Rumaisa Hausa Novel

Rumaisa Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Rumaisa Hausa Novel

بسم الله الرحمن الرحیم

 

*_Ina fatan kamar yadda Allah yasa na fara wannan littafi lafiya yasa na gama shi lapiya_*

 

 

*Page 1&2*

 

_____📖Gidan yayi shiru bakajin komai sai k’aran ruwa da kwanoni wata mata ce gefe d’aya tana wanke-wanke. wanke kwanoninta take cikin kwanciyar hankali har ta gama tamik’e a tsaye tagyara dauri zaninta,

Duk’awarta keda wuya zata dauko kwanonin data gama wankewa taji kamar antura ta haka tafad’i a k’asa lokaci d’aya tajita a wani bak’on yanayi dak’yar tamik’e tana dafe da kanta ahankali take takawa har ta isa k’ofar d’akinta ta fad’i saman tabarma kwacetanata faman juyi hannayanta dafe da d’an cikin ta se matse kafafuwa take tana rintse ido bakinta na neman taimakon Ubangiji. wata matashiyar yarinya ce tashigo hannunta d’auke da kara tana rera waka,tana kai idanun ta kan matar dake kwance babu excuse tajuya aguje harda bal tayi da kwanoni dake aje suka watse bakidaya. Ba’ajima ba mata buyu suka shigo gidan hakkalin INNA atashe lokacin data hango ‘yar ta a shinfide kan tabarma.aguje ta k’araso har tana tuntib’e da kwanoni dake watse a tsakar gidan.

 

“Innanillahi wa’inna ilaihirraju’une,MADINA!MADINA!.” takira sunan ta shiru madina ko motsi bata yi,matar dasuka shugo atare take cewa ,”Inna daukarta zamuyi mutafi likita da’ita,tasuma tasuma SUWAIBA!dan allah taimakamin da ruwa.” Ayanayin datayi maganar ne yasa jikin Suwaiba yayi sanyi tausayi INNA yak’ara bayyana k’arara a fuskarta da hanzari ta nufi wajan randa ta d’ebo ruwa D’akin dake kusa da randar aka fito da sauri “ah !ah !ah !mezan gani haka Suwaiba da kanki menene zakiyi a b’angare na, kuma waya aikoki.”ta jero mata tambayoyin a tare.

 

Suwaiba tayi tsaye shiru tana mamaki dama akwai mutun cikin gidan katse mata tunani tayi ta hanyar anshe robar dake hannunta wanda zata iban ruwan dashi “Bakijina ne Suwaiba nace uban mekike nema anan?” “wai dama Adama kina nan.”cewar Suwaiba. “ga zahiri kuwa, mikeke so kisani.”inji Adama. “amma wlh bakida imani kwata_kwata bakida tausayi a rayuwarki.” “ke rufemin baki rashin kunyarki har yakai ki kalli tsabar idona kice min banida imani.” “Ai ba’a rashin imani kad’ai kika tsaya ba ,na lura kishin naki har da na bak’in ciki ga kuma hassada dayafi komai yawa daga cikin halayanki.” Katse ta tayi da cewa,”ke Suwaiba ni zaki isko har k’ofar d’akina kina gayamin wannan magagganun, to ya isa haka ruwa ne kuma bazan bayarba tinda bani na sumar da shegiyar ba.”

 

Suwaiba zatayi magana taji muryar INNA tana cewa ,”hanzarta Suwaiba ko babu ruwan ne?”

Gaba d’aya ta k’ara rud’ewa ko kula da Adama bata yiba wadda itace tahana Suwaiba k’arasawa iban ruwan.

 

“Adama kibani na ibi ruwa bakiga halin da Madina take ciki bane.”

Tayi maganar cikeda magiya tanamata nuni da Madina dake kwance INNa akan ta tana mata fita da mayafin dake jikinta,Adama Juyo da kallon ta tayi ga Suwaiba bayan ta gama kalle Madina tace,”to ai yanzu Madina bata bukatar ruwan dakuke son zubamata,kamata yayi kije ki sanar dame gari azo akaita makoncinta.”

 

Cikin rashin fahimta Suwaiba ta zaro ido,” me kike nufi Adama?” “Ina nufin MADINA ta dad’e da mutuwa.” Ta bata amsa kai tsaye cike da jin haushin kalaman Adama, Suwaiba tayi kukan kura ta k’wace roba tayi jifa da ita gefe daya, dum kaji Adama tafadi reras akasa. “wayyo hannu na , k’uguna, shikenan takarya ni Suwaiba muguwa allah ya’isa.”

 

ko ta kanta bata biba ta ibi ruwa aguje tamik’ama Inna. ana yayyafamata ruwa tafara nishi sama-sama cikin hanzari Suwaiba takamata suka nufi hanyar hita Inna nabiye dasu baya.

 

munute 30 dazuwan su hopital ,suna tsaye dan jira sakamakon ubangiji.

Wata yar karamar likita tafito dauke da jaririya tana kukan fitowa daga cikin mama,Suwaiba takarb’i jaririyar, Inna kuwa hankalin ta naga likitar tana tambayar halin da ‘yar ta take ciki,ba ta bata amsa ba takoma.

Muttuna biyar suna tsaye docteur yafito ya sanar dasu cewa,”Madina tananan Lafiya saidai tasha wahala wajen nak’uda tana bukatar hutu shiyasa nayi mata allura bacci nan da awa hudu zata farka.

 

Inna tayi godiya sannan tacema Suwaiba, “jeki tahoma Madina da kayan dazata canza sannan kid’oko duk wani abu da’ake buk’ata.” “cike da farin ciki Suwaiba tajuya zata tafi aikyan INNA hartakai k’ofar fita Inna tabiyo bayanta tana kiranta,”Suwaiba²!” ta juyo tareda k’arasowa wajan Inna. “dama dan ince miki ne dan allah kar ki kulla Adama duk Abidda zatace ki k’yaleta yanzu ba lokacin fitina bane.”

 

Suwaiba tayi murmushi sannan tace, “insha allah bazan biyema taba Inna.”

“yauwa,kuma kitura Surayya gidan megari dan sanar dasu muna asibiti.” “to Inna.” inji Suwaiba ta juya ta tafi.

Tana chiga gidan tafara waige waige ko zataga Adama ganin alamar bata gidan yasa ta shigewa d’akin Madina da sauri-sauri ta gaggama kayan da tazo d’oka tafice daga gidan tana cikin tunanin ina zata ga surayya,cen ta haggo wata’yar matashiya zata shiga gidan su Madina.

 

Karin wasu littafai da zaku so

“NABILA !NABILA.” Ta kira sunan ta Nabila ta juyo dan ganin wake kiranta ?ganin Suwaiba ce yasa ta d’an sakin fuskar ta tare da k’arasowa inda take tsaye. Nabila ‘yar budurwa ce tanada shekaru 14 ,bayan sun gama gaisawa ta sanar da ita haihuwar Madina tare da cewa taje ta sanar da yan gidan su.

Gudu² sauri² Nabila tak’arasa gidan su.

Babban gida ne doke da d’akuna jere har guda bakwai se d’aki d’aya yana kallon d’akuna , yana d’oke da makekiyar ruffa a gaban d’akin.

 

Mata uku ne lantizawa zaune acikin runfar,Nabila tadoso wajan su tana washe da baki d’aya daga cikin matan ne tafara magana kamar Haka, “ta dini ikon allah kamar bakece kika fita yanzu da b’acin raiba yanzu kuma kamar wadda aka biyawa makkah, abamu muji, koko dai shamsudin ne yadawo?” takarasa maganar tana k’aifta mata ido cikin irin wasar data saba yimata,Nabila da har yanzu bakin ta a bud’e kamar ta fasa ihuu dan farin ciki ta ce, “Anna , Adda , Baba albishirin ku?”

 

Anna ta amsa dacewa goro Nabila ta b’ata rai cikin shagwab’a tace “Anna kad’ai zata bani goro Baba keda Adda bazaku kulani ba?” Adda ta kalleta sannan tace,”ke idan bazaki fad’i abinda ya maido kiba to kifice min da gani.”

 

K’ara yamutse fuska tayi kamar zata kuka shiru tayi tana kallon ADDA ,kome ta tuna sai ta fashe da dariya ta haye saman k’afafuwan Adda tace,”ai wannan albishir d’in bana ayi zuciya bane atafi ak’i fada, ko za’ayi kuka ne sena fada, Adda kina jina baba da Anna ku saura reni da kyau, ku shirya tarben zuwan kishiya dan Baffa yasamu amarya fal aleda.” ta ida maganar tana tashi daga saman k’afar Adda.

See also  Rauf Aregbesola and Tinubu Are they fighting

Baba wanda ke gefe daya tana ta faman tsince duwatsu dake cikin aya wadda take shirin yin kunu da ita da sauri ta d’ago fuskar ta tace ,”mikike son cewa Nabila, wane albishirne kike son gaya mamu ”

 

Nabila tace,”Madina ta haihu tasamu d’iya yanzu nagamu da manma Surayya tazo d’okar kaya tace nazo nasanar daku suna likita,”. Baba da kamar an gaya mata mutuwa haka taji maganar da k’yar tace Allah ya raya taci gaba da aikinta.

 

Anna kuwa zaro ido tayi tace,”Madina ta haihu kuma tana nan lafiya da abinda ta haifa shima yana nan lfy?”ta tambayi Nabila.

 

Nabila dake tsaye takasa gane kalar tambayar da Anna tayi mata se sake jin wata tambayar tayi daga bakin Adda,”keh Nabila gayamin badai Suwaiba ce takai Madina likita ba ,to da izinin wa sukaje?”

 

B’ata b’ata fuska tayi sannan tace,”Adda haihuwa nazo gaya maku ba kisan kaiba ko ince ba mutuwa ba ,kamata yayi kuyi farin ciki….

 

“yimin shiru shegiya marar zuciya , da ace ‘yan asali kika zo gayamin sun haihu da kinga murna harda bud’a, amma kizo sanar min cewa shegiya ‘yar tunanin marar asali ta haihu kuma kiyi tinanin zanyi farin ciki?”Cewar ADDA wanda itace mahaifiya ga Nabeela.

 

Cike da jin haushin kalaman mahaifiyar ta tajuya zata bar wurin

Muryar baba taji tana cewa,”laifin ai duk na Suwaiba ne, tad’oki Madina kamar k’auwar uwar ta , har zata shigo cikin gida tad’o keta ta kaita likita, to da umarnin uban wa?”

 

Nabila ta gilgiza kai da sauri ta Nufi k’ofa zata bar gidan dawo wa tayi ta nufi d’aya daga cikin d’akunan da sallama ta shiga bata jira amsa ba ta bud’e ridon d’akin.

 

Matar dake kwance saman mantela ta amsa sallamar tare da tashi zaune kusa da k’afafuwan ta Nabila ta zauna ganin Nabila tayi shiru bata ce da ita komai ba sannan yanayin jikin ta duk yayi sanhi,Matar tafara magana kamar haka,”ta dini lapiya na ganki haka waya tab’o mini ke?”Nabila tace,”su baba ne, wai nazo gaya masu samun k’aruwa amma kamar na gaya masu tashin hankali,kowa se fada yakemin to HAJJA minene laifin Suwaiba?” ta ida maganar tana kallon wadda takira da Hajja.

 

Hajja tace,”ke gayamin mikika fad’ama masu?” “Madina ta haihu tana likita.” Hajja ta hiddo idanu tace,”yaushe Nabila?” tayi dariya sannan ta ce ,”yazzu_yazzun nan ba’a jimaba Suwaiba tagayamin”……

 

 

*_YANZU LABARIN YA SOMA KUBIYONI DANJIN KALAR SAKON DAYAKE TAFE DASHI_*

 

 

_Pls Comment & Share_

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحیم

 

*Page 3 & 4*

 

📖…. Hajja ta miÆ™e tsaye tare da rangaÉ—a buÉ—a ,” alhamdulillah allah ya sauki Madina lafiya baiwar allah,

mi aka samu?” ta tambayi nabila.

 

Nabila tamiÆ™e tsaye murna tadawo sabuwa. sannan tace, “Hajja kishiya kuka samu.

Hajja taÉ—oko mayafinta tana cewa,”bade kishiya ba zomuje ki gayamata ta makara dan mun kulle Æ™ofa saidai abuga a tsakanin mu idan tayi nasarar fidda É—aya daga cikin mu seta shigo.”

 

Dariya Nabila tayi sannan tayi Æ™asa-Æ™asa da murya tace ,”kinsan kowa za a fidda idan zata shigo?”

 

Hajja tana Æ™oÆ™arin yafa gyalen ta tace ,”inajinki ta dini.”

 

“Baba, baba ita zata fita takoma daga inda tafito.”

 

“ja’irar yarinya kin medamu kamar wasu kakan ninki ko?” inji Hajja.

 

 

Tana dariya har suka fito , Hajja tak’araso wajan su Adda, Ganin tanufo wajan su yasa sukayi shiru da maganar da suke kowa ya d’aure fuska.

 

“Zamu tafi asibiti wurin su Madina.”

 

Bawadda ta amsa mata seda ta juya zata tafi Anna tayi k’arfin halin cewa ,” ku gaida mejego.”

 

Suna ficewa daga gidan Baba ta sauke ajiyar zuciya tace ,”Adda kinga waccen munafikar matar yau gurinta yacika tasamu damar dazatayi amfani da’ita ta kwashi rabon ta.” Adda ta medo hankalinta bakid’aya wajan Baba.

“ban fahimce kiba mikike son cewa?”

 

“kinfi kowa sanin yanda megari yake ji da Madina toya zata kasance idan aka kai mishi labarin haihuwar ta ,ke ba wannan bama kinsan irin kud’in da ake kashewa abikin gidan nan ballen tana ace bikin jika na farko ga megari ya kike ganin bikin ze kasan ce?”

 

Adda tayi shiru bata ce komi ba,

 

Baba taci gaba dacewa ,” bari nafito maki a mutum duk wata siyayya daza ayi a bikin nan Megari shize bada kud’i daga ke har ni bawanda zenufo da zancen siyayya balle yabamu wasu kud’i,waccen Hajja datake nuna son Madina ita zebawa komi sannan idan tace yakawo ko nawane za’a sayen wani abu to babu gardama zai dank’a mata,

To seki gayamin mu shikenan mutashi tutar babu kennen .”

 

Adda tayi sauri daga murya,”billahil azim baze tab’a yuwuwa ba nasan yanda zanyi ki barni da’ita.”

 

Bayan an sallamo su daga likita misalin k’arfe 5 na yamma ‘yan barka ne suketa kai komo duk wanda ya kalli jaririya seya tanka farin ta gami da jikin da take dashi masha allah wata mata data shigo cewa tayi ,

 

“duba kiga Madina kinyi irin haihuwar nan ta turawa seka rantse ba a k’auyen nan aka haifi wannan ‘yar ba.”

 

Suwaiba dake gefe tana gyara shinfidar jaririya tace ,”masha allah,Amina dan allah idan kinje gida kicewa malam ya taimako mu da rubutu na baki abawa jariryar nan kowane me baki ya shigo bazai gani ya k’yale ba.”

 

“dole ne Suwaiba, duba fa kigani kin tab’a ganin irin haihuwar nan a k’auyen nan?”

 

Suwaiba tatarin numfashin ta dacewa ,” shiyasa nace kicewa malam ya taimako mu da na baki saboda idan munsan bakin ku bamusan bakin wasu ba.”

daganan Amina bata k’ara cewa komi ba har tabar gidan .

 

Kusan k’arfe shidda gidan ya d’an tsagai ta da mutane, ya rage daga MADINA sai INNA dan haka tace da ita, “Madina inason tafiya na baro gida abude saidai banaso nabarki ke kad’ai.” Madina tace ,”yanzu duk inda Adama take tana hanyar dawowa dan lokacin dawowar baban gida yayi,sannan yanzu Nabila zata zo …. ”

 

Bata ida rufe baki ba sega sallamar Nabila Inna tamik’e tana cewa,”yawwa bari ni naje, zuwa safe zan dawo zamu san abinyi.” bayan tafiyar INNA gidan yarage se Nabila da Madina.

 

Adama ta dawo gaf da magriba hannunta a É—aure anyi mata É—ori acewar ta Suwaiba ta karya ta ….

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحیم

 

 

*Page 5&6*

 

_____📖Kowa na gefan sa, Adama ko kallen inda Madina take batayi ba.

duhu yafara, Moustapa ya chigo da sallamar shi, benufi ko inaba se wajan Adama da d’an buhun sa ahannu.

“Mizan gani Adama, miya sameki ?” ya k’arasa wurin ta da sauri

 

Muryar Nabila yaji tana cewa, “baban gida gaisuwa”

Shareta yayi ya ajiye buhun shi, jiki na masa zanzana ya zauna kusada Adama yaci gaba da tambayar miya faru da ita??

See also  Download Angon Mata Biyu Hausa Novel

 

Adama tafara dacewa, “dama kai nike jira Mustapa,tinda yanzu ni banida wani ‘yanci ko mutun ci cikin gidan ka, dole najira kazo, saboda kai ka’ajeni seka nemamin mutun ci na”

Cikin rashin fahimta yace, “Adama ki sanar dani miya sameki?”

 

Nan ta kwashe komi tagaya mishi harda cewa, Suwaiba da Inna suka kwashi ta, suka nufi likita,ko wace tsiyar sukayo kuma suka kwaso suka dawo da’ita”.

(nikuma nace tap bakima san kun samu beby girl ba)

 

Cikeda masifa yakecewa, “Ai idan akwai me mutun ci da ‘yanci be wice keba, kuma yau zan nuna maki kinfi kowa daraja a gidan nan; wacece Madina da har Suwaiba zatayi tink’awo da ita tashigo har cikin gida na ta dukar min mata,

To yau sedai ki kwana gidan Suwaiba badai a gidan Mustapa ba .”

 

Madina batace komai ba se kallo da take biyar shi dashi.

 

Nabila tace, “Baban gidan, kafin ka yanke hukunci kafara yin bincike, sannan murna ta dace dakai ba b’acin rai ba”

Cikeda tsiwa Adama tace, “ke Nabila yaushe kika fara fad’a idan magajin ki yana magana,kokode kema angama dake kamar yadda aka gama da baban naku”

 

“k’yalewar ki Adama, ke Nabila xo ki wice, dama Madina kikazo tayawa kwana, to yau itama bazata kwanar min agida ba”.

 

Se yanzu Madina tafara magana tace, “Mustapa, wlhy ko zaka koreni, yanzu dai bazan fita daga gidan nanba”.

Da sauri yayo kanta yana cewa, “to bari na nuna maki nikeda gidana ba keba”.

Turus yayi tsaye cak ganin jaririya saman cinyar Madina kwance , Adama ma haka, tana biye da shi baya , ganin jaririya ne yasa itama tayi tsaye, bata k’arasa wurin suba

 

Sallamar da akayo daidai lokacin ne yasa gabad’ayan su suka maida hankali dan ganin masu shigowa

 

Hmmmmm Nabila ta sauke ajiyar zuciya “yauwa, gara da allah yasa kukaxo yanzu, gayanan cewa yayi mubar masa gida daga ni har Madina wai bazamu kwana a nan ba”

 

Adda tafara magana

 

“mike shirin faruwa ne naganku curko curko”

 

Nabila zatayi magana, Mustapa yayi sauri cewa, “bakomi Adda, shigowa ta kenan gidan bamma san anyi haihuwar ba se yanzu Nabila take gayamin”

“yazaka ce babu komi baban gida, kunne na yajimin Nabila tace, kace bazata kwanar ma a gida ba,to data yimaka mi?”

 

“Nima naji tace harda Madina to da’akayi mi?” Cewar Anna

Mustapa yace, “dama raina ne ab’ace,Suwaiba ce tazo har cikin gidan nan ta karyama Adama hannu”

 

“Baban gida idan ba a gabanka akayi abu ba, na gaya maka, kadena kama zantuka barkatai, yazaka dubi Adama kace Suwaiba ta karya ta, Suwaiba duka ta yaushe?” inji Adda.

 

Baba da se yanzu tafara magana tace,”abar zancen nan, mu samu wuri muyi abinda ya kawomu”

 

Nan suka zauna rumfar Madina,

Mamaki ya isheta, karo na farko kenan dasuka fara zama a kusa da ita (Madina)

 

Nabila ta dawo da’ita daga duniyar mamakin data tafi, lokacin dataji tana cewa, “kinga ko Baba, Anna matso kema kigani duk kauyen nan babu wanda yakai bebin mu kyau,kuduba ku gani”.

Adda tad’aga mata kai alamar E.

Baba kuwa ko kallan inda bebin take batayi ba, se Anna dake k’ok’arin d’okar ta tace, “bari nagani, ance tafimu Kyau, nide nasan bata hini kyau ba sedai insu Baba zatafi”

 

Madina tayi murmushi tana kallan ikon allah.

 

Adama dake gefe tsaye itama mamakin take tarasa gane mike shirin faruwa.

 

Adda ta gyara murya sannan tace, “Baban gida samu wuri ka zauna, ka saurari abinda yakawoni”

 

( Mustapa wanda ake kira da baban gida shine d’a nafarin ga megari, Adda itace mahaifiyar shi )

 

Shima mamakin yake, ya zauna kusa da Madina yana kallan d’iyarshi sabuwar haihuwa dake hannu Anna, Nabila nata zuba mata surutu baisan lokacin da yayi murmishi ba.

 

Adda tafara dacewa,

“dama dan ingayama kane, gobe Madina zata koma can gidan mu dazama, har se tayi arba’in sannan zata dawo, dan haka ke Madina seki shirya tinda sassafe zuwaira zatazo tatafi dake (yar aikin gidan me gari ce)

Madina tace, “to Adda, amma da anbarni har ayi bik…

Baba ta katseta dacewa, “seda mukayi tinanin haka, amma bikin acan zefi Kyau,sannan mun riga mungama yanke shawara da megari kinga ko maganar shi bame tashi bace”.

Madina tace, “to allah yasa alkhairi”.

Amineee.

 

Bayan tafiyar su, Mustapa yace, “Nabila jekifara tattara mata kayan dazata tafi dasu, bari na watsa ruwa sena kama maki k’ulle kayan”

Tace “to”.

 

Adama kuwa, koda su Adda suka tafi ta shige d’akin ta tana sake² aranta cike da mamakin yadda Adda take magana kamar batasan da ‘ita agidan ba, toya akayi haka, lokaci guda suka sauya, koko dan Madina ta haihu ne, Aiko idan hakane nima naci alwashin sena haihu kota halin yayanee,. Hummm lalle Adda watan rabuwa da É—anki yakama, itakuma Madina kunja mata rabuwa da Mustapa……

 

 

 

*Plss Comment & Share*

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحیم

 

*Page 7&8*

 

____📖”Nabila tashi ki fara had’a ma Madina kaya”

Nabila tamik’e tsaye tana cewa ” to baban gida bari nayi maza, inaso naje gidan su Surayya muyi zancen anko daga nan kuma muje mu sanar da sauran k’awayen mu”

 

” Nabila uwayen zanzana ai kyabari har gari ya waye”

 

” ah ah ai dare beyi ba kuma kusane inda zamuje ba dad’ewa zamuyi ba ”

 

“to kina nufin Madina itakad’ai zaki bari”

“Ba gaka ba ” inji Nabila

 

Shuru yayi kafin yace ” nida zani masallaci, nimafa saurin nake na sanarwa mutane cewa nazama baba ”

Dariya ta kubcewa Madina itama Nabila dariya takeyi. Murya Adama sukaji tace” Mustapa inaso nayi magana dakai.” babu gardama yamik’e suka nufi d’akin ta.

 

” Anya kuwa wannan y’ar takace!?”

 

Kalmar data girgiza baban gida lokacin da Adama ta jefo masa tambaya.

 

“Ban fahimceki ba Adama mikeke son gayamin”

 

” lalle akwai wata ak’asa ni nasani,ba banza ba” inji Adama.

” wai mikike nufi ne, kin sakani a duhu, dan allah Adama kitafi da maganarki kai tsaye”

 

Adama tace ” ko tantama banayi wannan y’ar bataka bace ”

” miyasa kika ce haka”.

“Dubawa zakayi da kyau gabad’aya bata kama da kowa a cikin dangin ku , hasalin ma komi nata iri d’aya da na Madina ne , sannan ka duba da kyau wannan jaririyar batayi kama da d’iyar yan kauyen nan ba, jaririya sekace aljana komi nata fari ”

 

Shuru baban gida yayi Adama taci gaba da cewa ” ni tsoro na kar azo abinda ake zargi kan Inna da Madina yazama gaskiya.”

 

Tana fad’in maganar idanun ta kan Mustapa wanda tsoro ya baiyana Æ™arara a fiskar shi…..

 

_Wacece Madina kubiyoni dan jin amsar wannan tambayar_.

 

 

*Share & Comment*

 

Niger

 

بسم الله الرحمن الرحیم

 

*Page 9 &10*

 

____📖 zaune yayi saman d’an k’aramin gado dake manne a d’akin jikin sa a sanyaye ya rasa ta inda zaya kamo maganar Adama ya fassara ta; lokaci guda yafara tinanin yadda aka d’aura auren su da Madina…

See also  Tambadaddiya Hausa Novels

 

 

Wani lokaci abaya

 

….k’auyen Ciro,gari ne me nisa, ana tafiyar awa d’aya daga Agadez kafin akai Ciro. Basuda yawan mutane amma akwai albarkatun gona wannan yasa duk ranar juma à da laraba garuruwan mak’onb ta su kanje cin kasuwa dake tsakiyar k’auyen.

 

Alhaji Bala shine shugaban k’auyen wanda ake kira megari mahaifin Mustapa.dattijo arziki me fad’ar gaskiya da son cigaban k’auyen sa, kowa yasa halin shi baya goyon bayan k’arya, gashi da yawan sadaka; fara’a da son yara wannan d’abi’ar shi ce da take birgue mutane.

 

wata rana a fada misalin k’arfe biyar na yamma , megari na zaune suna tab’a hira shida mutanen sa , sallamar da akayi ce tasa su maida hankali ga me sallamar, Ali ne kowa yasan shi a k’auyen yana bada gudumuwa sosai ta b’angaren shige da fice , ana ganinshi fada to lalle akwai wani labari ; sedai bashi kad’ai yake tafe ba a wannan karin, ya taho ne tare da wata dattijuwa fara tas tana rik’e da yarinya me kimanin shekara 10 itama yarinyar fara ce amma batakai hasken dattijuwar ba. Ali na gaba rik’e da k’ulli kayan su, sukuma suna biye dashi baya.

 

Seda aka basu izini sannan suka zauna, kowa hankalin shi da idanuwan shi na kan bak’in fiskokin nan.

 

“Ali ina kake tafe da uwannan turawa?” inji bafade.

 

Ali yace ” ranka shi dad’e y’an lab’e nazo wicewa ta iyakar cikin gari da fadama, na gamu da wannan baiwar allah tare da d’iyar ta, ta cemin dan girman allah suna buk’atar taimako; nikuma nace baride nakawo su fada shine muka taho gasunan.”

 

Megari yace ” ina wini baiwar allah”

 

Murya a wahal ce ta amsa da k’yar cewa ” dan allah ranka ya dad’e ataimaka min da wirin zama”

 

” baiwar allah daga ina kike, kuma wacece ke ??” inji megari

 

” ranka ya dad’e sunana Zeinabou ana kirana da Inna, wannan y’a ta ce sunan ta Madina, muna zaune ne a k’auyen Diffa, sakamakon rashin kwaciyar hankalin da muke fama dachi ne yasa bama fita waje, ko kasuwa maza basa zuwa sabida tsoron ÿan ta’adda, yau kwanan mu ukku kenan da watsamu da’akayi cikin daji, wasu an kashe su,antafi da wasu , allah kada’ai yasan inda yan uwana suke , miji na da yaro na bansan inda zamu had’u ba ”

 

kuka ne yaci k’arfin ta tayi shuru tana shara hawayen dake kwaranyya a fiskar ta……

 

 

*

_Écrit_ _par_ _Roufaida_ _laouali_

 

 

 

_{{ wannan Æ™ungiya ce É—ai tamkar da duba kullum burinmu shi ne mu faÉ—akar da al’umma domin su gane gaskiya,(AlÆ™alaminmu ‘yancinmu Æ™asarmu abar alfaharinmu )}}._

Niger

 

بسم الله الرحمن الرحیم

 

*Page 11 & 12*

____📖”Innanillahi wa Inna ilaihir raji’un , allahummah ajirni fi musibati wa’akalifni khairi minha, ya ubangiji ka shiryar da wannan bayi naka da suka damu al’ummah Annabi , idan kuma ba masu shiryu wa ba ne ya allah kayi gaggawar d’okar mataki a kan su”

 

Gabad’aya suka amsa da amin.

 

Megari ya kai Inna gidan shi tare da y’arta Madina. lokacin da suka shiga gidan Adda ce zaune tana d’aure wa Nabila kai . bayan sun zauna megari yace” Ta dini jeki yomin magana da sauran iyayen naki ” ta amsa da toh.

 

Bayan dukkannin su sun fito, kowaccen su ta samu wiri ta zauna fiskokin su d’oke da alamar tambaya musamma Anna Wanda itace matar megari ta buyu.

 

” Baba, Hajja, Anna, da ke Adda, inaso ku dubi wannan baiwar allah, tazo ne tana buk’atar taimakon wajan zama sakamakon yan ta’adda da suka kai hari a garin su, sun k’arb’e masu komi sannan sun raba su da k’auyen su , yan uwa da mazajan su duk sun watsa su abin tausayi”

Yaci gaba da cewa ” ni a matsayi na na megarinnan na karb’e su, zata zauna itada yarta a k’auyen nan , abinda yasa na kiraku dan na sanar daku ne sannan ku bada shawarar ina za’a bata ta zauna itada yarinyar ta har allah yasa ta had’u da mijin ta ko wani dangin ta.”

 

Anna tace ” allah sarki megari masu aikin lada hakan yanada kyau , amma wani hanzari ba gudu ba, allah ya taimaki shugaban mu baka tinanin taimako yazame mamu aiki duniyar ga data lalace , ban hana a taimaki wannan dattijuwar ba sedai tsoron kar azo k’arya ta shirya maka, ayimin afuwa idan na fad’i bâ daidai ba.”

 

” kin fad’i gaskiya Anna kuma wannan shine tinanin duk wani d’an Adam idan har be sa allah agaban shiba ya sa tsoro a zuciyar shi , sannan akwai wata k’issa da tazo cewa tsoro idan yayi yawa jahilci ne , karki yarda tsoro yayi tasiri a ranki hakan yana sa rashin yin nasara ya haifar da fad’uwa, sannan akwai rashin yarda wanda yake haifar da zato, ba se na gayamaki ba zato zunubi ne koda yazama gaskiya haram ne , dan allah karku kawo rashin yarda , maimakon aikin lada ku haifar ma kanku zunubi.”

 

Anna batace komai ba se Baba Wadda idanun ta na yawo kan Inna da Madina ita tace ” hakane megari allah ya bamu ikon zama lpy gabad’aya.”

Hajja wadda itace amarya mata ta hud’u ga megari tace” sannun ki dazuwa, minene sunanki da kuma sunan yarinyar ki? ” fiskar ta d’oke da murmushi tace ” sunana Zeinabou ana kirana da Inna , ita kuma sunan ta Madina y’a ta ce ta buyu tanada d’an uwa Isma’el amma bama tare ban san inda yake ba.”

” kiyi hakuri insha allahu idan da rabon zaku had’u se kiga nan bada jima wa ba allah ya bayya na maki shi.”

 

Bayan sun gama yanke shawarar inda Inna zata zauna;

da farko megari yaso abata d’aki a gidan sa amma hakan be yiyu ba dalilin Anna, alamu sun nuna bata buk’atar zaman ta a gidan shiyasa ya bawa Inna makulli wani d’an aramin gidan sa ta zauna a ciki.

 

Nifa ga bakid’aya ban yarda da wannan matar ba , wlh hankali na be kwanta da ita ba , ba kwa ganin tafi kama da irin mutanan nan wa yanda ake koro su idan suna maita, sannan gata fara tas har tafi yar ta haske se kace aljannu, wlh Adda ki iya gayama megari kar azo garin kwashe kwashen shi ya kawo ma mu annoba ga gari.”

 

” dan allah Anna ki bar maganar nan , idan megari yaji bazaya ji dad’i ba, idan bakin ki ba zaya fad’in alkhairi ba to kiyi shur…”

 

” Hajja kidena saka mani baki idan kinji ina magana ta koko yanzun nan na fad’amaki wadda zata maki zafi” inji Anna.

 

Allah ya baki hakuri, kalmar da Hajja ta fad’a kafin ta mik’e ta shige d’akin ta.

 

Yau kwanan Inna ukku , labari ya gama zagaye gari cewa anyi wata bak’uwa tare da yarinya baturiya, megari ne ya sabke su gidan shi wanda babu kowa. Yara, matasa maza da mata sunata kai komo dan ganema idan su Madina , wasu suna shiga su gaisa wasu kuma daga k’ofa suke lek’e dole se sunga wannan yarinyar da ake cewa tafi gabad’aya yan k’auyen kyau. Suwaiba itace mak’onbciyar Inna ahankali suka fara sabo har tana shiga gidan suna hira wasa da dariya lokacin Suwaiba nada cikin Surraya tareda kishiyar ta Asabe…..

 

 

​

 

 

Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


*Plz share & comment*

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top