Hausa Novels

Rudin Kuruciya Hausa Novel Complete

Rudin Kuruciya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: rudin kuruciya

Page 1

 

Harabar makaranta ce babba sosai, ɗauke da manyan ajujuwa, da dogayen ƙawatattun benaye, wanda suka sha tiles, a kowane aji yana ɗauke da na’urar sanyaya guri, ko ina ƙal ƙal babu datti ko ƙazanta, kallo ɗaya zaka yiwa ɗaliban dake zirga zirga, da ita kanta makarantar kasan cewa tabbas duk ɗan dake wannan makaranta, ɗan masu ido da kwalline, ko wanda ya tsaya masa ya tara masu gidan rana.

 

Ɗalibai mata sanye suke da shuɗin skirt me cizawa ga mata, maza kuma wando, se farar riga ‘yar ciki me dogon hannu, se kuma ‘yar saman kalar skirt ɗin, se ƙaramin farin hijabi ga musulmai mata, saka ƙaramin hijjabin ma ra’ayi ne, babu tilas saka shi ga ɗaliban, da yawa ɗalibai matan skirt ɗin nasu iya gwiwa ne, wasu kuma da kaɗan yafi gwiwar su, da yawansu Uniform ɗin nasu sun matsesu matuƙa, kuma galibin ɗalibai mata suna cire rigar saman kayan su bar ta cikin suna yawansu.

 

Da yawa masu wannan shigar, za kaga matasan ‘yan matane, da suke kan tashen balaga, gasu ‘yayan gata, dan haka suna ɗauke da ƙirane me matuƙar kyau da ɗaukar hankali, haka ɓangaren ƙananan yaran ma da suke firamare, wasunsu kansu ko ɗan kwali babu, kai kace makarantar ƙasashen ƙetare ne, saboda yanayin tsarin makarantar da ɗaliban da ke ciki.

 

Ɗaliban sunata hada hadarsu, sun fito break, wasu na ciye ciye, wasu wasanni wasu kuma suna hira, ƙararar sautin jiniyane ya karaɗe ilahirin makarantar, wanda hakan ke nuna lokacin komawa aji yayi, domin cigaba da ɗaukar darasi.

 

Nan ɗaliban suka shiga komawa cikin azuzuwansu, dan cigaba da ɗaukar darasi.

 

Gaba ɗaya makarantar tayi tsit, an koma aji, dan tuni wasu sun fara ɗaukar darasi ma.

 

wata tawagar ɗalibai maza da mata ce ta ɓullo harabar makarantar, a ƙalla sun kai su goma, suma sanye da Uniform suna tafe suna hirarsu suna ƙoƙarin bin wata baranda dan komawa ajin su.

 

Wani malami ne yai musu tsawa da harshen turanci “hey, from where are you? ”

 

Wata zaƙaƙura a cikinsu ta kalli malamin cikin iyayi tace. “we went out for breakfast”

 

‘who gives you the permission to go out? Don’t you know that you supposed to be in your classes by now?”

 

Malamin ya sake maganar cikin tsawa.

 

Wani ɗan kyakkyawan saurayi ne a cikinsu ya ɓata rai sosai, ya kalli malamin Yace “No need to seek permission from anyone, we have the right to go where ever we want at any time to have our break, we are semifinalist, and the teachers have to wait for us to come back, because our parents pay for it, hope I made myself clear?”

 

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

Cikin zafin rai malamin Yace “Are You stupid?, is this the way you supposed to talk to me? Semi finalist ɗin banza, me ka taka a harkar karatu da kake gayamin wai You Are semi finalist”

 

Matashin ya ɗage kafaɗa alamar oho maka, sannan Yace “it seems that you are New here, anyway this is our policy you have to go and know more about it”

 

Shewa sauran ɗaliban suka dinga yi suna.  “Weldone The Lion prince, munga yazo da zafinsa yana ji da izza, zamu sauke masa duk wannan zafin kan nasa”

 

Suka tafi suka bar malamin baki buɗe yana binsu da kallo, a ransa yace ‘in dai dagaske haka yaran nan suke, to basu da tarbiyya sam”

 

Ya juya ya nufi ofishin Director.

 

Sukuwa ɗaliban ajinsu suka nufa, suna sake koɗa wannan matashin,ya kallesu Yace ‘kuje class, ni zan tsaya inga sanyin idaniyata”

 

Yai maganar cikin sanyin murya, wanda ke tabbatar da abunda yake faɗa har ransa.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Ɗaya daga tawagar ɗaliban ya daki kafaɗarsa yace. “shegen kaya, kai dai ka dage akan yarinyar Nan’

 

Murmushi yayi, bece komai ba suka wuce aji, shikuma ya nufi wata hanyar.

 

Window wani aji yaje ya tsaya ta waje, ba malami a Ajin, ɗaliban ajin kowa na abunda yaga ze fishseshi, wasu na hira, wasu na waƙe waƙen su, suna rawa.  can ya hango ta a gefe ɗaya ita kaɗai, ta duƙufa tana ta rubuce rubuce, ta nutsu sosai ta maida hankali akan abunda take yi, fito ya yayi da ƙarfi wanda seda ya janyo hankalin da yawa daga cikin ɗaliban, suka waiwayo.

 

Da sauri ita ma ta juyo dan ganin wanda yake fiton,  ta ganshi a jikin window yana kallon ta.

 

Yai mata alama da hannunsa da tazo, mmurmushi tayi, sannan ta miƙe tana nufar hanyar fita daga ajin, cikin takunta na ƙasaita me cike da nutsuwa da kamala, me tafiya da zuciyarsa.

 

Gaba ɗaya ya ƙura mata ido, gani take duk takun da take tamkar tana girgiza jikinta ne, ta fito tazo inda yake tsaye tace ‘good morning’

 

Seda ya gama ƙare mata kallo sama da ƙasa, sannan ya murmusa ya shafi sumar kansa da ke ta ƙyallin mai yace “Morning my love, baki zo class ɗinmu ba yau, lafiya dai ko?”

 

Tai murmushi, wanda ya sanya fararen haƙoranta bayyana, ta ɗan rausayar da kanta  tace “lafiya ƙalau classwork nakeyi, shiyasa”

 

Yai murmushi Yace “kinci Abinci kuwa?’

 

Ta jinjina masa kai alamar eh.

 

Ya ɗan gyara tsayuwarsa yace “Ƙarya kike, naji a jikina bakici komai ba, ga Abinci nan nazo miki da shi, kije ki ci, sannan ki bani classwork ɗin, zanje aji in Miki”

 

Cikin shagwaɓa tace “what if I was asked, to explain how I did it?”

 

Yace “You should tell them, that am the one who did it, bana son gaddama, karɓi takeaway ɗin nan, ki ɗakkomin littafin, zanje class ɗinmu in miki ki zauna ki huta”

 

Tasan halinsa, idan ta cigaba da jayayya ransa ze iya ɓaci, dan haka ta koma class ɗin nasu ta ɗakko masa littafin da take classwork ɗin, ta dawo ina da ta barshi a tsaye ta miƙa masa, ya karɓa ya bata ledar hannunsa, ta karɓa cikin jin kunya tace “Thank you very much”

 

“Meye wani Thank you kuma? Is my responsibility to take care of you baby, idan na gama zan kawo miki, koma class Ina kallonki, kar wani abu ya taɓa min ke”

 

Tai murmushi ta juya, yabi bayanta da kallo, seda taje ta zauna yana kallonta ta window, sannan ya juya, ya koma nasu ajin.

 

“Yallaɓai yaran nan basu da tarbiyya sam, baka ga yadda suke min magana ba ɗazu, duk premises ɗin makarantar nan be isa suyi break ba se sun fita? Kuma su dawo lokacin da suka ga dama, ana kallonsu na musu magana suna nema su zageni”

 

Director ya gyara zaman Glass ɗin fuskarsa sannan Yace “Naji abunda duk ka faɗa corper Nazir, Amma abunda baka sani ba shine, wannan yaran na ss2 lallaɓasu muke mu rabu lafiya, dan ko na samansu ss3 basa bamu ciwon kan da suke bamu, duk yaran makarantar nan da yawansu yaran manyane, sedai kusan na Ss2 iyayensu manyane sosai masu faɗa aji, taɓa yaran nan tamkar barazana ne ga makarantar nan, shiyasa muke binsu sannu a hankali, hadda ‘ya’yan ministoci da kwamishinoni a cikinsu”

 

“amma Yallaɓai, bafa karatu kawai suke buƙatar a koya musu ba, harda tarbiyya fa, wannan zasu iya baka kunya wataran a gaban wanda bekamata ba, makaranta ba gurin koyon karatu bane kawai, yarane matasa da ake sa ran sune Manyan gibe, yakamata su tashi da tarbiyya”

 

“Nazir, yaran nan jarine a gareni da makaranta ta, daga ‘ya’yan manyan sojoji sena ‘yan siyasa, kuma duk competition da aka fita da su se an ciyo shi, ga iyayensu suna sakin kuɗi sosai, mezesa in bari a ɓata musu rai? Kuma duk wata tarbiyya ai ana musu a gidajen su, su sun san yadda suke tarbiyyar yaransu, amma taɓa yaran nan matsala ne babba, kawai ka dinga kau da kanka, kana haɗawa da haƙuri dan ba kowane ubane yake yadda da a horar masa da yaro ba”

 

Corper Nazir yabi director da kallon mamaki, be sake cewa komai ba ya tashi ya tafi, dan ze shiga Jss2 yanzu.

 

Shikuwa matashin yaron nan ajinsu ya koma yaje ya duƙufa, yana solving classwork ɗin daya karɓo.

 

“Prince, waime kake yi ne haka?”

 

Cewar wani daga ɗaliban, ya ɗago idanunsa ya ɗan kalleshi Yace “Farhan na kewa classwork”

 

“amma meyasa kake mata? Naga yarinyar dai itama ƙwaruwace a ajinsu fa”

 

“eh nasani Amin, na kai mata Abinci ne, idan ban karɓa na mata ba, ba zata maida hankali taci Abinci ba”

 

Al’amin da sukewa laƙabi da Amin yace “gaskiya kana yin yarinyar nan over prince”

 

“Ƙwarai kuwa, Farhan is my wife to be inshallah”

 

Kwashewa da dariya Amin yai yace

 

“How? Yaushe ka gama karatu, kayi jam’ia ka aureta? Jiranka zata tsaya yi, just enjoy your life with her, beauty one’s are yet to born, zaka samu wata zazzafar da fita ne ka Aureta”

 

Prince ya girgiza kai Yace “I have a plan for our feature, dan haka bana wannan lissafin da kake yi, Farhan kawai”

 

Amin Yace “gaskiya ne mutumina, Allah ya kaimu lokacin, amma dai wannan kamar tayi ƙanƙanta kasamu mace me suna mace mana”

 

Prince yace “Amin, ka kalli Farhan da kyau, za’ayi babbar mace nan gaba, nidai a haka nake sonta, size ɗinta da komai yai min yadda nake so”

 

“To Allah ya barku Tare”

 

“Ameen ya Allah”

 

Ya duƙufa seda ya kammala mata class work ɗin, kasancewar yana da yawa , yana kammalawa ya miƙe ya tafi ajinsu Farhan, kamar kullum tana zaune a gefe ɗaya, ‘yan ajinsu basa wani shiga harkarta kasancewarta ba ‘yar masu kuɗi kamarsu ba, saboda ita scholarship ne ta samu, saboda wani competition da taci, aka bata scholarship ɗin, gata suna ganin bata waye ba kamar su, dan haka basa involving ɗinta a sabgarsu, itama bata musu shishshigi kullum tana gefe, ba ruwanta da kowa se karatunta, sekuma Yanzu da Prince ya shigo rayuwarta.

 

Duk hayaniyar da ake a ajin, Prince na shiga sukayi tsit, dan juniors suna tsoronsa, saboda akwai dealing, baya son raini sam.

 

Ya ƙarasa seat ɗinta ya zauna a kusa da ita Yace  “Baby gashi na gama miki” yai maganar yana ajiye mata littafin.

 

Ta sa hannu ta ɗauka tana dubawa, ta ɗago tai murmushi tace “Nagode sosai Prince”

 

Maimakon ya mata magana, seya kashe mata ido ɗaya.

Sunkuyar da kanta tayi cike da jin kunya.

 

Yace  “ya kika wani sunkuyar da kai? Ina fatan babu wata matsala dai ko?”

 

Ta jinjina masa kai alamar eh.

 

Yace “Ai idan ma akwai matsalr bazaki iya faɗa ba, ke naga maganar ma wahala take baki Farhan, nasan maybe yanzu malami ze shigo muku, bari in koma ajinmu, amma kisani zanzo musamman kimin hira, ina son dinga jin muryarki sosai, saboda tana sani nutsuwa”

 

Ji take kamar ƙasa ta tsage ta nutse dan kunya, gashi ya tsareta da idanunsa, gaba ɗaya nauyinsa take ji.

 

Corper Nazir ne ya shigo ajin, ɗaliban suka miƙe suna gaisheshi, banda Prince dake zaune, Nazir yabishi da kallo, yana tunanin meya kawo wannan fitsarraren yaron kuma Jss2.

 

Prince ya miƙe ya kalli Farhan yace

“Mu haɗu in an tashi’

Daga nan ya juya ya fice abunsa.

 

Corper Nazir Yace  “Ke Farhan, meye haɗinki da wannan yaron mara ɗa’a?”

 

Farhan ji tayi kamar Nazir ya soketa, Sadik ɗinta ne wai mara ɗa’a.

 

Shiru tayi ba tace komai ba, “Am talking to you Malama” yai maganar cikin tsawa.

 

Sunkuyar da kai ta sake yi, jikinta na rawa amma ta kasa furta koda kalma ɗaya.

 

Daga can gefe wani ɗalibi yace  “sir saurayinta ne”

 

“Saurayi kamar yaya?”

 

“Ai duk makarantar nan, babu wanda be san budurwar prince bace, saurayinta ne” cewar ɗalibin.

 

Aikuwa Cikin faɗa Nazir Yace  “baki da hankali ne? Kina Jss2 harkinsan wani saurayi? Shi iyayenki suka turo ki yi? Kuma ma wannan shegen yaron mara ɗa’a kike kulawa, zakiga saurayi sena zauna da babanki na gaya masa, come out here and kneel down, stupid girl kawai, zaki ɓata rayuwarki kina jss2 amma kin san wani saurayi”

 

Gaba ɗaya ido ya dawo kan Farhan, ta fito jikinta na rawa, kamar ta nutse tazo gaban class tayi kneel down.

 

Nazir ya ƙaremata cin mutunci tsaf a gaban ‘yan ajinsu, taji zafin abinda malam Nazir ya mata, dan haka nan da nan se ta fara hawaye, wani na bin wani kuka sosai, kamar ƙaramar yarinya.

 

“Will you shut up your mouth, stupid girl kawai, a haka kamar mutuniyar kirki, kin biyewa wannan sakaran yaron”

 

Sadik daya koma ajinsu kuwa, ya tarar classmates ɗinsa maza sun haɗa kai suna kallo a waya, matan kuma suma sun ja nasu gurin, suna Magana ƙasaƙasa suna shewa.

 

Ya ƙarasa ya leƙa abunda su Amin suke kallo, sedai ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, yaja uban tsakiya ja da baya.

 

Amin ya ɗago ya kalleshi Yace  ‘babban yaro ya dai, ku matsa masa yazo ayi dashi mana”

 

Cikin damuwa ya girgiza Kai Yace  “Ni bazan iya kallon wannan shirmen da kuke kallo ba”

 

Nasir ya kalleshi yace  ‘ji banza sekace ba namiji ba, wannan ba shirme bane alaji, just come an enjoy”

 

Sadik ya girgiza Kai Yace  “I can’t, kuma Allah ya shiryeku, dan ubanku zaku makance da wuri ne, kawai ku kewaye waya kuna kallon blue Film, shegu zakuyi bayani idan Allah ya tona muku asiri”

 

Amin Yace  ‘dan Allah malam ƙara gaba, tunda bazaka kalla ba ai shikenan”

 

Sadik ya samu kujera yai zamansa ya ɗakko wayarsa, yana Game.

 

Seniors ne suka shigo class ɗin Ss2, kansu ɗauke da colored ties, mazan kuma huluna alamun prefects ne, wata zaƙaƙura a cikinsu cikin harshen turanci kamar baturiya tace  “who ever knows he spoke vanacular, should come out and pay his 500, before I call names”

 

Banza sukayi musu, basu ko ɗago kaiba balle su tanka musu.

 

Nan ta ƙame ta fara kiran sunayen wanda sukayi Hausa, Sadik yana ji aka faɗi sunansa, amma ƙafafunsa na kan benci yana cigaba da game ɗinsa.

 

Babu sunan kowa a ciki sena Sadik, dama shi duk wata doka a makarantar nan, shine ke fara karyata a makarantar nan.

 

Ɗaya daga cikin prefects ɗin yace “Sadik, magana fa ake maka”

 

“Bazan biya ba” ya basu amsa

 

“You Are still speaking vanacular , you know you must pay’ cewar wadda ta kira sunayen.

 

“Ke wallahi bazan bayar ba, baza’ayi turancin ba, yaren uwatane kona ubana? Ko meye haɗina da wasu turawa da senayi yarensu, har a wani dinga cewa wanda yayi hausa seya biya, baza ai turancin ba, kuma bazan biya ba tunda ba ubankine yake bani kuɗin ba”

 

Dukan benci tayi ta nuna Sadik tace “don’t insult me Sadik”

 

‘idan na zagekin me zakiyi? Jeki gayawa duk uban da zaki gayawa, yarene a makarantar nan se wanda naga dama zanyi, bazan turancin ba, uban turancin, ke uban mungo park da sarauniyar England, ƙaryar banza kawai ba za’ai turancin ba”

 

Fitina sosai Sadik yaso tayarwa, dan da an ƙyaleshi ze iya dukan yarinyar nan.

 

Wata ɗalibace ta shigo ajin tana faɗin  “Prince, ga Farhan can an sata kneeldown a rana, tayi wa wannan corper ɗin laifi, kuma wai tayi vanacular ance ta biya kuɗin vanacular tace “bata da kuɗi”.

 

Ashar Sadik yayi Yace  “what! Farhan ɗin?”

 

Beyi wata wata ba yai waje, hakan yai daidai da shigowar wani malami, da aka sanar masa ana rigima da Prince a ajinsu, ya taho yai maganin abun, sukayi karo da Sadik a hanya, yana masa magana amma yayi masa shiru, ya ture malamin yai hanyar ajinsu Farhan da hanzari.

 

Baiwar Allah, Farhan tana ƙofar ajinsu tayi kneeldown tana ta zubar da hawaye, ga zafin rana.

 

Sadik yaji tamkar ya ɗora hannu a kai yai ihu, ya ƙarasa inda take da sauri Yace “waye ya saki wannan abun?”

 

Kasa magana tayi, se kuka da takeyi beyi wata wata ba, ya jata office ɗin director.

 

Sadik se huci yake, director ya kalleshi Yace “Prince Sadik, what’s wrong? Why is she crying?”

 

“Sir, ka shiga tsakanin mu da wannan new corper ɗin, why Will he gave her such kind of punishment, and that stupid Tina humilate her because of 500 naira, is she not a human being?”

 

Director ya kalli Farhan dake ta faman kuka, idonta yayi jawur, shidai yasan Sadik bashi da alaƙa da Farhan,  amma yana gudun ɓacin ran wannan yaron, Yaron fitainanne ne, akwai taurin kai da rashin ji, sedai uwarsa zata iya ɗaure malami akan sa, ana ji da shi a gidansu kamar ɗan gwal, sama baya taɓuwa yarin nan, dan haka Yace “is ok my Boy, zan ɗau matakin daya dace, kayi haƙuri , Farhan kiyi haƙuri kinji”

 

Farhan dai ba tace komai ba, se kuka da take yi, Sadik yai waje a zuciye tabi bayansa, ya rakata har bakin toilet,yace ta shiga ta wanke fuskarta, ya jirata ta shiga ta fito, ya kalleta Yace

“duk wanda ya kuma saki wani purnishment a makarantar nan, koya miki ba daidai ba kizo ki gayamin kinji ko? Ko ”

 

Ta jinjina masa kai, Yace  “Akwai inda yake miki ciwo ne?”

 

Cikin muryarta me narkar da zuciya tace  “kaina yana ciwo, da ƙafata”

 

“shikenan, muje class ɗinmu ki huta in Baki paracetamol”

 

Ba musu ta bishi, dan bata iya kaucewa umarnin Prince Sadik, ko da wasa bata zaton zata iya kaucewa umarninsa.

 

Tabbas nickname ɗin nasa na Prince ya dace da shi, saboda gashi Young adult be gaza shekaru goma sha shida zuwa sha bakwai ba, amma yana jida kansa, giyar arzikin iyayensa da tashen balaga na matuƙar ɗawainiya da shi.

 

Suka je ajinsu, ya bata paracetamol, ta karɓa ta sha, ta kifa kanta akan benci ta lumshe idanunta.

 

Babu daɗewa, aka kunna jiniya, alamar lokacin tashi yayi.

 

Farhan ta tashi, Sadik yaje class ɗinsu Farhan ya ɗakko mata jakarta, suka fito harabar makarantar, inda dandazon motoci suke taruwa, domin ɗaukar yaran gata.

 

Farhan tace “bani Jakar, zanje in hau napep in tafi gida”

 

“No ga motar gidanmu nan, muje semu saukeki a gida, kinga baki da lafiya”

 

A ɗan tsorace tace  “za’ayi min faɗa fa a gida, idan aka ganni a motar ku”

 

“Karki damu, ba wanda ze miki komai”

 

Haka yasa ta shiga motar, shima ya shiga, ta gayawa direban inda gidansu yake, suna tafe Sadik yana jera mata sannu, Tare Da yin ƙwafa lokaci zuwa lokaci.

 

Aka zo bakin layin gidansu Farhan, ta kalli Sadik tace  “Nagode sosai Prince”

 

“Ki kirani da suna irin na masoya mana, haba my Farhan” yai maganar yana sunkuyo da fuskarsa daidai tata.

 

Rufe fuskarta tayi cike da jin kunya, yace  “idan baki faɗa ba, zamu yi ta zama a motar nan ne fa” yai maganar yana sake kafeta da idanunsa kamar wani babban saurayi.

 

“Toni me zance?”  Tai maganar a shagwaɓe.

 

Kasa magana yay, se ido da yake binta dashi, a hankali yace “koma meye kice kawai my wife”

 

“Thank you my Love” ta faɗa cike da jin kunya, kamar wadda tai saɓo, kasancewar shine mutum na farko data furtawa kalma me girma haka.

 

Ya lumshe idanunsa Yace  “ina sonki my Farhan, jeki gida kar ayi miki faɗa, idan aka yi miki faɗa bazanji daɗi ba”

 

Tai murmushi ta buɗe motar, ta fita har direban zeja motar, Sadik Yace  “tsaya inga ta shiga gida mana”

 

Direban ya tsaya yana mamakin, wannan taɓara da ƙarfin hali  gami da tsaurin ido na wannan Yaro, ko secondary school be kammala ba, amma yasan ya tsara yarinya ta soshi, itama kuma ta biye masa maimakon ta maida hankali akan karatunta, Koda yake duk RUƊIN ƘURICIYA ke damunsu.

 

Sadik kuwa bin bayan Farhan yayi da kallo, duk da ta ɗora ƙaton hijjabi akan uniform ɗin nata, seda ya dena hangota sannan Yace  “mu tafi gida”

 

Direba yaja mota suka nufi gida.

 

Suna zuwa tangamemen gidan, direban ya kutsa da motar yai parking, Sadik ya buɗe motar ya fito, kai tsaye cikin gidan ya shiga, sakamakon shriye shiryen bikin Yayansu da ake, mutane suna ta shige da fice a gidan nasu.

 

Yana kallon mutane a falo, amma ya hau bene, ba tare da ya kula kowa ba.

 

Yayar mahaifiyarsa ce ta hangoshi ta shiga kiran sunansa  “Sadik, kana kallon mutane amma ka wuce baka kula kowa ba?”

 

“Zan kulaku anjima idan kuka ragu, duk kun cika mana gida”

 

Be jira me zata ce ba ya ƙara gaba, ɗakin mahaifiyarsa ya shiga, ya tarar da ita tana ɗakko kaya a wardrobe ɗinta, ta dubeshi tace  “sweetheart, ka dawo ya school ɗin?”

 

Cikin shagwaɓa Yace “Am so much tired , gashi duk an wani zo an cika mana gida da hayaniya”

 

“Sorry, kasan shirye-shiryen bikin yayanka ake yi, dole mutane suzo amma ko zaka ɗakinka na BQ ka kwanta ka huta?”

 

Girgiza kai yayi Yace  “No, a ɗakin Daddy zan wanka in kwanta, a kawomin Abincina nan”

 

Ta shafa sumar kansa tace  “considered it done my auta”

 

Yace  “Mother dan Allah a miƙomin jallabiyata, idan kin sauka ƙasa”

 

Ta jinjina masa kai, Sukayi murmushi tare, ta fita daga ɗakin.

 

Banɗaki ya shiga ya watsa ruwa, ya fito daga shi se gajeren wando ya tsaya a gaban mudubi, yana ƙarewa kansa kallo, Farhan ce ta faɗo masa rai, a hankali ya lumshe idonsa, yana saƙawa da warware abubuwa da dama a ransa.

 

Buɗe ƙofar ɗakin akayi tare da yin sallama, ya amsa ba tare da waiga ba, saboda yaga me shigowar ta mudubi.

 

“Sadik manya, ashe ka shigo amma ba labari, ko neman mutane baka yi”

 

Murmushi yayi Yace “ai ban san kina gidan nan ba, na dawo kawai na tarar an wani cika falon, babu ma hanyar da zanbi in wuce ɗakina, shiyasa kawai na taho nan”

 

Ta ƙarasa inda yake tsaye, ta ajiye kayan Abincin, sannan ta ɗora masa ash ɗin Jallabiyarsa a kafaɗarsa tace “gashi nan, Mother ce tace in kawo maka, sarkin rashin son Mutane”

 

Yai murmushi, yana ƙoƙarin zira jallabiyarsa, ta ƙura masa ido sannan tace  “Semi finalist, next year by now insha Allah an kusa grad, kaima ka wuce Dubai”

 

“Waye yace miki zanyi SS3, this year zan gama makaranta ni”

 

Tace  “meyasa zaka gama this year? Jumping zakayi kenan?”

 

Ya juyo ya fuskanceta sosai sannan Yace  ‘Khairat, jumping zanyi in kammala secondary School this year insha Allah, saboda Aure nakeso, Aure zanyi nan kusa”

 

Kwashewa Khairat tayi da dariya tace  ‘look at you, dan kaga kana da girman jiki? Secondary school fa zaka gama, Yaya Usman ma daza’ayi Aurensa Yanzu, seda yayi PHD, wakake tunanin ze maka wani aure yanzu?”

 

Ƙurawa khairat ido yayi sannan Yace “kina ganin nayi ƙanƙanta inyi auren ne?”

 

‘ƙwarai kuwa, guda nawa kake zakayi zancen wani aure? Better build your future my friend, and stop talking this rubbish”

 

Tai maganar tana dariya, ta bar ɗakin.

 

Sadik ya daɗe a tsaye a gurin yana tunani, sannan ya ɗakko sallaya ya tada salla, bayan ya idar yaci Abincinsa ya kwanta.

 

Farhan ma harta koma gida, ta shirya ta tafi islamiyya, tunanin Sadik ɗinta ne a zuciyarta, tana tuna yadda yake yawan kyautata mata, amma abun tambayar anan shine, zasu iyayin aure kuwa ita da Sadik? Ita dai tana jin ƙaunarsa sosai a cikin ranta.

 

Se yamma sosai Sadik ya tashi, yai sallar la’asar sannan ya sakko ƙasa, har yanzu gidan da mutane sedai sun ragu ba kamar ɗazu ba, Yayyansa ne maza zaune tare da Yayar mahaifiyarsu, suna shirya atamfofi a cikin akwati, wanda za’a kaiwa Usman na lefe.

 

Sadik ya nemi guri ya zauna, yana bin kayan da kallo.

 

Mamansu Khairat ta kalli Sadik tace “dan ƙaniyarka ina maka magana ɗazu, amma kamin banza ko?”

 

Yai murmushi Yace ‘na gajine, kaina na ciwo, gashi kuma an cika falon, shiyasa ban tsaya ba, wai wannan kayan duk na lefen ne?”

 

Maman Khairat tace  ‘eh gasu nan, jibi zamuje mu kai masa insha Allah”

 

Usman Yace “Autan mother Babu ko kara, ko ‘yar sarƙa baka siya ka bani ba, a matsayin gudunmuwa”

 

Sadik Yace  “gaba ɗaya fa siyayyar nan kaɗan ce akayi maka a Nigeria, duk a waje aka yota, kowa yazo baka kuɗi kawai yake kaida Mummy, kuma kace Sena saimaka abu na  baka duk kuɗinka Bross”

 

Faruk Yace  ‘ji ɗan rainin hankali yaron nan dan Allah, duk gidan nan babu wanda ake sakarwa kuɗaɗe kamar ka fa”

 

Usman yace  “wallahi kuwa, yaron nan kuɗine dashi kamar banza a account bema san me zeyi dashi ba”

 

Sadik ya karkace ya gyara zamansa akan kujera yace  “aini na dena cin kuɗina, nima lefe zan fara tarawa, next year by now za’a kamin nawa lefen”

 

Maman khairat tace “Usman, dan Allah makemin mara Kunyan yaron nan”

 

Sadik yace “Nifa Mummy dagaske nake, aure zanyi nima, zamu yi magana da Daddy idan ya dawo gari, nifa banƙi a haɗa bikina dana Yaya Usman ba”

 

Umar ne ya kai masa duka Yace “yi mana shiru dan ubanka, mara kunya kawai, ubanwa ze maka auren? Ko dan kana ganinka ƙato haka? Better concentrate on your study, shikansa Bross Usy seda ya haɗa PHD ze aure balle Kai, da yanzu Balagar ta zo maka ”

 

Harar Usman Sadik yayi Yace  “meye wani PHD?  Aure ze hanani karatune? Ai da sauƙi tunda balagara ta zo, Zan baku mamaki kwanan nan.

 

Ya miƙe yana zumɓura baki ya bar falon.

 

 

 

 

 

19 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!