Hausa Novels

Ruwa Hausa Novel

Ruwa Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

[23/09, 9:06 pm] +234 806 897 4831: *RUWA…!!*

Adventure story🌊

 

PAGE 2

 

Shiru Nur tayi har suka isa gida shi kuwa aljanin ruwan bai fasa bin su ba har gida. Kasancewar Masunta suna kafe gidan su kota halin k’ak’a yasa shi tsayawa a kofar gidan, yana kallon su har suka shiga domin yana ganin gidan kamar anyi an mishi katangar karfe da shiga gidan, cikin fushi ya juya a saman iska ya koma ruwa.

 

Tunda suka shiga cikin gidan, Sarkin Ruwa ya wuce wurin dan uwan shi ya zauna rai a jagulee. Kafin ya fara magana.

“Yaya ina son a nisanta Nur da garin nan domin akwai matsala”

“Matsala kuma? Kamar ya?”

Idanun sarkin ruwa ne yayi jajjur sannan ya ce mishi.

“Itama kamar Attahiru take”

 

Yadiko da take kofar shiga dakin sake akushin hannun ta tayi, tana me juyawa dakin ta da sauri ta sami Nur tana saka kaya.

“Ban gane ba Abubakar?” Ya tambaye shi a rude.

“An haife ta da wannan alamar a gadon bayan ta, shi yasa take mugun kaunar Ruwa! Kuma kasan shima ya hakura ne domin al’umma su rayu”

 

A dakin kuwa wani irin runguma yadiko ta mata, tana me fashewa da kuka.

“Kema kamar Attahiru ne? Don Allah kar ki tafi ki bar ni ina da sa rai akan ki ”

“Yadiko me kuma Abbana yayi?”

Wani irin kuka ne ya kwace mata, tana me rike hannun ta.

“Don Allah kar ki ce zaki amince kamar yadda yayi ”

..

“Kana nufin sun ki amincewa da Hadayar kenan?”

“Shine gaskiyar maganar, sunce ita suke buƙata amma.”

“Hmm!”

“Koda iya numfashin mu da nata ne ya rage zan bada nawa rayuwar tatta rayuwar ya rayu, dan haka a fitar da ita daga wannan gari kota halin k’ak’a”

 

.. A dakin Yadiko tayi kuka tayi matukar shiga damuwa da firgici, domin dakyar tayi sallah tana manne da Nur. Koda dare yayi kasa cin abinci tayi amma taga Nur din hankalin ta kwance.

 

Da wannan al’amarin suka kwana hankalin a tashe.

*””

Kasancewar akwai masu fita fitto a daddare, dan haka suka fita niman kifi wanda washi gari zasu kawo gari a saya. A can ƙasar ruwa karkashin ruwa sosai wata hadaddiyar daula ce me zaman kanta inda al’ummar aljanu suke rayuwar su cikin kwanciyar hankali. Koda ya fada ruwa nutsewa yayi ya dira a babban birnin su me suna Furr. Ganin yadda ya diro yasa kowa ya fara gudu ga yarima Ashman ya fito abin da ba a cika gani ba, ai kuwa ya takarkare ya fasa wata uban ihu sai da ya janyo wata kamar girgizan kasa wanda ya haifar da ambaliyar tekun babu ji babu gani. Da wani irin gudu ya isa cikin fadar su yana kallon yan uwan shi da sauran al’ummar su.

“Ita nake so!”

“Kayi hauka, Ashman Raudah da tace Attahiru take su mutuwa tayi balle kai, bil adam irin su suna amincewa da sadaukarwa ne ba da shirme ba, kuma suna mana biyayya ne ba dan suna tsoron ba, wancan banzan tsohon yaja kome makiri kawai”

“Rayha kana nufin kai baka amsar haddyar ce?”

 

“Bana amsa domin babu dalilin yin haka an amsa daga gare su kamar bautar mu suke, Allah ya halicci mu ne dan mu bauta mishi ba wai su bauta mana ba”

“Rayha kai yi min shiru na bar maka mulkin nan ba wai dan bana so bane a’a kawai nayi haka ne dan bani son wahala amma Nur nake so kowa ya sani ita nake so ”

“Ai kuwa da alamu zaka koma makomar da Raudah tayi domin su bil adam ba a musu dole ba a tilasta musu ba tare da sun nime taimakon Ubangiji ba”

 

“Kayi min shiru ” ya daka mishi tsawa, dan dole Rayha yayi shiru, kafin ya girgiza ya zama katon kifi ya ficce daga fadar domin bai da abin zai kuma musu Haushin kowa yake ji, wakili ne ya bi bayan shi yana faɗin.

“Kayi hakuri mu shawo kan matsalar wannan ba wani abu me wahala bane idan ta kama ka aure ta ba shi kenan ba, yadda babu me kuma maka wani abu ”

 

“Fita ka bamu wuri munafiki” ya fada yana daka mishi tsawa, baki daya hankalin shi da rayuwar shi ya koma ga Nur. Yarinyar da bata san me suke yi ba.

*TOP-NOTCH WRITERS*

 

 

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*

 

_Kasancewar bikin kanwata ake ta biyar me suna Zahrah sai kaiwa da komawa nake Hankalina yana kan Babbar kawata Farisah tsaki nayi na wuce can na kuma dawowa na zuba mata ido cikin takaici mahaukaciya ta zare_

 

_Malama kin zo biki ne ko kin zo karanta chat kin yi shiru kin b’ata shiru_

 

_Wani banzan dariya ta saka min tana d’age min gira_

 

_Hmmm Bestie wai ke ko irin karance-karancen social media baki yi irin su Wattpad,Okada, Arewabooks baki yi?_

_Sake baki nayi ina kallon ta. When rabona da Hausa Novel Allah na tuba tun Iyatuh Abba tana karanta a gidan Radion B.R.C tabe baki nayi na ce mata_

_Ke rabani da kayan wahala rabona da Hausa novel tun zamanin Iyatuh Abba_

 

_Innalillahi!, Tace tana kallona kafin ta ce. Jasmin yanzun don Allah duk cigaban da aka samu baki san da shi ba? Lallai kin wuce yadda nake tunani kin gani wuri na karanta book din da nake fama da shi_

 

_Cikin mamaki na wuce na dawo na zauna kusa da ita nace mata don Allah daura ni a hanya ina ganin kowa na karance-karancen amma ban dani_

 

_hmmm lallai zata fashe… Toh saurara da kyau nan da kike gani na karanta books nake na marubuta daban daban amma idan ana dara ana fidda uwa… Kin ga last na ga The Governor’s Wife, one to three, after ma gama na karanta Zaytoonah…. Abun dad’i sai na cikaro da Affiyah da Unaisah_

 

_Allah Aunty Rukayyah kina karanta online hausa novel ne? Lallai toh ai yanzu ina karanta Zayn Malik Jiya na gama karanta Zanen ƙaddarata,_

_Kanwata Amaryan da muke bikin ta ta saka mana baki a she ba banza yarinyar nan ta nace daga gama sakandare tace a direta gidan miji_

 

_Amarya Zahra toh kuwa nima Zayn Malik nake karantawa musamman rigimar Hajiya da Uncle Bashir, da Zayn da Abul amma kin san zata fashe on October?_

 

_Don Allah fa_

_Hmmmm gamayyar marubutan nan sun hade wuri guda za ta fashe sun fitar da sunan Team din su_

 

_Aunty Don Allah ya sunan Team din?_

_TOP-NOTCH…. Za ta fashe a books uku Sahla A Paris, Bani Da Laifi Abin da Ya baka Tsoro_

 

_Wow da gaske?_

_Zan Miki karya ne?_

_Ina da number Mai_Dambu bari na duba nasan zata daura a status…._

 

_juyawa tayi ta kalle ni ina bin su sa kallo ke kuma ko garzaya Wattpad ko duba Ribar Uwa, Mutum Mugu, Wadata, Uwargidan Bahaushe, Bororoji,Kallabi does story sun tab’a ni_

 

_Kut nace sannan na cigaba da cewa don Allah ga Iphone dina daura Wattpad ke kome ma daura min nima ta fashe dani_

 

_Tabbas za ta fashe amma fashewar alkhairi….._

 

_Books din da zasu zo kamar haka_

1- Sahla A Paris

2-Bani Da Laifi

3-Abin Da Ya baka tsoro.

Dukkan su Uku 1k

_Guda daya_ 350

_Guda Biyu_700

_Guda Uku_ 1k

 

_Zaku iya payment ta  to 3091721807 A’isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria_

 

_and send evidence to does number_

*+234 813 731 1900*

Or

*08130269641 or 09063467258*

_Dukka zaku iya tura shaidar biya_

 

_Ga masu turo katin MTN zasu iya turawa Zahrahn Addah Ramlat da kuma Yan Nijar zasu turawa Nana A’ishah_

 

*+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah

*+22784506476*

 

_Welcome ta Top-notch Team_

[23/09, 9:06 pm] +234 806 897 4831: *RUWA…!!*

Adventure story🌊

 

PAGE 1

 

Karamar makarantar sakandare ta Bada gari. Dalibai ne sanye da uniform fararre, sai hira suke suna shewa, kasancewar rana yayi domin makarantar yan rana ne, da safe akwai yan primary.

 

Da sauri take hada kayan ta, tana kallon Yadiko da take ta mita.

“Fisabilillahi Rahilah ayi mutum kullum sai ya maka kin san damina ce ruwa ya kawo!”

 

“Yadiko!” Ta kira sunan a shagwab’e sannan ta dauki jakar ta tana faɗin.

“Yawuto sai na dawo”

 

“Allah ya tsare ban da wasa a bakin ruwa don Allah ki wuce babu ruwan ki kin ga sha biyu tayi”

“Toh yadikona”

Sannan ta dauki jakar ta tana faɗin.

“Matar Alhaji Buba toh na tafi don Allah kar ki manta ki ajiye min sauran farfesun kifin”

“Toh Uwale sai kin dawo”

“Toh Allah ya nufa”

 

Kasancewar lokacin damina yau ne aka samu sarari na rana da aka yi. Tafiya take tana kallon yadda ruwa yake kara tambatsa. Murmushi tayi shi yasa baki daya yau taki saka safarta. Tana isowa yar gadar da zata tsallaka da ita. Ta tsaya tana kallon ruwan yadda yake kaiwa da komowa.  Da sauri ta sauka ta isa bakin ruwan ta cire takalmin ta, ta cilla kafarta a cikin ruwan tana jin wani irin dad’i. Allah ya daura mata son ruwa.

 

“Nur me kike yi a bakin ruwa?”

“Baba Sarkin ruwa ina wasa da ruwa ne?”

“Allah ya shirya ki wuce maza”

“Toh naji”

Ta fada tare da juyawa ta shuri takalmin ta.

Ta haura gadar. Sunkuyawa sarkin ruwa yayi ya zuba abinda ya zo da shi. Cikin kwantar da murya ya ce.

“Ayi mana afwa.” Darewa ruwan yayi wani dattijo me suffar kifi rabin shi rabin shi mutum. Ya juya yana kallon Nur.

“Ayi hakuri sarki Marainiya ce ta rasa uwa da Uba sanadin RUWA al’amarin zai mata nauyi”

“Dan tana jikar dan uwanka?”

“A’a sai dan tana karama ne bata san kome ba”

“Ba zamu karbi hadayar ka ba, ka mai da shi ita muke bukata”

D’ago kai Sarkin ruwa yayi ya kalli Nur da ta tsallaka can gabar ruwan. Hawaye ne ya zubo mishi.

“Ai nasan kuna son ta, idan kayi hakuri ai kuna da wasu jikokin amma wannan tamu ce”

 

“Kayi hakuri Nur ta rayu ko a cikin yarana wani ku dauka amma ita rayuwar ta yana da muhimmanci ne sama da ta sauran”

“Sarkin ruwa na gama magana ita muke bukata”

“A’a ba a bukatar ta wakili a karbi hadayar su” wani matashin kifi ya ratso. Ya juya yana kallon gadar.

“Sarkin ruwa haddaya ta amso na fanshi nur, wakili idan baka manta ba ai an karbi abubuwa daga gare su daga farkon Damina zuwa yau mutane nawa RUWA taci? Ita kuma tatta rayuwar yana bukatar farin ciki. Sai dai akwai abu ɗaya. Idan ina raye babu wani mahalukin da ya isa rabar ta. Ka amince?”

 

Shiru Sarkin Ruwa yayi sai yaga bai da zabin da ya wuce amsar sharadin matashin kifin ya ce.

“Allah ya baka nasara na amince ” sannan suka juya abin su. Ruwan ta koma yadda take.

 

Mikawa Sarkin ruwa yayi yana jin kamar ya saka a dauke Nur daga garin Bada gari, toh ya zai yi? Haka ya nufi hanyar gida yana share kwalla domin shi kan shi yasan shekaru goma baya kusan kwatankwacin abinda ya faru kenan akan Mahaifin Nur, kuma gashi ya kuma fadowa kan shi. Kasa isa gida yayi ya zauna a kasar itaccen maina ya fashe da kuka wannan wacce irin masifa ce, kullum basu da ƙwanciyar hankali da zaran damina tayi, shi kenan RUWA tayi ta bukatar mutane matukar suka makara da bada sadaka, idan bako yazo a daidai wannan lokacin sai dai a tsinci gawar shi a saman ruwa. Idan kuma tsiyar Ruwa ya motsa masunta basu isa yin su ba, domin za a tsinci gawar su saman ruwa.

 

Yayi danasanin rashin bada hadayar da wuri, gashi nan abin ya dawo kan sanyin idaniyar su, yarinya karama me hakuri da kyau. Ga son mutane da fara’a ya Allah ka shigo lamarin Nur. Ya fada a ran shi.

 

Ita kuwa Nur tana tsalleke gadar ta nufi hanyar Makarantar, hankalin ta kwance har ta isa makarantar lokacin ana tsaren lati.

Kallon ta masu tsaron get din suka yi. Kafin suka daka mata tsawa.

“Sai yanzu zaki zo makaranta? Ajin ki nawa?”

Kwal-kwal tayi da idanun ta sannan ta ce musu.

“Ba zan kuma makara ba”

“Ajin ki nawa?”

“Jss1”

 

“Wuce kar ki kuma lati”

“Nagode ” ta fada tana shigewa cikin makarantar.

Abin su ta shiga ta wuce wurin zaman ta, ta zauna sannan ta sauke ajiyar zuciya tana me ciro safarta ta saka.

 

Can malami ya shigo musu ya fara darasi, yana gamawa ya fita wani ya kuma shigowa. Karfe biyu suka fita break. Bayan an koma malami ya shigo musu. Yana fita malamin addini ta shigo musu ya gabatar da ajin.

 

Karfe hudu da arba’in da tara aka tashe su, da wuri ta nufi gida. Sai da ta wanke kafar ta a bakin ruwa sannan ta haura kan gadar. Tun da ta isa tsakiyar gadar. Take jin busar sarewa. Me dadi da wani irin iska kamar tana yawo a sama.

 

Wani irin abu take jin yana yawo a jikin ta, sai niman inda busar yake tashi babu, sauran daliban garin kowa ya wuce ya bar ta tana ta niman inda busar take, cigaba tayi ta tafiyar har ta sauka sannan ta kuma dawowa gaban ruwa ta durkusa ta wanke kafarta da fuskar ta. Busar yana tashi.

“Nur!”

“Baba Sarkin ruwa yanzu na dawo fa”

Ta fada tana tura baki.

“Tashi muje gida”

“Toh” haka ya rike hannun ta, suka shiga tafiya.

“Sarkin ruwa kar ka fara abin da ba zaka karasa ba”

Bai ce uffan ba.

“Sarkin ruwa ka kyale min ita”

Bai tanka ba.

“Sarkin ruwa” ya sha gaban shi.

Tsayawa yayi Nur ta kalli Sarkin ruwa ta ce mishi.

“Baba Sarkin ruwa ya kaci burki ka manta wani abu ne?”

“A’a yarinya na, ina tsoron kar wani abu ya faru dake makamancin irin abin da ya faru ki ce kin zabi rayuwar wasu kin bada taki”

Kasancewar bata da yawan shekaru ta d’ago kai zata yi magana ya cigaba sa tafiya da ita….

*Labarin ruwa labari ne da yake faruwa a duk inda aka samu garin da ruwa yayi yawa har aka samu wasu a cikin ruwan suna raye so labarin Aljanu da mutane ne….. Babu update kullum*

#Mai_Dambu ….. Jikar masunta🥰🌊

 

TOP -NOTCH ….the touch of excellence, just for you

 

Trailer! Trailer! Trailer!

 

“Bad luck! Bad luck! Bad luck everywhere Sahla”

 

Shhhh

 

“Ba ki da sa’a ko kaɗan a rayuwarki Sahla”

 

“Dan Allah kar ku bari Sahla ta shiga min kitchen dan na san tana shiga yau abincin gidan nan ba zai ciwu ba”

 

Hmm

 

“Ni fa ko addu’a na yi sai dai a samu akasin abinda na tambaya. Kar ku ce ina da raunin imani fa, kawai dai abinda na lura shine wasu rayuwarsu yadda take tafiya tamkar su suka ɗau alƙalami suka rubuta ƙaddarar rayuwarsu, komai sai ka ga ya tafi daidai da jin daɗinsu. Amma irinsu Sahla kam tamkar da ƙafar hagu suka faɗo duniya”

 

***

 

Wato sha’anin Bature sai a hankali. In dai batun soyayya da kare ne sai dai a shafa musu Fatiha kawai.  To ma ni miye ruwana tunda kuɗi ake biyana.

Amma Allah ya isan talauci. Karen Mrs Julie fa abinda yake ci a kuɗin Nigeria a kullum ya kai naira dubu ɗari biyu da hamsin. Wani shegen kwayyane, au kwainane. Mtsw kwaimane, kai dole sai na yi Hausa ne ma. Nan fa Paris ne, Babban birnin ƙasar Faransa.  To ni Sahla idan ban yi Hausa ba Uban me na iya a Farasancin?  Na san dai Mrs Julie na yawan cewa karanta Le mo ( L’amour)

 

Shi kuma Mr Dodo idan yana Faransanci ba ji nake ba, kallon bakinsa nake da hanci dan gani nake shaƙewa zai yi, ina ankare inji ya shaƙe na kawo masa ruwa.

 

Aff! Kar ku gaya masa ina kiransa da Mr Dodo fa. Dan Wallahi idan ya ji labari Nigeria zai mai da ni. Duka-duka yaushe na zo Paris ɗinma balle ace za a maidani wata ƙasa wai Nigeria, a’a Lanjeria. Walle ni da Lanjeria sai dai a mafarki. Taɓ! Irin azabar da na sha a Lanjeria.

Ai, ashe ina maganar karen Mrs Julie ne. Barin faɗa muku gaskiya ba kare ɗaya nake kula da shi ba. A sati sau uku zan kwashi karnuka guda biyar na tafi yawo da su na tsawon awa biyu, sai na dawo da su gida. Amma shegen karen Mrs Julie ne ya fi bani haushi, matar nan har wanka take masa a cikin bath tube ɗin ta. Ni wa ya sani ma ko auren karen ta yi tunda mun sha jin labarin Bature na auren kare, ko kuma ya barwa kare gado, shiyasa na ce muku al’amarin Bature mai jan kunne da kare sai dai a shafa Fatiha.

 

To dai sunan Karen Mrs Julie Sky, eh nace Sky kamar sararin samaniya kenan da Hausa. Amma kun san me? Wallahi Titiɓiri na ke kiransa idan na fita da shi park.

Sauran karnukan ma duk na chanja musu suna daga Bingo, Kubuwa, Sakadale ( karen yana da tudun mazauna. Opps, Allah ya shiryeki Sahla)

Ta ƙarshen wata ‘yar ficila da ita wai sunanta Princess amma Tsillirilli na saka mata.

 

Na ga sai wani hararana kuke, wai na baro Lanjeria na zo Paris ina aikin  Dog walking. To kun sanni ne? Kun san ma daga ina na fito ne? A ‘a haka kawai kuna wani ƙananan maganganu a kaina saboda tsabar gulma da tsugudidi. To in gulmar kuke so ku biyo bayan Topnotch writers mana, sai na ji daɗin baku labarina da dalili.

 

Aisha Faridan Sir Najib tana gaishe ku (Sakatariya ta)

 

Asiya Shahidar Gwamna SS Kachallah ma tace kar ku manta ku bibiyi marubutan Top-Notch (Matar Gwamna)

 

 

Zaytoonan Justice Yunus-Zannoon ma ta ce ku bi Sahla a Paris, kar ayi ban da ku (Chronicles of Zaitoonah)

 

Coming soon…

 

 

Littattafan Top-Notch za su faso a October 2022 Insha Allah

[23/09, 9:06 pm] +234 806 897 4831: *RUWA…!!*

Adventure story🌊

 

PAGE 3

 

Baki daya masu kula da harkokin shi suka sunkuyar da kai, suna tsoron abinda zai fada ko zai musu.

Taku yayi daya biyu sannan ya kuma juyawa yayi kafin ya kalli kan shi.

“Ku tabbatar kun girgiza bil adama a duniyar su ku fantsama ruwan ya shiga cikin gari da ko ina ku tabbatar kun kashe duk wanda ya shiga su. Ku janye arzikn mu daga gare su.. ba zan lamunci kuskure ba ku tafi”

 

Dunkule hannu suka yi a gefen kirjin su, sannan suka amsa da cewa..

“An gama shugaba”

Fita suka yi a fusace domin sauke fushin me gidan su ga bil adam.

Kallon mudubin yayi yana hango hoton Nur da take tafiya dazun. Mashi aka wurga jikin madubin ya juya da sauri tsaye take akan iska kyakyawar gaske ce. Gashin kanta ya lullube kirjin ta.

“Ashman me nake ji?”

Banza yayi da ita, ya wuce dakin shi kafin ya shiga ya same ta a saman gadon shi a tsaye.

“Ina magana kayi banza dani”

Nan ma shiru yayi mata yana me kwanciyar shi.

“Ashman”

“Bunanah fita kafin na yanke bindinki”

Da sauri ta fita, domin kaf cikin duniyar su babu wata budurwan Mermaid da ta kaita kyawun tail, dan yanayin ta kawai zaka gane irin kyawawan kifayan nan ne. Yana kwance yaji shashekar kukan ta, tasan weak point din shi baya son jin kukan mace a rayuwar shi, yadda take durzan kukan yasa shi mikewa ya fita , kura mata ido yayi kafin ya bude mata hannu, da wani irin gudu ta iso gare shi.

“Ashman ina son ka”

“Son da nake mata ban san dalilin da ya kama ni ba”

“Ashman na yarda yanzu kayi tarayya dani”

“Tunda na saka idanu akan ta ba zan iya tarayya da wata mace ba sai ita, ina son ta a kamar yadda uwa take son danta, Bunanah zan zauna dake amma ba zan fara auren ki ba sai na fara da ita domin tazo a uwargidana”

 

A hankali ta janye jikinta tana mishi wani irin kallo na zargi da son rai.

“Amma ka san kaf duniya babu aure tsakanin aljani da dan Adam ko?”

“A kaina za a fara domin da narasa Nur Gara na rasa rayuwa ta.”

 

Wani irin kishi ne ya kamata ta juya zata fita a fusace tace mishi.

“Ba zaka tab’a samun ta ba, har abada domin babu wani yadda zaa hada ruwa biyu a wuri guda ita bil adam ce kai kuma Aljani.. ina sonka kana son ta muga waye zai same abin da yake so”

 

Cikin fushi ya watsa hannun shi sai ga wasu sarka sun fito a take ya daure ta, yana huci ya ce.

“Zan wulakanta duk wanda ya min Katsalandan akan soyayyar Nur ”

Duk da azaban da take ji bai saka ta yi kasa a gwiwa ba, ta ce mishi.

“Koda zaka shafe ni a doran kasa ba zan fasa adawa da yarinyar ba, shege ka fasa.” Cillata yayi ya daka mata tsawa, yana nuna mata hanya. Sai da ta mishi maganar banza ta fice a dakin.

 

A can saman ruwa suna fitowa suka samu ana ruwan sama, ruwa ya cika ya tumbatsa, dan haka suka koma da baya suka kara ta’azzara ruwan yadda ya fantsama cikin gari babu shiri, mutanen da suke fitto kuwa take suka nutsa dasu, suka kashe su. Wannan al’amarin ya faru ne daga ruwa zuwa cikin gari, kafin kace kwabo ruwa ya lalata gonannakin mutane, sannan ya tafi da wasu abubuwan jama’a kama daga dabbobi zuwa dukiyoyin al’umma, wasu ma dakyar suka sha domin har cikin gidajen mutane ya shiga. Lokacin da aka ta fitowa ana ceton rayuwar al’umma, a lokacin mutanen Ashman suka yi ta shiga jikin yara da mata, ba a lura ba domin hankalin mutane yayi gaba. Sai Washi gari aka farga da wani abu da ya faru, dan haka aka tafi gidan Sarkin Ruwa da maganar tashin da hankalin da ya auku, anan ya fada musu gaskiyar halin da ake ciki, ana hada yar gidan Liman ta fadi a gidan su tana aman ruwa bata ci kome ba.

 

Dakyar aka samu me zuwa ya fada a gidan Sarkin Ruwa, nan shima Yaron ya fadi.

“Gaskiya a duba wannan lamarin ba zaa tsaya sanya ba, dan haka kowa ya koma gidan shi ya duba ko lafiya”

 

Kusan kowa yayi na’am da batun Sarkin ruwa, koda ya shiga cikin gidan ya samu Nur lafiyar ta lau. Dan haka yayi maganar kar a sake Nur ta bar gidan duk abinda zai je ya dawo. Kafin ya koma dakin shi, yayo yar dabarbarun irin nasu na masunta, sannan ya fita aikuwa kamar yasan haka zai faru can wurin tsakiyar rana sai ga yaran da aljanu suka buge sun zo daukar Nur. Amma sun kasa shiga cikin gidan, duk bala’in son shiga gidan sun gaza dan haka suka zagaye gidan suna dakon ta.

 

A bakin ruwa kuwa an kai ruwa rana da mutanen ruwa domin sun marawa Ashman baya lallai su a bashi Nur, abin da ya fusata Sarkin ruwa kenan ya ce musu.

“Idan kun isa kuzo ku dauki Nur baku da kafar zuwa ne, matukar kuka ga Ashman ya mallaki Nur toh wallahi bana numfashi ne amma matukar ina raye wallahi Nur ta wuce sanin shi da tunanin shi.”

 

“Lallai Sarkin ruwa zaka ga aiki da cikawa, idan baku bada Nur ba mun rantse baku da kwanciyar hankali sai kun bada ita.”

 

Haka suka ya bar bakin ruwa cikin tashin hankali da damuwa, yana shigowa gari ya samu tashin hankali a kofar gidan shi, ga iyayen Yaran da suka tisa shi a gaba dole ya wuce wata kauye me suna kan tudu wurin malamin shi. Bai isa gidan ba sai da bayan magariba, anan ya samu malamin kan tudu, yana masalaci yayi alola yayi sallah. Bayan yayi addu’a sannan ya shafa kafin ya nufi wurin Malam ya zauna yana suke ajiyar zuciya dan damuwa ta mishi yawa.

“Ita Nur din ku rabata da garin kafin nan dole ku zubda jini amma tabbas aljanin shu’umin gaske ne, sai an kai ruwa rana kafin a zauna lafiya yanzu… Ita kuma ka mai da ita can nesa da garin Hayi ba ma bada gari ba hayin baki daya zata bari har abada kuka sake ta tsalleke ta shigo hayi akwai matsala a haka bawai ba zai iya niman ta bane a’a sai dai kun yi dagaske, muje na baka hayaki a saka a gidan ka duk wani me matsala Allah zai yaye mishi amma.”

 

Baya bata kaɗan….

*TOP-NOTCH WRITERS*

 

 

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*

 

_Kasancewar bikin kanwata ake ta biyar me suna Zahrah sai kaiwa da komawa nake Hankalina yana kan Babbar kawata Farisah tsaki nayi na wuce can na kuma dawowa na zuba mata ido cikin takaici mahaukaciya ta zare_

 

_Malama kin zo biki ne ko kin zo karanta chat kin yi shiru kin b’ata shiru_

 

_Wani banzan dariya ta saka min tana d’age min gira_

 

_Hmmm Bestie wai ke ko irin karance-karancen social media baki yi irin su Wattpad,Okada, Arewabooks baki yi?_

_Sake baki nayi ina kallon ta. When rabona da Hausa Novel Allah na tuba tun Iyatuh Abba tana karanta a gidan Radion B.R.C tabe baki nayi na ce mata_

_Ke rabani da kayan wahala rabona da Hausa novel tun zamanin Iyatuh Abba_

 

_Innalillahi!, Tace tana kallona kafin ta ce. Jasmin yanzun don Allah duk cigaban da aka samu baki san da shi ba? Lallai kin wuce yadda nake tunani kin gani wuri na karanta book din da nake fama da shi_

 

_Cikin mamaki na wuce na dawo na zauna kusa da ita nace mata don Allah daura ni a hanya ina ganin kowa na karance-karancen amma ban dani_

 

_hmmm lallai zata fashe… Toh saurara da kyau nan da kike gani na karanta books nake na marubuta daban daban amma idan ana dara ana fidda uwa… Kin ga last na ga The Governor’s Wife, one to three, after ma gama na karanta Zaytoonah…. Abun dad’i sai na cikaro da Affiyah da Unaisah_

 

_Allah Aunty Rukayyah kina karanta online hausa novel ne? Lallai toh ai yanzu ina karanta Zayn Malik Jiya na gama karanta Zanen ƙaddarata,_

_Kanwata Amaryan da muke bikin ta ta saka mana baki a she ba banza yarinyar nan ta nace daga gama sakandare tace a direta gidan miji_

 

_Amarya Zahra toh kuwa nima Zayn Malik nake karantawa musamman rigimar Hajiya da Uncle Bashir, da Zayn da Abul amma kin san zata fashe on October?_

 

_Don Allah fa_

_Hmmmm gamayyar marubutan nan sun hade wuri guda za ta fashe sun fitar da sunan Team din su_

 

_Aunty Don Allah ya sunan Team din?_

_TOP-NOTCH…. Za ta fashe a books uku Sahla A Paris, Bani Da Laifi Abin da Ya baka Tsoro_

 

_Wow da gaske?_

_Zan Miki karya ne?_

_Ina da number Mai_Dambu bari na duba nasan zata daura a status…._

 

_juyawa tayi ta kalle ni ina bin su sa kallo ke kuma ko garzaya Wattpad ko duba Ribar Uwa, Mutum Mugu, Wadata, Uwargidan Bahaushe, Bororoji,Kallabi does story sun tab’a ni_

 

_Kut nace sannan na cigaba da cewa don Allah ga Iphone dina daura Wattpad ke kome ma daura min nima ta fashe dani_

 

_Tabbas za ta fashe amma fashewar alkhairi….._

 

_Books din da zasu zo kamar haka_

1- Sahla A Paris

2-Bani Da Laifi

3-Abin Da Ya baka tsoro.

Dukkan su Uku 1k

_Guda daya_ 350₦

_Guda Biyu_700₦

_Guda Uku_ 1k

 

_Zaku iya payment ta  to 3091721807 A’isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria_

 

_and send evidence to does number_

*+234 813 731 1900*

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Or

*08130269641 or 09063467258*

_Dukka zaku iya tura shaidar biya_

 

_Ga masu turo katin MTN zasu iya turawa Zahrahn Addah Ramlat da kuma Yan Nijar zasu turawa Nana A’ishah_

 

*+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah

*+22784506476*

 

_Welcome ta Top-notch Team_

#Mai_Dambu

Leave a Comment

error: Content is protected !!