Rugar Fulani Hausa Novel Complete

Rugar Fulani Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*RUGAR FULANI*

_Love and romantic story_

 

 

_TSARAWA DA RUBUTAWA_

 

_*HASSY SOJA CE*_

TSOJA CE

 

_*Da sunan Allah Mai Rahma mai jin’Æ™ai,tsira da amincin Allah su’kara Tabbata ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu rasulillahi sallahu alaihiwasallam*_.

 

 

_Ya Allah Yanda nafara littafina lfy Allah kasa nagama lfy ameen_.

 

 

 

*Littafina na kudine banyarda Wani Ko wata yakaranta batare da kunbiyani hakkina ba,’dari ukku kacal shine kudin littafina na Zaku turo kudinku tacikin wannan accnt no 1437185058 Hassana Ibrahim Access bank* .

 

*Idan kuma baki da Accnt no to ki turo katin MTN dari ukku ta wannan number 07063617906*

 

*Zaku turo shaidan biya ta wannan no 07063617906 ,Niko xan sambadaku Cikin group Na RUGAR FULANI*

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
*Free page daga 9&10 ne free*

 

 

_Bismillah Rahamani Rahim_

 

 

*Page ___________1&2_________*

Wasu motocin ne guda ashirin da hudu ne suka jiro sai jiniya suke wiwi wiwi wani haÉ—aÉ—in company suka shigo cikin Æ™atun fili parking sukayi da sauri security suka fito daga cikin motocin da gudu suka zo gurin wata irin haÉ—aÉ—in motar da akirar Prado Hank Williams baÆ™a da baÆ™ar tint da sauri aka buÉ—e Æ™ofar motar zuro kafafuwan sa ya É—auke kusan minti biyar kafin ya fito a hankali ya fito daga cikin motar fuskar sa babu Rahama tsaye yayi yana kallon Company wani security ne ya zo da sauri ya buÉ—e wata motar ya ciro riga da jakarsa da sauri ya dawo gurin matashin saurayi ya saka masa rigar da É“akin glass sannan wasu suka shiga gaba aka saka shi tsaka tafiya yake cikin gadara da izzah suna binsa abayan mutane tunda suka ganshi jikin su har rawa yake gaisawa suke masa Amman ko kallon su beyi ba sai dai É—aya security ya É—aga masu hannu haka suka shigo cikin wani office mutane ne zaune maza da mata saman kujeru suna jiran sa shigowar sa ne ya saka kowa ya miÆ™e tsaye Æ™arasowa yayi gurin da sauri security yazo ya goge masa kujerar sannan ya zauna buÉ—e masa jakar yayi ya ciro laptop da wasu file din wasu takardu ya ajiye masa Table ya komai gefen sa shiru akayi kowa kallon ikon Allah kawai suke shiko gogan lumshe idanuwan sa yayi sannan aka fara gudanar da abubuwan da za’ayi sannan wani daga cikin su yace”Sir ko kana da magana”!?.

See also  Love Cycle Hausa Novel

 

Shiru yayi be ce komai ba security yace “eh to akwai wasu abubuwan da zamuyi Amman ana samun kuÉ—adi masu yayi Amman zuwa wani lokacin zakuji mu insha Allah ” buÉ—e idanuwan sa yayi ya kalle security da hannu yayi masa magana da sauri ya É—auke file ya mayar cikin jaka da laptop din ya rufe jakar miÆ™ewa tsaye yayi sannan ya kalle su ya juya ya fice daga cikin office É—in security bayansa ya bi da sauri da kallon su besa É—aya daga cikin su yace”tabba É—i jam yanzun kun ganin abun wannan yaron yayi muna”!? Himm ku ne baku san waye Saheeb ba kuwa ” cewar wani ni wlh tunda nagan shi yake ban haushi ace mune kawai muke magana mtsss himm! Ni ko wai ko jinin sarauta ne”!? Kwarai ma kuwa mahaifin sa sarkin London ne kuma anan Nigeria É—an siyasa ne atajiri ne jin jina kai sukayi sannan kowa ya miÆ™e tsaye, Saheeb kuwa koda ya fito daga cikin office É—in gurin motocin sa ya tsaya aka cire masa rigar sannan ya shiga cikin motar aka rufe jin gina kansa yayi sitiyarin motar shi, yana tsotsar leÉ“en sa na Æ™asa ajiyar Zuciya yake buÉ—e firji yayi ya É—auko ruwan sanyi ya rufe shan ruwan yayi yana ajiyar Zuciya Amman har yanzun beyi buÉ—e idanuwan sa ba dafe kansa yayi saboda tsabar hayaniyar mutane da sukayi masa shi ya saka ma ciwon kai gudu suka fita daga cikin company gudu suka shararawa saman titi wata Irin Unguwa ce suka shigo sai da sukayi tafiya mai nisa sosai sannan suka iso wani irin haÉ—aÉ—in gida ne wanda ya amsa sunan sa gida horn akayi da sauri ya wangale get É—in haka suka shigo cikin gidan haka suka wuce get shida sannan suka iso cikin Æ™atun gidan parking akayi sannan aka buÉ—e masa kofar fitowa yayi daga cikin motar tafiya yake cikin izzah da gadara cikin gidan ya shiga security na biye da shi da sauri, koda ya shigo cikin wani haÉ—aÉ—in parlour ne wasu wasu haÉ—aÉ—in mata ne zaune saman kujeru É—aya bazata wuce shekara 46 ba É—aya kuma bazata wuce shekara 50 ba tana karatun jarida sa samari guda ukku sai Æ´an matan guda ukku sai wata Æ´ar Æ™aramar yarinya shigowar sa ne ya saka dukk Æ´an mata da Æ´an samarin suka miÆ™e tsaye suna kallon sa da gudu Æ´ar yarinya tazo tana cewar “oyoyo Sweet Daddy gurin sa tazo ta rungume sa É—aukar ta yayi, yayi sama da ita yana murmushi kallon sa suke kallo É—aya yayi masu ya É—auke kansa Sultan da Aliyu da Ubaidullah suka cewa “welcome black my Sweet”hannu ya É—aga masu Raihana da Na’imah da Zulfa’u suka ce”my Sweet Brother barka da dawowa ya hanya”!? Jin jina masu kai yayi.

See also  Triplets Hausa Novel Download

 

Ammi ta ajiye jarida da take karatu tace “My Sweet son”Ajiye yarinyar yayi ya Æ™araso gurin cikin ladabi ya gaishe da su kamar be son magana zaunawa saman kujera yayi ya É—aura kansa saman cinyoyinta yana ajiyar zuciya ita kuma Mami kallon su take tace “Sweet har andawo”!? Uhmm abun da yace kenan ke Raihana tashi kije kitchen ki É—auko masa abincin sa da sauri ya buÉ—e idanuwan sa yana harara Raihana ita kuma Raihana Kwalla ne suka fara zubo mata tace “Ammi kin san halin Sweet bayan cin girki mu” Aa ni fa ban son jaraba yanzun fisabillah daga dawowar ka har ka fara saka Æ´arana kuka cewar Mami tana Hararar sa………

 

 

A cikin garin Yola kuwa akwai wata RUGAR FULANI wace take da É—auke da mutane masu yawan gaske sai dai kuma acikin wannan rugar akwai wata rugar fulani wace tsakinta da wacan rugar akwai tafiya mai nisha sosai ita wannan Rugar Allah yayi mata Allah abubuwan noma ba wani girma gareta sosai ba Wani dattijo ne ya fito daga cikin wata Æ´ar buka yana kallon shanu zan kai dubu dari biyar da tallatin da ukku akwai raÆ™umai da akuyoyi da kaji da zakaru da tallo tallo da awaki can ya hango wata haÉ—aÉ—iyar Æ´ar budurwa ce bazata wuce shekara sha huÉ—u ba aduniya farar sosai kamar aÆ™anta jini ya fito tana da zara zaran gashin ido da gira zaune take tana wasa da jaririyar shanuwa fuskar ta É—auke da murmushi dumfull din ya lotsa sanye ta da kayan fulani rigar ta bata wuce cibiya bayarta ba sai zani datake É—aure da shi ga kunkurun ta yace”Ƴar Anna!! Zubur tayi cikin muryar ta mai shegen dadi tace “Baffa Awalijam(ina kwana) murmushi yayi yace “Saijam(lfy klau) Amma yaushe zaki fita kiyon dabbobin nan”!? Baffa yanzun zan tafi da su dama kai nake jira kafito mu gaisa” jin jina kai yayi yace “to Æ´ar Anna ki kula sosai da kanki”.

See also  Nimcyluv Novels

 

 

 

Murmushi tayi sannan ta É—auko Æ´ar sandar ta ta fara kora shanun jaririn shanun Baffa ya É—aure su sannan ya fice daga gurin kora su take sosai har sai da suka gama fita Sannan tayi ajiyar zuciya tace “Aradun Allah nagaji sosai “tafiya ta cigaba da yi sai dai ba nisa tayi da gida ba É—an wani guri ta samu ta zauna tana wasa da Æ´ar sandar ta tana waÆ™oÆ™in fulatanci haka tayini gurin yamma ta fara sai ta miÆ™e tsaye tana kallon su ahankali ta fara korar su haka suka wuce gida koda ta shigo cikin gida Baffa ne zaune saman tabarmar kabba yana karatu da sallama ta shigo É—ago idanuwan sa yayi yana.

 

 

 

kallon ta yace “sannu Æ´ar Anna Allah yayi maki albarka” Amin ya Allah Baffa Nayalijam (an yini lfy) Alhamdulillah cewar Baffa gurin da shanu suke taje ta É—aure su Sannan ta koma gurin akuyoyi ta É—aure su Sannan tadawo gurin Baffa ta zauna tana kallon sa É—agowa yayi yace “Ƴar Anna akwai Nono ya kamata idan kin huta kije gidan Abu kicewa Inna ta tabaki fura ki kawo mani da sauri ta kalle sa kwalla ne suka fara zubo mata muryar ta na rawa tace “Baffa ni wlh tsoron su nakeji “.

 

 

Jan numfashi yayi yace “hakuri zakiyi kije gida “jikinta babu kwari haka ta mike ta fita daga cikin gidan tafiya take tana kuka jikinta na rawa har ta iso kofar gidan jikinta sai mazari yake sosai laÉ“ewa tayi gefen soron gidan tana tsaye tana kallon gidan wani matashin saurayi ne ya fito daga cikin gidan da gudu ta koma bayan wata Æ´ar gina ta laÉ“e jikin kirma yake murmshi yayi yasan bakowa bane gurin sai Ƴar Anna girgiza kansa yayi cikin sanyin murya yace “Aa Æ´ar Anna sarkin tsoron mutane to ki fito ni ne Hamma Habu “jin muryar sa ne yasa ta fashe da kuka sosai jikinta yana kirma………..

 

*Dan Allah Dan Allah Dan Allah,Karki futarmin da book sbd littana na kudine.*

 

*Duk wacce ta futarmin da book bazan miki Allah ya is ba sai da inaso kiyiwa iyayena Addu’a Allah ya jikan su da rahama Amman dan Allah sau daya zaki fitar da shi idan ko ya wuce haka zan barki da Allah kowacece Ke sbd kasuwanci nane*.

 

*Sannan Duk wacce ta takaranta matukar ba freepage bane lallai kizo kibiyani hakkina inko kinki nabarki da Allah*.

 

My phone number 07063617906 .

 

​

 

 

Name: [My Novels (www.mynovels.com.ng)]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram



Powered by: www.mynovels.com.ng

1 thought on “Rugar Fulani Hausa Novel Complete”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top