Rumah Hausa Novel by Oum Hairan
Rumah Hausa Novel by Oum Hairan
*Oum Hairan*
*Page 1-2*
“Rumasa’u! Wato ke kunnenki bayajin magana baki da hankalin gane daidai ko? To aje tsintsiyar nan maza É—auki bokiti ki É—ebo ruwa ki wanke kayan waÉ—ancan Æ™annen naku Æ´ar Æ™undun uba take fama da tsayi kamar taliya”
Metroom Lami ta faÉ—a tana Æ™oÆ™arin kai mata rankwashi tayi saurin zarar bokatin ta nufi burtsatsen da sassarfa tana haÉ—a hanya, hawaye ne ya tsiyayo daga cikin idanunta lokacin da tazo zata gifta wasu yammata da bazasu wucce tsaranninta ba taji sun kama yi mata dariya É—ayar tace “Banza a banza wai nasara yaga zagin sarki saikace ba tsintacciya ba” ta rasa meye yasa tana rayuwa a gidan marayu amma bata Æ™aunar ace mata tsintacciya kalmar tana baÆ™anta ranta har ta rinÆ™a tunanin dama da mahaifiyarta taji a ranta bazata iya riketa har girma ba da kasheta tayi ta huta, takanyi hasashen yanzu itama shegiya ce kenan? Batada dangi batada taÆ™amaiman wanda zata kama ta kalla matsayin uba?” Koda ta isa burtsatsen bata Æ™arasa ba jikin wata bishiya ta samu guri ta zauna ta haÉ—e kanta da gwiwarta tanata rera kukanta me ban tausayi da haka taji an fara kada Æ™ararrawar sallah hakan ya sata saurin mikewa ta É—auki bokatin ta É—ebe ruwan ta nufi É—akinsu Baba Lami tana ganinta tace “kin gama iskancin naki sannan kika É—ebo ruwan”
Rumah Hausa Novel by Oum Hairan
Sunkuyar dakai tayi ta aje ruwan ta nufi cikin dakin ta É—auki hijjab ta zura ta É—auki Æ™ur’aninta uzu sittin ta fito ta wucce baba Lami tsaye tana Æ™wafa ta nufi masallacin dake yau juma’a ce gidan sukanyi baÆ™i daga waje hakan yakan sa a basu uniform su sanya saboda tsoron kada su gudu.
Saida taje É—akin sanya kayan ta cire na jikinta ta sanya wani sannan ta fito ta nufi inda suke taruwa a raba musu karatun.
Lokacin data isa har an fara rabawa tun daga nesa ta hango Mal Ahmad shine yake rabawar tarasa meye yasa jininsu bai haÉ—u ba ba kamar mal Amin ba da yake janta a jikinsa sosai tare da dagewa wajen ganin ta fahimci komai yanda yake
Koda ta isa Saida yayi mata Æ™orafin makara kamar yanda ya saba sannan ya bata addu’ar da zata karanta yayin buÉ—e taron na yau bata wani bawa abin muhimmanci ba ta karÉ“a tayi gaba ta sami guri jikin hall É—in da suke taro idan za’ayi manyan baÆ™i ta zauna tana duba addu’ar tayi ajiyar zuciya ganin ta riga ma ta haddace ta a darasin da Mal Amin ya bata Æ™arshen satin can.
Ganin kowa yana neman hanyar shiga hall É—in domin samun matsuguninsa yasa itama ta tashi ta nufi cikin hall É—in can nesa da mutane ta zauna tsakaninta da yammatan dake daidai da ita da Æ´ar tazara mazan kuma suna nasu É“angaren duk wanda zai wucce cikin mazan saiya É—aga mata hannu amma matan kowacce kawar dakai takeyi ko kuma ayi mata tsaki, Asma’u ce kawai ta samu arziÆ™in isa gareta ta zauna tare da dafata tayi firgigit ta dawo hayyacinta sukayi ajiyar zuciya tare Asma’u tace “Bansan yaushe zaki daina keÉ“ance kanki daga cikin Æ´an’uwanki ba RUMAH shifa kowanne bawa da rubutacciyar Æ™addararsa kece Amiran masallacinmu kina É—aya daga cikin mutanen da suke fada mana abinda ya dace da rayuwarmu kuma Ni ina ganin wannan cire kanki É—in da kikeyi kamar shine dalilin da yasa suma suke janye jiki daga gareki domin basu mu’amalanceki ba bare su san wacece ke”
Jinjina kai tayi ta É—ago ta dubi Asma’u tace “Nasani da hakan ma Asma’u amma na kasa dainawa idan naga kowa a gidannan yana dariya Ni sai na rinÆ™a jin meye daÉ—in duniya bayan zama kusa da iyaye da har zai sani dariya? Meye abinda zai burge zuciyata da zai gusar min da ganin naÆ™asun rayuwata har na manta da tawayata nayi dariya irin dariyar shashashai Asma’u wannan tunanin dashi na budi idanu na ganni kuma bansan ranar gogewarsa ba.
Murmushi Asma’u tayi me É—auke da Æ™wallah tace “Shin dauriyar É—aukar nauyin Æ™addara muka fiki kenan da muke iya sanya dutse mu danne waÉ—annan tunane tunanen da suke bijirowa zukatanmu, anya Rumah imaninki dirarre ne da kike ja da hukuncin ubangiji….”
Saurin É—aga mata hannu tayi tace “Ba haka bane Asma’u mubar wannan maganar kawai Kinga manyan baÆ™i har sun fara zama….” Me gabatar da taron ne ya fara buÉ—e taro da sallama irin ta addinin Musulunci kafin ya kira Rumasa’u wadda kusan shekara guda kenan ita ke buÉ—e taro da addu’a, miÆ™ewa tayi ta nufi gurin da aka tanada dan tsayawa ta fara karanto addu’o’in nemawa Æ™asa zaman lfy da larabci take gabatar da komai har ta gangaro kan jihar ta ta Kano sannan ta fara gabatar da saÆ™on godiya, kamar haka.
“Hakika muna godiya ga Allah subhanahu wata’ala da ya azurta duniya da mutane masu jinÆ™an Æ™asÆ™antattun cikinsu tabbas maraici abune me ciwo da cin zuciya, duk da cewa siffa ce ta wasu nagartattun mutane amma babu wanda yake fatan ya buÉ—i idanu ya gansa cikin wannan hali saidai har in ya zama dole a karÉ“eshi don babu yanda za’ayi da hukuncin ubangiji.
To bare mu namu da ake Æ™irÆ™irar mana shi don ganganci da son zuciya abubuwa mabambanta sune suka zama Æ™addarar kowannenmu ta tashi ya riski kansa a wannan gida marashin cikakkiyar daraja a idanun al’umma duk da haka mukam muna godiya ga Allah daya sanya muka tashi muka ganmu cikin bayinsa waÉ—anda suke cikin bayyananniyar jarabawarsa……
Taci gaba da bayaninta cikin nutsuwa ta yanda sosai bayanan suke ratsa jikin duk wani wanda yake zaune a wannan gurin, bayan ta gama ta sauka a wajen gabatar da taron ne ta fice daga cikin hall É—in wanda kusan hakan ya zame mata É—abi’a bata iya zama a gama taro take ficewa ta koma can bayan hall É—in cikin ciyayi ta zauna tana karanta wasikar jaki.
Rumah Hausa Novel by Oum Hairan
Tananan zaune a gurin tsayin lkc tana ta tufka da warwara taji alamun tsayuwar mutum a kanta tayi saurin miÆ™ewa domin Allah ya jarabceta da tsoro musamman na maza hakanne yasa tana ganin baÆ™uwar fuskar taja baya da sauri tana shirin yin magana taga Mal Amin ya nufosu taja ajiyar zuciya ta mayar da hankalinta kan Mal Amin ya iso yace “Afwan chief House ne ya aiko kiranki sanin halinki da shegen tsoro yasa na biyo bayansu karki firgita ki zuba jeji da gudu”
Numfashi ta sauke tana wasa da yatsunta tace “Kay Sheikh wato tsoro ne gareni to ai tsoron ma cikin imani yake” murmushi yayi yace “Hakane biyoni” babu musu bare gardama ta nufi hanyar da taga sun bi suka nufi office É—in shugaban gidan suna zuwa aka bata umarnin shiga ta shiga cike da mamaki tasan dai ita iyakar rayuwarta a gidan tsayin shekara sha bakwai bata taÉ“a shiga wannan office É—in ba koda wasa to meye dalilin da yasa yau ake nemanta kuma neman a wannan office me daraja? To kodai wani laifi tayi? Gabanta ne ya faÉ—i tace “Na shiga uku idan nayiwa Chief laifi na mutu na lalace ni Rumasa’u”…..
Masu son karanta wannan littafi zaku tuntuɓe Ni ta wannan number a WhatsApp 09013718241, 300 ne PC 600 babu VIP ko ku tura ta acct 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin MTN.
*Oum Hairan*
*Page 3-4*
BankaÉ—a kabilan tayi sallamarta a karkatse tayita suka amsa ta zube a Æ™asan tiles É—in cikin yanayi na tsoro tace “Ina neman sassauci da yafiya idan wani abu na aikata wlh banyishi da niyya ba saidai ya kasance rashin sani….”
Dakatar da ita yayi ta hanyar É—aga mata hannu ta kuwa nutsu sosai tayi Æ™asa da kanta yayi gyaran murya yace “Bani nake nemanki ba Rumasa’u ga bawan Allan da yakeson ganinki…” ÆŠagowa tayi da sauri idanunsu suka haÉ—u tayi saurin yin Æ™asa da nata Duk da cewar nasa cikin farin tabarau suke hakan bai hana yi mata kwarjini ba.
Cikar kamala da kwarjinin izza ta mutumin ta sanyata jin wani shayi gami da sabon tsoro sun ɗarsu a zuciyarta yanda ya kafeta da idanunsa da iyakar su kaɗai kawai ake gani cikin naɗin rawanin me ɗauke da kunnuwa dake nuna tabbas yanada wani babban jiɓi da sarauta.
MiÆ™ewa yayi batare da yace komai ba ya nufi hanyar fita Mal Nasir yanata zuba masa gdy suka fice daga office É—in Chief ya dubeta yace “Rumasa’u kina iya tafiya”
Duk da yanayin kiran da yanayin sallamar sun bata mamaki bata iya cewa komai ba sai miƙewa da tayi ta fice ɗin kamar yanda ya umarceta ta nufi rumfar su ƙirjinta na bugawa da ƙarfi don tasan yau ta kaɗe da masifar Baba Lami. Aikuwa tana zuwa ta cafke ta ta rufe ta da duka tana masifar ta raina mata hankali tasan zatayi mata wankin kayan sabbin yaran da aka kawo mata taje tayi zamanta saboda ta rainata.
Haka ta karÉ“i wankin tana hawaye tana komai ta wanke ta shanya taje ta zauna a kusa da ita ta É—auki yarinyar É—aya tana bata madara tace “Baba Lami yaushe zaki nunamin Iyaye na?” Murmushi Baba Lami tayi tace “To ni yanzu me kikeso nake cewa dakene da zaki yarda Rumasa’u bansan inda zan samo iyayenki bayan suna da aka rubuta Miki da rezar a hannun ki RUMAH da manyan baÆ™i babu wani abu da aka bar Miki shaida kuma an kawomin kene tun kina shekara É—aya da rabi Kinga babu wani bayani da zaki iya bamu bare muyi rubutu akai saboda irin wannan ranar”
Rumah Hausa Novel by Oum Hairan
Jinjina kai tayi cikin tausayin kai da sallamawa muradin rai tace “yanzu Shikenan bazan taÉ“a ganin iyayens ba…” Masifa Baba Lami ta rufe ta da ita tana cewa “Bansani ba kajini da yarinya kinzo kin wani titsiyeni to wama ya sani ko bakida iyayen ballagazar uwar taki gajiya tayi da gantali dake ta zaÉ“i jefar dake…” Nandanan zuciyar Rumah tayi duhu mafi munin kalma a jiÉ“antata da zina abin yana nuÆ™urÆ™usar ruhinta.
Dare ya fara shiga amma bai hanata tashi ta fice daga É—akin ba ta nufi bayan dakin can da nisa ta sami guri ta zauna matasa ya ita yammata da samari sunata harkokinsu amma banda ita.
Guri ta samu ta zauna ta haɗa kai da gwiwa tana jan zuciya wannan ita ce babbar damuwarta a duniya ta kasa jurewa ta kasa rungumar wannan ƙaddarar kullum ita kenan cikin kunci da damuwa takanji dama ace tare take rayuwa da iyayenta koda sunfi kowa talauci a duniya.
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza uku Hausa Novel
-
Doctor Eshaat Hausa Novel
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi Hausa Novel
-
Aure da haihuwa Hausa Novel
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya Hausa Novel
-
Gangar Shedan Hausa Novel
-
Angon mata biyu Hausa Novel
-
A gidan mu take Hausa Novel
-
Bafulatanar Rugga Hausa Novel
-
Matar yaro Hausa Novel
-
Mr Bello Hausa Novel
-
Mijin Buzuwa Hausa Novels
-
Gidan Uncle Complete Hausa Novel
-
Yar aiki return Hausa Novel
-
Raggon namiji Hausa Novel
-
Uncle Datti Jikina yake so Hausa Novel
-
Fataucin Mata Hausa Novel
-
Juhud Hausa Novels Complete
-
Moon Hausa Novels PdfÂ
-
Yarima Ashman Hausa Novel
-
Bandirawo Hausa Novel
-
Matar makaho Hausa Novel
Powered by: www.mynovels.com.ng
Tana son tsira da mutuncinta a wannan rayuwa bata fatan nasabarta na nasheta kullum tana rokon Allah ya kawo mata sauÆ™i da salamar zuciya cikin wannan rayuwa daya nufeta da riskar kanta a ciki ta É“ata lokaci a gurin kafin ta rarrashi kanta ta tashi ta nufi inda ta baro tayi alwala tayi sallar magrib da Isha ta kwanta ranta a jagule ba wani isasshen bacci take samu ba kamar yanda baba Lami ta saba Æ™ananun marayun suna fara mata kuka ta tashe su ita da Asma’u sukayita aikin rarrashi ita tana baccinta basu suka samu suka koma ba sai gab da asuba suna komawa aka kira sallah dukkansu bacci a idanunsu haka suka nufi masallaci daganan suka tafi islamiyyar asuba bayan an taso ne sukayi ayyukansu na yau da kullum dake sun gama secondary hakan ya basu damar kwanciya bacci ya É—auke su suna kwance bacci me daÉ—i sukaji ana tashinsu Asma’u ce ta fara tashi ganin me tashin nasu yasa tsoro ya É—arsu a ranta ta tashi Rumah suka kalli juna me tashin nasu tace “kirane daga office na Maman gida” Tuni Asma’u ta nuna alamun tsoro itako Rumah me arhar hawaye hawaye ta fara sharewa ta miÆ™e ta É—auki hijjab É—inta Asma’u tace “Inajin tsoron kada muma abinda yake faruwa da sauran ya faru damu Rumah an kwana biyu ba’a fitar da mutane a gidannan ba abinda yake bani mamaki sai ace makaranta aka kaisu ko gurin koyon sana’a amma bantaÉ“a ganin wanda ya fita ya dawo ba anya Rumah gsky ne?”
Itadai Rumah bata iya cewa komai ba saboda abin faÉ—a na me baki ne kurma sai kallo, fita sukayi zuwa office É—in Maman gida tun daga bakin harabar gurin suka Æ™ara tattare nutsuwarsu ganin wasu dogarai tsaitsaye sunata muzurai kamar Mala’iku, da nutsuwa suka isa inda ake nemansu Maman gida ta dubesu sosai tace “Rumasa’u Asma’u yau lambarku ce ta fito mun saba fitar da yara irinku idan girma ya sauko musu mata muna kaisu Hukumar kula da marayu tana auraddasu maza muna kaisu su koyi sana’o’i don dogaro da kansu, to kuma yau insha Allahu zamu fitar daku yanzu an fita da Æ´an’uwanku domin auraddasu ke Rumah jiya munyi babban baÆ™o a gidannan Mai Martaba Sarki ya nuna bukatarsa da son Æ™ara bayi a gidansu yace yanason mutum uku maza biyu mata cikin matan yace yanason a haÉ—a masa da Amiran masallaci wannan tasa naga dacewar na haÉ—aki da Æ´ar uwarki Asma’u tunda akwai shaÆ™uwa zakufi sakewa kuyi abinda ya dace.
Ina rokonku kamar yanda na bayanku basu bamu kunya ba kuma kuyi abinda zaisa ace ala sam Barka ba Allah wadarai ba sannan kuyi Æ™oÆ™arin riÆ™e amanar maraicinku kuma kuyi hÆ™r da sabbin mutanen da zaku fara mu’amala dasu.
Jinjina kai sukayi jiki a mace ta nuna musu mutanen da suke tsaye don tafiya dasu suka miÆ™e Asma’u ta fara ficewa itako Rumah jan Æ™afarta kawai takeyi ta isa ga motar suna shiga sauran dogaran dake tsaye duk suma suka shiga motocin suka fice daga gidan sai lokacin wani kuka me sauti ya Æ™wacewa Rumah karon farko na fitowarta daga gidan nasu gidan data taso ta riski kanta a cikinsa tun bata fara fahimtar bambamcinsa da sauran gidaje ba har ta gane ashe da tazara me tarin yawa a tsakani.
Asma’u ce ta dafata ta É—ago da kanta tana girgiza mata kai tace “A yanda muka taso muka riski kanmu Rumasa’u ba komai ne ya kamata ya rinÆ™a taÉ“a mana zuciya har yasa mu ringa zubar da hawayenmu ba” riÆ™e hannun Asma’u tayi tace “na sani Æ´ar uwata amma bazan iya hana zuciyata matsa idanuna don fitar da ruwa ba yanzu mu Shikenan a haka zamu Æ™are bamu da wani farin ciki a tsarin ginin rayuwarmu mun taso ababen tsangwama da Æ™yanÆ™yami saboda naÆ™asun nasaba yanzu kuma zamu Æ™are guntuwar rayuwar a Bauta haba Asma’u yanzu wannan bai isa kuka ba?”……..
Masu son karanta wannan littafi zaku tuntuɓe Ni ta wannan number a WhatsApp 09013718241, 300 ne PC 600 babu VIP ko ku tura ta acct 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin
MTN.


​
Name: | [Rumah Hausa Novel by Oum Hairan] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV
Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi

Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi

Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram
