Hausa Novels

Rudin Duniya Hausa Novel

Rudin Duniya Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Rudin Duniya Hausa Novel

*RUƊIN DUNIYA!*

 

 

 

 

*NA_NAFISAT ISMA’IL LAWAL*

_UMMUDAHIRAH_

 

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*

 

 

 

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*

 

“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS)“`

 

/

 

*P.W.A*

 

 

 

 

 

*Romantic Book ne, kuyi haƙuri sabida salon labarin ne ya zo a haka; babu yadda na iya.*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_________________________

 

*BABI NA ƊAYA*

_______________ *KADUNA ZARIA*

A garin Kaduna ƙaramar hukumar Zaria; anguwan tudun wada. Malam Iro me kifi, sana’ar sa kenan siyar da kifi. Gado ne da yayi wajen mahaifinsa marigayi, tun yana saurayi yake sana’ar wadda ta kai yanzu har Aure yayi a cikin sana’ar, kuma alhamdulillah yana samu dai-dai gwargwado kuma har ya rufawa kansa Asiri. Mahaifiyar sa tana raye kuma shi yake kula da ita tunda shi kaɗai ne ɗa namiji da suka haifa, sai ƙannin sa biyu mata waɗanda yanzu haka sun yi aure da jimawa, sai dai Allah ya yiwa ɗaya rasuwa a lokacin da zata yi haihuwar fari. Shi ya ci gaba da kula da matafiyarsu tare da nasa iyalan, wanda a lokaci ɗaya jinyan mutuwa ta tarar da mahaifiyar tace ga garin ku nan.

 

Shekaru da dama sun shuɗe, wanda har ga shi girma ya soma tarar da Malam Iro; amma har yanzu cikin sana’arsa ta gado yake. Yanzu haka Allah ya albarkace sa da Yara huɗu Mata; wacce matarsa Harira ta haifa masa. A cikin rayuwar Malam Iro akwai dogaro ga Allah da tsantsan tawali’u, duk abun da Allah ya ba shi yana ƙoƙarin karɓa da hannu bibbiyu sannan kuma ya yi mishi godiya. Sai dai kuma matsala guda ɗaya ce a rayuwar sa da yake samu, wanda kuma a yanzu ta zame mishi babbar matsala da yayi sanadin soma gurɓata rayuwar ƴaƴan shi

 

Harira Mace ce mai tsananin son abun duniya, haƙiƙa duniya tana matuƙar ruɗanta wanda ta kai har ba ta iya bambance abu mai kyau da mara kyau a rayuwarta, ita burin ta kawai tayi kuɗi, me zata taɓa ya zama kuɗi? Sannan aina zata samo hanyar da zai kawo mata kuɗi? Shi ne tunanin ta a koda yaushe. Tun farko Harira irin matan nan ne kyawawa da Allah ya zuba musu kyau; kasancewar ta bafulatanan nan cikin Zaria cikin anguwan Fulani, tallen fura da nono take kawo wa nan cikin kasuwan tudun Wada, wanda har Malam Iro ya ganta kuma tayi masa a zuciya, babu ɓata lokaci ya bayyana mata irin ƙaunar da yake mata, to, itama bata ja zancen ba ta amince domin a lokacin kaf cikin samarin ta shi ne wanda take ganin yana da ɗan kyan gani da sura me kyau, duk da a rayuwarta ta taso da burin auren shahararren me kuɗi; kasancewar yanda ake ce mata tana da kyau, irin su masu kuɗi suko so, domin irin su ne ake ajiyewa a gaban mota, to, ga shi kuma har ta kai wannan lokacin babu wani me kuɗi da ya taɓa cewa yana sonta, tun tana saka ran zata same su domin ta ƙi aure tana jiran irin su, amma kuma shiru kake ji sai irin ƴan iskan samarin nan da suke kawo mata hari ko yaushe. Haƙiƙa ta ji daɗin shigowar Iro cikin rayuwarta, wanda babu ɓata lokaci ta ba shi dama ya tura gidan su, aka yi komai na al’ada aka sanya musu ranan aure.

 

Bayan lokaci yayi aka ɗaura musu aure ta tare a gidan su, tana zaune tare da mahaifiyar sa. Sai dai tunda aka yi auren ɗabi’un Harira waɗanda be san su ba suka soma bayyana, Mace ce fitinanniya ga shegen rowa, ko abinci tayi ba ta ba wa mahaifiyarsa, sai dai idan shi ya dawo ya nema mata abun da zata ci, sosai mahaifiyarsa take kuka da irin halin Harira saboda kasancewar ta Mace mai haƙuri, haƙiƙa tana ƙunsan baƙin ciki a wajen ta, ga shi ko kaɗan ba ta ganin girman ta har zagin ta take yi tayi ta gaya mata maganganu mara sa daɗi, shi kansa Iro haƙuri yake yi da ita sabida shima irin mahaifiyarsa ne, tun yana tanka mata yana tsawatar mata har ta zo ta fi ƙarfin sa yanzu, domin a yanzu ta sake kilewa rashin mutunci sai wanda ya daɗu a gunta, bare yanzu tayi ƙawaye matan masu kuɗi masu hannu da shuni, a wurin su take koyo duk wasu abubuwa da bata san su ba a baya, ita rayuwarta kawai tana hangen waɗanda suka fi ta ne shiyasa kullum fitina ba ya ƙarewa a gidan su, kullum da abun faɗan da zata yiwa Iro, ya gaji dai ya ƙyale ta ya fita harkan ta.

 

A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Harira ta haifi ɗiyarta Mace ta fari, aka sanya mata sunan Ƙanwar Malam Iro da Allah ya karɓi abun sa, Nana Firdausi. A lokacin da Harira take da cikin ƙanwar Firdausi har ta kusa haihuwa, sai kuma mahaifiyar Iro ta rasu, sanadin da aka maida wa yarinyar sunan ta, Ummu Kulsum, suna kiranta da Ummu, ita dai Harira da sunan ta gatsau take kiran ta babu ko kunya. Bayan kamar shekaru huɗu sai ta ƙara haihuwar Mace, itama aka saka sunan uwar Harira, Fatimah suna kiranta da Zahra, sai kuma Auta da aka haifa bayan shekaru uku da haihuwar Zahra, sai dai fa tunda aka haifi yarinyar nan Harira ta ɗaura buri na duniya a kanta sabida ganin yadda yarinyar ta fita daban da sauran ƴaƴan ta, tsananin kyawun ta da kaf ƴaƴan ta basu biyo ta ba, duk kyawun Harira ta ninka ta a kyau nesa ba kusa ba, shiyasa tunda aka saka mata suna A’isha Humaira, sai ita Hariran take kiranta da suna Arab sabida tsantsan kyawun ta, kuma sunan ta ji shi ne a wajen wasu masu kuɗi da suka sanya wa ɗiyar su, shiyasa itama take ce mata Arab, shiyasa sunan ya bi ta har girman ta, wanda daga ita ne kuma bata sake haihuwa ba. A wannan lokacin Harira wacce yaranta suke kiran ta da Inna; babu irin sana’ar da ba ta yi don kawai ta farfaɗo da rayuwar ƴaƴan ta, kuma ta sanya su a inda zasu yi gogayya da yaran masu kuɗi, shiyasa tun suna yara makarantar kuɗi suke yi, ita take biya musu kuɗi da komai bata damu da sai Malam Iro ya bayar ba, wanda a yanzu shi kuma yaran suke kiran shi da Baba, sai dai idan ya samu kuɗi yana taimaka musu sosai tunda zuciyarsa bata mutu ba, bazai iya gani yaran sa suna rayuwa be da amfani a tare da su ba, sai dai bai da wani iko dasu tunda sai abun da Harira tace a gidan ake yi, tuni ta mallake shi domin har biye-biyen Malamai take yi yanzu.

 

Tunda yaranta suka girma bata da wani buri a yanzu sama da su samo mata masu kuɗi, kowanne iri ne idan yana da kuɗi; to, tana son yaranta su samu, shiyasa bayan sun gama secondary school; Ummu da Zahra, sai ta saka su a nan F.C.E Zaria, duk sanda suka je makaranta suka dawo zata ɗaura musu tallan shinkafa su shiga cikin kasuwa suyi talla, ita a ganin ta idan suna yawo kwararo-kwararo hakan ne zai sa masu kuɗi su gansu har su zo gare su

 

Yayinda ita kuma Firdausi tana zaune a gida ta ƙi makaranta, sabida ita bata da buri sama da tayi aure, kasancewar rayuwar gidan su yana mugun ɓata mata rai, kwata-kwata ta tsani halayyar da Innarsu take shirin jefa su a ciki, shiyasa ita kaɗai ce ta fita zakka a gidan su, wadda ita ta biyo halayen Mahaifin su ne sak, shiyasa yake tsananin ƙaunarta saboda tana bin maganar sa, yayinda ita kuma Inna Harira ta tsane ta kuma ta fita harkan ta, dalilin da yasa tace, “baza ta biya mata kuɗin makaranta ta ci gaba ba tunda ba ta mata biyayya.” Ita kuma dama bai dame ta ba bare ta saka hakan a ranta, duk da Babansu yayi mata alƙawarin, “idan har ya samu kuɗi a wannan shekaran zai saka ta sai ta riƙa bin ƴan uwanta”. Amma ita furr tace, “ba ta so.” Tace mishi, “ita aure take so yanzu, kuɗin da zai saka ta makarantar gwara ya siyan mata kayan ɗaki.” Kasancewar tana da saurayin da yake neman ta tun tana secondary school, sun shaƙu da shi sosai. Ɗan Kaduna ne amma yana zaune da Kakarsa a nan

 

To hakan ya yiwa Baba daɗi, shiyasa ya samu Nafi’u saurayinta yace mishi, “ya turo magabatan shi.”

 

Karin wasu littafai da zaku so

Abu kamar wasa har aka sanya ranan aure kusan shekara biyu, a haka Baba yayi kurɗa-kurɗan shi har ya samu ya yi mata komai da uba yake yiwa ɗiyarsa

 

Ba tare da ko sisin Inna ba, tunda ita tace, “ta ƙi bin umarnin ta sai abun da take so zata yi, to ta je tayi auren idan hakan shi ne zai fishshe ta.”

 

Haka kuwa aka yi auren lokaci yana cika. Aka kai Amarya gidan ta da ke can Kaduna, alhamdulillah Nafi’u yana da rufin asiri dai-dai gwargwado tunda yana aikin sa kala-kala. Haka dai ya fi ma Firdausi tunda tayi aurenta ta baro gidan su, su ma ƙannin ta tana fatan ace wata rana sun gane gaskiya su gane cewa Inna tana saka su ne a cikin *RUƊIN DUNIYA!* wanda hakan babu inda zai kai su sai dana-sani.

 

Ƙaramar ƙanwar su wato Arab, wacce a yanzu tana S.S 2 ne, ita kuma Inna Harira tana mata awara ne da yamma tana siyarwa a can bakin layin su. Gaba ɗaya yaranta ban da Firdausi ta ɗaura su a tirban da take buƙata, kuma su kansu sun tashi idanunsu a buɗe basu da buri sama da su cikawa uwar su burin ta, su kansu suna jin haushi musamman ganin su a gidan ƙasa gidan talakawa, ga ƙawayen su duk yaran masu kuɗi, shiyasa basu da aiki sai ƙarya, idan ka gansu baza kace yaran talaka bane sabida suturun da suke saka wa, kamar baza su taka ƙasa ba don yanga da iyayi. A duk cikin su ukun; Arab ta fi su fitsara da rashin kunya, domin ita halin mahaifiyarta ta ɗauka har ta zarta ta a son kuɗi, dalilin da yasa kenan ta soma ba wa maza kanta tun a wannan lokacin don kawai ta samu abun duniya, ga ta da samari ko ta ina, duk inda ta gibta sai ta samu saurayi, sai dai ita babu aure a tsarin ta a cewar ta, “sai nan gaba, sai ta gama karatu sannan zata yi aure”. Dalilin da yasa take gara kan samari kenan, ga shegen wayon; sai ta ci kuɗin saurayi kuma ta hana shi abun da yake so sai ta gama jan mishi rai ko kuma ta gama wulaƙanta shi. Arab kenan yarinya mai zamani wacce take cin duniyar ta da tsinke a yanzu, a duk faɗin tudun Wada da kewaye babu wanda bai santa ba, har kirari ake mata da sunan, ‘Arab Matar manya, kin fi ƙarfin Yaro’.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Yau ma kamar kullum yanda Inna Harira ta saba yiwa Arab awara domin ta fita mata dashi; hakan ne yau tayi mata, sai dai na yau ya fi na kullum yawa saboda ganin yanda ake ciniki sosai, ba ta daɗewa yake ƙarewa idan ta fita dashi, shiyasa tace wa Arab ɗin, “Autana yau da yawa zan yi miki tunda naga kina dawowa da wuri yana ƙarewa.”

 

Arab tace, “ai kuwa Inna dama ina so in yi miki magana ki ƙara yawan shi don naga ba ya isan su suna son awara na wlh.”

 

Baki Inna Harira ta washe ita kuma tana cewa, “ai dole ne su so awaran ki sabida daɗi, Ni na san na iya ai, ko kayan da nake kashe wa wannan awaran dole su riƙa santin shi.”

 

Dariya daga Arab har Ummu da take jin su suke yi

 

Ummu tace, “Inna ai Ni ina ganin hannun ki ne mai albarka, ko abincin nan da muke fita dashi ba ki ga yanda ake wawa ba wlh, mu ma idan za ki sake yin mana sai ki ƙara yawan shi, ki haɗa ma har da kunun aya don shima ana yawan tambayar mu.”

 

“To shikenan Allah ya kaimu goben za’a ƙara, dama ina ta tunanin siyan fridge wlh, to yanzu tunda kin ce haka kinga ban ga ta zama ba, yanzu ki taso ki shiga kasuwa sai ki siyo min abun kunun mu fara mu gani; Allah ya bamu sa’a.”

 

“Amin AMin.” Duk suka amsa daga Ummun har Arab

 

Sai Inna Harira ta kuma cewa, “yi sauri Auta ki shirya yanzu zan yanka miki ki wuce.”

 

“To Inna.” Arab ta amsa tana tashi daga bakin ƙofan da take zaune tana yankan ƙumba, ta wuce cikin ɗakin su, kayan jikinta ta cire ta ɗaura zani daga iya ƙirjin ta, kana ta fito kanta babu ɗankwali ta kamfaci ruwa a rijiya ta shiga wanka. Ta jima kafin ta fito tunda dama haka ta saba yin wankan ta, bayan ta shiga ɗaki ta gama shiryawa ta fito wajen

 

Ummu ta soma koɗata tana cewa, “iyen ba Ƙanwar mu, kin ga yanda kika tsatso kyau kuwa? Anya wannan baza ki haɗa gosilo a titi ba? Tirƙashi.”

 

Dariya kawai Arab ɗin take yi tana duba jikinta

 

Yayinda itama Inna Harira sai washe baki take yi tana koɗa ta tana cewa, “ƴan matana ta fi na kowa kyau, iyee! Kin yi kyau sosai Auta na, na san yau akwai kasuwa kenan.”

 

Fari tayi da manyan idanuwan ta tana taunan chewing gum ɗin bakin ta, yayinda ta furta, “sosai ma Inna, sai mun dawo kawai kiyi min addu’a.”

 

“To Allah ya tsare Allah Ubangiji ya bada Sa’a, Allah yasa a samo mana rusheshen me kuɗi wanda zai kai Ni Makka bana.”

 

“Amin AMin innarmu.” Duk suka amsa suna dariya

 

“Ke ma tashi ki shirya ki wuce kasuwan nan kinga yamma tana yi.” Tayi maganar tana kallon Ummu

 

Ita kuma Arab ƙaton farantin da aka jera mata komai, kama daga kan; icce, matsama, ashana, kalanzir, kafi-tankiya da Robbern zuba awaran idan ta tsame, duk suna kan farantin saboda ƙato ne, sai ta riƙe Robbern awaran a hannu tunda shi mai hannu ne, irin bokitin nan ne fari amma ƙato sosai, ta yiwa Innan sallama ta fice a gidan tana ci gaba da taunan chewing gum ɗinta, ƙararas-ƙararas kawai ake ji tana tafiya kamar zata karye tsaban yanga. Sai da ta ɗan yi nisa da gida sannan ta hangi Zahran su a cikin wata ƙatuwar jib ita da saurayin ta, shiyasa ta nufi wajen don ta ƙi wucewa sai ta kwashi rabon ta, tunda ta hangi wannan motan to akwai maiƙo a wajen, shu’umin murmushinta ta saki har da cije laɓɓa; tana wani gyara tafiyar ta cikin tsananin yanga ta nufe su tare da rangaɗa musu sallama

 

Gaba ɗayan su suka kalle ta suna amsa mata sallaman,

Yayinda Zahran tace, “Ah har kin fito Auta?”

 

Yatsina fuska tayi tana kallon ta tace, “eh wlh na fito, shi ne na hango ki nace bari in zo, dama Inna ce tace idan na ganki in amshi Naira ɗari biyu zan ƙara icce dashi, sannan kuma in siya yaji da sauran.”

 

Zahra tace, “to ai Ni bani da kuɗi, ban fito da kuɗi ba, sai dai ki koma…”

 

Tun kafin ta ƙarisa zancen saurayin nata yace, “a’a Baby bari in bata.” Sai ya sanya hannu a cikin Aljanu cikin sauri ya zaro kuɗi daga ciki, ƙirgawa ya soma yi

 

Yayinda Arab sai zuba murmushi take yi har tana ƙara leƙawa tana lanɗe baki, idanunta suna ware a waje tana ganin yanda yake sarrafa hannayen nasa wajen ƙirga kuɗin, a zuciya kuma tana taya shi ƙirga

 

Sai da ya ƙirga dubu goma cif kafin ya miƙo mata yana mata murmushi yace, “yauwa ƙanwata ga shi.”

 

Ta miƙa hannu cike da yanga ta amsa still tana murmusawa tace, “na gode.”

 

Murmushin ya kuma yi ko ƙyafta idanu ba ya yi a kanta yace, “babu komai ƴan mata yiwa kai ne, amma Baby ƙanwar ki ne da gaske?” Ya ƙare maganar yana mayar da idanun sa a kan Zahra

 

“Eh ƙanwata CE love, ita ce take bina kuma ita ce ƙaramar mu.”

 

“Masha Allah gaskiya kyakykyawa ce, ga kama nan ma na gani sabida duk kuna yanayi ai.”

 

Dariya kawai Zahran tayi,

Inda ita kuma Arab ta lanƙwashe murya tana sake mishi godiya

 

Yace, “babu komai ki je kawai.”

 

Da haka ta wuce ta tafi; Zahra na mata, “sai ta dawo”.

 

Tana wucewa saurayin yace, “Baby gaskiya duk ta fi ku kyau wannan ƙanwar taku, wow! Allah yayi halitta a nan.”

 

Haɗe fuska ita kuma tayi tana cewa, “to me kake nufi ne wai kake ta koɗata a gaba na?”

 

Murmushi yayi yace, “Baby Sarkin kishi, ai saboda tana ƙanwar ki ce nake koɗata a gaban ki, amma babu wani abu a raina, yanzu mu je shan icce cream ɗin ko mu fasa?”

 

Murmushi tayi tare da cewa, “mu je idan har baza a jima ba.”

 

“No Baby baza mu jima ba wlh, just thirty minutes ma ya isa.”

 

“Ok mu je.”

 

Daga haka suka rufo ƙofofin motan sannan ya ja suka tafi.

 

 

 

 

 

 

 

 

_In ana comments za a iya ganin posting koyaushe, so ku ba da haɗin kai please, idan kuma babu wani comments ba na bukatar ƙorafi don Allah, duk sanda ku ka ga sabon update shikenan._

 

 

*RUƊIN DUNIYA!*

 

 

 

 

*NA_NAFISAT ISMA’IL LAWAL*

_UMMUDAHIRAH_

 

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT *

 

 

 

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*

 

“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS)“`

 

/

 

*P.W.A*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_________________________

 

*BABI NA BIYU*

______________Wayanta ne ta soma Ring, sai ta ɗan dakata daga tafiyar yauƙin da take yi, tare da ajiye Robbern awaranta ta soka hannun ta a cikin Aljihun doguwar riganta; tare da zaro wayanta tana kallon me kiran. Sunan Besty ne ya fito ɓaro-ɓaro a kai, ba tare da jan lokaci ba tayi peacking tana karawa a kunne da cewa, “ya dai Besty?”

 

“Lafiya, ke nake jira tun ɗazu gani a wajen suyan ki, ko dai yau baza kiyi bane don naga time yana wucewa?”

 

Yamutsa kyakkyawar fuskarta tayi cike da yanga irin nata tace, “No gani nan a hanya ai, ina zuwa.”

 

“Ok kiyi sauri da Allah, akwai labari wlh.”

 

“Haba nawan?” Tayi maganar tana ɗan sakin fuskarta kaɗan

 

“You just have to come and see for yourself. ”

 

“Ok. I’m coming” Sai ta zare wayan a kunnenta tare da zura ta a cikin Aljihun, sannan ta ɗauki Robbern awaran ta ci gaba da tafiya. A haka tana yi kamar baza ta taka ƙasar ba har ta fita layin gidan su, duk inda ta wuce gungun maza kallon ta suke yi, majority wasu gulman ta suke yi, ƙalilan kuma suna mata magana kasancewar mutanen ta ne. Sai dai ta gaisa dasu kawai ta wuce har sanda ta kai babban titi inda take yin tuyan awara

 

Da sauri Ibrahim her friend; ya taso daga saman wani benci da ke gaban shago a wajen; ya sauke mata farantin saman kanta yana dariya tare da cewa, “Oyoyo my Besty, I’ve seen you before everyone.”

 

Murmushi tayi tana ajiye Robbern tace, “uhm Ni ban ga alama ba, bayan yau kwata-kwata ban ganka ba sai yanzu, ina ka shige ne?” Ta ƙare maganar tana narkar da manyan idanuwanta a cikin nashi, tare da sauke mishi wani kallo da ke rikitar da duk wanda ta yiwa shi

 

Shima ɗin kafe ta yayi da idanun yana cije leɓe cike da tsantsan sha’awar ta da ƙaunarta yace, “oh my Besty! Me kike ci na baka na zuba? Ai abun da yasa na kira ki kenan ki ƙariso don in shafa miki labarin abun da yake faruwa… Amma tukunna dai bari in soma hura miki wutan nan don naga time na gudu.” Sai yayi saurin ɗaukar kafi-tankiyan ya ajiye sannan ya soma jera itacen a ciki, a haka ya gama ya hura wutan

 

Ita kuma har ta saka kujera ta zauna suna magana a tsakanin su. Wani almajiri ta kira ta kalli Ibrahim ɗin tare da cewa, “Besty ba shi kuɗi ya ƙaro min icce, don wannan bazai ishe Ni ba.”

 

“Ok nawa kike buƙata?” Yayi maganar yana ɗago kai tare da kallon ta

 

“Two hundred is ok.” Sai ta kalli Yaron tace, “ka siyo min iccen ne na ɗari, sai yajin hamsin.”

 

“To.” Yace yana amsar kuɗin a wajen shi

 

Komai Ibrahim yayi mata hatta da ɗaura mai a wuta, sai da yayi zafi sannan ita ta soma jefa waran tana cewa, “My Besty bani labarin in sha na ƙosa.”

 

Dariya yayi yace, “Arab Sarauniyar son labari! Yanzu kuwa.” Sai ya gyara zama a saman bencin da ya ɗauko

 

Har zai soma maganar kuma sai wani saurayi ya iso wajen yana kiran sunan shi, tare da ba shi hannu suka gaisa, sai ya zauna a kan bencin shima yana kallon Arab tare da cewa, “Ƙin fi ƙarfin Yaro ya ne?”

 

“Dai-dai Sa’id.” Ta amsa shi batare da ta kalle shi ba tana ci gaba da saka awaran

 

Shi kuma yace, “but yau ba ki fara suya da wuri bane? I think zan zo inga wuri ya cika sai na iske babu kowa, yanzu ma kika fara ai.”

 

Yatsina fuska tayi da cewa, “wlh kuwa. I did not start early.”

 

“Ok. tunda na zo da wuri yau dai na taki Sa’a, za’a ajiye min na ɗari uku ina dawowa, don Allah yanzu ba jimawa zan yi ba kar in dawo inga an cika wurin sai na jira layi.”

 

“Ba ka da matsala, kawo kuɗin sai in ajiye maka.”

 

Sa’id ɗin da ya miƙe sai ya narke fuska yana kallon ta, tare da cewa, “haba Arab sai kace ba ki sanni ba? Zan ba ki mana kar ki damu ki zuba min.”

 

Taɓe baki tayi sai a lokacin itama ta ɗago manyan idanuwanta tare da zuba mishi su tace, “ka san hali na, a kuɗi bani da mutunci ka san da sani, Allah bazan ajiye maka ba idan har ba ka bani kuɗi ba, Ni na dena wannan gangancin.”

 

“Ibrahim ka sanya baki mana, wai kamar bata sanni ba? Yawa ne wannan wlh, kin san hali na nima na san naki, bazan miki wasa da kuɗi ba, don Allah ki ajiye min yanzu babu kuɗin ne a hannu na, kuma idan nace sai na dawo zan siya zan zo in tarar da layi, ƙarshe in rasa, kuma so nake yi in wuce da wuri saboda akwai inda zan je.”

 

Tsaki ta ja da faɗin, “zancen kake so, bani da lokacin ka wlh.” Ta mayar da hankalinta a kan abun da take yi bata sake bi ta kanshi ba

 

Yayinda shi kuma yana ta roƙon ta tare da ce ma Ibrahim, “ya saka baki ta ajiye mishi don Allah, wlh zai bata kuɗin.”

 

“Kaima da tuni ka je duk inda zaka je ka dawo, ka san halin Besty tunda tace baza ta ajiye ba, to; baza ta ajiye bane, ka je ka dawo Ni zan ajiye maka.”

 

“Ok. Shikenan sai na dawo.” Yayi maganar yana juyawa zai tafi tare da sanya hannu a aljihu yana zaro wayansa

 

Sai da ya tafi Arab ɗin tace, “bar ɗan iska, wlh bazan ajiye ba sai ya bani kuɗi, da ma ace ban san halin sa bane.”

 

Dariya Ibrahim yayi yace, “ke ma ba ki da dama Besty a kan kuɗi.”

 

Tura baki tayi tana tsikaro ɗankwalin ta a gaba tace, “Ah to, wa ke wasa da kuɗi? Ai Ni duk inda aka ce kuɗi, to; ba na wasa dashi, a kan kuɗi zan iya yin komai.”

 

“Gaskiya ne Besty.” Yafaɗa yana ƙyalƙyale wa da dariya, sai kuma ya sauko ƙasa ya duƙa setting kunnen ta yana raɗa mata, “kamu nayi miki fa, wlh wani babban Alhaji na samo miki me shegen maiƙo.”

 

Waro fararen idanunta tayi da cewa, “kai don Allah? Ba na son wasa fa me sunan Baba?”

 

“Ah to, wanne wasa zan yi miki? Kin san bamu saba haka ba, wlh da gaske nake miki, irin waɗanda kike so, bari ki ga.” Sai ya ciro wayansa ya danna kana ya nuna mata hoton wani ƙaton Mutum tulele wanda da ganin sa ka san ba ƙaramin Mutum bane, kuɗi ya zauna masa sosai, don ma a inda ya ɗauki hoton kana gani ka san waje ne na alfarma

 

Amsar wayan tayi da sauri tana dubawa

 

Sai shi kuma ya ci gaba da cewa, “a Abuja yake zaune, amma shi mutumin Bauchi ne, a can iyalan sa suke, ɗan hannu ne wlh sosai, nima ɗan small ne ya haɗa Ni da shi sabida ya san Mutumin, yace wlh ba ƙaramin kuɗi zamu samu a hannun sa ba idan har na tura ki wajen sa, shiyasa da gaggawa na amsa tayin nasa saboda Ni kaina sai da nayi bincike before in zo wajen ki.”

 

Ci je baki tayi tana ɗauke idanunta a kan hoton da ta kafa masa, ta mayar a kan Ibrahim tana cewa, “Ni ba wannan nake son ji ba. Ka tabbatar akwai samu a ciki sosai? Don ka san hali na ba na son harkan ƙaranta.”

 

“Haba tawan, kin san na fi kowa sanin halin ki, akwai nace miki, but kinga mutane sun soma yowa nan, ki bari zamu ƙarisa zancen idan kin koma gida, ko kuma muyi waya kawai.”

 

Baki ta washe cikin farin cikin da ya bayyana a kan kyakkyawar fuskarta tace, “ok. I would also prefer that.”

 

“Yauwa Besty na.”

 

Da haka suka ci gaba da magana suna dariya, yayinda wurin sai cika da jama’a yake yi, duk maza ne manyan samari da magidanta, har da masu kuɗi ƴan hannu zuwa siyan awaran nata suke yi don kawai suyi harƙalla da ita

 

Nan da nan sai awaran nata ya ƙare ko kiran sallan magriba ba’a kai ga yi ba, shiyasa ta tattara kayanta ta ba wa wani almajiri yayi mata gaba da su, sannan suka tako da Ibrahim zai raka ta gida

 

Wani saurayi ne a mota ya bi bayan su, ya tsayar da motan a kusa da su yana cewa, “ƴan mata ji mana.”

 

Tsayawa suka yi yayinda suka zuba mishi idanu. Gaba ɗayan su kallon yanayin tsarin zubin motan nashi suke yi tare da hasashen yanayin sa; kuma ba tare da tayi yunƙurin amsa shi ba

 

Sai ya sakar musu murmushi tare da cewa, “Aboki na ɗan bamu wuri mana, zan yi magana da ƙanwar taka.”

 

Shima murmushin Ibrahim yayi tare da shafa kansa yace, “ok ba damuwa Alhaji.” Sai ya kalli Arab yace, “Besty Ni zan wuce gida, zamu yi waya kawai.”

 

“Ok bye.” Ta furta cikin yanga tana ɗaga masa yatsu

 

Bayan wucewan sa ne sai saurayin ya buɗe mata ƙofan mazaunin banza yace, “shigo mana Gimbiyya.”

 

Sai da ta kalle sa ta tura baki cikin jan hankali kana tace, “a nawa?”

 

Murmushi yayi yace, “duk farashin da kika yanka min Ni na amince.”

 

“But ban yi tunanin da sauƙi hakan ba.” Tayi maganar tana kafe shi da kallon ta da ke rikita su

 

Still murmushin yayi yace, “ai ke ce kin fi ƙarfin hakan, ko dukiyata kika ce in ba ki domin mallakar ki; da gudu zan aikata hakan.”

 

“Allah ko?” Tayi maganar tana zaro ido waje kaɗan mai nuni da mamakin maganar sa, yayinda fuskarta ke ɗauke da shu’umin murmushin ta da ba kowa yake iya gane ma’anar sa ba

 

“Da gaske, kin wuce haka a wuri na, but na san tsokanata kike yi ke ma kin san da haka, ba Ni ne farkon faɗa miki ba.”

 

“No you were the first to tell me, in your mouth I began to hear, kuma kaga dole in yi shakkar amincewa da kai At the same time, bare yanzu da kidnappers suka yi yawa.”

 

Dariya yayi saboda yanda tayi maganar, cike da burgewa yake kallon ta yace, “haba Princess ban zaci haka a gare ki ba, anyway idan ba ki sanni ba Ni na san ki, cuz na daɗe ina bibiyan ki, kuma ina zuwa wurin nan sosai, but sai dai ba ki taɓa kula dani bane, but idan ma Ni kidnappers ne ai ba laifi bane, a kanki zan iya sace ki idan har hakan zai saka zuciyata ta samu natsuwa.”

 

“Ko?” Tayi maganar tana sake ware mishi kyawawan fararen idanuwanta a kanshi

 

“Yeah, please ki shigo ba don hali na ba, wlh na ƙosa in ji ki a cikin motata, idan ba haka ba zuciyata zata fashe.” Sai ya ɗaura hannun sa a setting zuciyar nasa tare da ƙarisa zancen da cewa, “saboda ba ki ji yanda take bugawa bane, saura ƙiris…” Sai ya cije leɓe yana sake faɗin, “wash Allana!”

 

Dariya tayi kaɗan cike da jan aji, sai tayi wal da idanunta cike da yanga tace, “afwan kyakykyawar saurayi, bari in shigo.”

 

“Yauwa ko ke fa.” Yafaɗa yana washe baki, “wlh bazan iya jure jan ajin nan naki ba, gwara ki taimaka min.”

 

Sai da ta shiga ta zauna before ta juya tana kallon sa da kyakkyawar murmushinta me shiga rai tace, “to kayi haƙuri na ce ai, gani na shigo.”

 

“To amma zan nemi wata alfarma.”

 

“Why not.” Tace tana ɗage kafaɗa

 

“Zan ɗan gyara parking sabida naga kamar a hanya nake.”

 

“Ok ba damuwa.”

 

Sai ya yiwa motan key ya ja zuwa gefe sannan ya faka, tare da juyowa kacokan yana kallon ta cikin tsantsan sha’awa da nuna zalaman sa, inda kyakykyawar murmushin sa ke gudana a kan fuskarsa

 

While itama yanda yayi tayi, ta zuba mishi narkakkun idanuwanta masu shegen kaifi da ratsa ɓargon Mutum, wanda lokaci ɗaya suke sake zautar da ma’abocin kallon su

 

Shiru suka yi babu mai cewa uffan a tsakanin su, inda suke sakarwa juna wani irin kallo me tattaro saƙonnin zuciyoyin su suna aikawa juna. Yayinda murmushin farin ciki ke kwance a kan fuskartasu cikin shauƙi; tamkar sun san juna da daɗewa a yanayin kallon da suke yiwa kansu

 

Tsawon mintuna biyar before ya ja wani irin dogon numfashi yana lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta, sai ya buɗe baki cikin wani irin yanayi yace, “Gimbiyyata.”

 

Ɗan waro idanu tayi cikin salo da guntun murmushin ta tace, “har na zama taka?”

 

“Eh mana, wace ce Gimbiyyata idan ba ke ba? Ai babu wata mace kyakykyawa a faɗin duniyar nan kamar ki, ba ki san jimawan da nayi ina bibiyan ki ba ko? Uhmm zuciyata ta jima da makancewa a kanki, ban yi tunanin zan iya kaiwa har wannan lokacin ban sanar da ke abun da ke raina ba, sai dai kuma ɗan wata tangarɗa da aka samu wanda ya hana Ni bayyanuwa a gaban ki, amma yanzu gani na dawo.” Sai yayi shiru yana sake zuba mata idanu kamar yanda itama take mishi wani irin kallo me saka shi a wani irin ɓigirin da be taɓa tsintan kanshi ba, “na san za ki yi mamaki idan nace miki na san komai game da ke, Arab zuciyata ta makance a tun sanda idanuwana suka soma tozali da kyakykyawar fuskarki, na kasa natsuwa tun sanda na ganki, wlh ban taɓa jin wata ɗiya Mace ta shiga raina kamar ki ba, na so in jure amma na kasa, don Allah na zo da ƙoƙon barata ki taimaka ki amshe Ni a matsayin masoyin ki na gaskiya, ina ƙaunar ki! I love You A’isha Humaira, i love You with all my heart!”

 

Lumshe manyan idanuwanta tayi sabida jin sunan da ya kira ta, ba kowa yake kiranta da sunan ba sai mahaifin ta, shi kaɗai ne ba ya kiranta da suna Arab sai A’isha Humaira. Buɗe idanun tayi ta zuba mishi tana kallonsa da shu’umin murmushin ta da a koda yaushe yake saman fuskarta. Bata yi magana ba illa kallonsa da take yi tamkar zata cinye sa babu wani ɗar ko jin kunya a tare da ita, hasali ma tsantsan gogewa ne irin nata na bariki

 

Shi kuma sai yace, “kin yi shiru Gimbiyyata? Ko so kike yi zuciyata ta buga?”

 

Wani guntun murmushi ta sauke before tace, “Ina wani tunani ne a raina that’s the reason da ka ji nayi shiru.”

 

“Amma ba ki yarda da Ni bane? Wlh ina ƙaunar ki! Don Allah kiyi min magana ko ya ya ne inji daɗi.” Sai ya saka hannayen sa biyu ya kamo nata da take faman shafa fuskarta dasu, ƙurawa junan su idanu suka yi na ƴan seconni before yace, “ina sonki! Me kike so in yi miki da za ki yarda?”

 

Still murmushin tayi tana cije baki tare da sake narke idanuwanta tana wani luuu dasu tamkar zata rufe sai kuma ta buɗe su, cikin wani irin kallonta me sake zautar da duk ma’abocin da tayi masa tare da fitar dashi a wani yanayi lokaci ɗaya

 

Wanda hakan ne ya soma tasiri a jikinsa har be san sanda ya sake damƙe hannayenta a cikin nashi ba yana wani irin murza mata cike da wani irin feelings da ya taso mishi

 

Hakan yasa tayi murmushi kaɗan tana cewa, “har yanzu ba ka sanar da Ni kai wane ne ba balle in so ƙulla alaƙa da kai.”

 

“Haba idan har don wannan ne kar ki wani damu, na sha’afa ne, suna na Tariq… Tariq Muhammad Auwal, Ni mutumin Samaru ne, ina zaune tare da iyaye na da ƴan uwana, kuma abun farin cikin bani da Mata.” Ya ƙare maganar yana mata murmushi

 

Yayinda ita kuma ta saki dariya kaɗan wanda ya bayyana haƙoran ta, still idanuwanta a cikin nasa, sai kuma ta sake sakin murmushinta tana janye hannayenta a cikin nasa tace, “meyasa za ka taɓa min jiki ba tare da mun yi farashi ba? I’m an expensive girl.”

 

“Don’t worry, I have the money to pay you until you say it’s enough.”

 

“Really?” Tayi maganar tana ɗan waro idanu waje wadda ya zame mata ɗabi’a; kuma yake ƙara mata kyau ainun

 

“Yeah. You just give me a chance.”

 

Leɓen ƙasan bakinta ta shigar cikin bakinta tana tsotsa cikin salo da jan hankali, sai kuma ta cire tana ɗage kafaɗa tare da faɗin, “fine. I answer you both hands.”

 

Dariya yayi cikin farin ciki tare da cewa, “gaskiya ke ta daban ce, na ji na ƙara sonki matuƙa, but yanzu kin bani damar taɓa hannun ki ko?” Ya ƙare maganar yana kashe mata ido ɗaya da murmushi a fuskarsa

 

“Me kake ci na baka na zuba? kar ka damu, har sai ka gaji da taɓawa.”

 

“Haba idan ko haka ne bazan taɓa gajiyawa da taɓa kyakykyawar halitta kamar ki ba, ba ki san yanda kike da matsayi a cikin raina ba.”

 

Bakinta ta ɗan turo gaba before ta ja numfashi tace, “ok. Zan tafi, ka ga dare yayi.”

 

“To, babu ko ɗan kiss haka zamu rabu?”

 

Ƙura masa idanu tayi tana kallonsa na ɗan wani daƙiƙu, sai ta saki wannan shu’umin murmushin nata kafin tace, “me kake yiwa sauri haka? Za ka samu abun da ya fi kiss ma, but not know.”

 

Langaɓe kai yayi, yayi mata fuskar tausayi tare da cewa, “Please Princess.”

 

“No. Zan ta fi.” Ta furta tana ƙoƙarin buɗe ƙofan

 

Sai yayi saurin kamo hannun ta da cewa, “haba Gimbiyyata kar ki tafi, I’m sorry to, na daina maganar.”

 

Hannunta ta zame tana kallon fuskarsa

 

Sai yayi mata murmushi yace, “to ki bani Numban ki mana.”

 

“Ok.” Kawai ta furta tare da karanto mishi numbern

 

Sai ya rubuta sannan ya buɗe lockern motan ya ciro kuɗi 20k ya miƙa mata

 

 

Ta sanya hannu kuwa ta amsa ko jan aji bata yi ba, sai ga kyakykyawar murmushin ta ya bayyana a kan fuskarta, yayinda take bin sa da kallo me ban sha’awa tace, “tnx. Bye.”

 

“Bye dear.” Sannan ya ɗaga mata hannu yana mata murmushi har ta fice, sai da ya ga tafiyar ta before ya ja motan ya bar wajen cike da farin ciki a zuciyarsa.

 

 

 

 

_Don’t forget to follow me on Wattpad, and voted . Tnx._

[

 

*RUƊIN DUNIYA!*

 

 

 

 

*NA_NAFISAT ISMA’IL LAWAL*

_UMMUDAHIRAH_

 

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT *

 

 

 

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*

 

“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS)“`

 

/

 

*P.W.W*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_________________________

 

*BABI NA UKU*

 

_______________A bakin ƙofan gidan su ta ci karo da mahaifinsu, wanda yake zaune tun dawowar shi masallaci sallan isha’i, ya shimfiɗa tabarma yana shan iska. Ganinta ne yasa ya kira sunan ta yana cewa, “A’isha Humaira daga ina?”

 

Yamutsa fuska tayi tana ɗan sosa kanta tace, “Baba daga wurin saurayi na.”

 

Shiru yayi yana kallon ta don ya san halinta ba kunya ne da ita ba, bata da ɓoye-ɓoye abin da ke ranta shi take faɗa. Ganin zata wuce ciki sai yace mata, “dawo ban sallame ki ba.”

 

Dawowa tayi tana faman tura baki tare da ƙunƙunai

 

“yanzu A’ishah Humaira abun da kika ɗaukarwa kanki kenan? Ban hana ku yawon dare ku kai war haka baku dawo gida ba?”

 

“To Baba ai nace maka wajen saurayi na naje, ba fa yawo na je ba ina nan bakin layi.”

 

“Shikenan. Allah ya shirya, idan kin shiga ki kawo min abinci na in CI a nan.”

 

Wucewa tayi ba tare da ta amsa mishi ba ta shige gidan

 

Yayinda shi kuma ya girgiza kansa a ransa yana takaicin wannan rayuwa na yaranshi, ya rasa yanda zai yi ya gyara su, ko yayi ma a banza tunda uwarsu tana warware wa, duk halin su ɗaya gaba ɗaya babu me kallonsa da wani ƙima, sun riga sun taso ba sa shakkar shi bare tsoron shi, tamkar shi ba mahaifinsu ba saboda yanda suka ɗauke shi, ko ince yanda uwar su tayi musu tarbiyya, Firdausi ce kawai ta fita zakka a cikin su, kuma duk hakan yana faruwa ne kasancewar sa me tsananin haƙuri kuma mara faɗa, yana da sauƙin kai ko kaɗan be iya faɗa ba bare ya ce zai ɗauki mataki a kansu, yana ƙaunar yaranshi shiyasa a kullum fatan shiriya yake musu, duk da abun yana matuƙar damun shi domin yanzu babu inda gidan shi bai zagaya ba a faɗin arean nan, kowa ya san yaran shi basu da tarbiyya, wasu ma don rashin ta ido har taren shi suke yi a hanya suna mishi zancen Yaran shi basu da tarbiyya, ya kan yi kuka wani lokacin saboda be san yanda zai yi ba, yayi nasihan duk wani abu da ya kamata uba yayi; yayi musu, amma uwar su ta ɗaure musu gindi, bai da wani fawa a gidan, bare yanda ta mallake shi sai abun da tace, shiyasa be da kataɓus a gidan, ko ya so ɗaukar mataki mummuna ba ya iyawa, sai dai ya zira musu idanu yana musu addu’ar shiriya, ya san wata rana Allah zai dubi maraicin sa ya shirya mishi su, fatansa kenan a rayuwa. Numfashi kawai ya ja yana ci gaba da jan carbin shi.

 

 

 

 

 

 

*******

 

Arab kuwa tana shiga gidan ko sallama bata yi ba

 

Yayinda su Inna suna zaune a tsakar gidan a gindin bishiyar Mangwaro da ke dirke a tsakiyar gidan suna shan iska, kasancewar garin akwai zafi sosai. Daga ita har su Ummu suke zaune suna cin abinci a cikin faranti ɗaya, tunda haka suke yi a koyaushe, Inna Harira Mace ce mai tsananin ƙaunar yaranta, akwai sabo mai ƙarfi a tsakanin su, ta ɗauke su tamkar ƙawayenta ne, a rayuwa babu abin da take ɓoye musu nata haka su ma, suna rayuwar su ne cikin ƙaunar juna da tsantsan shaƙuwa a tsakanin su, tun farko haka ta sabar musu cin abinci tare a kwano ɗaya, sai dai idan ɗaya ba ta nan ne ko tayi dogon zango shine zasu ci babu ita, ko kuma su jira ta idan ta dawo su ci tare, amma duk runtsi dole sai kaga cikin su wasu sun ci tare, shiyasa shaƙuwa me ƙarfi ta shiga tsakanin su, su kansu yaran suna ƙaunar junan su matuƙa, kuma basu yarda wasu sun shigo rayuwar su ba, kaf ɗinsu babu mai ƙawa sai junan su, su ne ƙawayen juna su kashe tare su binne tare, shiyasa duk da babu tarbiyya a tare dasu amma suna rayuwar farin ciki a gidan su, basu damu da surutun mutane a kan rayuwar su ba, a ganinsu rayuwar su ne babu wanda ya isa ya hana su tafiyar da ita yanda suke buƙata, duk wanda yace zai taka su sai inda ƙarfin su ya ƙare, kaf ɗinsu basu da haƙuri suna rayuwarsu tamkar ƴan tasha, musamman Arab wacce duk ta fi su sheɗananta, ita abun kunya gaba ta ba shi ba baya ba, ba ta shakkan kowa sannan babu wanda zai mata a duniyar nan bata mayar mishi ba, komin tsufan shi komin girman shi, wannan sun sha a nonon uwar su ne. Domin idan wani ya taɓawa Inna Harira yara abu me sauƙi ne ta bi Mutum har gida ta ci mishi mutunci ta uwa ta uba, kowa ya sansu a kaf anguwan su har da maƙota, ba a taɓa su su ƙyale, an sha yin dambe da Inna a kan yaranta, bata da mutunci ko kaɗan a kan ka taɓa mata Yara, musamman zata saka wandon dambe ta bi ka har gida ku caku. Shiyasa yanzu da yaran nata suka girma wani lokacin tare suke zuwa ayi ta dambe ana faɗa a anguwa, in dai aka tayar da husuma a anguwan nan to kowa ya san ƴan gidan Malam Iro mai kifi ne, su ne ba sa barin anguwan ta zauna lafiya, an sha kaisu police station a kan husuma, su yanzu har sun saba da kowacce fitina ba sa tsoron ko wanne shege, bare yanda kaf ɗinsu Yaran suna da samari a station ɗin, ana kaisu za’a sako su, wani lokacin ma ƴan sandan ba sa jirgawa ko nan da can da su, a wajen zasu kashe maganar, shiyasa ma ƴan anguwan suke musu kirari da gidan Fitina. Wannan kaɗan kenan daga rayuwar iyalan Malam Iro.

 

 

Kai tsaye wajen su ta nufa tana cewa, “Inna wai Baba yace a aika mishi da abincin sa waje.”

 

“Ga yi can a ƙofar ɗakina ki ɗauka ki kai mishi.”

 

Gyalenta ta cire ta jefa a saman tabarman da suke kai, sannan ta nufi coolarn abincin Baban nasu ta ɗauka ta fita da gudu ta kai mishi. Tana shigowa nepa suka ɗauke wuta, dogon tsaki ta ja tana cewa, “ka ga ƴan iskan mutanen nan, daga shigowa kuma sai ɗauke wuta? Ga shi ina son saka caji.”

 

“Haka suke yi matsiyata, yanzu suka gama wasa dashi, ga shi kuma sun ɗauke, idan ba wasa ba kuma sai tsakar dare su dasu kawo wutan nan.” Cewar Ummu bayan ta haɗiye abincin bakin ta

 

Inna kuma tace, “Auta kunna mana Gen ɗin kafin ki zauna, Allah yasa ma muna da ishashshen mai a ciki.”

 

Wucewa tayi ta kunna sannan ta wuce ta wanke hannu ta zo ta zauna, ta saka hannu a abincin tana cewa, “wai Aunty Zahra aina kika samu wannan guy ɗin ne?”

 

Zahra kallonta tayi tace, “wai Salisu? Ba ki sanni dashi bane? Shi ne fa wanda nace miki mun haɗu a bikin gidan Jamila ƴar gidan sanata da muka je mata, Ni ban ma san waye ya nuna mishi gidan mu ba, muna dai waya dashi kusan kwana biyu, sai yau kuma na ganshi ya zo.”

 

“To shi ɗan gidan waye ne? Ba ki bani labari ba Mamana?” Inji Inna tana washe baki

 

Dariya suka yi gaba ɗayansu

 

Yayinda Zahra take basu labarin Salisu da aikin da yake yi

 

Itama Arab kuɗin da Tariq ya bata ta ciro ta miƙa wa Inna duka tana cewa, “nima kamun wani nayi wlh, duk da ban san ɗan waye ba amma da alamu yana da fararen.” Ta ƙare maganar tana dariya cike da farin ciki

 

Haka su ma suna taya ta

 

Inda Inna tace, “ai na san ki Autana babu wasa a lamarin ki, sai dai idan ba ki fita ba, Allah yayi muku albarka baki ɗaya, haƙiƙa na haifi yara masu farin jini, hakan a jini na yake wlh, Ni na san da haka, duk wani me baƙin ciki sai dai ya mutu, ga shi yara mata suna share min hawaye.”

 

Dukkan su murmushi suke yi suna sauraron Innar tasu. Da haka suke ta hira abin su

 

Yayinda Arab ta tashi ita ta nufi bayi, bata jima ba ta fito ta ɗaura alwala ta wuce ɗakinsu ta rama sallan da ake bin ta na magriba da isha’i. Sai ta zauna a ɗakin tana waya da Ibrahim

 

A nan yake sake bata labarin Mutumin da ya samo mata, da komai nashi sai da ya faɗa mata, sannan yace, “ta kira shi su soma magana yanzu.”

 

Tace, “a’a sai zuwa gobe.”

 

Dariya yayi yace, “ai girman ki ne Besty na, ina jin daɗin jan ajin nan naki, gaskiya ke ta daban ce a cikin mata, har yanzu ban ga kamar ki ba, kina lokaci ƴan mata na, kin fi ƙarfin Yaro sai dai baban Yaro.”

 

Itama dariyan tayi tana cewa, “Besty kana fasa min kai da yawa.”

 

“Ai matsayin ki ne My Besty, ke ɗin ce ban san yanda zan kwatanta ki ba, amma wlh kin kere duk wata Mace da na sani a rayuwata, Allah ya barmu tare.”

 

“Amin.” Tayi maganar tana dariya, “shiyasa nake ƙara sonka Besty na.”

 

“Nima haka Besty, i love You wujiga-wujiga, ba don kin fi ƙarfi na ba da tuni nayi wuff da ke.”

 

Dariya take yi sosai

 

“Allah kuwa My Besty, yanzu meye tukuici na?”

 

“Oh Besty! Ba ka yin abu don Allah fa na lura?”

 

Kashe murya yayi tare da cewa, “haba dai, Ni na isa? Ai duk abun da zan miki don Allah ne, kin san Ni na sanki, Ni da ke ba ta ɓaci, Allah ne ya haɗa jinin mu, abun da kike so shi nake so, haka kuma abun da kike ƙi shi nake ƙi, ke ma kin sani ai.. kawai dai kwaɗayin nawa ne ya tashi wlh.”

 

“Uhmm shikenan. Let’s meet tomorrow.”

 

“Ok. But ba ki bani labarin Mutumin da kuka haɗu ɗazu ba?”

 

“Ai yanzu zan faɗa maka ka san ba na ɓoye maka komai.” Daga nan ta ba shi labarin yanda suka yi. Basu jima suna wayan ba ta katse sabida ganin baƙuwar number tana kiran ta. Bayan ta ɗauka sallaman Tariq ya doki kunnen ta, rage murya tayi tana kwanciya a kan gadonta, yayinda ta juya baya ganin Ummu da Zahra sun shigo ɗakin. Haka tayi ta wayanta baza ka taɓa cewa waya take yi ba. Sun raba dare suna tare da Tariq before su yi sallama ta kwanta

 

A time ɗin su Ummu su ma har sun yi barci.

 

Zuwa washe gari kuma suka ta fi makaranta. Dayake ita Arab text suke yi a school, saura two weeks su fara Exams, daga nan kuma sai su shiga S.S 3. Ƙarfe sha biyu ta dawo gida

 

A lokacin Baba yana gida domin dawowar shi kenan daga wajen suyan kifin sa; yake sanar da Inna halin da Firdausi take ciki. Mijinta Nafi’u ya kira shi yace mishi, “bata da lafiya, yanzu haka suna asibiti an kwantar da ita, duk da dai yace jikin da sauƙi yanzu.”

 

“To Allah ya sauwaƙe.” Cewar Inna tana wucewa cikin kichen tare da cewa, “Auta har kin dawo?”

 

“Eh Inna.” Ta furta itama tana shigowa tare da zama a kan kujeran zuƙuno, sai kuma ta kalli Babansu tace, “sannu Baba.”

 

“Yauwa Aisha Humaira. An dawo?”

 

Fitowar Inna tana kallonta tace, “wai ba karatun ne kika dawo da wuri?”

 

“Akwai mana, muna yin text ne kuma ba wani abu ake yi ba shiyasa na dawo.”

 

Baba ya kalli Innan yana cewa, “yanzu babu wanda zai je a cikin ku ne? Ai ya kamata ko ɗaya daga cikin yaran ne ya je ya zauna da ita, itama zata ji daɗi idan ta ga ƴan uwa, Mijin yace min idan da hali wata ta zo ta zauna da ita tunda kullum damuwar ta yaran nan ne, ta ce a tura mata ɗaya a ciki.”

 

Mitsitstsike baki Inna tayi da cewa, “a tura wa? Ai babu inda zasu je tunda kowacce ba zaman banza take yi ba, in ba iya shege ba ai ta san babu wanda zai je yayi mata bauta tunda ta san suna makaranta, kuma sana’ar nawa ubanta zai yi min?”

 

Shiru Baba yayi be iya cewa komai ba illa kallonta da yake yi, sai kuma ya girgiza kanshi sabida takaicin Inna

 

Arab tace, “Inna ni zan je domin dama ina son zuwa, yakamata ace ko sau ɗaya ne mun je amma har yanzu bamu ƙara zuwa gidanta ba tun auren.”

 

“To makarantar naki fa Auta? A’a babu inda za ki je.”

 

“Allah Inna zan je, ai Ni nace miki ina son zuwa, kuma makaranta bani da matsala da hakan tunda Exams ya rage kuma ba yanzu zamu yi ba, har zan je in dawo, zan mata kwana biyu sai in dawo.”

 

Baba washe baki yayi yace, “yauwa A’isha, ai zata ji daɗi idan ta ganku, to yaushe za ki tafi in ba ki kuɗin mota?”

 

“Ka bar shi kawai Baba ina da kuɗi, idan rana tayi sanyi sai in wuce.”

 

Inna tace, “don dai kin matsa ne babu yanda zan yi amma wlh da baza ki je ba, har wani ciwon ne sai an je an ganta?” Sai ta ja tsaki tana wucewa

 

Baba kuwa girgiza kansa kawai yayi, sai kuma ya kalli Arab da ta miƙe zata wuce yace, “bari in koma wajen sana’a na, kafin ki tafi zan dawo sai muyi sallama.”

 

“Sai ka ce wani tsiya za ka bata idan ka dawo ɗin? Aikin banza aikin hofi.” Inna tafaɗa bayan ta fito daga ɗaki tana dallawa Baban harara

 

Baba kuma bai ce komai ba ya wuce ya tafi

 

“Arab ki zo ki ɗibi abincinki ki ci, sai ki zo ki amso min ƙanƙara wajen Lantana in sa a kunun nan. Na san yanzu zasu dawo tunda sun ce ƙarfe ɗaya zasu gama karatun.”

 

“To ina zuwa.” Arab tafaɗa daga cikin ɗaki, kayan makarantarta ta cire ta saka wani doguwar rigan Abaya wanda ya fito mata da kyakkyawar shafe ɗin jikinta, sosai rigan ta kama ta saboda yanda aka matse mata dai-dai jikinta, sai ta ɗaura ɗankwalin Abayan a saman kanta da ke ɗauke da ƙananun kitso da aka yi mata, sun zubo har kafaɗunta, kana gani ka san ta haɗa jiɓi da Fulani saboda yanda gashin suka nannaɗe gunin sha’awa, sai dai ƙarshen kitson duk ya tsefe duk da kuwa kasancewar kwana biyu kenan da Ummu tayi mata, kasancewar ita tana son kitso shiyasa ko yaushe za ka ganshi a kanta duk da gashin nata ba ya zama da kitso, yanzu idan ma ta bar shi kafin sati ya tsefe da kanshi don da kanshi yake tugewa, shiyasa bata da wahalan ta sake wani kitson tunda tana da masu yin mata, har Inna tana yin mata, ita kaɗai ce me son kitso a cikin su, don su Zahra ma bai dame su ba sun fi son barin kansu a haka tunda su ma nasu gashin ba ya son kitso, ko sun yi warware wa yake yi, duk Innarsu suka biyo. Flat shoes ta saka a ƙafanta sannan ta fito

 

Inna tace, “nace ki bari ki ci abinci sai ki wuce.”

 

“A’a ba na jin yunwa, bari in amso miki, idan su Aunty Ummu sun dawo sai mu ci tare.”

 

“To.” Innar tafaɗa tana wucewa kichen ta sauke abincin siyarwan da take yiwa su Ummun

 

Itama kuma Arab ta sa kai ta fice. Bata jima ba ta dawo tunda a maƙotan su Lantanan take

 

Time ɗin su Ummu sun shigo su ma. Shiyasa suka zauna suka ci abincin tare

 

A nan Arab take sanar da su, “zata je gidan Aunty Firdausi.”

 

Zahra tace, “ai da na bi ki kuwa, amma babu hali tunda karatu yayi zafi, sai dai ki gaishe ta, nima zan kira waya in Yi mata ya jikin.”

 

Itama Ummu tace, “Auta ki gaishe ta don Allah, ko zuwa weekend ne zamu zo, amma yaushe za ki dawo?”

 

“Kwana biyu kawai zan yi, tunda kun ce zaku zo sai in tsaya mu dawo tare.”

 

“Eh hakan yayi, Allah ya kaimu Asabar zamu zo sai mu dawo a ranan.”

 

Inna dai na jinsu bata ce musu komai ba. Sai da ta gama abun da take yi sannan tace, “ga abincin nan na gama don Allah ku tashi ku wuce, kunga har biyu tayi.”

 

“To Inna.” Duk suka amsa mata

 

Yayinda Zahra CE ta soma tashi tayi alwala ta shige ɗaki

 

Itama Ummu alwalan tayi; tayi sallan sannan suka shirya suka fita

 

Arab tace, “Inna bari in Yi wanka kawai in wuce, ki bani dubu goma a kuɗin jiya saboda babu kuɗi a hannu na.”

 

“Ki shiga ɗaki ƙasan Matashi na suna nan na ajiye a wajen.”

 

“To.” Tace tana wucewa. Sai da ta ɗauki kuɗin ta je ta saka a jaka sannan tayi wanka ta shirya. Riga da wando ta saka masu tsantsi, rigan milk color da flowers a dai-dai setting ƙirjin ta da aka yi da kalan maroon color kalan wandon, wanda shima ƙasan wandon aka yi flowers da milk color, kayan sun yi mata kyau ainun sabida kasancewar ta me sura me kyau wanda duk namijin da ya kalle ta sai kyawunta ya bizge shi, bare uwa uba yayi arba da kyakykyawar cuty face ɗinta, fuskar nan nata ta sha makeup me ɗaukan hankali, bakinta sai shaining yake yi, gyalen kayan ta ɗauka kalan milk ta yafa a kanta sannan ta jefa jelan a gefe da gefen kafaɗunta, sai ta saka takalmi masu shegen tsini white color, sai da ta jefa chewing gum a bakinta domin ita mayyar cin chewing gum ne, ya zama sabon ta ba ta rabo dashi, Hangbag ɗinta ta ɗauka na takalmin shima kalan fari ta rataya, sannan ta fito cikin yauƙinta ta wuce ɗakin Inna

 

Inna na ganinta ta washe baki saboda farin ciki, “ga farar zinariya alkyabbar Mata, kin kerewa kowacce Mace sai dai su biyo bayan ki, kinga yanda kika haɗu kuwa?”

 

Dariya tayi tana taunan chewing gum ɗinta ƙas-ƙas-ƙas, sai tace, “na san haka Innata, amma nayi  zam-zam ko babu wata mishkila?” Ta ƙare maganar tana juyawa a gaban Innar

 

Inna tace, “babu abun da yayi saura, ai ke me kyau ce Autana, ko ba ki yi kwalliya ba komai yin miki kyau yake yi, Allah yasa ki samo mana wani me gwaɓi-gwaɓi wanda zai kai ni Makka da Madinah.”

 

Arab tayi dariya tace, “Inna kar ki damu insha Allahu zan cika miki burin ki wata rana.”

 

“Kai Allah ya amsa addu’ar ki Autana, amma ki kula fa don bazan so wani abu ya same ki ba, Allah ya tsare.”

 

“Amin Inna.” Sai tayi dariya tana cewa, “to Inna ba ki ce in gaishe da Aunty Firdausin ba?”

 

Taɓe baki tayi tace, “to har sai na ce? Ai ta san ina gaishe ta”.

 

Sosai Arab take dariya a wannan lokacin, tace, “Innarmu na Aunty, Allah ya bar ku tare, zan ce kina gaishe ta sosai, zan biya sai in Yi sallama da Baba a kasuwan. Babu wani abun da zan kai mata ne?”

 

“To me nake dashi da zan ba ki? Gaisuwar ma ta isa.”

 

“To Inna na tafi, bye.” Sannan ta fice ta shiga ɗakin su, jakarta da ta zuba kayan sakawanta ta ɗauka, ƙaramar Trolley ne, ta janyo ta fito. Har waje Inna ta raka ta suka sake sallama sannan ta tafi.

Leave a Comment

error: Content is protected !!