Shagalalliya
*Page 1*
Aguje ta isa dandalin matasan dattijan ta tsaya a kansu tana haki dafe da ƙirji, sai mayar da numfashi take yi ɗaya bayan ɗaya ta kasa magana, dukansu suka bita da kallo suna sauraren jiran jin abinda ya kawota, musamman dai shi kawunta da baya raba ɗaya biyu akan cewa wurinshi ta zo, ganin hakin ya ƙi barinta ne yasa ta faɗi zaune daɓas cikin ƙasa sannan ta ce.
“Kawu Mani Kandala ta ce in kiraka asiri rufe ka je ka ci kwaÉ—on garin kwak…”
Cikin sauri wanda ta kira da sunan kawu manin ya miƙe tsaye yana saka talkaminshi, zuciyarshi cike da jin haushin wannan tonon sililin da ta yi masa cikin abokan firarshi, ya fara tafiya ba tare da ya waigo ba ta ɗaga murya ta ce
“An gama yanzu yanzun nan ta ce ka je tun kafin ya yi ruwa ya lalace”
Mani kam ko waigowa bai yi ba ya ci gaba da tafiyarshi, wani daga cikin abokan firar ta shi ne ya kalleta a lalace ya ce
“Ke dai Bintoto an yi watsatsiyar yarinya, ke shi kenan ba zaki iya rufa asirin ba duk jan kunnen da aka yi maki akan ki kirashi asiri rufen?”
Bintoto ta miƙe tsaye tana kakkaɓe zanenta da ya ɓace da ƙasa ta ce
“To ai na faÉ—i nace masa asiri rufe ko baka ji ba ne kai?”
Ta ƙare maganar tare da murguɗa baki tare da ɗaukar wani dogon kare ta fara yin mota da shi tana gudu tana faɗin
“ziiiiiiiiiiih ba burki ba burki duk wanda na kaÉ—e yasin babu ruwana”
Haka take gudun da dogon karenta tana nanacin ba burki har ta ci karo da wani yaro da ke ɗauke da bokitin awararshi a kai, wanda fitowarshi kenan daga gida da nufin zuwa wurin talla, ai ko sai jin ƙarar faɗuwar bokitin na yi tare da tulin awararshi da cike fam da bokitin, da ba wani jinkiri ta watse gaba ɗaya ta baje cikin ƙasa, sai tsintar yaron na yi dafe da kai yana tsalle tare da ihun faɗin
“Wayyo ni awarata WALLAhi sai an biyani awarata”
Kafin ka ce me mutane sun fara taruwa wurin suna tambayar miye mafari?, Bintoto ta rike ƙugu tana kallon awarar da ke watse cikin ƙasa tana huci ta ce
“Kam buhun uban nan kai, me ka ke nufi? Lalle ma ni ce zan biyaka awarar?”
Yaron ya yo kanta ya ruƙunƙumeta yana ihun faɗin WALLAhi sai ta biyashi, Bintoto ko sai faman ƙwatar kanta take yi tana faɗin
“Tun farko ba sai da na gaya maka motar ba burki ba ka Æ™i, to ai yanzu sai in ga uban da zai sa a biyaka”
Ai ko dambe ya sarÆ™e tsakanin Bintoto da mai awara, mutane suka yi dafifi aka fara rabasu suna Æ™in bari, har sai da wani dattijo ya saka kare ya fara dukansu, sannan suka daina yunÆ™urin sake yin wani damben, daga nan aka fara tambayar ba’asi gano Bintoto ce bata da gaskiya, kai tsaye aka kwashe sauran awarar da ta rage, don tuni wata kam yara sun tsince an cinye sai kaÉ—an da aka bari, aka tasa Æ™eyarta sai gidansu da bokitin awarar da ta rage da mai awarar, da nufin akaiwa kakarta Æ™ara su biya tunda itace da laifi.
ÆŠanÉ—ano daga SHAGALLIYA
Daga Alƙalamin D/Auta
*Page 2*
Suna zuwa ƙofar gidan ta yi suruf ta faɗa cikin gidan tana faɗin
“WALLAhi Kandala Æ™arya su ke man ba ni ce na zubar da awarar ba…..”
Mutumin da ya raba faÉ—an ne ya bi bayanta da kallo cikin takaici, sannan ya fara rafka sallama wata bayan wata cikin É—aga murya, ai ko sai ga muryar Kandala ta nufo soron gidan tana sababin faÉ—a, don tafiya take yi tana gyara zanen da ke É—aure jikinta tana faÉ—in
“Sai na ga wanda zai sakani biyan awarar tunda an ce da kuÉ—in banza gareni, haka kawai a dinga É—orawa yarinya jarfa kullum ba za’a barta ta huta ba?, To ahir É—inku WALLAHI ALLAH kurwar Bintotona kur akanku, gane zaku ganta don ta ALLAH ba ta ku ba WALLAHi, awara kuma sai na ga wanda zai sakani biyanta a kaf faÉ—in garin nan na MAIDALA”
Ta ƙare maganar tare da kwance ƙullin goronta da ke gefen kallabinta ta gutsura, sannan ta mayar da shi a gefen zanenta ta ɗaure ta soke, tana tamnar goron tana ƙarewa kowa kallo ɗaya bayan ɗaya.
Mutumin baki a sake yake kallonta sannan cikin tausasa murya ya ce
“Inna kin ga yaron da ta zubarwa awara, zan wuce ne na ga suna rigimar shine na rabasu, kin ga bokitin fa gaba É—aya ta zubar ma sa da awara, saboda Allah hakan da ta yi kin ga ta kyauta?”
Ya ƙare maganar tare da nuna mata cikin bokitin awarar, in da sauran da ta rage ta yi buɗun buɗun da ƙasa.
Kandala ta bi bokitin da kallo a lalace sannan ta ce
“Ina ko zan ga rashin kyautawarta tun da ba a gabana aka yi ba?”
Ta juya gefenta ta riƙo hannun Bintoto da ke raɓe jikinta tana muzurai, ta fito da ita gaban mutumin ta ce
“Ki fito tsakiya ki tsaya tsaf ki yi bayanin abunda ya faru, tunda dai ba kasheki za’a yi ba don kin zubar da awara”
Bintoto ta fito gabanta ta tsaya tana muzurai tana hararar yaron sama da ƙasa sannan tace
“Kin san ALLAH kwarankwatsa dubu ta faÉ—o kan Malam Idi idan har ni ce na zubar da ita, wallahi ALLAH Kandala na fi son aradu ta faÉ—o maki, da dai ace in yi wannan ta’asar ai ke ma kin san ba zan aikata ba ko??”
*NA HADIZA D/AUTA*
*Page 3*
Kandala ta sakar mata wani wawan dundu a baya har sai da ta yi tsalle tare da fasa ƙara tana sosa wajen, Kandala tana kwaɗa mata jar harara tace
“Don ba ki da imani kike kiran aradu ta faÉ—o man?, To kafin ta faÉ—o man ke zata fara faÉ—owa a cikin kuÉ—in asusunki”
Ta kalli mai awarar ta ce
“Nawa ne kuÉ—in awararka”
Yaro ya washe baki tare da kai kallonshi ga awarar da ke cikin bokitin, ya fara ƙirgawa da baki sannan ya ɗago ya ce
“Ta É—ari biyar da sittin ce aka lissafa man kafin in fito, kuma tun da na fito ko É—aya ba’a saya ba, wannan kuma da ta rage ta É—ari da ashirin ce”
Kandala ta maka masa wata uwar harara ta ce
“KuÉ—inka aka ce ka faÉ—a ba wani lissafin banza ba, idan kuma kana so in barka da ita ne sai in koma ka riÆ™eta ta biyaka, da wani hancinka kamar an baje fankasu”
Yaron ya É“ata fuska yana gyara tsayuwarshi ya ce “To ai a cire É—ari da ashirin cikin É—ari biyar da sittin, sai a lissafa abunda ya rage a bani cikon kuÉ—in”
Kandala ta sake wurga masa wata hararar ta buga tsaki ta ce
“ÆŠanbantar uba idan ba ka iya lissafin ba to ka je Uwarka ta lissafo maka don ma ka samu za’a biyaka shine zaka yiwa mutanen É—ibar albarka?”
Ta juya da nufin komawa cikin gidan Malam Idi da ke tsaye ya yi saurin faÉ—in
“ÆŠari huÉ—u da arba’in ne kuÉ—inshi”
Ba tare da ta juyo ba tace “to ku jirani in kawo maku ai dama an ce É—an kuka mai jawa uwarshi jifa, to yau kam jifar akanta zata Æ™are don asusunta zan fasa in baku kuÉ—inku, gobe ma ta koma in taga dama”
Ai kuwa abunda bata sani ba tuni Bintoto ta É—auke asusunta ta sake masa maÉ“oya, shi yasa ta ci biÉ—a duk inda take sa rai bata gani ba, cikin É“acin rai ta fara faÉ—a tana Æ™wallawa Bintoton kira, Bintoto da ke bayinsu ta lafe tana jin sautin kiranta ta yi saurin haye yar guntuwar katangar bayin ta dira abunta, Kandala ta fito tana faman Æ™walla mata kira amman ko alamu babu na Bintoto a gidan, cikin Æ™unar rai ta kwance kuÉ—in da ke gefen zanenta, ta fara lissafawa tiryan tiryan har ta fitar da É—ari huÉ—u da arba’in, sannan ta mayar da sauran ta Æ™ulle ta nufi Æ™ofar gidan tana masifa, tana zuwa ta wurgawa yaron kuÉ—in bakinta yana kumfa ta ce
“Ga kuÉ—inka nan babbaÆ™un matsiyata waÉ—anda ba su san da Æ™addara ba”
Yaro ya duƙa ya ɗauki kuɗinshi ya cusa aljihu tare da ɗaukar bokitinshi ya bar ƙofar gidan, Kandala ta ɗaga murya tana faɗin
“Saura kuma gobe ka bari ta sake zubarwa WALLAhi Allah sai dai ayi abunda za’a yi amman kwandalata ba zata yi ciwon kai ba, miyagu azzalumai haka kawai ku kasa kula da kayanku sai anyi maku É“arna ku dami mutane da surutun banza, to gobe ma ka saki ta zubar WALLAhi sai dai Uwarki ta É—auki asarar baÆ™in munafukin banza da wasu kunnuwa kamar dangin zomaye”
Ta kalli sauran yaran da ke ƙofar gidan suna kallo tace
“Ku kuma duk wanda ya kalleni to ya kalli uwarshi yan hanyar uba”
Ta juya sai kumfan baki take yi har ta kai bakin ƙofar ɗakin matar ɗanta Mani ta fara bubbuga Kofar ɗakin tana faɗin
“Ke kam Kulu in ba ki rage wannan baÆ™in baccin naki ba, sai an saceki wata rana baki san anyi ba, mace sai kace kasa bata da aiki sai baccin tsiya, ta saki baki tana nasari kamar wacce za’a yanka, miyau suna zuba Æ™uda suna lasa”
Kulu ta fito tana goge yawun baccin da suka É“ata mata baki ta ja buta ta nufi bayi, Kandala ta bita da harara tare da guntun tsaki tana faÉ—in
“ALLAH wadaran naka ya lalace”
Ta kai ƙofar ɗakinta ta zauna kan tabarmar kabar da ke shinfide ta ce
“Ke ko Bintoto yau sai naga mai rabani da ke cikin gidan nan baÆ™ar almura, haka kawai kin janyo man asarar jikka biyu da murtala biyu ban ci ba ban sha ba”
Akafta