Sirrin Rike Miji

Sabbin Kalaman Soyayya na Samari da Yan Mata

Sabbin Kalaman Soyayya na Samari da Yan Mata

 

 

 

 

 

 

 

 

Ga wasu jerin kalaman soyayya masu dadi na saurayi da budurwa wanda zaku iya turawa masoyanku mace ko namiji.

 

Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina.

Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama, amma ba za’a hada son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, ina son ki.

 

A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa ta ke tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a ko da yaushe.

 

Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.

 

Kasancewar ki a tare da ni, ya sa ni jin kaina a matsayin wani mutum mai daraja ta musamman. Ina son ki, so irin wanda kalmomi ba zasu iya bayyanawa ba.

 

Matata Uwar ‘ya’yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki d’aya, ina cike da zumud’in son dawowa domin cin girkin ki mai dad’i. ki kula min da kan ki, sai na dawo. Ina son ki matata.

 

Shin masoyina izuwa yanzu ko ka fara jin gajiya a jikinka kuwa? Saboda ka kasance kana motsi a cikin zuciyata a tsawon dare ka kuma kasance mai zagaya dukkan jikina ta kafar da jinin jikina ne kawai yake gudana a cikin kowace safiya da yini. Ina son ka.

 

Ina son ki zamo mallakina a cikin mafarkina da kuma a zahiri, ki zamanto cikin hirata da sauran dukka zantukan bakina faruwar hakan zai inganta farin cikin zuciyata. Fatana a kullum ki gamsu da cewa, Ina Son Ki.SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d’aure zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin zuciya ta.

 

Soyayyar Aure Ko Iyaye

 

Duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar wace sai ke Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kadai Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni.

 

Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina Kinfita daban a cikin mata.

 

 

kalaman soyayya

 

 

1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!