Sabon Salon Gidan Uncle Hausa Novel
Bayan na gama Shiryawa zan fita office sai Amaryata ta fito da shagwaɓa ta rike hannun jakar dake rataye a kafaɗa ta tace “Darling yau a gida zaka zauna kayi min kitso ko” sai na juyo na dubeta tareda dafa kafaɗarta nace ” amaryata kiyi hakuri sai na dawo” cikin lallausan murya tace “to My Dear” na tafi har naje bakin kofa sai naji tace ” HONEY”. Juyowar da zanyi sai tayi min wani kallo mai karya zuciya. Bansan lokacin dana saki jakar dake hannuna ba, nan take nayo kwana, na zauna abakin doguwar kujera nace “zo inyi miki kitson” na ture dan kwalin dake kanta na kama lallausan gashinta ina ja tareda shafawa. Ban ankara ba… Saidai naji saukar Mari,Raassss! na mike a firgice ashe wai mafarki nakeyi, Gemun yayana (Uztaz) da muke maleji a katifa ɗaya na kama inata ja. SADIQ wane irin iskanci ne wannan zaka dinga jamin Gemu ina barci? Yayi ta fada a fusace. Kwana nayi cikin takaici ni ban gama mafarkin ba kuma nasha mari Gwauranta batayi ba kuje kuyi Aure.
: *WASU ‘YANSANDA MASU TSORON MUTUWA***
A wata unguwa ce aka wayi gari aka ga wani akwati a wani lungu wadda ake kokwanton bom ne a ciki inji Sa’ad Khalifa Yakubu (Sky) don haka sai aka garzaya aka kira ‘yan-sanda da sauri.
Da ‘yan-sanda suka zo sai sukayi cirko-cirko aka rasa mai shiga cikin lungun don tsananin tsoro sai D. P. O. Ya tura qaraminsu wai yaje yaga ko zai iya tsayar da bom din kar ya tashi su (dpo) suna daga nesa suna hange.
Qaramin dan-sanda yana kuka yana cewa wallahi yalla6ai ina da iyali da yara qanana a gida da yawa amma zaka tura ni in mutu. Sai D. P. O. Yace yaje ai ba komai don ya sadaukarwa da qasa ransa don za a karrama iyalin nashi idan ya mutu.
Sai Qaramin dan-sandan ya sayar da ransa ya shiga cikin lungun… Yana shiga jikinsa na rawa don tsoro ya bude akwatin sai yaga kudi jibge a danqare a ciki maqil da akwatin. (Ashe wasu 6arayi ne suka sato suka boye a lungun) sai dansandan ya fito a guje yace bom ne ya kusa tashi sai kowa ya hau gudu harda da dpo ogansu.
Da sukayi nisa sai Qaramin dansandan yace wa dpo zai iya qarawa bom din adadin lokaci tashinshi idan za a sami mai iya kawar dashi amma ba zai iya kashewa bane. Sai dpo ogah yace kasan dai ni ogah ne ina da amfani sosai a qasarnan bai kamata inyi ganganci ba, don haka kai kaje ka daukeshi a bayan mashin dinka kaje chan bayan gari ka jefashi a cikin dam don kar ya kashe kowa sai kifaye.
Sai qaramin dan-sanda yace toh shi zai sayar da ransa ga qasarsa nanjeria amma idan ya ku6uta toh yakamata a qara masa muqami zuwa sufeton ‘yansanda, sai yace a samo masa buhu sannan yaje ya dauki akwati ya tafi bayan gari ya juye kudin a cikin buhu sannan ya cika akwati da duwatsu ya jefa a ruwa ya dawo gida ya adana kudinsa shi da iyalinsa ya kudance yabar aikin dansanda ya shiga siyasa har aka bashi muqamin minista har ana masa bodyguard harda ogansa dpo cikin masu kula da rayuwarsa masu tsayawa a bayansa.
*KULA DA LAFIYARKA
(yadda zaka wanke kodarka da kanka)
Ka samo ganyen gauta sai ka wanke dakyau kasa a tukunya mai tsafta kasa ruwa mai kyau ka tafasa kamar na tsawon minti goma sai ka sauke ka bari ya huce sai ka tsiyaye ruwan kasha cikin kofi. Lokaci kadan za kaga yadda zai wanke kodarka ka fitsarar da daskararren gishiri da wasu cututtuka su fita daga jikinka kaji garau.
[27/10, 11:14 pm] +234 708 279 6822: Watarana awani kauye wata bazawara tana da bazawarinta wanda suke shashanci, rannan sai wani daga wani kauyen yazo yace yanasan wannan bazawara. To bayan anyi aure sai yadauke ta yatafi da’ita garinsu. To sai rannan suka hada baki da wancan abokin shashancin nata yace zai yi shigar mata yakawo mata ziyara. ……da yazo sai tace wa mijinta ai kanwar mahaifiyar ta ce tazo sai yayi murna yazo ya gaida ita yaganta kuwa tasha kunshi, sai matar tasa tadau tulu ta tafi rafi debo ruwa…. …… fitarta kedawuya sai mijinta yazo wucewa… Kwatsam….. sai ya ga wannan bakuwa tayi wawan zama sai kau ya ga ashe namijine!…. haba ai sai gogan naka yadau takobi yabi matar nan tasa rafi a guje…. …..ai ko da matar ta hango shi da takobi a hannu sai kawai ta rafka ihu tana sallallami…..-. Sai gogan naka ya dakata yace me kike wa kuka? Sai tace yanzunna aka aiko min wai duk mazan garin mu sun zama mata, matan kuma sun zama maza. .ai ko da gogan naka ya ji haka sai jikinsa yayi sanyi. Sai yace to wacce kika bari a gida ma ta zama…. Sai kije kigani….
Leave a Comment