Salon So Hausa Novel Complete
Salon So Hausa Novel Complete
Salon So Hausa Novels Complete
Salon So Hausa Novels Complete
******SALON SO*******
1 to 6
:
:
BY SULAIMAN BOMBOY.
. Kyakkyawar yarinya ce ‘yar kimanin shekara goma
sha bakwai, direbanta ya yi parking da mota ya
zagayo ya bude mata ta fito ta shiga cikin wani
hadadden gida kerarre, ke da kallon tsarin ginin
kin san hoto ne daga kasar waje aka yi irin sa. A
kofar falon ta yi sallama ta shiga. Matar da take hakimce akan kujera cikin tsantsararriyar kwalliya
ta kece raini, tana ta girgiza kafa da wayar sadarwa
a hannunta da take hira.
Tana ganin shigowar yarinyar ta dire wayar cikin
fara’a ta tare ta, tare da cewa, “A’a Jawahir ‘yar
Dady yau a gari? Ko dai batan kai kika yi ne?” Jawahir ta yi murmushi yayin da ta durkusa
gabanta ta ce, “Aunty ina yini?”
“Lafiya lau Jawahir, amma dai a nan za ki kwanar
min ko.? Tun da gobe ba ku da makaranta.”
Jawahir ta yi dariya tare da cewa, Tafiya zan yi
Aunty yau Dady zai dawo daga saudiya, da kuma ya dira a kasar nan ni zai fara tambaya, kuma ni
ma ba zan so ya dawo ba mu hadu ba.
Aunty ta yi murmushi ta ce Jawahir gidan Daddy
ke dai kullum kina like a gida kamar daddawar
daka ba kya son zuwa ko ina ko?” Amma zan je na
samu mommy dinki na ji ko ita take hana ki zuwa.”
Jawahir ta yi murmushi, “Wallahi Aunty babu rawan
mommy Daddy na ne baya son na rinka fita.
Sallamar da ta ji ce ta sa ta yin shiru, sai da aka
amsa masa sannan ya shigo. Ya zauna a kan kafet
tare da rissinawa ya gaisar da Aunty. Aunty ta amsa cikin kulawa ta musamman ta kalle
shi ta ce, Ba dai har ka dawo daga office din ba?”
“Wallahi Aunty vacci nake ji shi ya sa na taho gida
don na kwanta na huta.”
Aunty ta girgiza kai tare da cewar, “Ba ka kula da
bakuwa ba ne?” Sai sannan ya kalle ta ya ce, “Wallahi ai kamar
jawahir ko.?”
Au ka mance ma?
To ita ce, Jawahir ta dan rissina ta ce, “Yaya
Haidar ina wuni?” Ya amsa cikin kulawa sannan ya
ce, “Ya su Dady?” “Daddy ba ya kasar, yau dai muke sa ran
dawowarsa.”
“To Allah ya dawo da shi lafiya, Abin da Haidar ya
ce kenan ya mike ya nufi sashensa.
Jawahir ta mike Aunty zan tafi” “Haba jawahir har
tafiya zaki yi.?” “Wallahi Aunty tafiya zan yi doki nake yi ne na je
na fara shirin tafiya taryar Daddy.
“To ‘yar Daddy ki gaishe min da shi, kafin na zo
gobe yi masa sannu da zuwa. “Ta fito da sauri,
direbanta ya karbi kayan da yake hannunta ya
zuba a but ya bude motar ya shiga ya tayar suka miki
hanyar gida
Littafan Hausa Novels Guda 1000 masu dadi
Matar Makaho Complete Hausa Novel
Hotunan Lalle Masu Kyau Kunshin Gam
Hajiya Gwale Hausa Novel Complete
Tsofaffafin Hausa Novels Watpadd
+++++++++++++++++++++
Alhaji Ibrahim shine mahaifin Jawahir, mutumin
kirki ne, akwai shi da son jama’a ga yawan
kyautatawa na kasa da shi, sam ba shi da kyamar talaka. Yana da dadin zama idan ka kiyaye
abubuwan da ba ya so, na farko ba ya son raini,
kuma shi kaifi daya ne, in dai ya ce, “I, ko “A’a”
to ba wanda ya isa ya tankwara shi sai uwarsa.
Su uku ne a wajen iyayensu, shi ne babba sai Aisha
wato Aunty babar Haidar sai Aminu, wanda shi ne autansu.
Ubansu da suke kira da Baffa ya dade da rasuwa
sai mahaifiyarsu Rahmatu da suke kiranta
Inna mace ce mai kirki da hakuri ga ta da son
zumunci, duk inda aka ce ga dan uwa ko ta yaya
suka hadu ta jawo shi a jiki ita bare ma jawo shi take yi don ya zo ya ci arzikinta.
Tana zaune a unguwar sabon tatin mandawari.
Tana matukar son jawahir don a cikin jikokinta
babu wanda ya kama kafar son da Inna take yi wa
jawahir. Alhaji ibrahim matarsa daya Hajiya Hafsatu,
ita ce mahaifiyarsu Jawahir, suna ce mata Mommy.
Mommy tana da ‘ya’ya shida biyar maza daya
mace. Akwai Abba me sunan kakansu sai
Abdullahi, sai Nasir, sai Jawahir da Auwal da Sani.
Jawahir ita ka dai ce mace a gidan, kowa ji yake da
ita ba ma kamar Alhaji ibrahim da yayyanta. Suna son ta suna shagwabata amma duk da haka
ba ta sangarce ba don tana tsoronsu tana kuma
jin maganarsu.
Jawahir yarinya ce kyakkyawa tana da hankali da
nutsuwa akwai ta da biyayya ba ta da rowa. Sai dai
miskila ce ba kowa take iya sakewa da shi ba, ba ta fiya son magana sosao ba, in kinji hirarta
ce ne da Daddynta ne ko yayyanta sai mommynta,
to shi ne za ki ji har da dariya.
Amma shagwababbiya ce ta kin karawa don ita har
kannanta Auwal da Sani shagwaba take yi musu
bare kuma su Yaya Abba da uwa uba Daddynta. Bayan Auwal ne ya dauke min babban turarena da
ya fi kowanne tsada.
Shi ne kike kuka? Rabu da shi zai gamu da ni ne
je ki cikin dakina kan mudubi ki zabi wanda kike
so share hawayenki ki yi dariya. Ta fada dakin
Dady da gudu tana murmushi yaya Abba ya ce, Su jawahir sarkin rigima. Shi kuwa
Haidar a zuciyarsa cewa ya yi, Kai wannan yarinyar
tafi ya shagaba shi ya sa take ba ni haushi sai na
ga kamar na doke ta in ana lallabata. Yarinya sai
shagwabar tsiya sai ka ce ita ce Auta.” Tunaninsa
ya katse ne a dai dai lokacin da jawahir ta fito daga dakin, hannunta rike da sunkumemen turare.
Ta nunawa Dady ta ce, Dady ga shi na dauka.
Yace, “To ‘yar Dady ya yi miki wannan din?” Ta
daga kai, “To maza ki je ki boye abunki ki ta
fesawa. Ta durkusa fuskarta cike da murmushi ta
ce,Na gode Dad Allah ya kara girma, Ya shafa kanta yana murmushi ta yi waje a guje.
Takaici ya cika Haidar a zuciyarsa ya ce, Ya za a yi
ma wannan ‘yar yarinyar a ba ta wannan turaren?
Ya za ta yi da shi? don kudinsa wajen dubu goma
sha biyar ne,to ita ta san darajar kamshin ne ma.
Yanzu haka wasanta za ta yi da shi kawai. Yaya Abba ya girgiza shi tare da fadin, Haidar me
kake tunani ne? ko ka tuno America ne? da yake
tare suka yi karatu a can shi da Haidar din.
Dariya suka yi suka tafa.
Kiran sallar da aka yi ne ya sa su tashi don zuwa su
ba da farali. To irin wannan halayyar ta Haidar ita ce take bawa
jawahir haushi don haka ko gidansu ya zo ba ta
kula shi karkari ta ce masa ina wuni ta wuce shi
ba tare da ta jira amsarsa ba. Dan mulki kenan.
Ita jawahir duk da miskilancinta ba ta da daukan
kai kuma akwai ta da yi wa mutum murmushi tana da halin kyauta duk inda ta ga talaka ko
kaskantacce in dai ta san mai bukata ne, to za ta
gayawa Daddy ya taimaka musu.
wannan halayya tata ita take kara sa kaunarta a
zuciyar Daddynta. Kamar yau da safe jawahir ta
gama baccinta ta fada toilet a yi wanka ta fito ta tsaya gaban mudubi aka
shiga kalailayar jiki, a shafe nan a goge can, ta
tsara kwalliyarta cikin boyal shudi rigar fitet da
zane ta sa hadadden fashion dinta yari da sarka da
abin hannu me shudin dutse, Daddynta ne ya siyo
mata daga london. Ta hadu iyakar haduwa fuskar tata sai sheki take yi
ta feshe jikinta da turaruka ta fito ta nufi sashen
Dady.
Ta kwankwasa ya yi mata izini ta bude ta shiga.
“A’a ‘yar Dady kwalliyar ta yi miki kyau, Ta yi
murmushi ta durkusa ta gaishe shi, “Don Allah Dady ina so yau zan je gidan Inna.
“Kin sani jawahir ba na so ki rinka yawan fita
amma tun da gidan Innata za ki je ba komai sai ki
je.
To me za kaiwa Innan? Jawahir ta dube shi tana
murmushi ta ce, Dady duk abin da ka ba ni.
To shi ke nan ‘yar gidan Dady, daman ke ake jira
tashi mu je a yi brek.
Mominta ta fito daga cikin dakin Dadyn cikin
rantsatsiyar kwalliya kamar me shirin zuwa fati.
Jawahir ta yi saurin zubewa ta gaishe ta, mommy Daddy ya bar ni zan je gidan Inna
Ta ce, “Yauwa koke fa, ai gwanda ki je kusan
kullum Inna sai ta yo miki waya ta ce ba ta jin
dadi idan ta dau lokaci ba ta ganki ba.
Suka fito babban falo suka hau tabir inda ‘yan
samarin suke jiransu. Jawahir ta gaida Yayyanta inda ita kuma kannenta
suka gaishe ta, al’adar gidan ke nan kowa sai ya
gaisar da wanda ya girme shi.
Ta kalli Nasir ta ce, “Yaya Nasir za ka kai ni gidan
Inna? Ya harare ta, Ni direbanki ne ina amfanin Idi
direban da aka ajiye muku?” Yaya Abba ya ce, Wai kai me ya sa kake haka ne?
duk yanda direba zai kula da ita ai ba kamar dan
uwanta ba ko?
Ki bari mu gama break sai na kai ki. Ta ce, “Yauwa
Babban Yaya na gode Iyayen dai
suna jinsu ba su tanka musu ba. Bayan gama break dinsu jawahir tanufi dakinta ta
kara gyara fuskarta ta sako shudin takalmi da
shudin mayafi ta fito, Dady za mu tafi,”
To me za ki kaiwa Innarki? shiga sito ki jido mata
abin da kika ga za ki kai mata Nasir ya ce, Wallahi
Dady sito din Inna cike yake da kayan abinci da na masarufi. ka manta
shekaranjiya ka ba ni kayan abinci da na amfani
mota guda na kai mata?
kuma da muke zuba mata a sito din ma akwai
wasu a ciki. Abba ya ce, To sai a kai kudi kawai.
Momy ta ce, Ki je wajen Rahane me aiki ini ta gama gasa kaji dana sa ta da akwai cake da
samosa da na bayar akayi mata, sai soyayyiyar
miyar zabi dana yi mata tun jiya.
Alhaji ya ce, Wallahi dalilin da ya sa kenan kullum
Hafsa nake kara son ki, kike dada shiga rai na don
duk hanyar da za ki faranta min kin san ta, ga yanda kike kula da mahaifiyata, ni kuwa me za ki
nema a wajena na kasa yi miki.
Ta yi murmushi, Ba komai Alhaji Inna ai uwatace,
ba abin da ba zan iya yi mata ba, don albarkarsu
muke nema.
Auwal da sani su ma suka ce, Dady mu ma za mu je gidan Inna.
Jawahir ta turo baki, Gaskiya Dady ba za su bi ni
ba, damuna za su yi ta yi da hayaniya sun fiya
surutu. Dady ya ce, Ku yi hakuri Auwal ma je da ku
da
daddare, kun ga islamiyya za ku je in karfe biyu ta yi ku kyale ta ta tafi.
Yaya Abba da jawahir suka fita suka nufi gidan
Inna Yana tsayawa da motar ta fito a guje za ta
shiga cikin gidan Abba ya kira ta, Zo ki debi wasu
kayan mana.
Ta ce, To suka kwashi kayan suka yi ciki. Salamu alaikum ‘yar tsohuwa, kina nan?”
“A’a wa nake jin magana kamar bera?”
Kai Inna ki ga zankadediyar budurwa ki ce mata
bera.?” Inji yaya Abba. Inna ta ce, Ai lallai kuwa ‘Yar
dady ta girma don ko
yanzu ma a ka yi mata aure ai zama za ta yi. Jawahir ta rufe fuskarta da hannuwanta ta ce, Haba
Inna yarinya ta da ni ni da ko saurayin ma ba ni
da shi.”
Inna ta ce, “A’a ba kya dai kula su ga Hafizu abokin
Abba nan duk nacin da yake yi kin ki kula
shi.” Jawahir ta ce, Ai ke kuma yanzu kin ga za mu bata.
Abba ya duba agogo ya ce, Inna ni zan wuce
office.
To maigidana sai ka dawo. Yaya Abba ya tafi.
Jawahir tana cinyar Inna tana yagar cinyar
gasasshiyar kaza suna ta zuba hira. A hankali aka yi sallama a kofar falon aka shigo cikin takama da
isa.
Jawahir sanin me shigowar ne ya hana ta amsa
sallamar bare ta dago kai ta kalle shi. Inna ta kama
washe baki, “A’a yau saraki ne a gidan tsohuwa?
Lallai kam batan kai aka yi. Yayi kasaitaccen murmushi ya durkusa gaban Inna
ya gaisheta, ta ce, Bature ba a ganinka sai an cike
form ko?
Yayi kasaitaccen murmushi ya ce, Inna sai dai idan
ba a so ganin namu ba.
Ta ce, Wai yaushe za ka yi aure ne? ko so kake yi ka za ma tuzuru?
Ya ce, Inna me kike ci na baka na zuba, kwanan
nan zan kawo miki dakakkiyar yarinya ‘yar jami’a
me cikakken ilimin boko wayayyiya. Inna ta ce, Ba
dai cikakkiya ba sai ka kwaso min
kwaila. Ya ce, Haba Inna me za ayi da kwailar mace, duk
yarinyar da ba ta je jami’a ba ai ba ta waye ba
namijin ya sha wuyar zama da ita, don hauka za ta
yi ta yi masa.” Jawahir ta san duk da ita yake
wannan habaicin maganar ita kuwa ko kallo be
ishe ta ba. Inna ta ce, Jawahir kina kallon Yayanki ba za ki
gaishe shi ba.?
Jawahir ta yamutsa fuska tare da kau da kai gefe
daya ta ce, Ai ban gane shi ba ne, Maganar ta yi
masa ciwo amma da yake ba da shi ake maganar
ba sai ya yi shiru yana jin su. Inna ta ce, Kin ci gidanku, in.. ban da iya shege
yaya za ayi ke da dan uwanki ki ce baki gane shi
ba?”
Jawahir ta ce, To in ban da abinki Inna ai sai kana
yawan ganin mutum za ka san shi ko.?
Inna ta ce, Ba na son dogon surutu, ni dai ina horonku da ku rike zumunci, don zumunci ba abin
wasa ba ne, don Allah Subhanahu wata’ala ya ce,
Duk wanda ya yanke zumunci ba shi ba rahamar
Ubabgiji. Jawahir ta ce, Inna ni fa ba yanke zumunci
zan yi
ba, gane shi ne kawai ban yi ba, to ba sai a yi min bayani ba.
Ya mike, “Inna bari na karasa office.”
To Haidar ba a abin da za kaci a gidan tsohuwa,.
Ya girgiza kai tare da yamutsa fuska, Inna ba zan
iya cin komai ba a nan don zuciyata tashi take yi.
Ya bawa inna kudi ta yi masa godiya tare da sa masa albarka. Ya yi gaba jawahir ta mike ta ce wa
Inna bari na raka shi bakin motarsa. Inna tace,
Yauwa ko ke fa, ai gwanda ku rinka karfafa
zumunci, don bi so nake kullum na ga kanku a
hade.
Jawahir ta same shi a harabar gidan yana kokarin bude motarsa ya shiga, Jawahir ta ce, A dai taka a
hankali a daina jin kai da wulakanci, don duniyar
ba matabbaciya ba ce, wata rana a karkashin kasa
za a saka mutum.
Ya kalle ta ya yatsuna fuska tare da zuba mata
harara ya tofar da yawu gefe daya ya sa hannu ya toshe hanci wai doyi take yi. Ta yi shigewarta ciki ta
bar shi a wajen yana
kokarin shiga motarsa. A zuciyarsa ya ce, Lallai
yarinyar nan ba ta da kunya amma zan yi
maganinta ne,.
Jawahir sun zana jarabawar fita daga Secondary har sun hada fatin gama secondry. Duk yawancin
samarin da suke kawo kansu gare ta ba ta kula
kowa sai wani Faruk da jininsu ha hadu daga
mutunci suka zarce da soyayya. To suna son
junansu don duk yanda jawahir take kin samari da
an ce Faruk zai zo kaga rawar kai da girin girinkidishin yin tsararriyar kwalliya ta taron
masoyi. Sannu sannu soyayya mai zurfi ta shiga
zuciyarsu.
******************************
Aunty tana zaune a falo Abvan Haidar ya fito daga
toilet ya zauna kusa da ita ya ce, Kin sani ne, Wallahi tun satin da muka je saukarsu Jawahir
zuciyata ta matsu da sha’awar halayyar yarinyar
nan. Tana da hankali da nutsuwa ga girmama
nagaba da ita. Abin da ya fi bani sha’awa da ita
yanda take karatun Alkur’ani a wajen saukar nan
tasu, ta iya fitar da harafi ga zakin murya da bawa kowanne baki hakkinsa. Ni yanzu shawarar dana
yanke zan je na samu Alhaji ibrahim da ya tallafa
ya bawa Haidar auren jawahir.
Aunty ta yi ajiyar xuciya ta ce, Wallahi da hakan za
ta faru da na fi kowa farin ciki, amma abin da nake
tunani Alhaji anya kuwa hakan za ta yiwu ka san halin miskilancin danka kada ya ki a zo
zumincinmu yana baci a banza, gaskiya Alhaji ka
duba ka gani.”
Ya ce, Karki damu Aisha, Allah ya ga niyarmu ta
kara donkon zumunci ce a tsakaninmu, insha
Allahu ba za su bamu kunya ba. Ta ce, To shi kenan Allah ya taimaka, Ubangiji ya sa
a yi a sa’a amin
Da magariba Abban Haidar ya nufi gidan amininsa
Alhaji ibrahim. Suka karbi junansu da murna da
farin ciki.
Suna sitting room dinsa. suna yin sallar insha’i a masallacin gidan suka dawo sitting room din suka
ci abinci. Daga nan Abban Haidar ya zayyanawa
Alhaji ibrahim shawarar da ya yanke na game da
hada ‘ya’yansu aure jawahir da Haidar.
Alhaji ibrahim ya yi dariya ya ce, Amma na ji dadi.
Gaskiya wannan ai shawarace me kyau. Allah ya tabbatar mana da alherinsa, to amin. Allah ya sa ayi
da mu.”
Ko da Abvan Haidar ya tafi Dady ya shiga gida ya
gayawa mommynsu jawahir komai. ita ma addu’ar
ta yi tare da sawa abin albarka.
Da safe bayan sun kammala break dinsu. Alhaji ibrahim ya kalli jawahir ya ce, To jawahir a yau
nake son sheda miki lokacin aurenki fa ya yi, zan
aurar dake don cika unarnin Allah subhanahu
wata
ala.
Ta dafe kirji. Dady shekarata goma sha bakwai fa.” Ya ce, To menene, ai kin isa ko ba ki da saurayi ne?”
Ta boye fuskarta a cikin hannuwanta ta ce, Daddy
akwai Faruk, amma ce masa nayi ya dakata sai na
fara zuwa jami’a tukunna na yi masa magana ya
fito.
Alhaji ta ce, Uhm jawahir ki kyale maganar Faruk ki ba shi hakuri kawai don ni na riga na yi miki miji.
Ta dafe kirji cikin kwalalo ido ta ce, Na shiga uku
sai kuma kuka don Allah Dady ka yi hakuri ka bar
ni na auri Faruk shi zuciyata take so.”
Alhaji ya girgiza kai, Kada muyi haka da ke, ki yi
hakuri ki bi umarnina ki auri mijin dana zaba miki, insha Allahu ba za ki taba da na sani a rayuwarki
ba, kin ji. Ta dafa kanta.
Ta amsa da To Dady Allah ya zaba mana mafi
alheri, Ta mike ta yi dakin mommy tana kuka.
Momy ta ce, Lafiya ke kuma kike kuka?
Ke da wa? Me aka yi miki? Mommy ki
taimake ni Dady zai yi min auren dole, Ta kwashe
komai ta gaya mata.
To ke tun dsya ce yayi miki miji to ki hskura da
Faruk din mana.
Jawahir ta kuma fashewa da kuka, Don Allah momy
ki taimaka min ya bar ni na auri Faruk.
Momy ta ce, Kin ga kawai hakura ki bi zabin
mahaifinki ni ba ruwana ina zaman lafiya ba za ki
jawo min tashin hankali ba. Ki bari zan yi nafila da
addu’0’i zan miki istihara don neman zabin Ubangiji, amma ba na so ki tayar da hsnkali, don
komai mukaddari ne daga Allah, kin ji,ki share
hawayenki kar ya gane har yanxu kuka kike yi.
Ta ce,,To momy ta mike ta nufi dakinta.
******************************
A gidan Haidar kuwa Alhaji ya gama gayawa Aunty yanda suka yi da yayanta. Aunty ta ce Nina san
yaya zai amince ni dai tsorona yaron nan ka san
jin kansa kar a yi auren ya zo yana wulakanta min
‘ya.”
Alhaji ya ce, Kirawo min shi mu ji ta bakinsa, ta
daga waya ta danna lambobinsa ta yi ringin ya fi sau nawa kafin a daga sai can ya daga.
Hello wallahi ban san ke ba ce sai da na kalli
wayar sai na ga lambarki lafiya Aunty.?”
Lafiya kalau ka zo falo Abbanka yana son magana
da kai yanxu”
To Aunty ga ni nan zuwa Suka ajiye kan wayar. ya yi sallama tare da tura kofar ya shiga bayan sun
amsa masa, Ya zauna gaban Abbanshi a kan kafet,
Abba ga ni.
Ya ce, Yauwa Haidar na kirawo ka ne daman don
na ji ko ka tsayar da matar da zaka aura?
Haidar ya ce, Wallahi Abba ni ba ni da lokacin kallon matan ma bare na ga wacce ta yi min.
Alhaji ya ce, Ni kuwa ka ga ina da lokacin kallon
su, don har na samo maka matar da za ka aura,
don nasan za ta yi maka yar uwarka ce Jawahir.”
A firgice ya daga kai ya kalli Aunty ya ga karatunta
ma take yi ya juya ya kalli Abbansa ya ce, Abba jawahir fa ka ce, Haba Abba me zan yi da wannan
kwailar yarinyar, yarinyar karama zan aura? Haba
‘yar da ko kilewa ba ta yi ba, kwanan nan fa ta
gama secondary.
Alhaji ya daga masa tsawa, Kai ba ma son zancen
banza, ni ita na zaba maka kuma ita nake so ka aura ta zamo uwar ‘ya ‘yanka.
Haidar ya marairaice kamar zai yi kuka, Wallahi
Abba jinina bai hadu da yarinyar ba ta da kunya
shi ya sa na tsane ta.
Aunty ta zaburo ta rufe shi da fada, Yar tawa kake
cewa marar kunya ka tsane ta? To bari ka ji na gaya maka ko kana so ko baka so aure bsbu fashi,
munyi niyyar hada ku kuma sai mun yi, in ya so
ranar da aka kai ta dakinka ka yanka ta gunduwa
gunduwa ka kawo mana namanta, wannan shi ne
maganin kiyayya marar kunya wanda bai san
mutunci ba. Abba ya dakatar da ita, To fadan ya isa haka, na
san bai yi dai dai ba amma ki yi hakuri. Ya kalli
Haidar, Ka tashi ka tafi amma ka sani jawahir ita ce
zabinmu ba gudu ba ja da baya, sai ka je ka yi
tuananin abin daka ya fi dacewa da rayuwarka.
Haidar ya taso cikin bakin ciki, zuciyarsa tana kuna ya yo dakinsa yana magana a zuciyarsa yana
zagaye falon nasa maganar har ta fito fili.
Haka kawai a rasa yarinyar da za a ce na aura sai
wannan figaggiyar yarinyar ‘yar karama, yarinyar
da
muka yi rainonta? me zan ji a jikin wannan kwailar, yarinyar da kyar ma in ta fara kirgar dangi? Haba ai
an cuce ni, yanda nake ji da kaina nake so na auri
katuwar mace wadda ta gama jami’a me hankali
wadda za ta fuskanci halina ta bi ni yanda nake so
mu zauna lafiya yaushe za a hada ni da wannan
faratun? Yarinyar da ba ta fi ta tsaya min iya ciki ba, gaskiya a canja shawara, don in har yarinyar ta
yarda ta aure ni sai ta gane kurenta.
,
​
.
[…] Salon So Hausa Novel Complete […]
[…] Salon So Hausa Novel Complete […]
[…] Salon So Hausa Novel Complete […]
[…] Salon So Hausa Novel Complete […]
[…] Salon So Hausa Novels Complete […]
[…] Salon So Hausa Novels Complete […]