Hausa Novels

Sha’awar shi nake Hausa Novel Complete

Sha’awar shi nake Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

*SHA’AWAR SHI NAKE

 

*Zahra Surbajo*

 

 

*FREE BOOK*

 

_Bissimillahirrahmanirrahim_

 

*wannan labari ƙirƙirarrene,komai kaji yayi daidai da rayuwarka/ki arashine.*

 

 

 

*1*

 

 

Jannat Mus’ab ƊanMusa,Matashiya ƴar kimanin shekaru goma sha bakwai a duniya,

Fara ce me ɗan matsakaicin tsawo,tana da round face ɗauke da fararen idanu,cycle masu ɗan girma da take yawan lumshe su.se ɗan madaidaicin baki daya dace da fuskarta ɗauke da fararen haƙora,masu ratsin wushirya a tsakiyarsu,kumatunta ɗauke da dimple,kyaƙkyawace ajin farko,dan duk inda akeso mace takai jannat ɗanmusa takai.

 

Ƴa ce ga Attajirin ɗan kasuwannan Alhaji Mus’ab Ɗanmusa.ɗan asalin garin ɗanmusa dake jihar katsina,amma zama da yanayin kasuwancinsa ya maidashi kano da zama,a unguwar nasarawa GRA.

 

Alhaji Mus’ab ɗanmusa ya jima yana neman haihuwa Allah be bashi ba hakanne yasa yake ɗauko ƴaƴan ƴanuwansa yake riƙesu wasu har ya aurar dasu.

Bayan shekaru sun ja,shida matarsa,sika fawwalawa Allah lamuransu,inda aƙarshe ya amshi roƙonsu,ya basu haihuwa,inda suka haifo,jannat wacce tun daga kanta basu sake haihuwa ba,so da ƙauna da gata na gidan duniya ba wanda jannat bata ganiba,tun tasowarta zuwa girmanta.

 

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

Alhaji Musab yafi kowa gatantata,shiyasa komai tayi daidaine,duk meson ɓacin ransa ya taɓota, yanzu ze nuna ma kurenka kuma duk matsayinka agunsa ka taɓo jannat yanzu zaku saɓa

 

Wannan kenan.

 

“mamy yanzu a can australia ɗin wa ye ze dinga goyani,?”cewar jannat wacce ke goye a bayan mahaifiyarta kamar jinjira dan har da zani tasa ta ɗaureta a bayan.

 

Murmushi mamy tayi sannan tace”ay antynki zata dinga goyaki dan na faɗa mata bana son kisha wiya,”

 

“Anty muniba faɗa takemin kinga ko ay bazata goyani ba,kawai muje hutun tare mamy in dake bazatamin ba”cewar jannat cike da shagwaɓa.

 

“kwantar da hankalinki jannati na,Abbanki ya gargaɗeta kuma tace bazata takuraki ba” cewar mamy cikin nuna kulawa.

 

Haka hirar tasu taci gaba da wakana kan hutun da jannat zataje gun antyn ta Muniba ɗaya daga cikim ƴaƴan da Abbanta ya riƙa kuma ya aurar da ita ga abokinshi dake gudanar da harkokinsa acan ƙasar ta Australia Alhaji Bukar.

 

 

Muje zuwa

 

 

Surbajo for life.

1 Comment

Leave a Comment