Shi nake so Hausa Novel Complete

Shi nake so Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

SHI NAKE SO!!*

 

Littafin Karimatu Abdulhamid

( *MUMMYN MINAL*)

 

 

*HAMDALA WRITER’S ASSOC…..

 

 

BISSMILLAHIRRAHA’MANIRRAHIM

 

*DA SUNANKA ALLAH NAKE FARAWA YA ALLAH KAYI’DA’DIN TSIRA GA SHUGABANMU HABIBUNMU ANNABINMU MUHAMMAD SALALLAHU ALAIHI WASALLAM*

 

*YA ALLAH KAYI RIK’O DA YATSUN HANUNA WAJEN RUBUTA ALKAIRI, YA ALLAH KA HANENI DA YA’DA ALFASHA, ALLAH KASA YANDA NAFARA LITTAFIN NAN LAFIYA NA GAMASHI LAFIYA DANI DA MASU KARANTAWA*

 

 

*NA SADAUKAR DA LITTAFIN NAN GA MAKARANTAR ABDULLAHI BIN MAS’UD POTISKUM YOBE STATE*

 

*SAK’ON GAISUWA GAREKU K’AWAYEN MUTUNCI UMMU FA’DIMA💓 & UMMU MAHIR MISS GREEN💚*

 

PAGE 1&2

 

MUTTALA MUHAMMAD LAGOS AIRPORT.

 

Wani babban jirgine yake k’ok’arin sauk’a ababban filin jirgin muttala muhd, dake cikin garin Lagos State, da misalin 4:30pm mutane ne da dama suke jiran sauk’an wanan jirgin, ciki kuwa hardani Mummyn Minal ina tsaye a gefe rik’e da takarda ta da alk’alami na, domin d’auko muku rahoto, da mamakina bayan jirgin ya sauk’a kamar da minti biyu can sai aka bud’e k’ofar jirgin, mutanene suka fara fitowa ciki kuwa harda d’alibai maza da mata jikinsu sanye da fararen jallabiya maza biyu Mata uku wanda daga k’asar saudiya suke, daga gurin yin mussabak’a ajerin d’alibai mata ne da suke fitowa na hango wata kyakyawar budurwa me kimanin shekaru 18 sai fara’a takeyi. tana gama sauk’a daga matakalar benin ta ruga aguje domin taje gurin ‘yan uwanta kawai sai taji ta sunyi karo da mutum da k’arfi har sai da k’aramar jakar dake hanunta tafad’i k’asa.

 

‘Dago kanta tayi sai taga kanta kwance akan k’irjin wani kyakyawan saurayi hand some Man, da sauri taja da baya tana had’a hanayenta alamun ban hak’uri, shiko saurayin cikin takunsa na nutsuwa ya duk’a, k’asa domin ya d’auki jakarta ya bata, a daidai lokacin ne itama ta duk’a k’asa dan tad’au jakarta, shi yafara kai hanunsa kan jakar, itako batare da ta lura ba itama takai hanunta kawai sai taji tata’ba abu mai laushi kamar auduga, arazane tad’ago kanta, shima dai-dai lokacin ya d’ago idonsa, ai kuwa suka had’a ido take taji wani abu ya tsikareta tindaga kanta har zuwa babban d’an yatsan k’afarta.

Bata ankara ba taji anfisgeta tamik’e tsaye kyakyawan mari aka wanketa dashi sai ji kakeyi tas!

 

Da sauri wasu mutane mace da namiji suka iso gurin, namijin yaja hanun yarinyar yana cewa,

“Lafiya Wacece wanan FALAK ta mareki?

 

“You are very stupid”

Matar da tamari FALAK tace. Sanan taci gaba dacewa cikin harshen turanci banzayen mutane dabobi ku Hausawa nan kwata-kwata baku da hankali mutanen k’auye kawai masu datti”

 

wani irin takaici FALAK taji ya ziyarceta ita sai lokacin ma ta duba wacce ta mareta d’in wata matashiyar mace ta gani wanda a k’alla zatayi shekaru 32, jikinta da wata guntuwar riga iya gwiwa sai wani makeken belt a tsakiyar rigar wanda ya tsuketa, ga wani takalmi mai k’asan kwalba mai tsini sosai a k’afarta sai kanta da yasha uban attach har kukuminta, ga farcen k’ari ahanunta sunyi zak’o-zak’o sunsha uban fenti, da ka ganide kasan arniya ce, tsaki tayi sanan cikin harshen turanci tace ” kinyi sa’a daga k’asa mai tsarki na dawo da yau sai na nunamiki hausawa sunfi uwarki da ubanki da raja”

 

Ihu matar tayi danjin zafin abunda FALAK tace tayo kan FALAK, dake rik’e hanun yayanta, wata mata ce tataho da sauri,itama de daga ganinta kaga arniyar ta rik’e matashiyar dake k’ok’arin dukkan FALAK cikin harshen turanci tace.

“FATILISHA meke faruwa”?

“Mum wannan datti girl d’in ce marar hankali tataho a guje ta ture my lovely na, kuma haka bai isheta ba, har sai da ta kwanta akan k’irjinsa” FATILISHA tace cikin harshen turanci.

 

“What? Yarinyar Hausawa kwance ak’irjin d’ana tayaya hakan ya faru”?

Matar tatambaya.

“Yes Mum sbd iskancinsu mana”

 

Cikin fushi Mum ta dubi su FALAK tace ” kinsan waye shi da zaki bigeshi har ki kwanta a k’irjinsa to shine d’an gidan Ministan man Fetir, sbd haka sai kinsan dattin jikinki ya ta’ba na yarona”.

 

Shiko wanda ma ake fad’an danshi ya koma gefe yana tsaye ya zuba hanayensa a cikin aljihun suit d’in sa.

 

Shiko wanda yake rik’e da hanun FALAK cikin fishi yace ” amma wa’yanan mutanen basu da hankali su basu san kuskure ba kenan, ku wuce mutafi kawai”

 

Haba nan FATILISHA ta hau masifa akan maganar da yayan FALAK yayi da hausa dan acewarta wai ya zagesu, itako Mum d’in wayarta ta zaro acikin Pos ta fara k’ok’arin k’iran police. Wanda ake fad’an danshi ne ya tako ahankali cikin harshen turanci yace ” please Mum muje ga shican anfara k’iran masu zuwa deri Sallam.

 

Murza ya tsun hanunta Mum tayi a saitin FALAK suka bada k’ash-k’ash. Sanan tayi k’wafa tace ” oya DEVID muje” itama wanda aka k’ira da FATILISHA, wani mugun kallo tayiwa FALAK, sanan ta juya suka tafi.

 

 

Itako FALAK bayan wanan saurayin tabi da kallo, itako matar da suke tare dasu FALAK tsaki tayi mmttss sanan ta juya tatafi, shiko yayan FALAK janhanunta yayi yace ” me kike kallo ne FALAK, mutafi”.

Murmushi FALAK tayi sanan tace ” YA SAIFU Ni wa’yanan matan sunso su ‘batamin farin ciki na”

See also  Matar Yaro Hausa Novel 2021

Shiko YA SAIFU murmushi yayi sanan yace ” ai ni wasu k’abilun suna ban mamaki sufa wai adole basason ba Haushe”

Murmushi FALAK tayi daidai lokacin da suka iso bakin motarsu suka bud’e suka shiga tare da bissimillah, YA SAIFU kuwa mazaunin driver ya shiga yayinda matarsa ta zauna a kusa dashi, FALAK kuma ta shiga baya, bayan sun fita a airport d’in ne FALAK tace ” ai kuwa k’abilunan ba yanda suka iya damu duk bak’in cikinsu dole su barmu su k’ale”

Shide YA SAIFU Baice komai ba domin kuwa ya mayar da hankalinsa ga tuk’i.

 

Murmushin gefen baki matar YA SAIFU tayi sanan tace ” nifa banga laifin k’abilu ba dan sun tsani Hausawa domin kuwa wasu hausawan munafukaine”

 

FALAK kuwa murmushi tayi sanan tace ” Anti Sadiya kenan su kuma hausawan munafurcin me sukayi, na gade kema bahaushiyar ce, kuma ai ba yaran da ba mutane marasa kirki acikinsa,sbd haka kayi kishin yaranka ma yana da amfani”

 

“Tsaki Anti Sadiya tayi mmttss sanan ta mayar da kanta gefe tana kallon window d’in motar.

 

Shiko YA SAIFU kai tsaye a abakin get d’in gidansa dake cikin unguwar Siamese ya danna horn, security d’in dake gadin gidanne ya gwanle musu k’ofar gidan, YA SAIFU ya danna hancin motar cikin gidan.

A parking space dake cikin gidan YA SAIFU yayi parking, sanan yafito daga cikin motar, itama matarsa ta fito, Sanan FALAK, YA SAIFU ne yafarin cikin gidan, matarsa na biye dashi, itama FALAK tana biye dasu a baya, kai tsaye babban parlour d’in suka shiga tare da Sallama a bakinsu, Anti Sadiya sama ta haye, itako FALAK jakar hanunta ta ajiye a k’asa ta haukan kushin ta zauna, YA SAIFU kuwa har yahau kan upstairs ya fara tafiya sai kuma ya juyo yace ” FALAK d’auki jakarki ki biyoni”

FALAK kuwa d’aukar jakarta tayi tabi bayan YA SAIFU, suka haura saman, d’akunan bacci ne guda 3 awajen biyu ajere da juna sai kuma d’aya daga gefe yana kallon biyun, d’ayan YA SAIFU ya tura k’ofarsa ya bud’u ya dubi FALAK yace ” shiga ciki”

Shiga FALAK tayi tare da sallama, Shiko YA SAIFU k’ofar yaja mata, FALAK kuwa tana shiga d’akin ta cire kayan jikinta ta d’aura towel, ta shiga bed room ta watsa ruwa tare da d’aura alwala sanan tabud’e k’aramar jakarta tafito da wata bak’ar jallabiya mai kyau tasaka, dadduma ta shinfid’a tayi sallar azahar da la’asar, bayan ta idar da sallar ne tayi addu’oi ta shafa ta hau gado domin ta d’an huta, kafin mangariba tayi rintsa idonta tayi amma me sai taga fuskar matashin da ta bige a airport yana murmushi, bud’e idonta tayi da sauri tana tinanin wani abu, can kuma ta k’ara rintse idonta ha’ilau kuma sai taga sanda taduk’a zata d’au jakarta har ta d’aura hanunta akan na saurayin, sai kuma kwayar idonsa mai cike da haske take gani sanda suka had’a ido a airport, da sauri FALAK tabud’e idonta tace ” YA SALLAM!

Sanan tatashi ta zauna akan gadon amma duk da haka batade na kallon fuskar Saurayin ba, a cikin kwayar idanunta, tashi FALAK tayi tafara zage d’akin azuciyarta kuwa tana cewa ” wai meke shirin faruwa danine ni FALAK wanene wanan saurayin dake min gizo acikin k’wanyar kaina da idanuna? Wata zuciyar ce tace Mata “DEVID d’an gidan Ministan man Fetir, kamar yanda matar nan ta fad’a a airport, “YA SALLAM! FALAK tace. Tare da dafe k’irjinta, can kuma tafara tinanin ‘yan gidansu domin tasan suna can suna murnar dawowarta daga k’asa mai tsarki wato Saudiya, ita Allah-Allah take gari ya waye gobe taganta a Kano a cikin gidansu, tana cikin wanan tinanin taji k’iran sallar mangariba, bathroom takoma tayo alwala tayi sallar mangariba taita zikiri har aka k’ira isha’i.

 

Bayan ta iddar da sallar Isha’i ne taji anmata knocking, “Yes” tace.

Amma taji shiru ba a shigo ba, dan haka sai ta tashi ta nad’e daddumar ta ajiye tare da hijab d’in datayi sallar da shi mayafin jallabiyarta ta d’auka ta nad’e kanta dashi, sanan ta bud’e k’ofar ta fita amma bataga kowa ba, dan haka sauk’a tayi downstairs anan taga YA SAIFU da Anti Sadiya suna kan dining, YA SAIFU ne ya d’ago kai ya kalleta yace ” FALAK zomuyi dinner, k’arasa tayi ta zauna akusa da kujerar da Anti Sadiya take zaune, ta sunkuyar da kanta k’asa, shiko YA SAIFU tashi yayi ya d’auki flet da spoon ya ya zubawa FALAK pride rice Wanda Tasha k’oda da hanta tare da lemon kwa-kwa da dibino, sanan ya tura mata gabanta yace ” k’anwata maza ci abinci”

Itako Anti Sadiya mmmmmmttttttttsssssssssss taja dagon tsaki sanan tatashi tabar gurin cikin fushi.

 

Shiko YA SAIFU baki ya ta’be yace ” Allah ya kyauta” yaci gaba da cin abincinsa.

FALAK kuwa spoon ta d’auka tana jujuya abincin, acikin k’wanyar idonta kuwa fuskar mata shinan kawai take gani yana mata murmushi, to itama FALAK murmushin tafara yi, YA SAIFU ne yad’ago kai ya kalleta, ahankali yace ” FALAK”

Amma ina batasanma yana yi ba.

“FALAK” ya kuma k’iranta.

Amma duk abanza domin tayi nisa batajin k’ira.

Sai da ya tafa hanayensa biyu a setin fuskarta, sanan tadawo haiyacinta, YA SAIFU kuwa tsareta yayi da ido yace ” FALAK tinanin me kikeyi kina murmushi?”

Cikin inda-inda FALAK tace ” YA SAIFU ina ina tinanin ‘yan gidane”

“Kin tabbata”? YA SAIFU ya tambayeta.

“EH” tace tana duk’ar da kanta k’asa.

 

“Shikenan kici abinci kije ki kwanta gobe da safe idan Allah ya kaimu jirgin 8:00am za mubi zuwa Kano,dukkanmu zamu tafi har Sadiya, nima kuma akwai maganar da nakeso muyi da Mallam”

‘Dago kai FALAK tayi ta dubeshi, sai taga ya zuba mata kwayukan idonsa masu matuk’ar kwarjini, sunkuyar da kanta k’asa tayi, cikin sark’ewar murya tace ” Allah ya kaimu. Sanan taci abincin kad’an tatashi ta haye sama shiko YA SAIFU bin bayanta yayi da kallo yana k’issima wani abu aransa.

See also  Yar harka hausa novel

 

 

WAI WACECE FALAK WAYE KUMA YAYA SAIFU DA ANTI SADIYA?

 

kubiyoni domin jin sud’in su waye.

 

Ruwan sharhinku ne zaisa naci gaba da rubuta wanan daddad’an labarin.

 

 

DAN GIRMAN ALLAH IN KI/KA KARANTA KU TURA A SAURAN GROUP-GROUP NAGODE🙏

 

 

 

*MUMMYN MINAL CE*

Mai son farin cikin ku.

*SHI NAKE SO!!*

 

Littafin Karimatu Abdulhamid

( *Mummyn Minal*)

 

*Hamdala writer’s assoc….*

 

Marubiciyar

 

1: Auren Lagos

2: Wanijikiri Alkairi ne

3: Gimbiya Na’im

4: Idan zuciya ta gyaru

5:Samiha’yar mace

6: Ummul khairi

7: Gimbiya Kareemat

8: Nusaiba ‘yar Amana

9: Mijinki miji nane

10: Aishatu Humaira

11 Sarauta ko zalinci?

 

Page 3&4

 

A cikin garin kano akwai wata unguwa da ake k’ira kurna, kurna unguwace da masu hannu da shuni dama talakawa suke zaune acikin unguwar amma mafi akasari mazaunar unguwan masu k’aramin k’arfi ne, acikin unguwar Kurna akwai wani layi da ake k’iransa da babban layi, acikin babban layi akwai wani gida da’ake k’iran gidan da gidan Mallam Abashe, gidan Mallam Abashe babban family house da yake da sassa daban-daban, Mallam Abashe babban malamine na addinin musulunci da duk unguwar ta Kurna ansanshi, har ma da sauran unguwanni acikin garin kano da k’auyukanta duk sun sanshi, Mallam Abashe yana da ‘ya’ya da Almajirai, ‘ya’yan Mallam Abashe goma maza shidda mata hud’u sune kamar haka Baba isiyaku, Baba yusufa, Baba muntari, Baba Hashim, Baba idiris, Baba lirwanu, mata kuma da akwai Umma Safiya, Umma Mero, Umma jarku, Umma shatu, matan mallam Abashe uku matarsa ta fari itace Kaka Saude, yaranta hud’u maza uku mace daya, Bab Lirwanu da baba yusufa da baba hashim, sai umma Safiya, sai matarsa ta biyu Kaka Binta yaranta biyar Baba Isiyaku da Baba Idiris da Umma mero da Jarku, da Umma Shatu, sai ta uku Kaka Halima Wanda itace amarya kuma bayan ta haifi d’anta d’aya Muktar ta rasu tabar jariri, haka aka ci gaba da bawa yaron Nonon akuya har ya girma, domin sauran matan fir sunk’i shayar dashi domin kuwa suna matuk’ar kishi da uwarsa dan Mallam yafi sonta

Kaka Saude itace uwar gidan Mallam Abashe, Kuma kaka saude ‘yar tijara ce ta k’arshe sauran ki shiyoyinta duk tsoronta sukeji, kuma d’anta Baba Lirwanu shine babba acikin ‘ya’yan gidan, kuma dukkansu mazan gidan matayensu acikin gidan suke domin gidan babba unguwa guda ne

, kawai duk wanda zaiyi aure saide ya yanki fili yai gina iya adadin d’akin da yakeso, Baba Lirwanu Matansa biyu Inna Hansai da Inna Falmata ‘ya’yan sa kuwa sunkai goma, Inna Hansai Yaranta shidda akwai YA SAIFU da k’anansa maza uku, da mata biyu, Anti zuhuriya wanda take aure a cikin G.R.A, sai Nuriyya wanda yanzu shekarunta 18 Inna Falmata kuwa yaranta hud’u maza biyu mata biyu.

 

Haka Bahba isiya ku shima matansa biyu Inna Fatima da Inna Hadiza, yaransa goma sha biyu sanan baba yusufa shima matansa biyu, yaransa takwas maza da mata, sanan Bahba Idirs matansa biyu yaransa tara maza biyar mata, hud’u, sai Baba Hashim matansa uku yaransa Sha shidda yaransa, sai Baba Muntari matarsa d’aya Inna Salamatu, yaranta hud’u maza uku Abbas shine babba wato mesunan Mallam, sai Lirwanu muna kiransa Abba, sai Musa, sai auta FALAK.

Haka yaran mallam Abashe mata suma duk suna da ‘ya’ya daga me goma sai me sama da haka, sai me k’asa da haka, kai jikokin Mallam Abashe sunfi hamsin. Yaransa kuwa duk cikin su bawanda yayi gadon malintarsa domin kuwa shi Baba Lirwanu sana’arsa ita ce sai da kayan gwari, wasu de gyaran mota, baba isiyaku kuwa tela ne shi yake d’in kawa alhazan unguwar kayansu me k’aramin k’arfi acikin su shine Baba Muntari domin kuwa sana’arsa itace facin tayar keke. A tak’aice de kaf gidan bamai arzik’i, haka ko wani shashi na gidan suke malejin ratuwarsu matan mallam kusa basa girki saide idan duk matar da tadafa zata zuba a kwano mai kyau akai shashin mallam.

 

Mallam Abashe yaso ko da acikin jikokinsa ne wani yayi gadonsa na malinta tinda iyayensu ba wanda yayi, sanan Mallam kaf acikin jikokinsa yafison YA SAIFU, shi yasa tin YA SAIFU yana k’arami mallam yake koyar dashi karatu da kansa, amma da Ya Saifu ya girma sai ya nuna baya ra’ayin malinta, da yake yayi karatun boko, wani Alhajine daga cikin almajiran da Mallam ya koyar, ya samarwa YA SAIFU aiki a wani babban company dake garin Lagos.

 

YA SAIFU shi d’an Baba Lirwanu shine d’ansa na miji Babba, kuma duk yagirmi jikokin gidan maza, kawai Umma shatu da Umma Safiya ne, suka girmeshi, YA SAIFU ya taso yarone nitsattse bashi da rawar kai gashi da ilimin boko dana addini, gashi kyakyawan gaye hausa Fulani, YA SAIFU yasha gwaramar rayuwa domin a lokacin da ya nuna yana so yayi karatun boko duk iyayensa k’in yarda sukayi, kasancewar gidan Mallamai ne basa karatun boko sai na Allo, Ko da YA SAIFU yafad’wa Baba Muntari, yana son shiga makarantar boko, Baba Muntari bai musaba ya kama hanun YA SAIFU ya kaishi, ya masa komai ya siyamasa yunufon kuma kullum idan YA SAIFU zai tafi sai yabiya gurin Baba Muntari ya bashi kud’in Tara, har de Mallam yasan YA SAIFU yana zuwa makarantar boko yaita fad’a amma Baba Muntari yabawa Mallam hak’uri yace laifinsa ne domin shi ya kaishi, shiko Baba Lirwanu ba ruwansa baiyi magana ba.

 

Inna Hansai kuwa da tasamu labari haka taitataki har shashin Baba Muntari taci mar mutunci wai akan me bakai d’ansa Abbas ba sai d’anta wato yakeso ya lalace ya zama d’an iska ya kasa moruwa to ita wlh tafi k’arfinsa, haka de Inna Hansai taita jaraba, shiko Baba Muntari ya sunkuyar da kansa k’asa bai kulata ba, kasancewar ta matar babban wansu, Inna Salamatu ce a lokacin tana da tsohon cikin Musa tace ” dan Allah Yaya kiyi hak’uri mude bama fatan SAIFUDEEN ya lalace idan yayi karatunan dukka zuri’ar nan kowa zaiji dad’in karatuns………………… “Yi min shiru sallamamiya to wlh zuri’a ta tafi k’arfinku akan me baku kai mesunan Mallam da Abba makarantar ya hudawanba sai d’ana sbd kana bak’in cikin kai d’aya mahaifiyarka ta haifa ta mutu, shine zaka nemi ka ‘bata mana zuri’a ko? To a hird’inku, haka Inna Hansai taita jaraba har Kaka Saude tajiyota itama tagarzayo shashin suka had’u suka ciwa Baba Muntari mutunci harda masa gorin yafi kowa mutunci, shide ficewa yayi yabar musu gidan Kaka Saude kuwa harda zungurin k’eyarsa, Salamatu kuwa da yaranta sai kuka sukeyi, Baba Lirwanu ne ya dawo daga kasuwa zai wuce shashinsa ya jiyo jarabar uwarsa da matarsa, ai kuwa ya kwad’awa matarsa k’ira yace ” kuma wlh idan baki fito ba, har nabar gurinan to abakin aurenki”

See also  Do I still get Child Benefit if I move abroad?

 

Hakan da Inna Hansai taji ne yasa ta tabar shashin, itama kaka saude tabi bayanta, Inna Hansai kuwa suna zuwa shashin su Baba Lirwanu ya rufeta da fad’a yace muddin ta k’ara shiga shashin Muntari da sunan fad’a abakin aurenta, hohoho wanan magamar tayiwa Inna Hansai zafi ranar kwana tayi a gidan tana tijara, haka de rayuwar gidan ta kasance kowa tashi ta fisheshi da dad’i da badad’i wata rana ma shashin Baba Muntari haka za’a wuni ba aciba, amma haka Kaka Saude zatazo taita zaginsu wai kowa ya kaimata abinci banda su sbd sunfi kowa talauci, domin kuwa ita tana ganin Muntari bak’ar k’afar uwarsa ya d’auko, haka Baba Muntari zai ringa kwalla domin zagin da Kaka Saude take masa yana masa zafi, gashi bayason yasanar da Baba Mallam domin kuwa ya tsufa Sosai ko tafiya bai iyayi. Sanan ba yaso ya fad’awa yayansu Lirwanu dan gudun fatina.

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
 

Haka de rayuwa taci gaba da tafiya yau dad’i gobe mad’aci har YA SAIFU yagama primary ya tafi secondary ta maza ta kwana da take dala, kuma bako sisin iyayensa duk Baba Muntari ne yake hidima da karatunsa, wata rana in anemi abu amakarantar haka iyalen Baba Muntari zasu kwana da yunwa domin kuwa duk abunda ke jikin Baba Muntari haka zai biyawa YA SAIFU buk’atar makarantar sa, ‘yan gidan kuwa Mata da yaransu ba irin zagin da basawa Baba Muntari wai mugune bekai ‘ya’yan makarantaba sai YA SAIFU sbd mugunta kai har Baba Mallam sai da ya sanjawa Baba Muntari haka de rayuwa tai ta kayawa, har YA SAIFU ya gama secondary ya dawo gida zaman jiran saka mako alokacin inna Hansai tana da cikin, itama Inna Salamatu tana da ciki, ga yara k’anana ga talauci dan haka YA SAIFU yaji yana tausayinsu dan haka yake shiga shashin su Baba muntari yake taya Inna Salamatu aiki kamar iban ruwa a rijiya da wankin kayan su Abba, haka Inna Salamatu zatai ta masa godiya tana sama sa Albarka, da fari de ranta bayason aiyukan da yake tayata sbd tijarar mahaifiyarsa, amma da taga SAIFU baida niyar bari ai kuwa takyaleshi nan YA SAIFU da Inna Salamatu suka d’inke ta zama uwar d’akinsa, duk wani kayansa mai kyau da ‘yan kud’ad’ensa ita yake bawa ajiya, Itako Inna Salamatu har tsokanarsa takeyi tana cewa SAIFU inde na haifi mace to matarka ce kai zan bawa ita, shiko SAIFU sai yayi murmushi yace ai Inna Salamatu Allah yasa cikin nan ki haifi mace kinga dama baki da ‘ya mace idan kinsamu zan sangartata da ado iri-iri

Inna tayi dariya tace Allah ko SAIFU? A lalle kana son matar nan taka da zan kawo maka, haka de rayuwa taci gaba da tafiya, YA SAIFU sosai yake taimakawa Inna, YA SAIFU sbd yana jin tausayinta ita da mijinta domin a gidan anrenasu ko dan aga Baba muntari baida d’an uwa da suka fito ciki d’aya ne oho.

Ai kuwa da Inna Hansai tasamu labarin aiyukan da SAIFU yake taya Inna Salamatu, hohoho ina wuta tasaka shi, nan taringa bala’i da zage-zage a gidan wuni tayi tana abu d’aya ‘yan ziga kuwa suna zugata, itade Inna Salamatu tana jiyosu a farfadar gidan, amma tak’i fitowa bare ta tanka, haka Innar su SAIFU taita jaraba wai ita wlh bata haifawa ko wacce shegiya d’a ba sbd haka a kyale mata yaronta, haka taita jaraba har Baba Lirwanu ya shigo gidan, bai kulata ba yai wucewarsa ciki, bin bayansa tayi da yake tasan halinsa, tana zuwa tace ” sannu da zuwa Baban yara”

Cikin masifa Baba Lirwanu yace ” ki rik’e sannunki bana so, wlh Hansai kin isheni Tabbas kin kusa k’arawa gaba, ai ga abokiyar zamanki nan Falmata ba a ta’ba jinta da kowa ba sai ke a yagi.

 

Cikin masifa Inna Hansai tace ” nayi masifar, Lirwanu nace nayi masifar ni shegiyace da zan haifi d’a inbari wasu sugaje kuma kace bazanyi magana ba, k’arya kenan wlh, awani dalilin za su ringa morarmin yaro? Sun tayani na k’udarsane”?

 

Tas! Baba Lirwanu ya wanke Inna Hansai da mari cikin ‘bacin rai yace na kula ke shed’aniya ce Hansai to mu gidanmu gidan Masu ilimi ne ba gidan shed’anu ba sbd haka kije na katse igiyar aurena d’aya da ke kanki” fuuuu Baba Lirwanu ya fice yabar gidan ransa a ‘bace, ihu Inna Hansai tasaka tace ” wlh k’arya ne da girmana da tsohon cikina ka rangad’amin saki tabbas kataro jaraba da bala’i ita kuma Salamatu sai naci abu takazar………..

 

Niko Mummyn Minal nace ASSTAGAFIRULLAH

 

To fa ran manyan mata ya ‘baci fans sai ku kawo agaji a Inna Hansai.

 

Gaskiya idan banga zazafan comment ba sai nayi Sati d’aya banyi muku ci gaba ba.

 

 

 

Dan girman Allah in kin/ka karanta ku watsawa sauran GROUP nagode.

 

 

 

Mummyn Minal ce

Mai son farin cikin ku

 



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

​

 

 

Name: [ Shi nake so Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top