Sababi Hausa Novel

Yar wanke wanke

Sababi Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag:  SABABI

 

 

 

 

EXQUISITE WRITER’S FORUM

 

TAURARI BIYU⭐⭐,DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU.

Amina Ibrahim(Oum Ameer)

Fatima Muhammad Gurin.

 

“SABABI”

Na Oum Ameer

TARE DA

“GAMON JINI”

Na Fatima Muhammad Gurin

Duk zasu zo muku a farashi mai rahusa.

Guda biyu 500

Idan kuma ɗaya kike buƙata 300

Zaku iya biyan kuɗinku anan:

3118518476

Fatima Muhammad Gurin.

First Bank.

Sai ku tura da shaidar biya ta:

09039206763.

Bama son katin waya Please.

 

 

 

PAGE 1

Free page……

 

Garin Gusau, unguwar Nasarawa bayan Gusau hotel.

Lokacin bazara, yanayi ne wanda ake doka zafi sosai da tsananin rana,wanda a irin wannan yanayin zaka samu mutane suna neman inda zasu sami wurinda yake da damshi da inuwa domin su samu su huta kuma su rage zafin da suke ji.

 

A irin wannan lokacin ilahirin mazauna unguwar maza,manya da yara  zaka same su a ƙarƙashin bishiyoyi,ko sassanyar baranda suna hutawa akan tabarma suna taɓa fira.

 

Tafe take tana tura baron ruwa (kura) mai ƙafa ɗaya,da duk iya karfinta,sai zufa take haɗawa wanda kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci akwai gajiya a tare da ita,sanye take cikin doguwar riga ta atamfar roba,sai hijabinta ta yadi uku,tsab-tsab take babu alamar ƙazanta a jikinta.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Tafe take a hankali tana nishi,saida taji da gasken ta gaji sannan ta ɗan tsaya domin ta huta,bayan ta huta ta tura zuwa gaba,tana kawowa daidai saitin majalisar su Malam Habibu ba tare da ta tsaya ba tace“ ina wunin ku?”

 

Cike da zolaya da munafurci munafukan cikinsu suka amsa ta suna mata kirari da “Sannu Asiyar Balaraba,’ya ɗaya tamkar da dubu”

 

Murmushi kawai tayi taci gaba domin ita wannan ba baƙon ta bane,masu gulmar ta a unguwar daga mazan har matan ba wanda ta damu da shi,buƙatar kawai itace taga cewar tayi iya yinta wurin kyautatawa mahaifiyarta ta ko wane fanni.

 

Har takusa shanye kwanar shiga gida tajiyo sautin tafiyar shi a hankali a bayanta,domin mutum ɗaya ne a duniya zata iya yana yi mata irin wannan ɗabi’ar,cikin sauri ya sha gabanta ya riƙe baron ruwan, tare da ɓata fuska yace“ Haba Asiyah! Ya muka yi dake ne akan ɗibar ruwan nan ?”

 

Murmushi ta sakar mishi tana girgizar kai tare da haɗe hannayenta wuri ɗaya alamar yayi haƙuri tace“kayi haƙuri Haris,mama tanada bukatar ruwan nan kuma kai ka tafi makarantar ta ka,kaga idan nace sai ka dawo na zama mai son kai kenan,ka wuni baka nan ka dawo ka gaji sannan kuma ka shiga ɗiban ruwa kaga abin sam baiyi ba…….”

 

“Dan Allah ki daina ma wannan maganar Asiyah,ni fa masoyin ki ne na haƙiƙa,zan iya komai domin farin cikin ki,idan kina waɗansu abubuwa sai in ga kamar baki gama aminta da ni ba”

 

A irin yanayin yanda take kallon cikin ƙwayar idanunshi shima yake kallon nata,hakan ya tabbatar mata da cewa duk abinda yake gaya mata bakin gaskiyar shi ne, ganin kallon bamai ƙarewa ba ne da sauri ta janye idanunta tana faɗin “ To shikenan Haris kayi haƙuri dan Allah, Insha Allah bazan sake ba ”

Hanyar gida ta nufa yayin da ya tura baron shima ya nufi inda ta nufa.

Haƙiƙa a duk lokacin da suke tare da Asiyah ya kanji farin ciki da nutsuwa ta musamman ta maye dukkan ilahirin jikinshi,ba kamar idan ya tuna yanda yake,shi ɗalibi ne a jami’a kuma kafinta bashi da komai bai kuma ajiye komai ba kawai dai shi mai nema ne,amma a haka Asiyah ta amshe shi hannu biyu biyu tayi amanna ita da iyayenta,ba tare da tunanin neman komai ba a wurin shi,ta tsaya kai da fata tace sai shi,duk wani ƙyale ƙyalin duniya baya gabanta,ita dai miji nagari mai rufin asiri kuma ga shi Allah ya bata, to taya bazai tsaya tsayin daka ya ɗauke musu duk wani nauyin da yasan zai iya ba?

Har yakai ƙofar gidansu da kyakkyawan murmushi ƙunshe a fuskar shi,ƙofar ta buɗe mishi da kyau ya shigar da baron.

 

Mama da ke zaune a farlour tana kallo a TV da sauri ta fito da taji sallamar shi,bayan ya sauke musu ruwan,yazo gabanta ya tsuguna cike da alkunya yace “ Mama ina wuni,ya gida ”

 

Cikin mutuntawa mama ta amsa da “ lafiya ƙalau Harisu ya makarantar?da fatar andawo lafiya ”

 

“ Alhamdulillah”

“Tau masha Allah, Allah ya taimaka ya ƙara rufa asiri……”waigawa tayi ga Asiyah wadda ke ta wasa da gefen hijabinta tace“Asiyah ki kawo mishi abinci….”

 

Miƙewa yayi yana faɗin “ A’a mama nagode,saida na ci abinci na fito ”

 

“To babu laifi,mungode sosai”

Cikin ɗaki mama ta koma shi kuma ya fice yayinda Asiyah ta bishi domin ta rakashi.

Sai dai suka zo ƙofar sannan ya tsaya yana murmushi yace“Asiyah ki tsaya a nan ki koma wurin aikin ki,nima tun da safe mai gida ya kirani yace idan na dawo daga makaranta akwai aikinda ke jirana a shago”

 

Ɗaga kanta tayi sama tana nazari sai can ta kwaɓe fuska cike da shagwaɓa tace “ Nifa wannan mai gidan ya cika takurawa masoyina da yawa,kullum shine Harisu kana jina kuwa,kazo ka yanka katakon gado,Harisu kazo ka ɗinka ƙyallen kujeru,Harisu mutanen sun zo sun ɗauki kayansu kuwa?….”

 

Dariya yake sosai har yana duƙawa,yanda take maganar da gaske kamar itace Oga Yahya,saida ya gama dariyar sannan yace “ Asiyah kiyi haƙuri karki manta halal fa muke nema,dole na in fita in nema domin in kare mutunci na in kuma kare miki mutuncinki da na mahaifiya ta da kuma ƙannena,yanzu haka ma Awwalu  ya kira ni ya sanar da ni akwai aikin fenti da saka tayils wanda ya samu weekend ɗinnan,Kiyi haƙuri addu’ar ki kawai nike buƙata masoyiya ta”

 

“ Ok tau shi kenan, Allah ya taimaka ya bada sa’a, Allah ya kare ka daga sharrin haram komai yawanta ya sadaka da alkairin halal komai ƙanƙantar ta ”

 

Lumshe idanunshi yayi tare da faɗin“ Ameen Ameen gimbiya ta”

Sosai yake jin Asiyah a ranshi,wato yana yi mata wata irin ƙaunace ta musamman…….

“Hey! Kana mafarki ne?”

Sai yanzu ya buɗe idanunshi yana dariya yace “yanzu aikin mi zakiyi ne?”

“ Yanzu ? Uhmm! To wanke wanke kawai ya rage min sai muci abinci da mama, in ɗan yi rihazal in ɗora tuwon dare,sannan zuwa karfe huɗu in yi wanka in fita islamiyya”

 

“ Ok,to Allah ya taimaka,Nagode ki huta lafiya”

“ Allah ya kaika lafiya,ina gaida Oga….”

Wata uwar harara ya maka mata tun kafin ta rufe bakin ta sannan yace “ Anƙi a faɗa mishi ɗin ”

 

Dariya ta fashe da ita da gudu ta shige gida,tasani sarai bazai faɗa ba,a ranta tana mamakin yanda Haris yake da mugun kishi ko Awwalu da yake babban abokin shi wani lokacin yana jin haushin yaga suna gaisawa.

Bayan ta shige saida saida yakai kusan minti uku yana kallon ƙofar kamar wanda yake jiran dawowar ta sannan ya ja ƙafafunshi yana murmushi ya ƙara gaba.

 

★★★

 

Zaune suke akan kafet tsakiyar farlour suna cin abinci kamar yanda tace,bayan sun gama ta kwashe kayan takai kitchen sannan ta ɗaukko ƙur’aninta kamar yanda tace,zaunawa ƙasa tayi yayinda mama ta koma kan kujera ta zauna.

“ Asiyah yau har ina kika samo ruwan nan ne? naga kin daɗe baki dawo ba,koda yake ruwan ne babu”

Ƙara gyara zamanta tayi da kyau tana faɗin “ cab! Kinsan wurin gidan ‘yan bautar ƙasar nan ko? Can samaru,har na can na ɗebo su wani gida,ga matar sai masifa take ta yi mana wai kada mu dawo,nace oho dai tunda na samo ma mama na ruwa ai ita tasani”

 

Waya mama ta miƙa mata da ‘yar damuwa akan fuskar ta tace“ Asiyah ungo ki kiramin kawunki yau duk banji shi ba ina fatar lafiya”

 

Wayar ta karɓa tana faɗin “Tau jinin soyayyar yaya da ƙanwa ya motsa ko?”

“ Eh ko akwai wanda ya isa ya hana ne?”

 

Dariya tayi tace “ Ah! Allah ya baki haƙuri mama na…..”dai dai nan ya ɗaga wayar da sauri ta ɗora mata a kunne tace “ ya ɗaga ”

 

Murmushi mama ta saki tare da ɗora hannunta akan na Asiyah da niyyar ta riƙe wayar, girgizar mata kai tayi a hankali tace “ Gimbiya mama yau ni ce zan riƙe miki wayar har ki gama”

 

Murmushi tayi tare da amsa sallamar da yayi tace “ Alhaji ina wuni,ya aiki”

“ Lafiya lau Balaraba ya gidan? Kinga yau duk baki jini ba ko? Yi haƙuri aiki ne yayi min yawa a office shi yasa,ya gida ya kuma ƙarin haƙuri?”

 

“ Alhamdulillahi,yasu Hajiya Fatima da Mariya? Da duk sauran yaran gidan?”

“ Kowa lafiya lau,ina Asiyah?”

Waigawa tayi ta kalleta sannan tace “Asiyah gata nan lafiya ƙalau yanzu saboda na ce ta kira ka shine ta fara yimin mita wai….”

Zaro ido Asiya tayi tare da sanya hannunta ta rufe bakin mama tana ta girgiza mata kai alamar ta daina,ƙirjinta kuwa sai dukan uku uku yake kamar wacce za’a ce ta aikata wani laifi.

Tsakani da Allah tana matuƙar jin kunyar kawunta ko zuwa yayi na wuni ɗaya daga sun gaisa take ta shi ta basu wuri,har yau ta kasa sabawa.

Bata ankara ba taji mama ta janye hannun ta da ƙarfi taci gaba da wayar ta,daga ƙarshe yace“ Baku da matsalar komai ko? Komai akwai ”

“ Alhamdulillah,komai muna da shi, Allah dai ya saka maka da mafificin alkairinsa, Allah kuma ya bar zumunci”

“Ameen ameen,adai ci gaba da haƙuri, Allah yasa mu dace”

“Ameen yah Allah ”

 

Sai da suka gama sannan ta kalleta tace “ Sannu uwata dole ki hanani magana saboda kece kika sayamin wayar….”

 

Shagwaɓe murya tayi tana faɗin “ Wayyo mama,wayyo mama dan Allah! Taya zaki faɗawa kawu wannan maganar? Nifa wasa nike miki”

Dariya tayi tace“ Nima wasa nike miki Asiya ta sha lele ta, Allah dai yayi miki albarka,yi maza kinga lokaci ya tafi kiyi ki tashi kada kiyi latti”

 

“ To mahaifiyata jaruma ta,ina sonki ina ƙaunarki sosai ”

“ Nima haka”

 

★★★

 

Kaduna….

Gidan Alhaji Abdul Rashid Makama.

Misalin ƙarfe goma da rabi na dare,mota ce ƙirar marcedes baƙa wulik a harabar gidan sai walwali take da ɗaukar ido na sabunta,dukkan ilahirin gilasan motar a rufe suke dif da baƙi wanda ake kira da tintek,idan ba anbuɗe motar ba bazaka iya gano miye yake cikinta ba.

Mammalakin motar na gani zaune a ciki sai wata kyakkyawar mace fara ajin farko zaune a gefenshi.

A irin yanayinda na gansu ya tabbatar da suna cike da farin ciki da annushuwa irin na manyan masoya.

Sallar Isha kawai ya gama ya bugo mota yazo, sun daɗe suna firar su ta soyayya yanzu kuma da ya nuna mata dare yayi yana so ya tafi shine take ta ɓata rai wai ita bata so ya tafi domin bata gama ganin shi ba.

Sai wani narkewa take kamar anɗora man kitse a rana.

Daga ƙarshe tsura mata ido yayi yana kallon kyakkyawar fuskarta yace “ Ayrah Please! Ki barni na tafi dare yayi ya kamata kema ki shiga gida yanzu”

 

“ No! No gaskiya nidai har yanzu ban gaji da ganin kaba,ina sonka sosai baby,wallahi ina mahaukacin sonka….”

 

“ i know that,nima ai kinsan abinda yake raina…”

 

“Cike da ƙorafi yanzu take magana da cewa “ Baby haka kake cewa kullum ai ni nasan nafi sonka fiye da yanda kake so na,kuma zan ƙara tabbatar maka da hakan ne idan munyi aure”

 

Yasan halin ta sarai yanzu sai takai safe tana yimishi ƙorafi akan wannan,nazari yake ta ya zai samu ta tafi gida,sai kyautar da yazo mata da ita tazo mishi a rai.

Waigawa yayi bayan motar ya ɗaukko mata ledar yace“ Ga wannan kada ki buɗe shi sai kin je gida”

Cike da zumuɗi ta karɓa tana faɗin “ Thank you so much my Abdallah,I love you ”

 

“I love you too my Ayrah, please kije gida kada Hajiya tayi faɗa dare yayi”

Ji take kamar ta rungume shi,ko kuma ta yi kissing ɗinshi but tasani sarai yanzu idan ta yi zasu fara faɗa ne wanda zasu kai sati basu shirya ba.

Da haka sukayi sallama ta shige gida shi kuma ya fito ya nufi gida.

 

 

 

 

*OUM AMEER*

 

 

 

Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.