Hausa Novels

Sadauki omar complete hausa novel

 

 

Bisimillahir rahamanir  rahim.

 

 

*ARASHI*

 

‘kirkirarran labari ne daga ni marubuciyar banyi don inci zarfin wani ko wata ba Wanda yaga yayi dai-dai da yanayin na rayuwarsa to a rashin sani ne.

 

 

*GARGADI DA JAN KUNNE!*

 

Ban yarda wani ko wata ya juya min yanayin labari na ta ko wace siga ba ba tare da izina ne ba ban yarda ka/ ki siyar min da littafi ba duk Wanda yayi d’aya daga cikin biyu na barshi da Allah!

 

 

 

*SADAUKI! OMAR*

 

Kai daga jin sunan littafin kasan ya tsaru zai kuma bada ma’ana Ina ma’abota karatun littafan Hausa kuyi maza Ku garzayo ku samu naku littafin SADAUKI OMAR yazo muku da sabon salo mai sanya Ku nishadi ilimantar wa fadakarwa nishadantarwa duk a cikin wannan littafin babu shakka! Wannan daban yake da sauran!! *SADAUKI OMAR*  Iya sarauta iya mulki tsantsar soyayya muskilanci bakin kishi! Bak’ar gaba! Tsananin jarumta!!! Duk a cikin wannan littafin kar ku sake abaku labari!!!!

 

 

 

Free Pege

 

 

 

 

Masarautar *KANO*

Cikin wata ‘kwaleliyar rana na hangoshi tsakiyar filin motsa jiki ya na sanye da ‘bakar vest had’e da wani bugujejen wando mao dogon madauri vest din ta  matse jikinsa sosai kamar ma taso yi masa kadan saboda yanayin halittar  jikinsa mutum ne murd’adde ‘kakkarfa! Wanda ko daga nesa ka hangoshi zaka shaida hakan wani ‘katon ‘karfe me mugun nauyi yake d’agawa yana saukewa gumi sai yanko masa yake daga ko wace ga’ba ta jikinsa. Duk girman gurin shi kadai ne tsaye daga can sama kuma ko wace baranda ka kalla  mutane ne keyawe da ita suna kallonsa kana kallon fuskokinsu zaka fahimci  jarumtar *Omar* din  na burge su.

 

 

Erotic ideas

 

 

 

Cikin isa da kasaita take tafiya tun kafin ta ‘karaso jama’ar da sukayi dafifi gurin le’kensa suka fara kaucewa suna zubewa ‘kasa hade da sunkuyar da Kansu suna mik’a gaisuwa gare ta, ko kallonsu bata yi ba ta wuce tana ya mutsa fuska wata baiwa na biye da bayanta. Can karshen barandar ta ‘karasa ta d’ora hannayen ta akan ‘karfen tare da rankwafawa jikin ‘karfen tana ‘kare masa kallo. Minti biyu ta d’ago kanta tana jan siririn tsaki!  Ikilima dake tsaye kusa da ita tace”Allah ya taimaki Uwar dakina ko a dauko abun zama ne.”? Girgiza kanta tayi da kyar tace”Kira min Tafida.” Da sauri Ikilima tace”Angama ranki shi dad’e.”

 

 

Can ‘bangaran maza ta nufa minti uku sai gasu tare da Tafida ya zube kasan gurin yana kwasar gaisuwa ba tare da ta amsa ba tace”Je ka kira min wancan Wawan.”! Tafida ya kasa fahimta Wanda take nufi cike da ladabi yace.” Ranki shi Dade ban fahimci Wanda kike nufi ba.” Filin gurin ta kalla  har yanzu yana nan yana abunda yake ta ‘kara Jan tsaki a karo na biyu Cikin ‘yar tsawa tace”Ina na kalla yanzu. “!? Tafida yace.” Filin Hazo!   Kauda kanta tayi ba tare da ta sake cewa komai ba. Tafida ya mike jikinsa a sanyaye ya bar gurin.

 

 

 

Akwai tafiya sosai kafin ya isa inda yake Yana ganin zuwan Tafida yasan akwai matsala saboda ‘ka’ida ne idan yana wannan abun ba’a zuwa gurin har sai lokacin da aka d’iba ya ciki don mai Martaba ba ma har yanzu bai futo ba.   Tafida ya ‘karasa gurin jin babu ‘kwari yace.” Ran SADAUKI! Ya Dade yana ‘karko.”!! Yana cigaba da sama da ‘kasa da dotsen yace.” Ya akayi ne Tafida ka karya doka fa kayi maza ka bar gurin nan kafin mai Martaba ya futo shi.” Yace.” Gimbiya Aysha! Ke kiran ka.” Da d’an mamaki! Yake kallonsa kafin yace.” Ka bar gurin nan kafin ranka ya ‘baci! Tafida yace.” Allah huci zuciyar jarumin maza!! Murmushi yayi yace.” Kaje kace mata ‘naki zuwa idan ta cika Mara kunya ita tazo gurinan.” Tafida yace.” Ayi min afuwa bazan iya fad’ar haka ba zan shirya wata k’aryar dai.” Murmushi yake yana kallon Tafidan lokacin da yake barin gurin  motsa jikinsa yake yana mamakin Yarinyar bai San me yasa ba  take shiga harkasa Sam! Baya shiga sabgarta saboda yanayin halayen ta tunda  tunda yake da sai ya irga iya adadin maganar su amma ya  lura a ‘yan kwanakin nan tana nema ta dunga shiga gonarsa kwata-kwata baya so take kula shi! Amma ta kasa fahimta shi mutum ne Wanda baya daukar raini ko wulakanci dalili kenan da ya killace kansa daga hurumin ta ya lura sai ya taka mata burki sannan zata daina damunsa, mamaki ma yake ko kiran me take masa oho! Shi dai na farko baya daya daga ciki n hadimanta ballanta tace Tsaki kawai yake yaja yana cigaba da aikinsa gefe guda kuma yana tunanin hanyar da zai bi gurin ganin ya yanke alakarsa da ita.

 

 

 

“Gyara kintsi dai! Takawar ka lafiya dan toron giwa.” Muryoyin fadawan sarki ke tashi gurin wannan ya tabbatar min da cewar sarki ya futo filin *Hazo* filin nuna bajinta kenan. Guri ya nutsu duk wata hayaniya da ake gurin kamar anyi ruwa an dauke busa da sarewa ne kawai ke tashi a gurin  daf da sarki zai zauna fadawa kusan su goma masu jajayen kaya suka baza manya-manyan rigunan su suka kare sarki sai da suka tabbatar ya zauna kan kujerar shi sannan ko wanne ya koma gurin tsayuwar sa, daya bayan daya masu rawani suka dunga futowa irinsu galadima Waziri Wambai ko wanne ya zauna gurun zaman shi saman k’atuwar barandar inda suke hango Omar tsakiyar filin cikin kwaleliyar rana yana gwada jarumata shi .

 

 

Wani irin murmushi sarki yake yana Yana kallon Omar jarumatar yaron na mutukar burgeshi da bashi sha’awa yaso ace ‘Daya daga cikin ‘yayan sa na da kwatankwacin irin jarumatar Omar din sai dai kash! Allah ya bashi ‘Yaya lusarai marasa jin magana da gangarewa….. Yarima Faisal yana kallon mahaifin nasa yana sakin murmushi ya lura bajintar Omar din na mutukar burgeshi take yaji wata irin tsanar Omar din cikin zuciyar sa ya lura Sarki na mutukar sonsa duk cikin bayin dake cike da gidan ya fifitashi fiye da sauran Dole ne su dauki kwakkwaran mataki kansa don yana gani sarkin zai iya bashi wata sarautar ko kuma ya ‘yan tashi cikin bayi babban abunda ya tsana kenan a rayuwarsa ya fiso kullum Omar din ya dauwama cikin kaskanci da aikin bauta.!

 

 

Wani irin tsalle yake kafad’arshi dauke da ‘katon dutsen kwanjinsa sai sake murd’ewa yake saboda tsabar jin karfi ya kai ya kawo tsakiyar rana gumi na yanko masa daga ko wacce kusurwa ta jikinsa OMAR kenan SADAUKI JARUMIJ NAMIJI. wannan abun da yake ya dauki hankalin duk Wanda yake gurin Sarki ya mike daga kujerar sa yaje ya dafa barandar gurin yana kallonsa fuskarsa dauke da murmushi na ya bawa bajintarsa, Muryarsa mai cike da kamala da nutsuwa Yace.” SADAUKI! JARUMIN NAMIJI! Kafin kice kwabo duk wanda ke gurin ya amsa da fadin kalmar SADAUKI! JARUMIN NAMIJI!! Zuciyoyin mutum uku a gurin kamar su babbake don bakin ciki da takaici Yarima Faisal ya kalli Galadima dake hakimce kan kujerar sa ya sha kunu tamkar Wanda aka aikowa da mala’kan mutuwa tunda ya zauna a gurin ko motsi yaki yi kawai ya futo ne ma Don yana gudun b’acin ran Sarkin amma da babu abunda zai sanya ya futo ganin ma kaskancin bawa irin wannan. Yarima Faisal yayi ‘kwafa tare da mi’kewa a fusace! Alkyabbar jikinsa ya buge da karfi yana wani irin huci! Ya sauka daga gurin. Gimbiya Aysha kuwa Wani irin takaici ne ya kamata ganin yanda ake wani murna da ihu! Duk akan bawan da ta tsana a rayuwarta tayi alk’awarin sai ta ‘kaskantar dashi gaban bayi da wad’anda suke bashi girma domin ta lura da yanda yake wani isa gami da ji da kai da miskilanci yana a matsayin bawa! In dai tana raye cikin masarautar su babu Wanda ya isa ya bashi girma sai ya ‘kaskanta. Rai a bace itama ta buge alkyabar jikinta da sauri Bayin ta suka take mata baya.

 

 

Kimanin awa guda Omar ya dauka yana wannan Abu kafin Sarki da kansa ya sauka! A nutse yake ratsa gurin har ya isa inda yake tsaye wani farin karamin towel ya dauko ajihunsa ya shiga tsane masa gumin jikinsa Kafin ya kamo hannunsa suka bar gurin…. Take yanayin busar da ake a gurin ta sauya Sarki sai da ya shigar da Omar b’angaran su fadawa na binsu a baya suna Fad’in”Mai Martaba ya Yaba da jarumatar ta SADAUKI JARUMIN NAMIJI kayi godiya guri Sarkinmu Mai adalci.

 

 

Suna isa k’atuwar kofar da zata sadaka da dakunanan bayan masarautar Sarki ya saki hannunsa Omar ya zube kasan gurin yana jinjina hannunsa guda da fad’in Godiya nake Mai Martaba Allah ya ‘kara maka nasara da lafiya mai amfani.” Sarki ya Dora hannunsa a kansa har yanzu fuskarsa da murmushi Yace.”Omar Jarumin Namiji ina alfahari da kai duk cikin bayi na.” Sarki! Na gama maganar shi ya juya da niyyar tafiya manya-manyan rigunansu suka baza suna Fad’in “Gyara  kintsi toran gwiwa gaba salamu baya salamun Mai farar Aniya!!  Omar kansa a kasa sai da ya tabbatar da wuce war Mai martabar sannan ya dago kansa, a nutse ya mike daga gurin ya nufi d’akinsa domin wanke jikinsa Omar ya kasance mutum mai tsananin tsafta da tsantsani.

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

Ma dai dai cin daki ne Wanda yake dauke da karamin gado mai dauke da k’aramar katifa k’arama sai kafet dake shimfid’e a dakin kalar Kore labulayen dake kewaye da dakin ma koraye ne sai k’aramar sif mai murfi  biyu jingina jikin bangon dakin gefe da gefen gadon kananun drowars ne mai dai  dai ta akwai band’aki cikin dakin mai daidaici nan naga ya nufa bayan ya dauki towel mai Dan fadi dake sa’kale jikin hanga  Minti goma ya futo daga bandakin jikinsa daure da towel din sai da na tsorata ganin zahirin hallitar jikinsa  wani irin kakkarfan mutum ne murdadde kai da ganinsa a ido kasan zaiyi karfi fuskarsa na kalla na ganta a had’e kamar bai taba dariya ba ya nufi bakin karamin gadon coco butter naga ya bude yana shafawa a jikinsa ya rufe naga ya dauko karamin Abu sai da na kura ido tukkuna na gane kwalli ne naga ya bude ya zaro tsinken yana dadurawa a idonsa kwayar idonsa ya bude nayi saurin matsawa baya ganin wasu irin idananu lafiyayyu masu dauke da wani irin kwarjini da haiba sun sha kwalli rabad’au! Na sake kallonsa lokacin da yake sake dadura tsinke kwallin cikin idonsa ya bude idonsa tar! Nan na gane Allah yayi masa baiwar kyawu Wanda sai ka tsira masa ido tukkuna kake ganin tsantsar baiwar sa karamin bakinsa kewaye yake da wani irin bakin kashi gazarzar! Da alama yana yawan gyaran fuska ya  wani yadi mai laushi naga ya dauko ruwan Zuma dinki ‘Yar shara ya dauko wata hula irin ta Fulani mai kunnuwa ya sanya kansa wani k’aramar kwalba naga ya dauko cikin drwar ya bude nan na gane turare ne cikin kwalbar ya goggoga a jikinsa ya maida kwalbar ya aje kofa ya nufo da alamun futa nayi saurin kaucewa. Sai naga ya tsaya wuyansa ya shafa naga ya nufi toilet minti biyu ya futo naga yana d’aura Abu a wuyansa nan na fahimci irin abunda yake daure a damtsan sa ne so nake na tabbatar shin menene gani nake kamar laya Oho na kasa gane menene na dai fi ganin masu mulki na d’aura irin shi, ko me ya hada shi da kayan masu sarauta shi da yake ma’kaskancin bawa inji Gimbiya Aysha. Kofar futa ya nufo a karo na biyu nayi saurin matsawa ya wuce na juya da sauri ina kallon yanda yake tafiya kamar zai tsaga ‘kasa.

 

***

 

“Allah ya ‘kara mik lafiya da nasara Uwargijiya ta Allah yaja Zamann ki Gimbiya Aysha d’aya tamkar da dubu sarauniya kyakyawa kike tamkar zinare farar mace alkyabar mata cike kike kin cika da ‘kasaita ba’ayi ba kuma baza’ayi ba insha Allah babu wacce zata kamo ki a fagen kyau da Iya kasanta.”!!  Ikilima kenan dake gurfa ne gaban Aysha take faman banbad’anci ga yabo ga Uwar d’akinta saboda ta lura da yanayin da take ciki na b’acin rai duk lokacin da ta shiga yanayin b’acin rai sai tayi mata irin wannan kirarin take sauraran su.

 

 

Ajiyar Zuciya ta sauke ta Dan gyara kishingidar da tayi a nutse tace” Ikilima yau raina yayi masifar b’aci wallahi.” Ikilima ta sake sadda kanta kasa kafin tace”Allah ya huci zuciyar gimbiya.” Shiru gurin yayi na minti biyar ta mik’o hannu zata dauki apple din dake Jere cikin wani irin ture na silver Ikilima tayi saurin mik’a mata a nutse ta karba ta Dan gutsira tana ya mutsa fuska k’wafa tayi a fili tace”Ikilima wai da me wancan bawan yafi sauran bayin dake masarautar nan ne naga Sarki naji dashi sosai shi kuma na lura yana alfahari da hakan babban abunda ya ‘bata min rai shine bai wuce ganin Sarki da kansa ya sauka filin Hazo har ya goge masa gumin jikinsa Gaskiya raina ya baci da wannan lamarin Ina mutukar jin haushi inga kuna girmama shi kar Ku manta daku da shi duka d’aya ne a cikin gidanan, daga yau sai yau na fad’a miki duk sanda na sake ganin kina bashi girma sai nayi mugun bata miki rai da kaina zan kai ki gaban Sarkin Horo! Ya Zane miki jikin ki shine hukuncin ki.”!

 

 

Ikilima tayi ‘kasa da kanta cike da tsoro da fargaba tace”Allah yaja zamanin ki insha Allah zan kiyaye.”! Tsaki taja ta gutsri apple kadan tana taunawa kamar bata so tace”Dallah tashi kije kice ina kiransa yanzu-yanzu.”! Ikilima ta mike da sauri tana fad’in”Angama ranki shi dad’e.” Da sauri ta futa daga Palo ita kuma ta cigaba da gutsirar tufar tana ya mutse fuska da alama ta saba da hakan tunanin irin kaskancin rashin mutumci da zatayi masa take.

 

 

 

Ikilima na futa ta tsaya tana cizon ya tsaya ya ma za’ayi ta iya tunkarar Sadauki da wannan sa’kon, duk da yake bawa a masarautar amma yafi su yanci ta ko wane fanni kuma a tsakaninsu suna mutukar Shakkar sa gami da girmama shi tana jin nauyi taje tace Wai yazo inji Gimbiya, tunda gaban idonta dazu da Tafida ya kirashi yaki zuwa wannan karon ma tana gani ba zuwa zaiyi ba…….Atika CE ta karaso gurin hannunta rike da wata irin k’atuwar tsintsiyar kwakwa tace.” Ke kuma me kike tsaye a gurin nan tun d’azu.”

 

 

Da sauri Ikilima taja hannunta suka matsa gefe rad’a-rad’a take fad’a Atika tace”Zo muje in rakaki wallahi dama INA so in sake ganinsa ke nifa wallahi da zai aure ni sonsa nake kamar in kashe kaina.”!

 

 

Ikilima tace”Lallai Atika wallahi ki iya bakin ki dube ki don Allah ‘yar gajera dake ina zaki kai ingarman namiji irin wannan ai sai ya kashe ki.””” Cikin jin haushi Atika tace”Aikin banza meye abun ba’a a ciki kin San dai na fiki kyau sai dai ki nuna min tsayi kuma waye yace miki girman namiji na kashe mace ke har yanzu baki san kome ba.”

 

Ikilima tace”Ni kiyi shiru muje mu tsoron masifar gimbiya nake kin San dai halinta.” Tafiya suke suna hirar Omar Atika na sake fad’awa Ikilima yanda take bala’in kaunar Omar din.

 

 

 

 

Dake ko da yaushe gate din gurin a bude yake yasa suna isa suka hango shi can gurin dokuna tsugune a tsakiyar su da alama abinci yake basu….. Yunusa ya hango su ya karaso gurin tare da fadin”Wai kuke nema ne? Kun San dai dokar cikin gidanan mata basa shiga b’angaran maza hakanan maza basa shiga b’angaran mata.”! Ikilima tayi saurin cewa”Dama Gimbiya ce ta aiko mu gurin SADAUKI! Yunusa ya kalli can gefen da yake yace.” Bari in fad’a masa.”

 

 

 

Can ya nufa ya na isa yace.” Omar Gimbiya tayi aike.”! Idanunsa ya d’ago yana kallon Yunusa  da sauri naja baya ganin yanda idanun NASA sukayi wani irin jaza kwayar idon ta kara baki sai shek’i take….. Babu walwala tare dashi yace.” Wacece Gimbiya. “!? Yunusa yace.” Gimbiya Aysha mana ga can bayin ta kofar shigowa don na hanasu shigowa gudun samun matsala.” Kansa ya sunkuyar ya cigaba da abunda yake….. Yunusa yace.” Dad’i na da kai Kenan ka mayar da kanka kayi shiru baka bani amsa ba….. Yana mik’awa doki ruwa yace.” Kace musu nace su ce mata baza’a zo ba.”!! Yanda ya fad’i maganar zaka fahimci a cikin b’acin rai yake. Yunusa yayi jimm! Kafin ya bar gurin ya iske su inda suke tsaye rana na bugun Kansu yace.” Ku fada mata yace.” Yana da uziri.” Suka amsa da “To” duka suka juya domun tafiya

 

6 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!