Sabon fim mai suna Gidan Dambe na dauke da yan wasa 500
AƘALLA ‘yan wasa 500 ne aka tsara za su fito a fim ɗin nan mai dogon zango na ‘Gidan Dambe’, wanda fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) ya ɗauki nauyin shiryawa.
Daraktan shirin, Ilyasu Abdulmumin (Tantiri), shi ne ya bayyana haka a Instagram.
Tantiri ya ƙara da cewa za a fara ɗaukar shirin a garin Katsina a ranar Alhamis, 20 ga Mayu, 2021.
Daraktan ya ce ‘Gidan Dambe’ na kamfanin Rarara Multimedia shiri ne na barkwanci wanda ya ƙunshi “jaruman barkwanci na da da na yanzu”.
Da ya ke bayyana sunayen wasu daga cikin sanannun ‘yan wasan, Tantiri ya ce sun haɗa da Aminu Ali (Baba Ari), Rabi’u Ibrahim (Daushe), Tijjani Asase, Adam Abdullahi Adam (Daddy Hikima), Ayatullahi Tage, da Ɗankuda Kabo.
Tarihin Lawan Ahmad na Izzar So
Akwai kuma Tukur S. Tukur (Ɗandugaji), Auwalu Malam Dare, Bawa Maikanwa, Auwalu Zomuleƙa, Yusuf Baban Chinedu, Shagiri Girbau daSulaiman Bosho.
A jarumai mata kuma an gayyato Maryam Adam (Kiimono), Suwaiba Abubakar (Makauniya), Nadia Adamou, Ikilima Yusuf, Maryam Aliyu (Madam Korede), Hauwa Waraka, Hajara Abubakar (Dumɓaru), Teema Makamashi, Sadiya Umar Sidi, Jamila Umar Nagudu, Hauwa Garba Auta (‘Yar’auta Sabira), Maryam Gombe da Saudatu Othman (Ummi Darling).
Idan kun tuna, kwanan nan mujallar Fim ta ba ku labarin yadda aka tsara yin wannan fim na ‘Gidan Dambe’, har mu ka kawo maku hira da Dauda Rarara da kuma wanda ya rubuta labarin fim ɗin, wato fitaccen marubuci Maje Elhajeej Hotoro.
Leave a Comment