
Sakayya Hausa Novel Complete
Tag: SAKAYYA!!!
( A touching heart story)
Written by gimbeeya
(Mss 1love )
Page 1-5 !
Da sunan Allah me rahama me jin kai ,tsira d aminci su qara tabbata agun annabinmu Muhammad saw ,yacce na fara rubuta littafi nan Allah yabani ikon gamashi lapia Allah yasa mu amfana d saqon dayake ciki Ameen !!!!
————-tindaga inda yake zaune akan sallaya yake jiyo qamshin turarenta me dad’in qamshi da d’aukar hankali,riga d siket ne ajikinta na atamfa wanda yay matuqar amsar jikinta se d’an qaramin veil data yafa ,yayinda take qoqarin maqala jakarta tana cewa ” to nide na fita sena dawo ”
Kallon sama d qasa ISHAQ yamata yace “haba zahra’u shin kinmanta da cewa Ke matar aure ce ,yanzu da wannann shigar zaki fita,sannan inaso nasan ina zaki ???dannasan cewa ba inda kika sani a garinnan ,yau kwana nawa da Allah ya yayemiki jarabtar da ya d’oramiki ? Yanxu …..
aikafin ya rufe baki zahra ta dakatar dashi da cewa “Kaga ISHAQ dakatamin tsawon shekaru d’ai-d’ai har ashirin da uku bana ganin komi aduniyarnan se duhu,yanxu kuma d Allah ya yayemin se ahanani ganin duniya kafiso naita zama awannan gidan qasan!! Ina fama da murhu da ice wanda hayaqinsama kad’ai ya isa yamaidani gidan jiya,dan haka yanxu idona ya bud’e Kuma ba wanda ya isa ya hanani naga duniya ,duniya taganni,idan kaga dama ka zauna dani,inbakai niyyaba Kasan abunyi “daga haka tafice ji kake bammm taja qofa wacce takusa karyewa tinda dama qofar ta langa-langa ce .
Wani irin hawayene me d’umi ya sauka a idon ishaq,zuciyarsane Ke masa wani irin suya,ahankali yadafe saitin zuciyarsa tare da rintse idanunsa,nan take kwakwalwarsa tafara tariyomasa rayuwar baya alokacin da ya Kyalla ido yaga Zahrau.
SHEKARU 8 DA SUKA WUCE…
Zaune suke ashagon d’inkinsu shida abokinsa sun duqufa akan aikinsu ganin sallah ta matso ga d’inkunan mutane ahannunsu,jin yatsaya da takun keken yasa faisal kallonsa inda yaga ya kurawa bakin shagonnasu ido juyowa yay domin yaga abunda ya d’aukemasa hankali,wannna makauniyar yarinyarce tareda qanwarta inda take riqe da hannunta yayinda d’aya hannun sandace take laluba hanya da ita,juyowa yay da kallonsa wajen ishaq yaga be d’auke idonsaba har seda suka wuce ,”kai abokina yanxu meye na qurawa makauniya ido haka ??”Faisal yafad’i yayinda yake kuma murzan kan keken d’inkinsa.
“Hmmm wlhy faisal bazaka ganeba yarinyarnan tana matuqar bani tausayi sosai,ba ilimi ba wata rayuwa me kyau ga makanta gata mashalllah kyakkyawa Amma ba idon gani ”
Batare da yad’ago yakallesaba yace “ishaq kenan duk yacce Kaga mutum kabarshi haka yacce Allah yaso yaganshi,komi Kaga mutum ya samu koya rasa ni’imace da Allah yamasa,Allah ne yasan manufar jaki dabe yishi da qahoba kai yacce take da kyannan daba makauniya bace Allah ne yasan…”aikafin ya qarasa ishaq yadakatar dashi “haba faisal kadinga kyautatawa d’an adam zato ni wallahi inaji ma nasamu matar aure ”
“Cafff !! Lalle ishaq bakada hankali makauniyar zaka aura,ai wallahi ko sarauniyar kyauce bazan aure taba wannan ai wahala zaka aura ana aure Dan ahuta taya mutum ze d’akkowa kansa wahala,yarinyarnan kuma tin da aka haifeta bata gani bare asa ran zata warke ”
Ishaq ne yace “koda haka zata mutu bata gani ni zan kula da ita har qarshen rayuwarta,faisal na dad’e ina tausayin zahra,seyanxu nagane cewa tausayin wani reshene daga cikin qaunarta,”
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
Faisal daya sandare saboda tsananin mamaki bayan makantarma qazamar yarinya wanda gidansuma bacin yau bare na gobe Amma ya lura abokinnasa yay nisa bayajin kira shiyasashi cewa “to Allah yabada sa ‘a”
Ranar wata asabar da yammaci sakaliya ,ruwan da akaine yasa unguwar sheshe dake cikin gari yin wani luffff,zaune inna hajara take tana tankad’en fulawa wacce sumayya qanwar zahra take wainar fulawa aqofar gida da magriba,sallama sukaji yaro yayi tare da cewa Wai ana sallama da zahra’u,inna hajara dake tankad’e d sauri ta d’ago kai dan maganar ta girgizata anyakwa gidannan aka turosa,dan koda wasa bawanda ya tab’a zuwa qofar gidan da niyyar yanason zahra kallon yaron tai tace “jeka cemasa wata zahran?,anyakwa nan gidanne?”
Jimmm kad’an yaron ya kuma dawowa yace “eh nan gidan ne yace zahra’u yayar sumayya ”
Ainan mamaki yakama kowa agidannan abunka da gidan cikin gari gidan yawa,da sauri inna hajara tashiga d’aki tace wa zahra’u ta tashi ana sallama da ita,seda gabanta yace rasss ahankali tace “inna waini ake sallama dani??”
Inna tace “eh,”maza kitashi nan danan inna tad’akkomata hijab tare da d’an shafamata powder da jambaki abinka da kyakkyawa seta qara wani haskawa ,innace tabata sandarta tare da mata jagora zuwa soro.
Har ta fito wajen ta tsaya batasan a inda yakeba d’aya gefen takalla tana “inayini?”ganin haka yasa ishaq saurin dawowa b’angaren yana “lapia lau,yake me hasken idaniya da kyan kallo ”
Murmushi tai dan tinda take arayuwarta ba atab’a yabontaba sedaima amata gori da itad’in makauniyace ,wani dad’i taji aranta tace “shin da gaske idanuwa sunada haske ?”
Yace “matuqar haskema ”
“Sedai bana gani dasu “tabashi amsa araunane
Wani abu yaji yadaki zuciyarsa yarda tai maganar amarairaice,had’iye abun yay yace “innace inasonki zaki amince ki aureni?”
Wani rass taji aranta,inna data lab’e asoro dan taji dame yazo kar acutarmata da ‘ya ganin bata gani aidataji ya ambaci kalmar aure nan take tai sujjada aqasa tana godiya ga Allah harda hawayen farinciki.
“Bawan Allah dan Allah inda wasa kake kagayamin,Taya mutum ze rayu da makauniya,nakasashiya Irina ,ba wanda ze iya d’aukan wannan nauyin se wanda suka kawoni duniya wato iyayena”
Ishaq gyara tsaiwa yay yace “zahra ba maganar wasa amaganarnan ked’in awajena tamkar kowa kike ,mutane Ke ganinki makauniya Amma aguna Ke rayuwatace amincewarki kawai nake nema ,kuma banso ad’au lokaci sosai ”
Nan danan zuciyarta tafara jeromata tambayoyi “Ashe dama za’asamu wanda ze sota??? Ashe dama ita d’in a idon wani tamkar kowa take ??? Ashe de itama zatai aure ?
Muryar sace takuma katsemata tinaninta inda yace “karki damu zanbaki lokaci ki tinani zuwa wnai satin zan dawo ”
Tace “tom badamuwa nagode ”
Murmushi yay duk d bata ganinsa yace “Nima nagode zahra se anjima ki kula da kanki ”
Harya juya zetafi tace “Amma meye sunanka?”
Ataqaice yace “ishaq mukhtar ”
Ahankali ta maimaita sunan ishaq yayinda take qoqarin shigewa gida,inda take ta maimaita sunan tana so ta tina ina taji sunan ,bade shine wanda rahila Ke mutuwar soba,rahilan datake wulaqantata take kyamarta tabbas inshine rahila zata gane cewa makauniya tafita tinda har takasa samun soyayyar shi Amma gashi yazo yana neman ta makauniyar datake kyama!!!!!
Share plx
Leave a Reply