Sarkakiya Hausa Novel Complete
*SARƘAƘIYA*
NA
ABDUL-JANIT
*GARKUWA WRITTER’S ASSOCIATION*
{ _Marubuta masu garkuwa da alƙalami domin fadakar da al’ummah_}
BANYARDA WANI KO WATA SU CANZAMIN LABARI TA KOWACE SIGABA. SANNAN LABARINNAN MAI SUNA A SAMA LABARINE DATA KUNSHI, TSANTSAR SOYAYYA, KAUNA, CIN AMANA, SADAUKARWA, YARDA DA KADDARA, TAWAKKALI, HAKURI, JURIYA, SARKAKIYA, GAME DA BAN TAUSAYI.
Page 1️and2️
Bismillahirrahmanirrahim
*_Sunana faruq abota itace sanadin hadda suwar dukkannin abin da ya faru a Labarin rayuwata_* *_Duk da karfin abota alkawarin aminta yakan iya sauyawa wata rana, kamar yadda yafaru_*
*_Bawai abin a iya kaina bane ba, akoi wata rayuwa data shigo mana. nau’ikan rayuwar kala biyu ne, mafi girma acikinsu shine SOYAYYA_* _*cikakkiyar amincewa, sadau kantar da rayuwa, tare da bayar da farinciki.*_
*_Shin ya zuciya takeji alokacin da soyayyarta ta nisan ceta?_*
*_Shin ya zuciya takeji alokacin da wanda ta baiwa so ya kaurace ta?_*
N
Garin Taraba state, cikin Jalingo, shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, (2015) karfe biyar da minti sha biyar (5:15). Unguwar sabon gari cin-cirin don jama’a ne ke kewaye awani kofar gida suna kallon abin mamaki da al’ajabi.
Malam Dauda ke rike da akwatin trolley yana ja yana kururuwar wallahi sai Sumayya tabar mishi gida Mahaifiyar Sumayya Inna Rabi na riki da a kwatin Itama tana rokon sa da Allah karya raba ta da yar ta. Sumaiya baiwar Allah ko tsaye take a gefin su, tana riskar kuka gwanin ban tausayi abin duniya kap ya haɗu yamata yawa, ko uffan ta gagara furtawa, hawaye ne kawai ke shatata a kuncin ta haguda da dama, addu’a take aranta Allah ya ɗau ranta ko zata samu sauki ko sas’sauci daga ra daɗin da zuciyar ta ke mata. fincike akwatin Malam Dauda ya yi daga rikon da inna Rabi tamai yana wurgawa Sumayya shi, wanda silar hakan ya dawo da ita duniyar da yanzu ta ke ganin ta baki kirin.
Silar fisgewar da ya yi ne yasa inna Rabi faɗi kasa tana kuka mai cike da tausayi sheko faɗi yake.
“ki jeki duk inda zaki je amma ba gida na ba kuma wallah ko a hanya kika ganni karki nuna kin san ni yar iska kawai, ni zaki zubarwa mutunci, ya faɗa yana nuna kirjin shi, Malam Musa makwabcin Malam Dauda ne ya shigo layin nasu yaga dan dazon jama’a, ɗan sa Bala ne ya je wajan sa da gudu yana masa oyoyo nan yake tambayar sa meke faruwa yake faɗa mai cewa Anty Sumayya ce baban su ya kore ta saurin kara sawa wajan ya yi yana faɗin “Haba Malam Dauda me kake ai’kata wa haka da girman ka.