Sanadin Besty Hausa Novel Complete

Sanadin Besty Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Anty!! Anty!! Anty!!

Mommy ta ce ki tashi daga bacci nan kafin ta zo da ƙanta.

 

Dogon tsaki ta ja, ƙara gyara kwanciyar tayi ba tare da ta tashin ba, ganin haka ne yasa Arya fita daga ɗakin da gudu ta nufi parlour, wata mata ce a kalla zata kai shekara arba’in, tana zaune a kujera, waya ce a hannun ta da alama magana ta gama yi a wayar, ganin yar autar tata ta dawo ba tare da wacce ta aika a kira ma ta ba ne yasa ta cikin hassala ta ke faɗin

 

“Arya, ina Raudar take? Ko baƙi je kin taso min ita bane”?

 

Bude baƙi Arya tayi a shagwabe ta ce :

To Mommy na je amma ta ƙi tashi kuma fa tana ji ina ce da ita Mommy na ƙiran ta, shine ta ƙara jan bargo bata kulani ba”

 

Shikenan! Go and call Saleem” cewar Mommy ta fita a parlour’n tayi hanyar dakin Raudah, ita kuwa Arya da gudu ta fice compound din gidan dan kiran Saleem kamar yadda mommy ta aike ta.

Tech Site

Mommy na shiga ɗakin Raudah ta hango ta nannaɗe a gado tana barci, charger ta cire a jikin socket ta nufi gaɗon, tana isa ta yaye bargon ta zuba ma ta a cinya, wani ƙara Raudah ta saki, ba shiri ta miƙe ta na sosa wajan ɗan taji zafi sosai, bacci ne fal a idon ta amma dole ta tashi ganin Mommy ce da ƙanta.

 

“Yanzu fisabillilahi Raudah kin ma ƙan ƙi adalci kenan? Sau nawa ina aiko Arya ta tashe ki? Duk yau aikin gidan ni nayi abu na, wallahi idan ki ka ce da wannan lalacin zaƙi je gidan miji wahala zaƙi sha dan kuwa babu namijin da zai jure wannan halin na ki”

 

Shiru ta yi tana shagwabe fuska ganin Mommy na ta sababi yasa ta yi shiru, ba ta ce komai ba, ita kuwa Mommy ci-gaba ta yi da fada, ɗan halin na Fauzah ya fara isar ta yarinya sai lalaci, sai da tayi mai isar ta sannan ta fice a ɗakin.

See also  Illar Goge Maniyyi Da Tsumma Daya Bayan Saduwa

 

Mommy na fita Raudah ma ta fice a ɗakin, tsakar gida ta je, ganin har rana ta fito sossai yasa ta hanzar ta daukan boƙiti wankan wanƙa ta nufi kitchen, ruwan zafi ya gani a kettle an tafasa, da hanzari ta juye ta shige bayi, koda ta fito daga wankan ba ta bi ta ƙan abin ƙaryawan da a ka ajiye ma ta ba ɗan tasan zuwa yanzu ya gama sanyi, wayar ta iPhone 7 plus da ke kan gadon ta ɗauka, ganin sha daya saura minti takwas yasa ta ce

 

“Wayyo Allah na!! Allah yasa Bestynah bai yi fushi dani ba dan yau kwata_ƙwata ba muyi magana ba” tana fada tana kokarin kiran number BESTY …

 

Sai da ta ƙira sau biyu ana uku ya daga bai ce komai ba ta fara magana cikin shagwaba

 

” Haba BESTY tin da kaga ban neme ka ba ai sai ka kira ni kuma ƙasan munyi da kai yau za ka raka ni wajan tela”

 

Shi ma daga can ɓangaren shagwabe murya ya yi ya ce

“Kiyi hakuri BESTY na ban tashi da wuri ba ne, kin ganni nan ko fitowa ban yi ba har yanzu ina daki, ban ma san wacce wainar aka toya a cikin gidan ba, tashi na kenan sai ga call ɗin ki”.

 

Narƙe murya tayi ta na faɗin ” ba mun yi alƙawarin ba zamu dinga zama da yunwa ba, though nima tashi na kenan ɗan da charger waya ma Mommy ta tashe ni”, har da yin shesheƙar ƙarya kamar yana gaban ta, da sauri Besty ya riki ce sai cewa ya ke

“Kashhh!!amma dai Mommy bata ji miƙi ciwo ba ko? Ni fa da wani abu ya same ki gwara mulkin Buhari ya dawo farko, ya karshe maganar yana dariya, ita ma Rauda sai da ta ɗara jin abinda ya ce.

 

Waya suka ci-gaba da yi cike da kulawa ganin call ɗin Ya Noor yana ta shigowa ne yasa ta ce

” Ammm besty bani minti biyar pls, Ya Noor yana ta ƙira na ko me zai ce mun ohoo, ba na fada maƙa ba ranar, tunda ya kawo sadaki sai ya dinga min wasu abubuwa kamar iko _ iko, Ni wlh na gaji da halin shi, mutum sai shegen miskilancin masifa, mtseww”,

See also  Silar Fyade Hausa Novel Complete

 

Shiru ya yi bai ce mata komai ba sai da ta karaci mitar ta sannan ya ce ma ta ” kinga malama kin dame ni da maganar mutumin nan, ai tin ba yau ba nace ki rabu dashi ƙin ki ji, oh saboda ban isa dake ba ne, hmmm ai nasan matsayi na, mutumin da ko kallon arziki baya min, ta yaya ma zan ji dadi ace bestyna tana tare da wanda baya mutunta Ni? Indai har da gaske ni better half ɗin ki ne, to ya zama dole ki rabu dashi mu nemo wani saurayin” ya faɗa in a serious tone,

 

Zufa ne ya fara karyo wa a jikin ta, tabdi!! tama isa ta ce ma Baba bata son Nura? Ai Wlh sai ya sumar da ita daga ita har Bestyn, gashi kuma bata son ɓacin ran besty’n na ta, ganin tayi shiru ne yana ta magana shi kaɗai yasa ya kashe wayar shi gaba ɗaya, ai kuwa sai ga kiran Noor ya sake shigowa a karo na uku wayar ta, tin da taga kiran da Noor yake ya yi yawa tasan wani abu zai fada ma ta mai muhimmanci ɗan shi Noor call daya yaƙe mata idan bata daga ba to ba zai kara kira ba har sai ta neme shi da ƙanta, ta inda BESTY ya fishi kenan sai ya mata missed call biyar ko shida koda kuwa hira kawai yake so suyi da ita.

 

Sai da call ɗin ya kusa yankewa sannan ta daga, bata ce mai komai ba, hakan ba karamin fusata Noor ya yi ba, lallai ma Raudah ba karamin raina shi ta yi ba, ya zama dole ya yi maganin ta…

 

 

 

Tana kwance a saman ƙirjin shi, wasa take da gashin da ƙe kwance a saman faffadan kirjin shi, hakan ba karamin nishadi yaƙe sa ka ta ba, kallon ta ya yi da rinanun idanuwan shi, da kyar ya ke iya kamo numfashin shi saboda wata sha’awar ta daƙe ƙara azalzalar shi, babu abinda yake so sama da ya ga ya yi sex da ita amma taƙi bashi hadin kai, tsawon watanni 5 kenan da haduwar su,kuma babu irin sabon da basu yi ba, ta yadda bata iya tsallake maganar shi, abu ɗaya ne ya kasa samu daga wajan ta, sai dai duk lokacin da suka haɗu suyi romancing ɗin junan su, a wanan lokacin hakurin shi ya ƙare,

See also  Ni na raineta Hausa Novel

Hannun ta ya cire daga jikin shi, ganin hakan ne ya sa tayi saurin kallon shi

“Haba mana Adnan, me yasa za ka hanani yin abinda nake matukar so da kauna” ta fada kamar zata fashe da kuka,

Wata iska ya furzar da kyar ya aro jarumtar yin magana

 

“Ya kike so nayi ne Fadeelah” ɗan baƙi san yadda na dauke ki bane, tin lokacin da muka fara abota har nasan damuwar ki da wancan tsohon saurayin na ki, na daukar wa kaina alkawarin share miƙi hawaye duk rintsi duk wuya, bani da burin da ya wuce na faran ta miƙi rai, amma ke kin gagara fahimta, ko da yaƙe dan kin ga na damu da ke ne shi yasa!

 

Tabbas taga ɓacin rai a idanun Adnan, amma kuma fa ba zata iya bashi ƙanta ba, wannan tanadin sai gidan miji, to amma ya zata yi da rigimar da yaƙe neman ɓullo ma ta?

 

Innaaa!! Ba abu bane mai yiwuwa, tab ai ba zata taba yadda ya aikata abinda yake so da ita ba, zina kenan fa, ta fada a ranta, shi kuwa Adnan yana nazartar yanayin ta ba tare da ya ce komai ba ya miƙe ya shiga toilet, bata yi ƙasa a gwiwa ba wajan tashi ta bi shi cikin toilet ɗin gudun kar ranshi ya ƙara ɓaci…

 

 

Toh fa reader’s da alama besty zai yi halin na shi🤣

 

VOTE

 

 

 

COMMENTS

 

 

 

SHARE

 

✍️

BADAWEEYERH

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top