Rudin Shedan Hausa Novel Complete
Rudun Shedan Hausa Novel Complete
RUƊUN SHAIDAN
*_Daga Alƙalamin gamayyar marubuta Tsaganyar Adabi*_
_*TAKEN MU SHINE*_: *Don Tsaftace Adabin Bariki*
*Marubuta labarin✍🏾*
*1-Usman Ango Ɗan Anacen Marubuta*
*2-Oum Mashkur*
*3-Abba Abubakar Grateful*
https://chat.whatsapp.com/GK28DnzrKgrKi3Jz9fm3uR
*Page 1 to 5*
*_Yusra_* event Centre, babban ɗakin taro ne da ke ɗaukar fiye da mutum ɗari uku a lokaci ɗaya, amma duk da haka sai da mutane suka cika shi tamkar babu masa tsinke a cikin sa.
Mafi yawan mahalarta wannan taro manyan Hajiyoyi ne matan wane da wane a cikin kasar nan, da kuma giggan ƴan daudu da su ka yi shiga irin ta mata, farat ɗaya idan ka kalle su, sai ka rantse da Allah suma mata ne.
Zaune a saman kujerun da Ango da Amarya ke zama idan ana shagalin bikin Aure, wata Attajirar mata ce mai suna Hajiya Hamida ƴar kimanin shekaru arba’in a duniya, da kuma wata budurwa mai suna Yusra ƴar kimanin shekaru goma sha tara a duniya, su duka sun zuba Ado na gani na faɗa, yayin da masu ɗaukar hoto, da kuma mahalarta taron ke ta faman ɗaukar su hoto.
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza uku Hausa Novel
-
Doctor Eshaat Hausa Novel
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi Hausa Novel
-
Aure da haihuwa Hausa Novel
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya Hausa Novel
-
Gangar Shedan Hausa Novel
-
Angon mata biyu Hausa Novel
-
A gidan mu take Hausa Novel
-
Bafulatanar Rugga Hausa Novel
-
Matar yaro Hausa Novel
-
Mr Bello Hausa Novel
-
Mijin Buzuwa Hausa Novels
-
Gidan Uncle Complete Hausa Novel
-
Yar aiki return Hausa Novel
-
Raggon namiji Hausa Novel
-
Uncle Datti Jikina yake so Hausa Novel
-
Fataucin Mata Hausa Novel
-
Juhud Hausa Novels Complete
-
Moon Hausa Novels Pdf
-
Yarima Ashman Hausa Novel
-
Bandirawo Hausa Novel
-
Matar makaho Hausa Novel
Powered by: www.mynovels.com.ng
Zuwa can sai mai gabatarwa ta karɓi na’urar yin magana ta fara da cewa,
“Mata dangi na, mata uwaye na, mata ƙawaye na, ni Dj Shatu ina taya Hajiya Hamida da Baby Yusra murna da zuwa ranar soyayya, kuma ranar nuna kauna, don haka jama’a a tafawa Hajiya Hamida da masoyiyarta yusra.”
Gaba ɗaya wajen ya ɗauki tafi da shewa a lokaci ɗaya, sannan sai mai gabatarwar ta ci gaba da cewa,
“A gurguje saboda lokaci na ƙurewa, muna gayyatar Hajiya Hamida da Yusra su jaddada ƙaunar da su ke wa juna a gaban ƴan uwa da abokan arziƙi, wanda hakan zai ba su damar kasancewar jini da hanta, kuma hakan zai tabbatar da babu sauran ƙawance tsakanin su da wasu”.
Wajen ya sake ɗaukar shewa a lokacin da Hajiya Hamida da Yusra su ka miƙe tsaye suna rike da hannayen juna, sannan suka fito tsakiyar filin taron, wurin da aka ajiye wani ƙaton Cake.
Da zuwan su sai mai gabatarwar ta umurci Hajiya Hamida ta yanka Cake ɗin ta bawa Hamida a baki, cikin bin umarni Hajiya Hamida ta sakawa Yusra Cake a baki, sannan mai gabatarwar ta ce da Yusra ta haɗa bakin ta da na Hamida ta ciyar da ita cake din.
Suna murmushi da kuma rike hannayen juna cikin shauƙin ƙauna Yusra ta haɗa bakin ta da na Hajiya Hamida. Sai Kwatsam kamar daga sama su ka ji ɗakin taron ya kaure da ihu, wanda hakan yasa Uwar taro Hajiya Hamida da Yusra su ka kai duban su wurin domin ganin ko me ke faruwa.
Ƴan sanda su ka gani mata da maza sun shigo cikin taron da sanduna suna bugu da kuma kama na kamawa, yayin da masu tserewa da ke tserewa. Kafin Mai Hajiya Hamida da Yusra su yi wani yunƙuri, sai ganin wata sangamemiyar ƴar sanda su ka yi a gaban su ta na saka masu ankwa a hannaye.
****
*Zaune* Zulfa’u take a kan kujera tana mai ƙurawa laptop ɗin dake gabanta ta idanu. Kai da ganin ta cikin wannan yanayi, a take za ka tabbatarwa kan ka da cewa ta daɗe da lulawa cikin tunani mai zurfi.
Bayan ta shafe fiye da mintina talatin a haka, kwatsam! sai ta ji wayar ta na ƙara alamar kira ya shigo. Ajiyar zuciya ta yi, game da jan ɗan ƙaramin tsarkin da bai da sauti mai ƙarfi, sannan ta kai duban ta gurin da wayar ta ke ajiye domin ganin waye ke kiran ta a dai-dai wannan lokaci da ta ke ƙoƙarin saƙa zaruruwan sabon sarƙaƙƙen labarinta.
Baƙuwar lamba ta gani a jikin screen ɗin wayar, wanda hakan ya sa ta yi murmushi, sannan ta kai hannu ta dauki wayar tare da amsa kiran, domin a zaton ta ɗaya da ga cikin masu jin daɗin labaran ta ne su ka kira su yi ma ta jinjina.
“Assalamu alaikum!”
Zulfa’u ta faɗa bayan ta ɗaga wayar, zuwa can sai ta ji an ce da ita,
“Yar ki Yusra ce ta sa a kira ki, yanzu haka tana tsare a hedkwatar mu ta yan sanda”.
Kafin ta ce wani abu sai ta ji an datse wayar, yayin da nan take ta ji numfashi ta na neman tsayawa ba tare da ta shirya ba.
Tambayar farko da ta fara zuwa a zuciyar ta ita ce, “Me Yusra ta aikata da Ƴan sanda za su kamata?”
Da sauri ta miƙe tsaye ta figi gale, tare da saka takalmi daban-daban ta fice daga gidan zuciya cike da tashin hankali.
Kai tsaye Hedkwatar ƴan sanda Zulfa’u ta nufa, da zuwan ta ba ta tsaya ko ina ba sai ofishin da ke kula da zirga-zirgar mutane, da zuwa sai ta hangi Yusra a cikin zugar ƴan mata da ƴan Daudu a bayan kanta.
Ido rufe ta nufi bakin kantar tana mai kiran sunan yar ta ta, yayin da ita ma Yusra ta nufo gurin da mahaifiyar tata take tana kwala mata kira.
Wata tsawa su ka ji an da ka masu, wadda dole su ka su shiga cikin hankalin su,
“Nan wajen ba wurin wasa bane, ko kuma wajen koke koke, saboda haka ku shiga hankalin ku”
Muryar wata yar sanda ce ta daɗi haka a lokacin da ta ke ganin suna neman wuce gona da iri.
“Me ta yi dan Allah aka kamata ?”
Zulfa’u ta tambaya fuska yamuste.
“Mun kama ta ne suna ƙoƙarin ɗaura Auren Jinsi tsakanin ta da Waccan Hajiyar”.
Ƴar sanar ta faɗa tana nuna Hajiya Hamida da doguwar sandar ta.
Zare idanu Zulfa’u ta yi, ta na mai dafe kirji, tare da cewa,
“Auren jinsi! Yusra da lesbian!” “Innnalillahi wa Inna ilahi raji’um!”
Wata ƙara ta ji a bayan ta wadda ta sa duk wanda ke wajen kai duban sa gurin da tsawsr ta fito, kwatsam sai Zulfa’u ta ga Ibrahim babban ɗan ta ɗan kimanin shekaru Ashirin da biyar, ƴan sanda sun zagaye shi da sanduna suna dukan sa ta ko ina.
Wannan dalili ne yasa ta manta da halin da Yusra take ciki, kuma fargabatar ta ƙara ƙaruwa fiye da farko, daga nan ba ta san lokacin da ta ruga da gudu gurin da Ibrahim yake tsugunne ba, da zuwa sai ta rungume ɗan na ta ta na kare dukan da ake masa.
Cikin zafin rai wani ɗaya daga cikin ƴan sanda ya janye ta gefe ɗaya, sannan ya ce da ita,
“Ka da ki sa ke shigar ma na aiki, idan ba haka ba mu haɗa da ke,
Hailala game da salati kawai Zulfa’u ke saki, sannan ta ce da shi murya a raunane,
“Dan Allah ku yi masa afuwa ɗa na ne, me ya aikata maku kuke dukan sa haka ?”.
Koda jin haka sai Ɗan sanda ya yi wa sauran abokan aikin sa magana da su daina dukan sa, sannan ya ce da Zulfa’u,
“Tun ɗazun muke nema ya bamu lambar ɗan uwan sa da za mu kira mu faɗa masa ya na hannun mu, amma ya ƙiya, sai ma yayi ƙoƙarin guduwa bayan ya daki ma’aikaicin mu. Laifin da ya aikata shine, mutanen unguwar ƙauna su ka kawo mana shine ya lalata wani almajiri.
*Ku biyo mu domin cigaban wannan labari mai ɗauke da ɗumbin darasi a cikin sa*
[10/12, 5:15 pm] +234 708 595 8544: *👺👹RUƊUN SHAIDAN👺👹*
*Daga Alƙalamin gamayyar marubuta Tsaganyar Adabi*
_*TAKEN MU SHINE*_: *Don Tsaftace Adabin Bariki*
*Marubuta labarin✍🏾*
*1-Usman Ango Ɗan Anacen Marubuta*
*2-Oum Mashkur*
*3-Abba Abubakar Grateful*
https://chat.whatsapp.com/GK28DnzrKgrKi3Jz9fm3uR
*Page 6 to10*
_*Fiye da*_ yadda mata ke daka a turmi, haka zuciyar Zulfa’u ta ringa bugawa, a wannan karo sai ta rasa me ya kamata tayi, salati, hailala koko istigifari ?.
Ƙarar da wayar ta tayi ne ya ɗan rage mata wutar da ke ci a zuciyar ta, cikin sauri ta kai hannu da nufin ta datse kiran, amma sai ta kasa sakamakon ganin sunan Nafisa Ƴar ta ta biyu da ya fito ɓaro-ɓaro a jikin screen ɗin wayar, ganin haka yasa gabanta ya yanke ya faɗi, nan da nan idanun zuciyarta suka fara gano mata lallai babu alheri a cikin wannan kira, wannan dalili ne yasa har wayar ta katse ba ta kasa ɗagawa.
Juyawa ta yi ta kalli Yusra dake layin manyan matan da wasu sun yi jika da ita, waɗansu sun yi ƴa da ita, waɗansu kuma sun girmeta da kuma tsararrakin ta, a hankali ta mayar da idanun ta gurin da Ibrahim ke a tsugunne ya na nishi sama-sama kamar wanda ran sa zai fita saboda tsabar dukan da ya sha, kafin sake yin wani yunkurin wani abu, sai ta sake ji wayar ta na ƙara a karo na biyu. Da sauri ta kai idanun ta jikin screen ɗin waya, a yayinda ta sake ganin Sunan Nafisa ya sake bayyana.
Hannu na kyarma ta ɗaga kiran, sannan ta kara a kunne tare da runtse idanunta ta na jiran ta ji baƙin labari, kamar yadda zuciyar ta ke faɗa mata, zuwa can sai ta ji an ce da ita,
“Hello ina magana da Maman Nafisa ce?”
A dabarce Zulfa’u ta ce da matar da ke magana da ita,
“Eh ni ce, me ya faru da Nafisar ne, kuma tana ina a yanzu ?”
“Kwantar da hankalin ki Maman Nafisa, ga ƴar ki nan tana samun kulawa a wajen mu, amma dai ki zo tana son ganin ki ta gaggawa”.
“Dan Allah ki faɗa man me ya faru da ita!”
Zulfa’u ta faɗa murya na rawa,
“Ba wani abu ba ne mai yawa, idan ki ka zo zaki gani da idanun ki”.
Har ta buɗe baki za ta sake magana, sai ta ji an kashe wayar, wannan dalili ne yasa ta ji jiri na neman ɗaukar ta, sakamakon ƙwalwar ta da ta kasa raba tarin saƙwanin dake shiga da fita a cikin ta, babban abinda ya hana zulfa’u faɗuwa ƙasa a wannan lokaci bai wuce salati da hailalar da take ja cikin zuciya da bayyane ba, bayan ta ɗan dai-daita numfashi ta da ya nemi tsayawa, sai ta sake kallon Yusra da ta duƙar da kai ƙasa ta ki yarda ta kalle ta, sannan ta mayar da duban ta gurin Ibrahim a karo na biyu. Kai ta jinjina cike da takaici da kuma rasa me ya kamata tayi masu a wannan lokaci, domin duk wani tunani na neman mafita a wajen ta ya tsaya cak.
A hankali ta rabu daga jikin bangon da take jingine, sannan ta nufi hanyar fita daga cikin Hedkwatar gaba ɗaya, yayin da zuciyarsa ke kuka marar misaltawa, sanann kuma fuskarta babu abinda take zubarwa sai hawaye.
Mai Adaidaita sahu ta tsaida, sannan ta ce da shi ya kaita Babbar Asibitin koyarwa ta Malan Aminu Kano. Cikin abinda bai wuce daƙiƙa goma sha biyar ba ta bayyana a Asibitin, kuma kai tsaye sai ta nufi ɗakin bada agajin gaggawa da Nafisa ke kwance,
Haidar ɗan ta na biyun ƙarshe, wanda ke bi wa Nafisa ta gani zaune a bakin gado ya zuba tagumi ya na kallon yayar sa a kwance shame-shame a kan gado tamkar ba ta da rai.
Da sauri Zulfa’u ta ƙarasa bakin gado ta zauna tare da kiran sunan zulfa’u, tana kuma mai sa hannunta saman kirjinnta domin a tunanin ta mutu bata da rai.
“Bacci take Umma!”
Haidar ya faɗa a cikin ƙaramar murya marar sauti.
“Me ke damuta ta ne?”
Zulfa’u ta tambaya ta na tsare Haidar da ido,
Shiru yayi ya kasa bata amsa, wanda hakan yasa ta ji zuciyar ta na cigaba da bugawa da sauri da sauri.
“Tambayar ka fa na ke Haidar ka na yi ka yi shiru ka kyale ni, sai ka ce ba da kai na ke ba”.
Hawaye ta gani jikin idanun sa, yayin da ya fice daga cikin dakin da sauri yana goge hawayen ba tare da yace da ita komai ba, wannan dalili ne yasa ta mike tsaye zuciya cike da fargaba ta bishi wajen.
Har ta buɗi baki zata sake jeho masa tambaya, sai ta hangi ɗaya daga cikin ma’aikatan jinyar da ke kula da marassa lafiyan wajen, da sauri ta ƙarasa wajen ta, bayan tayi mata sallama, sai ta ce da ita,
“Ni ce mahaifiyar Nafisa da wancan taron ya kawo bata lafiya,
Kai ta ɗaya ta dubi yanayin da Zulfa’u ke ciki, sai tayi ajiyar zuciya ta ce da ita,
“Sannu da zuwa, zauna ga waje!
Zama zulfa’u ta yi saman kujerar dake kallon matar, sannan matar tace da Zulfa’u,
Na ga duk kin rikice baiwar Allah, ki yi hakuri ƙaddara ce tana kan kowa, sai dai a kiyaye gaba, kuma a haɗa da addu’a”.
“Ban gane Ƙaddara ba, me ke faruwa da Nafisar ne ?”
Zulfa’u ta tambaya a lokacin da tashin hankali ya ida mamaye zuciyar ta,
Ganin haka yasa matar dai-idaita tunanin ta gaba ɗaya akan Zulfa’u, sannan ta ce da ita,
“Ki kwantar da hankali ki baiwar Allah, kina nufin ba a faɗa maki abinda ke faruwa da ita ba ?”
“Eh ba a faɗa man ba, kuma dan Allah ka da ki ɓoye man komai, dan wallahi zuciyata na iya bugawa”.
Shiru matar ta yi tana nazarin hanyar da za ta faɗawa matar maganar a cikin sauki, zuwa can sai ta ce,
“Yar ki ta yi ƙoƙarin shan maganin zubar da ciki domin ta zubar da cikin da ke jikinta, sai dai bata samu nasara ba, dalilin haka yasa maganin ya nemi ya raba ta da duniya gaba ɗaya!”
Miƙewa tsaye Zulfa’u ta yi tana numfashi sama-sama, har ta buɗe baki za ta yi magana, sai ta ji baƙin yayi mata nauyi, nan da nan sai ta fara gani gani dishi-dishi da idanun ta, a take ta ji juwa ta ɗaga ta sama ta rafka da ƙasa, daga nan bata ƙara sanin gurin da take ba.
Cikinsauri ma’aikatan jinyar wajen suka yo kanta, da zuwa suka cicciɓeta babu rai tare da ɗora ta saman gado, sannan suka fara kanikancin dawo mata da numfashi ta, yayin da Haidar ke gefe guda dafe da kai yana rusa kuka sakamakon ganin faɗuwar ƴan Bori da mahaifiyar sa ta yi, nan da nan nadamar abun da suka aikata da yayar sa Nafisa ta sake cika masa zuciya, yayin da kuma idanun zuciyar sa suka ringa hasko ma shi abubuwan da suka aikata tamkar yana kallon bidiyo.
*****
*_Abinda_* Haidar ya fara gani a idanun zuciyar sa shine, gashi nan akwance cikin dakin gidan su, a lokacin babu kowa sai shi kaɗai, yana kuma rike da waya yana karanta Wani littafi na Batsaa waya, idan ka kalle shi a lokacin zaka tabbatarwa da kan ka hankalin sa gaba ɗaya yana wajen littafin saboda shaukin da yake ji a cikin zuciyar sa da ƙwalwar sa.
Sunan labarin ‘Ni da Matar Yaya na kashi na ɗaya, bayan ya samu fiye da mintina talatin yana karanta wannan labari, sai ya ajiye wayar yana haiƙato abubuwan da suka faru a labarin tamkar gabansa ake yi, babban abinda yafi jan hankalin sa shine, yadda Matashi Yausf dake cikin labarin da ya karanta ya saci Pant da Brezia na matar yayansa, ya je ya yi amfani da su ya kawar da Sha’awar matar yayan nasa Amina da su.
Ajiyar zuciya yayi a lokacin sai ya fara tunanin ina ma zai samu damar da Yusuf ya samu? Tsaki ya ja tare da mikewa tsaye ya shiga ƙuryar ɗakin domin ya sa ya saka caji, sai kwatsam! Ba zato babu tsammani idanun sa suka kai kan Panties da Brezia sakagale jikin kusurwar ɗakin, wanda da gani ka san shanya su aka yi.
Tsayawa yayi cak yana kallon su, yayin da ya ringa jin wani abu kamar kwari na yi masa tafiya a cikin kwalwa, kuma nan da nan ya fara ganin tamkar labarin Yusuf ne zai faru dashi a zahiri, a maimakon ya nufi gurin da cazar sa ke maƙale, sai ya nufi gurin da aka ajiye Panties din da brezia ya kai hannu ya dauko su, sannan ya fara amfani da su kamar yadda ya karanta a cikin labarin.
Tuni yayi nisa a cikin shaukin Sha’awar da ya tayar wa kansa da kansa ta hanyar fara karanta littafin batsa, da kuma amfani da underwires ɗin yayar sa Nafisat, wanda hakan yasa ya daina ji da ganin komai sai ƴar uwar tasa.
Kamar daga sama sai yaji an ce da shi,
“Haidar me kake yi da Underwires ɗin na ?”
Firgigit yayi ya mike tsaye tare da ɓoye su, Nafisat ya gani tana kallon sa tana murmushi,
Nan da nan itama ta fara tunanin wani zazzafan labari da ta karanta na Matana Aure, wanda hakan yasa a nan wajen suka aikata muguwar aika-aika.
Kai Haidar ya dafe, sannan ya fara rera kuka da zuwa nan a tunanin sa, yayin da nadamar karanta labaran batsa ta zo masa a cikin zuciya karo na ba adadi, zuwa can sai zuciyar sa ta ce da shi,
“Ga shi dai shekara ɗaya da rabi kuna maganin sha’awar ku kai da ƴar uwar ka ba tare da kowa ya sani ba, daga ƙarshe rana ta ɓa ce ka yi mata ciki, cikin da ba zai taɓa fita ba sai dai a haife shi ko uwar sa ta mutu.
*Ku biyo mu domin cigaban wannan labari mai ɗauke da ɗumbin darasi a cikin sa*
[10/12, 5:16 pm] +234 708 595 8544: *👺👹RUƊUN SHAIDAN👺👹*
*_Daga Alƙalamin gamayyar marubuta Tsaganyar Adabi*_
_*TAKEN MU SHINE*_: *Don Tsaftace Adabin Bariki*
*Marubuta labarin✍🏾*
*1-Usman Ango Ɗan Anacen Marubuta*
*2-Oum Mashkur*
*3-Abba Abubakar Grateful*
10 to 11
Kuka haidar ya cigaba da yi tamkar ransa zai fita, babu shakkah sai yanzu ne yake nadamar abinda suka dad’e suna aikata wa, shin da wanne idon zai dubi iyayen sa ya fad’a musu shine uban cikin dake jikin yaya nafisa?
Da k’yar ya samu ya lallashi kansa ya mik’e jiki a matuk’ar sanyaye ya shiga d’akin da aka kwantar da mahaifiyar sa, mutanen dake gurin gaba d’aya suka bishi da ido cikin tsananin tausaya masa ganin yanda marasa lpy har biyu sun had’e masa gashi kuma mata ne.
Lokacin da ya shiga d’akin, zama yayi a gefen gadon nata ganin ta samu bacci ya dubi hannunta Wanda aka jona mata k’arin ruwa, a hankali hjy zulfa’u take sauke numfashi, kifa kansa yayi a gwiwar sa yana sauke ajiyar zuciya, tunanin kiran y’an uwansa ne yazo masa don haka ya lalubo wayarsa ya kira yayan su Ibrahim haka wayar ta gama ringing d’in ta har ta katse ba’a d’auka ba, saida ya kira kusan sau uku amma shiru don haka yayanke shawarar kiran yusra haka itama wayar ta k’araci ringing babu amsa, cikin tsananin fargaba gami da mamakin abinda ya hana y’an uwansa d’aukar wayarsa ya danna kiran number ihsan itama k’anwar sa ce ita ke binshi, yasani ita kam tana gida, ringing 2 ihsan ta d’auka tare da sallama ajiyar zuciya ya sauke yana runtse idonsa wad’anda tashin hankali suka maida su jajur, bai tsaya amsa sallamar da take yi masa ba yace. “Ihsan kina gida ko, don Allah kizo asibiti ki taimaka min umma da yaya nafisa duk babu lafiya.”
Daga can 6angaren ihsan ta fara salati jin haka yasa yayi saurin kashe wayar, har ga Allah ya tsani a tanbaye shi abinda ya faru saboda bai san amsar da zai bayar ba kuma yasan tana gama salatin abinda zata tanbaya kenan, bayan ya kashe wayar ya mik’e tsaye ya fara zagaye d’akin cikin tsananin damuwa babu shakkah ya sani duk cikin gidan su babu na kirki kamar ihsan, ya dad’e da sanin yaya Ibrahim yana huld’a da maza tun wata rana da yayi kuskuren shiga d’akin sa ba tare da sallama ba, haka yasha kama yusra suna romances da k’awayen ta, shi yasa yake jinjina musu shi da yaya nafisa da suka iya shafe tsawon shekara d’aya da wani abun suna alak’a ba tare da an fahimci komai ba, ashe su nasu asirin idan ya tashi tonuwa sai yafi na kowa muni, yafi jin kunyar mahaifin su fiye da kowa, a koda yaushe abban su bashi da magana sai ta su tsare mutuncin su, yau gashi suna shirin ajiye masa jika shege.
Ji yayi ya tsani kansa sannan ya tsani wayar sa, tun farko ita ce da kuma son zuciyar sa suka jefa shi cikin wannan masifar, a ransa kuwa babu Wanda yake tsinewa sai writer zuraifat itace wacce yake yawan karanta littattafan ta masu jefa shi cikin matsanancin feelings.
_____________________Ihsan dake zaune tare da abban su suna cin abinci dawowar sa kenan daga Abuja wajen taron su na y’an siyasa, kasancewar ya saba da rashin kulawar matar sa shi yasa ko nemanta baiyi ba sannan dama ya kwaso yunwa hakan tasa yaci birki wajen d’iyar sa ihsan dake zaune tana cin abinci ita d’aya, zuba mata ido alhj mukhtar yai jin irin salati da salallamin da take yi, ta ajiye wayar tare da kallon mahaifin nasu, shima abban tsare ta yayi da ido yana son jin abinda ya tayar mata da hankali lokaci guda, kafin yayi magana tace.”Abba wai umma da yaya nafisa suna asibiti ba lafiya. ”
Alhj mukhtar ya dube ta cikin mamaki sannan yace.”au dama zulfa’u bata gidan nan “?
Ihsan ta mik’e tsaye cikin damuwa sannan tace.” Eh, abba amma bata dad’e da fita ba kiran gaggawa akayi mata tace min bazata dad’e ba.”
Shima mik’ewar yayi sannan yace. “Okay tashi muje asibitin muga abinda yake faruwa.”
Abban ya fad’a tare da mik’ewa ya d’auki mukullin mota.
Tare suka fito suka taho asibitin Mlm aminu kano,alhj mukhtar yai parking motar sa sannan suka shiga ciki yana shirin kiran wayar haidar ihsan ta hango shi a reception ya kifa kansa da gwiwa har yanzu bai daina kuka da nadamar abinda suka aikata ba.
Kai tsaye wajen sa suka nufa, sam bai san sun iso ba kasancewar kansa na k’asa ihsan ta dafa kafad’ar sa tare da fad’in. “Yaya haidar ina su umman?”
Firgigit ya d’ago yana kallon su, sosai k’irjin sa ke bugawa musamman da yaga ihsan tare da mahaifin su, ganin hawaye jage-jage a fuskar sa tasa hankalin alhj mukhtar da na ihsan ya k’ara tashi, cikin sauri Abba yace.”me ya faru dasu ne aliyyu? Ko dai accident suka yi ihsan ta fad’a min umman taku bata dad’e da fita lafiyar ta klw ba.”
K’asa magana haidar yayi don bai san me zai cewa mahaifin nasu ba, hankalin alhj mukhtar ya k’ara tashi ko dai wani abun ya faru da matar sa da kuma d’iyar sa, yana shirin k’ara tanbayar haidar suka ji ance.
“Ina y’an uwan zulfa’u rabi’u su shigo tana son ganin su.”
Wata ma’aikaciya daga cikin nurses ne tayi maganar tana kallon mutanen dake zaune a reception d’in da sauri ihsan da abba suka shiga d’akin da aka nuna musu, shi kam haidar wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke don har ga Allah yaji dad’in zuwan nurse d’in koba komai ta ku6utar dashi daga tanbayar abban don da bata zo ba wace amsar zai bawa abban sa,wata zuciyar tace.”cewa zakayi nine nayiwa yaya nafisa ciki bak’in cikin hakan yasa umma zubewa.” Wannan itace amsa ta gaskiya sai dai ko giyar wake haidar yasha bai isa ya furta hakan a gaban mahaifin sa ba.
Ganin zancen zucin bazai kai masa ba ya mik’e yana tangad’i shi kansa da zai samu gatan da za’a kwantar dashi jiki da zuciyar sa suna tsananin buk’atar hakan saboda rud’anin da yake ciki, d’akin shima ya shiga ya same su zaune a gaban gadon zulfa’u hannun ta cikin na ihsan, tamkar Wanda za’a kama a d’arare ya k’arasa wajen da suke yana yiwa umman tasu sannu, kai kawai take iya d’aga wa saboda nauyin da bakinta yayi mata a ranta tana jinjina abubuwan da suka faru da ita cikin y’an a wanni, wai Ibrahim d’anta shine yake luwad’i sannan ga nafisa dake binsa kwance tana neman rasa ranta saboda cikin da tayi, runtse idonta tayi tana tuna yusra y’ar autar ta wacce tafi so fiye da kowa cikin yaran ta itama wai lesbian take harda shirin yin auren jinsi ba tare da ta sani ba, hawaye ne ya fara zirara ta gefen idonta yana sauka bisa kuncin ta har yanzu idonta a rufe yake babu shakkah sai yanzu ta fara nadamar yin wasarere da tarbiyyar yaranta abinda yake gabanta shi kawai take yi, sam tak’i yadda ta bud’e idonta don bata jin zata iya kallon k’wayar idon alhj ta fad’a masa abubuwan da suka faru ta sanadiyyar sakacin ta, wayar zulfa’u ce tayi k’ara alamar shigowar sak’o abba ne ya d’auka ya duba tare jan d’an k’aramin tsaki ganin sak’o ne daga company.
Wayar ya zura a aljihunsa ba tare da tunanin komai ba, haka suka cigaba da zama kusan minti biyar kafin alhj mukhtar ya mik’e tsaye tare da kallon haidar yace.”zo muje ka kaimu inda nafisa take mu duba ta.” A tare suka fito da yusra koda suka je d’akin sun samu tana bacci bata farka ba, Allah-allah haidar yake su fita daga d’akin don gani yake kamar dady zai gano abinda yake faruwa, alhj mukhtar ya dubi haidar tare da jefo mishi tanbayar da ta hautsina y’ay’an hanjin sa.
“Wai menene ya faru dasu naga kamar ba accident suka yi ba.”
Shiru haidar yayi yana raba idanu yasan koda kalma d’aya ya furta alhj zai iya gane gaskiya, mik’ewa alhj mukhtar yayi yana fad’in. “Na lura akwai abinda kake 6oye min bari naje wajen doctors nasan su zasu fad’a min komai.” Ya k’arasa maganar yana k’ok’arin fita daga d’akin, ya gama fahimtar akwai abinda haidar baya son ya sani shi yasa yake masa kauce-kauce, shi kam haidar kusan daskarewa yayi a wajen zuciyar sa ta fara k’issima mishi abubuwa masu yawa ciki kuwa harda wacce ke bashi shawarar ya gudu.
Yana fita kai tsaye office d’in doctor ya nufa, yayi knocking aka bashi damar shiga, da sallama ya shiga haka kawai yake jin bugawar zuciyar sa na k’aruwa da k’arfi, bayan an bashi waje ya zauna ya dubi doctor jameela yace. “Doctor nine mahaifin nafisa mukhtar, kuma miji ga zulfa’u rabi’u, nazo ne don naji abinda yake damun su.”
Kallon sa doctor jameela tayi cikin nutsuwa kafin tace. “Am dama alhj ba wani abu ne ya faru dasu ba face, ita yarinyar nafisa tasha k’wayar da zata zubar mata da cikin dake jikinta ne, shine aka samu matsala maganin ya kusa hallaka ta, ita kuma zulfa’u fad’uwa tayi ta suma da taji abinda d’iyar ta ta aikata wannan shine abinda ya faru.”
Wani irin juyawa k’wa-k’walwar alhj mukhtar keyi nafisa y’ar sa ce da ciki? Anya kuwa likitocin sun tabbatar da hakan, kafin ya dawo daga tunanin da yake yaji wayar dake aljihunsa tana ringing kallon wayar yayi kamar ya share kiran saboda wayar zulfa’u ce, sai yaga an sanya Ibrahim d’a na, don haka ya gane babban dansu ne, cikin sauri ya d’aga bayan ya fita daga office wata kujera ya samu ya zauna, kafin ya furta komai yaji wata murya me amo na fad’in.
“Hajiya kizo head quarter commitioner of police na son magana dake akan wad’annan lalatattun yaran naki da kika kasa yi musu tarbiyya.”
Sosai kansa ya kulle sam bai fahimci ma abinda ake nufi da maganar ba don haka yace.”ina Ibrahim me wayar.” Cikin tsawa d’an sandan yace.”kai kuma waye a wajen sa ?”
Tsintar kansa yayi da cewa.”ni mahaifinsa ne.” Saboda ya matsu yaji abinda yake faruwa, daga can d’an sandan yace.”OK kai yakamata ma kazo, saboda ankama yaron ka Ibrahim yana lalata wani almajiri, sannan bayan shi akwai yusra wacce muka kama suna shirin k’ulla auren jinsi da wata Hajiya, ma’ana dai ita d’in ma y’ar lesbian ce.”
Wata irin hajijiya ce taso kayar da alhj mukhtar dukda a zaune yake, a hankali bakin sa ya fara karanta innalillahi wa innailaihirraji’un……
[10/12, 5:16 pm] +234 708 595 8544: *👺👹RUƊUN SHAIDAN👺👹*
*_Daga Alƙalamin gamayyar marubuta Tsaganyar Adabi*_
_*TAKEN MU SHINE*_: *Don Tsaftace Adabin Bariki*
*Marubuta labarin✍🏾*
*1-Usman Ango Ɗan Anacen Marubuta*
*2-Oum Mashkur*
*3-Abba Abubakar Grateful*
12to13
Runtse idonsa yayi yana cigaba da karanta duk addu’ar da tazo bakinsa, kansa na wani irin juya masa, da taimakon Allah da kaifin addu’a ya fara jin sauk’in rad’ad’in da zuciyar sa keyi masa, a hankali ya yunk’ura ya tashi ya nufi d’akin da aka kwantar da zulfa’u wani irin haushin ta yake ji don babu laifin Wanda yake gani face nata saboda itace keda hakkin kula masa da tarbiyyar yaransa idan ba ya nan, yafi jin takaicin yanda k’ima da darajar sa zasu zube a matsayin sa na shahararren d’an siyasa Wanda ludayin sa ke kan dawo, ya sani dole idan wannan al’amarin ya yad’u a duniya zai shafi takarar sa ta d’an majaslisar tarayya da yake nema, y’an adawa har sharri da k’age suna yiwa mutum balle kuma sun samu wannan labarin dole su samu abun yad’awa a kafafen yad’a labarai don a ruguza masa burin sa Wanda yakai kimanin shekara 3 yana nema, gashi ya samu a wannan lokacin don tuni anyi primary election kuma yaci, abinda ya rage shine babban za6e Wanda yake da yak’inin ya gama cinye wa, kwatsam wannan al’amarin zai 6ullo dole ne a samu mafita, da wannan tunanin ya shiga d’akin.
Haidar ne zaune a gaban nafisa ya zuba mata ido har ga Allah yafi tausaya mata fiye da yanda yake tausaya wa kansa, koba komai ita d’in y’a mace ce me rauni sannan a gabansa ta dinga murk’ususu da matagungun lokacin da maganin da tasha ya kusa aika ta lahira, haka kawai yaji rashin kyautawar sa muddin ya gudu ya barta cikin wannan halin yasani muddin abbq yasan abinda ya faru to babu shakkah kashin su ya gama bushewa, hawaye ne ya ziraro daga idonsa zuwa yanzu ko goge hawayen baya yi, dai-dai lokacin nafisa ta farka, kallon haidar tayi cikin second d’aya ta tuna da abinda ya faru Wanda shine dalilin zuwanta asibitin, cikin sauri ta mik’e zaune tana me kafe shi da ido kafin cikin raunanniyar murya tace.
“Haidar cikin ya zube kuwa.” Bai iya yi mata magana ba sai girgiza mata kansa yayi cikin karayar zuciya, wani irin kuka nafisa ta fashe dashi don ta gane abinda yake nufi ta dube shi cikin sheshshekar kukan sannan tace. “Na shiga uku haidar shikenan asirin mu ya gama tonuwa mai zamu fad’a wa iyayen mu idan suka fahimci halin da muke ciki?”
Shima haidar kukan yake cikin kukan yace.”Aikin gama ya gama yaya nafisa tuni umma tasan kina d’auke da ciki hakan ne ma ya sanya ta fad’i har da suma yanzu haka itama tana kwance a asibitin nan, shi kansa Abba ya dawo kuma yana office d’in doctor nasan zata fad’a mishi duk abinda yake faruwa. ”
Ya k’arasa maganar cikin tsananin jin haushin abinda suka aikata, k’walalo ido nafisa tayi tana dafe k’irjin ta da hannun ta Wanda babu komai a jikinsa, k’ara fashewa tayi da kuka me ban tausayi tana shafa cikin ta tana sanbatu.” Me yasa muka biye wa son zuciyar mu, shin me yasa muka sanya kanmu cikin masifar karanta novel na batsa, wlh Allah sai ya saka min akan wannan tsinanniyar marubiciyar *zuraifat* bani da aiki sai karanta littattafan ta wad’anda suke jefa ni cikin mawuyacin hali,haidar da ace bana karanta littattafan ta babu abinda zaisa mu fad’a cikin irin wannan halin.”
Zaro ido haidar yayi cikin mamaki yace.”kema littafan *zuraifat* kike karanta wa, wlh nima wani aboki na ne ya koya min da babu ruwa na, a gaskiya marubutan batsa suna cutar da y’ay’an mutane kuma sai Allah ya saka mana. ”
Ajiyar zuciya nafisa tayi sannan tace. “Hakane haidar babu shakkah da laifin su amma fa mu munfi su laifi saboda idan sun rubuta basu samu wad’anda suke karanta wa ba dole su daina, sannan shed’an da kuma son zuciyoyin mu ne suka sanya muka aikata zina, gashi yanzu kusan sau uku ina shan maganin zubar da ciki amma yak’i fita sai bak’ar wahala da nasha wacce ta kusa kaini lahira a gaskiya ni dai kam ba zan tsaya ba haidar guduwa zan yi wlh, don bazan iya kallon iyaye na da wannan mugun abun kunyar ba” Ta k’arasa fad’a tana k’ok’arin cire k’arin ruwan da aka sanya mata, mik’ewa tayi tsaye dukda jikin ta babu k’wari amma haka ta daure cikin k’arfin hali ta sanya hijabin ta tare da kallon haidar tace.”idan iyayen mu sun zo ka nema min gafara a wajen su haidar.”
Shima haidar cikin sauri ya mik’e tare da fad’in. “Tare zamu tafi yaya nafisa baza ki barni ba, ni kaina ina tunanin yanda zan dubi iyayen mu na sanar dasu tare muka aikata wannan mugun abun, gwanda mu zama jaruman cikin littafin zuraifat d’in da hujja.”
Cikin rashin fahimta nafisa tace.”Wane littafi kake nufi?” Kai tsaye yace.”*NI DA K’ANI NA*mana.”
Shiru tayi tana tuna littafin babu shakkah abinda yake cikin littafin ne ya faru dasu, tamkar a mafarki haka kawai taji zuciyar ta ta k’ek’ashe dole ta maida kanta khalisat jarumar cikin littafin don haka cikin sauri ta d’auki katin da aka rubuta mata magani ta juya bayan sa tayi rubutu me d’an tsayi sannan ta ajiye akan gadon, ta juyo ta kalli haidar tare da cewa.”Bamu da ishashshen lokaci haidar kazo mu bar asibitin nan tun kafin abba yazo ya same mu.”
Ba tare da musu ba haidar yabi bayan ta suka fice daga d’akin, cikin sa’a kuwa har suka fice daga asibitin basu had’u da wata matsala ba, cikin gaggawa suka tare napep suka hau saida suka koma gida sanin cewa babu kowa a gidan baba me gadi ne kawai don haka suka shiga sauri-sauri suka had’a kayan da zasu buk’ata tare da d’iban kud’i me yawa suka fice daga gidan cikin gaggawa.
______________________Alhj mukhtar ya shiga d’akin cikin tsananin fushi, wani irin bak’in ciki yaje ji yana ratsa zuciyar sa, babu abinda yake d’aga masa hankali sai yanda yaran sa uku suka lalace yana tsoron wannan labarin ya isa kunnen y’an adawan sa don ya tabbatar babu shi babu takarar sa don za’a yad’a shi a duniya akan ya kasa tarbiyyar yaransa.
Ko sallama baiyi ba ya fad’a d’akin, cikin sa’a ya samu zulfa’u ta tashi ihsan tana bata ruwan tea Wanda take sha tamkar me shan magani, ganin alhj mukhtar a d’imauce yasa ta fahimci ya gane abinda yake faruwa, aikuwa sai ji tayi ya fara watso mata maganganun da suka hautsina y’ay’an hanjin ta, yace.”zulfa’u kina aikin me yara na suka lalace haka, ashe dama rashin tunanin ki ya kai ki bar min yara su zama y’an iska? Me kike so na fad’a wa mutanen da nake son jagoranta alhalin ni na kasa bawa yara na tarbiyya, to wallahi kisa a ranki muddin na rasa kujerar nan sakamakon wannan abun zan d’auki mummunan mataki akanki da ke da yaran ki.”
Shiru zulfa’u tayi wani hawayen takaici da bak’in ciki na sauko mata, jin zuciyar ta take tamkar zata fashe, da k’yar ta yunk’ura ta mik’e tsaye tare da fad’in. “Kayi hak’uri alhj mu kar6i wannan jarabawar da ta fad’o mana da hannu biyu, kada mu butulce wa mahaliccin mu, ni kaina na san ina da sakaci me yawa akan hakan amma ya zanyi da k’addarar da Allah ya rubuta zata kasance? Yanzu ni ina ganin abinda ya kamata muyi shine mu nemi mafita tuna dai mai faruwa ta faru.”
Wani irin takaici ne ya k’ara turnuk’e zuciyar abba sai dai yasan maganar zulfa’u gaskiya ce, mafita ce kad’ai abinda ya dace ya fara nema, a sukwane ya bar d’akin ya nufi d’akin da aka kwantar da nafisa zuciyar sa na wani irin tuk’uk’i, yanda yake jin zuciyar sa zai iya shak’e nafisa ta mutu da ita da shegen cikinta ya kwammace ya rasa ta da dai ta haifa masa jika shege, duk cikin al’amarin yafi jin takaicin na nafisa tunda shine me tabo Wanda baya warke wa, ganin yanda ya tafi rai a jagule yasa zulfa’u da ihsan suma suka bi bayan sa cikin sauri.
Da k’arfi ya hankad’a k’ofar d’akin ya shiga, sai dai ga mamakin sa babu nafisa babu haidar, abinda yai matuk’ar bashi mamaki kenan dube-dube ya fara yana neman inda zai ganta, dai-dai lokacin zulfa’u suka shigo cikin fargaba zulfa’u tace.”alhj ina nafisan take.”?
A kid’ime ya juyo yana fad’in “ban ganta ba, har ma haidar ina suka tafi ko dai an sallame su.”
Wani tunani ne ya ziyarci zuciyar zulfa’u da sauri ta fara duba ko ina har toilet ta lek’a babu nafisa babu dalilin ta, cikin tsananin tashin hankali tace.”na shiga uku ko dai guduwa nafisa tayi.”
Jin haka da alhj mukhtar yayi sosai hankalin sa ya k’ara tashi zama yayi a gefen gadon yana jin zuciyar sa na suya, ihsan ce ta lura da rubutun dake jikin katin da sauri ta d’auka ta nuna wa iyayen zuwa yanzu sun gama amincewa guduwa nafisa tayi, zulfa’u ta kalli ihsan murya a raunane tace “karanta mana da k’arfi ihsan.”
Itama ihsan d’in jikin ta yayi sanyi sosai dukda bata san abinda yake faruwa duba takaddar tayi ta fara karanta wa a fili.
“*Assalamu alaikum, yaku iyaye na ina me matuk’ar baku hak’uri sakamakon abinda muka aikata gare ku, ni da d’an uwa na haidar mun sani bamu yi muku adalci amma ku sani ya ku iyaye na kunyar ku da muke tsananin ni ce ta sanya muka gudu, a k’arshe ina me bak’in cikin sanar daku haidar shine uban cikin dake tare dani, don Allah iyaye na kada kuyi mana baki kuyi hak’uri, daga y’ar ku nafisa*”
Ba alhj mukhtar da zulfa’u ba, hatta ihsan dake karanta wasik’ar ta shiga cikin tsananin firgici da damuwa, hawaye dukkan su suke har shi kansa abban don zuwa yanzu zuciyar sa bazata iya juriyar d’aukar wad’annan abubuwan ba, yara 4 wannan wacce irin rayuwa ce, babu shakkah yanzu ba iya laifin zulfa’u yake gani ba har da nashi, yasan bai bawa yaran sa kulawar da ta dace ba, siyasar sa ce kawai a gabansa, burin sa shine yaci za6e babu abinda ya dame shi yau yana Abuja meeting gobe yana kaduna campaign, kuka sosai suke babu me rarrashi, wayarsa ce tayi k’ara alamar kira da sauri ya d’aga ganin me kiran wani babban abokin sa ne tare suke komai na siyasar su, alhj kabir cikin tashin hankali yace. “Wai alhj mukhtar kaga abinda yake yawo a social media kuwa?”
Cikin tsananin rud’ewa Abba ya girgiza kansa kamar yana gabansa sannan yace. “Me nene yake faruwa alhj?”
Saida alhj kabir ya sauke ajiyar zuciya kafin yace. “D’iyar ka yusra naga ni tana auren jinsi da wata hajiya, ina me tabbatar maka wannan al’amarin ya watsu kaima yanxu da zaka hau social media zaka gani.”
“Innalillahi wa innailaihirraji’un, na shiga uku alhj shikenan abinda nake gudu ya faru wayyo Allah na.”
Zulfa’u ta dube shi cikin sheshshekar kukan da take yi, taji duk abinda ya faru a wayar kasancewar hands free ya sanya, wani irin kuka da nadama mara misali suke daga alhj mukhtar har zulfa’u babu me lallashin wani balle ma su samu damar tattauna matsalar su, ita dai ihsan tayi shiru zuwa yanzu ta gama fahimtar bayan matsalar nafisa da haidar akwai matsalar k’anwar ta yusra.
*RAYUWAR GIDAN KAFIN FARUWAR AL’AMARIN*
Ku biyo mu a pg na gaba domin jin rayuwar wannan gida don mu gane wanene yafi sakaci tsakanin zulfa’u da alhj mukhtar yanzu aka fara wasan.
Usman ango
OUM Mashkur
Name: | [Rudun Shedan Hausa Novel Complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Leave a Comment