Sha’awar shi nake Hausa Novel
Tag: SHA’AWAR SHI NAKE
*Zahra Surbajo*
*FREE BOOK*
_Bissimillahirrahmanirrahim_
*wannan labari ƙirƙirarrene,komai kaji yayi daidai da rayuwarka/ki arashine.*
*1*
Jannat Mus’ab ÆŠanMusa,Matashiya Æ´ar kimanin shekaru goma sha bakwai a duniya,
Fara ce me ɗan matsakaicin tsawo,tana da round face ɗauke da fararen idanu,cycle masu ɗan girma da take yawan lumshe su.se ɗan madaidaicin baki daya dace da fuskarta ɗauke da fararen haƙora,masu ratsin wushirya a tsakiyarsu,kumatunta ɗauke da dimple,kyaƙkyawace ajin farko,dan duk inda akeso mace takai jannat ɗanmusa takai.
Ƴa ce ga Attajirin É—an kasuwannan Alhaji Mus’ab ÆŠanmusa.É—an asalin garin É—anmusa dake jihar katsina,amma zama da yanayin kasuwancinsa ya maidashi kano da zama,a unguwar nasarawa GRA.
Alhaji Mus’ab É—anmusa ya jima yana neman haihuwa Allah be bashi ba hakanne yasa yake É—auko Æ´aÆ´an Æ´anuwansa yake riÆ™esu wasu har ya aurar dasu.Bayan shekaru sun ja,shida matarsa,sika fawwalawa Allah lamuransu,inda aÆ™arshe ya amshi roÆ™onsu,ya basu haihuwa,inda suka haifo,jannat wacce tun daga kanta basu sake haihuwa ba,so da Æ™auna da gata na gidan duniya ba wanda jannat bata ganiba,tun tasowarta zuwa girmanta.
Alhaji Musab yafi kowa gatantata,shiyasa komai tayi daidaine,duk meson ɓacin ransa ya taɓota, yanzu ze nuna ma kurenka kuma duk matsayinka agunsa ka taɓo jannat yanzu zaku saɓa
Wannan kenan.
“mamy yanzu a can australia É—in wa ye ze dinga goyani,?”cewar jannat wacce ke goye a bayan mahaifiyarta kamar jinjira dan har da zani tasa ta É—aureta a bayan.
Murmushi mamy tayi sannan tace”ay antynki zata dinga goyaki dan na faÉ—a mata bana son kisha wiya,”
“Anty muniba faÉ—a takemin kinga ko ay bazata goyani ba,kawai muje hutun tare mamy in dake bazatamin ba”cewar jannat cike da shagwaÉ“a.
“kwantar da hankalinki jannati na,Abbanki ya gargaÉ—eta kuma tace bazata takuraki ba” cewar mamy cikin nuna kulawa.
Haka hirar tasu taci gaba da wakana kan hutun da jannat zataje gun antyn ta Muniba ɗaya daga cikim ƴaƴan da Abbanta ya riƙa kuma ya aurar da ita ga abokinshi dake gudanar da harkokinsa acan ƙasar ta Australia Alhaji Bukar.
Muje zuwa
Surbajo for life.
*SHA’AWAR SHI NAKE*
*Zahra Surbajo*
*FREE BOOK*
*2*
“jirgin nasu na dare ne,pls muniba yazamana kina airport ze sauka,kinga bata taÉ“a zuwa ba se wannan lokacin”cewar daddyn jannat lokacin da suke waya da muniba kan tasowar jannat É—in yau.
“daddy karka damu insha Allahu zamu jira isowarta,karka damu game da hakan”muniba ta bashi amsa.
“ba damuwa yanzu zamu kaita airport”ya faÉ—i sannan ya kashe wayar ya juyo ya dubi mamy fuskarshi ba walwala yace.
“ji nake kamar zan rasa wani sashi na jikina,hajiya,ko kaÉ—an banson tafiyar yarinyar nan,dan de kawai kar suga na musu ba daidai bane yasa zan barta ta tafi”
“in banda abunka Alhaji sati biyu ne fa kawai zatayi kamar yau ne zaka ga ta dawo”cewar hajiya cikin sigar rarrashi.
Jannat ce ta fito sanye da riga da wando kanta ba kallabi se gashinta da ta É—aure da ribon ya sauka har gadon bayanta,bame kallonta ya É—auka bahaushiyace dan tafi kala da turawa,kyakkyawa ajin farko.
Cikin Takunta na burgewa ta iso gaban iyayen nata tace a shagwaÉ“e “dad time is going fa,kasan by 3 zanyi caching flight akwai buÆ™atar in isa airport yanzu”
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
Powered by: www.mynovels.com.ng
Ba musu suka miƙe su duka suka mara mata baya dan tuni komai nata ansa a mota.
Suna shiga mota,driver yaja suka fice zuwa airport,se hira suke a motar kamar karsu rabu.
Isowarsu tayi daidai da fara kiran fasinjoji,dan haka basu wani jima tare ba sukai sallama tana tafe,tana waigo su suna É—agawa juna hannu har ta É“ace musu.
Su daddy na nan tsaye jirgin su jannat ya tashi,sosai kewarta ta mamaye zuciyarsu da jikinsu,fatan sauka lafiya sukai mata,sannan suka dawo gida.
Haka suka isa gidan kowa jiki asanyaye na kewar jannat ɗin,wanda suka alaƙanta hakan da sabo.
Wayyo rayuwa,awanni biyu da tashin jirgin,ba tare da ansan musabbabin faruwar matsalar ba ya kama da wuta tun daga sama,har dirowarsa ƙasa.
inda ya faɗo a wani ƙaramin ƙauye,da ke yankin ƙasar ethopia,ya raunata mutane da dama mazauna ƙauyan.
Motocin agajin gaggawa ne suka iso gurin,inda akai ta ƙoƙarin kashe wutar,sede kafatanin jamaar dake cikin jirgin ba wanda ya fita da rai ciki ko harda jannat,
Se wata matashiya wacce baa cikin jirgin take ba,hatsarin ne ya rutsa da ita,bata mutu ba,sede ta ƙone sosai,itako jannat tuni rai yayi halinsa
Tashin hankali ba’a sa maka rana.
Surbajo for life
​
Name: | [My Novels (www.mynovels.com.ng)] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | June, 2022 |
Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe
Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…
Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram
Powered by: www.mynovels.com.ng