Shi ya dace da ni Hausa Novel
*SHI YA DACE DANI*
_Na Maman afrayh Ik_
~Editing by Mugirat Musa.~
_Da sunan Allah mai rahama mai jink’ai._
_Wannan labarin k’agaggen labari ne,duk wanda wannan littafin yayi kamanceceniya da labarin rayuwarsa to yayi hak’uri,ban rubuta wannan littafi don in ci zarafin kowa ba nayi ne domin in k’ayatar da masoyanah._
*PAGE* 1️⃣
Wata yarinyace ‘yar kimanin shekara ishirin da d’aya zuwa da biyu ce, tafe da cemarah ahannunta tana d’aukar picture a wani gidan tarihi,da yake ba ita kad’ai bace ba,kuma gurin ba kowa daga ita sai k’anwarta da k’awayenta guda hud’u duk abokanin aikinta ne su,suna cikin motar da suka zo sai motar gidansu wadda ke d’auke da k’anwarta da direbansu,tana ciki ko tsoro bata ji da yake gun da ta shiga babu motsin kowa.Su kuma da suke ta jiran ta fito sai suka ja motar suka wuce su kace ga direbansu nan shi ya wuce da ita,su suna da gun da suke son zuwa ba kowane k’awayen nata ba illah Safara’u,Zainab,da Hadiza sai kuma namiji d’aya mai suna Suleiman suna kiransa da Sulem,bayansu Sulem sun wuce suma direban nasu ya bisu baya acewar k’anwarta Zulaihat don ita duk d’aukarta ko zatonta suna tare da yayar tata mai suna Merah,ta zata tare ta wuce da k’awayenta shiyasa bata bi ta kanta ba,gashi itama ta kirata don ta zo nan su wuce tare tayi tafiyarta,gashi tabar waya da jakarta a motar tasu,bayan sun jera tare sun wuce da mota ita kuwa Merah koda ta fito ta bud’e k’ofa sai ta jita rufe,gashi kuma ba waya ahannunta tana nan tana tunanin mafita,sai kawai ta yanke shawarar tabi wata k’ofar data gani a bud’e ko nan ma hanyar fita daga gidan ce,domin gida ne babba mai d’umbin tarihi na shekarun baya aru aru,abinda yasa taji k’ofar rufe shi maigadin gidan ya zata kowa ya fita,don yaga wucewar mototi har biyu kuma yaga su ya bud’ewa get d’in gurin suka shigo,bayansu ba wanda ya sake shigowa shiyasah bai yi tunanin da wata ciki ba ya rufe ya wuce.
Wani k’yak’k’yawan saurayi na hango zaune cikin jirgin sama rik’e da computers ahannunsa, yana dudduba dukkanin wad’anda sukayi shige da ficen ziyartar gidan tarihi, ba wani abu yake dubawa ba bayan picture d’in Merah da yayiwa computer tasa gurbi ya tsura mata ido yanata kallon hotonta kamar ya samu madubi,ya matsu jirgin ya sauka yaje gun Merah,shi saurayin nan k’yak’k’yawan gaske ba kowa bane face Hisham, wanda iyayensa suka saka masa Hashim,dayake sunan kakansa ne suka saka mashi shiyasah suka maida shi Hisham.
Merah kuwa duk ta firgice don tasan mahaifanta sai sun shiga damuwar rashin dawowarta gida da wuri,gashi komai dad’ewarta awaje bata wuce k’arfe biyar ta koma gida ko shi biyar d’in da take kaiwa don yanayin aikinsu ne ke sata kai wannan lokacin…………………….
_Ko ya zata kaya da Merah ta samu hanyar fitowa,?Ku cigaba da kasancewa dani Maman Afrah Ik domin jin yadda k’ayataccen labarin nan zai kasance a gaba._
_Comment’s and Shares._
Leave a Comment