa ta fito , cikin ikon Allah kuwa sai gashi yafito bayan tayi yunkuri me karfi .

Ajiyar zuciya ta soma sauke wa akai akai ganin Uwar sossai ta tsorata , cikin rawar murya tace ” wannan ai ya kusa kai girman jaririn ,

Takun tafiyar da taji ne yasa takai duban ta akan wayanda ke shigowa duk a zaton ta khadija kawar ta ce , hakan yasa tafara neman jan zani dan ta rufe jikin ta , Azabure taga wannan baiwar Allah tashigo duk da mawuyancin halin da take ciki hakan be hanata ja da baya _ baya ba , cikin tsananin tsoro da fargaba ga jini sai malala yake daga kasan ta , Itakuwa Matar da Fuskar ta babu Annuri karasowa dakin tayi tana kwabe bakin ta , wani kallon banza take bin dakin dashi Murya a khausashe tace ” au harkin haihu kenan ? bushewa da wani firgitaccen Dariya tayi wanda amon muryan ta saida ya karade dakin , cikin kankanin lokaci kuma ta hada rai kamar ba ita ba , tsuke fuskar ta tamau tayi , tana mai bin kwaryan dake hannun ta da kallo , budewa tayi tareda karasowa gaban ta , tana tafiya cikin Salo na mugun ta , kwabe baki tayi ganin Uwa a kasa ga jini ta ko ina , watso mata wani ruwa tayi me kamar jini daga kwaryan dake hannun ta , wanda yayi Sanadin nan take Fadila halittar tafara sauyawa , jikin ta yafara canza launi izuwa mummunar halittar, cikin wani irin yunkuri sai juyi take kamar maciji tana mika da fisge _fisge cikin zazzare idanu , nan wani , hayakin kamar daga sama yaringa bin dakin gabadaya ya gauraye ko ina , hayaki na lafawa atake ta sauya izuwa Wata halittar , ita kanta matar duk rashin imanin ta saida ta razana ganin wannan Babban abun dake tsalle _tsalle hakan yasa tayiwa wanda yake tsaye kusa da ita , yana duba mata in akwai wani me zuwa ya sanar mata , cikin hanzari tace ” yashigo su dauka , kada asamesu acen din zata rikide tazama kamar halittar da suke so , aikuwa hanzarta shigowa yayi shikuwa yana kallon mummunar halittar nan , yanda ta kura masa idanu hawaye cike a idanun ta , saida ya firgita cike da tsoro da farga suka yi nasarar daukar Mummunar Halittar nan kai tsaye barin dakin sukayi dashi , suna buga uban sauri gudun kada asamu matsala.

 

Bangaren Sufiyan

 

 

Safiyan kuwa yana ajiye jaririyar wajen makociyar tasu , Alfarma ya nema dan Allah tayiwa Yarinyar wanka , acen wajen Fadila sannan ta taimaka mata , zeje kasuwa yasiyo mata kayan da za’a sanyawa jaririyar , makociyar cike da jin dadi ta karba tace ” mashaAllah Fadila Allah yayi ta sauka lafiya , kuka ta soma tuno halin da Fadila ke ciki , hakan yasa tace au to tunda inada ruwan zafi , kamata yayi in mata wanka , kana inje cen in hada mata nata tareda bata taimakon gaggawa.

 

Yana cikin kasuwar duk hankalin sa ya rabu gida biyu tunani yake _ ya ake siyyayar ne , ganin bashida mafita hakan yasa yaje mikawa masu shagon kayan jarirai kudi yace dan Allah ku hadamun duk kayan da mejego take bukata da kuma kayan jarirai , hannun sa na rawa ya mika musu kudi , kai tsaye shagon provision ya nufa Fuskar cike da damuwa dan duk yakosa yaga yakoma gidan nan , nan ma kayan shayi bonbita , madarar peak ta gwangwani hade milo komai dai yahada mata yana fadin inshAllah bazakiyi jegon banza .

 

Yana gama uzurin sa be bata lokaci ba wajen daukar hanyar sa tazuwa gidan sa , koda ya isa kai tsaye wajen makociyar yaje ya iske har tayiwa Jaririyar wanka , har kaya saida ta sanya mata na jarirai dayake ita me yara ce .

Mika mata kayan yayi , tana karba tace muje wajen Fadilan zan kai mata ruwan zafi tasamu tayi wanka , asamu agyara dakin nata .

See also  Download Forbidden Love Hausa Novel

Barin dakin sukayi atare yana gaba tana bin sahun sa .

 

Ahanzarce sukayi dakin nata , sallama dauke abakin nashi yana shiga dakin kai tsaye kurya ya nufa cikin hanzari domin ya kosa yaga ta samu ta danci wani abu .

Cikin tsananin mamaki yake kallon dakin da jini ya malale , karasowar makociyar yasashi waigowa yana kallon ta yace ” banga kanwata ba ” ? Makociyar tace ” Kila ko tashiga bandaki ne tana kokari ajiye jaririyar saman gado zata gyara dakin , shikuwa sossai ya yarda eh lallai Fadila bandaki tashiga , ganin har angyara dakin an goge shiru bata dawo ba , yasa hankalin sa yayi mummunar tashi , Makociyar me suna Khadija tace ” amma fa ta dade a bandakin nan , anya babu abunda yake samun ta kuwa tayi magana cikin ayar tambaya , Sufiya rike da baki yace ” please dan leka muna bandakin nan ki gani ko ! Khadija cikin barin jiki tashiga Bandaki ganin wayam babu alamar anshiga bandakin yasa cikin damuwa tadawo ta sanar masa, daura hannu akai yayi yace ” Fadila ko ta sake guduwa ne ? Gaskiya intayi hakan bata kyauta ba , saida na mata nasiha akan tayi hakuri da kaddarar nan amma ta nuna ta yarda yanzu ya zanyi da jaririyar nan , Khadija tace ” a’a bana tunanin ta gudu ne , ai duk rashin imanin Uwa dole ta so abunda ta haifa .

Sufiyan kasa fita aiki yayi duk lissafi ya kunce masa, Fadila kadaice take yawo a kwanyar kansa , ganin babu mafita ne yasa cikin Azzama yakara komawa kasuwar yasiyo madarar jarirai , yana dawowa zuwa yayi yakaiwa Khadija cikin damuwa yace ” gashi abata harda fida nasiyo, tunani yake wani suna ze sanyawa yarinyar hakan yasa cikin sanyin murya yace ” na sanya mata *NI’IMATULLAH* hawaye nabin kuncin sa .

Ita kanta Khadija sai jijjiga Jaririyar take , tana mai tuno firar su ta karshe itada Fadila , inda take Fadin .

” wallahi inajin kaina a ba mutum inajin kaina acikin yanayin daba na mutane ba , inajin kaina shin rayuwa nake koko a barzau nake rayuwa , numfashi Khadija ta Fesar a fili ta furta InshAllah Fadila zamu ganki duk inda kikaje , inada yakinin kilan mafarkan ki ne suke zaburar dake kokuma iskoki ne suke damun ki .

 

_____________

 

Su kuwa suna barin Gidan da mummunar halittar nan har wata kasa suka nufa da ita , tafiyar doki sukayi inda suka ringa bin cikin sahara, da zaran sunji kishi zasu tsaya sudan sha ruwa daga nan suci gaba da tafiyar nasu kwanan su biyu ahanya sannan sukaci rabin tafiyar , ganin Alamun sun kusa shiga gari ne , yasa anan cikin jejin suka jefar da wannan mummunar halittar.

Suna jefar wa suka bushe da dariya , Matar tace byee byeee Fadila sai a darul salam , namijin dake tare da ita duk jikin sa yayi mugun sanyi , yana ji yana ji yana gani matar ta kama hannun suka bar wajen tareda karasowa cikin garin dan anan zasu kwana agobe , su bi jirgin daze kaisu Garin kaduna, Dokin nasu kuwa kyautar dashi sukayi ga wani Farin dattijo me aikin kula da jakai da dokuna .

 

 

_____________

 

Bayan wata daya

 

khajida kullum batada aiki sai kuka akan rashin Fadila , domin har mijin nata shima yashiga damuwa sossai hakan yasa yace ” haba kidaina sa damuwa nasan banza bazata gudu tabar yar ta ba , kuma ni Sufiyan yana bani tausayi jibi duk yanda yabi ya rame bashida walwala , amma saide abunda ke dauremin kai shine iyayen ta , sunada masaniya kuwa akan batar yar su koko basuda labari?, Khadija cikin raunin murya take kallon sa da idanun ta da suka kada jajir tace ” wallahi bana tunanin sunada masaniya amma dai bari ya dawo zuwa yamma please kaje wajen nasa ka bincika mana , dan yakamata asan abunyi wata daya bafa kwana daya bane takarashe zancen tana mai daukar jaririyar dake kuka , Madara ta kada mata acikin fida saida tadan saka acikin ruwan sanyi yayi sanyi kadan sannan ta saka ma ta abakin ta , wawar cafka jaririyar tayiwa fidar yayinda taji yashiga bakin ta , cike da so da kauna take kallon baby idanun ta cike da hawaye shiko Mijin nata dake kallon su kada kai yayi tareda tashi domin zuwa Sallah juma’a da ake huduba a Massalacin garin nasu .

See also  Asgar Hausa Novel Complete

 

____________

 

_*TCHAD*_ *Djammena*

 

A wannan yankin da nayi duba dasu naga zallan su kamar ba hausa bane , amma kuma baza’a rasa masu jin hausar ba .

Ahankali nake bin layi *RIDDINA* domin zuwa dauko muku rahoto da dumi_dumin sa , da zallan mamaki na tsaya daidai wani gida da dukan Alamun gidajen manyan masu Arziki ne , ne masu fada aji a garin .

Makeken Gate din naga an wangale cikin azzama , cikin shock na dan tsaya daga gefe .

Mai gadin gidan cikin yaren su na yan tchad naji yana fadin barka da fitowa yallabai cike da ban girma , kyawawan Dattijon dake cikin motar a gefen sa yaro ne wanda akalla baze wuce shekaru 18 ba , yaron cikin halin ko in kula yake jifar mai gadin da kallo zaka zata hararan sa yake , yanayin halittar sa ce a hakan , Alhajin yana fita da motar amsar gaisuwar me gadi yayi yana mai daga masa hannu , tareda bankawa motar tasa wuta , agujeee ya diba kamar ze tashi sama dan sauri , Ikon Allah shine me gadin ya furta yayinda yake kai dubansa akan yanda motar tashi take tashin hayaki , dawowa da baya _ baya yayi yana girgiza kai cikin mamaki yace ” oh Allah yasa lafiya dai wannan uban saurin da Alhaji yake diba .

 

Alhaji kuwa sunyi tafiya mai nisa kafun suka iso bakin beach teku daidai nan yafaka motar sa .

Kiciniyar bude murfin motar yake , yaji muryan yaron yana fadin Abba kabar shi zanbude dakaina yayinda yake kokarin budewa yayi daidai da zagayowar Alhaji , Hannun sa na rawa yace ” A’a Dana kasan banason kayi koda aikin daga kofi ne nasha gayamaka yanzu de gashi na kawoka bakin tekun nan kamar yanda ka bukata , ina nan zaune ina jiranka duk sanda ka gama uzurinka sai mu tafi ko? Cike da nutsuwa yaron yafito , kallo daya na masa naga kyakyawan ne ajin Farko shi ba fari ba kuma baza’a saka shi jerin bakake ba , hancin sa dogo ne kamar biro , labban sa daidai misali , ga kwayar idanu hade da yalwataccen gashin gira , sajen dake kwance saman fuskar bakaramin kara masa kyau da kwarjini yayi ba .

Kallon Mahaifin nasa yayi cikin zuciyar sa yanajin nutsuwa a fili kuma sam baka gane dariyar sa ko akasin haka hannu kawai ya daga masa , yana mai saka hular sa akan sa , kasantuwa kaya ne jikin sa irin na kwallo hade da takalmin kwallo a kafar sa , gudu yake yanajin iska na kadashi , harya iso bakin tekun nan , hannun sa yasa cikin ruwan wannan Al’ardar sa ce diban ruwan teku yadan kurba , wannan karan yanakai hannun sa da mamakin sa yafara ganin jini_jini na tashi a awajen , ahanzarce ya dauke hannun sa , yana kara kura Idanun sa awajen da jinin ke fita , cikin tsananin mamaki yaga ya’yan kifaye sunayin sama dube _dube yake inda idanun sukayi tozali da crabe 🦀 murmushi ya saki kasan zuciyar sa domin a bayyane baka taba ganin haka , sossai yakeji dadin ganin crabe na yawo abakin teku , cigaba da tafiyar yake inda yake shirin zuwa inda abokan wasan buga kwallon kafar sa yake , acikin ruwan yaji sautin kuka na tashi da babban murya me Amo , firgit ya waigo jin an ambaci Habibullah ! Habillah ! Ha ….bi ….llah da wani irin marayan murya , cikin gigita yake kallon yanda ruwan take………….

 

 

_LITTAFIN NAN NAKUDI AKAN FARASHI NAIRA DARI BIYAR KACAL_

 

_DOMIN KARIN BAYANI KU TUNTUBE AKAN LAMBAR WAYA KAMAR HAKA_

 

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA ALLAH

 

 

Kuyi following dina a arewabook

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top