Sakacina Ko Halin Maza Hausa Novel

Sakacina Ko Halin Maza Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: *SAKACINA KO HALIN MAZA?*

 

 

 

*RUBUTAWA:-*

*JAMILA LAWAL ZANGO*

 

 

 

*FIRST CLASS WRITER’S ASSO….*

 

 

 

*SHAFI NA ƊAYA*

 

 

Sanin cewar a kwai banbanci a cikin duniyar da Allah subuhanahu wata ala ya halitta masu ɗauke da halittu mabanbanta jinsi,bayan ya halicci duniyar mutane, da kuma waɗanda ba’a ji ko gani gare su sai dai duk wanda ya yi imani,ya na da yaƙinin samuwarsu a cikin duniyar da muke cikinta,da sauran halittu na dabbobi.Allah gwani wanda ba shi da abokin tarayya a cikin gwanintar halintunsa,ya halicci mutane ya kuma nuna babu wani banbanci a tsaƙanin su,sai wanda ya fi wani tsoron kiyaye abin da ya sharaɗa game da bautarsa,tabbas wannan haka ya ke a gurin Allah,amma kuma yayin da jinsi na bil’adama suka ɗauki sabanin haka,sun ɗora mizanin hankalin su suna auna banbanci na jinsi ta hanyar duba ga mulki,kuɗi ko kyawu na halitta.Su na kallon waɗanda suka mallaki waɗannan ababen na more rayuwa ga mafi ƙololuwar more rayuwa,wanda duniya ta yi maraba da zuwan sa kuma su ke kurɓan ruwan mafi ƙololuwar ɗaɗi a cikin ta.

Haka ta kasance ga wannan matashi mai cike da kyawu da kuɗi da kuma baiwar ilmi da Allah ya azurta shi dashi,ya na ji da kansa da kuma kalar rayuwar da ya tsinci kansa a cikin ta,bai san a kwai wani ƙunci ko wani ƙalubale da Allah ya ke jarabtar bayin sa,waɗanda suka yi imani domin ya gwada ƙarfin imanin su da shi.

Tabbas duniya ta na gara masa ƙwallo yadda ya ke so,domin ya fito daga cikin farin jadawali na tsarin rayuwarsa don ya yi gam da katar da bai fito daga cikin baƙin jadawali ba!Waɗanda da duniya ta ke musu kamun kazar kuku, su shiga halin ƙaƙa na iya tare da tunanin makomar rayuwar su.

Sanye ya ke cikin shadda ruwan bula gizina,sai ɗaukar ido da sheƙi take ga wani daddaɗan ƙamshi da ke tashi a jikin sa wanda ya ke sanyaya zuciyar duk wanda ya shaƙi ƙamshin.

Tuƙi ya ke cikin gwanance wa da kuma yanga,dan yadda yake jan motar ya ke kamar mai jin bacci ya na lumshe idanunsa masu kama da mai jin bacci.Gefen sa amininsa wato Ak ya ke zaune a kujerar mai zaman banza da wayarsa riƙe a hannunsa ya na dannawa.Jefi-jefi su na taɓa hira duk da hirar ta su,ba ta wuce na ‘yan daƙiƙa yayin da shuru yafi yawa a tsakanin su,kasancewar ta kowannen su ya na ji da kansa, dan sun haɗu ta ko ina ga kyau kuɗi da kuma wayewa da tsantsar ilmi.

 

Wani irin ƙara motar ta yi ya ja birki ya tsaya cikin tashin hankali ganin wani tsoho ya shige masa gaba har ya buge shi da motar.Ya tsaya ya na kallon gurin da takaici,ganin yadda tsohon ya ke son ɓata mishi lokaci.

Da sauri ya kuma buɗe murfin ƙoofar zai fita ya na faɗin”Wannan wawan mutumin zai ɓata min lokaci,an gaya mishi bani da aikin yi ne?” Ya fice ba tare da ya kula Ak da yake mishi magana ba,da sauri Ak shima ya fito sanin halin shi sai dai kafin ya ƙara sa Am ya wanka ma wannan tsohon mari har guda biyu.

“Ba ka da hankali ne da wannan banzan ƙarfen na ka zaka ɓata min lokaci?Shashasha kawai!”

‘Dan tsohon ya yi taga-taga ya faɗi har ya na fasa baki,da sauri Ak ya kama hannunsa ya mike sai kawai ya fashe da kuka,don shi kaɗai yasan halin da yake ciki.

“Haba A.m ya zaka mari wanda ya haifeka rashin mutincin na ka ya kai haka?Dubi halin da yake ciki amma baka tausaya mishi ba.”

Harara ya watsa mishi kamar ba zai ce komai ba,har ya fara taku zuwa motar shi sai kuma ya buɗe baki ya ce,

“Kai baka ganin abin da ya yi min?Jiya na fara hawa motar nan amma ya ƙuje min mota.Nasan kaf zuriyarsa babu wanda zai iya siyan ko da tayar motar ce.”A.k ya yi shuru ya na kallonsa cikin takaicin halin sa,na rashin daraja talaka da nuna tsantsar tsana da hantara,amma shi a ganin sa ya kama ta ya dinga kawaici saboda yasan waye Ak kuma waye asalinsa.

“Da izinin Allah sai ka sami dai-dai da kai ya faɗa ya na jin tsoro kasancewarta yasan waye shi ɗa ne ga Alhaji Muhammad Turaki,waye bai san wannan family masu ji da kuɗi da ilmi da wayewa.Cikin sa’a sai A.m bai ji abin da ya faɗi ba don ya juya ya nufi motarsa ya na tsaki.

A.k ya zaro kuɗi masu yawa ya miƙa mishi ya na ce wa.” Gashi Baba ka yi haƙuri don Allah ka je asibiti a duba ka.” Ya faɗa ganin duk ya ƙuje a hannunsa.Da sauri ya karɓe ya na godiya,ganin kuɗ’in da ya ba shi dan shi gaba ta kai shi ,dama ya fito zai je ya saida kekensa gashi kuma ya sami wannan kuɗi.

‘Dan tsohon ya dinga saka mishi albarka ya na hawaye kamar zai yi mishi sujjada, juyawa ya yi ya nufin motar da A.m yake ƙoƙarin tayar wa,sai kuma ya tsaya ya na kallon titin da alamun abin hawa yake nema a ransa ya na jin kawai ya haƙura da abokantakansu don ya sama ma zuciyar sa salama,da irin cin kashin da A.m yake yi wa talaka a gaban sa.

A.m ya kashe motar ya fito ya na mishi maganar ya shigo,amma ko kallon inda yake bai yi ba sai ma juyar da kansa da ya yi,ya na kallon titi fuskar sa kamar an aiko mishi da mala’ikan mutuwa.

“Well.” Ya ce tare da ɗaga kafaɗunsa ya juya ya na faɗin”Shike nan tun da baza ka taho muje ba ni na tafi,sai mun haɗu a ofis ka taho min da fayal ɗin da mukai maganar dakai,sannan ka shirya gobe ne tafiyar mu”. Ya ta da motar ya bar gurin A.k na kallon motarsa har ta ɓace wa ganinsa,ya ja numfashi mai zafi ya fesar ya riƙe habbar shi ya na jiran ɗan acaba,sai kuma ya fasa hawa mashin ya fara taku ahankali ya na jiran adaidaita.Tafiya kaɗan ya yi ransa a jagule ya na jin zafin yadda yake nuna tsanar talaka karara baya kawaici a gabansa,yasan cewar bazai taɓa iya canza aminin nasa ba don tsanar talaka a jinisa yake kasancewar duk family d’insu basa son talaka ya rabe su,shi kansa don Allah ya bashi tarin baiwar ilmin kasancewar Allah ya yi mishi baiwa da samin na’ura mai ƙwaƙwalwa,kuma saida suka mai da shi wani don yanzu ya na jin kansa a cikin jerin masu hannu da shuni.

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Murmushi ya so ya suɓuce mishi sai kuma ya dake,ya kauda kansa tamkar bai ga motar A.m da ta yi ribas ta dawo ba,da ma yasan dole ya dawo kamar yadda suka saba duk sanda suka yi faɗa a tsakaninsu, wanda ba ya wuce sati don A.m bashi da haƙuri ko kaɗan gidan su da gurin aiki duk sun san haka,shi kuma A.k ba ya ɗaukar raini mafi yawancin lokuta mutane su na mamakin yadda abokantakarsu ta yi ƙarko a haka don kullum cikin faɗa suke kamar wasu yara Daddy shi ne ɗan sasanci,sam baya gajiya kasancewar ya na ji da shi saboda irin ci gaba da ya ke kawo mishi a cikin kampanin sa,ya sani cewar in har babu A.k to kampaninsa bazai ci ga ba.

A.k ya kauda kansa bai tanka mishi ba sai wayar sa da ya ciro da nufin ya kira direban sa ya zo ya ɗauke shi,don ya fasa shiga cikin a daidaita.”Ganin ya taho kamar zai buge shi da motar amma bai kula ba,sai ɗauke kansa da ya na kallon gefe don cike yake dashi.

A.m ya leƙo ta tagar motar sa ya ce ya na murmushi mugunta,don daga ganin yadda ya yi ya san ya gaji matuƙa.”Don Allah ka zo mu tafi kasan dole na dawo,Daddy ya kira ni ya na son ganin mu”. Banza ya yi da shi ya ci gaba da tafiya,ganin haka ya fito tare da kashe motar sai kawai ya kama shi da kokuwa zai tura shi cikin motar,kamar dai yadda suka saba duk lokacin da suka yi fad’a.

Bai wani ja ba ya shige cikin motar ransa a haɗe,dariya sosai A.m yake mishi don ya na matuƙar son aminin nasa saboda riƙo da gaskiya, kuma bashi da shishshigi a lamuran sa.

Tun da suka shiga cikin motar babu wanda ya yi ko tari a cikin su,da ma ɗabi’ar su ce shirin basu cika magana ba kasancewar kowa naji da kansa.

Wayar A.k ta yi ƙara alamun ana kira amma sai A.m ya kai hannunsa ya kashe wayar baki ɗaya,don yasan mai kiran taɓe bakinsa ya yi ya ci gaba da tuƙi cikin kwanciyar hankali.A k ya ja fasali tare da buɗe baki da nufin ya yi magana,amma da ya kula rigima yake ji sai kawai ya kauda kanshi bai ce ƙala ba don har yanzu ransa a ɓace yake da abin da A.m ya yi ma mutumim da ya haife shi.

Ko da suka ƙaraso tangamemem get ɗin gidan mai gadi ya buɗe musu get,A.m ya yi parking bai kula da gaisuwar da maigadin yake mishi ba ya shige cikin gidan,yayin da A.k yabi bayan sa kasancewar ba’a yi mishi shamaki da cikin gidan ba.

 

*******

Juwairiya zaune a gefen ƙanin ta Ibrahim ta zuba mishi idanu, ya yin da hawaye suke gasar turarreniya a fuskarta,ji ta ke kamar ta yi hauka tsabar damuwa ta na jin wani irin baƙin cikin halin da suka tsinci kansu. Zura hannunta ta yi a cikin kofin ruwa ta shafi fuskar Ibrahim da yake kwance rai kwakwai mutu kwakwai,sai kuma ta kama shi ganin yadda ya zaburat amkar zai shiɗe.

Mama da ke tsaye a bakin ƙofa fuskarta ɗauke da tsananin damuwa da ƙunci ta janye tagumin da ta yi tare da ajiyan zuciya mai ƙarfi.”Anty Juwairiya mutuwa zan yi ga shi Baba ya ƙi dawowa.”

Ya faɗa da wata irin murya da yake ƙoƙarin haɗa kalmomin da su.”Baza ka mutu ba Ibrahim ciwo ba ya kisa.”Mama ta ce cikin tausayin sa.

Juwairiya kuwa ta kasa magana sai kuka ganin gudan jinin na ta ƙanin ta tilo na cikin wani mawuyacin hali, ji take da ma ace ciwon a jikinta yake.Sun jima suna tsaye a kansa da numfashin sa yake baraxanar ɗauke wa,hankalin su a tashe sai shafa masa ruwa suke yi suna kuka gunun ban tausayi.

Juwairiya ce ta miƙe ta na faɗin”Mama bai kama ta mu zuba mishi ido mu na kallon sa a cikin wannan halin ba,tunna Baba bai dawo ba zan fita na samo abin da za’a kaishi asibiti.Ta ce cikin kuka Mama ta kasa ce mata komai duk da ta na tunanin in da za ta samo kuɗin,amma har ta na shirin fita ba ce komai ba.”Juwairiya na shiga uku!Ya sume.”Ta ji muryar Mama cikin ƙaraji dai-dai lokacin da ta fice da ga gidan.

 

 

 

 

*Follow,read,comment,share.*

[29/09, 10:10 pm] +234 803 192 1625: *SAKACINA KO HALIN MAZA?*

 

 

 

*RUBUTAWA:-*

*JAMILA LAWAL ZANGO*

 

*SADAUKARWA GA:-*

 

*SUMMY M NA’IGE*

_(Aminiya)_

 

 

*FIRST CLASS WRITER’S ASSO….*

 

 

 

*SHAFI NA BIYU*

 

 

Da sauri Juwairiya ta dawo ta rungumshi da hannunta ɗaya,ɗayan kuma ta na shafa mishi ruwa, ajiyan zuciya ta sauke mai ƙarfi ganin ya buɗe ido,don hankalin su ya tashi maƙura gani suke kamar mutuwa zai yi ganin yadda idanunsa suka ƙaƙƙafe.

Juwariya ta miƙe ta na faɗin.”Tun da ya farfaɗo bari na je na naimo mishi magani.”Miƙewa ta yi ba ta jira amsar da Mama zata ba ta ba ta fice da ga cikin gidan ta na sharar hawaye.

A hankali ta ƙarasa shiga cikin shagon na sa ganin yadda ya haɗe rai tun da ya hangeta ta na tahowa,tamkar an aiko masa da mala’ikan mutuwa ya haɗe ransa babu wani walwala.Jikin ta ya yi sanyi sai ta tsaya a bakin ƙofar ta kasa mishi magana kuma ta ƙi ta tafi duk da kallon kora da hali yake mata.

“Lafiya ki ka yi min tsaye kofar shago kamar na saki ki?Ya faɗa ransa a ɓace”Don Allah ka taimake ni Bala kasan mai ya kawo ni a karo na biyu,wallahi suna cikin wani hali na rantse maka wannan karon zan naimi kuɗin ka na baka.”Ta faɗa da muryar kuka fuskarta bayyane da damuwar halin da take ciki.

“Ni ina ruwana na gaji da baki bashi kuma ba kawo min kike ba,sannan na nuna miki hanyar da zaki bi mafi ɓulluwa kin nuna a’a wai ke ustaziya,to sai kije can amma ko maganin biyar ba zan baki ba.”Tamkar zai kai mata duka yake magana ganin haka sai kawai ta juya,dan ta saka a ranta yau bazai bata ba.

“A’a Juwairiya tafiya zaki yi.”Ya faɗa da sanyin murya ganin ta kama hanyar fita,sai kuma ya ƙara matso da fuskarsa gurin ta yace.”Kin cika kafiya ki yadda ki amince ko sau ɗaya ne,Allah zan baki duk abinda kike so.Kin san ina son ki Juwairiya na san babu yadda za’ai na same ki,wannna dalilin ya sa nake so ki amince min kar soyayyata ta faɗi a banza.”

Ƙarashe fita ta yi da ga shagon dan abin da yake so bazai samu ba.Mahaifiyarta kullum ta na mata nasihar ta tsare kanta da ga aikata zunubi mai girma wanda Allah yake fushi da wanda ya aikata,kuma ya yi hani ga bayinsa muminai na ƙwarai.

Gidan ƙawarta Mariya ta wuce ta same ta zaune akan tabarma a cikin falo ta na gugan kayan ta da dutsen guga na gawayi,sallama kawai ta yi ta zauna a kan tabarma ji take kamar zatai hauka.”Juwairiya lafiya kike mai ya faru?”Mariya ta jera mata tambayoyin da ta kasa ba ta amsa ba,sai ta janye hannunta da Mariya ta kama tare da share hawayen da ya gangaro mata.

Mariya ta ƙarashe share mata sauran hawayen ji take ita ma kamar ta saka kuka,ta ɗago idanunta da suka kaɗa suka yi ja ganin ƙawar ta ta na kuka tace.”Ki yi min magana Juwariya!Kin san ba na jure ganin ki a cikin wannan hali,abin da ya sa naƙi dawowa kin san halin Baba Sani na rasa yadda akai ya takurawa rayuwar ki baya son kowa ya raɓe ki,dan haushin koron da yake yi nake ji irin kullen da yake miki ko fa yaran sa baya yi mawa,lamarin sa akwai ayar tambaya ,dan ina tunanin akwai lauje cikin naɗi!”Ta ja fasali ta na kallon Juwairiya da kukan ta ya tsananta,tuna yadda ya tsane ta yake azabtar da rayuwarta.Mariya ta ci gaba da magana cikin ɓacin rai ta na cewa.

“Ina jin takaicin halin da kike ciki amma ki sani bawa bai isa ya canza ma wani rayuwar sa ba,kin ga da Baba Sani baya miki kulle sai na sama miki aikatau ni bashi nake yi ba hankalina kwance.

Juwairiya ta sauke ajiyar zuciya duk da baƙin cikin da take ji na ƙin barta ta yi aikatau,wanda mahaifinta ma ya amince amma ƙememe ya hana ta da ta na yi ƙila da basu shiga cikin uƙubar rayuwa ba,gashi tun da ta gama sakandiri ya hana ta karatu amma yaran sa duk sun yi.

Duk da lamarin na ci mata tuwo a ƙwarya amma ba ta ce ƙala ba,sai dai zuciyar ta cinkushe take da damuwa tare da tunani iri-iri.

Mikewa Mariya ta yi ta shiga kicin ta zuba tuwo da miyar kuɓewa ta kawo mata ta na faɗin.”Gashi tun ɗazu na so na kawo muku amma ina tunanin wannan Baban naki,kuma Auwal tun da ya tafi islamiya bai dawo ba balle na bashi ya kawo miki.”Ta miƙa mata tare da kwance ƙullin zaninta ta ciro naira ɗari biyu ta miƙa mata.

Tsabar murna sai kawai ta rungumeta tare da fashewa da kukan murna,Mariya na taimakon ta ƙwarai ta na fatan Allah ya bata ta taimaka mata.

Rako ta ta yi ta siya magani sannan ta kaita dai-dai kwanar lungun gidansu.Da sauri Mariya ta saki hannunta ta na faɗin.”Na shiga uku wallahi gashi nan duk da ƙin kaiki gida da na yi amma ya na nan ya na sa ido ya san ki fita,ke Juwairiya wannan ko mijin ki ne sai haka.”Ta ruga da gudu har ta na tuntuɓe bayan ta gama maganar don Allah ya saka mata tsoron shi,bashi da mutunci in dai akan Juwairiya ne.

Juwairiya da jikinta ya fara rawa ji ta yi kamar ƙasa baza ta iya ɗaukar halintar ta ba,ta tsorata iya tsorata zabura ta yi kamar zata ruga sai kuma ta fasa ta na karanta wallahu galibun ala amrih ganin ya tunkaro ta.

Ya ƙaraso ya na mata wani irin kallo da shi kaɗai yasan ma’anarsa.”Ina kika je?”Ya tambayeta da murya kakkausa tare da saka ƙafafunsa ya take mata ‘yan yatsun kafar,ta rintse ido ta na jin wani iri madarar azaba ya na taso wa daga kan ‘yan yatsun na ta ya na zagaye ilahirin jikinta,taso ta matsa domin akoda yaushe ya tsaya kusa da ita ta na ƙalubantar yadda yake matsowa daf da jikinta.Amma hakan ya ci tura ganin yadda ya take kafarta ya hana motsinta.

“Bana hana ki yawon maula da uwarki ta koya miki,bayan Yayana bai rage ku da komai ba.”Ya faɗa ya na ƙara kusanci da ita fiye da na ɗazu.

“Don Allah kayi haƙuri bani ta yi wallahi ban roƙe ta ba,kuma Ibrahim zan bawa.”Tace yayin da taƙi shaƙar numfashi ba ta son ta shaƙi iskar hucin bakin sa da take jin sa a fuskarta.Ya ɗa ga kafafun na ta ya na ƙare mata kallo hakan ya bata damar shirin arcewa ko takalminta bata ɗauka ba,dan ya zame lokacin da ya take ƙafarta.

Da gudu ta ruga amma sai ta faɗi ƙasa yayin da miyar tuwon ya zube,amma duk da zafin da take ji bai saka ta yadda tuwon ya zube ba,ta zabura ta miƙe hanyar gida dai dai sanda ta ji ya na faɗin.”Ni da kene a duniyar na baza ki taɓa jin daɗi ba matuƙar ina raye,haka kawai na yi sakaci har tunanina ya faru mu zu ba mu gani

Juwairiya na shiga cikin ɗaki ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro,a ranta ta na jin baƙin cikin halinsa bata san mai ta tsare mishi ba,amma ya saka ma rayuwarta ƙahon zuƙa.

Koda ta shigo Mama ba tace komai ba har ta sha kukanta ta ƙoshi don tasan mai ya faru,tunna babu abin da za ta iya shi yasa bata tanka mata ba,sai ta jawo kwanon tuwon ta ba Ibrahim sannan ta bashi magani ragowar taci ta ragewa Juwairiya duk da babu miya kuma ta ji ƙasa-ƙasa a tuwon.

Bayan ta gama kukan taji sanyi a zuciyar ta dama kukan shi ke sanyaya mata zuciya,duk lokacin da ya yi mata hakan don babu wanda yake ko tari a cikin iyayenta,su kansu tsoron sa suke yi duk da mahaifinta shine babba.

Miƙewa ta yi ta ɗauro alwala ta yi magariba sai ta yi zamanta ta na jan carbi yayin da hawaye ke zuba fuskarta,wani gefe na zuciyarta ta na hasaso mata lamura sosai game da Baba Sani.

Baba Sani ya yi tsaye a gurin bayan tafiyar ta ya na tunani sannan ya ƙarasa dakalin ƙofar gidan ya zauna ya na gadin masu zuwa gurinta,ko da ka kira sallar isha’i ya yi sannan ya dawo ƙofar gidan ya ci gaba da gadin gurin.

Sai misalin tara na dare mahaifin Juwairiya ya yi sallama ya shigo da ƙullin leda mai ɗauke da garin rogo gwangwani biyu da siga.Mama ce ta amsa sallamar ta ƙarbi ledan tare da shinfiɗa mashi tabarma,lokacin har baccin wahala ya fara ɗaukar ta don yunwa take ji matuƙa kuma kamar zazzaɓi yake son kama ta.

Jin sallamar ya sa ta buɗe idanu ganin leda a hannun Mama ya sa ta miƙe tare da ƙarban ledar bayan ta yi mishi sannu da zuwa ta fice dan ta jiƙa garin.Ya kalli Ibrahim dake kwance ya na bacci ya shafa fuskarsa ya na faɗin.” Ya jikinsa?Ina can amma hankalina ya na nan kin san jiya ƙafarsa ta bani tsoro.”Yace ya na lasar bushashshen bakinsa dan rabon sa da abinci tun jiya da yamma da suka girka taliya leda ɗaya gashi ya wuni ya na faskare.

“Da sauki amma ya kama ta a maida shi asibiti gaskiya,yau ya bani tsoro ina ki kamar zan rasa Ibrahim saboda halin talaucin da muke ciki.”Tace sai kuma ta rushe da kuka ta na fyace majina.

A sanyaye Juwairiya ta ije garin da ta jiƙa ganin Mama ta na kuka ta koma gefe ta zauna ta na jin zafin Baba Sani dan ita gani take shi ya takurawa rayuwarsu da ya hana ta naimi aiki,in da ace ta na aiki rayuwar su ba ta yi muni haka ba,ga Mariya da take aikin suna jin daɗi kuma matar ta na taimaka musu.

“Ki bar kuka dan Allah da kin san halin da na wuni da kin tausaya min!Na dage tuƙuru ina faskare sai da na gama Malam Aminu yace bashi da kuɗi sai gobe,daƙyar na samu ya bani naira ɗari biyu wai shima kwana biyu ba cinikin iccen.

Shuru sukai cikin jimamin rayuwar su kowa ya na takaicin yadda suke tsotsan tsamiya,ganin Baba ya dawo Juwairiya ta miƙe tare da yi musu sai da safe ta tafi ɗakin da take kwana.

Washegari da safe misalin bakwai da rabi ta shafa addu’a,sannna ta miƙe ta nufi waje dan wanki zatai da aka kawo musu da safe kuma ana so anjima,murna sosai ta yi dan aka wo kuɗin wankin za su sami su yi girki.

Da sauri ta ƙarasa ta na faɗin.”La Mama har kin fara.”Bata ce mata komai ba sai botiki da ta miƙa mata ta ibo ruwa a randa.

Basu gama wankin ba har misalin tara da rabi bayan sun gama Juwairiya ta fita tayo musu cefanen taliya suka dafa da mai da yaji.Bayan ya dawo daga sallar asuba ya kwanta don ji yake ko ina na jikin sa ya na ciwo,bai tashi ba sai da aka gama girki shi ma sai da Juwairiya ta tashe shi,dan tasan yunwa ce ke damunsa.

Bayan yaci abincin ya miƙe tare da fita ya na son ya ga kanin nasa,akan maganar komawa da Ibrahim asibitin da kamar yadda likitocin suka faɗa.

Ya na ƙoƙarin shiga shashinsa suka yi kicibis saura kaɗan su yi karo,Baba Sani ya matsa ya na kallon ɗan’uwan nasa ya ce.”Lafiya yaya baka da lafiya ne?Ji yadda ka koma kamar wanda ake iban shi ana miya.”Yace da maganar shi ta izgilanci ya na karkaɗe jakar zuwa aikin shi,dariya kawai ya yi mai kama da yaƙe yace.”A irin wannan rayuwar ka na sane da halin da nake ciki ni da iyalina,yanzu ko taimakon da kake yi min ka daina.”Ya ƙarashe magana da takaicin yadda ɗan’uwan nasa ya daina taimaka mishi tun tsawon shekaru da irin butulcin da ya yi mishi.

Hannun shi ya watsa ya kalleshi ya na kallon agogo.”Sauri nake yi yaya kaga na yi latti kuma kasan yanayin aiki na,yi sauri ka faɗi abinda ke tafe da kai.Kuma da kake maganar ba na taimaka maka nauyi ne ya yi min yawa kowa ya ji da kansa.”

“Haka ne Allah ya shige mana gaba,amma ya kama ta ka duba rayuwar Juwairiya kaga ni bani da shi da zan saka ta a makaranta,kuma kace ba aure zakai mata ba baka da ƙuɗin auren da ita.”

“Haka na ce don ni yanzu ba ta aure nake ba,sabon gidana nake son na kammala.Ya bashi amsa a taƙaice sannan ya ɗora da ce wa.”Kuma da kake maganar na saka ta a makaranta baka ga yadda take mara kamun kai ba can zata dinga watsewa da mutane,ka na sane da irin ƙorafin da nake maka a kanta ni nasan halinta da nake zaman gida.”

Shuru ya yi ya na takaicin abinda ya faɗa ransa ya yi zafi,shi dai yasan kawai ya tsaneta ne amma yasan wacece ‘yarsa wani irin hali take dashi.

“Yaya na fa gaya maka aiki zan tafi amma ka tasa ni gaba kana ta wasiƙar jaki,ina sauri ne in kima baka da abin faɗe na tafi imna dawo saimu tattauna.”Ya ce dashi ya na ƙoƙarin fita da sauri ya tare shi sannan ya ce.”A kan maganar komawa da Ibrahim asibiti ne,kuma gashi bani da kuɗi dan Allah ka taimaka….”

“Haba yaya kasan fa bani da ƙuɗi nima hidima tayi min yawa kowa yaji da kansa,amma ga dubu ɗaya kuje Allah ya ba da lafiya.”Ya miƙa mishi ‘yan ɗari biyar guda biyu ya fice ya barshi a tsaye kamar sanda ya na tunanin butulci irin na ƙanin nasa.

A sanyaye ya shigo cikin sasan sa ya zauna akan turmi kamar babu laka a jikinsa,bai ce komai ba har zuwa wani lokaci sannan ya ja numfashi ya na kallon Mama dake ninke kayan da suka wanke har sun fara bushewa.

“Lailai ɗan adam butulu ne.”Yace cikin raunanniyar murya sannna ya ɗora da cewa.”Wai yau ni Sani yake wulaƙanta wa kan kuɗi ya manta yadda na wahala dashi dan ya sami ingantacciyar rayuwa.Mama ba tace mishi komai ba sai gyaran murya da ta yi,dan babu wani abu sabo a cikin halinsa duka sananne ne a gurinta.

Juwairiya na kwance bayan ta tashi ta yi sallar nafila ta yi addu’a ta koma ta kwanta,idanunta babu alamun bacci sai juyi take yi ganin haka sai kawai ta janyo carbi ta na ja,idanunta a rintse zuciyar ta na fatan samun maslaha a rayuwar su tunannin ta inda za’a sami kuɗi a mai shi asibiti,don likitocin suna tunanni aiki za’ai mishi a ƙafar.

Kawai sai ta ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakinta tsoro ya kama ta,tunawa da ta yi ta manta bata saka sakata ba da ta fita zuwa alwala.Tsananin tsoro ya kama ta ta rintse idanunta ta na tunani ta ya ya kai wani ya shigo cikon gidan su,dan Baba Sani ya gyara gidan kuma akwai ƙofa na masu kuɗi mai ƙarfi gidan.

Ba ta gama wannan tunanin ba ta ji mutum ya shigo ya nufi makwancinta,ta buɗe baki da nufin ta yi ƙara sai kawai taji an toshe mata baki da wata irin murya da nufin a ɓatar da tunanin mutum ga sanin mamallakin muryar aka ce.”In kika yi ihu saina kashe ki?Ya faɗa tare da soka zungureriyar wuƙa dai dai cikinta,amma ta yadda bazai cutar da ita ba.

Wani irin tsoro da tashin hankali ya ziyar ce ta taji tamƙar numfashinta zai yi balaguro zuwa wata duniyar wacce take da banbanci da wacce take rayuwa a cikinta.”Da gaske abin da sautin amon kunnnuwana suke gaya min muryar Baba Sani take amo a cikin dodon kunnuwana?To mai ya shigo dashi cikin ɗakina a wannan sulusin daren?”Irin tarin tambayoyin da suke ta bijiro mata a cikin zuciyar ta wacce ba ta samu ko da amsar ɗaya ba.

_Kar dai ku manta sunan labarin “SAKACINA KO HALIN MAZA” Mu haɗu a shafi na uku dan har yanzu shinfiɗa ne har ba’a fara ba.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

 

 

Kuma a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.

Kar dai ku man da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA’IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

 

 

 

 

*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*

[29/09, 10:10 pm] +234 803 192 1625: *SAKACINA KO HALIN MAZA?*

 

 

 

*RUBUTAWA:-*

*JAMILA LAWAL ZANGO*

 

*SADAUKARWA GA:-*

 

*SUMMY M NA’IGE*

_(Aminiya)_

 

 

*FIRST CLASS WRITER’S ASSO….*

 

*SHAFI NA UKU*

 

 

 

Hannun Baba Sani ya sauka a ƙirjin Juwairiya tare da wasu tagwayen hawaye masu tsananin zafi da ƙuna a fuska.Ta jin wani irin tsananin tashin hankali a zuciyarta yayin da take ji a cikin zuciyar ta tamkar za ta haɗiye zuciya ta mutu.”Da ma burin sa kenan a kai na ya hana rayuwata samun sukuni,kullum ya na bibiyata tare da daƙile farin cikina?Me na yi masa wanda ba zai iya ɗauke mugayen idanunsa a kaina ba,a matsayina na ƴar wansa wanda suka fito ciki ɗaya?Wayyo Allah ina ma ace ranar mutuwa ta ce aka nuna min ba wannan ranar mai baƙin gani da muni a cikin zuciya ta ba.Ihu ya kama ta na yi ya kashe ni kamar yadda yace ko na yi shiru ya ɓata min rayuwa?”Ta tambayi kan ta cikin tsananin ruɗani dai-dai lokacin da ta ji saukar hannun sa a hurumin da ba na shi ba.Sai ta rufe idanunta ta na kiran sunan Allah tare da karanto duk addu’ar ta da fito daga cikin bakin ta.

Da sauri Baba Sani ya janye hannun sa daga ƙirjin ta tare da fasa abin da ya yi ninya,jin motsi daga waje.”Sannu Malam ka yi a hankali jikin ka babu ƙarfi.”Suka ji muryar mahaifiyar Juwairiya ta na magana cikin tausayi.

Hankalin Baba Sani ya tashi sosai ya daɗe ya na dakon wannan ranar tun lokacin da Juwairiya ta fara girma ya saka kwaɗayin sa a kanta,gashi ya sami dama amma kuma kamar hakonsa bai cimma ruwa ba.

Dai-dai saitin kunninta ya saita tare da raɗa ma ta.”In kika yi magana sai na kashe ki.”Hakan ya sa Juwairiya kame bakin ta ta yi shuru sai hawaye dake zuba a fuskarta.

Ya tsorata iya tsorata ganin sun shige cikin bayin ya buɗe kofar ya fice cikin sanɗa,Juwairiya ta fashe da kuka tare da fita daga cikin ɗakin a ranta ta ƙudirta ba za ta ƙara kwana a cikin sa ba.Fitowar ta ya dai-dai da lokacin da suka fito daga cikin bayin.Faɗawa kan jikin Mama ta yi ta fashe da kuka ta na wani irin kuka mai ƙarfi da ta da hankali ba ta damu da daren da ya tsula ba.Cikin tashin hankali da tsoro Mama ta rungume ta ta na faɗin.”Lafiyar ki ɗaya Juwairiya dare ne fa?Ko kin yi gamo ne.”Irin tarin tambayoyin da take mata amma ba ta kula ta ba sai kuka da take yi mai ɗaukar hankali,ganin kukan na ta ba na ƙarewa bane Mama ta ja hannunta suka shiga cikin ɗaki lokacin Baba har ya shige ya kwanta,saboda gudawa da yake fama da shi ya kasa tsaya wa ya tambayi abin da ke faruwa.

“Mai ya same ki lafiya?”Mama tace don zuwa yanzu kukan ya fara ba ta tsoro ta na ganin kamar Juwairiya gamo ta yi,yayin da ta wani gefen ta fara ba ta haushi bacci ne sosai a idanunta.

Juwairiya ta kasa magana sai kuka haka Mama ta yi ta gaji ta koma ta kwanta yayin da ta barta zaune tamkar ta haɗiye zuciya ta mutu.

Washegari da safe Mama duk lallashin da ta yi mata akan ta gaya mata abin da ya faru,amma taƙi ƙarshe sai dai ta yi mata ƙaryar mafarki mara kyau ta yi.Mama ba don ta yadda ba ta ƙyaleta amma zuciyar ta ta na gaya mata a kwai ɓoyayyen lamari,kasancewar Juwairiya ba ta taɓa kasa kwana ita kaɗai ba.Hankalinta ya tashi musamman da Juwairiya tace mata ba za ta ƙara kwana a ɗakin ita kaɗai ba,sai dai a haɗa ta da Ibrahim wanda Mamma bata iya kwana sai da shi saboda ciwon sa,gashi ta na da mugun bacci.Duk da jikin Baba da ya kwana babu daɗi amma haka nan ya shirya ya fita bayan ya sha magani.

Wunin ranar Mama ta kasa gane kan Juwairiya duk irin tarin tambayoyin da take mata,don ko ruwan koko da ta dama taƙi sha daga ƙarshe wani ƙarya sake yi mata tace ba ta da lafiya.

******

Gidan cike yake da mutane kai da gani kasan ana farin ciki a dalilin bikin ƴaƴan gata, ga kayan abinci da na tsotse-tsotse da a ke ta fita da shi.Bikin na yaran manya ne waɗanda duniya take hannun su kuma ta yi na’am da zuwan su duniyar,suke rayuwa a yadda suka tsara kuma suke ƙurɓar ruwan daɗi a cikin ta.

Naira ta na tsala kuka tare da nai man taimakon agaji da son ɓoyeta domin ta adana kanta ga masu buƙatar ta.Ruwan kuɗi kawai yake tashi da jerin gwanon motoci wanda ba zasu irgu ba.Wannan biki ne wanda ya amsa sunan sa kuma ya buƙaci a buga a jarida,wato bikin Muhammad Dawood Turaki da amaryar sa Zainab Abubakar mai shadda.Waye bai san waɗaɗnan hamshaƙan masu kuɗi da samu rayuwa mafi ƙololuwar daɗi a gare su ba.

Muhammad Dawood ɗa ne ga wani hamshaƙin mai kuɗi daga cikin turaki Family,wanda duniya ta san shi har da ƙasashen waje don ma yafi gudanar da harkokin sa a can.Tsarin rayuwar su irin na turawa da zallar boko.Gida ne na ƴanci da rayuwa babu taƙurawa da samun kwanciyar hankali.Suna da matuƙar kyau da asali mahaifin sa haifaffen garin Zariya ne.Ya gina katafaren gidan sa mai kyau a unguwar Zangon shanu,gida mai kyau na bene da tsari.Matan sa biyu Hajiya Khadija wato mahaifiyar A.m sai amarya Hajiya Binta Yaran sa bakwai Muhammad shi ne na farko wanda aka fi sani da A.m,sai kanin sa na miji sauran mata ne guda biyu sai kuma bangaren amarya ta na da uku.Suna zaman su lafiya kuma kan su a haɗe yake.

A.m mutum ne mara daɗin sha’ani ga rashin haƙuri ga saurin ƙulewa,ba ka taɓa gane in da ya sa gaba shi kullum mutum a gurin sa bai iya ba kuma ba a yi mishi gwanin ta ba.Kannin sa suna shan faɗa shi ya sa basa ƙaunar ya zauna a gida in kayi magana,yace ka faye surutu in kayi shuru yace ya na magana an raina shi.Shi komai a gurin sa laifi ne sannan ba shi da fara’a ko wasa ba ya yi dasu.Faɗin halin A.m abu ne mai wuya domin ya na da murɗaɗɗen hali baka gane in da yasa gaba,wannan dalilin ne ya sa ba shi da wasu abokan sai A k wanda ya jure halin sa duk da wani lokacin shi ma hutsu ne,amma ya san yadda yake tafiyar da shi.Muhammad ɗan gata ne a gurin mahaifin sa ga shi fari kyakykyawa dogo mai aji da tsafta.Wan mahaifin sa Alhaji Sama’ila ya na matuƙar ji da shi domin a hannun sa,ya tashi ya ma fi Daddy sa kuɗi sai dai shi Allah bai ba shi haihuwa ba.

Ya na matuƙar son yaga ya haihu saboda ya samu magaji har ƙasar waje ya kai matan sa uku a ka yi musu dashen kwai,amma Allah bai nufa cikin zai tashi ba,ƙarshe daga baya kan dole ya fauwala ma Allah lamuran sa ya na addu’ar Allah ya sa ya na da rabon haihuwa a duniya.

Tun kafin a haifi A.m mahaifin sa ya yi ma Yayan sa alƙawarin ba shi duk abin da ya haifa,saboda haka ana yaye shi aka miƙa ma matarsa Karime.A.m ya taso cikin gata da shagwaba bai san damuwa ko a kasin haka ba.Duk karatun sa a ƙasar waje ya yi in da ya karanci (Economis)bayan ya kammala ya dawo gida Nigeria amma ba ya wata yake fita waje.

Family ɗin Turaki mutane ne da ba ruwan su da harkan talaka ba sa hurɗa dasu,kuma ba sa shiga sha’anin su.A.m da ya tashi ɗauko tsanar talaka sai yafi kowa a cikin Family ɗin na su,don shi tunanin sa laifin sa ne da yaƙi tashi ya nema ya tsaya lalaci.Saboda mugun tunanin sa akan talaka ya sa ya tsani ma’aikatan gidan su kullum cikin hantara da mari yake musu laifi kaɗan zai kai duka,musamman masu aikin cikin gida.

Zainab Abubakar ƴar gidan wani ɗan majalisa ne da yake tashe a yanzu kuma hamshaƙin ɗan kasuwa.Yarinya mai tashen kyau da ƙuruciya ta na ji da kanta tare da alfahari da kyan da Allah ya yi mata,ga ɗagawa da son nuna ita ma wata ce mai ilmi da kuma nera.Sannan ra’ayin ta yazo ɗaya da A.m na ƙin talaka ba ta da kirki sosai,amma in baka shiga sabgar ta ba ba zaka gane hakan ba.Zainab likita ta karanta a ƙasar indiya.Mahaifinta ya na ji da ita don ita kaɗai ya haifa,sukai hatsarin mota ya samu naƙasa ba zai ƙara haihuwa ba.

Saboda haka yake ji da ita ba ya son ya ga ɓacin ranta komai take so shi take yi,gara mahaifinta ya na ɗan jan ido akan lamuran ta musamman shigar ta da ya tsana,amma mahaifiyar ta Hajiya Mariya ba ta barin ya tsawa ta mata a cewar ta in basu ba ta gata ba wa zasu ba.

Zainab mace ƴar ƙwalisa da gayu ga ƙamshi a kwai son turare masu tsada da kamshi,ga son kwalliya ta na ɓata lokacin ta akan kwalliya ita rayuwar ta tafi ba ta hamimmanci akan kwalliya da charting,sai ta wuni ta na kalle-kalle a waya ko ɗaukar hoto.Kullum rana na duniya Zainab ta yi wanka sai ta ɗauki hoto ta yi posting ɗin shi ko da wankan kwanciya ta yi.Bayan kwalliya da take so a rayuwar ta sai waya ko da yaushe wayar ta ya na hannun ta.

Wani lokacin mahaifin ta ya na tonon ta ya na kiran ta suna mai aljanar hoto ta na son ɗaukar hoto ta tura a Social Media a yi mata comment da liking a na zuzuta kyawun ta,ko ta ɗora a tiktok. Zainab mace ce mai son jiki da hutu duk da ba ta da ƙiba sai dai jiki na mata,amma a kwai son jiki ko waya a kace ta ɗauko sai tace wash!Ta miƙo ta na ya mutsa fuska ko alamar gajiya.

A taƙaice ba ta cas ko as ɗakin ta kullum mai aiki za ta shi ga ta share,sannan mai wanki ta kwashi kayan ta hatta innerwears ɗinta,mai aiki take wanke wa ko al’ada ta yi sai dai mai aiki ta kwashe abin a bayi ta zubar sannna ta wanke.Ta na matuƙar alfahari da gatan da iyayen ta suka bata tare da yi musu addu’a.Mace sangartacciya mai son jiki da hutu da zallar wayewa mai ƴanci wacce rayuwarta a cikin fararen fata ta yi.

Zainab ta na da kyua na nuna wa tare da mannata a hoton irin matan nanne waɗanda ka na ganin su kaga hutu,ko kai mace in ka hansu sai ka yaba.Doguwa fara ga gashi da kyan diri sannan ta na ƙara zuzuta kyanta da mayuka na gyara gashi da fata da kuma sabulai masu tsada.Ita dai ta yadda ta bautawa jikinta ko da za ta karar da wunin ranar ne,shi yasa in ka kalleta dole ka ƙara.

Ta na da girman kai a gurin samari ga ta da farin jini,amma duk saurayin da yazo za tace bai yi mata ba.Mahaifinta ya na matuƙar son yaga ya yi mata aure don ta haifa mishi jikoki,shi yasa kullum yake lallashin ta akan ta fidda miji daga cikin yaran masu da shi da alhazawan da suke neman ta,amma taƙi ita ganin ta aure taƙurawa rayuwar tane.Tafi son rayuwar hutu da jin daɗi sannan ba ta son taƙura da shishshigi ga lamarin ta.

Abin da ƙara tsoratar da ita ganin ƙawarta Nihal da ta yi aure shekara ɗaya da ya wuce.Ta na da kyau da gayu,amma tun da ta yi aure ta haihu ta zama ƙatuwa ga tumbi da ta yi,sannan ƙirjinta ya zube,kullum cikin aikin yara ko a gurin aiki ta rage ƙokari,ga takurawa ɗan tiktok ɗin da take yi mijinta ya hana.

Wannan dalilin yasa ta ƙara tsanar aure ta na gani kamar koma baya ne a rayuwar ta,ganin mahaifinta na da kuɗi kuma ita ma ta tara kuɗin da za ta ɗauki nauyin kanta.Ta saka ma ranta ba za ta yi aure ba,in ma dole sai ta yi aure to ba za ta yadda ta haihu ba kawai za ta yi rayuwar hutu ne don gani take kamar tara yara wahala ce gata likita kuma bata son jikin ta ya canza.

Duk mazan da suke zuwa gun ta kullum cikin kushe su take yi ta na yi musu wulakanci,kuma in auren za ta yi tana son namji mai kyau wanda ya fita gayu da tsafta.Ba ta taɓa jin soyayyar wani a cikin zuciyar ta ba,shi ya sa take wulaƙanta duk wanda ya zo gurin ta.

Kwasam!Ta haɗu A.m a ranar wata daren alhamis da misalin ƙarfe shidda saura kwata agogon birnin a ƙasar London,ta raka yar gidan ƙanwar mahaifiyar ta siyo kaya.Suna zaune a cikin jirgin za su dawo A.m ya shigo hannunsa riƙe da waya da cingam a bakinsa ya na taunawa a yangace.A.m na son cin cingam kamar mace hakan ya samo asali ga matar Alhaji Sama’ila da ta rike shi ta na son cin cingam.Hausawa sun ce zama da maɗaukin ƙanwa shi ke kawo farin kai.Aiko haka ta kasance A.m ya koya cin cingam a gurin ta duk lokacin da ya ci abinci ko ransa yake a ɓace,sai ya huce a kan cingam ɗin.

Ran shi a ɓace yake akan taron da suka yi da safe a companin su,sam yadda yaso taron ba haka ya kasance ba,wannna dalilin ya saka shi baro London bai kammalla abin da ya kawo shi ba.

Ya shigo cikin jirgin fuskar sa kamar an yi mishi mutuwa,bai kalli kowa ba sai kujerar sa da ya nufa ya na murza tafin hannun sa tare da tauna cingam ɗin da ƙarfi saboda fushin sa ya ragu.

Wani irin kallo ya watsa mata ganin ta zauna masa a kujerar sa,da fari ya ɗauka makauniya ce saboda kowa da numbar kujerar sa amma ganin ta na riƙe da waya sai ya daka mata tsawa da ƙarfi yace.”Za ki iya tashi a ƙujerata ki nemi taƙi tunna baki je makaranta balle kin san yadda ake irga numbobi.”

A hatsale ta miƙe tare da faɗin.”What.”Ita sai yanzu ta kula ba’a gurin ta ta zauna ba,saboda hankalin ta na kan wayar ta sanda ta shigo.Ranta ya ɓace jin kalaman sa sai kawai ta ɗaga hannunta da nufin ta wanka ma mutumim da ya kira ta jahila mari,sai ya banbance waye ke da jahilcin atsakanin shi da tunna idanunsa sun kasa gane mishi wayayya mace mai a aji da class,wacce take tashe a tiktok.

 

Zainab ta sauke hannunta a hankali jikinta ya yi sanyi matuƙa ganin matashin saurayin da ya kafa mata manyan idanunsa ya na kallonta,cikin zafin rai a yadda idanun sa suka nuna jira yake ta mare shi ƙila ball zai yi da ita yadda ya haɗe fuska.

Ta shiga in ina ta na ƙoƙarin matsawa daga gurin ya tureta ya na faɗin.”Matsalar ƴan matan bahaushe kenan daga sunga sun fita waje su dinga nuna isa.Da kin mare ni wallahi sai na yanke duk yatsun ki na kai ma karan gidan mu nan gaba sai na ga da wane hannun zaki yi mari.”Ya ja tsaki tare da zama ya maƙala earpis a kunninsa tare da harɗe hannun sa duka a ƙirji,zuwa can ya cire earpis ɗin ya lumshe idanunsa.

 

 

Kar dai ku manta sunan labarin “SAKACINA KO HALIN MAZA” Mu haɗu a shafi na huɗu dan har yanzu shinfiɗa ne har ba’a fara ba.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

 

 

Kuma a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.

Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA’IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

 

 

 

 

*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*

[29/09, 10:10 pm] +234 803 192 1625: *SAKACINA KO HALIN MAZA?*

 

 

 

*RUBUTAWA:-*

*JAMILA LAWAL ZANGO*

 

*SADAUKARWA GA:-*

 

*SUMMY M NA’IGE*

_(Aminiya)_

 

 

*FIRST CLASS WRITER’S ASSO….*

 

*SHAFI NA HUƊU*

 

Jiki a sanyaye ta koma kujera ta zauna ta na jin wani shauki ya na ratsa bargon jikinta,hannu ta sa ta share zufan goshin ta tare da jingina kan ta da bayan kujera ta na kallon sa cikin wani irin yanayi.Ganin halin da ta shiga Imsal ya matso dai-dai kunninta tace.”Gaskiya gayen ya na da kyau sosai.”

Zainab ta ƙara lumshe idanunta ta na kallon shi ba tare da tace mata komai ba,amma ta na jin wani girmar lamari a tare da shi,zuciyar ta ta na bugawa da sauri-sauri haka bugun ƙirjinta.

A lokacin da jirgin ya fara tafiya Zainab ji take kamar ta je gurin sa ta yi mishi magana,ji take komai na ta ya sukurkuce,amma ganin yadda ya ɗaure fuska idanunsa na rufe ya sa taji karayar zuciya.

Wayarta ta ciro ba tare da ya sani ba ta dinga ɗaukar sa hoto,ta na turawa ma ƙawayen ta da ta yi saurayi.Ko da suka iso Nigeria bai kalli in da take ba,ya na janye da troley ɗin sa hankalin sa na kan A.k da yazo ɗaukar sa.

Da sauri ta ƙarasa gurin sa tare da shan gabansa saura kaɗan ta faɗi,amma ba ta kula ba ta tsaya ta na mishi murmushi mai ɗaukar hankali.

A.m ya juya bayan sa ya na kallo a tunanin sa wani take ma murmushi a bayan sa,don shi sam ba yarinyar ba ta yi mishi ba,saboda tsiwarta sannan shi a wannan lokacin babu so a tsarinsa,bai shirya aure ba duk da burin iyayen sa kenan.

Kallo ya bita da shi tun daga saman ta har ƙasa ta na da kyau shi ma ya san haka,amma hakan bai wani dame shi ba kasancewar ya sha haɗuwa da mata kala-kala.

Wani ƙarin murmushi ta ƙara saka mishi tare da bin sa da sauri ganin ya fara tafiya.”Don Allah ka tsaya ina son magana da kai,in ba damuwa ina son mu ƙulla abota.”Ta faɗa tare da miƙa masa hannunta .

Wani ban zan kallo ya yi mata mai kama da ya ga kashi yaci gaba da tafiyar sa ba tare da yace mata uffan ba.Jikinta ya yi sanyi ta na tsaye ta na kallon shi har ya shige cikin motarsa,wanda A.k ya tuƙo don ya ɗauke sa.Da idanunta da suka canza kamar za ta zubda ƙwalla ta kalli bayan motar.

TURAKI FAMILY

Abin da taga an rubuta keman a bayan motar wani irin farin ciki ta ji ganin A.m ko ɗan waye,sai murna ya kama ta sosai tasha jin mahaifin ta na waya da wani daga cikin family ɗin.Ba ta son wulakanci sannan ta sha wulaƙanta maneman ta,amma wannan karan ta na ji ranta sa samu kalan mijin da take so.

Ko da ta isa gida tunanin wannan kyakykyawan saurayin ya tsaya mata a zuci,da ta rufe idanunta kyakykyawar fuskarsa take hangowa.Tun kafin Abban ta ya dawo ta kira tare da bashi labarin saurayin da ta haɗu da shi,kuma ya tafi da imanin ta.

Dariya ya yi sosai kin yadda ta ruɗe akan shi ta na mishi shagwaba da ƙyar ya samu ya lallasheta,ta kashe wayar ta bayan ya yi mata alƙawarin gane ko waye daga cikin family Turaki saboda ya san Alhaji Sama’ila abokin cinikayyar sa ne.

Ko da ya dawo gida haka ta sa shi a gaba ta na ta yi mi shi magiya,har ya gaji da ƙorafin ta ya kira Alhaji Sama’ila.

Bayan ya gaya mi shi dalilin kiran sa dariya sosai tare da farin ciki ya yi,a ransa ya na roƙon Allah ya sa A.m ya so Zainab ko ba komai ya yi dacen mace,sannan zumuncin kasueancin su zai ƙara ƙarfi.

Duk yadda Abba ya yi da ita kan ta haƙura da numbar A.m da ta kafe sai an turo mata,amma taki daga ƙarshe kan dole ya ƙara kiran Alhaji Sama’ila ya turo mi mi shi da numbar.

Da gudu ta ruga cikin ɗakin ta da wayar ta a hannunta bayan ta kwashe numbar a wayarta.Kan gadon ta ta faɗa ta na ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske ,tare da ƙanƙame filo a ƙirjinta.

Ran ta ya fara ɓaci ganin ta yi kira ya kai sau biyar ba’a ɗaga wayar ba,da ga ƙarshe sai ta ji an kashe wayar jifa ta yi da wayar ta ta zauna akan gadon ranta a jagule.

Ko da Alhaji Sama’ila ya tare shi da zancen yarinyar da suka haɗu a jirgi,nuna ya yi bai gane ba in ma ya haɗu da ita ya manta.Ganin kauce-kaucen da yake mi shi sai ya yi masa umurni da yaje ya ganta ya na son ya nemi aurem ta.

Babu yadda A.m zai yi ba tare da ya so ba ya amince duk da a wannan lokacin ya fara tunanin lokaci ya yi, da zai yi aure ya huta da damun da iyayen sa suke mi shi a kan ya yi aure sannan ya na buƙaƙar ya ga yaransa ga ƙaninsa ya na da biyu.

Da wannan tunanin A.m ya amince ya je gidan su Zainab tamkar za ta yi hauka haka take ji a ranta,da ta gan shi ruɗewa don Allah ya saka mata son shi a birnin zuciyar ta.

Tun ya na share ta har ya bada kai bori ya hau.Zainab ba ta a cikin matan da namiji zai wulaƙanta ita kanta ta na alfahari da hakan.Haka suke shan soyayyar su kullum suna maƙale da waya ana ga ya ma juna kalamai so.

A hankali A.m ya fara jin tsanar wasu daga cikin halayan Zainab,musamman yanayin shigar ta da tsabon son jikinta,sannan shi namiji ne mai son mace wacce ta iya girki amma tunkafin su yi aure ta gaya mi shi ita ko ƙafar kicin ba ta shiga.

Dariya ya yi kawai don ya yi tunanin tsokanar shi take yi ganin ta wayayya mai aji,ya san babu yadda za’a ta bari ƴar aiki na yi mi shi girki,ko a gidan su Amminsa take mi shi abinci.

Haka dai aka dinga cin soyayya har Allah ya kai si ga aure.Bayan an gama shagali amarya ta tare a ɗakin mijinta.Shi kaɗai ya shigo bai nemi rakiyar kowa ba,ko A.k daga kofar gida ya tafi ya na ta mishi dariya.

Da gudu ta taso ta rungumshi ya janye ta jikinsa,kasancewa wannan ne karon farko da mace ta rungume shi,idanunsa ya kafa mata duk rashin kunyar ta sai ta ji ta kasa haɗa ido da shi ta sunkuyar da kanta.

Bayan sun yi sallah sun ci kayan daɗi da ya siyo musu,suka tsunduma kogin soyayya.Wani irin tarairayan juna suke yi ma junansu A.m bai san ya kamu da soyayar Zainab ba sai da ya aure ta yake jinta a zuciyar sa.Koda yaushe suna maƙale da juna in ba shi a gida suna kan waya.Ya na matuƙar ji da ita ba ya son ɓacin ranta.

Abu ɗaya da ya fara kawo musu cikas yadda Zainab take son jiki komai suka yi amfani da shi,a nan za ta barshi sai in shi ya ɗauke da fari abin bai dame shi ba,amma daga bisani sai ya ji ya na taɓa zuciyar sa.

Kusan shi yake ɗan wasu aikace-aikace na gidan.Sati biyu da auren su mahaifiyarta ta kawo mata masu aiki mata guda biyu.Da fari A.m yaƙi amincewa amma daga kan dole ya haƙura,saboda yadda shaƙar numfashin gidan yake son ya fi ƙarfin sa.Hankalinta kwance ta ci tasha ta tafi gurin aiki.Hakan bai wani dame shi ba saboda ya na matuƙar sonta.

Kamar yadda Zainab ta tsara ba tare da ya tsani ba take shan maganin ha na ɗaukar ciki a ɓoye,ba ta damu da mai zai faru ba duk da ta san illar sa musamman da take likita,amma yadda A.m yake yaba halintar ta ya sa take shan maganin don ba ta son canjin jikinta.Kuma mafiyawancin family ɗin su suna da ƙiba.

Tsaye yake a gaban madubi ransa a jagule ya na kallon kansa a madubi,zuciyar sa babu daɗi.Matuƙar yunwa yake damun shi amma ba ya son cin abincin masu aiki,saboda daɗin shi bai kai na amminsa ba ya na jin kunyar zuwa ƙarɓo musu abinci,wanda ita Ammin da kanta tace ya kama ta su fara girki saboda ta gama kawo musu na amarci,in bai manta ba rabonsa da abinci tun daren jiya da ya ci a gidan A.k.

Ya ɗauki kum cikin ɓacin rai ya na tunanin bayan ya na matuƙar kiahin Zainab,sannan ita ba ta da kiahin kanta don ko masu aikinta mata yadda take fito musu kamar tsirara ya na bashi haushi amma ita ko a jikinta.Da namiji zai ɗauko kuku ya dinga mishi girki.

A hankali ya ji an turo ƙofa an shigo wani ɗan murmushi dole ya yi mata ya na jiran ta ƙaraso,amma sai ya ji an yi shuru kamar ba’a shigo ba idanunsa ya ɗaga da nufin ya kalleta yau yangar ce ta motsa.

Sai ya ga mai aikin su wacce bai ma san sunan ta ba tsaye ta na kallon ƙirjinsa ta na lashe baki,idanunsa ya kai kan jikinsa tare da jin kunya don daga shi sai ɗan tawul iya gwiwarsa.”Ke!Uban me kike kallo ƙazama kawai?”Yace da ita ran shi a ɓace ganin yadda take kallonsa kamar wata mayya.

Da sauri ta matsa cikin tsoro muryar ta na rawa tace.”Madam ce ta bani umurnin na shigo na share ɗakin.”Ta ba shi amsa tana jin wani lamari dangane da shi.

“Tunna kin ga da mutum ba sai ki fita ba,banza mayya kawai.”Yace da ita bayan ya ƙara daka mata wani tsawan,da sauri ta fice har ta na buge kanta da ƙofa.

Ya zama dole na ɗauki mataki ba zan lamun ce da waɗannan ƙazaman arna suna shigo mim ɗaki ba,gajerun wandunan sa ya kwashe ya saka a sif ɗin sa ya na takaici don ya san masu aiki suka wanke.

 

 

Kar dai ku manta sunan labarin “SAKACINA KO HALIN MAZA” Mu haɗu a shafi na huɗu dan har yanzu shinfiɗa ne har ba’a fara ba.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

 

 

Kuma a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.

Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA’IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

 

 

 

 

*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*

[29/09, 10:10 pm] +234 803 192 1625: *SAKACINA KO HALIN MAZA?*

 

 

 

*RUBUTAWA:-*

*JAMILA LAWAL ZANGO*

 

*SADAUKARWA GA:-*

 

*SUMMY M NA’IGE*

_(Aminiya)_

 

 

*FIRST CLASS WRITER’S ASSO….*

 

 

*SHAFI NA BIYAR*

 

Juwairiya zaune a gefen Mama ta na yi mata kitso,Ibrahim ya na zaune a gefenta ya na wasa.Baba ya buɗe labulen ɗaki ya fito dai-dai lokacin da Baba Sani ya kwaɗa sallama daga nesa da su.Ganin sa Juwairiya ta zabura kamar za ta gudu,tun lokacin abin ya faru ta ƙara matuƙar tsoron shi ganin shi take kamar kumurci.

 

Baba Sani ya kalle ta da wani irin kallo wanda shi kaɗai ya san ma’anar sa,sannan ya miƙa ma Baba takadda yace.”Gashi na gaji da biyan kuɗin wuta ni kaɗai,yau za su zo ka biya ko kuma a yanke na ka.”Ya faɗa ya na kallon bangaren Juwairiya da ta rintse idanunta tun bayan da lamarin ya faru ta yi katanga da shi,ko ina ba ta zuwa islamiya ma ta haƙura gara ta din ga zama a gida da ta gan shi.

 

Baba ya yi kasaƙe ya na kallon sa na tsawon lokaci sannan yace.”Ka sa su yanke nawa in dai baza ka iya biya ba,bani da shi kuma na ga ko waya babu wanda yake da shi a cikin mu hasken kawai muke amfani da shi.”

 

” Oho ko ma me zaka ce kace na gaji da wahala.”Ya sa kai ya fice ya na bambami.

” Ikon Allah na rasa me ke damun shi ya canza gabaki ɗaya.Allah ya ganar da shi.”Yace sannan ya ɗauki gatarin sa ya fita.Juwairiya ta yi shiru ta na tunani a ranta zuwa can ta miƙe tare da shiga bayi ta saka kuka.

 

Mama ba tace komai ba illa baƙin cikin halin da yake nuna musu,wanda ta san tsananin ƙiyaryarta ya sa yake nuna musu hakan.Idanunta suka kawo ruwa amma sai ta yi ƙoƙarin sharewa,ba tare da Ibrahim ya gani ba.

 

Juwairiya ba ta fito ba sai da ta sha kukanta ta ƙoshi sannan ta wanke fuskarta ta fito,a ranta ita kaɗai ta san halin da zuciyarta take ciki.Duk da Mama ta gane kuka ta yi ba tace mata komai ba,domin ita ma da za ta samu dama kuka za ta yi ko zuciyarta ta rage raɗaɗin damuwar da take ciki.

 

Yanayin rayuwar da Juwairiya take ciki babu daɗi ji take kamar ta na rayuwa a gidan kurkuku!Kusan kullum sai ta yi kuka ta na matuƙar bakin cikin halin da iyayenta suke ciki,burinta bai wuce ace ta samu aiki ta na taimaka ma iyayenta ba.

 

Tsakanin ta da Baba Sani tun faruwar lamarin take jin wani tsanar sa mai tsanani ya na ƙara shiga cikin ranta,ko muryar shi ta ji sai ta yi ta’awizi a cikin ranta tsananin mamakin mugun halin sa take.

 

Duk yadda ta so ta taimaka wa iyayenta abin ya ci tura har takai su kwana basu ci ba,tashin hankalinta yadda Ibrahim yake yi,amma ƙiri-ƙiri Baba Sani ya hana matar sa basu abinci.

 

Ganin halin da suke ciki wani lokacin ta yi kuka kamar numfashin ta zai rabu da gangar jikinta.

Mahaifin Juwairiya na tsaye ya rataye gatarin sa a kafaɗa hankalinsa baya jikinsa,tunani yake sosai a cikin ransa ga wata irin yunwa dake ƙwaƙularsar.Tunani fal a cikin ransa ya na tunanin kuɗin aikin da za’a yi ma Ibrahim aiki a ƙafar sa.

 

Ya daɗe a tsaye ya na tunanin mafita daga bisani yaci gaba da saran iccen da yake yi cikin rashin kuzari,tare da rashin madafa sai tsaƙa da warwara yake a cikin zuciyar sa.

 

Ya ɗaga gatarin sa a sama ya na can ya na tunani bai ankara ba sai ji ya yi gatarin ya dawo tsakiyar kansa! “Innalillahi wa inna ilaihir ra ju’un.”Iya abin da yace kenan ya zube a ƙasa a sume jini na ta zuba kamar famfo!

 

Hankalin Malam Audi dake gefen icce ya na bayar da iccen ya fahimci abin da ke faruwa, da sauri ya iso garesa ya na salati cikin tsananin razana tamkar zai fasa ihu ganin halin da yake cikin.

Mutanen dake gurin suka yo kansa suna salati ganin abin da ke faruwa,kama shi suka yi aka saka shi a cikin mota suka nufi a sibiti da shi.

 

Lokacin da labari ya riske Juwairiya hannunta saka a ka sai kuma ta yi ƙoƙarin daƙile zuciyar ta da take ninyar kwarma ihu,ta fara salati ta na faɗin.”Inna lillahi wa inna ailaihir raji’un.”Sai hawaye bayan ta yi nasarar faɗin haka ta yi koyi da faɗe na ubangiji da ya umurci bayin sa da su faɗi haka duk lokacin da wata musiba ta same su.

 

“Wayyo Allah rayuwa ta me ya sa daga wannan sai wannan?”Ta tambayi kanta cikin tsananin ruɗani.Gabaki ɗayan su sun ruɗe ganin halin da yake ciki kai ya kumbura kamannin sa ya canza,sannan an ɗaure kansa da bandeji duk ya ɓace da jini.

 

A lokacin da suka je ko magana baya yi idanunsa a rufe ba ya iya ko buɗe idanunsa,daga ganinsa ya na cikin wani hali babu alamun numfashi tare da shi sai bugun numfashin sa da yake sauka a hankali a cikin tsananin wahala.

 

Rintse idanunta ta yi a jikinta take jin kwatankwacin zafin ciwon dake jikin Baba,ta kasa kuka sai hawaye da yake gasar sauka a ƙuncinta ba tare da sanin ta ba.

 

Suna zaune har tsawon wani lokaci amma bai farka da ga baccin da yake ba,saboda allurar baccin da aka yi masa.Har misalin tara na dare sai a lokacin Baba Sani ya shigo ya na ta zare ido,a cewar sa yanzu ya dawo gida ya ji labari.

 

“Ni na rasa wannan lamari na ka Yaya kamar wani mai bakin uwa,kullum rayuwarka ƙara taɓarɓarewa take.Haba wannan wane irin musifa ne! Tun ba yau ba nake maka maganar kabar yin faskare amma kaƙi ga shi nan abin da ka jawa kanka.”

 

Ire-iren kalaman da yake faɗi kenan ba tare da nuna tausayi a fuskarsa ba,sai dai nuna rashin damuwa da faɗin maganganu mara tsari.Juwairiya da ta kifa kanta da akan gadon asibitin ta na wani irin kuka.

 

Hankalin su ya yi matuƙar tashi ganin halin da yake ciki,Juwairiya kamar ta mutu haka take ji,ƙiri-ƙiri in aka buƙaci kuɗi Baba Sani yake ƙin bayar ba kullum da uzurin sa da yake faɗi.

 

Da ga baya Baba Sani yake zuwa ya na kwana da Baba.Baba Sani tsaye akan Yayan na sa da misalin ƙarfe ɗaya na dare,kallon sa yake da mugun nufi a ransa.Filo ya janyo tare da danne masa kai.

 

Allah Sarki bawon Allah da yake kwance a cikin mawuyacin hali ya fara mutsu- mutsu da ƙafafun sa,bai jima ba ya yi dip alamun babu numfashi a jikinsa.

 

” Gara ka mutu kowa ya huta kullum cikin wahala nake da kai da iyalan ka,sannan ɗan buƙata ta da nake son na biya na rasa.Kaje kawai Allah ya haɗa mu a kiyama!Abin da yace kenan ya kwanta da ninyar da safe ya fasa ihun ya mutu.

 

Washegari da safe Juwairiya tun da asuba take azalzala wa Mama da su je asibiti,irin mugayen mafarkin da take yi akan mahaifinta ya sa hankalinta ya tashi sosai.Mama ce ta ɗan ƙarfafata har suka dama koko suka sha,duk da dai Juwairiya ƙurɓar kokon take wanda ko siga babu hankalinta na gurin mahaifinta.

 

Ko wanka ba ta yi ba ta ɗauki ruwan kokon ta na addu’ar Allah ya sa ya iya sha,Mama dai ba tace mata komai ba duk da ranta babu daɗi.Ko da suka isa asibitin gaban Juwairiya ya yanke ya faɗi ras!Sai ta kira sunan Allah ta riƙe kofin kokon ta na wani irin tafiya zuwa ɗakin da yake tamkar wacce ƙwai ya fashe mata a ciki.

 

Gabaki ɗayan su suka yi mutuwar tsaye ganin Baba Sani tsaye, a ɗakin ya ɗora hannu a kansa ya na ƙwala ihu, da kuruwa tamkar yadda jahilan farko suke yi yayin da wata musiba ta afkawa ɗayan su.

 

Sautin kukan sa yake tafiya tare da bugun zuciyarta,ta rintse idanunta ta na addu’ar kar Allah ya sa mafarkinta ya zama gaskiya!In kuma da gaske ne ya za suyi da rayuwar su a duniya bayan ba mahaifin su?

 

Sai kawai ta fara ja da baya ta na girgiza kanta tare da nuna mahaifinta, ta na faɗin dai-dai lokacin da Mama ta saka kuka domin ta tabbata ya riga mu gidan gaskiya.”A’a bai rasu ba wallahi mafarki ne!Don Allah kar kuce min mafarkina ya zama gaskiya.Mahaifina ya na raye bai mutu ba.”

 

Sai ta ruga za ta fita waje tashin hankalin ta ta ya ya mahaifinta zai mutu ya bar ta da azzalimi!Mutuwar sa na nufin ya yi nasara akan ta zai cika mummunan nufin sa kenan?

 

Kar dai ku manta sunan labarin “SAKACINA KO HALIN MAZA” Mu haɗu a shafi na huɗu dan har yanzu shinfiɗa ne har ba’a fara ba.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.

 

 

Kuma a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.

Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA’IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.

 

 

 

 

*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.