Hausa Novels

Saji Kawu da Aunty ne sanadi Hausa Novel

Saji Kawu da Aunty ne sanadi Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_

 

Yayata bata daina min magana ba a cewar ta nasiha take min ni kuwa ko sauararon ta bana yi. Abinda kawai nake so shine na shiga motar nan kawai na bar garin nan. Ba wai bana son garin namu ba ne, kawai ina son shaƙar iskan wani garin ne. Hakan shi ne mafita gare ni, kuma ba ni fa na faɗa ba ita yayar tawa ce ta faɗa.

 

“Ina fata komai ya je daidai gare ki a cen…” Yaya Salmah ta ce da ni.

 

“Ba fa barin ƙasar zan yi ba, iyakata Niamey.”

 

Tun bayan rasuwar mahaifiyarmu wato wata huɗu kenan, yayata ta koma min kamar wata uwa gare ni. Duk da tayi aure amma koda yaushe tana bisa hanyar zuwa gani na, ganin idan ina lafiya, idan bana buƙatar wani abu. Ta kasance ƴar uwa ta alfahari gare ni.

 

Kuma barin Maradi da zan yi zuwa Niamey saboda ita ne. Ta kan ce zamana a gida a koda yaushe zai dinga tuna min Mama ne, yin nesa da gida zai fi min.

 

Yaron motar ya gama saka kayan a mota sannan yace min na shiga.

 

“Ki kira ni idan kin sauka.”

 

“Okay.”

 

“Kinada number Kawu Hashim ne?”

 

“Eh zan kira shi idan na kusan kai wa dan ya tarbe ni.”

 

“Yauwa kuma ki kula da kayanki.”

 

“Wai baki tunanin hakan ya isa? Ba fa yarinya ba ce ni yanzu ina faɗa miki.”

 

“Ai ba zaki taɓa tashi daga ƴar ƙaramar ƙanwata ba da nafi so. Shikenan jeki Allah ya tsare.”

 

Amsa mata nayi ta hanyar gyaɗa kai kafin na shige bus ɗin. Mijinta ya samar min wuri mai kyau kusa da window. Na zauna kamar da ƴan mintuna sannan wata mata tazo ta zauna kusa da ni. Irin mai jikin nan ce sosai, da har ta fara takure ni. Ina jin kamar in ce mata “ke kina tuƙe ni” amma da yake na samu tarbiya mai kyau sai nayi shuru.

 

Ban samu sheɗawa ba sai da ta sauka a wani gari, nan ma wata matar ta hau kuma ta zauna inda wancen matar ta tashi. Ita Allah yasa tana iya controlling jikinta.

 

“Sannu kina lafiya?” Ta ce min bayan ta zauna.

 

“Lafiya..”

 

“Ni ba zaki tambaye ni ba ya nake?”

 

“Ina tunanin lafiya kike.”

 

“Eh kinada gaskiya lafiya lau nake. Da alamu bakida surutu.”

 

“Eh banida surutu.”

 

Kallo na ta shiga yi na wani ɗan lokaci kafin ta ciro wayarta tana latsawa amma bata jima ba.

 

“Niamey zaki je?” Ta sake tambaya ta.

 

“Eh.”

 

“A wacce unguwa?”

 

“Ni ma ban sani ba gaskiya. Kawuna ne zai zo ya ɗauke ni.”

 

“Oh kenan ba cen kike da zama ba?”

 

“A Maradi nake amma a cen nake son yin karatu wannan shekarar.”

 

“Okay, hakan yayi kyau. Wajen kawun naki zaki zauna?”

 

Matar ta cika tambayoyi amma bana son yi wa babba rashin kunya.

 

“Eh gidan Kawuna shi da iyalinsa.”

 

“Da alamu yarinya ce ke mai nutsuwa, ga tarbiya. Inada ƴa itama ba zata wuce sa’anki ba. Idan ba zaki damu ba zamu iya musanyar numbobinmu wata ƙila ku zama ƙawaye ke da ita.”

 

Kawai haka nan? Da zan musa amma da nayi tunanin zata shafa min lafiya na yanke saka mata numberta, ita ma ta saka min tata.

 

Bayan haka ta cigaba da magana amma bana tunanin ina fahimtar abinda take cewa kuma bana iya tuna amsoshin da nayi ta bata.

 

Yaron motar da yayata ta yiwa kwatancen inda za’a ajiye ni ya nuna min inda zan sauka kuma dama tuni na kira kawuna yace min yana hanya.

 

Nayi zaune kamar da mintuna biyar lokacin da naji wani mutum na kiran sunana. Juyawa nayi na ga kawuna ne. Nayi tunanin ba zai gane ni ba domin ya jima sosai rabon da yaje Maradi.

 

“Ke ce Sajida?”

 

“Eh ni ce ga zahiri.”

 

Dariya yayi kafin ya ce “Toh ya kike ya hanya? Nasan an gaji sosai ko?”

 

“A’a wallahi ba gajiya ma sosai.”

 

“Kayanki ne wannan?” Ya tambaya yana nuna kayan da yatsa.

 

Gyaɗa masa kai nayi alamar eh. Ɗaukan su yayi sannan ya ce na bi shi. Hakan nayi har muka isa wajen motarshi ya saka kayan a but.

 

Kan hanya yake tambaya ta mutanen gidan. Sannan ya yi min jaje na rashin ummata. Har yau na kasa fahimtar dalilin da yasa bai je Maradi ba lokacin da Mama ta rasu. Alhali yaushe rabon ace Maradi na da nisa sosai da Niamey.

 

Bayan mun ɗan yi ƴar tafiya, motar ta tsaya bakin wani madaidaicin gida. Ba babba bane sosai amma kyakkyawan gida ne daidai gwargwado.

 

Ba mu kai ga ƙarasa fitowa daga mota ba, wata mata ta buɗo ƙofa ta fito ta nufo inda muke.

 

“Ikon Allah kece daman Saji? Nayi tunanin za’a kawo min renon ƴar ƙaramar yarinya ne ashe babbar budurwa ce masha Allah kin girma.”

 

Irin kalaman nan suna bani haushi a dubi mutum a ce wai ya girma kai kuma baka san amsar da zaka bayar ba.

 

Murmushi kawai na iya yi sannan na gaishe ta da ɗan duƙawata amma ta janyo ni ta rungume ni.

 

Kawuna ya ɗauki kayan ya shiga da su cikin gidan, mu ma muka bi bayansa.

 

Nayi tunani gidan babu kowa sai su amma daga baya naji muryar wata ƴar budurwa tana ƙwalla sunan Mama kafin ta bayyana gabana. Kallona ta shiga yi na wani ɗan lokaci, kallon nan na ƙasa da bisa wanda da ka gani kasan na raini ne mutum ke maka saidai ban bi ta kanta ba.

 

“Zainu zo ki gaisa da ƴar uwarki..” Cewar mahaifinta wato kawuna.

 

“Ƴar uwata?” Wacce aka kira da Zainu ta maimaita tana kallona.

 

“Ban faɗa miki cewa cousin ɗinki zata zo yau ba?” Baban nata ya tambaya.

 

“Ba zan iya tunawa ba.”

 

Daga nan ta matso gabana sannan ta miƙo min hannunta da niyyar mu gaisa nima na miƙa mata nawa. Hakan kuwa da alamu bai yi mata daɗi ba.

 

“Saji wannan ƴata ce, sunanta Zainu. Kusan shekarunku ɗaya amma ina tunanin ita ce babba…” Kawu ya gabatar da mu ga juna.

 

“Mama ki zo dan Allah cikin kitchen da sauri.”

 

Zainu ta tafi tareda mahaifiyarta ni kuwa na shiga ɗantsar akaifuna da baki har zuwa lokacin da kawuna yace na bi bayansa. Hawan stairs muka yi har zuwa cen ƙarshen corridor baƙin ƙofar wani ɗaki.

 

“Zaki zauna a ɗakin nan ke da ƴar aiki. Bata nan a halin yanzu yau weekend.”

 

Madaidaicin ɗaki da gadaje guda biyu da wardrobes guda biyu kusan kowanne gado. Sannan akwai wani ɗan ƙaramin center table da kuma kujera a tsakiyar ɗakin.

 

“Auntyn ki zata zo ta ganki nan da wasu mintuna kafin nan ki ɗan huta.”

 

Koda ya fita na faɗa kan gadon ragwaf. Katifar gadon akwai laushi naji kamar na kwanta nayi ta sharar bacci amma Aunty ta shigo.

 

“Auh har kin kwanta kenan?”

 

“Eh wlh.”

 

“Zaki ɗauki wannan gadon sannan ki saka kayanki a nan.”

 

“Okay, nagode.”

 

“Ba da jimawa ba abinci zai kai, dan haka idan kin gama wanka sai ki sauko ki ci.”

 

“Ok.”

 

Sai da ta nuna min bathroom kafin ta fita. Nayi wanka na sake kaya sannan na sauko ƙasa.

 

Bayan wasu ƴan mintuna Zainu ta zo da abincin a hannunta. Sai da na kusan amai da na kai loma ɗaya a bakina, shinƙafar bata ciyuwa kuma ba wanda ya damu tsakanin kawu da aunty. Idan nace zan tashi zan yi rashin ɗa’a dan haka na tilasta kaina saidai ina yin kamar loma shidda ban iya riƙe kaina ba na tashi.

 

“Ba zaki ci ba?” Cewar Aunty.

 

“Na ci, kawai dai bana jin yunwa ne sosai.”

 

Bayan wasu ƴan daƙiƙu kawu ya tashi sannan ita ma aunty ta tashi.

 

“Me yasa idan nayi girki ba mai ci?” Cewar Zainu tana zumɓurar baki.

 

“Wai da gaske kike?” Cewar Kawu da alamar wasa.

 

“Toh ba zan ƙara yin girkin ba ma.” Zainu ta faɗa tana ɗauke plate ɗin.

 

“Allah yayi.” Kawu ya faɗa saidai Zainu bata ji ba.

 

Na kasa yarda yarinya kamar wannan bata iya girki ba. Daga baya Aunty ta haɗa tea. Da alama mace ce ta gari, bata daina yiwa mijinta da ni murmushi ba a duk lokacin da muka haɗa ido.

 

Gajiyar mota har yanzu bata sake ni ba, dan haka na yanke zuwa ɗaki na kwanta. Bayan na farka na tuna da yayata, dandanan na ɗauki waya na kira ta.

 

“Sai yanzu kika yi niyyar kirana?”

 

“Wallahi mantawa nayi.”

 

“Mantawa da yayarki ko me? Da gaske? Kawu ya kira ni ɗazu.”

 

“Ah, okay.”

 

“Kin kira baba kin sanar da shi? Kawu ya kira shi amma ke ma ki kira shi.”

 

“Zan kira shi..”

 

“Ki kira shi yanzu.”

 

“Toh ta yaya zan kira shi alhali ina waya da ke.”

 

“Ki katse kiran mana.”

 

Sam bana buƙatar kiran mahaifina. Tun bayan rasuwar mahafiyata, familyn mu ya sauya ba kamar da ba. Matar mahaifina na son maye gurbin mahaifiyata kuma hanyar da ta biyo ba mai kyau ba ce. Sam bata sona kuma bata ɓoye hakan. Duk wata azabtarwa tana yi min ita a gidan nan, ba tareda mahaifina yace uffan ba.

 

Yayata ta kira ni domin ta ko na kira baba daga ƙarshe dai na kira shi. A ƙausashe yake min kamar koda yaushe.

 

To Be Continued…

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

*masu facebook kuma zaku Iya ziyartar shafin mu

Leave a Comment

error: Content is protected !!