Hausa Novels

Sadauki Omar Return Complete Hausa Novel

Sadauki Omar Return Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Sadauki Omar Return Complete Hausa Novel

A zahiri kamar cikkaken namiji amma abun kunya kamar ka shekara talatin da uku ba aure ace namiji kamarka mara tsoro mafarauci a dajika! amma a gida malalaci gauro tuzuru wanda ya gaza samawa kansa nutsuwa wannan jarumtar taka a banza tunda baka da aure har yanzu baka cika cikakken namiji ba.

Wata ‘yar tsohuwa ce take wannan maganar,

idona na kai kan wanda takewa surutun ya juya baya jikinsa sanye da kayan farauta ba’kin yadi mai kaurin gaske rigar mai fadi ce iya kafadarsa, ta tsaya iya kacin gwiwarsa sai yayi amfani da wandon jens kafarsa sanye da takalmi mai igiyoyi, bayansa kawai na kalla na gazgata maganar tsohowar, hakika duk inda cikakken namiji yake mai zati da kirar mazantaka to za a sanya guy a ciki dogo ne mai fadin kirji jikinsa a cike a murde babu rama ko ta kwabo a tare dashi, har yanzu be juyo ba da alama akwai abinda yake. Sadauki Omar Return Complete Hausa Novel

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

Tsaki taja tace.” *UMARU* ina magana amma dai yau a gida zaka kwana ko.”?

Ba tare da ya juyo ba yace.” A’a bah! zan kwana a gida ba”!! yanayin yanda yake magana a ciccije sai dana tsorata!. sake ‘buya nayi ina gyara biro da takardar dake hannuna.

Tace.”To koda naji ai gwara dana tambayeka saboda ana magariba zan rufe kofata kaje ka ‘karata.”

Uffan bece mata ba, na hangoshi yana d’aura wasu tafka-tafkan layu a damtsan hannunsa.

Ya dauki wata hula mai kunnuwa ya kwafa akansa kafin ya juyo, saurin sunkuyar da kaina nayi gabana na dukan uku-uku! yana da manyan idanuwa sosai amma sunyi wani mugun jaa! lebansa bakikirin, alamu sun nuna farin mutum ne amma tsabar busa hayaki gami da shaye-shayen magungunan tauri! fatarshi tayi wata irin dabbara-dabbara! Sadauki Omar Return Complete Hausa Novel

Kafin nayi aune! naji ya kurma uban ihu! ya dunkule! hannu kafin ya kalli gabas yamma kudu arewa ya fara yiwa kansa kirari kamar haka.

“Nine *Umaru!* Namijin duniya! mai tarwatsa namun daji! Na d’aya ‘kwal! a gurin uwa da uba! dubu jiran mutum dubu!! naci uwar d’an iska! naci uwar duk wani dan tauri! Ihuuuu!!! Nine Umaru! wanda wuka komai kaifinta bata ratsani! Nine dai Umaru! mai karnuka dari ba d’aya, mai masoya gabas! yamma! kudu! arewa! An buga an barni! naci dubu sai ceto! nayi tawa nayi ta wasu!! Umaru nake d’aga Tanimu jika gurin Uwale! Idan da wanda yake da yaja ya fito don uwarsa.”

Yana maganar yana zazzare ido da ciccije baki sai rarume-rarume yake a dakin. Uwale na ganin ya zaro labceceyar wukar dake rataye a kafadarsa taje gurin tana rirrikeshi, ya tureta gefe, fito da wukar yayi sai sheki take ya fara gurzawa a jikinsa.

Gabadaya jikina in banda kyarma babu abunda yake, yau garin neman labarai na kawo kaina mahallaka, da gudu! na fito daga bayan kyauren nayi waje! ba zan iya ganin wannnan tashin hankalin ba.  Sadauki Omar Return Complete Hausa Novel

A maimakon na kama hanya na gudu,sai na b’uya a bayan wata bishiya ina jiran fitowarsa, kimanin mintina goma ya fito, kallo guda nai masa na sunkuyar da kaina, gabadaya jikinsa kayan farauta ne, kwari da baka, wukake a soke a kowane sassa na jikinsa. Tirkashi ashirye yake na sheda cewa babana Umaru jarumi ne.

Wani irin fito yayi fit-fit! kawai sai ganin karnunka nayi suna fitowa ta bayan gidan, kafin wasu zaratan matasa kamarsa suka biyo bayan karnukan suna sanye da kwatankwacin kayan dake jikinsa.

Sun kai su goma suka zageyeshi kafin su farayi masa kirari! kamar haka, *GOJE!* jarumi a gida jarumi a waje! *UMARUL-FARUK!* ba ka san wargi ba, baka san tsoro ba! baka san wasa ba! kayi taka kayi ta wasu! Namijin duniya tarwatsa namun daji! *Zaki!* uban mafarauta! kaine jagora *GOJE!* Ja muje! Mudubi mai nuna mana hanya.”

Kallonsu kawai yake yana tattauna lebensa kafin ya gyada kansa, A ciccije yace.” Zamu kai sati muna gwagwarmaya ina fatan kowa ya sallami iyalinsa.”

Suka bashi amsa da fadin “Eh ranka ya dade munyi yanda ka umarcemu.”

Hanya kawai ya kama suka rufa masa baya tare da karnukansu dake faman haushi!! duk sun cika unguwar. sawun tafiyarsu kawai kake ji da sautin kukan karnukansu. Sadauki Omar Return Complete Hausa Novel

A daddaure suka shiga da ita motar suka sanyata a tsakiyarsu, kafin direban ya shiga ya zauna, a gaggauce ya figi motar suka fita daga masarautar, yau suna cikin farin ciki bukatarsu ta biya gurin kidnaping din yarinyar da suke sanya ran samun makudan kudi daga gurin iyayenta.

Wani irin nishi! take gumi duk ya jika mata jiki sun daure mata fuska da kyar take jan numfashi, kawai sai ta shiga nanata kalmar shahada watakila ajalinta ne ya sauka a cikin wannan dare.

Da yake dare ya tsala shiyasa motar ta samu sararin sharara gudu yanda ranta yake so,

Wani irin wawan burki motar taci! ji kake kuuuuuuu!! kafin ta gangara can gefe guda tana watangaririya!

Da azama! ya isa gurin jama’arsa na tare dashi, yayin da gurin ya cika da kukan karnuka abunka da dare!

Motar dake watangaririya ya durfafa! babu tsoro a tare dashi yasa kafarsa ya daki murfin motar, cikin ikon Allah ta bude, a take suka fara rige-rigen fitowa, lokacin da sukayi arba dashi suka tabbatar *Makashinsu* ne sai gudu! radada! direban kuwa kafin ma ya samu nasarar fitowa motar ta kama da wuta!
Tana kwance! magashiyan! ko ina na jikinta a daure! wucin wutar ya kama gefen zaninta! ta rasa yanda za tayi sai ta fara jan jiki tana gurnani!

Allah yayi masa ji! da sauri ya juyo yana haska gurin da wata katuwar fitila, da sauri ya mikawa daya daga cikin yaranshi fitilar ya sunkuya ya dauketa, a kafada ya sa’bata, wutar na cin gefen zaninta cinyoyinta wasu guraran duk sun kone! sai da sukayi nisa da wutar ya kwantar da ita kan ciyayi, gabadaya yaran sukayi masa rumfa karnuka sai ihu! suke a gurin suna zagaye.

Ya dago jajayen idanuwansa da fadin.” Ku matsa a gurun.” Da sauri suka watse!

Da hannu ya bubbuge sauran wutar dake jikin zanin.

Ya janye idonsa daga kan cinyoyinta da suka fito waje, tsigar jikansa ta dinga tashi, ya jima kafin ya sake kallonta, hannu yasa ya kwance zanin ya jefar ya fizge siket din da duk ya manne da fatar jikinta, Ido ta runtse! tana jin wani irin azabar zafi har tsakiyar kwakwalwarta.

Yayi saura daga ita sai wando, (pant) Fuskar nan babu walwala ya fara kwance mata daurin fuskarta, suka had’a ido, kuri! tayi masa yana gama kwance mata daurin bakinta, ta samu sararin d’aga hannu a zafafe! ta nufi fuskarsa zata gaura masa mari!

Da azama! ya rike! hannun murdeshi yayi da karfin gaske! yatsun suke bada sautin qararas!! lokaci guda ta shiga nutsuwarta, ya saki hannun ya dinga jale-jale! da alama wasu yatsun sun samu Matsala.

Zafafan hawaye suka dinga karakaina a saman fuskarta, tana kallonsa tana kallon cinyoyinta da suke waje muraran!

Ihu! ta kurma! ta nunashi da hannu da fadin.” Ni *Gimbiya Zinat* zaku wulakanta me kuke bukata? wanda masarauta ta gaza yi muku! wallahi sai kun gane kuskuranku.”!

Jajayen idanuwansa ya zuba mata, kafin yaja dogon tsaki! ya mike tsaye yana gyara kayan farautar dake jikinsa! da azama tayi nufin mikewa! azabar quna yasa ta koma ta zauna hawaye na cigaba da gudana a fuskarta.

Fito yayi alamun yana kiran yaransa, aikuwa kafin kiftawa da bisimillah sun kewayeshi har karnukan, ba tare da yace komai ba yayi gaba, suka rufa masa baya.

Hannu ta d’aga da fadin.” Kada ku tafi ku barni a wannan dajin ku mayar dani gaban iyayena.”!!

Babu wanda ya saurareta a cikinsu sai sauri suke suna taka ciyayi tare da ratsa itacuwa.

Cikin dauriya ta mike tsaye! tasa hannu ta lalubi tsommokaran da suka daure mata fuska, ta daura a jikinta hanyar da suka bi ta kama tana tafiya tana waiwayen bayanta, bata iya addua ba ballanatana tayi domin ta kare kanta ita a inda tafi kauri rashin kunya girman kai izzah! isa! jiji da kai maganar abinda ya shafi addini bata san komai ba tafi karfi bangaran boko gami dabin dabi’ar ‘ya’yan nasara.

 Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Sadauki Omar Return Complete Hausa Novel]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

3 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!