Littafan Hausa Novels

Rumah Hausa Novel by Oum Hairan

Rumah Hausa Novel by Oum Hairan

 

 

 

 

 

 

 

 

RUMAH Hausa Novel

 

 

 

*Oum Hairan*

 

 

 

*Page 1-2*

 

 

 

“Rumasa’u! Wato ke kunnenki bayajin magana baki da hankalin gane daidai ko? To aje tsintsiyar nan maza ɗauki bokiti ki ɗebo ruwa ki wanke kayan waɗancan ƙannen naku ƴar ƙundun uba take fama da tsayi kamar taliya”

Rumah

Metroom Lami ta faɗa tana ƙoƙarin kai mata rankwashi tayi saurin zarar bokatin ta nufi burtsatsen da sassarfa tana haɗa hanya, hawaye ne ya tsiyayo daga cikin idanunta lokacin da tazo zata gifta wasu yammata da bazasu wucce tsaranninta ba taji sun kama yi mata dariya ɗayar tace “Banza a banza wai nasara yaga zagin sarki saikace ba tsintacciya ba” ta rasa meye yasa tana rayuwa a gidan marayu amma bata ƙaunar ace mata tsintacciya kalmar tana baƙanta ranta har ta rinƙa tunanin dama da mahaifiyarta taji a ranta bazata iya riketa har girma ba da kasheta tayi ta huta, takanyi hasashen yanzu itama shegiya ce kenan? Batada dangi batada taƙamaiman wanda zata kama ta kalla matsayin uba?” Koda ta isa burtsatsen bata ƙarasa ba jikin wata bishiya ta samu guri ta zauna ta haɗe kanta da gwiwarta tanata rera kukanta me ban tausayi da haka taji an fara kada ƙararrawar sallah hakan ya sata saurin mikewa ta ɗauki bokatin ta ɗebe ruwan ta nufi ɗakinsu Baba Lami tana ganinta tace “kin gama iskancin naki sannan kika ɗebo ruwan”

 

Sugar Mommies Hausa Novel Complete

 

 

Sunkuyar dakai tayi ta aje ruwan ta nufi cikin dakin ta ɗauki hijjab ta zura ta ɗauki ƙur’aninta uzu sittin ta fito ta wucce baba Lami tsaye tana ƙwafa ta nufi masallacin dake yau juma’a ce gidan sukanyi baƙi daga waje hakan yakan sa a basu uniform su sanya saboda tsoron kada su gudu.

Saida taje ɗakin sanya kayan ta cire na jikinta ta sanya wani sannan ta fito ta nufi inda suke taruwa a raba musu karatun.

Lokacin data isa har an fara rabawa tun daga nesa ta hango Mal Ahmad shine yake rabawar tarasa meye yasa jininsu bai haɗu ba ba kamar mal Amin ba da yake janta a jikinsa sosai tare da dagewa wajen ganin ta fahimci komai yanda yake

Koda ta isa Saida yayi mata ƙorafin makara kamar yanda ya saba sannan ya bata addu’ar da zata karanta yayin buɗe taron na yau bata wani bawa abin muhimmanci ba ta karɓa tayi gaba ta sami guri jikin hall ɗin da suke taro idan za’ayi manyan baƙi ta zauna tana duba addu’ar tayi ajiyar zuciya ganin ta riga ma ta haddace ta a darasin da Mal Amin ya bata ƙarshen satin can.

 

 

 

 

Ganin kowa yana neman hanyar shiga hall ɗin domin samun matsuguninsa yasa itama ta tashi ta nufi cikin hall ɗin can nesa da mutane ta zauna tsakaninta da yammatan dake daidai da ita da ƴar tazara mazan kuma suna nasu ɓangaren duk wanda zai wucce cikin mazan saiya ɗaga mata hannu amma matan kowacce kawar dakai takeyi ko kuma ayi mata tsaki, Asma’u ce kawai ta samu arziƙin isa gareta ta zauna tare da dafata tayi firgigit ta dawo hayyacinta sukayi ajiyar zuciya tare Asma’u tace “Bansan yaushe zaki daina keɓance kanki daga cikin ƴan’uwanki ba RUMAH shifa kowanne bawa da rubutacciyar ƙaddararsa kece Amiran masallacinmu kina ɗaya daga cikin mutanen da suke fada mana abinda ya dace da rayuwarmu kuma Ni ina ganin wannan cire kanki ɗin da kikeyi kamar shine dalilin da yasa suma suke janye jiki daga gareki domin basu mu’amalanceki ba bare su san wacece ke”

 

 

 

 

Jinjina kai tayi ta ɗago ta dubi Asma’u tace “Nasani da hakan ma Asma’u amma na kasa dainawa idan naga kowa a gidannan yana dariya Ni sai na rinƙa jin meye daɗin duniya bayan zama kusa da iyaye da har zai sani dariya? Meye abinda zai burge zuciyata da zai gusar min da ganin naƙasun rayuwata har na manta da tawayata nayi dariya irin dariyar shashashai Asma’u wannan tunanin dashi na budi idanu na ganni kuma bansan ranar gogewarsa ba.

 

 

 

Murmushi Asma’u tayi me ɗauke da ƙwallah tace “Shin dauriyar ɗaukar nauyin ƙaddara muka fiki kenan da muke iya sanya dutse mu danne waɗannan tunane tunanen da suke bijirowa zukatanmu, anya Rumah imaninki dirarre ne da kike ja da hukuncin ubangiji….”

Saurin ɗaga mata hannu tayi tace “Ba haka bane Asma’u mubar wannan maganar kawai Kinga manyan baƙi har sun fara zama….” Me gabatar da taron ne ya fara buɗe taro da sallama irin ta addinin Musulunci kafin ya kira Rumasa’u wadda kusan shekara guda kenan ita ke buɗe taro da addu’a, miƙewa tayi ta nufi gurin da aka tanada dan tsayawa ta fara karanto addu’o’in nemawa ƙasa zaman lfy da larabci take gabatar da komai har ta gangaro kan jihar ta ta Kano sannan ta fara gabatar da saƙon godiya, kamar haka.

 

 

 

 

“Hakika muna godiya ga Allah subhanahu wata’ala da ya azurta duniya da mutane masu jinƙan ƙasƙantattun cikinsu tabbas maraici abune me ciwo da cin zuciya, duk da cewa siffa ce ta wasu nagartattun mutane amma babu wanda yake fatan ya buɗi idanu ya gansa cikin wannan hali saidai har in ya zama dole a karɓeshi don babu yanda za’ayi da hukuncin ubangiji.

To bare mu namu da ake ƙirƙirar mana shi don ganganci da son zuciya abubuwa mabambanta sune suka zama ƙaddarar kowannenmu ta tashi ya riski kansa a wannan gida marashin cikakkiyar daraja a idanun al’umma duk da haka mukam muna godiya ga Allah daya sanya muka tashi muka ganmu cikin bayinsa waɗanda suke cikin bayyananniyar jarabawarsa……

Taci gaba da bayaninta cikin nutsuwa ta yanda sosai bayanan suke ratsa jikin duk wani wanda yake zaune a wannan gurin, bayan ta gama ta sauka a wajen gabatar da taron ne ta fice daga cikin hall ɗin wanda kusan hakan ya zame mata ɗabi’a bata iya zama a gama taro take ficewa ta koma can bayan hall ɗin cikin ciyayi ta zauna tana karanta wasikar jaki.

 

 

 

 

Tananan zaune a gurin tsayin lkc tana ta tufka da warwara taji alamun tsayuwar mutum a kanta tayi saurin miƙewa domin Allah ya jarabceta da tsoro musamman na maza hakanne yasa tana ganin baƙuwar fuskar taja baya da sauri tana shirin yin magana taga Mal Amin ya nufosu taja ajiyar zuciya ta mayar da hankalinta kan Mal Amin ya iso yace “Afwan chief House ne ya aiko kiranki sanin halinki da shegen tsoro yasa na biyo bayansu karki firgita ki zuba jeji da gudu”

Numfashi ta sauke tana wasa da yatsunta tace “Kay Sheikh wato tsoro ne gareni to ai tsoron ma cikin imani yake” murmushi yayi yace “Hakane biyoni” babu musu bare gardama ta nufi hanyar da taga sun bi suka nufi office ɗin shugaban gidan suna zuwa aka bata umarnin shiga ta shiga cike da mamaki tasan dai ita iyakar rayuwarta a gidan tsayin shekara sha bakwai bata taɓa shiga wannan office ɗin ba koda wasa to meye dalilin da yasa yau ake nemanta kuma neman a wannan office me daraja? To kodai wani laifi tayi? Gabanta ne ya faɗi tace “Na shiga uku idan nayiwa Chief laifi na mutu na lalace ni Rumasa’u”…..

 

 

Masu son karanta wannan littafi zaku tuntuɓe Ni ta wannan number a WhatsApp 09013718241, 300 ne PC 600 babu VIP ko ku tura ta acct 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin MTN.

 

 

 

 

Idan kinason karanta Free Page na littafin nan ki shiga nan Please na roƙeku mata kawai banda maza.

 

 

 

*RUMAH!….*

 

 

 

*Oum Hairan*

 

 

 

*Page 3-4*

 

 

 

 

Bankaɗa kabilan tayi sallamarta a karkatse tayita suka amsa ta zube a ƙasan tiles ɗin cikin yanayi na tsoro tace “Ina neman sassauci da yafiya idan wani abu na aikata wlh banyishi da niyya ba saidai ya kasance rashin sani….”

Dakatar da ita yayi ta hanyar ɗaga mata hannu ta kuwa nutsu sosai tayi ƙasa da kanta yayi gyaran murya yace “Bani nake nemanki ba Rumasa’u ga bawan Allan da yakeson ganinki…” Ɗagowa tayi da sauri idanunsu suka haɗu tayi saurin yin ƙasa da nata Duk da cewar nasa cikin farin tabarau suke hakan bai hana yi mata kwarjini ba.

Cikar kamala da kwarjinin izza ta mutumin ta sanyata jin wani shayi gami da sabon tsoro sun ɗarsu a zuciyarta yanda ya kafeta da idanunsa da iyakar su kaɗai kawai ake gani cikin naɗin rawanin me ɗauke da kunnuwa dake nuna tabbas yanada wani babban jiɓi da sarauta.

 

 

 

Miƙewa yayi batare da yace komai ba ya nufi hanyar fita Mal Nasir yanata zuba masa gdy suka fice daga office ɗin Chief ya dubeta yace “Rumasa’u kina iya tafiya”

Duk da yanayin kiran da yanayin sallamar sun bata mamaki bata iya cewa komai ba sai miƙewa da tayi ta fice ɗin kamar yanda ya umarceta ta nufi rumfar su ƙirjinta na bugawa da ƙarfi don tasan yau ta kaɗe da masifar Baba Lami. Aikuwa tana zuwa ta cafke ta ta rufe ta da duka tana masifar ta raina mata hankali tasan zatayi mata wankin kayan sabbin yaran da aka kawo mata taje tayi zamanta saboda ta rainata.

Haka ta karɓi wankin tana hawaye tana komai ta wanke ta shanya taje ta zauna a kusa da ita ta ɗauki yarinyar ɗaya tana bata madara tace “Baba Lami yaushe zaki nunamin Iyaye na?” Murmushi Baba Lami tayi tace “To ni yanzu me kikeso nake cewa dakene da zaki yarda Rumasa’u bansan inda zan samo iyayenki bayan suna da aka rubuta Miki da rezar a hannun ki RUMAH da manyan baƙi babu wani abu da aka bar Miki shaida kuma an kawomin kene tun kina shekara ɗaya da rabi Kinga babu wani bayani da zaki iya bamu bare muyi rubutu akai saboda irin wannan ranar”

 

 

 

 

Jinjina kai tayi cikin tausayin kai da sallamawa muradin rai tace “yanzu Shikenan bazan taɓa ganin iyayens ba…” Masifa Baba Lami ta rufe ta da ita tana cewa “Bansani ba kajini da yarinya kinzo kin wani titsiyeni to wama ya sani ko bakida iyayen ballagazar uwar taki gajiya tayi da gantali dake ta zaɓi jefar dake…” Nandanan zuciyar Rumah tayi duhu mafi munin kalma a jiɓantata da zina abin yana nuƙurƙusar ruhinta.

Dare ya fara shiga amma bai hanata tashi ta fice daga ɗakin ba ta nufi bayan dakin can da nisa ta sami guri ta zauna matasa ya ita yammata da samari sunata harkokinsu amma banda ita.

Guri ta samu ta zauna ta haɗa kai da gwiwa tana jan zuciya wannan ita ce babbar damuwarta a duniya ta kasa jurewa ta kasa rungumar wannan ƙaddarar kullum ita kenan cikin kunci da damuwa takanji dama ace tare take rayuwa da iyayenta koda sunfi kowa talauci a duniya.

 

 

 

 

Tana son tsira da mutuncinta a wannan rayuwa bata fatan nasabarta na nasheta kullum tana rokon Allah ya kawo mata sauƙi da salamar zuciya cikin wannan rayuwa daya nufeta da riskar kanta a ciki ta ɓata lokaci a gurin kafin ta rarrashi kanta ta tashi ta nufi inda ta baro tayi alwala tayi sallar magrib da Isha ta kwanta ranta a jagule ba wani isasshen bacci take samu ba kamar yanda baba Lami ta saba ƙananun marayun suna fara mata kuka ta tashe su ita da Asma’u sukayita aikin rarrashi ita tana baccinta basu suka samu suka koma ba sai gab da asuba suna komawa aka kira sallah dukkansu bacci a idanunsu haka suka nufi masallaci daganan suka tafi islamiyyar asuba bayan an taso ne sukayi ayyukansu na yau da kullum dake sun gama secondary hakan ya basu damar kwanciya bacci ya ɗauke su suna kwance bacci me daɗi sukaji ana tashinsu Asma’u ce ta fara tashi ganin me tashin nasu yasa tsoro ya ɗarsu a ranta ta tashi Rumah suka kalli juna me tashin nasu tace “kirane daga office na Maman gida” Tuni Asma’u ta nuna alamun tsoro itako Rumah me arhar hawaye hawaye ta fara sharewa ta miƙe ta ɗauki hijjab ɗinta Asma’u tace “Inajin tsoron kada muma abinda yake faruwa da sauran ya faru damu Rumah an kwana biyu ba’a fitar da mutane a gidannan ba abinda yake bani mamaki sai ace makaranta aka kaisu ko gurin koyon sana’a amma bantaɓa ganin wanda ya fita ya dawo ba anya Rumah gsky ne?”

 

 

 

 

 

Itadai Rumah bata iya cewa komai ba saboda abin faɗa na me baki ne kurma sai kallo, fita sukayi zuwa office ɗin Maman gida tun daga bakin harabar gurin suka ƙara tattare nutsuwarsu ganin wasu dogarai tsaitsaye sunata muzurai kamar Mala’iku, da nutsuwa suka isa inda ake nemansu Maman gida ta dubesu sosai tace “Rumasa’u Asma’u yau lambarku ce ta fito mun saba fitar da yara irinku idan girma ya sauko musu mata muna kaisu Hukumar kula da marayu tana auraddasu maza muna kaisu su koyi sana’o’i don dogaro da kansu, to kuma yau insha Allahu zamu fitar daku yanzu an fita da ƴan’uwanku domin auraddasu ke Rumah jiya munyi babban baƙo a gidannan Mai Martaba Sarki ya nuna bukatarsa da son ƙara bayi a gidansu yace yanason mutum uku maza biyu mata cikin matan yace yanason a haɗa masa da Amiran masallaci wannan tasa naga dacewar na haɗaki da ƴar uwarki Asma’u tunda akwai shaƙuwa zakufi sakewa kuyi abinda ya dace.

Ina rokonku kamar yanda na bayanku basu bamu kunya ba kuma kuyi abinda zaisa ace ala sam Barka ba Allah wadarai ba sannan kuyi ƙoƙarin riƙe amanar maraicinku kuma kuyi hƙr da sabbin mutanen da zaku fara mu’amala dasu.

 

 

 

 

Jinjina kai sukayi jiki a mace ta nuna musu mutanen da suke tsaye don tafiya dasu suka miƙe Asma’u ta fara ficewa itako Rumah jan ƙafarta kawai takeyi ta isa ga motar suna shiga sauran dogaran dake tsaye duk suma suka shiga motocin suka fice daga gidan sai lokacin wani kuka me sauti ya ƙwacewa Rumah karon farko na fitowarta daga gidan nasu gidan data taso ta riski kanta a cikinsa tun bata fara fahimtar bambamcinsa da sauran gidaje ba har ta gane ashe da tazara me tarin yawa a tsakani.

Asma’u ce ta dafata ta ɗago da kanta tana girgiza mata kai tace “A yanda muka taso muka riski kanmu Rumasa’u ba komai ne ya kamata ya rinƙa taɓa mana zuciya har yasa mu ringa zubar da hawayenmu ba” riƙe hannun Asma’u tayi tace “na sani ƴar uwata amma bazan iya hana zuciyata matsa idanuna don fitar da ruwa ba yanzu mu Shikenan a haka zamu ƙare bamu da wani farin ciki a tsarin ginin rayuwarmu mun taso ababen tsangwama da ƙyanƙyami saboda naƙasun nasaba yanzu kuma zamu ƙare guntuwar rayuwar a Bauta haba Asma’u yanzu wannan bai isa kuka ba?”……..

 

 

 

Masu son karanta wannan littafi zaku tuntuɓe Ni ta wannan number a WhatsApp 09013718241, 300 ne PC 600 babu VIP ko ku tura ta acct 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin MTN.

 

 

 

 

 

Idan kinason karanta Free Page na littafin nan ki shiga Please mata kawai banda maza.

 

 

 

*RUMAH!….*

 

 

 

*Oum Hairan*

 

 

 

*Page 5-6*

 

 

 

 

 

Masu son karanta wannan littafi zaku tuntuɓe Ni ta wannan number a WhatsApp 09013718241, 200 ne PC 600 babu VIP ko ku tura ta acct 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin MTN.

 

 

 

Kwantar da kai Asma’u tayi duk yanda takai da son taga tabawa ƴar uwartata ƙwarin gwiwa yau kam itama bakinta ya mutu bazata iya ce mata komai da zaisa ta fahimci komai ba, shiru taci gaba da wanzuwa Asma’u na kallon hanya Rumah na kukanta da ta rasa gatan rarrashi sau da yawa takan raya da ace tana tare da iyayenta biyu uwa da uba da ba maganar kukanta akeyi ba saidai ayi na dariyarta amma yanzu a duniya bayan Asma’u batada wani wanda zai rarrasheta ita kanta Asma’u buƙatar kulawar takeyi.

Batasan sun tsaya ba Saida taji Asma’u ta kamo hannunta sannan ne ta samu damar dagowa suka kalli juna tace “Gidan sarauta me zamuyi a cikinsa?” Kallon da wani dogari ya watsa musu ne yasata shiga hankalinta itakam Rumah takaici ne yasa ta kasa magana a faɗa musu Mai Martaba Sarki ne jiya ya kawo ziyara ya buƙaci ƙarin bayi daga gidan shiyasa aka zaɓesu sannan har Asma’u ta rinƙa tambayar me zasuyi a gidan to me zasuyi bayan bauta da take tunani?

 

 

 

 

Wani hadimi ne ya buga musu tsawa yana cewa kuyi can zakuga inda ya dace daku, Rumah Sarkin tsoro har ta kiɗime tana neman bin inda banan ya nuna musu ba, sai Asma’u ce ta riƙo hannunta suka nufi hanyar daya ɗora su tunda suka taho mutanen da keta harkoki a wajajen suke kallonsu har suka isa wani guri me kama da gida ginin tubali wata wawakekiyar ƙofa ce suka isa gabanta sun sa kai zasu shiga sukaji Muryar wani ƙato ya daka musu tsawa sukayi baya da sauri suka ƙanƙame juna ya ɗaga bulalar hannunsa dorina da tasha man shanu yakai musu duka cikin rashin saa ya samu Rumah a bayanta ta ƙankame Asma’u tare da sakin wata ƙara da take fitar da sautin azabar da taji yayin shigar dukan ya kuma ɗagawa zai sake zuba musu yaji an riketa ta baya juyowar da zaiyi ya zube ƙasa cikin tashin hankali da firgici har yana sakin fitsari yace.

 

 

 

 

“Tuba nake Allah ya taimake ka garnaƙaƙi namiji uban mazaje ubangiji ya taimaki me taimak….” Tsawa wani cikin dogarin dake takewa mutumin dake tsaye cikin kayan alfarma irin na sarakai baya ya daka masa ya ɗaga tasa bulalar zai sauketa kan wannan bawa Rumah data waiwayo daidai lokacin tayi saurin riƙe bulalar ta nannaɗe a hannunta ta cije leɓe sosai taji shigarta cikin tsokar jikinta batasan sanda hawaye ya fara zuba a idanunta ba.

Fizgar bulalar dogarin yayi ya kuma ɗagawa a burinsa na dole saiya daki wannan bawa ta kuma kai hannu ta riƙe mamaki ya sanya duk bayin dake gurin sakin baki suna mamakin ita kuma wannan wacece meye taƙamarta.

Takaici ne yasa dogarin kai mata mari mutumin dake tsaye kamar gunki ya riƙe masa hannu, wannan tasa dogarin zubewa a gurin yace “Tuba nake baya goya marayu” “ku taho dasu” abinda mutumin ya furta kenan ba tare da kowa yaji ba wasu barori sukace angaisheka ya mai duniya ku kutashi ƴaƴan talakawa Sarkin sarakunan duniya nason barancewa daku….”

 

 

 

 

Sumsum suka bi bayan hadiman da suka rufa masa baya zuwa wata farfajiya nan su Rumah suka suma wajen kallon ikon Allah irin ƙawa da alatun dake wannan farfajiya abin ba’a cewa komai sai kallo da idanu, ɗagawa barorin hannu yayi duk suka rusuna sukayi gaisuwa suka bar gurin ya rage daga Rumah sai Asma’u saishi.

Idanu ya ɗorawa Rumah ya kafeta har Saida ta tsargu sannan suka tsinkayo Murya na magana da cewa “Ya dakeki kin hana a dakeshi meye yasa?” Ajiyar numfashi ta sauke jin ba wani laifin tayi ba tace “Ta yiwu nayi masa laifi cikin rashin sani tunda ni baƙuwa ce a gidan, Allah ya taimake ka Ni wacece da babban mutum da ubangiji ya karrama yayi masa gatan da ni ban samu ba badon baya sona ba ba kuma don yafi sonsa dani ba, ya dakeni zaace za’a rama min bayan haka ma ubangiji ya umarci bayinsa da su kasance masu saka sharri da alkhairi inason idan anyimin sharri nayi ƙoƙarin mayar wa da alkhairi, ranka ya daɗe indai don Ni zai dakeshi don Allah ayi masa afuwa”

 

 

 

 

 

Ta faɗa tana ɗaga hannu alamar neman gafara. Jinjina kai yakeyi tunda ta fara maganar yaja numfashi ya sauke yace “Meye sunanki” kanta a ƙasa tace “Rumasa’u” “Rumah!” Ya faɗa tare da kallon gefensa wani amintaccen hadiminsa ya taso basuji meye yace masa ba su dai yace su tashi su tafi kawai hakanan suka tashi suka kuma bin hadimin da kallo ya zubawa bayansu idanu tare da harɗe hannunsa a ƙirjinsa yana maimaita sunan Rumah! Rumah!! Rumah!!! Saida ya maimaita sau uku sannan ya nemi guri ya zauna saman wata kujerar alfarma me kamar lilo yana lilawa yana lumshe idanunsa zuciyarsa na neman aikashi inda ba can yakeso taje ba.

 

 

 

 

Sarki Ridwan Abbas kenan babban ɗa namiji gurin mahaifinsa sarki Abbas da Hajiya Ummah Wato Hajiya Tushi amaryar Sarki Abbas, gidan sarautar Wani irin hargitsattsen gidane wanda babu komai cikinsa sai ido ƙeta da son kai da uwa uba munafurci.

Shekarun Sarki Ridwan Abbas arba’in da biyu a duniya shekarunsa a kan mulki biyar cikin shekaru biyar ɗinnan abubuwa da dama sun faru ciki harda aure aurensa wanda a yanzu haka matan aure Uku gareshi wanda duk mahaifiyarsa Hajiya Tushi itace ke auro masa su daga masarautu daban daban duk a burinta na ganin ɗan nata namiji ɗaya ya haihu gudun kar sarauta tabar ɗakinta amma har yanzu shiru mace ɗaya ce ma Gimbiya Nana ita ɗaya ce tayi ɓari shekaru kusan shidda kenan har yanzu bata kuma ba.

Wannan abu na daga hankalin Hajiya Tushi domin ƴaƴanta sauran huɗun duka mata ne babu sauran namiji sai Lukman ɗan wajen uwargida Hajiya Asubi Fulanin Daura Hajiya Asubi irin matan nan ne da duniya bata damesu ba shiyasa basa jituwa da Hajiya Tushi saboda kullum Tushi cewa takeyi Fulanin Daura baƙin ciki takeyi mata saboda taga yanzu ɗan ta ne sarki ko kuma tace ai dama Hajiya Asubi ta rabata da Ridwan bata taɓa faɗa masa magana yaji, kai tasha cewa zuciyarsa ta mutu Hajiya Asubi ta kashe masa zuciya, itadai Asubi bata kulawa don bataga abin tsayawa suna tankawar ba girma ya riga ya riskesu kowacce ta kafu takance da Tushi yanzu banda abinki Fulanin Yola Ni me ƴaƴa takwas zaki fitar ko ke me biyar ce zaki fita ki barni? Ko kuwa Barebari ce zata tafi tabar yaranta huɗu Ni ina ganin yanzu kamata yayi kowacce ta aje makaminta mu rungumi yaranmu tunda wanda muke yi dominsa ɗin ma ya tafi ya bar mu”

 

 

********

 

Numfashi Sarki Ridwan ya sauke ya miƙe ya nufi ƙofar da zata sadashi da ɓangarensa. Sukuwa su Rumah ɓangaren bayin aka mayar dasu Saida aka nemo jakadiya tana ganinsu tace “Kawu waɗannan sune baƙin da akace za’a kawo?” Kallonta yayi yace “Ƙwarai kuwa

Jakadiya Mai Martaba yace “a damƙasu a hannun ki sannan kije yanason ganinki”

Dubansu tayi sama zuwa ƙasa tace “Ku kuma don taɓewa iyayenku suka barku kuka taho Bauta ga ɗaki can na baƙin da basusan aikinsu ba idan na dawo kowacce zataji aikinta amma kafin wannan ga kayana can a ninkemin su kan na dawo” ficewa tayi suka kalli juna Rumah tace “Asma’u a haka zamu rayu?” Numfashi Asma’u ta sauke tace “Rumasa’u jikina yayi sanyi Nikam wannan rayuwa Nima dauriyata ta kusan ƙare wa”

Kamar yanda ta umarcesu haka suka ninke kayan Asma’u tace “Rumasa’u yunwa nakeji kinsan fa ko karyawa bamuyi ba” sauke taguminta tayi tace “Nima haka har amai ne yake tasomin bari jakadiya ta dawo mu roketa ta sammana abinda zamuci” kafin Asma’u tayi magana Jakadiya ta shigo ta dubi Rumah tace “Ah Ni Sahura Jakadiya wannan yarinya da Sa’a kike Ki tashi muje na nuna Miki aikinki a ɓangaren masu garin” batayi musu ba ta miƙe ta riƙo hannun Asma’u Sahura Jakadiya ta harareta tace “An faɗa Miki ɓangaren ubanki zaki shiga da zakiyi gayya dalla saki hannunta ita munanan da ita” a sanyaye ta saki hannun Asma’u zatayi magana Asma’u tace “Kije insha Allahu alkhairi ne zai biyo baya ƴar’uwata.

Add Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!