Hausa Novels

Shawarwari Ga Ma’aurata Kafin A Daura Muku Aure

Shawarwari Ga Ma’aurata Kafin A Daura Muku Aure:

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Daga Yusuf Shuaibu

 

Da farko dai yana da kyau a fahimci cewa daura aure yana nufin kulla wata alaka ce da Allah ya yi umarni da ita.

 

Gaskiya ne cewa aure ya kasance daga cikin dabi’u na dan’adam, to amma duk da hakan Allah ya tsarkake wannan alaka wacce daga karshe take haifar da abubuwa masu kyau. Don haka bai kamata a dauki wannan alaka a matsayin wani abu mara muhimmanci ba.

Gyara Nononki Domin Daukar Hankalin Maza

Dole ne ku yi iyakacin kokarinku wajen kare wannan sabuwar alaka, kamar yadda kuke kula da sabbin tsirran da kuka shuka don su girma su zama bishiyar da za ku yi amfana da ‘ya’yanta.

 

Babu shakka miji da mata suna son gidansu ya kasance wajen kwanciyar hankali da nitsuwa gare su bayan sun gama aikace-aikacensu na rana, wannan wata bukatuwa ce da ma’auratan suke bukatuwa da ita a rayuwarsu ta aure; suna bukatar farin ciki da yanayin da yake samar da hakan. Mai yiyuwa ne macen ko namijin su kasance ‘yan kasuwa, ko kuma ‘yan siyasa ko kuma suna zama ne a gida don tarbiyyantar da yara, kai ko ma dai wani irin aiki suke yi, dukkansu su kan gaji, to a lokacin da suka dawo gida, suna bukatar yanayin cikin gida mai faranta rai, wannan kuwa ba wata bukata ce ta wuce guri ba, a’a, a dabi’ance haka lamarin yake.

 

Hakika lamarin ba shi da alaka da abin hannun da mutum yake da shi, don kuwa akwai da dama daga cikin masu abin hannun da ba su dandani dadin zamantakewar aure ba; rayuwarsu ta kasance cikin kunci, cike take da hassada da haramtattun bukatu da fata. Babu shakka mutumin da ke da wani mukami, wanda yake ba da umarni, ya kan iya fuskantar matsaloli daban-daban a gida, mai yiyuwa ne shi wannan mutum ko kuma wannan matan ya/ta samu abokin zama mai saurin fushi mara hakuri ko kuma malalaci.

 

Don haka dukiya, mukami, zaman birni ko kauye ba za su canza yanayin zamantakewar iyalai ba matukar dai babu fahimtar juna da yafewa tsakanin ma’auratan biyu.

 

Abu na biyu da zan gaya muku shi ne, yana da kyau ku fahimci cewa wadannan abubuwa ba a samunsu haka kawai, wato ba sa samun mutum haka kawai, dole ne ku yi kokari wajen samar da su. Hanyar samar da su kuwa ita ce dukkan ma’auratan su so junansu. Kamar yadda ake cewa ne: “Ba a iya tabbatar da so da kauna ta hanyar karfi da tursasawa”, lalle haka ne don kuwa so kamar karamar bishiya ce, dole ne a ba ta ruwa da kula da ita, don haka duk wani abin da za ku yi wajen kula da girman wannan bishiya dole ne ku yi hakan wa kaunarku. Hakan kuwa yana hannayenku ne ya ku matasa. Hanyar da za ku bi wajen cimma wannan abu ita ce ta hanyar kauna da biyayya ga junanku da kuma nuna wa abokan zamanku hakikanin so da kulawa.

 

Babu makawa, kusan dukkan kiraye-kiraye da umarnin da Musulunci yake bayarwa dangane da sanya Hijabi yana yinsu ne, saboda kare wannan alaka ta aure. Don haka idan har, a matsayinku na matasan da za su yi aure, ba ku kula da hijab a lokacin da kuka fita waje, ko kuma kuka bari idanuwanku suka koma kan wasu matan ko kuma mazan, zukatanku suka koma ga wasu sabanin abokan zamanku na aure, idan kuka bari har kuka kulla alaka da wasu mata ko mazajen da ba naku ba wadanda kuke gamuwa da su a wajaje daban-daban, to babu makawa aurenku na iya shiga cikin mawuyacin hali. Da farko dai abokin zaman naku zai/za ta fara rasa irin sha’awar da ke jawo hankalinsa/ta zuwa gare ka/ta da ke haifar da so da tausasawa.

 

Wani abu kuma da yake da muhimmanci ku fahimta shi ne cewa babu wani mutum, namiji ne ko mace da ba shi da irin wadannan rauni da kura-kurai, babu wanda yake ya cika komai. Hakan ne ma ya sa za mu ga cewa dokokin Musulunci suna kokarin kiyaye alaka ne ta aure.

 

Hijabi ma don haka aka yi umarni da shi, don ka da mace ta bude jikinta ga wasu na daban, ka da ta shigo cikin mutane ba tare da suturan da ta dace da mutumci da girma ba, don ka da ta ta da hankulan wasu na daban, dukkan wadannan abubuwan janyo hankula an kiyaye su ga abokin zamanta mijinta.

Leave a Comment