Hausa Novels

Ruwan Jakara Hausa Novel Complete

Ruwan Jakara Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: RUWAN JAKARA

_(idan ba’a sha a birni ba, asha aƙauye)_

 

*_GAMJI WRITERS ASSOCIATION_*

_Home of exceptional writers_

 

*_LITTAFN_*

_MARYAM HAMISU YUSUF (MAMAN BOY)_

_wattpad@mamanboy279_

 

_fitar farko *2019*_

_fita ta biyu *2022*_

 

*_1_*

_(shimfiɗa)_

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*_KACE “KUZO, IN KARANTAMUKU ABINDA UBAN GIJINKU YA HARAMTA AGAREKU”. WAJIBINE AKANKU KADA KUHADA ALLAH DA KOMAI, IYAYE KU KYAUTATAMUSU, KADA KU KASHE ‘YAYAYENKU DAN TSORON TALAUCI… MUNE MUKE AZURTAKU DASU (YAYANKU) KADA KU KUSANCI ALFASHA.. DA ABINDA YA BAYYANA DAGA GARETA DA WANDA YA BOYU… KADA KU KASHE RAI WANDA ALLAH YA HARAMTA FACE DA HAQQI.. WANNAN NE (ALLAH) YAYIMUKU WASIYYA IDAN KUN KASANCE MASU HANKALI (Q 6:V:151)_*

.______________________________

 

Ajin yayi shiru!! Yayinda duk macen datake Ajin ta shagalta da jin amon za zzakar muryata… Alokacin da nake rairo masu karatun alkur ani mai girma ina Koyar dasu.

Ban gusheba Saida nayimusu tafsirin ayar da na karanta musu….(suratun_nissa’i aya ta biyu) Yayinda suke jefomin tambayoyi nikuma ina basu amsa cikin kwarewa da kafa musu hujjoji da sahihan hadisan manzon Allah (SAW)….

Duk macen dake ajin (matan aure) danake koyarwa ayanxu babu wacce bata haifeniba wata ma tayi jika dani duk da karancin shekarun danake dasu sosai hakan bai hana dalibn nawa mutuntaniba kamr yadda nima nake tsananin mutuntasu…amatsayiinsu na wadanda suka isa su haifeni

Badan nagaji da amsa tambayoyinsuba na dakatar da karbar tambayoyin sakamakon lokacin Rufe makarantar islamiyyar da yayi (6:00pm) ..ttuni dalibai suka soma fitowa a harabar makarantar Hakan yasa mukayi addua muma muka fito……

 

Staff room na koma nasaka hannu alittafi na cike attedence dinmu na malamai… Sallama mukayi da malamai na fito

 

Sakin nikabina nayi wanda ke boye kyau da sigar da Allah yayiwa fuskata… Dara daran fararen idanuna kawai zaka iya hangowa ta cikin niƙabin ka shaida nidin kyakkyawa ce

Cikin nutsuwa da takon danakeyi tamkar ina tausayin kasa na karaso bakin gate.din makarantar …

Saidai kafin wani lokaci tuni garin yayi bakikirin da hadarin da haduwarsa kenan, nan da nan iska ta fara kadawa yayinda malamai da dalibai kowane ke kokarin sanin inda dare yayi masa dan gudun kada ruwa ya jikasu…. Kafin wani lokaci tuni ruwan ya fara sauka tamkar da bakin kwarya kuma da karfin gaske …..

 

Duk ƙokarina na samun mafaka Saida najike sosai acikin Ruwan har Allah yasa nakarasa gida…

Da sallama haɗi da sassarfa nashigo gidannamu mai tsakaicin girma da zubi irin na gajiyayyun talakawa, tarar da kofar dakin ummah na nayi a rufe.. Atake raina yasoma 6aci… Arayuwata na tsani bakin yawon da mahaifiyata takeyi cikin ruwannan kuma ko ina ta nufa a irin wannan yanayin garin na ruwa??.. Bansamu wannan amsar daga gareni ba nayi saurin nufar dn karamin dakina ina kokarin shigewa dan na sauya jiƙaƙƙun kayan da ke jikina, alokacin gwaggo kwazo ta fito tarbar ruwar saman da har lokacin basu tsagaitaba, tanamin sannu… (Dayake gidannamu na hayane.) . Na amsa Mata ina kokarin tura yamutsattsen kyauran dakinnawa tare da yimata sannu da gida nayi saurin shigewa dakin …..

 

Bantsaya wata² ba na fara cire zurmikekiyar hijab Dina da nikab na sauya kaya zuwa wani tsohon leshi na dinkin riga da skirt.. sai rawar sanyi nakeyi..

Alwala na dauro na gabtar da sallar magrib sakamakon Kirayen kirayen sallah da aka farayi saidai har aka yi sallar issha umma bata shigo ba…

 

Lumshe idanuna nayi tare da makurewa akan yar tsohuwar katifa na ina tunanin wannan bakin gantalin na umma Dana taso na ganta a ciki….

Shigowar gwaggo kwazo ta saka na bude idanuna dasuka min nauyi akanta… Langa ta ajiyemin agefe na tana fadar “uwar dakina har kinfara bacci da wuri haka babu fira yau kenan (Dayake sunan jikarta gareni)

Yunkurawa nayi ina yimata sannu..tareda kakaro murmushhi cikin nitsattsiyar muyata na bata amsa da cewa “banyi bacci ba goggo yanzu ma zan mayar da sallar issha.. ”

Na idar da maganar ina daidaita zamana akan yar karamar katifa na ,

Murmishi ƙwazo tayi ta turomin langar tana fadan”ga abincinki nan nasanki da wasa da cikinki “… Tana matsamin naci dan ita kanta tasan damuwata

Bance komai ba sai Godiya nayiwa gwaggo kwazo.. Domin duk lokacin da mahaifiyata ta tafi bulagoronta.. Itace me kula dani har ta dawo, nazama ganinan dai tamkar marar galihu da gata, mahaifiyata irin matananne da basu da ko yayan cikinsu ba kanta kawai ta sani da rayuwar data sanya agaba….

 

“Gwoggo yau Tun yaushe ummah tabar gidannan”…. Na dakatar da kwazo da tambayoyina dake kokarin fita. Juyowa tayi tana kallo na kafin tace “ai kina tafiya makaranta bada jimawaba itama ta fita kuma gashi har duhu yafara bata dawoba, inaga kila yau sai zuwa anjima Zata shigo …. ”

 

Lumshe idanuna nayi ina jinjina kai cikin ƙunar zuciya da takaici . alokacin gwaggo ta fice sakamakon sallama da mijinta yayi agidan …. “Ya Allah ka yayewa umma wannan jarababben yawon na bagaira ba sabab…. ”

Iya abinda Na fada azuciyara kenan ina janyo langar da ƙwazo ta ajiyemin

Bude langar da gwaggo takawomin nayi… Tuwon dawane miyar danyar kubewa duk da kayan miya basu wadaci miyar ba hkan bai hanata fitar da kamshi mai dadi ba

Kadan na ci na mayar na ajiye sakamakon yadda nake jin zuciyata namin zafi…..

Sai misalin karfe Tara saura kwata ummah ta shigo gidan , inajin lokacin data bude dakinta ta shiga hakan ya tilastamin tashi na nufi dakinnata domin nagaza bacci, haka nake kasancewa acikin yanayin damuwa da rashin sukuni aduk lokacin da ummana ta fice….

Tana kokarin ajiye mayafinta na shigo dakin tare da sallama….

Tunda ta kalleni ta watsar bata kuma bi takaina ba ta cigaba da ninke tsohon mayafinta dan Kuwa tasan abinda ya kawoni…..

“Sannu da dawowa nayimata…… Ba yabo ba fallasa ta amsamin…

Ta dora dacewa “kinci abinci Kuwa naga kinyi wani zuru² tamkar an shakare mage”…

Ta idar da maganr tana kallon yanayina. Kawar da kaina nayi kafin nabata amsa “eh gwaggo kwazo ta bani kamar yadda ta saba “… Na dora dacewa “ummah dan Allah ina kikajene haka sai yanxu ga shi an yi ruwa ga dare yayi “…..

Na idar da tambayar ina marairaice fuska cikin yanayin damuwa

Zama bakin gado ummah tayi tana rabka salati tare da tafa hannayenta jin yanayin tambayar da nayimata “BATULA zargina kikeyi kenan… Kinaso ki fadawa duniya wato gantali nake fita? Wato tuhumata da bin maza kikeyi”….

 

Cikin tashin hankali nayi Saurin girgiza kaina idanuna kuwa tuni sun kada sunyi jajir sunkuma cika da kwallah fara kuka jin yadda ummah take Neman lailaiya tambayata harma take tuhumata.. Cikin rawar murya na soma magana “Wlh ummah ba.. haka nake nufi ba.. Naga kin dadene shiyasa….

Gyara tsayuwarta ummah tayi cikin masifar da ke fizgarta tacigaba da cewa “wai ma batula mekike nufi idan ban fita na samo maku abinda zakuci ba amatsayinku na marayun da aka mutu aka barmin ba abarmin ko sisi na kula dakuba, so kike na zauna bakin cikin duniya ya kasheni da bakin cikin dangin ubanku..duk irin tarin dukiyar da allah yayiwa yayan mahaifinku alhaji mansoor Amma dai² da kwayar shinkafa baitaba yunkurib taimakamana da ita ba kodan saboda ku ya’yan kanensa da ya mutu ya bari.. Sai azumin bara ne Allah ya taimakamana ya kwato mana tiyan masara biyar sai taliya kwara uku .. Shin batula da wannan kikeso na zauna.. Koko zama zanyi ku taru ku cinyeni”.?

Share hawayen da suka jikamin fuska nayi nasoma magana batare da na dubetaba nasoma magana “ammah umma, ya usman da ya faruq su kadai sun isa su taimaka mana ba sai kindinga yawoba haka umma kefa macece kuma kinada yaya maza wadanda zasu tallafi rayuwarmu”…..

 

“Dallah rufemin baki batula su usman da faruq Dinne zasu rikemu… Sudin da jira sukeyi na ajiye su dauke… Agaban idanunki sun sha satarwa kwazo kudadenta… Kwanaki usman sabbin kayan mijina dazai saka a bikin yarsa ya dauke yaje yasiyar yadawomin gida abuge… Shikuwa faruq sai na kwana inwuni bansakasa a idanuna ba ya na can wurin tambada… Ke kadaice ta kirki acikinsu mai dama²..tadan sassauta murya daga fadan da take yimin kamar zata cinyeni tacigaba da cewa “dake kadai yanzu nake tunkaho kuma kedin buri na ce, wulakantacciyar rayuwa irin wannan vazan taba bari ki dawwama acikinta ba har ma dani, Yadda allah yayiki da kyau hka ga iliminnan naki so nake kisamu wani basarake ko dan gwamna.. Ko dan wani mai fada aji akasar nan ya aureki… Dan wlh kin fi karfin talaka bazan taba bari wannan kyan naki ya tafi abanza ba batare da mun moresaba”…,

Umma ta idar da maganr tana murmishi tana duban yanayina….

Takaici ya kuma cikani akan Kala man umma duk da idan da sabo nasaba da hakan mama zuciyata ma Gaza kure radadin yadda ummah ke nuna zallar maitar kwadayinta da burinta akaina…Duk Wani buri mahaifiyata ta azasa akaina… Nazamemata jari na ganin takaiga cikar burinta………

Tashi nayi kawai na fice ina hawaye mai tattare da kunar zuciya…

***********

*FATIMA* ko *FAƊIMA* *SAYYADA,* *BATOOLA* ko *ZARAH* babu sunan da Bana amsawa musamman abakin mahaifina…..

Mahaifina bafullatanin asalin jihar katsina ne Hausa.ma bata zauna bakin sa yadda yakamata ba… Su shidda ne awurin iyayensu mansoor shine babba sai sa’eed wato mahaifina.. Sai sa’adatu mai bimasa da umma jamila.. Sai habu da baba saratu…….gabadayansu uwa da uba daya ne suka haifa su.

Alhaji mansoor yanada Mata daya salamatu yayansu uku *ANWAR* siyama… da nazifa…

Mutum ne mai arziki sosai da ya shahra ta fanni shigo da shinkafa a kasar… Da kuma harkar shigo da suturu daga kasashe daban daban….

Mutum ne mai tsananin son ya’ynsa da sngartasu… Hkan yasa alokacin da ANWAR ya kammala secondary school.. Ya fitar dashi jamiar america acan yayi karatunsa fannin kasuwanci.. Ya hada degree da masters,dayadawo Nigeria babban office mahaifinsa ya baS a fannin kasuwancinsa Amatsayin general manager na company n na kera robobi wqnda baijima da budesaba

Shekarunsa bazasu Gaza ashirin da tara ba… Fari ne sosai yanada kakkarfan jiki da cikakkiyar siga ta da namiji da kuma kyau.. Saidai idanunsa sunfi Kama Dana jaraba bun mazannan wato sexy eyes.. Dan basu cika hhasskeba.. Suna da girma kuma alumshe suke Sangartaccene awurin abbansa da haji ya salamatu… kuma Tataccen marar kunya ne… Duk wata dabia ta Muslimin kwarai baida ita.. Shahrarrene wurin hulɗa da mata . Kamar yadda zaman clubs ya zame masa jiki.. Duk abinnan da yakeyi Alhaji mansoor ya ki hantararsa wai kuruciya ce ke damunsa, nawani lokaci ne zaidaina ko wa kuma da irin yadda ya yi kuruciyarsa…siyama da nazifa Kuwa kusan kansu daya suna a secondary tsadaddiyar private school sukeyi zamuzo kai daya da nazifa… Duk da shekara daya da rabi ne tsakaninsu..

Yarane yan kwalisa da suka raina kowa da suke tutiya da kyau da kudi, san sune masu fada aji awannan zamanin.. Basa ganin kowa da mutunci… Wannan yasamo asaline daga mahaifinsu…abun ajininsu yake baaa kaunar talaka barekuma ya raɓu a inuwar du Dan ko kadan baya kaunar dan uwansa ya rabe sa bare ya ya taimaka masa… Daga matarsa sai yayansa…. Kuma Alhaji mansoor shikadaine mutumin da Allah yayiwa arziki acikin family dinmu… kannen mahaifina Mata Kuwa duka mazajen da suke aure ba masu karfi bane… Har kara baba habu ba laifi yana, da rufin ssiri duk da shima din da albashi yake dogara…yarsa daya da Mata biyu.

Bakidaya sunja jikinsu daga alhaji mansoor sun rike talaucinsu..saidai hakkin zumunci da suke kokarin cikawa .

 

Wannan yasa mahaifinmu yaja jiki daga lamurransa saidai Sauke hakkin zumunci da ba’a rasa ba… Mahaifina malam sa’eed mutum ne mai wadatar zuci… Da sanaar sayar da tukane da murahu Da ita yke kokarin rikemu.

Mahaifina bai taba zuwa wurin alhaji mansoor da Neman ya taimaka masa ba haka shima bai taba, yunkurin .ya taimaka masa ba… Saidai mahaifiyata(hajara) tunda ta kyalla ido taga gidan Alhaji mansoor da maiko tafara kokarin kutsa kanta gidan… Duk da fada da abbahnmu yake Mata akan ta rike darajarta ta tsaya a inda allah ya ajiyeta amma taki harma wani lokacin takan rufesa da masifa wai girman kai ne dashi da baya iya zuwa ya nemi Abu agun yayansw alhaji mansoor inda aka fika an riga an fika….. Baitaba bi takanta ba idan tana masifa dan mahaifiyata macece mai kwadayi da hangen na wani ga masifar fada, maaifaffiyace sosai… Hka Allah ya jarrabi mahaifina da ummah dan shi mutum ne mai sanyin hali ga hakuri… Bakomai yake daga kai yayi magana ba……

Kwata² mu uku ne awurin iyayenmu… Ya faruq shine babba shekarunsa ashirn da hudu sai mai binsa usman sai da mahaifiyata ta kwashe shekaru bakwai kafin ta haife ni kuma, ni kadai ce mace daga kaina ta tsayar da haihuwar wai bazata iya cigaba da haihuwa da mahaifina da talaucinsa da yayimasa katutu ba..

Mun taso cikin kula daga mahaifinmu ya tsaya tsayin daka kanmu wurin ganin ya kyuatata mana…dukkan family dinmu kyawawane sosan gaske dan takoina munyi gadon kyau kamanninmu sun kusa zuwa daya.. Dan dakaga dan familynmu kanaganewa wannan yasamo nasaba daga kammaninsa da iyayenmu sukeyi da junansu..

 

Tun daga ilimin mu har cinmu da shanmu da suturmu Mahaifinmu ya tsaya akanmu…

 

Saidai fa karatun su ya faruq yatsaya daga secondary school… Dan mahaifinmu baida kudin dazai tallafa masu Suci gaba da karatu….. Sai ya zamana ni kadaice ke karatu ina jss one Ina kuma da shekaru coma aha biyu…. Duk yadda mahaifina yaso su ya faruq suyi karatun addini suka watsar.. Sune. biyewa batagarin unguwa sune shaye²… Duk da haka mahaifina bai Kara ya akansu ba ya na bakin kokarinsa akansu tare da musu adduar shiriya kowane lokaci, Saidai yakan samu nutsuwa idanyana tare dani.. Babu inda nabaro halayen mahaifina.. Inada son addini da son Neman ilimin addini sosai… Duka Dana boko ina mayar da hankali sosai… Allah ya bani kwazo da saurin fahimtar duk karatun da akayimin Tun daga Boko har islamiyya…

 

Inada shekara 13 allah ya albarkaveni dasauke alkur’ani mai girma… Nasha kyautttuka da yawa daga wurin mahaifina da sauran mutanen unguwarmu saboda ni macece mai farin jinin mutane.. Sainazama abun kwatance awurin iyaye idan zasuyiwa yayansu fada, kowace uwa burinta yarta tayi koyi da halayena.. Duk da mutane da dama na cewa Banyi dacen mahaifiyata ba dan kowa, yasan mahaifiyata macece mai gantali yau tna can gobe tana nan, sam babu halin kirki atare da ita…..

Tsararrakuna Kuwa, so sukeyi suyi abota dani… Atakaice dai inada ilimi gwargwado

duk da karancin shekaruna inada kaifn hankali ga nutsuwa… Zama daya zakayi dani na shiga ranka….

Ina da shekaru goma sha biyar Allah yayiwa mahaifina rasuwa, asthma itace tayi ajalinsa….

Allahu akbar naji imutuwar mahaifna domin Kuwa yadda na shaku da mahaifina banshaku da mahaifiyata haka ba..

Mahaifina baibar mana komai ba sai dan karamin gidan da muke ciki… Siyar da gidan umma tayi tarike kudin wai bazata iya zama babu kudi ahannunta ba.

bayan ta kammala takaba.. Zawarawa sukayo kanta… Bayan rasuwar mahaifina da, watanni bakwai ummah ta auri malam kabiru… Matansa biyu yayansa takwas maza biyu Mata shidda duk ya aurar dasu…. Gidan haya ya Kama Mata….dakuna uku manya guda biyu sai dan karamin wanda baiwuce akirashi da store ba. Wanda acikinsa e nake kwana .. Bisa sharadin zama da marayun da aka barmata ummah ta auresa…. Shima din sai ahankali dan bawani halin kirkin azo agani garesaba kuma yayansa maza duka babu na kirki….

A wannan lokacin kuma na kara zurfi acikin ilimin addini islama nasan litattafaida dama da hadisan manzon Allah saw… Su kansu malamai makarantar jinjina kokarinda sukeyi…. Hakan yasa suka, waremin azuzuwn dazan dinga koyarwa alokacin Dana gama (sanawiyya) da karancin shekaruna ina aji biyar a, secondary school… Ina koyar da matan aure da ajujuwan yn Mata……

 

 

 

_Wannan kenan_

 

Pls share and comment

[14/10, 10:15 pm] +234 802 734 6971: *_GAMJI WRITERS ASSOCIATION_*

_Home of exceptional writers_

 

 

*_RUWAN JAKARA…_*

_(idan ba’a sha a birni ba, asha aƙauye)_

 

*_LITTAFN_*

_MARYAM HAMISU YUSUF (MAMAN BOY)_

_wattpad@mamanboy279_

 

_fitar farko *2019*_

_fita ta biyu *2022*_

 

*_2_*

Yau ta kasance ranar asabar, da misalin karfe Tara na safe nagama shirina na tafiya makaranta kamar yadda na saba…

Katon hijab Dina na saka, nikab yana hannuna na fito tsakr gidan….

Inajin nutsuwa da farin ciki sosai araina koba komai nasan yau ummah bazata fita bulagurontaba, saboda mijinta agidan ya kwana… Bawai kuma dan tana tsoronsa bane take kin fita idan yana dakinta, tanayin hakanne dan basa kulawa tayadda hankalinsa ya karkato akanta sosai fiyeda sauran matansa, dan shi wani irin mutum ne dukwacce tafi tarairayarsa itace zaifi sakarwa bakin aljihu, sam baya da tsari ko adalci arayuwarsa ta iyalansa, zaman ummah da kishiyoyinta da ba agida ɗaya sukeba kuwa shi ake kira da iya ruwa fidda kai, duk wannan abun badan samun lada take yin saba saidan abinda zata samu daga garesa dan shidin matsolo ne na bugawa a jarida, sai ka taki sa’a zaka iyacin kwandalarsa, duk kulawar kuwa da ummah take basa daya saka kafa yabar gidan itama Zata fice.

Tun kafin na isa kofar dakin ummah nakeji yadda suke ta sa insa da malam kabiru akn dole sai tafita tunda ba abinda zai wadatar da ita ya barmata. Hakan ya tabbatarmin da cewa yau taɓaci tsakaninsu kenan. .

Shikuwa ya kafe akn babu inda zata tafi matukar shine yake aurenta kuma ko sisi bazai kara mataba….

Sallamr danayi ce abakin kofar dakin yasakasu yin shiru cike da haki ummah ta amsa min sallamr sannan na shigo….

 

Cirko² na Tarar dasu kamar masu shirin taka dambe.. Umma Kuwa sai huci takeyi… Durkusawa nayi muryata na rawa nace “zan tafi makaranta ”

harara ta wurgomin cikin son huce haushinta akaina tace “To zan hanaki ne ki tashi ki tafi mana ko kuma na huce takaicin wannan najadun aknki wallahi”….

Dasauri na dago da kaina ina dubanta … “Subhanallahi Anya mahaifiyata kuwa tasan darajar aure mijinta na sunnah take aibatawa da cin fuskarsa agabana, wai meke damun ummah ne…

Cikin jin zafin yadda ta watsasa agabana yadubeni fuskarsa ba yabo na fallasa “tashi ki tafyarki “ya mayar da dubansa ga ummah da ta rike kugu ta ke jiran jin abinda zai fito daga bakinsa.. Cikin kashedinsa da yake mata yace “ki kiyayeni hajara kan nan nawa da kike gani danye ne jagab wlh barikinah tafi taki”.ya idar da maganr yana Nuna umma da yatsa”

Tabe baki tayi ta jefesa da wani irin kallo taja tsaki taki matsawa daga gabansa saima gyara tsayuwarta da tayi tana jijjiga jikinta cike da masifa da rashin hakuri.

Ni kuwa Jiki amace natashi ina sharar kwallah zan fice naji muryar ummah tanacemin ” Idan Kin tashi daga makarantar ki wuce gidan Alhaji mansoor ya bamu wani abun Dan wlh na fara gajiya shima ai ubankune ko bayaso dan haka dole ya kula daku da nauyinku”. ……

 

Umma ta fada tare da tillo min wata tsohuwar Dari biyu wacce zanyi kudin napep dasu…

Durkusawa nayi nadauki kudin Allah Maya sani na tsani zuwa gidan babah alhaji (mansoor) .. Dan banason wulakanci ko kallon banza … Saidai ayadda umma take yanxu kamar kububuwa nayi Mata musu wani sabon masifar ne, mai yuwuwa ta hauni daduka Dan zuciyata fake zafi, hakan yasa na fice daga dakin dasauri….

 

Nikuma wannan ce tawa qaddarar, allah ya shiryamin mahaifiyata, Saida na tsaya a soron gidanmu na goge fuskana data gama baci da kwallah sannan na saki nikabi na nacigaba da tafiya ahnkali har na isa makarantar…..

 

Bayan na gama koyar dasu kamar yadda na saba ina kokarin fitane daya daga cikin dalibaina maman abbah ta biyo bayana “malama zarah akwai maganr da nakeso muyi dake amma dan Allah idan antashi makaranta inaso ki biyo ta gidana dan akwai abinda ke damuna.. “(Dayake a unguwarmu take)

Jinjina kai nayi na dubeta kafin nace allah yasa mu tashi lfy…. Amma bayan sallar zuhr zan shigo insha Allah.. Domin akwai inda zanje idan na tashi makaranta “…

Cike da shaawar halayena tayi murmishi bakomai malama zarah allah yasaka da alkhairi ya baki miji na gari… ”

Kunya tasaka nayi saurin Sakin nikab Dina na ta fi ina murmishi….

 

Bayan da aka tashi makaranta ina dai² fita daga get din makarantar naji a namin horn da mashin kirar super cup.. Duk da ban juya ba nasan arra isiI madrisa ne {shugaban makaranta)… Murmishi nayi tare da Sauke ajiyar zuciya na tsaya har ya karaso… Shima kallon nawa yake yana murmishi irin kallon dayake jifana dashi yasani saurin sunkuyar da kaina kasa.. Ajiyar zuciya yasauke tare da Lumshe idanunsa ya waresu akaina…. “Malama Zarah guduna ma kikeyi ko? Ko shigo makaranta bakya yadda muhade…. “Ya idar da magana yana kuma zubamin tsimammun idanunsa duk da shi kansa yasan inasonsa tsananin. Kunya ne yasaka nake gujemasa.. Barinma nidin yarinya ce…..

Sunkuyar da kai na nayi ina murmishi kafin nace “ba hka bane ya ra is”…

murmishi sosai yayi yana duban kwayoyin idanuna yace “To yayi sarkin wayau tunda bazaki karbi laifinkiba kome kenan gobe insha Allah zan shigo, ina da bukatar sauraron kalamai masu sanyi da zasu fito da amon wannan zazzakar muryartaki”..

Cike da jin kunyar yadda yake koɗani na Dago da fararen idanunaina dubansa tacikin nikab kafin nace “ai maman amira na kula dakai, fiye da ni …(kasancewar yanada mata) na kasa cigaba da magana sai boyayyen murmishin da nake ta cikin niƙab dina.

Dariya yadanyi tare da shafa gemunsa “aike ta dabance zarah Kowa da matsayinsa keda maman amira itama tasan da labarinki kuma takan yawan cemin na gaisheki…, ” ya numfasa yacigaba da cewa ” Zarah kibani dama nagana da iyayenki wlh aurenki nake so nayi.. Zanyi alfahri idan na zabawa yarana uwa tagari mai addini malama hafiza kuma irinki… ”

Yadda ya idar da maganr yana dubana kawai hakan ya tabbatar min da gaskiyar abinda yake fada….

Tabbas inason malam kamal sosai… To saidai gani nake nidin nawa nake.. Koba komai nasan mahaifiyata bazata taba karbar malam kamal amatsayin mijina ba dan bashine irin mijin da takeso na auraba…. Duk da shidin ba laifi yanada rufin asiri matarsa daya hannatu da yayansa biyu amira da ammar.. Shekarunsa biyar da yin aure… Tun ina yarinta kwarai malam kamal ke rainin soyayyata azuciyarsa har zuwa lokacin dayaga yadace yasanar dani….

A sanyaye na dubesa nace “ya ra is ka kara hakuri kasan komai akwai lokacinsa….

Ajiyar zuciya ya saki “a gaskiya na kosa na mallakeki please… Zarah, allah ya kawo lokacin fa, amma ta bangarenki na gaza gane inda kika dosa”…

Ya idar da maganr a kasalance kamr mai shirin samin kuka…..

Shiru na sanyi kafin nace “ba haka bane ya ra is, mu ci gaba da addua allah ya tabbatar mana da alkharinsa, rana nayi zan wuce “..

Sallama mukayi

Yaso yakaini gida amma naki.. Hakan yasa mukayi sallama dashi….

Mai napep na Tara na hau muka dauki hanyar gidan baba Alhaji mansoor…. Adai² katafaren gidan mai napep din yatsaya tamkar yadda nabasa umurni na ciro kudinsa na mika masa na nufin bakin gate din gidan na fara knocking zuciyata na tsananta bugawa… Na jima ina bugs gidan kafin mai gadi ya budemin gidan…. Kallon sama da, kasan da yake min ya tabbatar min da bai shaidaniba hakan yasa na yaye nikab Dina ina gaidasa….

Washe baki yayi dan yanxu ya ganeni…tsohon yanada mutunci duk wanda yake da alaka da Alhaji mansoor yana mutuntasa…..

“Aah malama zarah kece agidan da rana haka bismillah shigo”…..

Ya fada tare da kara budemin gidan… Na shigo inayimasa Godiya…..

A sanyaye na fara keta farfajiyar gidan zuciyata duk atsorace take dan banason abinda zai saka awulakantani…………

Da sauri na dauke idanuna daga abindasuka ganemin. ya Anwar ne shida wasu Mata su uku da kallo daya zaka musu kasan idanunsu abude suke suna da wayewar bariki sosai, sai kuma wani matashin saurayi da zaiyi sa’arsa suna buga wasan suluka a inda aka tanada domin buga wasannin.. Dan gidane mai she gen girma da bangarori daban daban… Daga shi sai farar singlet da 3quarter wanda ko gukwowinsa basu gama rufewa ba…. Hakan zaisa har gashin dake kwance akirjinsa da kafafunsa zaka iya gani…. mutum ne shi mai faffadan kirji da duj wata siffa dazati da allah yayiwa hallotarsa ta cikakken namiji. Ga wani irin aski da yayiwa sumar kansa da kasumbarsa da ya ajiye.. Yan matan dake gefensu kuwa basuda banbanci da a kirasu da kiristoci, ko kuma a kirasu da yayan musulmai marasa tarbiyya… Tun daga irin shigarsu har zuwa karan sigarin dake hannun su suna zuka…. Har gara abokinnasa Mubarak… Duk da, shima cikin shigar kananun kayan yake…

Rike sandar dake hannunsa yayi yana kokarin buga wasan shanyayyun idanunsa suka sauka akaina… Lasar busassun labbansa yayi yabini da kallon da za a kiransa na kurullah,kafin lokaci da ya yadauke idanunsa akaina ya watsar ya cigaba da buga game dinsa.

Cikin faduwar gabar da ta riskeni sakamakon tozali da nayi da idanunsa dasuke tsoratar dani Saurin kawar da kaina nayi nacigaba da tafiya a hnkli amma duk da haka kirjina na bugawa dan ajikina naji yana kallona duk da ban dubesa ba, batare da na dago da kaina akasaba nacigaba da tafiya har nashige cikin kayataccen falon nasu da ya gaji da haduwa da kayan more rayuwa tare da sallama ..

Falon babu kowa sai suwaiba me yimusu aiki tana goge² … Washe Baki tayi tare dayimin sannu da zuwa bayan ta amsamin sallama ta….

Zama nayi a daya daga cikin Kayattun kujerun falon…. Ruwa da lemo mai sanyi suwaiba ta ajeyimin agabana tare da tsiyayamin lemo tafara yimin firar yaushe gamo… Murmishi nayi na karba na fara kurba sanyinsa yafara ratsani musamman yadda na shawo rana duk da har ynxu banji motsin yan gidan ba….

Tambayar suwaiba nasoma yi su hajiya da kuma nazifa dan tunda nashigo banji motsinsuba.

“Ai hajiya na ciki tana falonta, idan kingnta babban falo to saida dalili , su kuwa yaranna basu tashi ba lokacin tashinsu ne baiyiba dayake kijsan safiya ce yanxu. ”

Jinjina kai nayi ina mamakin su yadda jindadin duniya ya shagaltat dasu, tambayarta nakumayi “abbah fa? “Kin kuwa taki sa’a yana gida bai kaiga tafiya office ba da yake hutun karshen sati ne (weekend).

Shigowar Alhaji mansoor da hajiya salmai yakatsemuna tattaunawarmu da suwaiba, tun kafin su idar da saukowa downstairs suwaiba takoma kan aikinta tafice da ga falon, yayinda nikuma na shiga daidaita nutsuwata ina jiran su idar da saukowa, kaina akasa har suka karaso tsakiyar falon yadda naga hajiya rike da briefcase na abbah ya tabbatarmin da rakosa tayi zaifice.. Saurin zamewa nayi daga kan kujerar na gaishesu.. Adakile hajiya ta amsa min gaisuwar da dukkan alamu zuwana gidan bai mata daɗi… Haka abbah mansoor atakaice ya amsamin gaisuwar cikin kosawa ya soma tambayata abnda ya kawoni…

A sanyaye na fadamasa sakon ummah daga haka naja bakina na tsuke inajiran jin abinda zai fito daga bakinsa…

Guntun tsaki abbah mansoor yadanja ya ce “zan duba inga abinda ya dace, amma pls banason yawan korafi, roko dakuma navi “…

Bance dashi komai ba ya karaci fadansa har ya fice kaina akasa zuciyata namin zafi, babu abinda ke saurin zubda kimar dan adam irin roko, babu abu mafi kaskanci da ya wuce kayi roko gun wani da ba allah ba, allah ka kara yimana wadatar zuci… Na sauke ajiyar zuciya cikin wani irin yanayi na dago da kaina, idanuna suka gauraya da na hajiya.. Taɓe baki ta yi itama cikin halin ko inkula taja tsaki marar sauti ta haye sama…

Daskarewa nayi a inda nake, idanuna namin zafi sosai kamar yadda zuciyata ke min zafi dangane da maganganun abbah mansoor, ya nuna tamkat mudin ba yayansabane, na cikinsa kawai yasani sukuma yake da hakkin ciyarwa..

 

Ko sallama banyiwa suwaiba ba na tashi na nufi kofar fita.. Ina kokarin murda handle din kofar aka rigani, cikin rashin sani mukayi kato da mai shigowa..

“Subhanallah ”

Nafada ina rike goshina tare da rntse idanuna kafin nayi karfin halin duban wanda nayi karo dashi…

Maman boy

[15/10, 2:23 pm] +234 802 734 6971: *_GAMJI WRITERS ASSOCIATION_*

_Home of exceptional writers_

 

 

*_RUWAN JAKARA…_*

_(idan ba’a sha a birni ba, asha aƙauye)_

 

*_LITTAFN_*

_MARYAM HAMISU YUSUF (MAMAN BOY)_

_wattpad@mamanboy279_

 

_fitar farko *2019*_

_fita ta biyu *2022*_

 

*_3_*

Idanunsa tarr akaina yake dubana yadda na dafe kaina sakamakon karon da mukayi da juna… Chest dinsa nagefen haggu yadan dafe da dukkan alamu anan na gware kaina kuma shima yadanji zafin hakan…

Lumshe mayun idanunsa yayi cike da miskilanci ya dan kalleni sama da kasa kafin ya watsar yasoma kokarin raɓani zai wuce… Nikuwa ganin ya anwar ne nayi karo dashi cikin razana nadan ware manyan idanuna musamman dana ga fuskarsa bavu faraa, (danshi baicika yin dariya ko murmishi ba gashinan dai kamar wani mutum-mutumi sai tarin iskanci da wulakanci akwanyarsa.. Cikin rawar murya nasona basa hakuri “dan allah kayi hakuri ban… Lura.. d.. a shigowarkaba ”

Saida ya karasa tsakiyar falon ya zauna akan kujera ya dubeni da har lokacin na fidda ran zai kulani, cikin isarsa ya dubeni, irin duban dana tsana wato kallon kurullah dana fahimci tamkar nikadai yake jifana da irin kallon kafin yace”is okey, ”

Hakan yasa nasoma kokarin ficewa daga falon.

“Ina zaki je ne”..

Ya jefomin tambayar rainin wayau yana kallon fuskata..

Kasa nayi da kaina muryata na rawa nabasa amsa da cewa “gida zan tafi “..

“Muje”

Cikin bani umurni yayi maganar tare da mikewa tsaye ya nufo inda nake…

Kirjina ya buga da karfin gaske ban iya yimasa musu ba har muka fito compound tare, parking area yawuce Ina binsa abaya kamar xariyar wando.

Duk illahirin jikina rawa yakeyi har ya isa daidai gun wata rantsattsiyar bakat mota ya bude min murfin motar, still cikin bani umurni ya ce “shiga ”

Tsananin tsoronsa da nakeyi na shige batare da na yimasa musu ba..

Shima shiga yayi ya zauna anazaunin driver ya sanyawa motar key ya kunna yasoma kokarin tayar da motar..

Nikuwa ina ta mazurai ganin ikon mallaka da nake gani agurinsa da isa kamar wani jinin sarauta…

Tunda dai ya tada motar ya fice daga gidan bancemasa komai ba, shima bai kulani ba, babu abinda kakeji sai sautin wakar naira marley da ya kunna.. Lokaci zuwa lokaci yake maming wakar …

saida muka yi nisa sosai yasanya nadinga yimasa kwatancen hanyar da zaibi mu isa gidanmu, dan ko gidan namu bai sani ba har muka cikin tsohuwar unguwarmu, bai iya shiga da motarsa kutsattsen lungun muba ya ja burki ya tsayar da motar dan motar bazata iya shiga lunfunmuba sakamakon kwatofi dasukayi yawa a unguwar..

“Nagode”… Nafada ina kokarin ficewa daga motar naji ya ce “meyema sunanki? ”

Banyi mamaki ba dan baisan sunana amatsayina na yar uwarsa ba, hakan yasamo asaline da rashin son zumuncin abbah mansoor…

 

“Suna na zarah”..

Na basa amsa a sanyaye..

Cikin shan kamshi ya dauke idanunsa akaina yace “ke kyakkyawace, ba iya kyauba kina da sirrin fizgar hankalin duk wani lafiyayyen namiji”

Iyakar abinda ya fada kenan yayi shiru tamkar ba shine yayi maganar ba yamayar da dubansa ga gefen hanya yana duban yanayin unguwar tamu azuciyarsa kuma akwai abubuwa da yawa da yake saƙawa..

Sunkuyar da kaina nayi kirjina na bugawa sosai dan ni har ga allah tsoron yanayinsa nakeyi.. Jin nayi shiru ne yasanya maido da hankalinsa aguna ya dauko kuɗade masu yawa ya miƙamin “ki kaiwa ummanki tayi bukatunta da naku”..

Yayi maganar yana min murmishi na gefen kumatu..

Duban kudin nayi na dubesa na gaza yimasa musu , kenan ya fahimci matukar nazo gidan su to bukata ce ta kawoni kenan..

Hannuna na rawa na karba nayi masa godiya na fice daga motar yana bin bayana da mayataccen kallonsa da na lura nikadai yakewa irinsa..

saida na shige lungunmu kafin yadauke

Idanunsa akaina yana sauke ajiyar zuciya.

 

 

Ina shigowa gidan bada jimawaba umma ta shigo Itama..

Ina dakina ina nazarin litattafaina umamh ta hankado labulen dakin KO sallama babu…. Dayake akwance nake shigowarta yasa na yunkura inayimata sannu da zuwa….

“Baibaki Komai bane shi alhaji mansoor din? “….

Ta jefomin tambayar amaimakon amsa sannun da nayimata….

A sanyaye na isa inda nake ajiye kayan sakawa na cikin ganamazgo na bude na dauko mata kudaden da ya anwar yabani na mika mata nayimata bayanin komai…

Washe baki tayi cikin farinciki tasoma lissafawa dubu hamsin ne cas ba daɗi ba ƙari

Idanu na zubawa umnah ina kallon yadda take kara fadada faraarta ta lissafe kudin ta soke a zane.. Cike da takaici nasoma magana cikin sanyin muryata “dan allah ummah ki daina aikena gidan abbah mansoor, duk da tamkar mahaifinmu yake amma banajin dadin yadda yake wulakantamu kafin ya bamu kudin, yau ba dan yaya anwar ba wlh ba abinda zamu samu, kisamu waTa sanaar kidingayi ummah dazamu dogara dakanmu….

bugemin bakina ummaa tayi da ya tilastamin yin shiru na saka hannuna rufe bakina da ina tsammanin le;ɓe ya fashe ina hawaye….

Tana cikin huci tare da takaicin kalamaina tasoma magana “ke kau kinji haushin rayuwarki batula.. Wannan gadon bakin ciki na bakin halin mahaifinki da kikayi bakiji dadinshiba…domin mahaifinki tun yanada rai idan akwai abinda ya tsana yaga ina cigaba arayuwa har yabar duniya bakin cikiyakemin, wato ke bakida buri daya wuce kiganni cikin bakar wahala ina neman yadda zanyi ko, to allah yafiki bakar aniyar ki tabiki…..

Fashewa nayi da kuma still ina shafa lips dina danakejin sun soma kumbura s ” kiyi hkr dan Allah baki fahimceni bane …. “… Na idar da maganr kuka na sarkeni

Huci kawai umma keyi kafin tanunani da yatsa “ai wlh bakincikinki ke zai ci.. Kuma kema zakiji ajikinki bazakici abincin da re ba dan kuwa ban memo dakeba wadannan ma bakida rabon ko ko kobo aciki… ”

Ta fada tare da ficewa kamar kububuwa.. Kifar dakaina nayi ina kuka ba, abincin data hanani bane yasakani kuka ba… Illah halayenta data gagara sauyawa…. Saida nayi mai isata na tashi na wanko fuskata na zira hijab dina dazummar tafiya gidan ma man abbah kamar yadda nayimata alkawari dan kawai nasamu sassauci azuciyata dan gaba daya gidan jinakeyi yamin baƙi…

 

Ina fitowa tsakar gida Kicibus nayi da gwaggo kwazo Tana shara.. Da dukkan alamu taji duk kwakwazon da ummah keyi….

Kiran sunana tayi tare da nufo inda nake “uwar dakina kici gaba da hakuri da halin mahaifiyarki.. Nasan kinayimata tsananin biyayya karki daina har lokacin da Allah zai kawomiki miji ku rabo lafiya kinji, kije Ki dawo abinda kike so zan girka wato dambu”…

Murmishi nayi tare da fadan “gwaggo Ngd Ki jirani na dawo yanzu sai muyi aikin atare “..

Dariya kawai tayi tare da min adawo lafiya….

Ahankali nakejin zuciyata na sanyi har na isa gidan ma man abbah…. Anan fa naga karramah Komai saida takawomin… Saidai bazan iyacin Komai ba saboda inason cin dambun gwaggo kwazo mai dadi… zoɓo kawai na kurba na ajiye danni ba mai yawan cin abinci bace…

Babu bata lokaci Atake tafara zayyanomin damuwarta game da mijjnta, da uwar mijjnta,ta nisa cikin damuwa tacigaba da cewa “Sam jamilu yadaina kulani zarah.. Baya kusantar duk wani abu dayake da kusanci dani.. Idan nayi girki byaci… Ba wai zantona sirrin aurenmu bane amma nadauki tsayin watanni takwas wata alakar aure bata haɗamuba, Ga sharrin mahaifiyarsa da kanwarsa kullum Kara yawa yakeyi. malama fadima kibani shawara.. Da ingantattun Addo in dazan dingayin Allah yajuyomin da hankalin mijina…

Taidar da maganar Tana sharar kwallah….

Zuba mata idanu nayi na tausayawa ma man abbah domin matar batada matsala dakowa haja rayuwar take kowa da abinda ya dameshi kuma kowa da irin kaddararsa ….

Cikin sanyin murya nasoma magana “kiyi hakuri maman abbah bakomai ne ke dawwama ba jindadi KO akasinsa… AbubUwa dayawa zasu zama tarihi. Idan mukayi hakuri da tsanani sai rangwame (sauki) ya riskemu… Shawarar dazanbaki Ki yawaita istigfari domin yana Kara kusantar da bawa ga ubangijinsa sannan kuma kowace sallah idan kingama Ki dinga karanta wallahu galibun ala amrihi kafa 41.. Da sannu Allah zai kawomiki daukinsa.. Ita addua bata faduwa kasa ….

Tunda na fara magana takafeni da idanu Tana share kwallanta…

Kamo hannayena tayi cikin jindadin shawarwarin da na bata tace “nagode malama zanyi amfani da shawarwarinki… Wlh zarah duk sallar dazanyi sainayi addua Allah ya bani ƴa datakeda koda rabin iliminkine da nutsuwar da kaifin harsher wajen iya tsara zance.. Wlh mahaifiyarki tayi farar haihuwa… Saura gwarzon namiji mai saa dazai daukeki….

Murmishi kawai nayi…. Ina, sunkuyar da kaina..

. Sai bayan sallar asar na baro gidan ta cikani da kayan arziki da humrori masu kamshi da, kayan kwalliya….

Ina isa gida umma harta kuma ficewa… Saida Muka gama dambun shinkafar hausa da yaji zogale nida gwaggo kwazo… Muna ci muna fira Tana bani labarai Na su na mutanen da nikuma ina aikin dariya harsaida nayi dam..

Wanka nayo domin tunbayan sallar issha nakejiran zuwan malam kamal.. Na shirya cikin wani leshi wanda jikar gwaggo kwazo ta bani shi.. Banyi make up ba na zira hijab dina nakwanta tare da lumshe idanuna ina tilawar hardata ta alkur’ani mai girma.. Hayaniya nasoma juyowa sama² hakan ya tilastamin ware idanuna tare da fitowa daga dakin… Ya faruq nagani tare da umma datashigo ynxu sai yaran unguwa da matar makwabcinmu malam mustapha wai ya faruq shine ya sacemata akuyoyinta…. Masifa akeyi agidannan ummah ta kafe Tana tarewa ya faruq duk da tasan shidin baida gaskiya… Jingina nayi akofar dakina kasancewar jiri danaji na diba na innalillahi nake karantowa sauba adadi…na fito tsakar gidan Hakan yasanya kwallar data taru a idona zubowa…..

Zuwan mijin gwaggo kwazo ne ya lallaba matar ta tafi dan Ana ganin kimarsa a unguwar… Yakuma kora yaran dasuka taru agidan sunayiwa ummah da ya faruq ihu…..

Fashewa nakumayi da kukan takaici na durkushe anan… Ummah kuwa da ta dawo daga zauren soron gidan tayi kicibus dani atsakar gida ina hawaye Wata uwar harara umma taballomin “wahalalliya ahaka idanunki zasu kafe indai akan wadanna tambadaddun yayyunnaki ne…. ”

 

“Aah hajara ba ayiwa ya’ya haka. Aisai su ida lalacewa.. Addua zakiyi Allah yashirya “…

Cewar goggo kwazo da suka shigo gidan tare da ummah

 

“Wlh kwazo bazan bata loakciba wurin yiwa su faruq addua ba shi dai ba yaro bane ….. ”

 

“Ance malama zarah tazo”….

Sallamr yaron takatse musu maganr su…

Cike da masifar da take shirin saukewa akan yaron da baiji bai gani ba ummah “Ubanwa Waye yake kiranta? ”

Atsorace yaron yabata amsa da cewa “wani ne “.

“Akan mashin yake kokuwa mota ce ya zo da ita? ‘”

 

 

 

 

Maman boy

[15/10, 8:38 pm] +234 802 734 6971: *_GAMJI WRITERS ASSOCIATION_*

_Home of exceptional writers_

 

 

*_RUWAN JAKARA…_*

_(idan ba’a sha a birni ba, asha aƙauye)_

 

*_LITTAFN_*

_MARYAM HAMISU YUSUF (MAMAN BOY)_

_wattpad@mamanboy279_

 

_fitar farko *2019*_

_fita ta biyu *2022*_

 

*_4_*

… “Kaje yafadamaka kowanene shi”…

cewar ummah tana zarewa yarob idanu cike da masifa

Da gudu ya fice bai daɗe ba ya dawo yace “Yace sunansa malam kamal.. Kuma awani mashin yake super cup Amma bai tsufa ba …

Yadda yaron ya zage yana korawa ummah bayani saida raina ya baci

Riƙe haɓa umma tayi kafin tashiga sallallami tana tafa hannuwa dan zuwa yanxu ta fahimci malam kamal ne yazo “oh ni hajara wannan mutumin idan mayene yakama mutum Bazai sakiba. Irin wannan naci haka… ”

 

Umma tafada tare da nufar hanyar kofar gida.. inda na tabbatar wankin babban bar go take da niyyar yiwa malam kamal..

Dasauri na dubi gwaggo kwazo duban da yake nuni da Ki hana ummah zuwa…

Saidai Tun kafin gwaggo tayi magana umma harta fice..

 

Jinayi kafafuna sun Gaza daukata.. Kuma bazan iya komawa dakiba.. Hakan yasa na durkushe anan na rafka tagumi tare da kashe kunne inji me zata kuma fadawa malam., zuciyata kuwa sai suya takemin idanuna namin zafi…

 

A kofar gida umma ta iske malam kamal ya kafe mashin dinsa ya zauna akan dakalin kofar gidannamu… Sanye yake cikin farar jallabiya da hular nan da ake kira ta6a kaji hadisi.. Yayi matukar kyau sosai dan malam kamal badai tsabta ba da iya wanka irinna ustazai ba…

 

Ganin fitowar umma yasakashi saurin tashi akan dakalin yana gaidata cikin ladabi…

 

Asheke umma ke kallonsa tana amsa wa kafin ta cigaba da cewa

“Akramakallahu kaine dindai ka sake dawowa… Da alamu gargadina bai shigekaba. . “…

 

 

Dago da idanunsa malam kamal yayi ya Dubi umma kafin ya mayar dasu kasa a hankali yasoma magana “kiyi hakuri ni kaina na kasa yin hakan Amma dan Allah karki tauyemu dagani har Zarah munason junanmu.. Kuma dagaske nake aurenta zanyi, kibani dama na tabbatar miki da hakan”….

 

 

“Dallah rufe bakinka alaramma… Ai sonake ka Gane ita din ba saar aurenka bace ka fahimci cewa ruwa ba saar kwando bane, Babu abinda zarah zatayi dakai… Dame zaka riketa da sanaar koyarwa din da albashinka baifi dubu bakwai zuwa takwas da su ne zaka dauke duk wasu bukatunta….”

Gyara tsayuwarta tayi tacigaba da cewa “aikuwa akramakallah kaso kanka, Kaga kaje kasamo kalarka.. Domin zarah matar manyace… Gari da yawa maye bazaici kansa ba…. Katsaya amazauninka na malaminta… Amma maganar aure.. Kada tsautsayi yakara sakaka Kace kanason zarah”…

Tunda tafara balbalin jarabarta malam kamal baice komaiba harta kakkabe tashige gida…

Shidai a iya saninsa zarah bata dace da mahaifiyaba… Ikon Allah kenan mai fidda kyakkyawa ajikin gur6atacce!!!

 

Umma nashigowa mukayi ido hudu da ita na rushe da wani irin kuka.. Dan duk abinda ta fadawa malam a kunnena. Tashi nayi na shige daki inajin zuciyata na gab da bugawa…

Wata uwar harara ta ballomin “shashasha wacce batasan meke mata ciwoba. . KO ubanme ya hada kifi da kaska “…

Itama gwaggo batace komaiba ta shige dakinta dan ta fahimci masifa kawai umma keji ayau… Haka ta karashi haushinta ta atsakar gida babu wanda ta tanka ta..

 

…,……

Anwar kuwa tun bayan da ya ajiye batool (zarah) yabar kazamar unguwarsu kamar yadda yasaka mata suna, baya tunanin zai iya bada ko kiwon dabbarsa a unguwar.. Sosai yake kyankyamin unguwar har ya barta..

 

Daya daga cikin gidan gonar da yake mallakinsa ya wuce.. horn daya zuwa biyu gate keeper ya bude masa gate din yalwataccem gidan gonar da ya tara ni intattun dabbobin gida…

Aparking area yayi parking motarsa ya gito, mai gadi nayi masa barka da shigowa da hannu kadai ya iya amsa masa bai dubesaba ya nufi sitting room dinsa da ya gaji da haduwa… Haka yake kasancewa matukar baya office to yana tare da abokansa ko yan matansa idan kuwa baya bukatar hayaniya direct yake kado kan motarsa yayo gidan kajinsa, haka ma yau din kawai yaji tunanin zarah ya hana sakat ya dabaibaye zuciyar sa ta yadda ko kwayar idanunsa ya rufe ita yake kallo, matukar yayi tozali da yarinyar cikin wani irin kasalallen yanayi yake kasancewa, yadaɗe yanajin wani abu agame da ita da ya tabbatar maitar sa ce ta hau kanta, baiyimusu da zuciyarsa ba fomin ba tunyau zuciyarsa ta kwadaita masa yarinyar ba, maaifar shaawar yarinyar yake tamkar mayen karfe da karfe, tun kafin ta ida zama ɗanyar cikakkiyar budurwa, duk da bai taba ganinta ba hijab ba, bakar jarabarsa da jarababben kallon da yake mata bai hanasa gane asalin sirrin kyan surar da ubangiji yayimata ba. Haka jarabarsa take babu kuma wadda yabari matukar ya daura maitarsa akan mace sai ya samu nutsuwa da ita ba ruwansa da yar talaka ko mai kuɗi, tana sonsa ko bata sonsa. Lasar busassun la66ansa kawai yayi, ya bude medium fridge din dake sittinroom din yadauko robar ruwa ya bude murfin ya kafa yasha ruwan sosai kafin ya ajiye robar ya zauna akan daya daga kujerun dake sittinroom din ya Kunna shisha cikin kwarewa yake zukar hayakin daga bakinsa yana fesarwa yana lumshe idanunsa dasuka soma sauya kala, kashe wayoyinsa yayi dan bayason ana yawan damunsa da kira yayinda zuciyarsa na cigaba da kawata masa kyau na zarah dayakeji kamar zai haukace akanta ayanzu

 

Yadauki lokaci ahaka kafin afara knocking din kofar.. Bude idanunsa yadanyi, yasan babu mai shigowa gidan sai billy, daya daga cikin yan matansa ne da yake son kasancewa da ita sosai, ita kanta tana masifar sonsa, tayadda bata iya daukar tsawon lokaci batare da ta kasance da shiba, yana son billy sosai, kuma duk cikin yan matansa ita kadaice zatazo inda yake kai tsaye aduk lokacin da taso.. , bai motsa daga inda yakeba yabata izinin shigowa ya mayar da idanunsa ya rufe.

 

batare da ɓata lokaci ba billy ta shigo falon kyakkyawar budurwace kamannunta da, shigarta kawai zasu Nuna maka gogaggiyar Yar duniyace da tasan hannunta

Sanye take cikin wasu fitinannun kananun kaya Riga da skirt.. …

Kannan nata yasha gashin doki.. Saidan karamin gyalen data aza akanta.. Hannunta janye da madaidaicin akwatunta….. Ta kafe katon g glass goshinta

Ware jajayen idanunsa yayi akan ta yana dubanta , itama tsakiyar kwayar idanunsa take kallo da suka cika da jaraba, da alama dai tazo adaidai, dan kallo daya tayiwa Anwar tagane yanayon da yake ciki, itakam tarasa waccce irin jaeabace garesa da baya hutawa rayuwarsa da ga janyewa ya mace

Cikin yaukinta ta karaso inda yake ta ajiye akwatunta shikuwa hannayensa ya ware ta shige ajiknsa Tana kara shigar da kanta a faffadan kirjinsa, shikuwa da dukkan hannayensa ya sanya ya rungumeta idanunsa a lumshe yake faman shinshina ta, aransa yana kisssimaa samun damar kasantuwa da zarah a irin wannan lokaci, shikansa ya rasa gane dalilin da lokaci daya karamar yarinyar ke nema hautsina tunaninsa..

Belly kuwa cigaba tayi da aikamasa sakonni ajikinsa da ke nuna zalkar yadda tayi kewarsa a yan kwanakin da tayi tafiya bata tare dashi

 

… “Imisse uh honey “… Ta fada cikin wata irin kasalalliyar murya tana hura masa iskar bakinta akunnensa.. Duk da ta fahimci yana cikin wani irin yanayi da ya haifarmasa da muruwar jiki. Amma hakan bai hanata gano tsantsar jarabarka daaddabarsaba duk da yanayin da yake ciki

 

Can kasan makoshi yasona magana ” Kin shammaceni… I missed uh too..

Yafada yana lasar lips dinta…. yana duban kwayar idanunta hannunsa na yawo a face dinta dayake shafawa ahankali..

Zuwan billy bakaramar nutsuwa ya sama masa ba, har lokacin da suka tabbatar sun samu gamsuwa da junansu amma anwar bau rabu da billy ba,

Saida suka tabbatar sun jiyar da junansu dadi kafin anwar yasamuba nutsuwa.. Duk illahirin jikin belly ya mutu dan sosai anwar yanunamata yadda yayi kewar ta… Shikansa yajisa daidai, Bacci maishegen nauyi yadaukesa…

 

Saida belly ta yi kwana uku atare dashi tamkar dai matarsa ta aure.. Idan ba office da yake fitaba babu abinda ke rabasa da ita Baije KO in stI’ll wayoyinsa aka she suna manne… Daddy yayi nemansa a waya har yagaji..

 

 

Da misalin karfe, huɗu na yamma ya dawo, a bedroom ya tarar da billy na bacci baibi takanta ba ya wuce bathroom ya sakarwa kansa ruwa infew minutes ya fito daga wankan, daure da towel a kugunsa sai dan karamin towek dake hannunsa yana tsane bakar lallausar sumar kansa..

Fitowar sa daga bathroom tayi daidai da farkawarta daga bacci da murmishi mai tattare da tsantsar soyayyarsa ta bisa da kallo har ya isa dressing mirror

 

Ta mirror yake kallonta yadda takafesa da idanunsa juyowa yayi yana smile… “Me kike kallo haka kamar kinga wani baƙo kona sauya Miki ne…”yayi maganar yana daga mata gira kafin yamayar da hankalinsa Wurin taje sumar kansa..

Lumshe idanu tayi “honey yaushe zakayi aure…. ”

Tambayar datayi masa taso sakashi dariya Amma ya danne dariyar yayi kamar bazai kulata ba kafin ya bata amsa “ada babu tsarin yin aure a rayuwata.. kinsan wayeni mace daya bazata isheni ba… But now I have change my desire… ”

yunkurawa tayi zaune cike da karfin guiwa tana smile tace “gaskiya honey yakamata muyi aure mu mallaki junanmu baki daya, … ” wannan lokacin sai da yayi dariya sosai har saida ya zauna saboda dariyar.. Wani irin kallo ya watsowa billy na bakida hankali “you are so funny ” ya fada yana tsagaitawa da dariyar

Yadda take dubansa with serous yasakasa cigaba da cewa ” Bazan iya auren gogaggr Yar bariki irinkiba gogewarki tayi tawa … Kamar matar da zan aura dole takasance… Ko hannunta wani baitaba rikewa ba. Bare tayi having sex da, wani Wacce zan bareta da kaina ba irinkiba sauran wasu… Kidaina wannan tunanin.. Ya idar da maganar yana ida dariyarsa yacigava da shirinsa

Ran billy ya baci sosai ta danne tare da dubansa tace “baby ni kake fadawa haka ? Well.. ai naga dan iska dole sai Yar iska zai aura kwarya tabi kwaryane idan ta bi akushi bazata moruba”….

Cikin jin zafin kalamansa ta mayar masa da martani

Murmishin gefen kuma tu Yayi yayi saurin katseta da fadan “wannan lokacin dan iska sai ustaziyya…” c

Yafada tare da ajiyemata kudi masu yawa agefen gadon…. Yadan daure fuskarsa ya ce “Zan fita inada AP da wasu offices a company by 8pm so idan kinshirya zaki iya wucewa… Dan bazan dawoba ayau….

Ya fada yana daga mata gira…

Dan karamin tsaki taja da ita kadai taji sautinsa ta bi bayansa da kallo har ya fice, tana azabtuwa sosai da soyayyarsa … Mostly duk macen dayayi having sex da ita…da, wuya ta barsa… Sautari kawo kansu sukeyi awurinsa dan ya iya salon tafiyar dakowace mace dakeji itadin mai lafiyace… Yayinda shikuma yadaukesu tamkar kayan dazai saka ya cire alokacin da yaso

 

 

Akasalance tayi wanka ta mayar da kayan jikinta tashiga kitchen nufa ta hado coffee tasha.. Tasaka kudadenta a Yar karamar hand bag dinta… Komawa tayi ta kwanta a kan gadon tana shakan sanyayyan kamshin turaren anwar da ya bari a bedsheet din sai lumshe idanu takeyi…..

 

***

Tundaga ranar da ummah tayiwa malam kamal wulakanci…. nakejin kunyar hada idanu da malam kamal.. Duk abinda zai hadani dashi a makaranta na kauracemasa… Hatta office dinsa nadaina zuwa Ga wata irin soyayyarsa dake addabar zuciyata..nikaina nasan inas son malam kamal saidai babu yadda na iya da lamarin ummah… A dan kankanin lokaci saida nayi rama…

Duk yadda malam kamal keson yaganni sai nasan yadda nayi na zille masa.. Sosai nake son nabasa hakuri.. saidai nauyin abinda umma tayi masa ya hanani hada idanu dashi……. Yau nadauki Anita zuwa har staff dinsa nabasa hakuri cinkashin da umma tayimasa a

 

Da misalin karfe hudu na yamma nagama shirina na tafiya makaranta…. Dakin goggo na shiga nayimata sallama….

cikin sanyin jiki nake tafiya harna fito kofar gida…. Cikin tsananin tashin hankali datsorata nayi Baya jikna yafara rawa litattafan dake hannuna suka zubo akasa…. Ganin Anwar a kofar gidanmu yaai masifar hautsina man ciki… Musamman yadda ya harde hannayensa a faffadan kirjinsa ya zuba man tsimammamun idanunsa kuma jajaye dasuka kara firgutani…. Tamkar dama nidin yake jira nafito…. Babu laifi yadanyi shigar mutunci aranar wacce Tafito dashi tamkar wani kamilin mutum.. Saidai Daka kalli lips dinsa da sexy eyes.. Zai nunamaka tsantsar tantirin dan bariki ne kuma.. KumaMashayin taba.

Dan guntun murmishi yayi dakansa ya karaso inda nake dan izuwa yanzu ya fahimci yadda nake azabar tsoronsa…can kasan ransa kushe tsantsar kauyancina da gidadancina yakeyi… Koba Komai aishi dan uwanane so for what zan dinga tsoronsa kamar naga azra Ilu.. .. Da wannan tunanin yake kokarin karasowa inda nake, cikin basar da ni ya dauke idanunsa yana kokarin kutsa kansa acikin gidanmu

Tun kafin ya karaso nasoma tattara litattafaina ina dauka…nikuwa cikin tsoronsa da allah yajarrabeni nake kokarin komawa cikin gida .. Saidai tunkafin na shige yasamu nasarar cafko hannuna tare da hijab dina… Dan ya fahimci ganinsa yasa zan koma cikin gidan….

 

Maman boy

Leave a Comment

error: Content is protected !!