Sardauna Hausa Novel Complete
Tag: SARDAUNA
Story & Written
By
Jiddarh Umar
بِسم الله الرحمن الرحيم
Sa ɗaukarwa ga masoyan FITILAR DARE,DA WATA TAFIYAR.
_______duk wani mahalukin dake cikin wannan unguwar ta Darussalam hankalin su a tashe yake,daga manyan su har yaransu saboda yanda ƴan sanda suka zagaye unguwar da manyan bindigogi a hannun su har izuwa kofar gidan Sarkin Dambe,wato Inusa.
Wani ɗan sanda na gani rike da wani abin magana mai ƙara wanda duk inda kake a cikin unguwar kana iya jiyo duk abin da yake faɗa”SARDAUNA ka fito ka mika kanka ga ƴan sanda ba tare da kaba kanka komu wata wahala ba,hakan zai sa mu ɗan sassauta maka, ka fito ka mika mana kanka ko mu shigo har cikin gidan naku!!ya ƙarasa faɗa da ƙarfi da kuma muryar gargaɗi.
A cikin gidan kuwa,gaba ɗaya hankalin su a tashe yake,kuma a tsorace suke,dukda ba wannan ne karo na farko ba da hakan ke faruwa ba indai akan Sardauna ne,amma kuma har yanzun sun kasa sabawa da hakan,domin ance ba a sabo da wahala ko tashin hankali.
Littafan Hausa Novels Guda 1000 masu dadi
Matar Makaho Complete Hausa Novel
Hotunan Lalle Masu Kyau Kunshin Gam
Hajiya Gwale Hausa Novel Complete
Tsofaffafin Hausa Novels Watpadd
Zaune yake saman kujera yar tsuguno hankalin shi kwance yana cin abincin shi tankar bai da wata damuwa.
Wata yar dattijiwar mata ce ta maso kusa da shi cikin fuskar tashin hankali da damuwa ta dafa kafadar shi”yaro kana jin fa abin da suke faɗa a waje,amma kuma kana zaune a nan haka”
Daga ɗayan ɓangare taji ance”ki ƙyale shi kawai su shigo su kashe dan banzan yaro kowa ma ya huta”
Juyowa tayi ta kalli mutumin wanda shima yake zaune a ƙofar dakin shi “Haba Malam ne yasa kake faɗar haka akan yaro,karka manta shi din danƙa ne,kuma hannun ka baya ribewa ka cire kayar, dan haka Addu’a ya kama ka mai”
“Sai dai in hannun bai ribe ba, sannan waye zaiyi asarar bakin shi wurin yi ma wannan takadaren yaron naki Addu’a,to bari in faɗa maki ko Addu’a yasan wanda yake kamawa amma ba irin wannan ɗan naki ba” Juyowa yayi wurin ƴanmata dake tsaye su biyu suna risgar kuka, cikin tsawa yace masu”kai ku jaye can,gaba ɗaya duk kun cika mana gida da ihu kamar anyi mutuwa,”tsit suka ja baki suka yi shiru.
Jirjiza kai kawai tayi,sannan ta juyo da kanta wurin Sardauna wanda ya kammala cin abinci ya mike tsaye,kallon matar yayi “Baaba a gafarta mana domin ko mu kashe ko a kashe mu” Ya faɗa da irin maganar nan irin nasu na yan daba,
Jin wannan ɗan sandar me karaɗi yana sanar da shigowar su cikin gidan yasa da sauri tashafa fuskar shi “ɗan Allah yaro banda kisa,Allah ya shirya min kai ya kuma tsare ka,”
“Amin Baaba” Har ya juya,sai kuma ya juyo jin yanda ta rike mai hannu,cikin marairaicewa ta ce “zaka dawo gida ko”
Kai ya gyada mata yana kallon yanda yan sanda suka fara shigowa.
“Zan ajiye maka abincin dare” Nan ma kai ya gyada mata,sakar mai hannu tayi ya juya cikin wani irin zafin nama ya taka wani dogon Turmin dake kife a jikin bangon kicin dinsu sai gashi saman garwan kicin dinsu, ihu ɗan sandan daya shigo yayi yana sanar da sauran gashi nan saman garwa,yanda kasan wani biri haka ya shiga tsalle daga wannan garwan zuwa wancan,ganin haka ne yasa su kuma ƴan sanda suka buɗe mai wuta,ta ko ina harbin shi suke da bindiga,gaba ɗaya unguwar ta kara yamutsewa ba kajin komai sai ƙarar harbi,yayin da shi kuma suna harbo mai harshashai yana rarkadewa kamar mai karaɗe ƙura a kinshi,sai dai kawai ka ga suna faduwa kasa,tun suna kirga zingin gidan da Sardauna ya ƙetare sai da ya kitare gida goma sha shida sannan ya dira a wani filin ƙwallo.
Tsayawa yayi a tsakiyar filin, yana kallon yanda mutane wurin ke ta gudu kowa na yin ta kansa,domin ba wannan ne karo na farko ba da za’a zo harbin Sardauna bai same shi ba sai dai ka ji ance harbi ya samu wani ya mutu,shi yasa da amfara ba mai tsayawa.
Ƙara zagaye shi suka yi,yayin da jikin shi ke wani irin ɓari da karkarwa na bacin rai,ƙara gyara tsayuwar shi yayi sannan ya ciro wata sharbebiyar wuƙa a ƙugunshi,cikin maganarsu irin ta cikakken dan daba ya fara magana da buɗaɗɗen muryar shi”Sai ni nan Sardauna,a jadani a barni,a duke bana dukuwa,a kamani kuma a sake ni,a zakeni in barar da haƙora,munga jiya munga yau,da yardar mai sama sai munga gobe,dan haka duk mai son uwar shi ta haife wani ya matso nan”
Kafin ƴan sandar su Ankara sai gani suka yi wasu gungun yara matasa wanda a ƙalla zasu tasarma mutum ishirin sun shigo cikin filin sun zagaye Sardauna,yayinda ya zamana shi yana tsakiyar su,ko wanne a cikin su rike yake da mugayen makamai,daga mai barandami sai mai Adda,mai Lauje,da dai duk wani nau’i na ƙarfe wanda zai iya huda jikin ɗan adam,kuma ya kai shi har lahira.
Ɗaya daga cikin yaran ne ya matsa kusa da Sardauna cikin girmamawa yace “ka garfarcemu Oga Sardauna mun makara, amma yanzun zamu auka masu,domin yau lahira zata yi baƙi”
“Ku dai saurara tukun Zuwiɗi domin yau na ma Baaba Alkawarin ba bu kisa,kuma kasan bana ƙarya Alkawari”
Bubbuga kafarshi yayi a ƙasa yana cije baki”kash,amma ba komai sun take sa’a yau, amma za mu sake haɗewa in dai sune na sani”
Wani police ne mai karan kwana ya matso kusa da su da bindiga a hannun shi yana saita su”ku miko mana Sardauna mu kuma zamu bar ku dan yanzun shi kadai muke buƙata”
Karanta Littafin Yarima Ashman
Wani irin kukan kura daya daga cikin yaran yayi ya cafko maƙogwaron dan sandan wanda nan take bai san sanda ya sake bindigar ƙasa ba, wani ne shima ya kara fitowa cikin yaran Sardauna ya tsaya a gaban wanda yake rike da ɗan sanda ya shiga haƙa rami da zungureriyar wuƙar dake hannun shi,ganin hakan ne yasa shi kuma ya kwantar da ɗan sanda yayin da kanshi ke saitin ramin,
Gaba ɗaya mutanen wurin dake ɓoye suna kallo da wadanda ke wurin, kai harma da ƴan sandar ba karamin tsorata suka yi ba ganin yanda suka Daura wuƙa a wuyan dan sanda suna ƙoƙarin yankawa,
Jin yanda wurin ya kara daukar hayaniya da ihu da salatin mutane ne yasa Sardauna fitowa daga tsakiyar da suka saka shi,ganin aikin da suke ƙoƙarin yine yasa ya karasa ya rike hannun yaron da wuƙar ke hannun shi,domin duk wurin an rasa wanda zai karasa wurin,gashi ɗan sanda da aka rikema makoshi sai kakarin mutuwa yake da shure shure domin ba karamin ruko yamai ba,”sakar shi Jagus”
Dago idanun shi yayi wanda kallo daya zaka mai kasan a mankas din shi yake”haba Oga Sardauna,ɗan Allah ka barni kawai in aika shege Lahira ”
“Ba yanzun ba”
Wani irin ihu ya kwarara na baƙin cikin hanashi aikata abin da ya so da akayi”waiyo Oga ka barni in kashe shegen tsuntsu mana,wai ba kajin yanda Lahira ke murnar zan turo mata Baƙo ”
Ba tare da yace komai ba ya ɓanbare hannun Jagus a wuyar mutumin,wanda yana tashi ba tare da ya jira komai ba ya bar unguwar da mugun gudu,dan ko waiwaye bai yi ba.
Ganin hakan ne yasa suma ƴan sanda suka juya suka bar wurin domin sun san wallahi ba abin da zasu iya diba ajikin yaran Sardauna bare shi.
Ganin ƴan sandan sun wuce ne Zuwiɗi ya ce”Sardaunan mu ina muka dosa?
Jagus ne yace”Oga Sardauna yau fa ake Gangin bikin Baban Ladi”
“Can za mu” gaba ɗayan su ihu suka sa na murna,sannan suka kwasa domin halaltar bikin Abokin su.
___________wasu ƴan Matasan ƴan Mata na gani su Uku suna tafiya,kayan makaranta Islamiyya ne sanye a jikin su,wanda daga dukkan alamu can zasu je.
Dayar ce ta kalle sauran “yau yayana ko kudin break be Bani ba,gashi ina son in tsiya gyaɗa”
“Ke dai Salmu duk randa baki ci gyada ba bazaman lafiya”
“Ke dai bari Fiddo,na riga na saba ne,waiyo Allah JAN MADAM kalle wata me gyaɗa tana wucewa”
Wacce aka kira da Jan Madam ne ta juyo ta kalle in da ake nuna mata,daga murya tayi “me gyada kawo mu siya”
Juyowa suka yi suka kalle ta”ki nada kuɗi ne? Cewar Salmu
“A’a ba ni da ko sisi, dan ni ma Baba kaka be Bani ba yau”
“To da wani kuɗi zamu biya ta” Inji Fiddo tana waro idanun ta.
Yarinyar ce ta katse su,wacce ba zata wuce tsaran su ba,Jan Madam ce ta kalle ta”la ashe Ƴar Sokoto ce”
Yarinyar ce tai dariya”Ni ce Jan Madam,Salmu yau ba za ki siya gyada ba ne?
“Eh ni yau ba ni da kuɗi”
Fiddo ce tace”yau Ƴar Sokoto ke kike talla,ina ƙanwar ki Wasila?
“Sai zuwa anjima zata fita tallan tuwo shi yasa na ke yin tallan gyada yanzun”
“Auna mana gwanwani biyu,kuma karki sa mana ruwa ruwa”
“To karki damu Jan Madam”tana gama aunawa ta zuba a leda ta kima masu,amsa tayi” Ku mu je “ai kuwa bin bayan ta su kayi zasu wuce,ganin haka ne yasa da sauri ta biyo su” Jan Madam baki bani kuɗi na ba?
Juyowa tayi ta kalle ta”ba ni da shi,kuma bana cin bashi,dan haka ƙarfi yaci,in ki nada shi ki kwata”
Da sauri Salmu ta mika mata ledar gyadar”karɓi abin ki dama banciba”
Da sauri Fiddo ta fiske ledar gyadar “kawo shi nan,ke dai Salmu an yi baƙar matsoraciya,matsa ki bamu wuri”
Ganin haka kuwa Yar Sokoto ta cakume hijabin Jan Madam “wallahi ba zan yarda ba sai kin bani kuɗi na,ai ke kika kirani”
Dariya tayi”ƴar Sokoto sake min hijabi kafin na hau ruwan cikin ki”
“Ni kan wallahi bani sakin ki sai ke bani kuɗi na”
Nan itama ta shaƙe mata hijabi,yayin da faɗa ya barke a tsakanin su,ƙarfin wanda ya saba da cin Tuwo ba ƙarfin su daya ba da mai cin Shinkafa ko Taliya,ganin Yar Sokoto ta barka ma Jan Madam hijabi yasa Fiddo itama ta shiga,nan suka kama hijabin Yar Sokoto suka yaga tun daga sama har ƙasa,yayin da jan Madam ta hau saman bayan ta ta shiga dima mata dundu,Fiddo kuma debo ƙasa ta yi ta dawo ta kanta “buɗe baki in miki brosh da ƙasa” Gimtse baki Yar Sokoto tayi.
“Jan Madam ƙara dima mata da ƙarfi mana”
Ai kuwa nan ta tattakura ta sake mata kulli a baya ji kake dim,ihu tayi jin kamar kashin bayan ta ya karye,hakanne yaba Fiddo damar tura mata ƙasa a baki.
Wani mutum ne yazo wucewa ta layin,ganin abin da ke faruwa yasa da sauri ya karasa wurin su”Subhanallah yara me haka ku keyi, maza daga ta “ya faɗa yana dago Jan Madam daga jikin Yar Sokoto,
” Me ya hada ku haka?
Cikin kuka, Yar Sokoto ta fara magana “Malam Bala ina tafiya ta zani talla to shine Jan Madam ta kirani suka tsiya gyada ta gwangwani biyu basu bani kudi ba,da na ce su bani kudi na shine sukai min taron dangin”
Kallon Jan Madam yayi”kai amma dai Fatima baki kyauta ba,gashi daga dukkan alamu Islamiyya zaku tafi shine kuka tsaya faɗa,oya bata kuɗin ta ku tafi ”
Turo baki tayi”mu bamuda kuɗi Malam Bala,kawai ta bari idan mun samu zamu kawo ma ta har gida ”
“Yaushe kenan zaku samu?
” Nima ban sani ba”
Jinjina kai yaya yana kuma mamakin hali irin nata,wai yarinyar babban Malami ne wannan amma take zagewa ta kwashi danbe a tsakiyar hanya,kai Allah ya shirya mana, juyowa yayi wurin Yar Sokoto “to ke kinji sunce in sun samu zasu kawo maki har gida”
“Wallahi ban yarda ba,nikam yanzun zasu bani kudi na”
“Wai har nawa ne kudin?
” Naira Hamsin ne”
“Kaji barauniya Murtala biyi ne kuɗin ki,dan gyada gwangwani Naira Ashirin ne” Cewar Fiddo.
“Na ji ya isa Hakanan,ke Yar Sokoto mu je bakin titi In yi canji sai in baki kuɗin,ku kuma ku wuce makaranta,gashi har biyar saura”
Murguda mata baki tayi”mun gode Malam Bala”
“Ba komai ai yiwa kai ne,Allah dai ya shirye ku”
“Kaga Jan Madam na murguda min baki ko?
Su dai nan suka wuce suka bar su,sun ɗanyi nisa kaɗan sannan Fiddo ta hango Salmu a labe a ƙofar wani gida tana leken su.
” Kalle Yar gidan ki”
Daga murya tayi”Salmu sai ki fito ai tunda ba a kashe mu ba”
Sumui-sumui ta fito”ku yi haƙuri ni ban iya faɗa ba ne shi yasa,kuma tsoro na keji ”
“Mu kuma gamu Ayagi ko?
” A’a ba haka nake nufi ba Fiddo ”
Tsaki taja”ina gyadar?
Da sauri ta miko masu”gashi nan ni ba zan ma ci ba ”
Kallon juna suka yi “kutmelesi wato ba zaki ci ba,ya zamana faɗar banza kenan muka yi,dan kin san dai ni bana cin gyada,sannan ita kuma Fiddo bai dame taba,amma shine zaki watsa mana kasa a ido?
” Kyaleta kawai Jan Madam,ko dai ta cinye shi duka,ko kuma mu mata ɗuran gyada,mu taushe ta ma ɗura mata har da bawon sai ta ci ”
Da sauri ta rungumi ledar gyadar “zan ma ci yanzun kuwa”
Dariya suka fashe dashi dama sun san halin Salmu da mugun tsoro.
Basu daɗe da shiga Aji ba sai ga wani malami yazo wai ana kiran su a ofishin Shugaban makaranta, malamin dake ajin ne yace su fito su tafi,kasancewar Salmu da Jan Madam ajinsu daya, Fiddo kuma ajin ta daban,a bakin ofishin suka haɗu,ko wacce da ido take tambayar Yar uwarta ko lafiya.
Suna shiga cikin girmamawa suka gaida shugaban makaranta da kuma wayanda suka gani a wurin,
Wani ne wanda ke zaune ya juyo yana kallon su “wacce Jan Madam”
Kamar ba zata bada amsa ba sai kuma ta amsa da “ni ce” Ganin yands duk suka zuba mata ido.
Jinjina kai yayi”A lallai kinci sunan ki Jan Madam “ganin irin farin da take dashi wanda yake da tsirki da ja.
” Fiddo fa”
Ita ma daga hannu tayi”gani”
“Na ganki,Salmu fa”
Cikin muryar kuka tace”ni ce”
Nuna masu gefen shi yayi”kun san wannan?
Duk juyawa suka yi wurin,ai tuni Salmu ta hau kuka”wallahi banda ni Ƴar Sokoto aini ban maki komai ba ko?
Mamanta ne tace”wallahi karya takai har da ita,dukkan su na”
Juyowa yayi wurin shugaban makaranta “to ka ji Malam dan haka zamu wuce dasu mu hukunta su,kamar yanda yake a doka”
“Yanzun ba bu yanda za’ayi kabar mana su anan mu hukunta su?
” Gaskiya babu domin ƙara aka shigar a kansu, amma karka damu zasu samu sassauci ”
Har bakin mota shugaban makarantar ya rakosu in da aka zuba su a ciki har da su maman Yar Sokoto har ofishin NDC,suna zuwa kallon su shugaban wurin yayi,ya sunan ki ya nuna Salmu dake sharban kuka”Salma Idris ”
“Ke fa”
“Fiddausi Isyaku”
Nuna Jan Madam yayi” Fatima Abubakar ”
“Shekarar ku nawa?
” Goma sha Biyar ”
“Dukan ku”
“Eh dukan mu shekarunmu daya”
Jinjina kai yayi”to Aje ai masu bulala biyar biyar”
Da Salmu ce kaɗai ke kuka,amma jin ance ai masu bulala biyar biyar ne yasa Jan Madam ta shiga Kwara ihu”na shiga Uka na bani,waiyo Allah Baba Kaka kazo ka taimake ni,Maman Yar Sokoto ki yi hakuri wallahi daga yau ba zan ƙara taba maki yarinya ba,kuma ina zuwa gida zan kawo maki kudin ki har gida ”
Kauda kai tayi”ka tabbatar sun zanu ta yanda gobe ko hanya ba zasu kara haɗawa ba da yarana”sannan ta ciro ɗari biyar ta mika ma Ogan NDC din,wanda su dama aikin su kenan hukunta yaran unguwa marasa ji.
Jan hannun yarta tayi suka wuce yayin da aka shigar dasu dakin horo.
Ba kajin komai sai kukan Salmu wacce akai wa bulala biyar a baya,sai Fiddo,yana daga bulala zai zuba mata,tsalle daya tayi sai gata makale a bayan shi,kamar dai ka goya yaro,ihu ta shiga yi kamar yana yanka ta,alhalin ita ke tsungulin shi,sai zagayen dakin yake da ita a baya,ga azabar mintsili ya ishe shi, da kyar ya samu ya banbarota a bayan shi,tana ganin haka ta kama hannun shi ta gatsara mai cizo,a tare kuma suka saki ihu,Ogan NDC din ne ya shigo”kai Yakubu baka da hankali ne, so kake ka kashe masu yara, kai kudi kuwuce gida ”
“Oga wallahi wannan yarinyar ba..
” Ya isa ba na son wata magana ”
Da gudu suka fita daga ofishin
“Oga ban samu na dake wannan farar ba,”
“Me yasa?
” Waiyo bayana, muguwar yarinya,wallahi Oga mintsili na tai tayi kslle in da ta cije ni”ya faɗa yana nuna mashi wurin.
“Ɗan Allah ja can ka bani wuri, ko kunya ba kaji wai ta cijeni, Wawa kawai” Ya ja tsaki ya fita.
Gaba ɗayansu kuka suke,yayin da suka nufi hanyar unguwar su,dama kuma ofishin yana bakin titin shiga unguwar su ne.
Kamar ance ta juya,ai kuwa sai hango Wasila ƙanwar Yar Sokoto tayi dauke da fanteka cike da tuwon shinkafa na tsiyarwa da kulan miya a hannun ta..
Share & Comment.
SARDAUNA
Story & Written
By
Jiddarh Umar
Sa ɗaukar wa ga masoyan FITILAR DARE,DA WATA TAFIYAR.
02
Da sauri ta share hawayen ta,ba tare da ta ce musu komai ba kawai sai gani suka yi ta koma ta hannun dama in da Wasila ke tafiyar ta,su dai tsayawa su kayi domin su ga me zata yi.
“Wasila ina zaki da ƙaton kwano akai?
” Tallan Tuwo zani ma na ”
Kallon kular da ke hannun ta tayi”miyar me nene?
“Zaki tsiya ne?
” Ki ka sani, kinga buɗe min gani kawai zan yi ”
Kamar zata ce wani abu sai kuma dai ta sauke Tuwon ta buɗe mata kular dan kawai ta gani ta bata hanya ta wuce,dan ta santa da kafiya.
Lafiyayyen miyar ganye ne wanda yasha Agushi,kafin ta ankara har ta ciko hannu da ƙasa ta juye mata a cikin kular miya,kafin wasila ta samu damar furta wata magana har ta riga ta “ki gaida Mamar Ƴar Sokoto ki ce mata itama ta fita harka ta ita da yaranta” Kafin su ankara har sun ne me ta sun rasa dan kamar wata walƙiya sai ganin tashin kuran takalmin ta suka yi,wanda suma suna ganin aika-aikan da tayi kuma ta gudu, nan suma suka cika ma bujen su iska yayin da suka baro Wasila na kunduma masu zagi tana kuka tana tsine ma Jan Madan.
Kamar wacce aka koro haka ta fado cikin gidan da gudu har tana cin karo da wani mutum wanda yake tsaye da Buta a hannun shi, sai ji yayi an bankade shi Butar ta fidi ruwan ciki ya zube,har ta wuce shi sai kuma ta dawo baya da sauri ta dauki Butar ta mika mai tana dan saisaita numfashin ta”barka da yamma Baba kaka ”
Leken ƙofar gida yake”wa ya biyo ki haka da har zaki shigowa gida ba tare da sallama ba?
In-in na ta fara dan tasan halinshi yanzun sai ya rufeta da faɗa “yauwa Baba kaka,ina wannan tsohuwar na gidan su Hanne?
” Maman Malam Inusa?
“Yauwa Baba kaka ita”
“To me ya same ta?
“Wai Allah ya mata rasuwa yanzun haka ko Zana’idarta ba a yiba”
“Innalillahi wa’inna’ilaihi rajiun,yi maza ki shiga gida sannan ki sanar da iyayen ki da su leka gidan idan sun idar da sallar magariba dan yanzun lokaci yayi”
Kaita kyada”to Baba Kaka”
Ganin ya wuce ne yasa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ƙarasa shiga cikin gida,da Mamar ta suka fara cin karo itama tana daura Alwala,
Dagowa tayi tana kallon ta tun daga sama har ƙasa,ganin haka ne yasa ta ce “Mama ina wuni ya aiki?
Idonta ne ya sauka a kan barkakken hijabin” Yau kuma ke da waye ki kayi faɗa ”
“Umm dama dama wata..
Daga bayan su taji ance” Mamana kin dawo”
Wani ɓoyayyen numfashi ta sauke dan tasan ko ba komai ta tsira dai yau”Ummu na dawo”
“To Alhandulillah,yanzun maza dauki Buta ki yi Alwallah lokaci yayi”
“Sister kina ganin yauma yanda yarinyar nan ta kara yin faɗa har ta barko sabon hijabin da ko sati biyu bai gama cikawa ba da aka din ƙoshin”
“Wannan ai ba abin damuwa bane tunda dama tun ba yau ba kin san Mamana duk sabon takar kaya bata taba kashe shi da kanta sai dai a barko shi wurin faɗa,ni dai da sauƙi tun da ban taɓa jin ta kawo min ƙarar wani ba”
“Amma ai sister ita kuma kullun cikin kawo karar ta ake”
“Sai mu bita da addu’a”
Fitowa daki tayi dan tuni har ta canza kaya “Ummu wai in ji Baba kaka wai in kun idar da sallah ku leka gidan Malam Inusa domin an ji rasu”
“Subhanallah waya rasu?
” Kaka, Mamar Baban su Hannatu?
“Kai Allah da girma yake, ni ko sister dazu fa naga tsohuwar nan,Allah sarki ashe ganin karshe zan mata”
“Dama haka rayuwar ya ke,Allah dai ya jikan ta”
“Da Amin suka amsa”
“To ku yi mu idar sai mu leka kafin mutane suyi yawa”
“To sister” cewar Mama wacce ta kammala Alwallah.
Su na idarwa suka fito,Mama ce ta leka dakin ta,a lokacin tana saman Darduma tana jan carbi”Zamu leka gidan rasuwar ki kula da gida”
Kai ta ɗaga mata alamun to,
Sake labulen tayi suka fita,kasancewar gida uku ne kawai a tsakanin su yasa nan danan sai gasu a ƙofar gidan,da sallamar suka shiga cikin gidan gaba ɗayansu da fuskar jimami,amsawa aka yi sannan aka basu izinin shigowa,
Sai dai fa suna shiga tsakar gidan turus suka tsaya sakamakon abin da suka gani,wanda ba komai bane face Kaka dake zaune saman Tabarma tana cin towa tare da ƴan jikokinta.
“A’a lale da matan malan,Bismillah ku karaso ku zauna” ta faɗa tana nuna masu wata tabarmar.
Mamace ta rike hannun Ummu da sauri,dan har ta fara jin cikin ta na duran ruwa,to ko dai Fatalwar Kaka ce ke musu magana, sai dai kuma gashi Matar Malam Inusa ta fito daki da kofin ruwa a hannunta ta ajiye a gaban Kaka”Mama ga ruwan nan”
Ganin dai da gaske ba su kadai bane suke ganin ta yasa suka sauke numfashi, ɗayan tabarmar suka zauna suna murmushin yake.
“Yau matan malan ne da kawo mana ziyar dare”cewar matar malan Inusa.
Ummu ce tai murmushin sannan tace” Eh dama kwanaki da kaka ta ɗanyi zazzabi ba mu samu damar shigowa ba,shi yasa muka ce bari dai yau mu leko ku”
“Ahh gaskiya kun kyauta Allah kuma ya biya ladan ziyara”
Basu wani jima a gidan ba suka musu sallamah suka wuce,har da kaka ta rakosu har kofar gida tana masu godiya.
Har suka isa gida ba wanda ya iya ce ma ɗan’uwan shi, dan Mama ba karamin takaicin abinda Jan Madan tai masu ta ji ba,shi yasa suna shiga gida kai tsaye dakinta ta tashi”yanzun kin kyauta kenan da zaki saka mu zuwa gaisuwar mutuwar mata alhalin mata da ranta da lafiyar ta”
Matsawa baya ta fara daga zaunen da take dan tasan halin Mama sarai tana iya kai mata bugu.
“Mama dan Allah dan Annabi ki yi hakuri kuskure aka samu”
Cikin masifa tace”kuskuren me?
“Dama wai cewa zan yi Kazar gidan su Kaka ta mutu,to shine garin sauri in faɗa sai na manta ban ambaci sunan Kaza ba sai sunan Kaka ya fito, shi yasa nace Kaka ta mutu”
Wani duka ta kai mata,kafin ya sauka a jikinta ta tsandara ihu”Ummu na,shi kenan na mutu a kai ni maƙabarta, La’ilaha’ilallahu”
Ji tayi an riƙe mata hannu “me haka zaki yi?
” Sister ki kyale ni in ma yarinyar nan dukan takaici, dan Allah ki dube ta,da zaran za a taɓata ba ta da aiki sai na kiran sunan Allah,kamar ta san shi,yanzun ki duba ki ga ace yarinya shekara koma sha biyar kuma wai a haka ta na babban makaranta University Two Hundred level amma ba ta da hankali ”
Ɓata fuska tayi”ya isa haka ba ta baki haƙuri ba, ai shi kenan,addu’a kawai zamu ci gaba da masu shi ne dai-dai”
Juyowa tayi wurin Jan Madan “ke kuma Mama na bana son irin haka,kuma babu kyau dan ya kama mutun ya dinga lura da abin da zai faɗa”
Kai ta kyada tana share guntun hawaye karyar data fara,dan a rayuwar ta ta tsane abin da zai taba mata lafiyar jikin ta.
Juyawa sukayi suka fita,yayinda suka ci karo da Malam Abubakar zaune saman tabarmar shi yaya sauraren labarai a ɗan ƙaramin rediyo shi, amma kuma duk abin da ya faru a kunne shi,domin shima kan haka yaje ya ma Malam Inusa gaisuwar mutuwar mahaifiyar shi,a nan yake shaida mai ai shikan yanzun ya barota gida kuma lafiyar ta kalau,nan ya tambaye shi ko a bakin wa ya ji, shi kuma tunda ya ji haka ya fahimci wato karya Fatima tamai, da fari ya so ya mata faɗa sosai akan haka,amma kuma sai ya kasance yana dawowa gida ya tadda iyayen ta mata na yi, shi yasa kawai ya haƙura,dan ba ya so ya kangarata da yawan faɗa,dama kuma shi ba mutum ba ne mai saurin duka, shi yasa kawai yake binta da addu’ar samun shiriya a ko da yaushe.
GOVERNMENT HOUSE MINNA.
Zaune yake yana jin labarai a gidan rediyo,in da yaji suna labarai akan wani hatsabibin yaro wanda har yanzun yan sanda sun kasa kamashi,abin sai ya zamana ma kamar ya raina yan sanda,haka kuma yaran shi wanda a ƙalla sun kai mutum talatin ba sa bari ko yaya ne yan sanda su taɓa shi.
A in da suke fadin dama ace Yan sanda zasu yi ƙoƙarin su kama shi da sun karya lagon waɗannan yaran.
Wayar shi dake ajiye a jefen shi ya ɗauka ya yi kira,
“Ina buƙatar ganin shugaban ƴan Sanda na jahar nan”
“To yallabai”
A jiye wayar yayi ya ci gaba da sauraron labarai.
Mintuna Ishirin sai gashi ana niman izinin shigowa,izini ya bada,wani dogon mutumi ne kakkaura ya shigo sanye da kayan ƴan sanda,Sara mai yayi”yallabai gani”
“Me yake faruwa ne a cikin gari?
” Yallabai komai na tafiya daidai ”
“Ka samu labarin abin da ya faru a wani unguwa me suna Darussalam kuwa?
” Eh yallabai?
“Wani mataki kuka dauka a kai?
Kame kame ya fara dan lamarin yaron abin tsoro ne” Yallabai muna nan muna shirya yanda zamu kama shi, dan wannan karon ba zamu mashi da sauƙi ba”
“Na baku nan da kwana uku ina son in ji labarin an kama SARDAUNA”
Sara mashi yayi “an gama ranka ya daɗe”
“Kana iya tafiya ”
________Darussalam
Bashi ya dawo gida ba sai ƙarfe Taran dare,kai tsaye ɗakin Baaba ya shiga da sallama,sai da aka amsa sannan ya shiga,har ƙasa ya tsugunna ya gaida ita,amsawa tayi cikin kulawa, ƙannen shi Nana da Nafisa ne suka gaishe shi,amma ko kallon su bai yi ba,
“Yaro ga abinci” Ta faɗa tana dauko mai kwanan abincin dake gefen ta,”Nafisa dauko ma yayanku kwanon wanke hannu ”
“To Baaba”
Gyara zama yayi,ya wanke hannu sannan ya buɗe kwanon,Tuwon Masara ne miyar danyen kuɓewa,Bismillah yayi sannan ya shiga ci cikin natsuwa,Nana ce ta kawo mai ruwa a kofi,sai da ya kammala sannan ya sha ruwa,
Juyowa yayi wurin Baaba”akwai abin da kuke buƙata ne?
“A’a yaro,babu komai”
“Kayan abinci fa?
” Akwai domin wanda ka kawo mana wancen satin bai kare ba har yanzun”
Kallon Nafisa yaye”ke yaya ne,naga sai wani kallo na kike ƙasa kasa,bayan kinsan bana son munafurci,dan haka fadamin menene kafin in karya ki”
Da sauri ta dawo kusa dashi cikin ladabi ta fara magana ” Yaya dama batun kuɗin makaranta ne,mun faɗa ma Baba shi ne yace shi bai da kuɗi tunda dama bashi ya saka mu makarantar ba”
“Amma ke kin cika munafukar yarinya,so kike ki zubar min da garmata a gidan ne da har zaki tambaye wannan tsohon kuɗin makaranta bayan ni na saka ku”
Tuni idonta ta ya kawo ruwa dan tasan ba karamin aikin shi bane ya kwasa mata Mari a gaban Baaba.
“Ka yi haƙuri Yaya ba zan ƙara ba”
“Nawa ne kuɗin?
” Dudu goma sha bakwai ”
“In Allah ya kaimu gobe da yamma zan baki”
Tare suka haɗa baki “mun gode yaya Sardauna”
Dubu uku ya ajiye ma Baaba,sannan ya mata sallama ya wuce,dan ka’ida ne sai yayi wanka kafin ya kwanta kuma zuwa ƙarfe goma yake kwanciya.
Name: | [Sardauna Hausa Novel Complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV
Gaskiya allah yakara basira