Saifudeen Complete Hausa Novel

Saifudeen Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Page«» 1*

_Kuka yake sosai gurfane a gun wani kabari,wanda yanayin kukan nasa ze tabbatar maka cewa haqiqa yayi babban rashi,musamman yanda idanuwan sa suka kumbura sukayi wani irin jajur ta yanda duk wanda ya kalle sa dole se nashi idanun sun ciko da qwallah sbd tausayi_.

_A nn gurfanen da yake ne wani yazo shima se kukan yake ya tada shi ya rungume shi sosai a jikin sa,se rarrashin sa yake yana bashi magana,amma sam ya kasa daina kukan har se da yaja shi suka fita daga maqabartar_.

 

*Baya Kafin faruwar hakan*.

««»»»«»»

Tsaye yake gaban mirror d’aure da farin towel a qugunsa yana taje sumar kanshi,wanda kallo d’aya zaka mishi kasan cewa hadadden guy ne shi,first class da sam bai aje kanshi kusa ba.

Sosai yake matuqar ji da kanshi sbd Allah yayi shi me tsananin kyau tamkar shi yayi kan shi.

Shiyasa sosai kyawawan en mata ke rubibi akan sa amma sam baya kula su,mace d’aya kawai yake kulawa wato “Sophie”wata classmate d’isshi da sukayi karatu tare a London wacce yanzu haka tana nn Nigeria ta biyoshi.

Bayan ya gama taje sumar kanshi ne ya tafi da cumb d’in yana qara kwantar da sajen fuskar shi dake kwance luf kan farar fatar shi tas wacce tamkar ka kwanta jini ya fito.

Sai da ya feshe jikin sa da body spray snn ya nufi kan bed inda ya ajiye kayan sawar shi da ya ciro,ya zauna tare da cire towel d’in jikinsa ya cillar gefe,ya janyo guntun wandon sa fari qal ya saka snn ya saka dogon wandon sa na suit silk fari,rigar ciki baqa yayi stocking da black belt,ya saka necktie fari,sucks baqaqe da takalmi baqaqe snn ya saka er samar shi fara,ya fesa turare kana ya d’auki briefcase d’issa ya fito bai zarce koina ba se 6angaren iyayen shi.

Ya sami mahaifiyar tashi ta fito daga kitchen tana jera breakfast kan dinning.

A natse ya gaida ta fuskar sa ba yabo ba fallasa,byn ta amsa yace am going.

Da sauri ta kalle shi tace”breakfast fa gashi har na kammala had’a komai ka d’an tsaya mana kaci ko kad’an ne”

Yace”No umma ina sauri ne”

Ba tare da ya jira me zata ce ba yasa qafa ya fita abin shi.

Ta bisa da kallo kawai tana mamakin yau ko Abban sa bai je ya gaida ba ko lafiya,nan se ga Abban na shi ya fito cikin shirin sa tsaf na fita,ta kalle sa tace kaddai kaima fita zakayi hakan nn baza ka ci komai ba kmr yanda saifuddeen ya fita.

Komai be ce da ita ba se d’an murmushi yayi had’e da girgiza kansa a lokacin da yaji tashin motar saifuddeen,kana ya qarasa gun dinning yaja kujera ya zauna yana fad’in”Halan me saifuddeen yace maki da zai fita?

Umma da ta janyo plate zata fara serving nashi tace”ce min yayi sauri yake”

Abba yace”haka dai ya gaya miki amma ba wani sauri da yake da akwai dalilin da yasa baya so mu had’u”

Umma tace”shi saifuddeen d’in?

Yace”shi d’in yaron da ko kad’an baya so in masa zancen aure amma jiya se gashi na ganshi da wata baturiya a office d’inshi yanda na gansu abun takaici matsayin sa na musulmi yana biye mata kan lalaci irin nasu na turawa.

Numfashi umma ta fitar snn ta zauna a hankli tana kallon Abba wacce da alama tasan saifuddeen na tare da Sophie ba yau ba amma se tace “kana nufin yanzu saifuddeen duk jiji da kanshi yana kula en mata.

Abba yace”Hm Mamn yusra knn ae duk namijin da kika ga baya kula mace to ba lafiyar sa qalau ba,amma irin kulawar da ake so shine namiji ya nemi mace da son aure ba irin shirritar da naga saifuddeen ya d’auko da wacce sam aure bazai ta6a shiga a tsakanin su ba,dan haka wlh sam bazan yarje masa wnn shashan cin ba,ni aure zan masa ko yana so ko baya so!

Yana kaiwa nn ya fara cin abincin da umma ta zuba mishi.

Umma dake kallon sa tayi shiru bata sake cewa komai ba,se abinci ta zubawa kanta ta fara ci cike da tunanin yanda zata shawo kan saifuddeen ya rabu da Sophie,dan ko kad’an bata son huld’ar sa da ita shiyasa ma bata so Abba yasan da ita ba.

 

Se da yamma liqis saifuddeen ya sake dawowa 6angaren su umma,sanye da qananun kaya a jikin sa,rigar fara ce tas me guntun hannu,rubutun jikinta baqi ne manya da aka rubuta *Being human*,wandon kuma fari ne tas tree quarter wanda duk da cewa fuskar sa ba annuri amma yayi matuqar kyau se qamshi ke fita a jikin shi sbd mutum ne shi da sam baya wasa da turare yana son qamshi sosai a rayuwar shi,shiyasa jinin sa ya had’u da Sophie dan haka take itama ko yaushe cikin qamshi take.

Umma dake zaune kan doguwar kujera hannun ta riqe da littafin addu’o’i ta kafe idon ta a kansa har ya qaraso ya zauna a kusa da kujerar da take zaune,still fuskar nn tasa ba annuri ya kalle ta yace”umma i will back to England”

Umma tace”meyasa?

Yace”kmr yanda suke buqata”

Tace”kmr ya u mean zaka kar6i tayin su ka koma can da aiki ka bar asibitin mahaifinka saifuddeen?

Yace”eh”

Da mamaki tace”why?

Muryar sa a hnkli can ciki yace”Abba yasa min ido umma ni kuma bana so”

Umma ta numfasa tace”saifuddeen knn idan Abban ka bai sa ido akan rayuwar ka ba to wa kake so ya kula da rayuwar ka ya nuna maka hanyar da ta dace kabi iye”

Shiru yayi kmr beji me tace ba taci gaba da cewa”saifuddeen kaifa musulmi ne bai kamata dan kayi karatu a qasar turawa ba kazo kana yin irin halayen su marassa kyau snn kuma a maka magana kaji haushi,ka sani fa ko kad’an Abban ka bai ji dad’in yanda ya same ka office kaida Sophie ba dan nasan ba makawa ita ce ya ganku tare tunda yace min baturiya.

A qufule yayi d’an guntun tsaki yace”umma bafa wani abu ya ganmu munayi ba fa,just ya samu tana kan laps d’ina muna magana shine kawai se ya balbale ni da fad’a wai kar ya qara gani na da ita,wat kind of this umma.

Umma dake kallon sa tace”Hum Saifuddeen yanzu kai a ganinka ba komai bane Abbanka ya ganka da mace kan qafafuwan ka,saif ae ko matar ka ce dole ka d’anji kunya bare Sophie wacce…..dafe kansa yayi sbd mgnr ta ishe shi,yace”umma plz a daina zancen nn haka is enough ni yunwa nake ji tun safe banci komai ba”

Ba yanda umma ta iya se ce masa tayi olryt me kake so kaci?

Yace”abu me d’an nauyi da zan iya ci.

Nan umma ta tashi a hnkli taje gun dinning wacce dama ta kammala girkin ta na yamma,ta d’ebo masa,tuwon semo ne da miyar agusi wacce taji naman rago sosai tayi kyau har ta gaji se qamshi ke tashi,ta had’o mishi ruwa da lemu ta kawo mishi ya kar6a tare da mata godiya snn ya fara ci.

See also  Iffah ko Hibbah Hausa Novel Complete

»»»

Da dare umma da Abba suna zaune a falo suna kallon labarai,Abba ne saman kujera umma kuma tana zaune a qasa manne jikin kujerar yayinda wata yarinya da bazata wuce shekara biyar ba wato wacce ake kira da yusra tana kwance kan qafafuwan ta tana bacci,umma na fmn shafa jikinta a hankli.

Abba yayi gyaran murya yana me kallon umma yace”Maman yusra wata magana nake so muyi”

Umma ta kalle sa tace”tou Allah yasa ba wani abu bane Alhj”

Yace”ba wani abu bane so nake ki amince na had’a auren saifuddeen da zarah.

Umma ta numfasa tace”cabd’i Saifuddeen da zarah fa kace Alhj?

Yace”Eh haka nace ko anyiwa zarah miji ne ban sani ba?

Aa ae kasan baza ma a fara ba baka ji ba amma dai kasan sam saifuddeen bazai ta6a yarda ya auri zarah ba ko.

Abba yace”Zarah bata da wani aibu da saifuddeen zai ce bazai so ta ba tunda gwargwado dei tayi karatu har gaba da primary”

To Alhj kasan fa zarah gabad’aya a qauya tayi rayuwar ta zuwan ta birni jefi jefi ne.

Abba yace”ae shiyasa nace ta dawo nn da zama dmn ki wayar mata da kai,na kuma sata a university taci gaba da karatu sannu sannu har su zo su saba ita da saifuddeen kafin nasa lokacin auren su.

Umma tace”gaskiya Alhj kawai da ka bashi za6i ya kawo wacce yake so dan bana tunanin saifuddeen ze ta6a sakarwa zarah fuska har sukai ga sabawa da juna bare har ace aure ya shigo tsakanin su abun da kmr wuya.

Yace”Maman yusra ba wani za6i da zan bashi Zarah nake so ya aura,dan haka abunda kawai nake so dake shine gobe ki shirya kije Rimin dako kizo da Zarah in yaso se kiyiwa inna bayanin komai nasan in taji baza ta qi ba inshaa Allah,ban sani ba ko dai ke ba kya son Zarah ta auri saifuddeen ne.

Umma tace”ba haka bane Alhj ae Zarah in taji nasan ba qaramin farin ciki zatayi ba dan dai sosai tana son zaman birni,a duk lokacinda naje ji take kmr ta biyoni.

Yace”to ai duk kece tun tana qarama ba yanda banyi ba kan tazo nn tare damu ta zauna kika qi alhali yarinya naso.

D’an murmushi umma tayi tace”uhm Alhj knn ae de yanzu komai ya wuce Allah ya nuna mana gobe lafiya se inje inzo da ita d’in”

D’auke da murmushi Abba yace “Amin ko ke fah”.

«»»««»SAIFUDDEEN«»»««»

 

By

*Billy giro*

 

*Dedicated to»»»Zarah gwandu*

 

*«»Page«» 2*

Washe gari tun da safe guraren qarfe 7 na safe umma ta kammala shirin tafiyar ta ita da yusra,driver yaja su suka tafi garin Rimin dako wato wani kauye dake cikin karamar hukumar 6agwai dake nan cikin jihar kano.

 

Awar su biyu kan hanya snn suka isa garin.

 

Gida ne d’an qarami suka paka motar su a gun,umma ta shiga daga ciki janye da yusra a hannunta ta sami wata yarinya da bazata wuce 17 yrs ba tana duqe a gaban murhu tana hura wuta da iskan bakinta,wacce tana ganin umma tazo aguje ta rungume ta cike da murna tana fad’in”oyoyo innan bunni shannun ki da zuwa”

Kasancewar su Fulani ne Hausar su bata bi dede ba.

Umma dake kallonta d’auke da murmushi tace”Yauwa Zarah ina mutan gidan suke ne naji shiru kmr ba kowa?

Zarah da ta kama hannun yusra washe da baki tace”eh kawu baya nn yaje gurin kiwo,dije kuma taje d’ibar ruwa(cewa da er kawunta wacce suke tsara)

Taci gaba da cewa mama asabe (wato mahaifiyar dije) yanzu ta siga bayi,inna kuma cewa da kakarta tana daga shiki kindirmo take damawa.

Murmushi umma tayi zasu qarasa daga ciki Zarah ke tambayar ta”Nusaiba fa naga yusra kawai aka zo da ita”

umma tace”eh Nusaiba bata nn tana Kaduna ta kai musu hutu.

Ta qarashe mgnr ne dai dai sun shigo d’akin inna,wanda d’an d’akine da aka yishi kmr bukka se mutum ya duqa yake iya shiga.

Wacce ake kira da inna tana zaune a tsakar d’akin qwarya a gabanta tana dama kindirmo kmr yanda zarah tace.

“A’ah Maraba maraba da mutan birni yau kune a garin?

cewar inna wacce tayi maganar ne washe da baki tana kallon umma.

Yayinda umma ta zauna kan d’an qaramin gadon karan da ke cikin d’akin tana fad’in mune inna ya muka same ku.

Tace”lafiya lau ya mutan birni kowa lafiya?

Duk suna lafiya Alhj ma yace a gaida ki da jiki da kuma lafiyar qafafu.

Inna tace”wlh Alhmdlh jiki yayi sauqi qafafu kuma se sauqi suke tunda na fara shafa wnn maganin da kika kawo min kwanaki.

Tace”to Allah ya qara sauqi inna”

Inna tace”Amin yayinda take kallon yusra wacce tazo gurinta d’auke da murmushi ta zauna kusa da ita tana kallon yanda inna ke dama kindirmo,inna dake kallonta tace”ko kin iya in baki ki qarasa damawa”

Da sauri yusra ta gyad’a mata kai alamar eh,inna ta lakaci hancinta cikin yanayin wasar jika da kaka tace”to naqi d’in salon ki mana dagwalgwale mu kasa sha.

A shagwa6e yusra ta kama ludayin ita se inna ta bata ta dama.

Umma dake kallon su tayi murmushi bata ce komai ba se kallon d’akin take sam bata son ganin d’akin nn haka,so take taga komai na zamani a ciki,wacce tuni ba yanda bata yi ba kan inna ta bari a gyara musu gida a sauya musu komai na zamani amma tace a’a ita bata son rabuwa da abubuwan gado.

Inna ce ta katse mata shirun da cewa”ni kuwa ina Nusaiba?

Umma ace”ae Nusaiba tana Kaduna ta kai musu hutu”

Inna tace”Ayyo wnn karon bamu keda hutun ba knn,to fad’ima je kawowa innar ki ruwa mana tasha.

Karin wasu littafai da zaku so

Umma tace”Aa inna ni bana jin qishi kindirmo de zan sha snn tare nike da audu driver yana waje a qofar gida Zarah d’auko kwanon shan ruwa a zuba masa snn ki d’auki tabarma da ruwa a kofi ki kai masa kafin a gama abinci naga yanzu aka d’aura.

Nan Zarah ta d’auko kwanon shan ruwa me kyau me marfi da kuma silver cup shima me marfi,taje waje ta d’auraye ta kawo ma inna kwanon shan ruwan ta ajiye snn ta nufi lungun ganbu riqe da kofin silver da akwai randa a lungun gambu nn cikin d’akin,dake d’auke da tsafta taccin ruwan dad’i da aka killace dan ruwan sha kawai,ta d’ibar mishi ruwan snn ta d’auki kindirmo da inna ta zuba mishi ta d’aura kwanon aka,ta fita riqe da sabuwar tabarmar da ta d’aukar mishi da kuma ruwan da ta d’ibar mishi a cup.

See also  Download Forbidden Love Hausa Novel

Nan umma ke snr da inna dalilin zuwanta.

Sosai inna taji dad’i wacce ba musu ta amince da zancen dan ita farin cikinta ne jikarta tayi aure birni.

Koda zarah ta dawo aka snr da ita har tsallen murna ta dinga yi zata koma birni da zama,se dai ba’a gaya mata cewa aure za’a mata ba idan an kwan biyu.

 

Bayan sllr la’asar

tuni Zarah ta kammala had’a komai nata na tafiya har ban kwana taje tayi da en uwa da abokan arziki.

Da zasu tafi har kuka dije tayi zainab zata tafi ta barta.

 

Koda suka isa kano se kiraye kirayen sllr magrib ake,kae tsaye umma ta kaita d’akin da zata zauna wato d’akin Nusaiba.

Byn sunyi sllh umma ta kaita gurin Abba suka gaisa.

 

Washe gari da safe umma da kanta taje ta kira zarah suzo suyi breakfast,suna tafe kafin su qarasa gun dinning ta nuna mata saifuddeen dake zaune shi kad’ai kan dining yana cin breakfast d’insa.

(dan shi haka yake idan yana jin yunwa baya iya jiran kowa)

Tace yayanki ne in munje ki gaida shi amma fa baya son surutu dan karki jashi da srt yaji haushin ki.

Zarah tace”to,amma waye si da baya son srt inna,ko sine wannan da keyin karatu a waje?

Tayi mgnr ne tana mae kallon umma”

Umma tace mata”eh shine”

Tace”inna ya ma shunan si ni mantawa nake?

Shiru umma tayi bata bata amsa ba sbd sun qaraso gun dining se jawo mata kujerar da ke dubin saifuddeen tayi,ba musu Zarah ta zauna kmr yanda umma ta mata nuni,wacce tana zama ta karkatadda kanta tana leqen fuskar saifuddeen da kansa ke duqe gabad’aya hankalin sa na gun cin abinci bai ko ji motsin isowar su gurin ba,se jin mgnr ta yayi kmr daga sama tace”hai shannun ka ka tasi lafiya,fad’ima shuna na kaifa ya shunan ka”

Da saurin sa ya d’ago sexy eyes d’insa yana kallon ta fuskar sa a yatsine,a ransa yana mamakin wnn abar fa daga ina!

Zarah da ta saki baki still kanta a karkace se kallon sa take tayi,a ranta tace”Aradu sina da kyau wnn”

Se gashi mgnr ta fito a fili

Saifuddeen dake kallon ta cike da tsana yace”of course!but to hell wit u mayya!mtsw!yayi tsaki tare da kallon umma yace”umma where did u get this abar,wata iri da ita haka tazo ta zaunawa mutane kan dining kuma kin barta baki koreta ba.

Kallon sa kawai umma tayi bata ce mishi komai ba,haushi duk ya cika shi yana kallon Zarah se duk yaji abincin ma ya fita ranshi nn ya ture plate d’in abinci gefe ya d’auki ruwa a cup yakai bakin sa,nn se ga Abba ya qaraso shida yusra janye a hannun shi wanda kai tsaye ya nuna Zarah yace da saifuddeen ka sani wnn da kake gani er uwar ka ce!

Ba shiri saifuddeen ya furzadda ruwan da yasa a bakin shi be riga ya had’iye ba,kmr yaga kashi fuskar sa a ya mutse ya nuna Zarah yace”haba Abba wnn ce er uwata wacce ko er aikin gidan nn bata isa ta zama ba se dai ko mabaraciyar kan titi.

Kul!

Cewar Abba wanda a fusace yace”kar in koma jin wnn kalmar ta fito a bakin ka,Zarah er uwar ka ce ta jini ko kana so ko baka so.

Shiru saifuddeen yayi yana kallon Abba kana ya ajiye cup d’in da ke riqe a hannun shi ya bar gurin cike da jin haushin yanda Abba ya alaqanta shi da Zarah dan shi sam be yarda akwai wata alaqa shida ita ba,kawai de Abba ya fad’a ne dan ya 6ata masa rai.

Jiki sanyaye Abba ya zauna ya kalli umma wacce tayi saurin d’auke idonta akan shi nn ya maida duban sa gun Zarah yace”kiyi haquri Zarah halin saifuddeen ne se shi kuma be san waye ke ba shiyasa”

Muryar ta a hnkli can ciki da alama taji zafin yanda saifuddeen ya mata tace”ba komai Baffa”

 

Nan sukayi breakfast har suka gama ba wanda ya sake cewa uffan.

Suna gamawa Abba ya fita shida yusra acewar zasu je granny house kasancewar yau weekend ne ba aiki.

 

Saifuddeen kuwa yana zuwa d’akin sa kae tsaye kan sofa yaje ya zauna ya dafe kansa idanuwan sa a rufe,Zarah kawai yake gani,a ransa yana mamakin ina umma ta kwaso ta da har ake alanqanta shi da ita ace wai er uwar sa ce ta jini wacce kaf dangin su yasan babu kucaka irinta.

Lallai idan har er aiki ce aka kawo zai yi maganin abun dan bazai ta6a barin ta ta zauna gidan ba,se dai a nemo wata da ta cancanci zama er aikin gidan.

[4/22, 12:42 AM] Paexer: _Monday/05/02/2018_ *«»»««»SAIFUDDEEN«»»««»*

 

By

*Billy giro😊*

 

*Dedicated to»»»Zarah gwandu*

 

*«»Page«» 3*

Tun daga lokacin saifuddeen bai sake komawa 6angaren ba har se a washe gari snn,koda yazo ya sami driver ya sauke su umma knn sun fito daga anguwa gurin tela sbd sabbin d’inkunan da za’a ma zarah.

Yana tsaye hannayen sa duka cikin aljifan wandon sa,da suka qaraso zarah ta duqa har qasa tana gaishe shi yayi kmr be jita ba ko gefen ta ma yaqi ya kalla se umma yake ma sannu da zuwa wacce ta amsa tare da nuna mishi Zarah dake durqushe still bata tashi ba tace”baka ganin Zarah na gaida ka”

Kallon Zarah yayi tare da dalla mata uwar harara ae kuwa ta tashi sum sum ta wuce ya bita da wani irin kallon tsana.

Umma ta girgiza kanta d’auke da d’an murmushi tace”saifuddeen wai meye aibun Zarah ne,naga ni banga wani abun nuna qyama a gare ta ba jiya jiya da fara ganin ta duk kabi ka d’aura mata karan tsana”

Fuskar sa a yatsine kmr umman ce Zarah yace”kawai umma ni bata min ba,i dnt wnt see her any more,plz ki nemo wata er aikin da ta cancanci zama a gidan nn not dis one”

Umma dake kallon sa tace”saifuddeen ka daina kallon Zarah a er aiki ita ba er aiki bace fa”

Yace”to waye ita?

Tace”very soon zaka san wace ce ita”

Daga haka taja hannun yusra suka wuce ba tare da ta jira me ze ce ba,

“very soon”

ya fad’a yana me kallon ta har ta shige.

In a shrug way ya kad’a kafad’un sa yayi gaba.

Umma kuwa tana shiga kae tsaye d’akin Nusaiba ta nufa gun Zarah,ta same ta zaune kan bed kanta qasa,ta qarasa gurinta ta zauna tare da dafa ta.

Zarah ta d’ago ta kalle ta idanuwanta cike tap da qwallah tace”inna ni bazan sake gaida shi ba tunda baya so”

Umma tace”No Zarah yayanki ne kiyi haquri kici gaba da gaida shi kinji”

Muryar ta kmr zata fashe da kuka tace”to inna baya so fa”

Umma tace”halin shi ne haka amma idan kika ci gaba da gaida shi ze daina kinji”

Tace”sikenn naji zanci gaba da gaida shi d’in tunda kince,yause ne Nusaiba zata dawo to?

See also  Waziri aku sai bango ya tsage

Umma tace”ae nusaiba na jin kinzo ta fasa qarasa hutun ta acan tana nn dawo wa jibi jibin nn inshaa Allah,idan ta dawo zan baki kud’i ta rakaki kasuwa ki siyo kayan kwalliya dama sauran abubuwan da kk buqata ko”.

D’auke da murmushi Zarah ta gyad’a kai cike da jin dad’i zata zama er bunni ga sabbin d’inkuna za’a mata snn kuma za’a je da ita kasuwa ta siyo kayan kwalliya,lallai kuwa zata yi ja gira tayi kwalliyar en bunni,in ma dan qauyan cin ta ne saifuddeen ke nuna mata tsana ko gaisuwar ta baya amsa to ze daina.

 

Bayan kwana biyu da faruwar haka ne Nusaiba ta dawo wato ‘ya ga umma wacce bazata wuce 15 yrs ba,amma kasancewar girman jiki ne da ita zaka d’auka shekarun su d’aya da Zarah dan ta cimma Zarah da komai.

 

A washe garin rnr da Nusaiba ta dawo ne umma ta basu kud’i su tafi kasuwa.

Nusaiba tayi kwalliyar ta acan acan ta zamani ta kuma yi kyau sosai dan ta iya kwalliyar kuma kwalliyar na mata kyau.

Zarah kam powder kawai ta shafa a fuskar ta se kwalli da red lip-stick da tasa a lips d’inta, dan tunda taga kwalliyar da nusaiba tayi tasan in tayi tata kwalliyar tantagaryar baqauya zata fito,amma duk da haka se tayi kyau hasken ta ya qara fitowa sosai sbd fara ce sol.

Gudun kar ta saka kayan da basu dace da fitar birni ba tace da Nusaiba ta za6ar mata kayan da zata sa,Nusaiba kuwa ta za6ar mata wata atamfa Holland ja da akayi zanen manya manyan leaf a jikinta milk in colour,ta had’a mata da wani hijab milk me hannu da ta gani a cikin kayanta da bazai wuce iya guiwa ba.

Ita kuma ta shirya cikin black arabian gown snn tayi rolling da d’an kwalin arabian gown d’in.

 

Koda suka fito garin luf luf dashi ba rana se iska me dad’i dake ta kad’awa.

Saifuddeen na zaune a farfajiyar gidan can kusa da flowers kan kujerar shan iska shida wani abokin sa da sukayi krt tare,ipad a hannun shi da alama wani abu yake dubawa ta yanda yake scrolling da ‘yan yatsun sa.

Tare Nusaiba da Zarah suka gaida su,abokin ne ya fara amsa musu,saifuddeen kuma gaisuwar Nusaiba kad’ai ya amsa wato ya amsa gaisuwar ne had’e da kiran sunan ta har yana tambayar ta ya mutan kd tace mishi lafiya qalau.

Bayan sun wuce abokin nasa ke cewa”A ina kuka sami fine yellow girl like nucy?

Ba tare da Saifuddeen ya kalle sa ba yace”ae Nusaiba d’in ce baka gane ta ba?

Abokin sa ya kalle sa had’e da girgiza kansa yace”ae kasan wacce nake nufi tafi nusaiba haske wnn d’ayar da kaqi amsawa gaisuwa@Fulani girl”

Still Saifuddeen be kalle sa ba se ta6e bakin sa da yayi had’e da fad’in”oho ni ban san a ina aka samo ta ba”

Ae da ganin ta er uwar ku ce kan yanda kuke kama kaida ita.

Abokin nasa ya fad’a.

Saifuddeen ya tsaya cak da abunda yake tare da sauke qafar sa dake kan d’aya yana kallon abokin nasa da fuskar sa da ta sauya lokaci d’aya,ya nuna kansa da yatsa cikin muryar 6acin rai yace”ni d’in zaka ce wae munyi kama da wnn abar!

Abokin nasa yayi dariya tare da dafa shi yace”wnn abar fa kace to maida wuqar ni da wasa nake maka,kawai so nake inji wace ce?

A fusace Saifuddeen ya buge hannun abokin nasa ya kuma nuna sa yace”to wlh kar ka sake min haka jamil bana so”

A hnkli jamil d’in yace”to naji yi haquri gaya min wace ce?

Tsaki Saifuddeen yaja ya tashi ya bar gurin dan jamil ya gama 6ata masa rai shida yau yake jin er fara’ar sa amma jamil yazo ya 6ata masa komai.

Jamil ya bisa da kallo d’auke da murmushi har se da ya daina ganin sa snn ya girgiza kansa yace”hm Saifuddeen halinka se kai”

Nan ya tashi yaja motar sa ya bar gidan cike da tunanin sanin wace ce Zarah dan shi haka kawai yaji lokaci d’aya tayi mae,lallai bazai yi qasa a guiwa ba da wuri ze bayyana soyayyar sa gare ta bazai tsaya zurfin ciki ba ya rasata kmr yanda ya rasa Nusaiba aka riga shi.

Dan yaso Nusaiba sosai amma ko Saifuddeen bai ta6a gayawa ba bare Nusaiba.

*«»*

Bayan sun dawo da kasuwa Nusaiba ce zaune a d’akin umma,umma na duba kayayyakin da suka siyo kayan kwalliya ne da turarukka se inner wears da kuma kayan bacci kala biyu.

Nusaiba dake danne danne a waya tace”umma ashe dama yaya saif yana nn?

Umma tace”eh yana nn me ya faru?

No umma ba komai kawai na d’auka ko yayi tafiya ne naga tun jiya da safe dana dawo bangan shi ba har se d’azun da zamu je kasuwa.

Umma tace”to ai kinsan halin yayan naki ba kasaifai yake shigowa 6angaren nn ba se cin abinci ke kawo shi ko kuma idan ze fita,kwana biyun nn ma ko cin abinci ya daina shigowa se idan ta mishi dad’i.

Nusaiba tace”hm yaya saif manya ne zanso inga mtr da zai aura dan nasan se ya darje ya za6o dai dai dashi”

Murmushi umma tayi tare da fad’in yayanki da baya ko son a masa zancen aure wai bai tashi ba tukuna.

Tace”to umma may be gimbiyar tasa na can waje tana karatu ita yake jiran se ta kammala tukun musha biki.

Murmushi kawai umma tayi bata sake cewa komai ba.

Se duba kayan taci gaba dayi bayan ta gama duba kayan ta maida su a leda ta miqawa Nusaiba tare da fad’in”to gashi naga kayan sunyi se ki maidawa zarah nata ne ita kad’ai kin sani,kinada naki dan haka kowa ya tsaya kan nashi bana so inga wani na aiki da kayan wani dan nasan halinki ga me da kayan kwalliya ko kinada naki se kinzo har d’akin nn kinyi kwalliya da kayan kwalliya na na rasa wane irin ruwan ido ne dake”

Cikin turo baki Nusaiba tace”kai umma jefi jefi ne fa kawai nake d’an zowa d’akin nn ina yin kwalliya ko shi sbd mirror d’inki yana fitowa da mutum sosai amma bawai ruwan idon kayan kwalliya nake ba,bare Zarah da kwana biyu tafiyar ta zatayi”

Umma tace”Waya gaya miki Zarah kam tazo knn nn zata ci gaba da zama tare da mu.

Cike da murna nusaiba tace”da gaske umma!

Umma ta gyad’a mata kai d’auke da murmushi.

Tsalle Nusaiba ta daka tace”kae amma wlh naji dad’i dama zaman gidan nn ni kad’ai ya ishe ni yusra ce tayi qarama ba fira take taya mutum ba.

Nan ta kwashi kayan cike da murna ta fita umma ta bita da kallo d’auke da murmushi a fuskarta har ranta tana jin dad’in yanda Nusaiba bata d’auki kanta kowa ba,duk yanda d’an uwanta yake,talaka ne ko baqauye bata nuna masa qyama se ma qoqarin take ta shigar da shi a jikinta sam halin su ba iri d’aya ne dana Saifuddeen ba.

1 thought on “Saifudeen Complete Hausa Novel”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top