Sanadin Gidan Amarya Hausa Novel Complete

Sanadin Gidan Amarya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: SANADIN GIDAN AMARYA

 

*MALLAKAR*

*Zainab Muhammad*

*(Indian girl)*

 

 

*ĎĮÃϻỖŇ ŴŘĮŤẸŘ’Ŝ ÃŜŜỖČĮÃŤĮỖŇ*

*D.W.A*

 

 

*Salon na dabanne fa sisters dan haka ku motsa sha’aninku a 200 kacal domin kaunarku gareni da nima ita nake muku*

 

*Espisode 1*

 

 

Gidan kunshine cike da jama’a yayin da mai kunshin ta kasance ita ɗaya take yi a gidan.

 

Can na hango wasu taron ƴan mata suna zaune akan tabarma su nata hira,wata haɗaɗɗiya kyakykyawa na hango mai tsananin kyau da diri kyanta ya wuce misali kyan nata na dabanne,farace doguwa mai ɗan jiki tana da hips mai jan hankali tare da manyan boobs masu tsini. Fuskarta doguwa mai ɗan faɗi mai lauke da dogon hanci da dara-daran idanu masu haske haɗi da zara-zaran gashin ido,bakinta ɗan ƙarami irin na shan sweat.

 

Tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan kyakykyawar halitta mai tafiya da imanin maza harma da matan.

 

“Wallahi na gaji da zaman nan kun san fa ni bana son zama idan ba a gidanmu ba”

 

Zazzaƙar sexy voice ɗinta ta faɗa,tsabar daɗin muryarta ma sai ka kusa suma.

Gidan Uncle Hausa Novel

dda da alama itace babbar ƙawarta,Tace”Wallahi Basma nima kin san irin mu ɗaya”

 

Ɗayar ita kuma Tace”Ni kuma wallahi ban damu ba saboda ni duk inda naje gidane”

 

Duk sukai dariya amma banda Basma.

 

Miƙewa Basma tayi ta gyara zaman hijab ɗin dake jikinta (dake ita ko a gida bata zama ba hijab saboda irin halittarta ta jan hankali).

 

Mai ƙunshin ta ɗaga kai ta kalleta kafin,Tace”A’a sis ina kuma zaki? Nafa kusa zuwa kanki”

 

Basma ta ɗan ya tsina fuska,”Wallahi na gaji da zamane gashi zanje gyaran gashi”

 

Kafin mai ƙunshin tai magana wata daga cikin ƴan ƙunshin da tun zuwanta idanunta suka sauka akan Basma taji tana sonta,Tace”Amma ƴar uwa da kin tsaya tayi miki naga kamar ke amaryace ma ko?”

 

Basma ta kalleta dake ko bata san mutum ba bata da hulaƙanci,Tace”Ƴar uwa abubuwa ne sunyi yawa,eh ni amaryace”

Mai ƙunshi ta shimfiɗa tabarma lokacin da ta ƙarasawa wadda takewa,Tace”Sis zauna nai miki tunda uziri yai miki yawa kuma dama layin ya kusa zuwa kanku”

 

Basma ta zauna aka fara yi mata zanen jan lallan,nan fa wasu daga cikin waɗanda suka riga su Basma suka hau surutai da maganganu wai dan anga Basma kyakykyawa shi yasa ake mata ai san kaine.

 

Basma ko ɗaga kai bata yi ta kallesu ba Zaliha ce ma ƙawarta taso ta kula su amma Basma ta hanata,haka aka gama mata akaiwa Maryam da Zaliha sannan akaiwa waɗancan.

 

Bayan ya kama ya yi ja sun cire sai aka ɗora masu da baƙi da ja da ake ya yi kyau ɗin na.

 

Basu suka bar gidan ƙunshin ba sai wajan ana kiran sallar magriba,a gajiye lis suka isa gida.

 

*WACECE BASMA*

 

Basma ƴace a wajan Alhaji Isma’il Sharif da Hajiya Zainab,sun kasance haifaffun garin sudan ne masu matuƙar kyau sannan suna da arziƙi familyn nasu sannan akwai haɗin kai da girmama na gaba.

 

Zainab da Isma’il family ɗin su ɗaya sannan kuma iyayensu wa da ƙani suke.Zainab kyakykyawace ta ƙarshe domin duk familyn nasu babu mai kyanta,ta taso kowa a familyn yana matuƙar kaunarta duk abinda ka samu Zainab.

 

Allah ya ɗorawa Isma’il soyayyar Zainab tun tana yarinya baya taɓa samun sukuni idan har baya tare da ita,hakanne yasa iyayensu suka bashi auranta,bayan sun girma aka ɗaura musu aure.

 

Suna zaman su cike da soyayya,Isma’il ya kasance yana zuwa garin kano tun da ƙuruciyarsa har ya ma zama idan ya tafi sai ya yi watanni acan har dai ya girma gashi ya yi aure.

 

Hakan yasa yace zai ɗauki matarsa su koma can saboda gaskiya ba zai iya dinga barinta yana tafiya waɗannan kwanakin ba tare da ita ba,da iyayen nasu sun so su hana amma kuma da kakanni suka sa baki sai suka amince.

 

Haka ya ɗauki matarsa Zainab suka koma kano,a sanda suka koma dama Zainab tana ɗauki da juna biyu na watanni 4.

 

Haka sukaci gaba da rayuwa gwanin sha’awa.

 

Watanninsu 5 da kwanaki Zainab ta haihu ta haifi ɗiyarta mace ranar suna ƴan sudan sun zo jinjinniya tayi farin jini sosai yarinya taci suna Safina amma zasu dinga kiranta da Safna,bayan suna duk aka watse aka bar su su kaɗai.

 

Shekarar Safna 2 aka sake haifar namiji kyakykyawa kamar su ɗaya da mahaifinsa komai da komai yaci suna Aliyu amma Haidar za su dinga ce masa,haka suka taso su biyu gwanin sha’awa shida Safna tana da shekara 4 yana da 2 ita tana makaranta a primary 2 shi kuma 1.

 

Yaran sun taso suna cewa da mahaifiyarsu Mammy mahaifinsu kuma Daddy.

Tun daga kan Haidar Mammy bata sake haihuwa ba sai da Haidar ya shekara 10,a sannan ne ta samu ciki.

 

Zo kuga tarairaya wajan Daddy lokacin da Mammy ta samu ciki komai yai mata ya hanata aiki,ita kuma Safna tana ɗan yi kamar su shara da makamantansu dake yarinyar akwai wayo da son girma.

 

Lokacin da cikin Mammy ya isa haihuwa da kyar take iya tashi,hakan yasa Daddy bai cika fita ba koda yau she yana tare da ita baya so yaji ko uhm tace.

 

Yau ya kama ranar lahadi kuma Mammy ta tunda ta tashi da safe take jin ciwo wanda ta tabbatar da cewa ciwon haihuwane,tun tana daurewa da ɓoyewa Daddy har ya gane suka tafi asibiti.

 

Da sauri likitoci suka ƙarɓeta sobada dama nan ne asibitin da suke zuwa idan basu da lafiya,lokacin da aka shiga da Mammy labour bata motsi hakan yasa likitan yace c.a za ai mata.

Hankali Daddy ya tashi amma ganin ba mafita sai haka yasa ahi amincewa tare da sa hannu,nan aka shiga da ita ɗakin da za ai mata aikin.

 

Sun ɗan ɗauki lokaci kafin a samu a fito mata da ƴarta mace kyakykyawa wadda har Mammy ma ta fita kyau kai hattama duk familynsu na Sharif family.

 

Likitocin kamar su sace yarinyar haka suka ji,bayan sun gyarata ne suka gyara mahaifiyarta sannan suka barta domin ta samu hutu.

 

Lokacin da su kaiwa Daddy albishir ba ƙaramin farin ciki ya yi ba wani kalar so yaji na yarinyar wanda kaf ƴaƴan nasa bai taɓa jin son su kamar yanda yaji soyayyat wannan new babyn ba.

 

Soyayyar bata sake tashi ba sai da ya shiga ɗakin da Mammy take ya ɗauki yarinyar sannan nan,haka itama mahaifiyarta data farka hakance ta kasance,harta ƴan uwanta su Safna da Haidar sunji kaunar ƴar uwar tasu sosai.

 

Bayan an sallamesu sun koma gida nan aka buga waya familyn Sharif aka faɗa musu zan cen haihuwar aikwa nan kowa ya cika da son yarinyar tun kan ma su ganta…

 

*#More Comments*

*#More typing*

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.