Hausa Novels

Shimfidar Aurena Complete Hausa Novel

Shimfidar Aurena Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Shimfidar aurena

“Prince ya kamata kayi wani abu akan lamarinnan,yin shurunka ne fa ke Ƙara haifar da tarin matsaloli acikin gidan nan,me martaba kanshi in yaji bazeji daɗi ba in baka ɗauki mataki ba”cewar Sadeeq

Wanda aka kira da prince gyara zamanshi yayi sannan ya lumshe ido,gami da taɓe baki,alamun abun be dameshi ba.

Sadeeq bin shi yayi da kallo,baki buɗe,dama yasan baze yi magana ba dan inda sabo ya saba da halayensa.cikin girmamawa yaci gaba da faɗin.

“Bayyanar video na tsiraicinka ranka ya daɗe abune da masarautarnan bazata iya kare zubewar mutuncinka ba,ya kamata ka duba batunnan”sadeeq ya sake faɗi cikin damuwa.

Har yanzu idonsa a lumshe suke,bashi da niyyar buɗesu,hakanne yasa sadeeq ya fahimci bazeyi magana ba yanzu,dole tasa sadeeq miƙewa yay masa sallama sannan ya fice daga falon.

Ba tare da damuwar komai ba ya gyara zamansa ya ɗauko remote ya sauya tashar da yakeson kalla,be jima ba ya miƙe cikin takun isa da ƙasaita yabar falon,yana tafiya kamar wanda aka yiwa dole.

Ƙofar da zata sadashi da ɓangaren mahaifiyarsa ya nufa,fadawa da bayin gida se zubewa suke ƙasa suna masa kirari,har ya shige ƙofar.

Koda ya shiga bata falon ƙasan,dan haka taka stairs yayi zuwa sama inda yasan ze sameta,ilai kuwa yana shiga yaganta kishingiɗe,ana matsa mata ƙafa,yayin da jakadiya ke gefenta tana bata labarai masu daɗi.

Sallama yayi ya shiga,suna ganinshi jakadiya da ɗayar matar dake matsamata ƙafar suka zube suna miƙo gaisuwa gareshi,ganin mahaifiyarshi na gurinne yasa ya amsa a daƙile sannan ya zube agaban mahaifiyar tashi yace”barka da hutawa mami”ya faɗi cikin wani daddaɗan sauti.
Miƙewa zaune tayi fuskarta ɗauke da fara’a tace “Aliyu hydara na kaine da rana haka?”

Shuru yayi bece komaiba,sema samun guri da yayi ya zauna,ita ta haifi abunta dan haka tasan halin kayanta.dan haka dubanta takai gun jakadiyya tace”ku ɗan bamu guri,zan gana da yarima”

Ba musu suka rusuna alamar girmamawa sannan suka fice daga falon.

Suna fita ya rarrafa ya isa gareta,ya kwantar da kanshi a cinyarta,yafara magana kamar ƙaramin yaro cike da shagwaɓa,”mami don Allah kisa baki Abbana ya barni in tafi Swizland ɗinnan,bada wasa nake ba na gaji da zama anan please mami”ya ƙarasa maganar cikin magiya yana jijjiga hannunta.

“Wai Hydar so nawa kakeso a faɗa maka ne,Abban ka yace bazaka koma ba,so yake ka fahimci shaanin mulki da kyau sabida kaine magajinsa,meyasa bazaka masa biyayya bane Hydar?”mami tayi maganar tana shafa gashin kanshi dake kwance lub kamar na larabawa.

Karanta Gidan Aurena 

Miƙewa zaune yayi ya tattaro dukkan natsuwarshi sannan yace”mami ke mahaifiyatace,nasan dole kinason farinciki na,kuma duk wani abu daze taɓa mutuncina bazaki so shi ba”

“wannan hakane Aliyu na”mami ta bashi amsa.

Ajiyar zuciya yayi sannan yaci gaba da faɗin”Mami wata ƙaddara ta faɗo min,ni ba mazinaci bane mami amma se ga wani video an turomin shi ni ɗin a tsirara tare da wata yarinya wacce ko saninta banyi ba,ana barazanar sakin videon a cikin masarautarnan”ya ƙarasa maganar cikin yanayin dake nuna ɓacin rai.

A zabure mami tasa hannunta akan bakinshi ta toshe masa baki wasu siraran hawaye na biyo idonta.

Rungumeta Aliyu yayi,ya saki wani kuka,wanda tunda abun ya faru be taɓa nunawa kowa ya dameshi ba,amma sosai abun ya ɗaga hankalinshi matuƙa,gaba ɗaya kanshi a kulle yake.se yanzu daya iso gaban mahaifiyarshi ne yasamu kukan yazo masa.

Hannunshi taja suka bar falon suka koma ɗakinta,kan gado ta zaunar dashi sannan ta kulle ƙofar,ta zuge glasan window,ruwa ta ɗebo masa a dispenser me sanyi ta bashi yasha,ya ɗan numfasa sannan tace cikin rauni.

“Tunda mahaifinka ya bayyana ka a matsayin mejiran gado Hydar nasan ƙalubalen rayuwane zasui ta tunkaroka,wanda sede ƙarfin addua ne kawai ze warware duk wata matsala,na yarda da tarbiyyar da nai maka Aliyu,ka ɗauki komai muƙaddarine daga Allah kuma ze wuce”ta faɗi tana shafa kanshi.

“Mami inaso ne na binciko koma waye yay min hakan,shine yasa nakeson zuwa can ɗin dan abun zefi sirri”ya faɗi yana ƙoƙarin kauda damuwarshi,dan yasan inde yashiga damuwa mahaifiyarshi na shiga wacce tafi tashi,kasancewar shi kaɗai Allah ya bata.

“kabar komai a hannun Allah zeyi magani,kabar batun tafiyar tukuna muga me ze faru”mami ta faɗi cikin ƙarfafa masa guiwa.

Dole ya bar batun tafiyar,ya ɗan zauna agunta ta gama yimasa nasiha da adduoi,sannan yay mata sallama ya tafi,koda ya baro gurinta babu me cewa shine yay kuka yanzu sabida ya dawo yarima hydar ɗinsa me cikar isa da ƙasaita.

Muje zuwa

Surbajo for life.

 

 

 

Name: [SHIMFIDAR AURENA HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


4 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!